Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma iska zai yi maka lahani tunda ba ka saba ba. Yace; Ke mai yasa bai yi miki lahani ba kafin ki saba? Tace: Ni? Ai babu abin da ke min lahani irin iska, kullum fa na koma gida sai na suma, mamata ta yi ta kwara min ruwa sannan na ke farfadowa.
Wannan yarinya ta gama raina masa hankali, abin da ya ayyana ke nan a ransa. Koda yake ya shiga tababa shi ma na zamantowarta mutum kamar yadda ita kanta ta ke tababa. Shi kam yaci alwashi ko ma aljana ce zai ci gaba da bibiyarta har ya gano ko wace ce ita. Da farko ya so sharewa da lamarinta amma a cikin kwanaki hudun da bai kulata ba, zuciyarsa ce ke azalzalarsa, ya shiga wani irin bahagon, yanayi na mararinta daurewa kawai ya yi yana kawar da kai ga duk abin da zai alakanta shi da ita, amma hakan ya ci tura.
Ya dai yarda ya kuma amince ya kamu da matsanancin son halittar da bai san tartibin daga cikin halittun da ta fito ba.
Ya ja gauron numfashi kafin yace: Kinga ni ma idan iskan ya yi min lahani sai maman taki ta kwara min ruwa na farfado. Wannan karon ma sai da ta kuma yin dariyarta, sannan tace;
Gaskiya mamana ba ta bari na je mata gida da wani, wai ba ta son ganin bakuwar fuska a gidanta. Ta fi son kullum ta ga fuskar da ta sani.
Ko me ye dalilin hakan? Ya bukata yana tsare ta da idanu.
Nima ban san dalili ba. Ta bashi amsa cikin yanayin damuwa. Na dai lura baki son naje gidanku.
To ai ban san me yasa kake son zuwa gidanmu ba. Ta fada. Ina son na gaishe da mahaifinki. Inji shi.
Ba zato ba tsammani yaga hawaye sha-shar na zuba daga idanuwanta, kafin yace wani abu ta ci gaba da cew:
Mahaifina Allah yayi masa rasuwa a gidan gonarsa, sanadin tuntu6e da ya yi da kahon LIBHAS, ya dinga aman jini daga karshe aka dangana shi izuwa asibit acan ya rasu, kuma a ranar aka haife ni.
Cikin yanayin tausayi da rudani yace: Me ye LIBHAS? Tace; Nima ban sani ba, kawai dai an fada min da shi ne yayi tuntu6e.
Wa ya fada miki? Ya bukata. Ta daga kanta sama kamar mai tunani can tace.
Ni ko shi mahaifin nawa ne ya fada min? Ko kuwa YAKUB ne? Inna Yaduwa? Kai ni na manta, ban ma dai sani ba. Amma kuma kamar da KAHON LIBHAS ya yi tuntu6en.......
Akwai alamar tambaya mai karfi na zamantowar Shuhuda mutum, saboda ya za a yi mutum da ta ce a ranar da ya rasu ta zo duniya kuma har ya samu damar fada mata da ya yi tuntu6e da shi? Kaddara ma shi din ne ya fada, sai dai ga waninsa da ta yi wayo kuma aka sanar mata.
Waye Yakub da Inna Yaduwa? Duk yadda aka yi tana da alaka da su kuma zai iya yiwuwa cikinsu din ne wani ya fada mata. Idan haka ne me ye gaskiyar lamarin MTUMCE ITA KO ALJANA?
.
Mu taru littafi na biyu.
.
.
MATA UL HAYAT BOOK 2
......... Yadda TSAUTSAYI ya hada mu
yanzu a gaba KADDARA zata hada mu......
....... Kafin hannun ya isa jikin Shuhuda sai ya sandare Inna yaduwa ta ji gaba daya jijiyar hannunta sun daskare kamar babu jini a tare da hannun.
..... An fada miki ana dukana? Ko don kinga ina raga miki? To sauke hannun....
...... Ai dik yawona ban kai TANZIF ba, wanda yana iya zuwa kasa goma a kwana goma.....
...... Na fada maka bana iya amsa tambaya don ni kaina ina da tambayoyin da zan yiwa kaina, to amma saboda wannan dalili yasa na kan ajiye tambayoyina har zuwa ranar da zan samu MATA'UL HAYAT......
...... Amma cikinta na juyawa kamar ana wana wani abu, kwatankwacin yadda idan an harba kwallo take.......
....... Wannan Shuhudar itace muka hadu fa da ita a birnin.......
Wadannan tare da wasu zallan chakwakiya dik zaku samu amsar su sinqi-sinqi a sassanqame a cikin wannan gida me Albarka.
.
.
Taku har kullum
Zahra'aru Baba yakasai
Maman Shureim.
.
Allah ya jikanta ya gafarta mata Ameen
.
Ta ku a kullum kuma a koda yaushe me muku posting Sadiq Halima (Sadin Mama) er mutan NIGER.
Hada Hausa Book stories
====MATA'UL HAYAT BOOK 2====- ==========¤¤11¤¤==========- Katse masa tunani ta yi da cewa. Mahaifina na sona amma sai Allah bai nufa za a haife ni a lokacin da yake da rai ba. Bayan mahaifina mutum daya ne yaso ni kamar mahaifin nawa, shi kuma ya ta fi kasar Senegal karatu. Uncle Hamza yace: Da gaske kike? Ta yamutsa fuska sannan tace: Ban gane ba? Yace: Mahaifinki ya rasu? Tace; Tabbas! To ina mahaifiyarki? Ko ita ce Inna Yaduwa? Ta girgiza kai, Ba ita ba ce Inna yaduwa, mahaifiyata ta yi aure. Ina zaune ne a hannun Inna yaduwa wadda ta haifi mahaifina. Yace: Allah ya jikan mahaifinki........ Ba ta amsa ba, sai suka yi shiru su duka can ya dago kai yana dubanta, yace; Rannan kin shigar da korafin kada na yi miki tambaya wadda ta shafi bil'adama ko me ye sanadi? Tayi murmushi tace: Saboda ka yi min bayanin waye dan Adam kuma na gamsu. A matsayinka na malamina nasan kana son dorani akan abubuwan da ban sani ba. To shi yasa na ce maka haka. Ka ga sai ka yi min tambaya a wasu halittun wata kila kai ba ka sani ba, ni kuma na sani sai na ba ka haske kamar yadda ka yi a gaske. Zai yi magana ke nan 'yan ajin wajen su goma suka danno kai, sakamakon lokacin da ya kare don haka ya fasa maganarsa. Ya mike tsaye ya koma gaban allo a inda kujerar malamai ta ke, don dama shi ne da darasi da zarar an dawo. Ya yi zaune yana tunanin maganganun da suka yi da Shuhuda ya dinga auna su a mizanin da ya dace ya ajiye su, amma dai ya gaza gane inda suka fi cancanta ya dora maganganun nata. A haka dalibai suka dawo gaba daya ya ci gaba da gabatar musu da darasi. ******** ********* ******* Tun daga wannan rana Uncle Hamza bai kuma samun sararin tsayawa da Shuhuda ba kasancewar ana cikin lokacin karatu ka'in da na'in sakamakon jarrabawar da ke tunkarowa. Gaba daya ya tattara al'amarinta ya kyale idan ma ya shiga ajin ba ya bari ko kwayar idanunsa ta gani koda yaushe cikin bakin gilashi ya ke. A haka suka cinye wannan zangon karatun aka yi musu hutu. Wata ranar laraba Shuhuda na kicin danwake ta ke yi. Yau tunda ta shi ta ke mitar a yi dan waken. Ita kuma Inna yaduwa ta tace ba zata yi ba, idan tana bukata ta shiga kicin din ai ita ma mace ce.
Dariya Shuhuda ta yi ta nufi kicin tana cewa: Kin dai san zan iya girkawa ko? Shi ne ta shigo kicin tana hakilon yin danwaken.
Inna yaduwa na falo tana kallon yadda Shuhuda ta ke shige da fice daga kicin zuwa falo.
Ta gama danwaken ta zo falon ta zauna ta yanka tumatiri, Inna yaduwa ta kawar da kai gefe guda ta nuna kamar ba tasan da shigowar Shuhuda ba.
Ana haka ne wani yaro ya yi sallama Inna yaduwa ta amsa? Yaron yace:: Wai an ce Shuhuda ta zo ana kira a waje. Shuhuda ta dago kai da sauri ta dubi yaron, tare da cewa: Ni din ake kira a waje? Yaron ya daga mata kai alamun tabbatarwa.
Tace: Ka je kace nan gidan babu Shuhuda. Yaron ya juya zai fita Inna yaduwa ta tsayar da shi. Kai tsaya. Ta aikawa Shuhuda sakon harara. Don tsiya an aiko kiranki za ki ce babu Shuhuda a gidan nan?
Shuhuda ta juyo ga Inna yaduwa idanunta jajur tace: To ina Shuhudan? Ina ce ni sunana YAKUB?
Inna yaduwa ta sake kulewa, ta kaiwa Shuhuda bugu da hannu. Amma kafin hannun ya isa jikin Shuhuda sai ya sandare, Inna Yaduwa ta ji gaba daya jijiyar hannunta sun daskare kamar babu jini a tare da hannun. Shuhuda tace:
an fada miki ana dukana? Ko don kinga ina raga miki? To sauke hannun.
Bisa ga tsanani al'ajabi sai hannun ya koma Shafal, Inna yaduwa ta tsorata ainun ga wannan lamari, shi kuwa yaron dariya ya kama yi, don bai da isasshen wayo.
Shuhuda ta dubi yaron tace: Ka je ka cewa wanda ya aiko ka nan gidan babu Shuhuda. Yaron ya juya yana dariya, ita kam Inna yaduwa gaba daya tsurewa ya yi. An ya kuwa wannan yarinyar ba aljana bace?
Jikinta na 6ari ta mike ta nufi dakinta. Waya ta dauka domin kiran 'ya'yanta ta sanar da su abin da yake faruwa. Amma wani rudanin da ta lalubo lambar da zata kira, tana kira sai kawai wayar ta kashe kanta, kuma ga cikakken caji, amma kiran ya ki yiyuwa.
Ta yi jigum tana mamaki, wannan aikin jinnu ne, babu tababa Shuhuda aljana ce, idan ta yi la'akari da kwararan hujjoji. Misali: An tsarga yatsanta an ga nono na zuba. Anje asibiti allurar da aka yi mata ta karye, daga baya labari yazo likitan ya rasu. Mas'ud ya ji mata rauni an ga nono maimakon jini, sannan tana wasu dabi'u wadanda sun zarce ace lalurin ta6uwar kwalwa ce.
Anya kuwa lokacin da za a haifi Shuhuda jinnu ba su yi musayarta da diyarsu ba?
Ba shakka wannan haka yake, jinnu sun dauke diyar Karimatu a ciki ko bayan ta haihu suka sauya mata wata 'yar da tasu.
Idan haka ne me ye abin yi? Zuciyarta ta ci gaba da bugawa ta rasa abin da ke yi mata dadi a rai. Tana cikin wannan hali Shuhuda ta shigo dakin a rude tana cewa:
Wayyo zai kashe ni Inna, ki taimake ni. Wallahi mugu ne! Ga shi can an hana shi shigowa , kashe ni zai yi! Kafin Inna yaduwa ta samu damar tofawa tuni Shuhuda ta 6uya a bayan Inna yaduwan. Sai kuka ta ke tana kiran taimako.
Kan Inna yaduwa ya daure sosai, tsoro ya sake shigarta ba tasan lokacin da ta rukunkume Shuhuda ba tana cewa.: Waye?
Shuhuda ta kasa magana kuka kawai ta ke yi kamar zata shide a gurin.
Cikin jarumta Inna yaduwa ta 6am6are jikinta daga na Shuhuda ta nufi falo. Ba ta ga kowa ba, tana tafiyar sanda ta fito harabar gidan. Nan ma ba ta ga kowa ba, hatta maigadi babu shi babu alamarshi, sai dai a kofar gida ta jiyo hayaniya, don haka kai tsaye can ta nufa.
Ta tarar da kofar gidan dankam da mutane, wai wani 6arawo ne aka kama ya shiga wani gida a layin yayi sayar Generator.
Da ta dawo gidan iske Shuhuda ta yi kwance dai-dai akan gado yadda kasan ta dauki lokaci tana bacci.
Inna yaduwa ta kai hannu tana bubbuga kafafun Shuhuda alamun tayar da ita. Shuhuda ta bude idanunta sun yi jawur saboda bacci ta ke kashir6an. Inna yaduwa tana hada ido da Shuhuda sai ta rasa me zata ce mata, hasalima duk sai ta ji ta manta abubuwan da suka faru a dazun.
Cikim muryar bacci Shuhuda tace: Inna lafiya kika tashe ni? Inna yaduwa tace: Kin gama cin danwaken ne? Ta girgiza kai. Ai na fada miki ya lalace, ba shi yasa na shigo daki ba don takaici?
Inna yaduwa ba ta san ya aka yi ba, sai cewa tayi. Af! Anyi haka fa! Amma duk da haka ki tashi baccin nan, ki dora mana girkin dare, kinga har uku ta gota. Shuhuda tace: Wallahi Inna ba zan iya kuma shiga kicin ba, har yanzu raina bai gama yin sanyi ba.
Inna yaduwa ta yi murmushi tace: Ai dama kallonki kawai nake amma yaushe zaka yi danwake ka zuba gishiri a cikin kwa6in? Shuhuda ta koma ta kwanta.
Ai na gama yin danwake har abada, ni sam ya fice min daga rai. Ta karashe maganar tare da lumshe idanu alamun zata koma bacci. Inna yaduwa ta koma falo ta zauna akan kujera tunaninta ya dan dawo, ta tuna abubuwan da suka faru ko kuwa a mafarki ne?
Ta shiga tababar yadda abubuwan suka faru kamar gaske, kamar kuma a mafarki? Mikewa tsaye ta yi a lokacin da zuciyarta ta gama yanke mata yanke mata duk abin da ya faru a bayyane ne don haka zaman gidan bai ganta ba, zama da aljana?
Sai dai me? Tana mikewa da wannan kudirin sai ta ji wata irin kasala ta zo mata ta ji kamar ta manta yanda abubuwan suka faru.
Bayan sallar magriba Inna yaduwa da Shuhuda suna zaune a falo tamkar kurame haka suke. Babu wadda ke yiwa wata magana, kowacce da abin da yake yi mata yawo a rai.
Alh Sada ya yi sallama tare da shigowa. Ya gaishe da Inna yaduwa. Shuhuda ta gaishe shi, sai suka yi shiru. Inna yaduwa na son sanar da shi abin da ya faru amma ta gaza daga harshenta bare ta furta.Wani irin nauyi ta ke ji harshen nata ya yi mata.
Shirun ya dauke su wani wani lokaci kafin daga bisani Alh. Sada ya katse musu shirun da cewa:: Inna jiya angonki yana tambayata ku wai ba ya samun wayarki.
Inna yaduwa ta yi gajeran murmushi tace: Bar ja'iri bai neme ni ba. Amma ni da wayata kullum ta ke da caji? Shima Alh Sadan murmushi yayi. Yace; Ni ma abinda nace kenan. Tace: Yaushe zai kare karatun na shi ya dawo ne? Alh Sada yace: Saura Shekara biyu ya fada min kila ma a can zai yi aiki. Saboda tun yanzun gwamnatin kasar ta fara kyarkyararshi. Kin san angon naki akwai himma.
Tace: Dama haka ake so. Alh. Sada ya dubi Shuhuda yace: Ke ya 6angaren naki karatun? Na ji an ce ba ki mayar da hankali. Wani malaminki ya same ni yace idan kin je makaranta babu abin da kike sai wasa, haka ne? Ya karashe maganar cikin yanayi na zolaya.
An ta6owa Inna yaduwa inda yake mata kaikayi, amma koda ta hada idanu da Shuhuda sai ta ga kamar tana yi mata gargadi kada ta yi magana. Ta daure cikin jarumta da niyyar furta abinda ke ranta, amma sai sa6anin hakan ya fito daga bakinta.
Ai kuwa ba a ce Shuhuda ba ta karatu ba, yarinyar da kullum ba ta da wani aiki sai na karatu? Kawai dai ina ganin irin wadannan malaman ne da suke da kyashi akan kwalwar da dalibansu suke da ita. Alh Sada ya fadada murmushinsa yace:
Gaskiya shi ma shaidar kirki ya yi mata yace duk cikin dalibansa babu wadda ya yaba da kwalwarta kamar Shuhuda, kawai na yi hakan ne don na tabbatar da abin da ya fada.
Inna yaduwa ta rasa me yasa ta kasa fada masa cewar: Shuhuda aljana ce, babu abinda ta sani sai shirmen aljanu! Shuhuda kam rusunar da kanta ta yi kasa kawai ta yi. Nan ya dan ja Inna yaduwa da labari yana sanar da i2a abinda malamin ya fada masa. Daga karshe yace:
Yaron yana da nutsuwa da maida hankali game da dalibansa. Yace min shi dan asalin katsina ne, sunansa Hamza. To yadda ya ga yarinyar na da kokari ne yasa ya biyo sawu ya yi tambaya ya gano ko su waye iyayenta, shi ne yazo. Da a ce za a dinga samun malamai irinsa lallai da iyayen yara sun ji dadi, don gaskiya ba karamin dadi na ji ba da har wani malami ya wanko kafafunsa ya zo musamman don ya yaba irin kojarin da Shuhuda take da shi ba.
Inna yaduwa dai ta yi shiru, don ta kasa furta abin da ya faru din, Da ta yi yunkurin hakan sai ta ji harshenta ya yi mata nauyi. Don haka har Alh Sada ya gama maganganunsa ya yi musu bankwana ba ta iya furta abin da ya faru ba.
Hutun 'yan makaranta ya kare, don haka daliibai da ke makarantar kwana suka soma komawa tun a ranar lahadin farko, Shuhuda kuwa da ke jeka-ka dawo ta wanke kayanta har ma da sabbin kayan makaranta da Alh Sada ya dinka mata.
Ta hada komai na komawa makaranta gari kawai ta ke jira ya waye ta ganta a cikin makaranta. A cikin satin nan gaba daya Shuhuda ta sauya ta koma wata irin yarinya mai tsananin natsuwa hankali da kula da addini.
Inna yaduwa tana ta tsananin mamakin yadda Shuhuda ta sauya kamar ba ita ba. Sam babu wannan shirmen nata, koda yake har yanzu Inna yaduwa ba ta aminta Shuhuda mutum ce ba. Sai dai ta rasa yadda aka yi ta kasa bayyanar da hakan ga wani, ko shuhudan ma ta kasa yi mata magana bare ta sake tabbatarwa aljana ce.
Washegari ranar litinin Shuhuda ta tafi makaranta, kasancewar makarantar ta kudi ce, shi yasa dukkan dalibai sun dawo gudun kada a hukunta su. Sa'adatu wadda suke kujera daya da shuhuda ita ta fara lura da sauyin da aka samu a tare da shuhuda, sannan sauran dalibai ma suka fahimta.
Kowa yayi murnar yadda Shuhuda ta samu lafiya, domin sun dauka cutar tata ta ta6in hankali ce, to yanzu kuma gashi ta warke. A ranar unlce hamza bai shigo ajin nasu ba, duk ma tsayin makon bai shigo ajin ba har sai da wani makon ya shigo.
da Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤12¤¤
Da ya shigo ajin ya yi darasi yaga sauyin da aka samu a tare da shuhuda anin ya ba shi mamaki, shin da gaske dama ta6uwar kwalwar ce gare ta? Ko kuwa kaifin kwalwarta ne ya soma da kushewa? Da aka fita break fast ya shigo ajin amma bai tarar da ita ba kamar yadda ta saba zama a ajin idan an fita break.
Sai da aka kusa komawa ya hangota tana tafiya. Ya yi wuf ya fito daga dakin malamai ya sha gabanta. Ta rusuna ta gayar da shi, ya amsa tare da cewa: Yau ya aka yi kika fita tara ke da kika ce daga gida kije ciwo abinci? Tace: Yau ban ci komai ba doki nake na zo makaranta.
Yace: Wata kila don kina son ganin malaminki ne mai shisshigi ko? Ta yamutsa fuska cikin rashin fahimta, amma ba ta iya cewa komai ba, ya daga gira sama kafin yace: Eh mana, ko ba a fada miki na je can gidanku Misra ba?
Ya karashe maganar cikin yanayin zolaya. Kanta na sunkuye kasa ba ta dago ba. Ya ci gaba da kallonta, yace: Har ma muka gaisa da dan'uwanki YAKUB? ya karramani, ashe dai gidanku babban gida ne?
Har yanzu ba ta ba shi amsa ba. Ya gyara tsayuwa yana murmushi yace: Ai na fadawa Yakub ina so ya ba ni aurenki, kuma da yake da ne mai karamci da yakana, sai ya ya bani har yace zai shige min gaba a gurin neman aurenki.
: Ta dago kai da sauri alamar ta razana amma ba ta tanka ba Shi kuwa Uncle hamza murnushi ya kuma yi, yace: Ko ba ki sona nw? Bata amsa ba sai kawai ta yi gaba , bai yi yunkurin dakatar da ita ba, saboda a ganinsa kunya ce ta hana ta tsaya. Sai ya cizi la66ansa ya koma dakin malamai ya zauna. Wani irin nishadi yake ji a zuciyarsa.
A da ya dauka shuhuda ba mutum bace, to amma tunda ya je gidan yayan mahaifinta ( Alh sada) ya tabbatar mutum ce sai kuma da ya je gidan Inna yaduwa. Dan'uwanta yakub ya fito ya karrama shi, shike nan ya sake sakankancewa, ya kuma yadda lallai ya kamu da son Shuhudan. Hakan ne ma yasa ya gaza 6oyewa har sai da ya tunyu6i yakub din. Kuma sai ya samu hadin kan Yakub inda har ma yake yi masa bayanin Shuhuda lafiyarta kalau. Kwalwa ce ta yi mata yawa, amma zai sha mamaki ranar da zai ganta a makaranta da sauyawar abubuwa da dama.
Don ya hanata yawan karatun nan na kure rai da ta ke yi da rana. Kuma sai ga shi din ya sha mamakin tunda ya ga sauyawar abubuwa da dama a tare da Shuhuda.
A ranar yana da darasi da su, har kosawa yayi lokacin ya yi ya shiga ajin ko don ya ji muryar Shuhuda cikin tsadadden turancin nan nata wanda ko dan kasar Amurka sai haka.
Lokacin na cika cije da doki ya nufi ajin nasu shigar da ya saba wadda ta ke kar6ar fatar jikinsa, wato shigar dogayen kaya, na danyar shadda ta tsadaddiyar hula gami da takalmi 'yan asalin kasar spain sai agogonsa kirar kasar Germany.
Duk wanda zai ga uncle hamza zai yaba da tsananin kyawun da ya yi don shi din mai kyau ne. Ga kuma dorinar ado da yake da ita. Zai yi wuya ya yi shiga ba a ga zahirin kyansa ba. Yana shiga ajin ya dora idanunsa a kujerar da Shuhuda ta saba zama. Yau din ma tana zaune kanta na sunkuye ga dukkan alamu littafin da ke gabanta ta ke dubawa. Amma jin hayaniyar gaishe da uncle hamza da daliban ajin ke yi yasa ita ma ta bi sahunsu ta gaushe shi.
Ya ba su umarni da su zauna . Kowacce ta zauna a hankali ya fara yanyara turanci yana yi musu bayani game da Equalibrium?
Kowacce ta nutsu tana saurarensa har ya kai ga yi musu tambayoyi ana ba shi amsa. Amma sai bai ji Shuhuda ta yi magana ba, shi kuma abinda yake so yaji muryarta.
Don haka kawai sai ya jefo musu tambaya akan Wave wanda ya shafi darasin physics kuma yana da yakinin ba su kai gurin ba. Ya dai san Shuhuda ce zata iya amsa wannan tambaya. Sa6anin hasashensa sai ya ji ajin ya yi tsit! Babu wanda ya koda motsa da nufin amsawa.
Ya sake saurarawa Shiru, sai ya yi murmushi yana duban Shuhuda yace: Ke ya baki bamu amsa ba? Ita ma murmushin tayi tace: Ban sani ba uncle. A kalla ya dai samu abinda ya ke so tunda ya ji kalma daga bakinta.
Ya zakuda kafada. Yace: Shike nan ya zama aikin gida(home work) zan kar6a gobe idan Allah ya kaimu. Yana karashe fada ya sa kai ya fice daga ajin. Washegari gaba daya Shuhuda ta hana kadaituwarsu, don lokacin da aka fita break fast ya shigo ajin bai ganta ba. Bata kuma komawa ajin ba har sai da aka shiga. Babu sararin kadaicewa da ita.
Da aka tashi kuwa yana hangota tana tafiya zuwa inda direban da ke kawota makarantar yake tsayuwar jiranta. Da saurinsa ya fito daga dakin malamai amma koda fitowarsa sai ya ga tuni har motar ma ta tashi.
Yaja turus ya tsaya yana cizon la66ansa. Ya yi tunanin ya bita har gidansu. Amma sai ya tuna maganar Alh Sada inda yake ce masa, ya ji dadin yadda ya zo har gida don yaba kwalwarta, amma ba su bukatar wata doguwar alaka tuinda Shuhuda yarinya ce, karatu ne yanzu a gabanta.
A lokacin uncle hamza ya yi matukar mamakin yadda farat daya Alh sada ya fahimci abin da yake cikin kwayoyin idanunsa, har ya yi masa irin wannan gugar zanan.
Wannan tunani da ya yi shi ya hana shi bin bayan Shuhuda ya yanke shawarar idan ya koma gida zai kira lam;bar da yayan Shuhuda(yakub) ya bashi don dama tunda ya kar6i lambar bai kirashi ba.
Kullum yana son ya kira sai ya yi tunanin abin da zaice da shi shi yasa bai kira shi ba tun can baya. To amma yana ganin yau yana da cikakkiyar dama ko don ya ji muryarta.
Hakana kuwa ce ta faru, bayan ya koma gida ya yi wanka ya ci abinci tare da sallah. Yana zaune a falo ya dauki wayarsa ya lalubo lambar yakub. Ya kira:
Mamaki ya kama shi lokacin da yaji sautin kiran maimakon trin-trin sautin da ake ji idan an kira layin MTN ko ZAIN, sai yaji Triiiiiiin! Kamar ya kira layin GLO ko ETISALAT. Shi dai yasan layin da layin da YAKUB ya ba shi MTN ne mai 0803, to amma sai ya ci gaba da kasa kunnuwa yana saurare. Har wayar ta ganma kara ba a daga ba, bai hakura ba sake nema ya yi a karo na biyu. Nan ma ba a daga ba, sai ya ajiye wayar a gefensa ya janyo laptop dinsa yana dube-dube.
Kira ya shigo a wayarsa, ya dauka ya duba, bakuwar lamba ce kuma ga dukkan alamu daga kasar waje ne, saboda yadda CODE din lambar ya fara da +2011.
Cikin rashin sanin wanda ya kirashi ya kara wayar a kunne bayan ya latsa malatsin O.K. Sallama aka yi masa wadda kana ji kasan mai sallamar harshensa ya karye da larabci. Uncle yace cikin Harshen Hausa. Waye akan layi? Daga

Please Login or Register in order to submit comment