Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Nigeria zai biyo ta nan Misra, hikimar hakan gurin malamin mai suna Dr. Outhman Ibn Abdulfatah shi ne, yana so ya samawa Isah aiki a ma'aikatar karafa da ya bude ta kashin kansa mai suna KHAIR METAL, saboda tun yana koyarwa a makarantar ya aminta da kaifin kwalwa irin na Isah, ba duka dan Nigeria ne ake samunsa da yin karatu idan ya shallake kasarsa ba.
Mafi yawancinsu sun fi mayar da hankali ne ga shashanci wajen kula mata da shaye-shaye, amma shi Isah ko kawance ba ya yi da mata, abin da ya kai shi kasar shi yake yi. Hakan kuwa ya kara masa kwarjini da cikar HAIBA a idanun malaman makarantar.
Yana saukowar daga jirgi tafiya kadan ya yi ya isa inda ake bincike, aka gama yi masa duk wani bincike da ya kamata a yi masa a matsayinsa na bakon kasar. A lokacin ne kuma ya samu layin da ake amfani da shi a kasar ya kira layin Dr Outhman ya sanar da shi ya kammala komai shi kawai yake jira.:
Bayan gama wayar akwai wani guri inda ake zama musamman don irinsa. Wadanda za a zo taryensu, ya zauna yana nazarin wani littafi SHOCK TREATMENT. Kamar an ce ya dago kansa, sai ya yi sai ya yi TOZALI da wata kyakkyawar mace, fara tas. Ma-abociyar cikar zati, idanuwanta narai-narai da kwalli radau a cikinsu.
Tana cikin shiga ta bakar jallabia ta yafa gyalen rigar a kafadarta, sannan ta nade kanta da wani yalolon dan kwali, wanda ya kara fitowa da kyawunta a sarari. Kana ganinta kasan balarabita ce, amma bisa ga tsanin al'ajabi, kai tsaye gurin da yake zaune ta tukaro, kuma koda isowarta cikin harshen Hausa ta yi masa sallama, tun kafin ma ya amsa ta soma jero masa gaisuwa.
Mamaki ya cika shi don bai yi tsammanin jin harshen Hausa a bakin wannan Balarabiyar da ke gabansa ba.
Baya da haka kuma yana mamakin saukin kai irin nata wanda har ya sa ta zo inda yake ta gaishe shi ba tare da shi ya yi hakan ba a matsayinsa na namiji wanda ya ga mace yana so zai tunkara.
Duk da ba ya mu'amala da mata, ya sha jin yadda aka tsayar da suke da girman kai musamman idan aka tsayar da su. To amma ita wannan mai sanyin hali ce, ko kuwa ita ma daga senegal din ta baro, sun yi tarayya a makaranta daya?
Murmushi ya sakar mata cikin harshen Hausa yace:
Kai duk ni kadai wannan gaisuwan? Ita ma murmushin ta yi masa, tukunna tace: Ai ka isa ne, gani na yi kamar na sanka, don Allah kai dan Najeriya ne, a birnin Kano ko?
Bai yi mamaki ba, don ya sha jin ana cewa duk inda DAN KANO ya shiga ba ya 6uya, wata kila hakan ne ya sa ta canki wannan tambayar. (Ta6! Ai ba ma hakan bane. Ni dai ban yadda ba. In dai ba mayintan san kudi ba, kanawa ba su san komai ba, sai shirme. Da ma dai 'yan zaria ne sune suka fita zakka a fagen gogewa da komai. Lolx)
Gira ya daga mata ba tare da ya yi magana ba. Tace; Haba, kofa naji, unguwar SALLARI ko?
Yanzu kam ya sha mamaki, don jin ta ambaci sunan unguwar su kakansa, yana dubanta yace:
Hala ke ma 'yar can unguwar ce a kano, kuma Najeriya? Ta girgiza kai tace: .......
.
1- Abubakar Ibn Khaddab
2- Shuhuda Ibn Khaddab
3- Yusuf Ibn Khaddab
Uncle hamza ya hadu da Abubakar ibn khaddab.
Isah kuma ya hadu da Shuhuda ibn khaddab
To ni kuma bari na arce watakil nine zan hadu da Yusuf ibn khaddab.
ada Hausa Book stories
MATAUL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤16¤¤
Ta girgiza kai tace: A'a, Ai ni 'yar wannan kasar ta Misra ce, na dai sanka, ko ba kai ne YAYAN SHUHUDA SAGIR RABI'U ba?
To yanzu fa mamakinsa ya kuma hau-hawa akan na dazun. Ya dube ta da kyau, yace: Kin ce ba a Najeriya kike ba, ya aka yi kika san garinmu, unguwarmu, dama kanwata?
Tayi murmushi, sannan ta ce dashi. " Ai sunanmu daya da kanwarka, ni kuwa duk inda mai sunana ta ke sai nasan wace ce ita.
Murmushi ya yi mata, saboda ya fahimci wasa ta ke, ita ma din 'yar Najeriya ce. Yace: Kina nufin ki ce min saboda sunanku daya dakanwata shi yasa kika santa, har kuma kika san ina da alaka da ita. Yadda duk inda kika ganni za ki iya shaida hakan?
Ta daga masa kai cikin tabbatarwa, ita ma fuskarta dauke da murmushi.
Yace: Ban yarda wannan zai zama karfaffiyar hujja ba, don haka kada ki wahalar da kanki gurin zolayata ta wannan hanyar, don ba ni kadai ba, duk wanda ya ji ma ba zai gasgata ba.
Tace: Wallahi rantsuwar dan musulmi ke nan ko? Na sanka, na san kai kuma yayan Shuhuda ne, da Babanta mai rasuwa da Babanka mai rai uwa daya uba daya suke.
Shi kam dariya ta ba shi matuka, yana daritar yace: Eh, ai ba cewa nayi ba ki sanni ba, na aminta kin san duk wadannan alakar da ke tsakanina da shuhuda, amma hujjar da kika bayar cewar saboda sunanku daya da shuhuda kanwata kika san haka ba mai kar6uwa ba ce. Idan ma har zata kar6un to cikin dayan biyu.
Ko dai kin hadu da shuhuda ko wani da yake da alaka da tsatsonmu, ko kuma kacokam a kasarmu, jaharmu kuma unguwarmu kike. Idan ba ta wadannan hanyoyin ba bazan ta6a yarda da abin da zaki ce ba.
Tace: Ni asalina 'yar wannan kasar ce, ban ta6a zuwa Najeriya ba, amma nasan kanwarka shuhuda sagir Rabi'u ta hanyar tsananin bincike da KAIFIYYA irin tawa...... Ba ma kanwarka kadai ba, a kasarku kuma jiharku, na san masu sunana SHUHUDA sama da trilliom, saboda haka kada ka yi mamaki.
Ya jinjina kai alamar jinjinawa, yace: Lallai kam kina da kokari tunda har kika yi wannan bincike, amma dai duk da haka kin san wani abu?
Ya nemi kawar da wancan zancen tunda ya lura 'yar barkwanci ce. Ta girgiza kai, tare da fadar: Sai ka fada.
Yace: Kin burge ni, har na ji ina son mu-amala da ke.
Ta yi murmushi, wanda ya bayyanar da siririyar wushiryarta, ba ta yi magana ba don haka ya ci gaba cewa. Da gaske sunanki shuhuda, kuma wannan kasar kike?
Ta jinjina kai. Tabbas sunana Shuhuda Ibn Khaddab, mu uku ne gurin mahaifinmu, ni da 'yan uwana Abubakar da Yusufa, iyaye da kakanni dukkansu 'yan kasar nan ne, sai me bayan haka?
Yana murmushi, yace: da ita: Lambar wayarki, da adireshin gidanku.
Tace: Tabdijan, lambar waya? Yanayinsa ya nuna tuhuma, yace: Ban gane mamakin da kika yi ba?
Tace: Eh, to ni da ba zama kasa daya nake yi ba, wace lamba zan baka idan ba so kake ka yi ta nemana ba ka samu ba? Yanzu ma fa kasar sudan zan je, kuma daga can wata kasar zan je?
Yanayinsa ya sake nuna damuwa yace: Ke kam duk me ya janyo miki wannan yawo haka sai ka ce 'yar kasuwa?
Ta yi dariya, tace: Haba dai? Ai duk yawona ban kai TANZIF ba, wanda yana iya zuwa kasa goma a kwana goma. Bare ni da idan na je kasa nakan samu kwana goma ban barta ba.
Isah yace: Waye kuma TANZIF? Tace: Ba ka sanshi ba. Yace: To amsa min tambayata me kike zuwa yi kasashe?
Tace: Yawanci ina zuwa majalisi ne na malamai. Sannan nakan ta6a kasuwanci.
Ya jinjina kai. Cewa zaki yi Ustaziya ce? Don haka ma daga yau haka zan dinga kiranki USTAZIYA SHUHUDA.
Ta duba agogon da ke daure hannunta tace: Ka ga har mun ci lokaci da yawa, sai nace sai gani na biyu ke nan?
Ya yamutsa fuska yace: To idan kin ce sai gani na biyu ta ya zamu sake haduwa, ba ki bani adireshinki ba?
Tace: Haka ne, amma.......
yadda TSAUTSAYI ya hada mu yanzu, a gaba KADDARA zata hada mu.
Yace: TSAUTSAYI KO KADDARA? Ban gane ba. Ta yi dariya wadda ga dukkan alamu dabi'arta ce, dariya ba ta mata wuya. Tace:
Idan na ce TSAUTSAYI, ina nufin tsautsayin haduwarmu bayan kuma zamu dade ba mu sake haduwa ba, wata kila kuma har abada.
Sannan idan na ce KADDARA ina nufin KADDARAR ALLAH ta hadamu sanadin mai sunana, idan na biyota har kasarta don........
Karar maganar da ke fita daga abin maganar da ke kafe a gurin ta soma bayar umarni ana neman wadanda zasu SUDAN don yin setting dinsu ta katse maganar da shuhuda ke yi. Tana dan hanzari tace da shi.
SAI WATA RANA!
Ya yi sauri yace:
Dan tsaya na ba ki lambata........
Tace: A'a kada ka damu, sai ka jini.
Ba ta jira abin da zai kuma fada ba, ta yi gaba ta barshi galala da baki cike da alhini, wannan yarinya da barkwanci ta ke.
Lokaci daya ya ji wani nishadi na kwarara a zuciyarsa, tunda yake a rayuwarsa bai ta6a yin soyayya ba. Don haka ya kira abin da yake ji game da yarinyar SOYAYYA.
( Kai wannan gayen akwai shirme, yanzu dai naga ya nuna halin kanawa. Lolx)
Farad daya maganarta ta fado masa a rai, wai haduwarsu tsautsayi, abin da kuwa zai sake hada su kaddarra, ke nan zata je Najeriya?
Mhm! Lamarinta gaba dayansa na barkwanci ne, don haka zuciyarsa ba ta aminta ita din 'yar kasar Misra ba ce, ya fi kyautata zaton Najeriya ta ke, birnin kano, unguwar sallari tunda har tasan sirrin ALAKA da ke tsakaninsa da Shuhuda, kuma ta yi ikirarin a sanadin kaddarar sunan Shuhuda zata je Najeria unguwar Sallari wadda ta ke mu'amala da kanwarsa.
Ba don haka ba, me ya hana ta kar6i lambar wayarsa tunda ita ba ta ba shi tata ba? Ai maganar ji ma daban ta ke, kawai dai ita irin mutanan ce masu barkwanci da zolayar wanda Allah ya hada su zama da su.
Yana nan zaune Dr. Outhman Ibn Abdulfatah ya iso airpot din, ba su wani tsaya ba suka rangaya gidansa.
Duk yadda Dr Outhman ya so da Isah domin ya tsaya ya yi masa aiki, ya tubere sai dai ya ce zai je Najeriya in yaso daga bisani idan mahaifansa sun aminta sai ya dawo. Kwanansa hudu, Dr. Outhman ya sake masa visa ta zuwa Najeriya bayan sun je babbar kasuwar garin wadda ita ce cibiyar kasuwar kasuwancin kasar, Isah ya duba zobe mai kyau na zallar azurfa ya sayawa shuhuda a cewarsa wannan zobe shi ne babbar tsarabar da zai ba ta, tunda kullum suka yi waya da ita ya tambaye ta abin da zai kawo mata tsaraba da shi, sai ta ce zobe. Wai ita a rayuwarta babu abin da yake burge ta irin zobe, shi yasa ta ke matukar son a yo mata tsaraba da shi. Burin Isah ya ganshi a birnin kano, ya ga yadda shuhuda ta koma. Yasan ta kara girma, kyau da komai ma, tunda lokacin da ya bar kasar tana yarinya. Yana zaune a kujerar jirgin max air ya tuna ranar da ya baro kasar shuhuda kuka ta ke kamar ranta zai fita, shi din ma har ya isa kasar senegal kukan yake. Ya yi murmushi, rayuwa ke nan, komai mai cewa ne ban da ikon Allah! Yau ga shi a cikin farin ciki saboda zai koma kasarsa ta haihuwa, zai koma cikin dangi, 'yan uwa, yarensa, addininsa gami da mu'amalolinsa da ya rasa su na tsayin wani lokaci, yau duk zai cike wannan gurbin da ya samu gi6insu. Karfe bakwai na dare jirgin ya sauka a filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu kano, babu 6ata lokacin fasinjoji suka soma saukowa. Alh sada, Alh Ahmad, Haj Asibi, Inna yaduwa da shuhuda su ne suka zo taryen Isah, saboda haka yana fitowa daga cikin jirgin da su ya soma tozali. Wani yalwataccen murmushi ya saki, yayin da shuhuda ta rugo da gudu ba zato ba tsammani Isah yaji ta rungumeshi. Wani irin tsau! Ya ji a gaba daya sassan jikinsa, tsikar jikinsa ta tashi, amma ya kasa cire ta daga jikin nasa, shi ma sai ya rungume ta tsam yana tuna tsananin shakuwarsu, yana tuna wannan rana da ta ki goguwa a idanunsa da ma zuciyarsa gaba daya, wato ranar tafiyarsa Senegal. Sai da suka dauki lokaci a haka, sannan Inna Yaduwa ta 6an6are shuhuda daga jikin Isah tana cew: Ke sakar min miji kada ki karya min shi. Bayan an gama duk abin da ya dace, kai tsaye gidan Inna yaduwa suka nufa don ta ce ita ce mai masaukin bako, shi ma dama gidan nata ya fi sha'awa tunda a nan ya yi rayuwarsa kafin tafiyarsa Senegal. BAYAN WATA UKU Har su Shuhuda suka kammala jarrabawarsu uncle hamza bai kulata ba, saboda a lokacin ya gama amanna ita din aljana ce, amma duk da haka ya kasa samun sukuni, kullum tunaninta ne ke nukurkusar zuciyarsa. Sai dai da yake shi din jarumin namiji ne haka ya daure yana ji yana gani har suka kammala jarrabawarsu suka bar makarantar. Wanda hakan ke nufin rabuwarsu ta har abada musamman wannan lokaci da abin al'ajabin ya faru. Lokacin da Goggo binta ta ce shuhuda mayya ce, wanda shi kuma ya karyata hakan ya fi alakantata da aljana, to tunda dama makarantar ce ta hada su yanzu kuma ta raba su. A 6angaren su shuhuda kuwa, shakuwar da aka ginata a 6angaren su shuhuda kuwa, shakuwa da aka ginata a wancan tubalin na aminta da kuma kuruciya an sabuntata ta dawo sabuwa dal! Don yanzu kam shakuwar da ke tsakanin shuhuda da Isah har ta zarta ta wancan lokacin. Kullum suna tare, hira suke yi yana ba ta labaran abubuwan da suka faru da shi a kasar senegal har tuhumarta ya yi ko tasan wata shuhuda ibn khaddab, amma tace ita sam ba tasan wata shuhuda ba, ita ba tama ta6a jin mai sunanta ba, don wani lokaci ma har tana tababan ingancin sunanta. To shi ma sai bai tsawaita bincike ba, don dama shi mutum ne mara son shiga harkar da ba tashi ba. Ana gama sallar isha'i ne yake shigowa dakin Inna yaduwa ya ci abinci tare da shuhuda, sannan ya zauna da su hira har sai karfe tara da rabi sannan yake yi musu addu'a ya ja musu kofa ya nufi 6angarensa. Wannan dabi'a ce da yake gudanarwa tun ranar da ya dawo, saboda haka babu wani guri da yake zuwa da daddare. A 6angaren maganar aikinsa kuwa Alh Rabi'u yace:o sam bai amince Isah ya koma wata kasa ba, shi ma ya tsaya ya amfanawa kasarsa, tunda ana bukatarsa. Bai damu ba, don tunda ya dawo ya dora idanunsa ga shuhuda sai ya ji sam baya bukatar abin da zai kuma janyo masa ya yi nisa da ita. Saboda haka aka soma nema masa aiki a kamfanoni da dama, duk da an yi tunanin bude masa kamfani na kashin kansa, to amma sai aka dakatar da wannan yunkuri saboda halin da ake ciki na karyewar tattalin arziki na al'umma. A haka har ya samu watanni uku da dawowa, izuwa wannan lokacin yana cikin wani hali wanda shi kansa ba zai iya kwatanta shi ba, domin dai ji yake kamar yana son ya auri shuhuda, kullum ta kawo masa abin karin kumallo ko na rana ko kuma idan suna hirar dare, wani irin nishadi yake ji na kwaranya masa. Idan ya gama yi musu hira ya koma dakinsa kafin bacci ya dauke shi, tunaninta ne ke bijiro masa ya dinga ganin kamar tana yi masa gizo. Da gaske babu tababa yana sonta, kuma yana son aurenta, amma ya kasa fada mata koda kuwa Inna yaduwa ya kasa fadawa, hatta da Alh Rabi'u wanda duk bayan, ya kasa 6usa masa maganar. Daga shi sai zuciyarsa, sai kuma Masanin halin da zukata ke ciki(Allah)
BABI NA TAKWAS .......... RUWAN ZUMA Inna yaduwa tana zaune a falo ita da dattijon mijinta tana 6are masa gyada mai 6awo yana taunawa a bakinsa, shuhuda ta shigo falon cike da murna kira ta ke. Inna! Inna kina ina? Tayi tsalle ta haye kan cinyoyin kakar tata, yayin da Isah ya shigo shi ma fuskarsa dauke da fara'a. Inna yaduwa tana kokarin tureta daga jikinta, tace: Ke ni daga ni shagwa6a66iya kawai, zaki wani shigowa mutane gida ba ko sallama. Alh Rabi'u ya dubi Isah yace: Abokina ya dai na ga amaryar tawa tana murna tamkar ranar sallah? Isah yace: Wallahi Baba takardunta ne suka yi kyau shine ta ke ta murna, tun fa a mota ta ke ta wannan murnar. Gaba dayansu sai farin ciki ya kamasu.
a Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤17¤¤
Alh. Rabi'u yace: Nima ba na shakka akan kwalwar amaryata, Allah ya sanya alkhairi.
Shuhuda ta washe baki tace: Amin Baba.
Ta ci gaba da zuba shagwa6ar farin ciki, Isah yana kallonta, yau hakurinsa ya kare, yana ganin rana ce da ya kamata ya yi amfani da ita ya sanar da shuhuda matsananciyar kaunar da yake mata. Ko ba komai ranar za ta zamo ta kafuwar tarihi masu dama a kundin rayuwarsa. Misali: Yau ranar ta kasance ta LITININ takardar shaidar tabbatuwar aikinsa da kamfanin NUEFI'A IRONIC METAL da ke jihar Ibadan ta same shi.
Ranar LITININ shuhuda ta dubo jarrabawarta Waec da Neco duka ta cinye, tana A1 a wasu darussan B3 a wasu.
Sannan ranar LITININ zata zamo cikin jerin abubuwan tarihi idan ya furta mata KALMAR SO.
Shuhuda ce ta katse masa tunani lokacin da ta mike tsaye. Inna bara na yi wanka tukunna na ci abinci ko? Ba ta jira amsa ba ta nufi hanyar daki don sauya kayan wanka.
Isah ya bita da kallo, tafiyarta ma dagwas-dagwas gwanin sha'awa. Shi ma sai yace: Bara na je daki na huta.
Alh Rabi'u yace: Anjima idan an gama sallar magriba ka zo zan aike ka gurin mahaifinka ka kai masa wasu kaya da a ka kai masa aikin hannu.
Isah yace: To. Sannan ya koma dakinsa yana ta kissima yadda zai tunkari shuhuda da bukatarsa ta soyayya, shin ko za ta amince ko ba zata amince ba?
Karfe hudu da rabi na yammacin ranar ya tarar da shuhuda zaune akan farar kujerar roba tana sanye da dorawar shadda shar da ita, dinkin fitted, rigar ta matse ta sai dai ba yadda al'aurarta zata bayyana ba, sannan zani ce aka yi mata don haka kwalliyar tata dai babu makusa.
Fuskarta narai-narai, har yanzu da akwai wannan murnar ta cinye jarabawa a tare da ita tana makale a fuskarta.
Kafin ya karasa gare ta ya yi tsaye yana kallonta, lallai idan ya sami nasarar auren shuhuda ya dace da kyalkyawar mace, wadda zata haifa masa kyawawan 'ya'ya. Sannan kamilar mace ce idan aka yi la'akari da yanayin shigarta.
Dubi dai yanzu yadda ta ci ado ta kame akan kujera, yadda kasan wata babbar mace ce ita, bayan duka-duka shekarunta sha takwas.
Kamar an ce daga kai! Ta dago kanta saboda kamshin turaransa da ya buwaye ilahirin gurin, suka yi tozali da juna. Sai ta sakar masa murmushi.
Ya tako a hankali ya ja kujera ya yiwa kansa mazauni, ta gayar da shi sai duk suka yi shiru shi da ita bayan gaisuwar, kanta na rusune a kasa yayin da shi kuma gaba daya ya dauki idanu ya daura mata.
Shirun dai ya dauki 'yan mintoci kafin Isah ya katse musu shirun da yin gyaran murya yace: Shuhuda!.
Ta dan dago kanta kadan tana satar kallonsa. Yace: Kin san me? Tayi shiru ba ta ba shi amsa ba. Ya ci gaba da cewa:
Wata magana ce mai muhimmanci nake son mu yi da ke, amma ina bukatar ki tattaro hankalinki da nutsuwarki zuwa gare ni. Kuma ina son ki fadan gaskiyar abinda ke cikin ranki.
Ba ta dai tanka ba, amma yanzu gaba daya ne ta ke kallonsa sa6anin dazun da kadan ta daga kai.
Ya kuma saka nutsuwa a tare da shi sannan muryarsa kasa-kasa kamar ba ya son wani ya ji. Yace:
Ko kin san me ye SO?
Yanayinta gaba daya ya sauya, 6acin rai ya bayyana a fuskarta, ta yi shiru ba ta tanka ba, kuma ba ta dauke idonta akan kwayar idonsa ba. Ya lura ba tasan so ba, wata kila ma ba ta ta6a yin katari da wanda yace yana sonta ba.
Shi kam hakan ya yi masa dadi sosai, saboda hakan zai ba shi damar kafa soyayyarsa a zuciyarta. Sai yayi murmushi mai kayatarwa ga wanda ya san sirrin murmushi, sannan yace da ita.
So wata kwaya ce da ke kafuwa a zuciya ta sababin wasu abubuwa masu muhimmanci, na farko KYAU, Idan mace ko namiji na da kyau, yana iya haduwa da masu sonsa ta sanadin wannan kyawun da Allah ya yi masa baiwa da shi.
ADDINI:- Idan mace ko namiji suna da addini ana iya sonsu saboda addinin da suke da shi. Ma'ana sun kasance masu yawan yin sallah akan lokacinta, kyautata addininsu da sauransu.
NUTSUWA:- Ita ma tana kawo a so mutum saboda ita.
KWARJINI:- Akwai mutanen da kwarjini ke sa a so su, ba don kyau ko addini ba, kwarjininsu zai sanya kawai idan aka gansu aji ana sonsu.
ASALI:- Nagartaccen asali yana sa a so mutum saboda an san asalinsa, tun daga nasabarsa zuwa mu'amalolinsa.
SHA'AWA:- Akwai mutanen da Allah ya yi su da raunin sha'awa, ma'ana idan za su ga mace ta yi shiga ko tafiya mai kyan tsari zasu kasance cikin sha'awar yin tarayya da ita, ba don asalin son ko kauna, illa sha'awar ce ta yi jagoranci.
A mafi yawan mutanen da suke soyayya sha'awar ce ke yi musu jagoranci, shi yasa ake yawan samun ma.......
Maganarsa ta katse sakamakon kwalla da ya gani shar a idanuwan shuhuda. Hankalinsa ya tashi, cikin rawar murya yace:
Sh....u.....hu......da........?
Ta rusunar da kanta kasa, ya matso kusa da ita cikin tausasawa yace:
Me ye na kuka? Ki fada min maganganuna ne suka 6ata miki rai?
Ta yi shiru tana shesshekar kuka, hankalinsa ya sake dagulewa, sai yake tunanin wata kila ta ta6a yin soyayyar, ko saurayin ya sota ne akan turbar SHA'AWA. Yanzu da yayi mata wadannan bayanan ta samu tabbacin sha'awar ce tsakaninta da shi.
Ko kuma ta yi soyayya da wani saurayi da yakan zaunar da ita ya yi mata kwatankwacin wannan bayanai, daga bisani Allah ya yi masa rasuwa.
Idan kuwa wannan zargin ya zama gaskiya, yana da yakinin ba karamar wahala zai sha ba kafin ya rushe wancan tubalin ya kafa nasa tubalin soyayyar ba.
SO RUWAN ZUMA, dole ne sai ya yi amfani da sanyayyen kalamai masu nutsar da zuciya gurin kawar mata da tunanin duk wani da namiji a rayuwarta, saboda haka ya ciro hankici daga aljihun rigarsa da nufin goge mata hawayenta.
Amma koda ya nufo fuskarta da nufin hakan, sai ta yi sauri ta kawar da kai gefe guda.
Ya yi murmushi yace:
To ki daina kukan idan ba kya son na goge miki hawayen.
Ta sa hannu ta goge hawayen, yana kallon kanta don fuskarta na rusune, yace: Shuhuda ina sonki!
Mikewa tsaye ta yi da sauri tana girgiza kai, muryarta na fitar da wani irin yanayi.
Bana soyayya saboda hatsarinta a gare ni. Bata bari ya yi magana ba ta ci gaba da cewa:
Bana soyayya saboda amsa tambaya, ita kuwa soyayya tana tafiya ne da amsa tambaya.
Bana soyayya saboda ban cancanta da ita ba.
Bana soyayya soyayya saboda ba zata sama min MATA'UL HAYAT ba, illa bankado da TASHIN HANKALI, wanda zai iya shafar duk wanda ya shafe ni.
Wani hautsinannen kallo yake mata na tuhuma, amma ba ya son tuhumarta tunda ya ga akwai mikin tabon soyayyar wani a zuciyarta, hanyoyin kafuwar tashi soyayyar ita ce a gaban shi.
Na ji, amma na tambayeki mana?
Ta daga masa hannu.
Na fada maka bana iya amsa tambaya, don ni kaina, ina da tambayoyin da zan yiwa kaina, to amma saboda wannan dalilin yasa na kan ajiye tambayoyina har zuwa ranar da zan samu MATA'UL HAYAT.
To wannan fa nasan zan iya soyayya har na samu damar amsa tambayoyi, nawa da na wasu ma gaba daya.
Ta daure masa kai matuka. Ya girgiza kansa, ya ce:
Shike nan, ni kuma zan jiraci wannan rana domin nasan ni ma zan samu MATA'UL HAYAT idan har na samu rasarar auren ki.......
Ta sake daga masa hannu.
Yah Isah kada ka jefa rayuwarka a hatsari, kada ka yi gaggawar sanya SOYAYYA a tsakaninmu, domin tana da mayukar hatsari.
Gargadi ne nake yi maka, ba shawara ko izina ba, idan ka ce zaka sanya soyayya a tsakaninmu hakan zai iya haifar da TASHIN HANKALI, RUDANI, TAKAICI da kuma NADAMA marar amfani.
Tana kammala zancenta ta yi gaba yana kwala mata kira amma sam ta ki tsayawa.
Ya dade zaune a gurin yana murmushi, yasan ba komai ne ke

Please Login or Register in order to submit comment