Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤02¤¤
.
¤Wannan Sadaukar wa ce zuwa ga..... Boss dina, Yaya na, Dan uwa na, Bappa na, wanda adomin sa na ke nan, Allah ya ba shi sa'a da nasara a komai nasa da sauran en uwa musulmai gabaki daya...
(MARABAS DAN ANTY) jinjina gare ka.¤
.
Ci gaban labari...
.
Yace; Me zan taho miki dashi? Tana murmushi tace; ''Goba'' Yayi dariya yace; Kedai kam ina ga sai kin haifi da mai kalar goba...Shikenan sai na iso.
Ya kashe wayar ya dauki makullin motarsa. Yana shirin fita ke nan Basiru masinja ya shigo ofishin rike da zungureren fayil(file) a hannunsa suka yi kici6us ya rusuna yace:
Yalla6ai ga takardun injinan nan da akayi bonanza daga ofishin peter yace akawo maka kasa hannu.
Ya kar6i fayil din ya dora akan tebur ya dauki biro yasa hannu(signing) sannan ya mikawa Basiru. Yana fita yaci karo da Alh. Sammani Sabo. Don haka dole suka koma cikin ofishin, suka gaisa Alh. Sagir yana dan fara'a yace;
Alh. Sammani jiya nake tunanin na kira ka ban samu sarari ba. Alh. Sammani yayi murmushi yace; kada ka damu ni gani nazo da kaina. Alh. Sagir ya dan yi shiru na wani lokaci sannan yace;
Gaskiya nayi tunani mai zurfi naga hakan bazata samu ba, musamman idan nace zan 6ullo da hakan a kungiya baza a aminta ba, don haka kawai nake ganin mu hakura......
Alh. Sammani ya bugi teburin da hannunsa yana dan murmushi yace; Kada ka damu Abokina,Aminina ni na san kai masoyi nane ko bayan ba raina zaka iya taimakon iyalina. Nagode da bayaninka yanzu yaushe ne za a dauka?
Alh. Sagir yace; Eh, to kamar yadda aka soma fada tun can baya. Alh. Sammani ya yunkura yace; shikenan aminina ba matsala, amma ni zan yi tafiya zuwa Dubai har sai bayan komai ya kammala zan dawo. Don haka ina neman afuwa ga kowa-da kowa, a kuma kula da ci gaba da abubuwan da ake yi yadda ya kamata.
Alh. Sagir yace; Yauwa aminina nagode kwarai da yadda ka hakura ka sadaukar. Babu komai.
Ya rako shi har bakin kofa, sannan shi kuma ya koma cikin ofis din ya dauko makullunshi daya ajiye cike da farin ciki ya fito ya tunkari inda suke ajiye motoci.
Ya kusa karasawa kenan yayi tuntu6e da wani 'Kashi ya kife kasa, bisa tsautsayi ya kama aman jini.
Mutanen dake shawagi a gurin suka ankara da abinda ya faru don haka da sauri suka tunkaro shi, don kawo masa dauki.
Aman jinin yake kashir6an saboda haka sai ba a tsaya 6ata lokaci ba aka kwashe shi aka nufi Asibiti dashi. Ko kafin a isa Asibitin ya gala baita sosai, da gaggawa aka shiga dashi Emergency room.
Alh. Saminu wanda ya jagoranci zuwa Asubitin yayi amfani da wayar Alh. Sagir ya lalubo lambar Alh. Ahmad ya kira shi. Bugu daya wayar ta shiga. Yana dauka yace; Yane Baban gobe? Ko an sauka ne? Alh. Saminu yace; Bashi bane Daya daga cikin ma aikatan gidan gonarsa ne, don Allah ka same mu a NAJNOOR HOSPITAL, Saboda oga yazo hawa mota yayi tuntu6e ya kama aman jini. Shine muka kawo shi Asibiti.
Cikin tashin hankali Alh. Ahmad yace; To gani nan zuwa. Mintin sha biyar a tsakani Alh. Ahmad ya iso Asibitin. A lokacin suna da damar shiga inda yake saboda an samu aman jinin ya tsagaita.
Suna shiga suka tarar dashi dik ya yamutse kamanninsa dik sun sauya,tamkar wanda yayi ciwon shekara. Alh. Ahmad ya matsa kusa dashi yaga idanunsa sunyi jajur kamar jan gauta. Wani irin siririn haske ne acikin idonshi,sai kace yana saitin hasken kwan lantarki.
Cikin tausayawa Alh. Ahmad yace; sannu Alh. Sagir. Bai iya amsawa ba, sai dai idanu kawai da ya zuba masa,kai kace wannan shine karo na farko da yayi tozali da shi.....
ada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA)
¤¤03¤¤
Dama baka lafiya ne ko kuwa sanadin tuntu6en ne? Har yanzu bai iya tankawa ba sai Alh. Saminu ya amshi zancen da cewa; Gaskiya nima ina tunanin bashi da lafiya, domin yaui sukuku yake a gidan gona,tunda ya shiga ofis dinsa bai fito ba sai da wannan sanadin ya faru.
Alh. Ahmad yace; To Allah ya bashi lafiya? Gaba daya suka amsa Ameen. Sun shafe mintuna goma babu wanda ya sake magana daga cikinsu. Sai zuwa can Alh. Sagir ya lumshe ido Alh. Saminu yace; Ina ga ma ya samu bacci.
Alh. Ahmad ya dago kai ya dubi Alh. Sagir, sai ya ga ya bude ido, amma kwayar idon ta sauya launi ta koma KORE shar, sannan ta koma DORAWA, sai ta koma BAKI. Shikenan ya maida idon ya rufe.
Gaban Alh. Ahmad ya fadi, bai fahimci abin da ya gani ba, ya dubi Alh. Saminu da sauri yace; Ku duba ku gani yadda kwayar idonsa ke sauya launi.
Da sauri suka dubi Alh. Sagir amma sai suka ga kwayar idonsa a rufe Alh. Saminu yace ai bacci yake. Alh. Ahmad ya dunga tunanin anya kuwa bai ga wani al'amari ya faru da dan'uwansa ba? Amma jin amsar da suka bashi yasa ya share maganar.
Alh. Saminu yace ya kamata a sanar da maidakinsa. Alh. Ahmad yace; Eh ba ma ita kadai ba harda mahaifanmu. Ya ciro waya yana niyyar doka kira kenan, Alh. Sagir ya mike a firgice ya dafe kansa da hannunsa guda da ba a dora masa ruwa ba? Alh. Ahmad ya maida wayar a aljihu ya matso da sauri kusa da dan'uwan shi yana tambayar; Ya jikin? Amma shiru bai tanka ba daga karshe sai ya koma yaraf! Akan gado. Gaba dayansu suka saka sallallami, daya daga cikinsu yayi saurin kirawo likita. Ya duba shi ya tabbatar musu da RAI YAYI HALINSA.
Kwalla suka sirnanowa Alh. Ahmad cikin karfin hali ya kirawo mahaifinsu ya shaida masa halin da ake ciki. Sannan ya kira Alh. Sada shima ya bayyana masa abinda yake faruwa.
Cikin kankanin lokaci suka gurfana a asibitin hankalinsu a tashe.
Cikin kankanin lokaci suka gurfana a asibitin hankali a tashe, aka gama dik abinda ya dace sannan aka basu mota (Ambulance) da zata kai musu gawar a gida.
Suka taho,kowannensu cike da wannan jimamin wannan BABBAN RASHIN da sukayi, Saboda rashin irinsu Alh. Sagir yana da matukar ta6a zuciya.
Jan gwarzo jarumi wanda ya tsayu da kyautatawa na kasa dashi, zai yi wuya talaka ya kawo kukansa ga Alh. Sagir ba tare da an share masa hawaye ba. Amma duk wannan yakana tasa bata hana ya amsa kiran mahaliccinmu ba.
Laillai Allah baya barin wani don wani yaji dadi!!! Kuma dik jarumtar rai da nuna hazikanci, dole ne ta dandani mutuwa.
(Dacin mutuwa mai ta6a zuciyar wadanda aka yi wa komai, ma'ana juriya da jarumta basu isa su hana rai dandanar mutuwa ba, yayin da suka rasa wani nasu)
mu samman ma Alh. Sagir da ya zamto tamkar shugaba a wannan tsatso, saboda yapi kowa kudi a cikinsu.
.
(ALLAH YA JIKAN MARUBUCIYAR WANNAN LITTAPIN YA GAFARTA MATA DA SAURAN MUSULMAI BAKI DAYA AMEEN)
.
Ci gaban labari...
KADDARA TA RIGA FATA Haj. Karimatu tana zaune a falo Haj Asmo ta shigo dauke da faranti a hannunta, fuskarta kunshe da fara'a tace; Yau dai ina sauke hakkin da ya rataya a wuyana. Haj karima tayi murmushe tace; uhm kaji manyan masu gida, don anyi min sanwa shine ake koda kai? To dama kin bari domin ba gwaninta kikayi ba tunda ba ci zanyi ba shi dai na karfen ya dawo yaci. Haj Asmo ta zauna a gefenta tace ke kin isa? Ai bazan wahala a banza ba. Haj Karima tace ; Ko yanzu ba kiyi wahalar banza ba,tunda dan'uwanki zai dawo,kinga kin hutashshe dani. Tace wlh kuwa ke nifa yau tinda na tashi nake jin gabana na faduwa komai ba yayi min dadi,hatta yawun bakina daci yake min. Ga shi dan da yake cikina yana ta yamutsamin 'ya'yan hanji. Haj Asmo ta danyi murmushi tace; To ko dai haihuwar ta zone? Don dama naga cikin naki yayi kasa sosai. Haj Karima tayi murmushi ita ma tace; Wai ita mai tsohon ciki babu wani ciwo ko damuwa da zata shiga sai dole nakuda? Ni fa wallahi tsoro ma nake kada na zo haihuwar nan na wuce. Haj Asmo tace; Ai haihuwa ba mutuwa bace ke dai Allah ya sauke ki lapiya, amma ki daure kici abincin nan zama da yunwa yana azabtar da mai ciki. Haj Karima tace; Bazaki gane me nake nufi ba, sam ba na jin yunwa kuma bana iya kai komai a bakina. Ke dai kici kawai ba ra na shiga daga ciki. Haj Asmo ta dan harare ta, ta wutsiyar ido tace; Ke dai ko wayo kike so ki yi min ki shiga daki ki haihu sai dai na jiyo kukan jariri? Dariya Haj Karima tayi tace; A'a wallahi kinga ma na fasa shiga dakin shike nan? Za tayi magana suka ji karar tsayuwar mota Haj karima tace; Ina ga ma gashi nan ya iso. Haj Asmo tace mai yuwuwa bashi kadai bane naji kamar karar tsayuwar motoci ne ba daya ba. Tace kila shi da Abokanensa ne Kafin su gama tantancewa Alh. Sada ya danno kanshi cikin falon fuskarshi babu annuri suka amsa sallamarsa. Haj Asmo ta dora da cewa: Ai naje gidanka baka nan shine na wuto nan kafin anjima na koma. A takaice yace; Ai gwara ma da kika zo nan din. Ya dubi Haj Karima yace ina makullin sitroom? Kafin ta bashi amsa sai da suka kalli juna ita da Haj Asmo sannan daga bisani tace; Yana daki, yace kawo min. Zata tambayeshi ya daga mata hannu yace: Hanzarta ana jirana a waje. Haj Asmo jikinta yayi sanyi ta dubi Haj. Karima tace; Ko ki fada min inda yake sai na dauko, tace; yana kan dressing mirror. Haj Asmo ta nufi dakin a hanzarce ta dauko makullin sitroom ta kawo masa. Ya kar6a ya fice ba tare da yayi musu bayanin komai ba. Sai da aka shigo da gawar Alh Sagir tukunna Alh Rabi'u ya shigo falon. Ga ninshi da suka yi gabansu ya tsananta faduwa, tabbas ya nuna musu akwai wani al'amari da yake faruwa sai dai basu san ta ina abin yake ba. Suka durkushe su duka biyun suna gaishe da shi. Bayan ya daidaita zaman shi akan kujera ya amsa musu ya dubi Haj Karima murya a taushe irin ta dattako yace.....
.
.
Gaskiya ban gane canzawar idanuwan sa ba!!!
Se ku cigaba da biyo mu, dan jin yanda za a kaya.......
Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA)
¤¤04¤¤
.
''Karima ina so ki sani Allah shiya halicce mu ba ya barin wani don wani kuma dikkan rai bata wuce wa'adinta. Allah yayi wa mijinki rasuwa!!!! Yana sitroom ki taso ki masa wanka don a sadar dashi da gidansa na gaskiya. Wasu taurari ta gani suna walainiya acikin idonta. Da sauri ta runtse idonta tana tunanin mafarki ne take amma koda ta bude idon sai ta ga dattijon surukin tsohon nata a zaune, wannan ke nuni da KADDARA TA RIGA FATA! Abinda kunnuwanta suka jiye mata tabbas haka yake babu tababa. Yayin da Haj Asmo ta fashe da wani irin rikitaccen kuka su duka biyun suka mike da sauri cikin faduwar gaba suka tinkari sitroom din. Suna isa suka ga gawar shi a shimfede a kasa an lullu6e shi da sauri Haj karima ta kai hannunta ta yaye mayafin da aka rufe mamacin idanuwanta suka yi tozali da jarumin mijinta ai bata san lokacin da ta kurma kara ba. Ta zube kasa sumammiya. Gaba dayansu hankalinsu ya dugunzuma ya tashi suka nufe ta suna sallallammi. Ba a jinkirta ba aka kwasheta zuwa asibiti ana tunanin ita ma rai yayi halinsa. Lokacin da ta farfado daga sumanta ta farka ne tana ambaton sunan mijinta. Haj Asmo dake gefenta ta shiga rarrashinta da tausasan kalamai. Ta rirrike zanin da yake shimfide a saman gadon da ta ke kwance tana wani irin madodawa, Likita ya shigo yana dubata yayi mata allura sannan ya dubi Haj Asmo yace; Haihuwace zata yi zamu kaita dakin masu haihuwa. Haj Asmo tace shikenan Allah ya raba su lafiya. Aka mayar da Haj Karima dakin 'yan haihuwa sai dai ta jigata sosai kafin ta haihu. Ta haifo 'yarta mace santaleliya son kowa kin wanda ya rasa. Haj Asmo tana zane da ita a dakin hutu rungume da jaririyar yayin da mai jegon take sharar baccin gajiya. Su Alh. Ahnad suka shigo ta sanar dasu an sauka suka yi godiya ga Allah da ya rabata da cikin lafiya. Haj Asmo tace har an rufo yayan? Alh. Sada yace Eh, Tace to Allah ya jikansa ya kuma raya bayansa. Su duka suka amsa da Ameen. Misalin karfe tara na dare Haj Karima ta farka da sauri Haj Asmo ta jawo kula ta zuba mata farfesu sannanb ta hada mata ruwan shayi mai kauri ta matso kusa da ita. Tashi kisha wannan don ki samu karfin jikinki. Tsananin yunwar data ke ji ne yasa ta kar6a tasha. Sai a lokacin ne ta lura babu cikin da ke jikinta. Sam hankalinta bai kai ga jinjirar dake rungume a hannun Haj Asmo ba ta soma kuka. Haj Asmo ta shiga rarrashinta Haj karima tace; Shima cikin nawa ya zube koh? Haj Asmo ta mika mata jinjirar dake hannun ta tace; Bai zubeba ga abinda kika haifa 'ya mace ce. Ta dubi jinjirar fara sol da ita kyakkyawa idanuwanta hancinta girarta dik na uwarta ne yankan bakinta da tsawon ga6a ne kawai na mahaifinta. Tsotasar hannu kawai take tamkar me shan nono Haj Asmo ta ga bata da niyyar kar6ar yar ta girgiza kai tace; Kar6eta ki bata nono muga zata kama saboda tin da ta zo duniya ambata madara taki sha sai tsotsar hannu take gasi kuma ga dukkan alamu yunwa take ji. Ai ta jigata da yawa Allah ma ya auna arziki da rabon zata rayu. A hankali ta miko hannu zata kar6eta amma sai ta kasa Haj Asmo tace; Bari na daura miki ita a jiki ki bata ta sha. Naga ba kya iya daukarta ma ko? Ta karashe maganar tana kokarin dora mata 'yar ajiki. Ana kuwa saka mata kan nonon a baki ta kama zuko shi? Haj Karima ta kama cije le6e saboda yadda jinjirar take jawo ruwan nonon da karfi. Ji take tamkar zata tsinke mata shi. Haj Asmo ta lura da hakan tace; Daure saboda yana sabo ne data saba ruwan nonon yazo sosai zaki daina jin zafin. Da kyar ta daure 'yar ta sha ya ishe ta ta 6ingire da bacci Haj Asmo ta dauke ta ta kwantar cikin gadonta sannan ta juyo kan Haj karima tana kuma lallaminta. Washe gari 'yan uwa da abokan arziki suka yi ta zuwa ganin jaririya da yiwa Haj karima gaisuwar mijinta. Ita dai kallonsu kawai take zuciyarta cike da radadin rashin data yi. Hakika tayi babban rashi a tsawon shekaru shiddan da suka yi da maigidan nata dai-dai da rana daya basu ta6a samun sa6ani ba. Kullum cikin tattali da nuna mata kauna yake. Ya koyar da ita matsanancin sonsa ta yadda ko wata unguwa yaje wadda zai kwana take samun kanta cikin kadaici. To yau gashi mai rabawa ta raba(Mutuwa) dole ne tayi kuka kuka kuwa mai ciwo, wanda baya da magani illa HAKURI da DANGANA. Kwananta biyu a asibiti aka sallame ta an so a sallame ta a washe garin data haihu to amma kasancewar tana fama da rashin afuwar jiki dole tasa aka jinkirta sai data kwana biyu. Ana sallamar ta kai tsaye gidanta aka zarce da ita 'yan uwa sai rarrashinta ake yi ana dannar zuciyarta don haka ta dan samu saukin zafin rashin da tayi.
Ranar daren suna Alh Sada yazo gidan da daddare ya same ta yana tambayarta tana da za6in sunan da za a sakawa yarinyar? Kuka ta kamayi sai da ya rarrashe ta tayi shiru sannan tace; Marigayi ya ta6a cewa idan mace na haifa SHUHUDA za a Saka mata . Idan kuma namiji ne JAMILU.
Alh Sada yace Shikenan za a saka mata Shuhudan sannan munyanke shawarar zaki zauna anan gidan ki shayar da yarki har zuwa lokacin da Allah zai fito miki da miji ki yi Aure.
Ba ta iya ce mishi komai ba amma ita a zuciyarta bata tunanin zata iya auren wani namiji anan gaba saboda da kyar ne ta samu wanda yake sonta kamar yadda mijinta yake sonta ba.
An yi taron suna da sadakar bakwai sai dai taron sunan babu armashi kamar yadda suka ci buri idan an haihu za a yi. Sai dai wani abu daya daurewa kowa kai shine; TSOTSAR HANNU da Shuhuda ke yi. Idan tana kwance aikin kenan haka idan wani ya dauke ta abin dake raba ta da tsotsar hannu to kuwa sai idan mahgaifiyar ta tana bata nono ne.
Ga shi yadda take tsotsar hannu abin ya wuce misali tsotsa take yi da karfi kamar me tsotsar nono. Goggo Zuwai kanwar mahaifiyar Haj Karima ita ta zauna a gidan kasancewar mijinta ya rasu kuma yayanta dik mata ne suna ma'auri.
Tana matukar kokarinta wajen ganin ta korewa Haj Karima damuwa ba laifi ana samun yadda ake so Haj karima ta rungumi kaddararta hannu biyu tana yawaita aikawa mijinta addu'o'in samun haske da rahamar Ubangiji a kabarinsa.
.
Tafiya sannu-sannu kwana nesa har aka samu tsayin shekar guda shuhuda tayi wayo sosai har tafiya ma tana dan ta6awa saboda ta tashi da kazarniya.
Zuwa wannan lokacin zawarawa sun yiwa Haj Karima caa yawancinsu duk abokanan mijinta ne sai dai babu wanda ta ke kulawa har yanzu tana kewar mijinta. Dangin mijinta sun yi maya halacci domin suna matukar kula da ita babu mai son ya ganta cikin damuwa sun rungume ta tamkar ita ce tasu ba mai rasuwar ba.
Tana matukar jindadin haka ko dama can farko aurensu da mai rasuwar sun nuna mata kauna kaunar ce ma har yanzu take bibiyarta. Ranar laraba da daddare misalin karfe takwas Haj karima da Goggo zuwai suna zaune a falo bayan sun gama sallar isha'i suna kallon labaran duniya.:
Inna Yaduwa( mahaifiyar mijinta) suka yi sallama ita da ISAH (dan Alh Sada mai kimanin shekaru bakwai). Bayan sun zauna an gaisa Haj karima ta kawo musu abinci suka dan ci kadan saboda a koshe suke.
Inna yaduwa ta dubi Haj karima tace; Karimatu musamman zuwan nan ba yi shi dominki. Gaban Haj karima ya fadi tsoroi ya kamata ta tuna ranar da Alh Rabi'u yazo mata da bakin labari tana gudu kada ace ita ma Inna yaduwan ta zo mata da bakin labarin mutuwar mahaifanta ne(Ance idan maciji ya sare ka tsumma ka gani sai ka ruga.
Inna Yaduwa ta lura da halin da Haj karima ta shiga sai tayi murmushi tace; Kwantar da hankalin ki shawara ce zamuyi dake. Ta sauke gwauron nunfashi yayin da Inna yaduwa ta ci gaba da cewa.
Shuhuda yanzu ta samu shekara daya sai dai duk wanda zai ganta zai dauka ta wuce haka saboda girman jikinta ga wayo tana da shi. To sai nake ganin me zai hana wata uku masu zuwa a cire ta daga nono tunda dama ba damuwa tayi da shi sosai ba??
Shiru Haj karima ta yi bata tanka ba saboda alkunya da yakana irin ta mutan da. Sai gwaggo Zuwai ce tayi magana; ............................................................
................. Nima nayi wannan tunanin tunda a yini bai fi tasha nono sau biyu ko sau uku ba musamman ma yadda zawarawa suka fito suna son aurenta sai na ga cire Shuhudan a nono tayi aure zai fi da cewa. Inna Yaduwa tace Sannan kuma mai zai hana Ahmad ya maye gurbin marigayi , tun da shima ya nuna yana bukata? Da sauri Haj karima ta mike tsaye tare da zaro ido waje sai dai bata iya cewa komai ba sai girgiza kai da take yi tana ja da baya. Inna Yaduwa tace Kinga zauna idan bai kwanta miki ba babu dole dama shawara ce saboda shi dan uwan sagir ne zai iya zaunawa dake da yarki amma a wannan zamanin da wuya ne samun mijin da zai rike agola. Koda ya riketa ma sai kinga bambanci,don haka na yi miki sha'awar auren Ahmad to amma tunda bai kwanta miki ba , kada ki damu Allah Ubangiji ya za6a miki miji nagari. Idan lokacin yayen yayi zan zo na kar6e ta na yaye miki ita. Tana karashe fadar haka ta dubi Isah tace; Kai tashi Muje. Yace Kai Inna mun fa yi dake a nan zaki bar ni gurin 'yar uwata. Ta yi dariya Idan na barka makaranta fa? Yace; Ba sai direban ya zo nan ya dauke ni ba? Tace; kai ni taso mu ta fi, ka ta6a ganin maigida na gudun matarsa? Ba don yaso ba dole ya mike, Inna Yaduwa ta dubi Haj karima tace; Mu mun tafi. Jiki a sa6ule Haj karima tace; Shikenan Inna na gode Allah ya sauke ku lafiya. Inna Yaduwa ta amsa da 'Amin' sannan suka fice daga cikin gidan. Bayan tafiyarsu Goggo Zuwai ta dubi Haj Karima tace: Ke kuwa 'yar nan meye aibun Alh Ahmad da kika razana don an yi miki sha'awar aurensa? Idon Haj karima ya kawo kwalla a idonta tace; Kin gane Goggo ba zan iya rayuwar Aure da Alh Ahmad ba, ba wai don baya da kyawawan halaye ba sai dai don idan na dube shi zan dinga tunawa da kaninsa kuma ma dai gaskiya ina jin kunya da tsoron matanshi. Goggo zuwai tace; Hakane to amma ai wanda ya rasu ya riga ya rasu, su kuma matanshi ai sun san akwai aure a tsakanin ku. Tsoron me zaki ji nasu? A kansu zaki zauna ko kuwa? Kowa zaman kansa zai yi don haka ina ganin shi ya dace ki aura. Girgiza kanta tayi

Please Login or Register in order to submit comment