Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ga ni amma babu shi, yanayin fuskarta ne ya sauya alamar rashin jin dadi.

" Shin ina ne kuma inda yaje shi " ta faɗi haka a zuciyarta.

Taɓa kafadar ta aka yi ta baya, juyowa tayi dan ganin waye, suman tsaye tayi lokacin da ta haɗa ido da wanda ke tsaye a gabanta.

" Wacece ke,kuma daga ina ki ke!?" Wannan sune abinda ta ji ya furta da muryar sa me dadin sauraro,satan kallon sa tayi taga yanda ya zuba mata ido hannun sa na zube cikin aljihun wandon sa.Jikinsa babu riga se lafiyayyar karfaffan jikinsa da yaci karfe,idonta ya sauka.

Sosa wuyanta tayi dan ji tayi wani irin kunya ya lullube ta,bata taɓa tunanin wannan ranan ze zo ba, ga shi yau ya kamata dumu-dumu tana lekensa.


" Bazakiyi magana ba?,ko de kurma ce ke?, ɓalle ma na san ke din ba kurma bace".
Ya faɗa yana kuma kafeta da idanunsa da suke da masifar haske.

Cikin inda-inda ta soma cewa " uhm_dama nazo wucewa ne na ganku kuna motsa jiki shine na tsaya ina kallon ku shi-shi-shi-kenan". Ta gama maganar gaba daya a daburce domin bakaramin gwarjini ya mata ba,jinta tayi kamar wacce a kace ta yi wani babban zunubi se ta ji kamar idanunsan suna nukurkusan sassan jikin ta.


Se da ya gama nazartan ta kafin ya ce

" Yau kwana goma sha uku kina zuwa nan wajen, lokacin da ki ka fi zuwa domin kin san kin fi ganina a irin wannan lokacin shine karfe ɗaya na rana,da kuma yammaci idan rana ya ɓace, shin kina da matsala da ni ne !?".


Cike da jin kunya ta ce " ka yi hakuri,nasan na aikata kuskure,ya kasance kana matuƙar burge ni ne yasa ko da yaushe nake kaɗaicewa a wannan karkashin bishiyar domin ganin ka".


Dariya ya yi wanda ya sake bayyana kyawun sa,sosai take kallon chocolate color face din sa yanda yake dariyar bakaramin tafiya da imaninta ya yi ba,a ranta ta furta

" Ya Salam,dama yana dariya haka, tabbas wannan bawa naka yanada tsananin kyawun da ya tafi da zuciyar Muzna Taifur Rahman".


" Shikenan nagode da burgeki da nake yi,ke din wacece domin ban taɓa kallon ki a wannan masarautar ba,sannan kuma abu na gaba ki rufa min asiri ki dena zuwa nan dan kar a ɗinga ganin ki saboda akwai banbanci sosai a tsakanin yar masu hannu da shuni da kuma ya'yan bayi".


" Sunana Muzna ".

" Ni kuma sunana Zubair amma an fi kirana da Sadauki Zubair".
Ya faɗa yana gyara tsayuwar sa.

" Ka cancanci sunan ".

Kawar da zancen nata ya yi ta hanyar faɗin " se de baki faɗa min ke din wacece ba,domin bana son wani abu ya biyo baya,ko da wasa bana son wani alaka ta haɗa ni da ya'yan manya".

" Saboda me yasa hakan!?". Ta tambaye sa cikin rashin jin dadi.


" Saboda a ko da yaushe kan su suka sani,ni kuma na tsani mutum me son kansa,na tsani mutum makaryaci da kuma mayaudari.bugu da ƙari ni din bawa ne, ɗan baiwa,ina iya kokarina wajen ganin na kare mutuncina".

Jikinta ne ya yi sanyi domin tasan muddin yasan ita din wacece tofa dole ze ja baya da ita,hakan yasa ta yanke hukuncin boye masa ko ita din wacece.


" Ni ba yar kowa bace hasalima ma ni baiwa ce a wannan masarauta ".

Cikin tuhuma yake kallon tufafin jikinta da yasan ko rigar da take sanye da shi ze iya ciyar dashi na tsawon shekaru uku saboda tsadar sa, fahimta da ta yi be yarda ba, saboda yanda ya ga tufafin jikinta hakan yasa ta yi saurin faɗin


" Ni na kasance me yiwa gimbiya hidima,shi yasa nake da kaya masu kyau domin tana yawan yi mini kyautar kayayyaki kuma tana da kirki ".

Hallau kallon tuhuma yake bin ta dashi kafin ya buɗe baki haɗe da fadin

" Wata gimbiya kenan!?".

" Gimbiya Muzaina,ita ce nakewa hidima " ta faɗa tana me addu'ar Allah yasa kar ya kuma cillo mata da wata tambayar domin ta lura yana da bin diddigi.


" Tom amma ya na ji sunan na ku na shigen kama da na juna !?".

Lokaci daya ta ji gabanta ya yanke ya tsinke,ta kuma shiga wani rudin domin yana daf da kure ramin karyar ta.


" Ehh,haka ne amma akwai banbanci".

A nutse ya furta " shikenan, Bismillah " ya faɗa yana me zama akan grass carpet din dake gindin bishiyar.

Zama ta yi itama tana sauke ajiyar zuciya a boye batare da ya gani ba.

" Amma shin ku yan ƙasar Kuwait ne "

Murmushi yay " eh kwarai ma kuwa,mu yan ƙasar Kuwait ne, saboda kin gan ni baki a gaban ki shisa ki ka min wannan tambayar ko!? " dariya suka yi a tare domin maganar tasa ya yi barkwanci.

" Ah ah ko kaɗan ba haka bane,na tambaye ka hakan ne saboda naga kaff cikin wannan masarautar ban taɓa ganin me kyawun ka ba kuma kalar fatar ka ya kuma sa ka kwanta min a rai sosai ".

" Hhhhhh Tom na gode " ya faɗa yana yar dariya.

Shuru suka yi babu wanda ya kuma magana a cikin su,.ganin shurun ya yi yawa ne yasa shi faɗin

" Amma a wani bangare na bayi ki ke,bangaren ƙananan bayi ko kuma,bangaren matsagaitan bayi!?,ko bangaren manyan bayi!?,domin ko kaɗan jikin ki be nuna alamar kina aiki sosai ko kuma kina bangaren ƙananun bayi ba".

Cikin gajiya da tambayoyin sa masu kiɗima ta,ta ce

" Manyan bayi ".

" Okay ayyah".

Tun daga nan suka kuma yin shuru babu me magana se satan kallon sa da take yi.

Kiran sallah aka soma yi a babban masallacin dake cikin masarautar hakan yasa cikin sauri ya miƙe haɗe da miƙa mata hannu ta kama ta miƙe itama.

Kallon ta yay sannan ya ce

" Tom ina me godiya Muzna,zan je sallah se wani lokaci kuma".

Yana gama magana ya tafi ya barta tsaye a gun har ya isa cikin filin daga tana kallon sa ya ɗauki goran ruwansa ya tafi. Murmushi tayi lokacin da taga ya ɓacewa ganinta sannan itama ta bar wajen.


Horn take dannawa da ƙarfi wanda a ƙalla yanzu ta kusan mintuna biyu a bakin masarautar tana matsa horn cikin ɓacin rai da hassala amma ba a zo an buɗe ba.

A fusace ta fito a motar da take ta jikin gate ta tura ƙaramar kofar nan ta tadda wasu da basu samu zuwa masallaci ba acikin bayin suna gabatar da sallah, tsayawa ta yi a wajen tana karkada kai domin ranta ya masifar hassala,da sauri bafaden da ya kasance shine me gadin ya miƙe bayan an sallame saboda suna sallah suna jiyo yanda ake matsa horn din.

Yana sussukuyar da kai ya nufo ta alamar bata hakuri,amma kafin ya kai ga buɗe bakinsa ta ɗauke sa da mahaukatan zafafan mari guda biyu hagu da dama. Dattijon mai gadin riƙe kuncinsa ya yi da hannunsa biyu yana zubar da kwalla,hatta su kansu sauran bayin dake wajen se da suka ji saukar marin kamar a kuncinsu,ganin yanda bata lura da girmansa ta dagargare ta dake sa.


Cikin takaici ta nuna sa da yatsa ta soma faɗin


" Har kai waye da zanzo ina horn ka ƙi buɗe min gate banza ƙaskantacen bawa wulakantacce".

Murya na rawa yana zubar da kwalla ya ce

" Kiyi min afuwa gimbiya sallah muke yi wannan ne yasa ban buɗe miki ba ki gafarceni ".

Wani irin wulakantaccen kallo take watsa matsa

" Dallah yi mun shuru,tsohon banza tsohon wofi daga rana irinta yau bazaka sa'ke maimaita dabbanci irin wannan ba ".

Key din motar dake hannun ta wurga masa a jiki ta ja doguwar tsaki ta sa kai ta bar su tsaye kai a ƙasa, ta shige ciki.


Seda suka tabbatar da ta ɓacewa ganin su kafin suka ɗago suna bin bayanta da kallo suna jinjina abinda ya faru.

Yarima Farasat dake tsaye a bayansu basu lura dashi ba duk ya ga kuma ya ji abinda ya faru, karasowa wajen ya yi ya bawa mai gadin da ta mara hakuri sannan ya bi bayanta.

A hanyar ta na shiga sashin ta ya cimma ta.ko da ta juyo taga shine hakan be sa ta tsaya ba ta shiga falonta.


" Muzaina meyasa za ki mari mutumin da ya kasance tsoho,ko bama tsoho ba ya dace ki yi haka!?".

Tana cire jacket din saman kayanta hankali kwance ta ce

" Saboda ya yi rashin biyayya a gare ni kuma dole ya karɓi hukunci".

Iska ya furzar a bakinsa " amma kin ga ai sallah su ke yi ko ba haka ba ?,a duk duniya akwai uzurin da yakai wannan gaida Ubangijin sa yake yi".

" Farasat " ta kira sunan sa.

Ba tare da ya amsa ta ba ya zuba mata manyan idanunsa.

" Shin kazo ne dan ka rama masa marin da na masa ko kuma kazo ne dan ka ci min mutunci!? Wanne daya ka zo yi !?".

Zama ya yi a kusa da ita, tabbas ya lura da Muzaina batada kirki ko kaɗan. ita duk girmanka zata iya maka duk abinda ta gadama,haka zalika bata da kara duk yanda ku ke da ita abu in ya haɗa ku se ta maka rashin mutunci.ya jima da observing nata, amma ya zeyi Allah ya ɗaura masa sonta babu yanda ze yi dole ya ɗinga nuna mata gaskiya.


Cikin dabara da lallami ya samo faɗin

" Babu ko ɗaya,amma abinda ki ka yi be dace ba,eh ya miki laifi be buɗe kofa da wuri ba,amma ki koyi yi wa mutane uzuri,ke kyakyawa kuma nutsatsatsiyar macece,be kamata a ce da girman ki a gan ki kina masifa ba,hakan ze zubar miki da mutunciki. sannan wannan kyakyawar farar hannun naki an yi sa ne domin wanke jikin ki da kuma yiwa hadaddiyar fuskar ki kwalliya, bawai kiyi duka dashi ba ya ke gimbiya ta,shi sa nake ce miki be dace ba,in Allah ya yi kece fa future queen din mu haba my love ".

Murmushi ta soma sakarwa tana shan kamshi cike da ji da kai da jin dadin yanda yarima Farasat ya dinga hura mata kai.


" Shikenan naji amma suma wa'yannan banzayen bayin suna da kayan haushi ".

" Zan faɗa musu su kiyaye,bana son in ga kina ɓata ran ki akan abinda be kai ya kawo ba ".

Murmushi kawai tayi,bata ce masa komai ba,hakan yasa ya miƙe haɗe da faɗin

" Ni zan wuce zan je in ga na da Ummu Xulaihah ".

Tafiya ya yi ya barta ita daya saboda bayin da aka basu ita ta hana masu yi mata hidima shigowa shashenta inde tana nan, a cewar ta kyama suke bata.



" Dazun da ki ka fita Mubeen ya kirawo wayanki domin sanar miki da hutun da aka ba ki ya ƙare,yakamata mu koma dan ki ci gaba da Film din da ku ka fara".

Tana baje zaune a kasan carpet din dakin,gashin kan ta da Haseena ta mayar mata dashi donot ta sa headband,jikinta kuma kayan bacci ne masu laushi, yanda ta kwabe fuska se ta koma kamar wata karamar yarinya. Ta ƙi cewa komai se sake turo baki da take yi domin Muzna duk inda ake neman asalin shagwababbiya ta ta wuce nan.

" Kin yi shuru ba ki ce komai ba ".

Murya a shagwabe ta ce " nayi matukar kewan Aba,da yana raye nasan da shi da kansa ze ce in koma amma yanzu ki ga Abbu Aleem ya ce bazamu ko ina ba ".

Zaro ido Haseena ta yi cike da mamaki " kamarya bazaku koma ba?".

" Haka ya faɗa wai saboda mun dawo gida kenan,dan Allah wannan magana ne!?,ni ina son in yi rayuwa ta cike da yanci,ina son in yi duk abinda nake so,banason dogara da kowa i want to be my own boss, amma suna so su daƙile min mafarki na. Haseena tunda nake ban taɓa sha'awar sarauta ko kuma wani abu na kasuwanci ba ko aikin gwamnati ba,ke kin san wacece ni". Tana magana hawaye na gangarowa daga kwarya idanunta.

Cike da tausayi Haseena ta sauko daga saman kujerar da take zaune ta zo ta rungume ta,.

" Kiyi hakuri komai ze koma dede,daga zaran sun fahimce ki zasu bar ki kiyi yanda kike fata kinji abar kauna!?".

Gyada mata kai kawai tayi tana share hawayenta.

" Yanzu ni gobe zan koma Russia domin na jima rabona da gida amma na miki alkawarin duk sanda na samu lokaci zan zo domin in gan ki".


Dago kai ta yi ta kalleta haɗe da faɗin " yanzu dagaske tafiya zakiyi Haseena bazaki bari ki ɗan ƙara wani lokaci ba !?".

Shafa kanta tayi " kar ki damu aina miki alkawari zan ɗinga zuwa in sha Allah".

Har cikin ranta bata ji dadin hakan ba,amma ya zatayi?,itama Haseena na da ahali bazata iya dakatar da ita ba.


" Shikenan tom Allah yakaimu,barin in je in ga Ummi,daga nan kuma zan yiwa Yarima Haysam magana a miki booking Flight ".

A haka suka rabu ita ta fice zuwa sashin Ummi ita kuma Haseena ta kwanta.



Ko da ta shiga dakin duhu ya mamaye ciki amma dake farin riga ne da farin hijab a jikin Ummi tana sallah, hakan be hanata ganinta ba kunna switch din ta yi sannan ta zauna tana me jiran ta idar da sallah.

Ta jima tana addu'o i kafin ta sallame,duban ta tayi kallo ɗaya ta mata ta gane wacece,domin ko da duniya ba zasu iya banbance su ba ita zata iya tunda ita ta haife su.

" Muzaina" ta ambaci sunan ta,tana miƙa mata hannu alamar ta zo,tasowa ta yi ta zauna haɗe da kwantar da kanta a jikinta.


" Meya hanaki bacci Muzaina har wannan lokaci!?".

" Ummi haka kawai na ji bana son yin bacci,na kasa yin bacci a can kila zan iya yi a tare da ke".

Duk da tayi mamakin maganar ta,amma se tayi murmushi domin abinda bata taɓa ji daga gare ta ba kenan.

Muzna da ta baro dakinta ne,ta shigo dakin Ummin bakinta ɗauke da sallama,zama tayi a gefen hagun sarauniya Fatima,suka sakata a tsakiya.


" Ummi na,yau anan zan yi bacci na ". Ta faɗa a shagwabe,shafa fuskarta tayi tana murmushi.

" Tom ku tashi muyi addu'a se mu kwanta ko?".
Addu'a suka yi sannan suka hau royal bed din suka kwanta tana tsakiyar su,sun ɗaura kansu a jikin ta tana shafawa.


Shuru ne ya ratsa dakin kamar wa'yanda suke bacci amma dukkanin su idonsu biyu ko wanne da abinda yake tunani.


" Kun san nima marainiyace kamar ku?, lokacin da baban mu ya mutu,bayan shekaru biyu da rashinsa mahaifiyar mu itama ta tafi ta bar mu,amma ban taɓa jina cikin maraici ba,kun san saboda me ?".

Girgiza kai suka yi alamar ah ah.

Ɗorawa ta yi da " saboda ina da yan uwa kuma sun soni sosai mun haɗa kan mu waje daya,bama taɓa yarda wani abu ya shiga tsakanin mu.
Mun rayu ne akan turban da iyayen mu suka daura mu na kaunar juna,dan Allah ku ma ina me rokon ku da ku kasance masu kaunarta juna ko da bayan rai na ne,kar ku sake kyale_kyalen duniya ya farraƙa ku,mulki,kudi,ɗaukaka,duk wanda kaga ya samesa to Allah ne ya riga da ya rubuto masa hakan tun kafin a san ze zo duniya,kun ji ko yarana?"

Tabbas maganganun ta sun yi matukar tasiri a zuciyoyinsu,jikin su ya yi sanyi sosai hakan yasa suka sake mannuwa a jikin ta kana Muzaina ta ce

" Ummi in sha Allah babu abinda ze rabani da Muzna ".

Murmushi tayi hakan ya mata dad'i

" Nasani domin kuna son junan ku sosai ". Ta faɗa tana ci gaba da shafa kan su

" Ummi ni banason yanda ki ke maganar ko bayan ran ki,in sha Allah ba yanzu za ki mutu ba,mu na nan har tsufan mu". Muzna ta faɗi hakan a yayinda siraran hawaye ke kwaranya a idanunta.


" Ya Allah,to meye na kukan Muzna?" Cewar sarauniya Fatima tana miƙewa zaune su ma suka zauna.

Hannu tasa ta goge mata hawayen " be dace ki yi kuka ba ta kan magana irin haka ba,rayukan mu ba'a hannayen mu suke ba,za mu mutu ne a lokacin da ubangijin mu yayi kira a gare mu, kamar yanda Aba din ku ya tafi haka nima wata rana zan tafi, ku ma za ku biyo mu haka kowa ma se ya mutu.
Kar ki zama raguwa mana,ni ban haifi ragwaye ba, ƴa'ƴana basu da rauni dukkanin ku jarumai ne,.ko bayan idona nasan zaku sani alfahari ".

Sunkuyar da kanta ƙasa tayi har lokacin hawaye ya kasa tsayuwa daga Idonta haka kawai take ji a jikinta kamar ta kusa rabuwa da wani gurbi na rayuwar ta.


Ɗan murmushi kan leben baki Muzaina ta yi ta soma faɗin

" Ummi ita fa da ma wannan ƙanwar tawa haka take ko banida lafiya in na ki shan magani se ta fara min kuka har se na sha ".

Ɗago kai tayi tana hararan ta jin abinda ta faɗa

" Ni ba ƙanwar ki bace saboda rana daya a lokaci daya muka zo duniya"

Dariya sarauniya Fatima da Muzaina suka yi mata.

Cikin dariya sarauniya Fatima ta ce

" Eh tabbas rana daya ku ka zo duniya,kuma a lokaci daya. sede saida aka fara fito da Muzaina kafin ke a ka ciroki, to Kinga kuwa ta ri ga ki shan iskar duniya ".

Cuno baki tayi tana " eh de duk da hakan de baran yarda ba".


" To shikenan ".

" Ummi gobe Haseena zata koma ƙasar su Russia gaskiya zan yi kewar ta sosai, yanzu kafin in shigo na samu yarima Haysam na masa magana kan ya mata booking Flight dan cewar ta da wuri take son komawa ".

" Allah sarki, Haseena yarinyar Kirki ce kuma naji dadi sosai da ya kasance kina ƙawance da ita Allah ya nuna mana safiyar ".


Har karfe biyu na dare idanunsu biyu suna hira se da sarauniya taga lokaci ya kure kafin ta basu umarni da su kwanta.

" Dare ya yi duk ku kwanta kar wacce ta kuma magana kun ji ko!?,ku yi bacci cikin aminci".


Washe gari


Miƙewa tayi akan gadon tana hamma haɗe da miƙa,ta kalli Muzaina dake gefenta tana baccinta peacefully.a gefe da gadon ta hango mahaifiyar su sarauniya tana gabatar da sallah asuba hakan yasa ta haɗe gashinta da suka hargitse ta ɗaure sannan ta soma tashin Muzaina ta hanyar bugun fillow da take kwance.

A hankali ta ware idanunta da bacci be ishe su ba ta ɗaura su akan ta tana me faɗin

" Meye kuma !?".

A hankali ta furta " ki tashi kiyi sallah gari ya waye".

A kufule Muzaina ta kuma maida kanta kan fillow tana me rufe Idonta ta ce

" Kar ki kuma tashina tam".

Tunda ta ji hakan tasan ba sallah zatayi ba, hakan yasa ta miƙe ta shiga toilet ta yi wankan safiya haɗe da Ɗaura alwala ta fito, ma'adanar kayan sarauniya taje ta buɗe ta dauko wata dogon rigar me shige da jallabiya ta saka sannan ta saka farar hijabi da tsayinsa ya tsaya mata a cikinta,ta shimfida sallaya a kusa da na sarauniya itama ta tayar da sallah.


Komawa sashen ta tayi bayan ta baro sarauniya Fatima nayiwa Muzaina faɗa akan sallah.


Zaune ta iske Haseena tana zaman jiranta .ta gama duk shiryawan da za ta yi tsaf,zama ta yi a gefenta tana faɗin

" Hasee bari in shirya na rigada na yi wanka ".

" To kiyi sauri Kinga lokaci na kurewa".


Shiryawa tayi cikin bakar dogon riga da jikinsa ya sha tsone, siririn necklace na Gold ta saka a wuyanta da yan ƙananun ɗan kunnen sa, sannan ta gyara gashin ta, tayi light kwalliya,flat shoe baki ta sa kafin ta ce

" Na kammala".

Haseena da tun lokacin da ta fara shiryawan take bin ta da kallo tana murmushi ne ta miƙe ta ce shikenan muje.

Bayi ne suka ɗauki kayanta izuwa motar da ze kai su airport,su kuma suka je wajen galadima domin tayi musu bankwana.sosai suka mata godiya da kuma yi mata alheri,haka suka shiga wajejen Ummu zaheenat da Ummu Xulaihah ta musu bankwana..

Waje na karshe da suka shiga shine wajen sarauniya Fatima, sosai ta yi mata godiya haɗe da mata kyautar zinari masu daraja sosai, Muzaina dake zaune akan kujera tana danna waya ko dagowa batayi ba ɓalle ta kalleta,haka itama ba ta bi ta kanta ba, fitowa suka yi suka iske Hamra da Jadwah suna jiran su a babban falo.


Motoci biyar ne ya musu rakiya izuwa airport,bayan sun isa suka fito riƙe hannun juna suka yi suna me yiwa junansu kallon kewa da zasu yi.

" Zan yi matukar kewar ki Haseena".

" Nima haka,zan zama ni kaɗai yanzu.amma ina addu'ar Allah ya sa'ke haɗa fuskokin mu".

" Ameen ya Allah,ki kula min da kan ki. a duk sanda ki ke da bukatar wani abu, ki min magana ina nan tare dake my Haseena. Sannan kuma ki isar min da sakon gaisuwa ta musamman a wajen kowa na gida".

Gyada mata kai ta yi hawaye na taruwa a Idonta, rungume juna sukayi na ɗan lokaci kafin ta sake ta tana manna mata sumba a goshi, rungume su Hamra ta yi kafin ta tafi ta barsu tsaye suna daga mata hannu.har cikin zuciyar Muzna tana jin babu dadi sun zo a tare sede Allah be yi zasu koma a tare ba.

Motar suka shiga suka ɗauki hanyar komawa masarauta,ko da suka shigo masarautar tun daga nesa ta hango Sadauki Zubair yana tunkaro su hannun sa na riƙe da Kwandon kayan miya.


Ganin yana kokarin ɗago kan sa izuwa ga motar ne yasa gudun kar ya hangota ta yi sauri kwantawa a jikin Jadwah,da kallo suka bita.

" Lafiya gimbiya"? Hamra ta tambaye ta,batace mata komai ba se ɗan dagowan da tayi tana leke ta glass,a jiyar zuciya ta sauke duba da ya ɗan wuce su,.

" Dakata ni zan sauka anan " cikin cika umarni driver da yake jan motar ya dakata.

" Me za ki yi"

Girgiza kai tai tana faɗin " zan ɗan yi abu ne, ku, ku tafi kawai" ta ƙarishe tana buɗe marfin motar ba tare da ta jira an buɗe mata ba,se da ta tabbatar da sun tafi tukuna dan tasan Jadwah zata iya biyo bayanta.

Cikin sauri-sauri ta bi bayan sa har ta cin masa amma bata basa damar fahimtar tana binsa a baya ba.
Tafiya suka yi me nisa tun daga nesa take hango wani gida madaidaici wanda ya kasance a gefen manyan sashen bayi.

A bangaren Sadauki Zubair kuwa tun lokacin da ta soma binsa ya ankara da sautin taku a bayan sa amma se be nuna alamun yasan a na binsa ba har suka yi wannan nisan.

Suna cikin tafiya ya ja burki ya tsaya batare da ya juyo ba,itama tsayawa tayi daga bayansa tana runtse ido haɗe da yin murmushi dan ta san yanzu kam ya gane ana binsa.

A hankali ya juyo ya ɗaura idonsa akan ta,ko kaɗan be yi tunanin cewa ita bace,tun daga kasa ya soma ƙare mata kallo ganin tafi ko yaushe kyau,.

Cikin dabur-dabur ta furta

" Uhmm amm barka dai....dama naganka ne shisa nace bari in zo mu gaisa".

Murmushi ya yi " shikenan amma kar ki ƙara irin haka domin wata rana za'a iya kawo miki farmaki,saboda duk wanda ana binsa a baya haka ze yi tunanin abokin gaba ne ".


Gyada kai ta yi cikin jin kunyar sa " in sha Allah".

Har ya juya kuma se idonsa suka sauka akan tsadadden sarkan zinari da dan kunnensa dake manne a dogon wuyanta da kuma kunnuwan ta.

Nu na su ya yi da yatsa ya ce " wannan zinarin fa, wannan zinarin me matuƙar daraja ce taya akai ki ka same sa !?".

Ya tambaye ta yana tsare ta da kallon tuhuma.

Se da gabanta ya fadi jin tambayar da ya watsa mata shi,banda girgiza babu abinda kirjinta yake mata ga ta gagara nemo abinda zata sanar dashi.

Fahimtar da ya yi ta faɗa duniyar tunani yasa ya kyasta mata yatsa a fuska wanda yasa tayi firgit ta dawo hayyacinta.


" Uhmmm wannan sarkan jabun na gimbiya Muzaina ce, lokacin da aka bata sarkan shine ta saka aka min jabunsa.saboda tana ji dani kuma na yabi sarkan sosai" ta karasa maganar tana satan kallon sa ta kasan ido,.

Har yanzu da kallon tuhumar yake binta domin be wani gama yarda da abinda ta faɗa ba, saboda a duk inda kaga jabun abu da na gaskiya seka gane.

Cikin son kawar da maganar ta ce " shin ina zaka je haka naga ka biyo ta nan? ".

Dago mata da Kwandon kayan miya yayi ya nuna mata ya na me cewa

" Yumma ce ta tura ni madafa domin samo mata kayan haɗa miya,nan kuma shine in da muke

Please Login or Register in order to submit comment