Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokacin kuma BARE ke zama NAKA”.
Ya dubeta cikin rashin fahimtar inda ta dosa da maganarta, y ace. “Ban gamsu ba”
.
.
Toh pa, ni dai nace na gamsu, don Shuhuda sai bare wato MAI JAR KOMA! Lol
.
Ta ce, abin da nake nufi a nan shine, wani lokaci zaka ga bare shi yake SADAUKAR da komai na rayuwarsa akan abin da yake so, amma sai ka gad an uwa ya kwanta rashin lafiya wadda yak e bukatar jinni amma duk cikin ‘yan uwa sai a rasa wanda zai iya sadaukarwa ya bayar da jininsa. Ka gamsu?”
Yayi murmushi, y ace,.....
da Hausa Book stories
MATA’UL-HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤24¤¤
Ya yi murmushi, y ace. “Na gamsu, sai dai ki sani bana daga cikin wadannan mutanen……….”
Ta katse shi da cewa. “Kash! Ba ba nufi na ken an ba, kuma ai ba a san mai cin tuwo ba……….”
Yana dariya ya karshe mata Karin maganar cewa. “Sai miya ta kare , amman kin san hasashe da tsinkaye na sa makeri yunkurin narka karfe ba tare da yana da tabbacin hakansa zata cinma ruwa ba ko?”
Ta ce, “A’a, dutsen day a ke cikin ruwa ai bai san ana rana ba, don haka ka daina ma tunanin akwai wani babban shamaki a cikin soyayyarmu”.
Ya girgiza kai cike da jin dadin yadda yadda ta karfafa masa gwiwa, y ace,. “To Allah Ya shige mana gaba”. Ta amsa masa da . “Ameen”. Y ace, Yadace a samara min kyauta ta musamman wadda zan gain na rinka jin dadi”. Ta yi dariya t ace masa”.
“Kyauta? Sha kuruminka, zan maka kyauta ta bajinta mai matukar muhimmanci”.
Yace, “Wace kyauta ce haka mai muhimmanci?”
Tace Dan mutum! Ko ba ka so na samara maka da?”
Ya juyo dube ta, wani sanyin dadi ta ratsa zuciyarsa tunda har tana yi musu fatan
samun sanyi idaniya.
Y ace, “Allah Ya kaimu lokacin”. Bata amsa ba, sai tayi hamma.
“Y ace ya dai? Bacci ne, ko yunwa?”
Ta ce, “Ina jin bacci ne, don jiya ban samu bacci ba”.
“Yace mai ya hana ki yin bacci?” Yayi tambayar zuciyarsa akuntace, don yayi has ashen tunanin Uncle Hamza ne ya hanata bacci. Tce, “Naje wani taro ne”. Ya juyo ya dube ta, y ace. “Taro? Wane irin taro, kuma a ina? Ta ce, “Ni ma ban san wane irin taro ba, kuma ban san gurin ba”. Ta ce, “Eh kasan akwai abin da za ka yi kai kanka ba kasan me ka yi din ba”. Ya girgiza kai, y ace.”A’a, na fi aminta cewar, kin yi mafarki ne, ko ba haka ba?” Ta ce, “Ina tunanin mafarki amma ni da nasan ban kwanta bacci bay a zan aminta mafarki na yi?” ya ce, “Hakan yana iya faruwa, wata kila saboda gajiyar hanya yasa kika fita hayyacinki har bacci ya sace ki baki sani ba, a cikin baccin kuma kika yi mafarki ana gudanar da wani taro da ke. Sai muyi fatan Allah Ya sa taron alkhairi ne”. Ya karashe maganar yana kallon hanya, yau ji shiru ba tanka ba, sai ya dan waigo, ya yi katari da ita tana sharer bacci.
Murmushi kawai ya yi, yasan har yanzu akwai gajiya a tare da ita, ya ci gaba da tafiya akan titi cikin nutsuwa da kwarewa.
Suna isa Karare ya juyo ya dubeta, har lokacin bacci take yi, ya ambaci sunanta, ba ta farka ba sai ya kai hannu ya dan bugi cinyarta. Da sauri ta bude ido kamar ta tsorata. Ya yi murmushi y ace,”Sha bacci ko?” Sai ta kuma dube-dube kamar ba ta yarda da kanta ba. Ta ce. “Ya na ganmu a nan?” Y ace, “To a ina dama za ki ganmu? Ko so kika yi ki tashi daga baccin ki ganki cikin gida?” Sai ta yi gum da bakinta. Ya ce, “Nuna min hanyar gidan”.
Ta dinga nuna masa yana shiga lungu har suka isa kofar gidan Alh. Jamilu, ya tsayar da motar Shuhuda ta fito fuskarta ba yabo ba fallasa ta taryi yaranda suka fito da ga gidan suna yi mata sannu da zuwa.
Ta kama hannun Amira zuwa cikin gidan, Isah ya dade a cikin motar bai fito ba yana kallonta har ta shige cikin gidan. Sannan ya sauke ajiyar zuciya yana auna matsanancin son da yake mata. Lokaci daya haduwarsa da Shuhuda Ibn khaddab a birnin Misra da kuma jiya da suka hadu a gidan mai ta nuna bata sanshi ba sam. Abin duk ya dawo ya zauna masa a ransa daram!
Yaran suna da salon barkwanci a cikin lamarinsu, abinda ya ayyan ke nan a ransa.
Sannan zuwansu gidan Uncle Hamza da abinda ya faru shi ma ya dawo masa. A bayyane ya ce. "Zan sadaukar da komai na rayuwata don ganin na kwalaka a kasa, domin ni na sha wahalar sonta tun tana cikin tsumma, tun bata mallaki hankalin kanta ba, har zamana cikin jajayen kunne bai sauya zuciyata daga alkiblar sonta ba...."
Shuhuda ta katse masa zancensa yayinda ta sunno kanta a tagar motar tana murmushi ta ce,
"Yaya, ka shigo mana ka tsaya a mota?"
Bai ce komai ba ya bude motar ya fito ya bi bayanta zuwa cikin gidan.
Haj. Karimatu ta karbe su hannu bibbiyu, kuma taji dadin yadda ta ga Shuhuda da Isah sun hada kansu, sika shigo mata da tsarabar da suka zo da ita. Alh. Jamilu ya dawo cin abincin rana ya tarar da bakin nasu. Ya dubi Shuhuda ya ce. "Ni kam bana marhabin da zuwanki tunda kinki zama da mu". Shuhuda tayi murmushi kawai, shi kam yana son ace Shuhuda ta dawo gurinsu da zama ko don yadda ya ke ga Haj. Karima na bukatar hakan, musamman tunda ya aure ta bata taba haihuwa ba. Amma da ya ke ita mace ce ta gari, sai ta rungumi 'ya'yan da Binta ta fita ta bari tamkar 'ya'yanta. Haj Karima ta ji dadin karar da ya nuna mata, ai a so naka ma wata martabace. Isah ya karbe zance da cewam "Ai yanzuma sai da na tursasa mata ta zo". Shuhuda ta juyo da sauri, ta ce. "Kai Yaya kar muyi haka da kai, ni fa na ce maka mu zo nan din". Shima sai ya auna mata harara cikin sigar wasa ya ce. "Kun ji ta da son kai". Alh. Jamilu ya ce. "To na ji ko ma ta ya akayi kuka zo munji dadi, kuma mun gode". Ya soma nufar dakinsa, Haj Karima ta bishi a baya.
Sun sha yini a kauyen karare, sannan daga bisani suka yi haramar tafiya kano, Alh Jamilu ya ce. "Ai na dauka zaku yi mana sati". Isah ya girgiza kai, ya ce. A'a, dama cewa muka yi bari mu zo mu gaisheku". Ya ce, "To madaLlah". Ya dauko kudi zai ba su, sai Shuhuda tayi saurin cewa. "A'a Baba ka barsu, ai ga kudi can mun ba Umma ta baka sako daga Alh". Isah ya cika da mamaki, da yaushe Alh ya bawa Shuhuda kudi shi bai sani ba? Amma sai ya basar, shi kuwa Alh Jamilun sai zuba godiya yake yana cewa. "Allah ya kara girma, ai kyautar dattijai ba a mayarwa".
Haka suka yi musu sallama suka tashi. Sun soma tafiya a motar, Isah ya ce. "Wai ke na tambayeki". Tayi shiru bata tanka mishi ba. Ya ci gaba da cew. "Yaushe Alhaji ya ba ki sakon kudi da kika bayar?"
Ya ji shiru ba ta tanka ba. Sai ya dago kai ya kalleta, ya ce. "Kina ji ina yi miki magana amman za kiyi shiru ki kyaleni?"
Har yanzu ba ta tanka ba, ranshi ya sake baci, sai ya faka motar a gefen hanya ya juyo gaba daya yana kallontta. Fuskarta a daure ta ke tamau kamar ma bata damu da shi ba.
Ransa idan ya yi dubu ya baci, cikin kakkausar murya ya ce mata. "Shuhuda ba magana nake yi miki ba ki ka yi banza da ni?" Ta dago kai ta ce. "Me ka ce?" Ya hasala da maganarta, ya ce. "Wannan wane salon rashin kunya ne haka?" Ta ce "kai ka ji ni dai Isah, me nayi na rashin kunya?"
Baki ya hangame yana kallonta cike da mamakin abin da ya fito daga bakinta, sam ba ta damu da abin da ta fada ba ko ya bata masa rai ko bai bata masa ba, ita dai ba ta damu ba. Ya ce. "Tambayarki nake, yaushe Alhaji ya baki sako ban sani ba?" Ta murguda baki ta ce. "Kuma lallai idan zai aikeni sai ka sani tunda kai kadai ne jikansa mai 'yanci?" Ya kara hawa sama ya ce. "Ko ba ni kadai ne jikansa ba, ai naga tare muka fito da ke ko? Ya akayi ban ga lokacinda ya baki kudin ba?"
Ta ce, "Idan zai bani wani abu ne? Me kake nufi? Ni fa ban son shiga sharo ba shanu, ina ruwanka?" Ya jinjina kai yana kallonta, ya ma kasa tofawa, sai kawai ya ja motar suka tafi ko wanne na hura hanci.
.
BABI NA GOMA SHA BIYU
GA KOSHI GA KWANAN YUNWA
Alhaji Rabi u yana zaune a dakinsa rike da carbi yana lazimi, Isah yayi Sallama ya shigo fuskarsa a daure. Zaunawa yayi akan kujera, yayinda Alhaji Rabi u ya dago kai yana murmushi, ya ce. "Ya akayi ne mazajen? Na jiyo muryarku kuna shigo wa". Isah ya dan saki fuska kadan, ya ce. "Barka da yini". Alhaji Rabi u ya amsa masa. "Yauwa, an dawo lafiya?" Ya ce "lafiya, suna gaishe ku". Alhaji Rabi u ya ce, "Muma muna amsawa". Isah ya gyara zama sannan ya ce. "Alhaji Jamilu ya ce ayi maka godiyar kudin da ka aika masa dasu ta hannun Shuhuda". Alhaji Rabi u yayi murmushi ya ce. "Babu komai ai shi magidanci komai kudinsa yana bukatar taimako, bare kuma irin Alhaji Jamilu, Ni kam bani da bakinda zan yi masa godiya akan rikon da yayiwa Karimatu, tunda ya aure ta dai-dai da kwana daya bai tab kawo min korafinta ba, haka itama, ba kuma taba jin ance anje gidansu da yaji ba". Ya karashe maganar yana alhinin rabuwa da Karima a cikin ahlin gidansa. Isah ya gaza yin hakuri, ya ce.
"Wai Alhaji yaushe ka bawa Shuhuda sakon kudin? Kuma mai yasa baka bani ba a matsayina na miji?" Alhaji Rabi u ya dube shi da yanayin rashin fahimta, ya ce.
A a, don zan bada sako dole sai a gabanka, ko kuwa kai kadai ne dan sakona?
Jin yadda Alh. Rabi u yayi maganar kamar acikin hasala ne, sai bai ji dadi ba, kuma dai gaskiyar Shuhuda ne, ai ba shi kadai ba ne jika ga Alh. Rabi u, to don me zai damu kansa akan an bawa Shuhuda sako ba shi ba? Ko da yake ai wani bangare dole ne ransa ya sosu, ai shi na miji ne, dama gaba ya ke da Shuhuda, zai di kyautuwa ace shi aka damkawa duk wani sako, ko don ta girmama shi, a'a duk ba ta wannan ba, me yasa lokacinda za a bada sakon ba a bayar a gabansa ba, kuma ba a sanar da shi an bata ba, sai dai kawai yaji ta bada sakon, me hakan ke nufi? Muryar Alh. Rabi u ta katse masa tunanin da yake.
"Isah kada dai ka ce min kana daga cikin mutane masu kyashi ga 'yan uwansu? Ai ko kana daga cikin irinsu bao dace ka nuna kyashinka ga Shuhuda ba. Musamman idan kayi la akari nan gaba kadan zata zamto mata a gareka, ka ga kuwa,wannan hali bai dace da kai ba sam".
Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤25¤¤
Da sauri Isah ya girgiza ka, ya ce. "Ba haka nake ba Alh, sam ban kyashi akan ka nunawa Shuhuda soyayya, ai ita ma jika ce gare ka, kuma marainiya. Shi kam maraya ana son a na son a nuna masa kauna a sarari ko don kada maraici ya dameshi".
Alh. Rabi u ya saukar da ajiyar zuciya ya ce, "Ko da naji, kasan zamanin ne ya lalace, sai ka ga dan uwa yana kyashin dan uwansa ya samu ci gaba, Musamman ga mata da miji, idan ya kasance matar ta fi mijin samun hanyoyi alkhairi, sai ka ga mijin na nuna mata tsana duk saboda haka, baya tunanin ko wane Dan Adam da hanyar arzikinsa". Alh. Rabi u ya kawar da wannan hirar, ya dora da cewa. "Ya maganar tafiyarka Ibadan?" Isah ya ce, "Tana nan, mako mai zuwa zan tafi". Alh. Rabi u ya ce, "To sai a kula, a san mutumcin kai da kiyaye addini. Nasan san ka mutum ne mai yawan ibada, saboda haka sai ka dage kada kayi watsi da addu a domin addu a takobin mumini ce, duk wanda ya juri yin addu a a rayuwarsa ba zai tabe ba".
Nasiha mai ratsa bargon jiki Alh. Rabi u ya yi wa Isah, sannan daga bisani sukayi sallama, isah ya fice daga dakin.
Kwana hudu sam Isah Isah ya rasa kan Shuhuda, ba ta kulashi, idan tana zaune a falo da zarar ya shigo sai ta tashi ta shige kuryar daki. Shi bai ga abin fushi da bata rai ba akan wannan dan sabanin da suka samu ba. A ganinsa tunda har rashin fahimta ne ya kamata ta tsaya ta saurare shi, amma ta kiya, ta ki yi masa uzuri a matsayinsa na dan Adam wanda yake da yawan ajizanci. To sai bai nuna mata ya damu da wannan hali da ta kirkiro musu ba, amma ya damun fushin nata na nukurkusar mai zuciya.
.
KUNGA MAZAN KIRKI, BA IRIN SU 'O'O BA! lol.... (Sadin mama)
.
Ana yau gobe zai tafi Ibadan yana zaune a falo shi da Inna Yaduwa suna hira wani yaro ya shigo.
"Wai ance ana sallama da Shuhuda"
Isah da Inna Yaduwa suka dubi juna duba na mamaki isah ya dago kai ya dubi yaron ya ce. "Waye ke nimanta?" Yaron yace. "Wai inji Hamza ne". Isah ya bata rai ya ce da inna yaduwa.
"Wani malamin makarantarsu ne yake neman ya shigar min hanci a kudundune, haka fa da muka je Katsina ya nemi tarwatsa mana farin ciki". Inna Yaduwa tayi shiru bata ce komai ba, yayinda Isah ya dubi yaron ya ce. "Ka je ka ce bata nan". Har yaron ya juya zai fita, tsallam! Shuhuda ta fito daga daki tana tsayar da yaron. "Ka ce masa ga ni nan zuwa". Inna Yaduwa da Isah suka sake kallon juna, yaron ya fice yayinda Shuhuda ta koma daki ta dauko gyale ta fito falo, ta nufi hanyar fita. Inna Yaduwa ta ce. "Ke Shuhuda ina zaki je? Ca na ke ance baki nan? Shuhuda ta juyo tana kallon Inna Yaduwa fuskarta a daure ta ce. "Yo mutum ya zo nemana sai ace masa bani nan, bayn kuma ina cikin gidan don kawai a raba hanta da jiji?" Inna Yaduwa ta ce "Amma tunda an bayar da ke, maiye amfanin tsayawa da wani?" Shuhuda ta ce, Ni fa ba zan auri mutuminda yake da tsattsauran ra ayi ba, mutuminda komai sai ya tuhumi mutum". Isah ya langwabe kai, yasan har yanzu fushin ne bai sauka ba. Inna Yaduwa ta ce, "Ai shi zaman tare haka ya gada, dole sai anyi hakuri da juna, kuma ina amfanin mace ta auri mijin da baya tuhumarta akn abubuwan da suka shafe ta? Idan ba ta haka ba ta ya zata samu ingatacciyar rayuwa?" Bata tsaya sake tofawa ba, ta sa kai ta fice abinta. Inna yaduwa tace da Isah. "Wai me yake faruwa ne haka?" Shiru Isah ya yi gabadaya wutarsa ta dauke, kada fa abin ya zama da gaske, Shuhuda ta daina sonsa,tana son mutuminda bai dace da rayuwarta ba, mutuminda zai kai ta cikin tsatson da za a dinga aibatata. Tsayin lokaci shi da Inna Yaduwa suna yanayin shiru, daga bisani kamar wanda aka tsikara da tsinken allura, firit ya mike tsaye ya nufi kofa, Inna Yaduwa ta ce. "Ina zaka je?" Ba tare da ya juyo da dubansa gareta ba ya ce. "Ina zuwa". Ya fice.
Tun daga nesa ya hango Shuhuda da Uncle Hamza sai faman dariya suke alamu da ke nuni suna jin dadin hirar da suke. Wani abu mai kaifi (kishi) ya soki zuciyarsa, ya tsaya kamar ba zai karasa ba, sai kuma ya ci gaba da takawa cikin kasaitaccen takunsa wanda duk wanda zai yi tozali da shi zai tabbatar nagartaccen namiji ne, domin Isah namiji ne mai kyakkawar shiga game da cikar haiba.
Cikin takunnasa ya isa inda suke zaune akan fararen kujerun roba, a gabansu akwai yalwar korayen ciyayi (grass carpet) don haka gurin sai tashin kamshin ciyayin yake. Lokacin da ya isa, su duka biyun sai suka gumtse fuska, dariyrsu ta dauke a lokaci daya. Isah ya mikawa Uncle Hamza hannu da nufin suyi musabaha a matsayinsu na Musulmai su duka. Uncle haamza bai tsallake tayin ladar da aka masa ba, ya mika masa hannu suka yi musabiha, daga bisani Isah ya dora da cewa.
"Ban so ka kasance cikin mutane masu taurin zuciya ba, ta hanyar yin nema cikin nema, wanda ko a musulunci ya haramta". Uncle Hamza ya ce kamar yadda ban so kai ma ka kasance cikin mutane marasa yiwa soyayyar gaskiya uzuri ba" Isah ya ce. "Ai babu uzuri ga abin da aka san haramtacce ne". Uncle Haza ya dan yi malalacin murmushi, ya dora da cewa. "Idan haka ne sai na ce ni aka yiwa hawan kawara, aka naushe ni kuma ake son a hanani zubar hawaye". Cikin takaicin maganarsa Isah ya ce, "ita ZUCIYA MUGUN NAMA ce, idan mutum bai dace da zuciya ta kwarai ba sai ta hada masa ZAFI BIYU, na radadin zuciya da kuma na kaskanci, don haka sai a yi ta ganin mutum yana abubuwa wanda basu dace ba, amma shi da yake bai dace da zuciyar ta kwarai ba sai ya ga duk abin da yayi dai-dai din ne a gareshi".
Maganganun Isah masu shiga zuciya ne, da kuma zafafata, to amma sai Uncle Hamza ya bude baki da nufin mayar masa da martani cikin sanyayan kalamai, kafin yiwuwar hakan Shuhuda ta riga shi da cewa.
"Yah Isah amatsayinka na yayana bai kamata kayi min wannan rashin adalcin ba, ina hira da wanda na ke so ka zo kana jifarsa da gugar zana. Ai ai ita mace uzuri ake yi mata, musamman da ya kasance na fada maka, ba zan iya auren mijin da zai jefa rayuwata cikin takura ba. Dona haka ka saurara mana, ka daina shigar min rayuwa".Gaba daya jijiyoyin sadar da magana da suke aiki a jikin Isah suka tsinke saboda jin maganganun da Shuhuda ke amayarwa a gare shi. Ba shi da abin da zai iya fada mata, saboda haka ya juya ya koma cikin gida cike da kuncin zuciya. Bayan tafiyar Isah daga gurin, Uncle Hamza ya dago kai ya dubi Shuhuda, ya ce. "Yayan nan naki yana da tsananin kishi, wanda kuwa bai dace da shi ba, domin mace idan tana budurwa, ma'ana tana a gidansu ba ta yi aure ba, kakarin da zaka yi ka kimtsa soyayyarka gare ta, wannan shine babban kishi mai amfani. Idan ka aure ta kuma sai ka nuna kishinka ta hanya wadatata da dul abin da yake hakki gare ka. Ka yarda da ita don gudun zargi kada ka ganta da dan uwanta ka zari wani abu".
.
TOH PA MAZAN WANNAN GROUP! Da patan kun ilmantu!!!
.
Shuhuda ta jinjina kai, hirar da ba a karasheta cikin dadin rai ba ke nan. Suka yi sallama ta koma cikin gida. Inna Yaduwa ta watsa mata wani mugun kallo, yayin da Isah yake zaune kansa a sunkuye, gabaki daya ba shi da sukuni . Shuhuda ta ce. "Kinga ni ban san harara ba sai kwayar ido ta fado. Haka kawai a takurawa rayuwata, in bacin tausayi da kuma shakuwa da tuni ba a kaddamar da mutum ba, amma sai a takurawa mutum a hana shi rawa gaban hantsi? Wallahi ba zata sabu ba bindiga a ruwa, ba zan juri wannan matsin ba, don ba da ni za a yi gamin gambizar nan ba". Inna Yaduwa bata tanka mata ba, Shuhudan ta shige daki. Isah ya mike tsaye ya dawo kusa da Inna Yaduwa, murya a raunane ya ce. "Inna ki taimaki rayuwata, wallahi Shuhuda ita ce zabina, matsawar na rasata hakika na rasa wani bangare na daga farin cikina. Ina son Shuhuda Inna, itace burin rayuwata, ki taimake ni kada na rasa ta!" Yanayinsa gaba daya ya sauya zuwa launin tausayi kallo daya zaka yi masa ka fahimci tsananin son da yake yiwa Shuhuda, wanda dama shi so na gaskiya ba ya buya, a cikin farin ciki ko akasin haka kake. So na gaskiya ba zai taba boyuwa ba.
.
Hmm, Isah da badan sunan ka ba, sai ince Sadin Mama zata yi da kai, amman ba laipi idan zaka canza zuwa sunan larabawa.... Lol
.
Isah kam yana son Shuhuda har cikin kalbinsa, ta zame masa NURUL KALBI, ta zame masa tauraruwa mai haske da kyalli, ta zame masa mahadin rayuwarsa idan kuwa ya rasa soyayyarta tabbas ba karamin rashi ba ne a gareshii. Cikin tausayawa inna Yaduwa ta ce. "Isah shawara zann baka ka yi hakuri da Shuhuda ka nemi wata". Tar! Tar!! Kwalla suka suka zubo masa, cikin sanyin jiki yana girgiza kai ya ce. "Bazan iya ba Inna, ba zan iya rabuwa da Shuhuda ba idan kuwa har zan iya rabuwa da ita, to hakika ba ta a doron kasa ne". Tausayinsa ya kara narkar wa Inna Yaduwa zuciya, ta ce. "Ba ka lura da abin da na ke so ka lura da shi game da yarinyar nan ba. Akwai abubuwa da yawa da suke faruwa wanda yasa nake tababa.........."
"Eh, ai ni mahaukaciya ce! Ba sai kin maimaita ba!" Muryar Shuhuda suka tsinkayo daga bakin kofa. Su duka biyun suka mayar da kallonsu gareta, fuskarta a daure babu ko digon fara'a. Sannan idanunta jajur sai ka ce jan gauta, babu wanda ya tanka mata, ta ci gaba da cewa. "Wallahi kuyi hankali da ni a cikin gidannan, ina nuna muku ni mai tausayinku ce, amma kun kasa fahimta. Duk ranar da na cire imani a kanku zaku sha mamaki.." Kausasan kalaman nata sunyiwa Isah tsauri, ya kasa jurewa ya mike tsaye tare da daka mata tsawa. "Don ubanki waye sa'anki a cikinmu da har zaki zo kina fada mana wadannan kalaman, ko don kinga ana kyaleki shi ne za ki juya mutane? To bari ki ji don na ce ina sonki ba yana nufin bani iya hukunta ki ba ne".
.
Su Isah MAZA!!!
.
Dariya ta fashe da ita.
"Allah ko? To ga fili ga mai doki, idan har ka isa ka sanya hannu ka buge ni. Idan kuwa ka kasa baka haifu ba, ku....."
Ya yunkura sai kai mata duka, inna Yaduwa ta yi saurin tare shi. "Kada ka dake ta, kyale ta da halinta". Ta juya ga Shuhuda, ta ce. "Ke kam ba ki ji dadin halinki ba, ace ba ki ganin mutumcin kowa a idanunki, rashin kunya da fitsara su kika sa agaba?"
Kai tsaye Shuhuda ta ce. "Gadon gidanmu ne!" Inna Yaduwa ta ce. "Karya kike wallahi, duk gidan nan babu fitsararre, amma ke....." "To ya fa isa, kuma fitsara da rashin kunya yanzu na soma". Isah ransa ya kuma baci ga shi Inna Yaduwa ta hana shi dukan Shuhuda, sai kawai ya ficce daga falon.
.
Da kuwa Isah anga sarkewar hannu. (Sadin Mama).
.
Shuhuda ta ce.
“Idan hark u masu zuciya ne kada wanda ya kara kulani a cikin gidan nan, kowa yayi abin da yake so ban hana ba”. Inna Yaduwa t ace da ita. “Ai mu ba kafurai ban e, bare mu zamo masu zuciyar kafurawa. Ke dai da kika ji zaki iya yin gaba dam u sai ki yi. Sai dai ina me tunatar da ke cewa, gaba dad an uwanka Musulmi haramun ce, bare kuma ga wanda suka zamo tsatsonki”.
Shuhuda ta murguda baki t ace, “Sai ki yi, ni dai na fi karfin dauk wani mai hankali”. Tana karashe maganarta ta sanya kai cikin daki. Inna Yaduwa ta bi tad a kallo tana girgiza kai, halin Shuhuda yana bat a mamaki, da daure mata kai, wani lokaci ta fassarata zuwa mara hankali, wani lokaci kam gaba daya ta fi dangantata da aljana ba mutum ba. Wannan ke nan!
BABI NA GOMA SHA UKU
MURDADDIYA
Isah ya tafi Ibadan cike da takaicin Shuhuda, a lokacin da zai tafi ma ko fitowa daga daki bata yi ba bare suyi sallama, shi ma bai damu da hakan

Please Login or Register in order to submit comment