Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace: Bazan iya aurenshi ba gwaggo. Tace To idan baki aure shi ba wa zaki aura? Kin dai san dole ne ki yi aure ko? Sai tayi shiri ta rasa abinda zata ce Tana da zawarawa da yawa wadanda sun fito ne domin su aure ta, kuma duk wanda ta za6a tana da yakinin zai kyautata mata sai dai ba zai kai ya mijinta ba. Don haka babu wanda ya kwanta mata. To amma tunda an 6illo da wannan maganar dole ne ta yo wani abu akai ko don tsallake wannan suradin. Maganar Gwaggo zuwai ta katse mata tunani tace; '' Aure a musulunci sunna ne daga cikin sunnonin Manzon Allah Muhammad(S.A.W) dama sauran manzanni da suka gabace shi Allah (S.W.T) Yace; Hakika mun aiki manzanni gabanka kuma mun sanya matan aure garesu da zuriyya(Ra'ad:38). Manzon Allah (S.A.W) yace ' Aure sunnata ce duk wanda yayi kyama ga sunnata to baya tare dani. Allah (S.W.T) yace '' ku auri abinda yayi muku dadi daga mata(Nisa'i:3). Akwai samun nutsuwa da kwanciyar hankali a 6angaren mata da miji. Allah (SWT) Yace 'Daga cikin ayoyinsa ya halitta muku mataye daga kawunan ku don ku natsu zuwa garesu? Ya kuma sanya soyayya da jin kai tsakaninku tabbas a cikin wannan akwai abubuwan lura ga mutane masu tunani kawai.(Rum:21). Manzon Allah yace (S.A.W) yace; '' Muna cewa duk namijin da bai yi aure ba to miskini ne komai yake da dukiya. Haka matar da bata yi aure ba miskiniya ce komai take da wadata''. A 6angare daya kuma duk wanda ya yi aure toya sami rabin addininsa,haka kuma al'umma suna mutunta da kuma fifita mai aure bisa ga wanda ba ya da aure. Idan kika tattara duk wannan bayanan da nayi miki ya isa ki san girma da darajar aure ga al'umma don haka kada ki bari zuciyarki tayi rauni ga gujewa abinda ya wajaba a gareki. Ita ZUCIYA MUGUN NAMA ce ko da yaushe anaso bawa ya dinga neman tsari da sharrinta domin idan ta gyaru gangar jiki ya gyaru,idan ta 6aci gangar jii ma ta 6aci''. ( ALLAHUMMA YA MU SARRIFAL QULUB SABBIT QULUBANA ALA DA'A TIKA) { YA UBANGIJI MAI SARRAFA ZUKATA KA SANYA ZUCIYARMU AKAN DA'ARKA)
.
Tayi shiru daga bayanin data ke yi yayin da Haj Karima ta kai hannu ta share kwallan dake zubowa daga idonta muryarta a raunane tace;
Gwaggo zan yi aure ba zan ta6a gufunsa ba Inshaa Allah zan fitar da miji amma bazan iya auren Alh. Ahmad ba.
Gwaggo zuwai tace Eh hakan ma yayi domin ba zamu tursasa ki auren da bai kwanta miki a rai ba kece zaki zauna da shi don haka idan zuciyarki bata aminta da shi ba ba zaki samu kwanciyar hankali ba Allah Ubangiji ya za6a na gari.
Can kasan makoshi Haj karima ta amsa ''Amin''
***** ***** *****
An shirya ranar juma'a da safe Inna Yaduwa zata zi ta kar6i Shuhuda don yaye ta kamar yadda aka tsara tun farko cewa idan tayi shekara daya da wata uku za a yaye ta.
To tun ranar talata da aka yi maganar yarinyar tayaye kanta anyi-anyi ta kama nono amma taki sai dai tsotson hannun kawai take . Hankalin Haj Karima yayi matukar tashi ganin har yammaci yayi amma shuhuda taki tasha nono abincin ma dan kadan taci kuma babu kuka babu fitina sai ma bacci da take yawan yi.
To a ranar anyu katari Gwaggo zuwai bata nan taje gidan yarta data haihu don haka gidan Haj karima ce kadai. Ta rasa yadda zata yu ita bata ta6a yaye ba hasalima bata ta6a ganin yadda ake yinsa ba saboda mace ce mai matukar tausayi bata son ganin yaro yana kuka yanzu ita ma ta kama kuka.
Ganoin yadda shuhuda taki kama nono sai ta dinga tunani ko dama haka ake yayen kafin ranar tazo yaro ya daina shan nono? An gama sallar magrib Gwaggo zuwai ta dawo gidan Haj karima ta kora mata bayanin duk abin da ya faru. Dariya tayi tace; Ai sai ki gode Allah dama haka wasu suke idan suka ji za a yaye su to sai su yi fushi da shan nono wasu kuwa lokacin ma zaki ga sun tsananta shan nonon.
Saukinmu daya daurin nan ya huda mata jiki don haka idan Allah ya kaimu safiya lafiya sai a kaiwa surukar taki ita..
da Hausa Book stories
MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA)
¤¤05¤¤
Haka kuwa aka yi gari na wayewa Gwaggo zuwai ta goye shuihuda a bayanta ta nufi gidan Inna Yaduwa da ita. Tun bayan tafiyarsu Haj karima shigewa daki tayi ta kama rusar kuka ta tabbata sai wani ikon Allah Shuhuda ta rayu a hannunta saboda ta lura da take-taken surukar tata so kawai take taga ta kar6e shuhudan tunda ai tana gidan mai rasuwar inna yaduwa ta kar6o Isah dan Alh Sada ya dawo hannunta tun daga yaye. Kwana biyu yarinya sai harkokinta take bata kuka sam! Sai dai tana da yawan bacci idan ta farka kuma shiru zaka ji tayi tamkar kurma,haka Isah zai zauna a kusa da ita yayi ta mata wasa. Idan yaje makaranta makaranta yayi mata siye-siyen kayan kwalam da ragowar kudin da ake bashi na tara(break). Shuhuda ta samu wata shida da yaye Allah ya fitowa Haj karimatu miji duk da ba wani kwanta mata arai yayi sosai ba,ta daure ta amince dashi saboda yadda mahaifanta da danginta suka dame ta da maganar aure dadin-dadawa kuma gashi Alh Ahmad na yawan zuwa gidan. Ita kuma ta gama karantarshi tsaf fuskace dai bata ba bashi ba shi yasa bai yi mata maganar ba. Alh Jamilu Ahmad Karare, dan asalin karamar hukuimar Batsari ne a wani kauye mai suna karare cikin jihar katsina Dan kasuwa ne sosai yana da mata biyu da yaya shidda maza da mata. Haj karima ta aminta da aurenn Alh Jamilu ne kawai don ba yadda zata yi ya fito ne 6angaren mahaifinta amma ba tursasata yayi ba, ya dai nuna mata idan ta auri Alh Jamilun zai ji dadi zai yi farin ciki yana da yakinin zata samu zaman lafiya a gidan aurenta. Duka-duka haduwarsu da komai bai fi wata daya ba aka daura aure sati daya zata tare. Ta shiga tunanin yadda za ayi ta kar6o shuhuda daga hannun Inna Yaduwa. Ranar Alh Jamilu yazo gurinta suna zaune a falo ta ke cewa dashi. Alh. Wata alfarma nake roko gurinka. Yana murmushi yace mata. Fada ai kin wuce haka a gurina. Tace Dama so nake na kar6o Shuhuda na riketa a gurina. Yayi jim na wani lokaci sannan yace; Babu komai ai da na kowa ne musamman ma rikon maraya lada ne da shi. Sai dai inda gizo yake sakar da ta nemi a bata shuhuda sam kin amincewa suka yi suka ce ba su yarda Shuhuda tayi zaman agolanci ba dole a hannun Inna Yaduwa zata zauna. Haj karima bata iya musu iya musu ba don haka ta sanyawa zuciyarta dangana ta bar musu Shuhuda. Amma a yadda ta so, ta so ace ta rayu da Shuhuda a inuwa daya domin ta dinga debe mata kewar mijinta data rasa sai dai ba yadda zata yi ita mace ce mai kawaici da hakuri don haka a nan din ma dole hakurin ta sakawa ranta. A haka har ranar tarewa tazo aka shiryata aka mikata gidan mijinta can cikin jihar katsina cikin karamar hukumar Batsari a karare inda gidan Alh Jamilu yake. Tun durar yan rakiyar amarya da ita kanta amaryar suka soma cin karo da cin mutunci saboda matan Alh Jamilu irin matan nan ne na kauye wadanda suka dauki kishi da zafi ,amma kowaccensu baka raina haduwarta ba.don kana ganin uwargidan kaga barumayar asali ita ma ta tsakiyar barumayar ce farare tas dasu illa rashin iya zama da miji da kyautata masa kadai dake dawainiya dasu. Sai uwa-uba kazanta ga rashin iya girki mai dandano ba.
Tun daga yan rakiyar har ita Hajiya kariman ba wanda ya kula da cin kashin da kishiyoyin suke yi haka suka gama komai suka ba wa Haj karima hakuri akan ta jure duk abin da zata gani ga matan nan idan ta yi haka sai ta ga komai ba komai ba. Suka yi mata sallama aka kwashe su cikin motocin da aka kawo su aka koma da su. ***** ****** ****** BABI NA DAYA IDAN AJALI YAYI KIRA........ Shuhuda ta tashi da wata irin bahaguwar rayuwa. Idan tana tsotsar hannun ko abincin bata cika ci ba . Inna yaduwa tayi fadan har ta gaji amma ba abinda ya ragu. Wata irin shakuwa ce tsakanin Shuhuda da dan' uwanta Isah ya kasance komai zai yi yana tare da Shuhuda makaranta ce kadai idan zai tafi yake rabuwa da ita. Har Inna Yaduwa na tsokanarshi tana cewa: Ka gama wayon naka amma baka isa kayi min kishiya da wannan bagidajiyar mai tsotsan hannu ba. Sai dai yayi murmushi kawai wani lokaci kuma yace; Kece bagidajiya amma shuhuda ba bagidajiya bace. Shuhuda tana da shekaru shidda aka sakata a makarantar islamiyya yarinyar tana da kwalwa sosai sai dai matsalar dake damunta tsorsar hannun nan nata. Yan ajinsu su yi ta tsokanarta wai ta girma tana tsotsar hannu bata damuwa don bata yi wayon da zata fahimci me suke nufi da hakan ba. Jarabawarsu ta farko sai ga shi Shuhudan ce tayi na daya har kyautuka aka yi mata a makarantar. Inna Yaduwa ta sanyata a gaba tana cewa: ' Kinga Shuhuda da zaki daina tsotsar hannu da sai kin fi haka kokari saboda mata masu tsotsar hannu ba sa da kokai. Don haka ki daina tsotsar hannu kin ji?? Tayi Shiru kawai ba tare da ta ce komai ba kuma ba ta daina tsotsar hannun ba. Shuhuda tana da kwalwa da kaifin basira ba ta yadda za a yi a koya mata abu ba ta dauke shi a kanta ba. Alh Sada suna matukar kulawa da ita tare da dukiyarta da mahaifinta ya rasu ya bari duk wata kadara tasa tun daga nan gida Nigeria zuwa kasashen waje babu abin da ba a kiblatasu ba kuma an ci gaba da tafiyar da harkokin kasuwancin yadda aka saba tun can baya.
Yau ya kama ranar lahadi Shuhuda tana zaune ita da yayanta yana koya mata karatun Islamiyya a lokacin ba ta fi mintina sha biyar daga tashi a bacci ba. Inna Yaduwa na zaune gefensu tana kallonsu Ta gaza hakuri saboda yadda taga ana koyawa Shuhuda karatu amma ta zurmuka ya tsanta a baki sai tsotsa take yi.
Ta mike tsaye da sauri cike da 6acin rai ta karasa inda Shuhuda take ta sa hannu ta gwa6e yatsan da take tsotsa. Ke kam kin ji haushin kanki kullum a yi ta abu daya dake sai kace mai kwalwar tumaki to na ga kin kara tsotsar hannun a gidan nan.
Isah yace; Ke Shuhuda ki daina tsotsar hannu kin ji ko? Ta yi shiru hannunta na ajiye a kasa Inna Yaduwa ta koma ta zauna akan kujera tana bambamin fadanta. Ai kuwa tana zama Shuhuda ta maida yatsan a cikin baki tana tsotsa Inna Yaduwa ta sake harzuka tace; Wai ni uban me kike tsotsa a yatsan nan ne da ba zaki dai na ba?
Dai-dai lokacin Salmai mai haja ta yi sallama a cikin falon Sam Inna yaduwa ba ta tsinkayo muryarta ba saboda tana rigima da Shuhuda tana son cire mata yatsan daga baki ita kuma Shuhuda ta kiya sai kakaniya suke.
Salmai tace Haba Yaduwa ni da me ye haka? Inna yaduwa tace Bar ni da yar nan Salmai ta raina ni ne, kullum sai nayi fama da ita akan tsotsar hannu amma kamar mai kunnen kashi ta ki ta daina ta maidani mahaukaciya.
Salmai tace Ayyah! Ai laifinki ne idan yaro yana tsotsar yatsa aka yi-akayi da shi ya ki dainawa mai dungurugum ake yi masa sai a samu zaman lafiya.
Inna Yaduwa ta yamutsa fuska cikin rashin fahimta tace. Ban gane mai dungurugum ba? Salmai ta yi dariya dai-dai lokacin da ta ajiye jakar hajarta kasa tace.
Tsarga hannun ake a saka masa borkono gobe ko cewa aka yi ya tsotsi hannun ba zai fara ba. Inna Yaduwa ta ce Ai ni tausayi nake ji bana iya tsarga hannunta da tuni na yi maganin abun.Salmai tace aikuwa idan ba ayi maganin abun da wuri ba haka zata mike har girmanta... Ke har ma ta haihu tana tsotsar hannu ga 'ya'ya a gabanta suna kallo wannan kuwa kuwa ai ba karamin faduwa bane.
Inna Yaduwa ta jinjina kanta tace ; Lallai kam to ni yanzu ban san ya zan yi da wannan 'ya ba taurin kanta har mamaki yake bani ga ta 'yar karama yarinya amma idan ta kafe akan abu babu wanda ya isa ya tankwarata.
Ai haka dama wasu yaran suke akan tsotsar hannu ka rasa me suke tsotsa. Haka kawai yaro ya sanyawa kansa fitina ko abinci sai ki ga sai an yi da gaske yaro ke ci. To ni zan yi miki maganin abun dauko min dakakken barkono da sabuwar reza kiga ikon Allah.
Isah ya yi sauri yace: Don Allah Inna kada ku tsaga mata hannu wannan zalunci ne!......
Inna Yaduwa ta kai mishi bugu. Kai ni rufe min baki sai a bar yarinya ta yi ta tsotsar hannu?
Ta mike a zafafe ta dauko barkono da sabuwar reza ta kawo wa Salmai, amma ta kasa rike Shuhuda wai bata iya ganin tsarga hannun saboda tausayi.
Ita kuwa Salmai ta kama Shuhuda take ta kokarun kwacewa, amma ina aikin gama ya gama. Tuni Salmai ta tsarge mata yatsa.!!!!
Tashin hankali wanda ba a saka masa rana ai ko da tsarge yatsan sai RUWAN NONO fari kal ya dinga ambaliya maimakon JINI!!!!!
Yau mun shiga uku!
Yayin da Isah duk ya kidime ita kam wadda abin ya faru gare ta babu alamar tsoro ko razana a tare da ita sai ma daga yatsan tayi sama tana gyarawa nonon gurin zuba.
Inna Yaduwa tana ganin abin da ya faru ga Shuhuda ita ma kidimewa tayi ta matso gurin tana sallallami. Isah yace; Inna kin ga abin da ake gudu ya faru. Ta juyo da dubanta gare shi tare da cewa :
Yi sauri ka kira min mahaifinka a waya. Jikinsa na mazari ya kira lambar Alh Sada kara daya ya dauka yace: Ya dai Isamanu dan maryama? A figice Isah yace Abba kazi inji Inna za a kai Shuhuda asibiti
Alh Sada yace Me ya samu Shuhudab ne???
.
Isah yace Rauni ne a hannunta. Yace To gani nan zuwa. Inna Yaduwa ta dubi hannun Shuhuda har yanzu nonon ne yake tarara iya rudewa kam ta rude da wannan murdadden al'amari.
Ita kuwa Salmai tsuru-tsuru ta yi hankalinta a matukar tashe ta rasa yadda aka yi hakan ta faru ita dai a saninta jini ne a jikin kowanne dan Adan, to ya akayi ita Shuhuda aka samu akasin haka?
Gaba daya jikinta nono ko kuwa a yatsan nata kadai ne ke da nonon a maimakon jini? Idan a yatsan kadai ne ke da nonon shi ta ke tsotsa maimakon kiwo(feeding) nata? Wannan wani bakon al'amari ne mai rudani da daure kai. Su dukkansu aka rasa mai abin cewa kowa yayi shiru da abin da yake sakawa a cikin ransa.
Ba a fi mintina goma sha uku ba Alh Sada ya dura a gidan Ko da ganin abin da yake faruwa hankalinsa ba karamin tashi ya yi ba ya dubi Inna Yaduwa yace; Inna ta ya aka yi haka ta faru.
Inna Yaduwa tace To tsautsayi ne da ba ya wuce ranarsa Ba musan hikimar tsotsar hannun da Shuhuda take ba na sa aka tsarga hannun ashe nono ne take sha a jikin yatsan?
Alh sada ya jimanta lamarin sannan yace; To shikenan Allah ya kyauta gaba ku taso muje clinic a dinke mata yatsan. Inna Yaduwa Isah gami da Shuhuda suka mike tsaye yayin da salmai take zaune a guri guda ta yi tsuru-tsuru da ita sai kace kazar da aka tsamo a cikin ruwa.
Kai tsaye suka nufi kofar fita sai a sannan Salmai ta samu damar matsawa ita ma tabi bayansu suna fita mota suka shiga ita kuwa Salmai ficewa tayi daga gidan da jakar kayanta tana tafiya sukuku kamar mai tsoron taka kasa.
FABCY CLINIC suka je Dr Ya'u ya jagorancui dinke yatsan /huhuda wanda har suka iso asibitin bai dai na ambaliyar da ruwan nono ba.
Abin mamaki duk inda aka sa allura don dinkewa a jikin yatsan sai gurin ya 6ule nono yayi ta tarara. Shi kanshi Dr Ya'u ba karamin firgici ya shiga ba da ganin yadda lamarin ke gudana.
.
.
Toh pa, ni ma se da na rude har waya ta ta pada ruwan jikin shuhuda...
Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA)
¤¤06¤¤
Da ya ga haka sai ya dauko wani garin allura ya zuba a cikin raunin ya kawo bandeji ya lika mata sannan yayi mata allura. Yana cire tsinken allurar daga jikin Shuhuda zance ya sake shan bam-bam domin tsinken allurar ya karye a jikinta.
Da sauri aka shiga theater room da ita aka samu da kyar aka tsinke allurar daga jikinta koda yake ita dakanta ta cire. Daidai lokacin ruwan nonon ya daina tarara sai wani irin nannauyan bacci ya sure ta.
Dr Ya'u ya fito daga dakin tiyatar ya dubi Alh sada yace Alhaji dole sai ta kwana saboda gaskiya yanayin jikin yana bukatar kyakkyawar kulawa.
Kaga bayan an samu an yi mata tiyata an cire tsinken allurar sai wani zazzafan zazza6i ya rufe ta. Yanzu dai ta samu bacci don haka ku yi hakuri ta kwana zuwa washegari sai a sallame ta idan komai ya dai-daita.
Alh Sada ya sauke gauron numfashi cikin matukar jimami yace: 8abu komai Allah ya kaimu goben lafiya ya kuma bata sauki.
Gaba daya suka amsa da ameen. Alh sada ya dubi Inna yaduwa yace Bari naje na kawo miki abubuwan da zaki bukata na amfani. A'ah bara mu je tare ai bacci take har maje mui dawo.
Yace To. Suka shiga dakin da shuhuda take tana kwance tana ta sharar baccinta don haka suka fito su duka ukun suka nufi gida. Sun isa gidan Inna yaduwa ta shiga ciki ke nan wani yaro ya shigo yace; Inna wai ance a fada maki SALMAI MAI HAJA ta RASU. Inna yaduwa ta zabura tare da doka sallallami ido waje tace Salman ce ta rasu? Yanzu fa muka rabu da ita? Yaron yace Eh mota ce ta kade ta take wuyanta ya KARYE, Yanzu ma za arufo ta.
Inna yaduwa ta sake jan sallallami ta dure tace; IDAN AJALI YA YI KIRA koba ciwo sai an tafi. Yanzun nan fa tabar gidan nan? Ta karashe magana tana nuna matukar alhininta. Yaron dai ya yi shiru yana sauraren ta.
Alh sada ya shigo cikin gidan ganin ta jima bata fito ba. Ya tarar da ita cikin halin jimami yace; Inna ya baku fito ba? Kada fa ta farka babu kowa a kusa da ita.
Tace.
Tace Mhm kai dai bari wai Salmai ce ta rasu!! Yace wace Salmai? Tace salmai mai haja mana yanzun nan fa ta bar gidan nan bayan ta tsaga hannun Shuhuda wai mota ta kade ta.
Ya ce Allah sarki kila tsabar rudewa ce ta sa ko gabanta ba ta gani har hakan ta faru. Allah dai ya jikanta ya rahamsheta. Tace Amin jiki ba kuzari ta hada kayan da zata hada suka nufi asibitin. Har lokacin Shuhuda bata farka ba bacci kawai take yi.
Alh sada ya yiwa Inna yaduwa sallama ya tafi tare da Isah suka barta a nan. Sai a washegari ne misalin shida da rabi na safe shuhuda ta farka. Karfe takwas yan uwa da mutanen arziki aka yi ta zuwa ganinta da yi mata sannu da jiki. Misalin sha biyu na rana aka sallame su suka dunguma gida.
******** ********* ******
Zaman gidan Alh jamilu dai babu dadi domin sam karima ba ta da sukuni matansa ba sa sonra sun tsane ta musamman yadda suka ga yana riritata yana kulawa da ita.
A ganinsu ya bam-banta su shi kuwa duk abin da yake yiwa karima ya na yi ne don mantar da ita alhinin rashin tsohon mijinta saboda a zahirin gaskiya karima ta yi rashi babba wanda take bukatar samun wanda zai maye mata gurbinsa.
Alh jamilu adalin namiji ne kuma jarumi gwarzo yasan duk wani salo na soyayya don haka ya yi amfani da wannan damar ya mantar da karima bakin cikin da matansa ke kunsa mata.
Koda yake a wani 6angaren ba ya da masaniyar irin zaman doya da manjan da ake yi a cikin gidan nasa. Saboda ya kasance mutum ba mazauni ba dan kasuwa ne da ke kewaya kasashen duniya.
Ta 6angarenshi kam karima bata da matsalar komai domin ta samu nagartacciyar kulawa daga gare shi matsalarta ga matansa take su ma yayan nasu basu kyalle ba ne domin sam yaran basu da yarbiyyar to su ma ba ta ishe su ba bare su baiwa wasu.
Rashin kunya kamar sa doke ta duj ranar girkinta yaran da iyayensu sun dinga yi mata korafi kenan.
Rashin kunya kamar sa doketa duk ranar girkinta yaran da iyayensu sun dinga korafi kenan wai tana rage kudin cefane. Bayan komai akwai shi a cikin gidan tsakanin mai gidan da matan alheri ne ba ya baiwa mace kudin cefane amma don rashin adalci sai suke cewa tana rage kudin cefane.
Wannan dalilin ya sa karima ba ta zama a falo koda yaushe tana cikin dakinta.
Idan ka ganta a waje to kicin ko bandaki zata shiga kasancewar bandaki daya ne a tsakar gida wanda kowa yake amfani dashi sai kuma na shi mai gidan shi kuma idan ba mace ke da girki ba ba ta da damar shiga.
Duk cikin yaran babu wanda yake kulata da maganar arziki ko gaishe da ita ba sayi to bata damu da hakan ba domin ba zamansu take yi ba. Zaman aure take shi kam zaman aure dan hakuri ne dama da mijin ta ke samun matsala wannan da da ciwo. Duk da wannan din ma da ciwo saboda zaman tare wani babban al'amari ne mai girma yana bukatar shakuwa da juna kyautatawa juna gami da taimakekeniya. To su lamarin matan Alh jamilu ba haka bane irin wannan banzan kishin ne suke na kauyanci kai yanzu ko a kauye a daina irin wannan kishin na hauka. Sam babu ragayya ba ta da ikon ta kwanta ta huta muddin aka ce ranar girkin ta ne. Habaici ko da yada bakaken maganganu abin ba a cewa komai har ma ta saba. Karima na kicin tana dafuwar miya ta gama kwashe tuwo miyar ce take son kadawa. Binta uwargidan Alh jamilu ta shigo kicin din tana bangaje karima ta dauko roba. Karima ta ja da baya sam batayi mamaki ba idan da sabo ta saba da irin wannan cin kashin da ake yi mata a gidan. Sai dai a ganinta izuwa yanzu yaci ace sun tsaya sun gina rayuwa mai kyau a tsakaninsu wannan zafin kishin babu inda zai kai su illa halaka. To amma ba yadda za a yi matan ne gasu nan dai kurum. Binta har ta kai kofa zata fita sai ta juyo tace; Allah wadaran naka ya lalace jakin dawa ya gana birni, Mace ba kyau ba ba siga ba amma sai shegen kilibibi da karfar baka to ni dai wallahi karyar duk wata juya bata isa ta fitar da ni a gidan mijina ba kowacce shegiya nan tazo ta tarar da ni don haka idan ban fidda mace ba ta yi kadan ta fidda ni.
Karima tace Me ya kawo wannan maganar kuma? Binta tace Ban sani ba sai na ji makara don na lura kwanan nan wani karfi karfi kike ji idan kina magana tamkar zaki daki mutum. To idan kin isa kina ganin kanki ke wata abace ki kwa6e mu daku, kiga idan akwai kutumar da zaki diba a jikina. Karima ta girgiza kanta tace Ni kam bazan iya fada da ke ba ba ma ke ba ni a rayuwata ba na fada kowa kika ganni da shi burina na zauna da shi lafiya. Binta ta daka mata tsawa tace Rufe min baki bakar munafuka baki fada da kowa amma kin iya karfar baka ko? Kin iya ki kalallame miji ki raba shi da matansa ki raba shi da 'yayansa? To wallahi kin ji na rantse miki kin yi kadan kin yi tsururu a gidan nan muddin kika ce wannan mummunar dabi'ar zaki tsuro a gidan nan. Karima tace: Allah ya baki

Please Login or Register in order to submit comment