Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

uku, manzon Allah (S.A.W) y ace, “ka so wad an uwanka abin da ka so wa kanka”.
Dukkan mu nan ababen halitta ne, banbancin jinsi shi ke tsakanimun, amma mu duka wajibinmu ne mu bautawa Allah.
Tun da kuwa mun yi tarayya akan abu daya (bautar Ubangiji) sai mu yi amfani da wannan hadisi mu sowa ‘yan uwanmu a musulunci abin da muke so wa kanmu.
Kiran da zan yi a gare ku, ba ku kadai ba duk wata al’umma da wannan labara zai kai gare su shi ne, kada mu yi sakaci da neman kariya daga shidan mai kawata mana MATA’UL-HAYAT (Kyale-kyalen rayuwa) a zukatanmu.
Iyaye su tsaya tsayin daka gurin sauke nauyin da Ubangiji ya dora musu na tarbiyyantar da ‘ya yan dashi (Allah) ya bas u amana.
Idan yaro ya samu dukiya a bincika cikin hikima a ga ta ya ya sameta?
Wane irin aiki yake da dukiyar?
Su waye mutanen da yake mu’amala da su?
Hakika idan iyaye suka bi wadannan hanyoyin ‘ya’ yansu za su kasance tsakanin Katanga daga shaidan, Allah zai kare ‘ya’ yan nasu daga fadawa halaka ba domin saka idanunsu ba, a’a shi (Allah) Yana kare bawansa a duk lokacin da ya so, amma wanna ma hakki ne da ya rataya a wuyan iyaye na kula da yadda ‘ya‘yansu ke a rayuwa.
Allah Ya yi mana jagoranci a bisa aikin a gari, Ya kare mu daga sahrrin shaidan (La’ananne), Ya shiryar da zukatan mu bisa tafarki na gaskiya alfarmar Sayyidul sadati”. Gaba daya gurin aka amsa mata da.
“Amin”.
Uncle Hamza ya dago kansa da ke rusune a kasa, y ace. “ni na sadaukar da rayuwata, zan je tsuburin domin kubutar da Shuhuda”. Jin abin da ya fada ya harzuka Isah, wato ma Uncle Hamza har ya fi shi son Shuhuda ken an da zai sadaukar da rayuwarsa a kanta?
Lallai ba zai amince da hakan ba, domin shi ne mutumin da yafi cancanta ya yi komai akan Shuhuda, shi ya fi dacewa da wannan sadaukarwar ko da ace ita zata rayu shi ya mutu, yasan har karshen rayuwarta ba zata manta da sadaukarwarsa ba.
Amma kuma idan ya mutu a gurin sadaukarwa Shuhuda ta rayu, shi ken an sai ta auri Uncle Hamza, ya same ta a sanga? Zuciyarsa ta karaya, ya ji wani kunci ya dirar masa a zuciya, karo na farko tsanar marigayi Alh. Sagir ta tsira masa dukkan bargon jikinsa domin bas hi ba hakan da ta faru ba.
Ga shi ya tafi ya bar su da azal mai razanarwa da rudar da hankali! Wani bangare na zuciyara kuma ya shawarceshi, kawai ya sadaukar, ko da ya mutun Uncle Hamza ya auri Shuhuda haka Allah Ya tsaro, kuma bas hi doron kasar bare abin ya dame shi.
Wannan shawara da zuciyarsa tab a shi ya sa yayi saurin cewa.
“ni ne zan sadaukar da rayuwata don ceto ‘yaruwata Shuhuda , tunda daman can ni din na sadaukar da rayuwata a gareta saboda a dalilin Shuhuda tsayin zamana a kasar Senegal ban taba mu’amala da wata ‘ya mace ba, itace na ba wa zuciyata tun kuruciya, don haka yanzu ma zan bata rayuwata don inganta rayuwarta”. Uncle Hamza yaji gaban say a yanke ya fadi, tsoro mai tsanani ya shige shi, a yadda ya ga fuskar Isah ya ayyana zai yi bakin naci kuma ga alama yanzu ma nacin zai yi!
Shi kam yana son Shuhuda kuma yana son nuna bajinta,ko don duniya ta shaida irin son da ye mata tsayin lokacin da ya soma ganinta (RIYA)
Kafin ya tanka Yakub y ace. “Dukkanku za ku iya jarraba sa’a domin mai nema yana tare da samu, kuma ba a san maci tuwo b sai miya ta kare. Sai dai ina so dukkanku ku nutsu ku san cewa Allah (swt) Ya haramta riya (yi don wani) a cikin littafin Ahlari an bayyana hakan. Idan kun san zaku yi aiki don riya ku sani aikin naku haramtacciya ce.
Su duka biyun wuta ta dauke musu, domin kowannensu ya gano kuskurensa akan abin da zuciyoyinsu suka kissima musu, wato zasu sadaukar da rayuwarsu domin duniya ta sahaida irin son da suke yiwa Shuhuda. A bangaren Uncle Hamza sai ya ga abin da zuciyarsa ta kissima masa bai isa ya zamo riya ba, tunda dai hark ace ta ceto masoyi daga halaka.
Yayinda bangaren Isah ya gano lallai idan ya sadaukar da rayuwarsa akan ceto Shuhuda don duniya ko ita Shuhudan su san irin dumbin son da yake mata, babu “Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un, La haula wala kuwwata illa billahil aliyul azim, subhanaka inni kuntu minaz alimeen”.
A cikin zuciyarsa, sai ya ji ya samu nutsuwa, ya kuma tabbatar zai sadaukar ne domin Allah makagin duniya da lahira da dukkan abin da suke cikinsu. Yakub ya yi murmushi , tukkunna y ace , ”Dukkanku kun amince wa zukatanku zaku iya sadaukar da rayuwarku domin ceto rayuwar Shuhuda Alhamdulillah kamar yadda na fada muku mu zamu dauke muku nisan tafiyar, ba gudu ba ja da baya kuma har kullum kamar yadda muka fara hidima Khashim Tsagem zuwa tsatson sa insha Allah zamu ci gaba da yi har karshen rayuwarmu”.
Alh. Rabi’u ya jinjina kai y ace, “mun godewa Allah mun gode muku, Allah Yayi mana jagoranci akan komai”. Shuhuda Ibn Khaddab ta dubi inda matasan samarin suke, t ace, “Isah da Hamza ina so na baku shawara, ku zamo mutane masu hankali da nutsuwa, idan n ace hankali ina nufin masau amfani da baiwa da Ubangiji Ya yi musu, masu jajurcewa da mayar da lamari ga Ubangiji, wadanda bas u dauki rayuwar da zafi ba. Masu so wa dan uwansu abin da suke so. Iadan kuma n ace ku kasance masu nutsuwa ina nufin, kada ku yi sakaci wani abu kalilan ya hargitsa ku, ya juyar muku da tunani hark u diga wasu-wasi wajen mayar da lamari ga Ubangiji.
Idan kuka kasance masu hankali da nutsuwa, hakika bau wani abu da ba zaku cimma nasara ba insha Allah”. Abubakar ma ya dora da cewa.
“hakkun ‘yar uwa, idan mutum ya kasance mai wadannan dabi’o’in lallai y agama dacewa, shi yasa ma ake so bayan mutum ya mallaki hankali da nutsuwa ya kasance kuma maizurfin ilimi, don su hankali da nutsuwa sun a samuwa ne ga bawa musamman baiwa daga Allah. Amma samun ilimin sai yakarawa bawa kwarjini a idanun wadanda ke kallonsa”.
Uncle Hamza ya kasa hakuri ya boye kishinsa, fuskarsa ta nuna hakan muraran, amma bakinsa bai furta ba. Shi kam Isah ya kosa ya je sadaukarwa, yana son ganin Shuhuda, yana kuma jin tausayin halin da ta samu kanta a ciki , ashe duk wannan rudaddun al’amuran da ke faruwa game da ita akwai boyayyen sirri? Hakika ba don Allah Ya so su da rahma ba Ya kawo su Yakub a cikin rayuwarsu lallai da sun yi BABBAN RASHI na tsatson su.
.
To 'yan uwa masoya Shuhuda, wa zai sadaukar???
ada Hada Hausa Book stories
MATA’UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤32¤¤
.
WANNAN PAGE IN, SADAUKARWA CE GA DUKKAN MASOYA NA WANNAN GROUP MAI ALBARKA
.
Wannan ma abin godiya ne matuka ga makagin sammai da kasai.
Shuhuda Ibn Khaddab ta kai dubanta ga Isah fuskarta da yalwa ta ce.
“A cikin budaddiyar wasika na fada maka zoben da ka ba wa shuhuda yana hannuna bisa wani dalili, kuma a cikin labarinmu ba mu yi maganarsa ba, to ka sani dalilin da yasa na dauke zoben shi ne, za a yi amfani da shacin yatsanka ta jikin zoben a shaye jininka, shi yasa ni ban ga amfanin zobe ba, wannan shi ne dalilin da yasa na dauke zoben”.
Isah ya yi godiya da wannan karamci da aka yi masa.
Dakin ya dauki shiru na wani lokaci, kowanne da abin da yake cikin ransa.
Sai zuwa can Yakub ya buda baki, y ace.
“Gobe idan Allah ya tashe mu lafiya ya kamata a yi tafiyar zuwa sokoto, saboda wasu dalilai da nake ganin alamun nasara ta hanyarsu.
Na farko dai, goben ta kasance lahadi, ranar jajibirin kafuwar kungiyar EROSU mai tambarin kwalwar kai, kuma a irin ranar yan kungiya sukan huta hasalima ba sa shan jinni a irin wannan ranaku.
Kum a irin wannan ranar ma ko da ace za a tarwatsa kungiyar ne to za a iya samun nasara, wata kila kuma akasin haka. Don idanun masu sirri kaifin haske gare su na sirri, amma da ya kasance an samu kaifin haske na ALKUR’ANI to la shakka kaifin haske na masu sirri zai koma DUHU.
Saboda haka lahadi it ace ta cancanta a yi wannan tafiyar, sai ku zamo cikin shiri karfe bakwai na safiya Insha Allah zamu tafiyar.
BABI NA ASHIRIN
GA FILI GA MAI DOKI…
Tun bayan da Uncle Hamza ya baro Gidan su shuhuda ya shigo dakinsa ya yi zugum, zuciyarsa na ayyana masa abubuwa masu yawa.
Hakikanin gaskiya shuhuda it ace mace ta farko da ya soma so a rayuwarsa, so kuwa ban a was ba, bayan ita bai taba son wata ‘ya mace ba’.
Zuwairiyya ita ke haukan sonsa, shi kuma ko a kwalar rigarsa, bai ga inda zai dasa wata kwayar son Zuwairiyya a zuciyarsa ba bare hart a yi tsirran da sonta zai samu muhalli a tare da shi.
Kallon da ya yi wa kwayar idanun Isah sai da zuciyarsa ta harba, domin ya ga sirrikan so masu tarin yawa a cikinsu, so irin wanda ya jima datsirga jinin jiki.
Ke nan zai sha fama da zogin zuciya ko da ya auri shuhuda tunda akwai alaka tsakaninta da Isah, dole wata rana za su hadu, idan sun hadu wane irin kallo Isah zai yiwa shuhudan?
Irin wanda ya gano a cikin kwayoyin madarar idanunsa?
Cab! Ashe shi ma dai yana a nasa salon kishin bai sani ba?
Ya yi juyi akan gado tare da rungumar filo, ya tuna yadda murdaddun al’amuran suka dinga faruwa har kawo wannan lokaci, hakika akwai so mai karfi da yake yiwa shuhuda.
Sai ya soma ayyana yanayin da ta ke ciki a yanzu, wai gat a can a tsakiyar jeji daure cikin sasari irin wanda ake daure dawakai, numfashinta na fita sama-sama.
Zumbur! Ya mike tsaye cike da tsoron abin da ka iya samun shuhuda.
Hannayensa ya soma bugawa a hankali, tare da cizon lebensa na kasa yana tattaki, wata zuciyar ta yi masa matashiya me yasa tun farko bai jajurce don gano sahihin abin da ke damun shuhuda tun kafin a kai ga wannan matsayi
Tabbas ko a zantukanta ya kamata ya gane wani abu makamancin haka, sannan kuma daukar hoto da suka yi da shuhuhan ya yi sabaninta da kiran waya wadannan duk sunyan jigogi ne da ya kamata ya gano abin da ke faruwa da shuhuda.
Ta tab ace masa ita sarauniya ce, ashe da gaske sarauniyar c eta matsafa?
Wa’iyazubillah, rayuwa mai kunci ken an, yarinya karama bat a san hawa ba bare sauka amma azal ta fada mata.
Shin ya matsayin mutanen da aka hallakar ta sanadinta? Hakkin kisan akan way a rataya? Bai sani ba, amma yana da yakinin shuhuda bat a da kamasho, saboda baita ke yin kisan ba, ana yi ne saboda ita.
Kuma ba ita ta kai kanta kungiyar matsafan ba, an kai ta ne tun kafin hankali ya shige ta.
Shin zai iya sadaukarwar ma don ceto rayuwarta?
Idan su duka biyun suka yi nasara suka dawo da ita ba tare da wani ya hallaka ba, ya za a yi?
Wa zata zaba cikin su biyin biyin shi ko Isah? Tunda dai dole namiji daya ne zata aura, ba duka biyun ba.
Har dare dai bai samu kwanciyar hankali ba, akwai son shuhuda a ransa, haka kuma akwai tsoron abin da zai biyo baya idan shuhuda ta kubuta ta zabi dan uwanta sama da shi!
Shi din ma bangaren Isah bai samu nutsuwar ba, tunaninsa bai wuce ta ya zai yiwa Uncle Hamza kub daya ba.
Lallai so marurun zuciya, duk irin son da Uncle Hamza ke yiwa shuhuda a hasashe ba za a kwatanta shi da wanda Isah ke yi mata ba, domin salon son Isah daban ne mai tafiya ne a jinin jiki, wanda yak e tsittsinka jijiyoyin jiki, ya makantar da kurumtar.
Dai-dai lokacin da y agama gyara makwancinsa, ya kishingida akan katifar yana tuno abuburwan da suka faru tun haduwarsa da shuhudan Misra har kawo yau, ashe boyayyen al’amuri ne zai fito fili?
Ya tuna lokacin da suka je Katsina, Shuhuda ta ce zata yi masa kyautar dan mutum har tana tambayarsa ko ba ya so, ken an dama manufar furucin ke nan?
Ya dai shiga rudani da shi da kansa ya saka kansa, domin da ya yi la’akari da labarin da aka bas u da bai ja ba, lamari da aka saka jinnu a ciki zasu aika.
Yanzu abin da yake cikin zuciyarsa shi ne, addu’a Allah ya bas hi juriya da jarumtar da zai iya sadaukar da rayuwarsa saboda Allah ba don wani ba, ya sanya a ransa idan ya samu nasara ta sanadinsa, shuhuda ta kubuta falillahi hamdihi, ya yi hakan ne domin Allah ba don shuhuda ko wani nata su yaba masa ba, domin shi a rayuwarsa ya tsani abin da zai yi don wani ya yaba.
Shi yasa ko lokacin da yana Senegal idan suna group discussion ya kawo idea da zarar ya ji wani ya fara yi masa godiya zai bar gurin, haka ko irin assignment din nan aka bas u ya taimakawa wani bay a bukatar a yi masa godiya, har ma wasu suka yi masa lakabi mai sadakatul jariya musulmai ken an!
Isah yana da kyakkyawar zuciya abar so da koyi ga kowa, don da ace matasa zasu yi koyi da irin halayya ta Isah, ko shakka babu rayiwarsu zata inganta, ta zamo abar kwantance.
Daren ranar asabar Isah da Uncle Hamza bas u runtsa ba, kowanne da yanayin da yake ciki.
Kusan a tare zan ce sun sami bacci, bayan sallar asuba ken an, wanda sun farka ne sun gansu a wari daya su duka biyun a cikin kungurmin daji bisa wasu buzaye.
Mamaki ya cika su ta yadda lamarin ya faru har suka soma tunanin ko a mafarki ne suka samu kansu a muhalli daya.
Isah ne ya soma yin Magana bayan dogon lokacin da suka dauka suna duban juna, inda yake cewa.
“Ta ya na ganni a wannan guri, ko mafarki nake yi ne?”
Shi ma Uncle Hamza hakan ya furta, su duka biyun suka rasa amsar da za sub a wa inna, sai dube-dube da waige-waige suke a tsakaninsu, babu gida a gaba bare a baya ko gefensu.
Daji ne sosai ga manyan bishiyoyi suna ta rangaji fiska na kada rassansu.
Duba da yanayin da gurin ya nuna zai iya shaida musu rana bat a yi sosai ba, hasalima za a iya kiran lokacin hantsi ya daga gari ya shaaa, saboda ransar ba ta da kaifi.
Suna cikin wannan yanayi na tababar gaske ne ko mafarki suka hango Yakub na saukowa daga wata bishiyar Rimi, fuskarsa dauke da fara’a.
Babu wanda ya samu dammar furta wata kalma har ya karasa saukowa ya iso gabansu. Tare da mika musu hannu don yin musabiha,bayan sallama da ya yi musu.
Babu wandan ya noke suka ba shi hannayensu suka yi musabihar, don sun yardarm wa kawunnansu yakub ba mai cutar da su ba ne,kuma ganinsa ya tabbar
Musu da duk yadda aka yi shi ne sanadin wanzuwar su a gurin.
lle-kuwa bayan gama musabihar yakub ya dora da cewa.
‘’kada ku wahalar da zukatanku wajen tunanin wanzuwarku a wanna bigire, domin ni ne na kawo ku bisa alkwarin da na dauka na yanke muku nisan tafiyar da ke tsakanin kano da sokoto.
A halin yanzu kuna cikin jejin da shuhuda ta ke a daure, tafiya kadan ce zaku karasa tsuburin. Kamar yadda na fada muku jiya cewar idan kun isa tsubum bannu ba zai iya kunce shuhuda ba, tabbasa haka abin yake.
Suratul waki’a ita za ku kalanta a yayin da kuka isa inda shuhuda ke daure, da yardar.Assamadu za ku kasance masu nasara. Sai dai abin da nake so da ku shi ne, ku zamo masui sadaukarwa, ma’ana ku yi rai ko akasin haka’’.
Ya dan saurara yana dubansu daya bayan daya, su din ma dubansa suke yi a nazaree
Tsayin mintina ba tare da wani ya tanka ba,sai can daga bisani yakub ya ci gaba da eewa.
“masu sirri wasu irin hatsabiban mutane ne, dole sai kun kasance cikin neman tallafi daga basani yakub ya ci gaba da cewa
“masu sirri wasu irin hatasabiban mutane ne , dole sai kun kasance cikin neman tallafi daga lillahi , ko da yaushe ku yi ta rook don shi mai rook ga mahalicci bay a zama kaskantancen bawa . kuma mahalicci yana son bawan da yake rokonsa ba don rokon yana amfanar da shi (Allah) kamai ba, face shi bawan da ya mayar da lamiri gare shi (Allah ) don haka abin da zan ce, GA FILI GA MAI DOKI , Allah ya ba wa mai rabo sa’a, yak are ku daga hatabibancin masu sirri, ya makanatar da su daga ganiku. Ya kawo tallafi da zaku zamo sila ta rushewar majalisin da ake farautar bayin Allah .
Majalisin da kafuwarsu bai zamo riba ga addinin musulunci ba, sai dauki dai- dai da ake yiwa bayin da ba su jiba ba su gani ba
Gaba dayansu suka amsa masa da
Amin
Yakub ya nuna hanyar da ta yi arewa ya ce
I dan kuka bi wannan hanyar tafiya kadan zaku yi ku tarar da wani fili daga nan sai tsuburin Allah Ya bada sa’a
Yana karashe fadar hakan suka neme kallon –kollo a tsakaninsu , kowanne fuskarsa turbine babu almar fara’a ko kadan
Uncle hamza ya dan ja gajeran tsaki ya soma taku da nufin tunkarar hanyar da yakub ya sanar musu zata sada su da tsuburin da shuhuda ta ke
Ganin uncle hamza ya nufi gurin sais hi ma isah ya yunkura da karkarfan takunsa ya tunkari hanyatr, su duka biyan sauri da azama suke ba tare da wani ya kula wani ba, a kasan zukatansu kuma suna ta yiwa kawunnasu addua
Wani ma keken fili suka yi tozali da shi fari fat da shimfidadden yashi ya yi shamal tsaye suka yi suna fuskantar juna, domin iya hangensu ba su iya hango karshen wannan fili ba, alhalin kuma an ce tafiya kadan ce za su yi su ruski inda shuhuda ke zaue
Ga su dukkansu sun kasance masu son abu daya bare us tambayi juna shawara
Yanayi fuskokisun kadai zaka kalla ka gane karayar da zukatansu suka yi muraran .
“ akwai matsala “
Isah ya ambata a ransa wannan yanayi da suka sami kansu ciki kadai ya is is aya sanar musu babu nasara a wannan yunkuri nasu
Tsayin mintina babu wanda ya mostsa, dace kuma wanda ya iya lalubo abin da ya dace ya yi a cikinsu
Isa shi ya yi jarumatar daga kafa ya soma tafiya yayin da uncle ya yi isah idanu yana yaba jaruntarsa, bai sani ina ya nufa ba.
Duk yadda yake ganin zai iya sadaukarwa don ceto shuhuda yanzu ya samu karaya ., koda yake a gurinsa bai ga laifinsa ba, iyakacinta ba, kwatan –kwacin a ajiye ka dakin da babu digon haske ace ana so ka lalubo kofa
Isah kuwa tafiya yake cikin rashin tsammani , yana kuma karanto duk adduar da ta zo bai san , abin da ya sanyanwa ranshi koda ace zai karashe rayuw a ta tsayin shekaru goma a wannan fili yana da fadi ba tare da ya san inda shuhuda ta ke ba, lallai ba zai yi kasa a gwiwa ba zai ci gaba da wanzuwa a gurin
Kamar yadda cikin littafin alhlari aka ce, wanda ya yi hijira domin Allah da Manzonsa, hijirarsa nag a abin da ya yi niyya, ya riga ya sanyawa ransa zai yi komai don ceto shuhuda mastsawar bai kaucewa addini ba, domin Allah
Ya yi nisa sosai a tafiyar tasa, har ya kasance nisan da ke tsakaninsa da uncle hamza zai kai na kilo mita ba zato ba tsammainni ya hango wani katon dutse a samansa turun hayaki ne yake tashi karmar an hura wuta.
Gabansa ya yanke ya fadi , koda ya yi rayuwa a senagal inda suke zuwa gurin duwatsu don yin nazari bai taba jin faduwar gaba ba idan ya ga hayaki sai da ya samu kansa a cikin firgici
Watakila hakan bay a rasa nasaba da lokacin da suka soma hango filin ba su ga karshiensa ba karmar yadda sam bas u hango wannan katon dusten ba , tunda tunda kuwa yanzu dutsen ya bayyana baa bin wahalar da kai ba ne , don an yi mamaki .
Samum saukin raguwar faduwar gaban nasa ya biyo bayan saurin lalubo aduo I da ya yi sai ya samu nutsuwa, har ya ji wani karfi ya zo masa. Ckikin azama ya tunkari katon dutsen ,ya matsen masa sosai , sai ya hango shuhda daure cikin sasari, irin wanda ake daure dawaki da su
Ta yi ligib idanunta a rufe ruf da alamas ko baccie ta ke, ko kuma babu numfshi a jikinta
Kusan rikicewa ya yi , har ya manta da yin tsinkaye da gargdin da yakub ya yi masa ya ruga da gudu da nufin isa gurin, zuci yar sa na harbawa kamari zata tsago kirjinsa ta fito .
Bisa tsautssay I kafaluwansa suka harde ya fadi a cikin yashi . ya jima kafin ya dago kai yana hango shuhuda , ga ta kamar a kusa da shi, amma akwai tazara sosai kafin ya isah inda take
Cikin rashin kuzari ya mike tsaye , wannan karon nutusuwa t a zo masa , ya yi saurin ambaton . “ innallahi wa inna illahi raju un “
Tukunna ya soma taku bisa diga -digan kafarsa babu ko takalmi , hasalima bai san ta ya ya watsar da sub a
Ya isa gab da inda ta ke ya yi tsaye yana kare mata kallo , sannan ya soma karanto suraturl wikia daga farkonta zuwa karshe
Yana dire aya , duk igiyoyin da jke daure da shuhuda suka tsinke, ta bude idanunta da sauri kamar wadda ta farka daga nannauyan bacci, ta ambaci
“ subhannaallah”
Cikin attausan lafazi , sannan ta soma akarewa gurin kallo
Ganin a inda ta ke da kuma isah da ke gabantan ya daga mata hankali , ta fashe da kuka tana cewa
Yah isah me yasa zaka yi min haka ? me na yi maka zaka kawo ni a cikin wannan bakar dajin? Ina rokonka alfarma kada ka keta min haddi , kayi min hakuari kada ka bata min rayuwa
Jin kalaman da ke fitowa daga bakinta ya tabbatar masa ba tasan duk wainar da ake toyawa ba . maganar yakub ta fado masa a rai inda yak e cewa , da zarar igiyoyin suka tsinke a yi kokarin barin jejin , domin a lokacin komai zia iya faruwa, masu sirri za su ji kubutar shuhuda a jikinsu
Sai ya ji wani karfi y a zo masa ya samu karfin gwiwar fizgar hannaunta yana mai karantao audo’iI ya soma gudu da ita
Yayin da ita kuma ta ke ta tsala kuka tana rokonsa kada ya bata mata rayuwa
Kamar hadari suka hanga a gabnasu iska mai matukar karfi ta taso wanda har ba su iya bude idanunsu illa yana ambaton Allah akan harshensa. Ya kuma rike hannun shuhuda gam, iskar ta raba su kamar daukewa wutar lantraki, sai ya ga komari ya yaye
Shuhuda ce a hannun wasu irin mutane sun kai mutun shida , kowance da shuhuda a hannunsa tana kuka, tana cewa .
“ yah isah . wyyo yah isah za su kase ni, za su sha jinina , ka taimake ni haya isha “
Kansa ya daure hankalinsa ya tashi , ya rasa wa zai kwata, wace ce shuhuda ta gaskiya a cikin su shiddan da ke hannun miyagun mutanen
Cikin dakiyar zuciya ya yi kabbara yana kiran sunan shuhuda , gaba daya dajin amsawa ya yake
“yayana ka zo gare ni, n ice shuhuda ka taimake ni ”
A fusace ya yi kan wani mutm wanda shi ne mataimakin shugaban kungiya , shi ke rike da shuhuda ta gaskiya , ya ce .
“mhm , kifi na ganinka mai jar koma (ANTY RAISAT KINDE JI lol….) , ko ka dauka duk yunkurin da kake na fita da shugabar mu a wannan guri ba ma ganinka ? bude kunnuwanka da kyau ka ji, kmar yadda basarake ba zai satu ga barawo ba saboda dogarawa , haka muma ba ma wasa da shugabar mu , don haka kan sani aa mu sha jinin shuhuda don ya halatta ga abin tsafinmu , kamar yada muka sha jinin dr ya’u,
Kamar yadda muka sha jinin masa’ud da zarar mun sha jinin shuhuda za mu jinin wannan jemammiyar tsohuwar sannan mu sha naka

Please Login or Register in order to submit comment