Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saurin katse ta da cewa: Ko daya Inna. Ai samun sahihiyar mace guda daya ya fi ka tara mata hudu da suke tayar maka da hankali. Ni kam a ra'ayina mace daya nake son aure, musamman don na samu zaman lafiya tsakanina da iyalina.
Inna yaduwa ta sake murmusawa tace: Sai aka ce maka idan mutum ya auri mace fiye da daya ba zai samu kwanciyar hankali ba?
Yace: A'a, amma ni dai ra'ayina mace daya ne, saboda nasan idan na auri biyu daya ta fi kayutata min, sai na nuna rashin adalci a tsakaninsu.
Shuhuda ta shiga cikin zancen tace: Ni kuwa a nawa ra'ayin ina son zama da kishiya, domin 'yar uwa ce, akawai matan da suke mantawa da girman amfanin zama da kishiya, suka dauki kishiya a marsayin abokiyar gabarsu.
Wasu sun iya KISHIN BIRNI su 6oye kishinsu a zahiri, sai dai karfar baka, ko kuma KISAN MUMMUKE, yayin da wasu kishin na su ke gaza 6oyuwa zaka ga ma wasu har buge-buge da yage-yage suke yi a junansu.
An sani dukkan mace an halicce ta da kishi, to amma babu mafi dacewa a yi kishin na nuna kyautatawa ga miji, a ririta shi, a mantar da shi damuwa ba wai a saka masa wata damuwar ba.
Tun da ta fara wannan bayanin ya ke kallonta, mamakin yadda tasan wannan mas'ala yake, a matsayinta na karamar yarinya wadda ba ta ta6a yin aure ba bare zama da kishiya, kuma ta rayu a gidan da babu kishiya.
Hakan ya tabbar masa ko wane mutum da irin NASIBINSA, ita kam ta samu nasibi mai kyau, sai fatan Allah ya sa ta dore da wannan halayya nata.
Inna yaduwa tace: Ke duk ya aka yi kika san haka?
Shuhuda ta yi dariya, tace: Haba Inna, kada ki ba ni kunya mana? A tunanina kinsan mace tana da sani game da lamuran kishi ko da kuwa ba ta shiga fagen ba, sai dai wata idan tana da raunin tunani ba zata gane hakan ba har sai ta shiga fagen. Ni kuwa na sani, kuma ina da ALAKAR da zan sani.
Inna yaduwa tace: Saboda kin zauna da kishiya ko? Shuhuda tace: Ko ban zauna da ita ba, zan iya sani, saboda ALAKAR na sanin.
Inna yaduwa tace: Lallai kam tunda ubanki yana da mata biyu(Alh Sada take nufi) dole ki sani. Sai duk suka yi shiru saboda girman maganar.
Inna yaduwa tace: Ja'iran kawai, ni ka tashi ka bamu wuri haka nan zamu kwanta.
Shuhuda dai ce, idan ba ka manta ba tun kafin ka je kasar masu jajayen kunne na sanar da kai ba zan ba ka aurenta ba.
Shuhuda ta yi tsagal tace: Haba dai! Ai ko ba ki ba shi aurena ba, ni sai na aurasa masa kaina.
Inna yaduwa ta daga hannu zata kaiwa shuhuda duka, sai ta tuna da abin da ya ta6a faruwa lokacin da ta yi yunkurin dukan nata, don haka ta yi saurin sauke hannunta, tana cewa:
Rufe min baki rasa kunya 6eran tanka. Isah yace: Yauwa amaryas, fada mata ta ji da kyau. An fada mata har yanzu kambun nata yana tasiri? Ya karashe maganar yana kokarin mikewa.
Inna yaduwa ta aika masa sakon harara, tace: Na ce ka wuce ina so mu kwanta. Yace: Ba sai kin kore ni ba, ni ma baccin nake ji. Ya soma tofa musu addu'o'i yace: Mu kwana lafiya. Bai jira amsarsu ba ya ficce.
A ranar bai yi mummunan mafarkinsa ba, tunda ya kwanta ko motsawa bai yi ba sai gabanin sallar asuba.
Lallai addu'a makami ce ga dan Adam, dubi dai kwanaki biyu matsalolin da ya samu akan rashin addu'a, amma yau da yake ya yi addu'ar sai ga shi da yin bacci cikin nishadi.
Koda ya gama sallar asuba dakinsu ya nufa, sai dai ya tarar da shuhuda zaune akan sallaya tana Azkar din safe, yayin da Inna yaduwa ta ke kujiba-kujibar dama koko, don ita Allah ya yi ta ba mai ganda ba ce, don haka ma ko 'yar aiki ta ki aminta a ajiye mata.
Zaunawa yayi a gefen gadon ya na jiran ta kammala lazimin su gaisa, amma har tsayin lokaci ba ta dakata ba, shi kuma yana son ta datse su gaisa ya koma daki don yin sababben baccinsa, hakan ta gaza samuwa.
Da ya ga ba ta da niyyar tsayar da lazimin nata su gaisa, sai ya mike tsaye ya fice daga dakin.
Yana fitowa falo suka yi kici6us da Inna yaduwa ta fito daga kicin. Ya rusunar da kai yana kokarin shigewa sashensa, Inna yaduwa ta ambaci sunansa, ya juyo yana kallonta. Ita kuma ta zauna akan kujera fuskarta a dan daure.
Ganin ta zauna ya tabbatar magana ta ke son yi da shi, sai ya dawo falon ya zauna ya yi shiru yana sauraren abin da zata fada.
Ta sauke gwauron numfashi, sannan ta dora da cewa: Isah magana zamu yi da kai ta fahimta, kuma shawara da gargadi ne a gare ka. Ka ga wannan yarinyar shuhuda da kake gani ko, bana son abin da zai ta6a ranta ko sakata a damuwa.
Abin da yasa ka ji na fadi wannan maganar wani abu ne yake yi min ciwo a rai, na rasa wanda zan kama na sanar da shi abin.
Yanayinta ya sauya gaba daya, ta koma kalar tausayi, hakan ya sa shi ma Isah yanayinsa ya sauya, ya dai kasa kunnuwa yana saurarenta.
Zata ci gaba da magana ke nan, shuhuda ta shigo falon, Inna yaduwa ra dago kai suka hada idanu, sai ta ga kamar launin idanuwanta sun sauya daga fari da baki zuwa wata WALKIYA, don haka da sauri ta rusunar da kwayar idanunta kasa.
Isah kuwa da ya dago bai ga komai ba, illa ya ga shuhuda tsaye a bakin kofa sanye da hijabin sallarta. Shuhuda tace:
Yaya don Allah kayi hakuri, wallahi idan ina azkar ba na son tsinkewa saboda idan na koma ba zan iya yin adadin da nake yi a kowacce rana ba.
Yana murmushi yace mata. Kada ki damu. Tana kokarin zama, tace: Hala wannan tsohuwar ta zaunar da kai zata yi maka shirme ko?. Babu wanda ya tanka mata. Bayan ta zauna tace: Yaya barka da kwana. Yace: Min tashi lafiya?.
Tace: Kalau, don na fi wannan tsohuwar, tunda na lura yau tunda ta tashi a suku-suku ta ke, ko kuwa neman rigima ta ke? Ba shakka don mun ce ba zamu je katsina da ita ba ne ta ke neman ayi rigima da ita.
Inna yaduwa ta yi murmushin karfin hali, tace: Sha kuruminki idan dai ni ce ko da kunce ba zaku je da ni ba, ba zan damu ba. Shuhuda tace: Ke dai ki ce kin yi abin nan da Hausawa sukan ce, Wai abin da baka samu gama shi da baka so, ko kuwa yaya? Ya girgiza kai yace: Kwarai kuwa.
Inna yaduwa ta mike tsaye, tace: Isah bai so tashin Inna yaduwa ba, ya so ta sanar da shi abin da yake damunta har ya ji tausayin 'yar tsohuwar ya kama shi. Wata kila ba ta jin dadin zama da shuhuda.
shi kam a yadda yake ganin shuhuda ba ya tunanin tana da wani mugun hali da wanda yake zaune da ita zai koka. Domin ta kasance kamilar budurwa, da ace irin 'yan matan yanzu ne yadda ta ke zaune da kakarta, da kullum sai ta sakata kuka, amma sam shuhuda ba ta da wannan hali, ba ta son ma yin irin wannan haramtaccen wasan na JIKA da KAK , don da yawa wasu wasanni da ake yi jika da kaka ya haramta. Wasa na rashin ganin girma da nuna kuruciya a zahiran.
Bayan tafiyar Inna yaduwa shuhuda ta dubi Isah tace: Yauwa Yah Isah, wai kana da Umdatul Ahkam? Yace: Me zaki yi da shi? Tace: Karatu. Yace: A'a ba ni da shi, amma anjima idan mun fita siyayyar tsaraba sai mu nemo ko?
Tace: Allah ya kaimu. Yace: Amin, amma kafin nan bari idan na shiga daki zan fito miki da wani littafin addini, don na lura kina son karance-karance.
Tace: Sosai ma kuwa, don littafan da na karanta na addini suna da yawa, ka ga kamar littafin Fikhul Wadii na ji dadinsa sosai, yadda aka yi bayani game da yadda al'adar mata ta ke zuwa, da kuma yadda take daukewa, har ma idan ta zowa mutum da matsala.
Kasan mafi akasarin mata ba su san jinin haila ba, ba su san rabe-rabensa ba, da kuma yadda idan sun dauki lokaci ba su yi ba, ba su san me ya haddasa hakan ba, su ba ruwansu kawai sun san cewa, idan wata ya zo karshe suna fitar da jini, babu maganar akwai matsala ko akasin ta idan ba gani sukayi sun kwanta ba......
Isah ya katse ta da cewa: Me ye matsalar matan? Sai ta yi murmushi tace: Au, na fa manta kai namiji ne ko?. Ta mike tsaye cike da jin kunya ta koma daki. Bai yi yunkurin tsayar da ita ba, ya yi mata uzuri, sai ya tashi ya koma dakinsa, don dama bacci ne ke cinsa.
Da yammacin ranar suka je Sahad store da Alh. Shehu super market suka yo siyayyar abubuwan da zasu yi tsaraba da shi, sannan suka wuce kasuwar kurmi shuhuda ta za6o littafan addini, daga bisani suka dawo Gida.
Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤20¤¤
Duk yadda ya so kadaicewa da Inna yaduwa don jin damuwarta hakan bai yiyuwa ba, saboda duk lokacin da ya shigo falon sai ya tarar da ita tare da shuhuda.
Washegari ma tun da safe ya nufo falon bai ga Inna yaduwa ba, ya leka kicin wai ko ya tarar da ita kamar yadda tayi jiya, amma sai ya tarar da shuhuda.
Bai wani jata da labari ba, saboda yana ganin dama ce ta samu, kawai ya je daki ya tarar da Inna yaduwa ya ji matsalarta tunda shuhuda na kicin.
Yana zuwa dakin ya tarar da ita kwance akan gado, idanunta a lumshe, yace: Matar bacci kike? Sai ta bude ido ta kalle shi tace: A'a jikina ne yake ciwo. Yace: Ayya, Allah kawo sauki. Tace: Amin, ai da saukin, kawai surutu ne ban so, ga shi ina so na dama koko.
Yace; Ai ga shuhuda can na yi. Sai suka yi shiru na wani lokaci, kafin daga bisani ya katse shirun da cewa: Jiya muna magana ba mu karasa ba shuhuda ta shigo?. Tace: Eh wallahi, ga shi kuma na manta abin da nake son sanar da kai. Ya dube ta cikin tuhuma, sai ta jinjina kai alamun tabbatarwa. Sannan tacce: Karfe nawa zaku tafi katsinan? Yace: Sai sha daya. Tace: Allah ya kaimu. Ya amsa da, Amin.
BABI NA TARA
RUDANI
Babu mai magana a cikin su biyun, tafiya kawai suke tamkar kurame, kowanne da abin da yake sakawa a cikin ransa. Ga karar kira'ar Sheik Ahamad Sudeis na tashi cikin tausasshiyar muryarsa, SURATUL MUHAMMAD ce ke tashi, wadda ta ke magana akan Manzon Rahama, Manzon tsira, Manzon da babu kamarsa duk cikin Manzanni. Dan Amina baban fadima, Angon nana khadija da nana A'isha, suruki ga sayyidina Aliyu(A.S) kaka ga Hassan da Hussain, wato Annabin Annabawa, amintaccen Allah, Yardajjen Allah, Annabi Muhammad(S.A.W).
Surah ce wadda ta ke da muhimmanci akan kowanne musulmi yasanta, duk da cewa babu surar da ba ta da muhimmanci ga kowanne musulmi ya sani a cikin littafi mai tsarki(Alkur'arni mai girma).
Littafin da ya shafe kowanne littafi, tun daga kan Injila, Attaura, gami da zabura. Domin littafin alkur'ani ya tattaro dukkan bayani kama daga kan asalin halittar dan Adam, abin da ke da akwai a aljanna da wuta. Bayani na kissoshiin Annabawa, bayani akan ranar tashin alkiyama da yadda aka halicci duniya da lahira, gami da abubuwan da Allah ya yi rantsuwa da su.
Lallai Allah(S.W.A) gwanin HIKIMA ne, Arrahim ke nan mai saukar da rahma, Arrahim(mai jinkan bayinsa). Arrazzaku(mai azurta bayinsa), Alfahatu(mai budawa bawa kofofin budi).
" An kar6o daga ubayyu dan ka'ab(R.A) cewar, manzon Allah(S.A.W) yace: Wanda ya karanta suratul GASHIYA, to Allah zai yi masa hisabi mai sauki. Kuma wanda ya karantata akan rumbun abincinsa to ya aminta daga cutarwarsa.
Haka kuma an kar6o daga ubayyu dan ka'ab(R.A) cewar; Manzon Allah(S.A.W) yace: Wanda ya karanta suratul BALAD har zuwa karshen surar, to Allah zai amintar da shi daga fushinsa ranar alakiyama.
Manzon Allah(S.AW) yace: Wanda ya karanta suratul LAIL, to Allah zai tseratar da shi daga duhu guda biyu, duhun zunubi da kuma duhun kabari. Wanda ya lazimci karanta suratul Lail sau dari har tsawon kwana arba'in tare da yin azumi da Riyadh(wato nisantar sa6o) to Allah zai yi masa khasafi(wato zai samar da shi 6oyayyun ilmi).
Wata rana Annabi(S.AW) ya cewa sahabbansa, shin ko kuna son Allah ya yi muku katanga daga shaidan kamar yadda ya katange Yajuju da Majuju? Sai suka ce: Eh, Sai yace: To ku karanta suratul QADR bayan sallar magriba, da bayan sallar asuba sau uku-uku kafin ku tashi daga wajen da kuka yi sallar. Sannan sai kace: " Ya Allahu, Ya sahibul kadri farraji auni hammi wakarbii"(ma'an
a:- Ya Allah, Ya mai iko, ka yaye min bakin ciki da 6acin rai).
Wannan duk daga cikin falalar alkur'ani ne, don haka alkur'ani rahma ne ga dukkan musulmi, karanta shi na saka nishadi, sauraren kira'arsa na gusar da bakin ciki.
Har suka isa birnin katsina babu wanda ya yi magana daga cikinsu.
Sai da suka zo Welcome to katsina(sabon garin Dandagoro) a sannan ne Isah ya dago kai ya dubi shuhuda tare da rage sautin karatun alkur'anin da ke tashi, yace:
Zamu biya NNPC mu sha mai, don na ga man ba zai ishe mu zuwa karare ba. Tace: To. Yaci gaba da sulalawa da motarsa har ya shiga gidan man, ya jera layi a bayan motoci hudu da suke gabanshi.
Shuhuda ta yi wata irin zabura tare da cewa: Subhanallah!! Da sauri Isah ya dago kai ya dube ta, kokarin fita take daga cikin motar, ya riko gefen hijabin da ke jikinta, yace: Me ya faru? Ina zaki??
Fuskarta cike da fara'a da kuma doki, tace: Wata kawata ce na gani, ga ta can, fita zata yi daga gidan man. Ta karashe maganar tana nuna masa budurwar da ke kokarin shiga motarta kirar hummer jeep da aka gama zubawa mai.
Kafin ya yi magana tuni har ta fita, ta karasa inda ta ke tana cewa. Shuhuda dama kina raye? Wadda aka kira da suna shuhuda ta juyo cike da farin ciki suka rungume juna suna masu murnar haduwa.
Isah da yake cikin mota yana hango su, ya ga kamar ya ta6a ganin fuskar.
Da farko da zai share, amma zargin da ya ke na kamar wata FUSKA da ya ta6a haduwa da ita watanni hudu da suka shude a birnin MISRA ya sa ya gaza hakuri, ya yi fit! Ya bude mota ya tunkare su.
Yana isa ya soma nuna bakuwar fuskar da dan yatsansa yana cewa: SHUHUDA IBN KHADDAB? Ta dube shi cikin yanayin tuhuma gami da mamaki. Ita kanta shuhuda mamakin ne bayyane a fuskarta, tace: Yaya ina kasan Shuhuda?
Bai amsa mata tambayarta ba, yace da dayar shuhudan.
Yaushe kika zi Najeriya? Ko kuwa dama dai maganata ce ta zama gaskiya ke 'yar Najeriyar ce tunda har kika san kanwata?
Mamaki ya sake bayyana a fuskar shuhuda Ibn Khaddab. Ta mayar da kallonta ga shuhuda Sagir Rabi'u tace: wannan kuma waye a gare ki? Shuhuda ta dubi Isah, tukunna ta maido da duban nata ga dayar shuhudar tace:
Yaya na ne Isah, wanda nake fada miki?
Shuhuda ibn khaddab tace: Auhi, Allah sarki yayanmu, barka da yini?
Kin amsawa ya yi, saboda ya ga ta raina masa hankali zahiran, in bacin rainin hankali su hadu da ita sannan yanzu ta nuna masa ba ta ta6a saninsa ba? Shuhudan ma ya dauke ta a wadda ta raina masa hankali, kuma MAKARYACIYA, ya tambaye ta shuhuda ibn khaddab ta nuna masa ba ta ta6a sanin mai sunan ba, sannan shuhuda ibn khaddab ta nuna masa shuhuda kanwarsa ba ta santa ba, hasalima ba su ta6a haduwa ba.
To ta ya kuma suka san juna bayan ya ji shuhuda kanwarsa ta yi ikirarin shuhuda ibn khaddab kawarta ce? Wannan salon rainin hankali ne da yawo da tunaninsa, abin da kuwa ba su sani ba shi ne, hankalinsa ya wuce nasu bare su sa shi a RUDANI, sa6anin haka ma sai dai shi ya saka su.
Shuhuda ibn khaddab tace gaba da cewa: Na yi ta neman yadda za a yi mu hadu na sanar da ke auren Sa'adatu ban samu ba. Shuhuda tace: Ayyah, ashe anyi auren Sa'adatu? Makaranta? Ta fasa ci gaba?
Isah ya ga za su dauke shi shawaragi sun share da shi sun ci gaba da hirarsu, saboda haka ransa ya sake 6aci, yace:
Shuhuda ina yayanki Abdallah ibn khaddab? Ta juyo da sauri alamun mamaki, sai ba tace komai ba, ta dubi shuhuda, tace:
Takwara wai don Allah ina yayanki ya sanni hat yasan Ya Abdallah?
Shuhuda tace: Ni ma mamakin da nake yi ke nan, saboda ba a nan ya yi rayuwarsa ba, kuma lokacin da ya dawo muna jarabawa har muka gama bai je makarantarmu ba, bare na ce ko a can ya sanki, yasan kuma yayanki da yake kawo ki makaranta.
Isah ya shiga RUDANI matsananci da wannan bayani da ya ji suna yi, anya kuwa shuhudan da ya hadu da ita ce a Misra yanzu a gabansa? Idan ba ita ba ce me ye alakar sunanta da sunan yayanta da waccan shuhuda? Idan ita ce me yasa ta ke son yawo da hankalinsa?
Tun ranar da ya soma ganinta da salon yawo da hankalinsa ta fara, tunda ita ta soma yi masa magana cewar ta ganshi kamar yayan Shuhuda Sagir Rabi'u, wannan kuwa idan ba kana da alaka da sanin hakan ba babu yadda za ayi ace bincike na sanadin suna ya kasance idan sun hadu ta shaida shi.
.
Ci gaban labari.
.
Bayan basu ta6a haduwa ba.
Abin tambayar a nan shine me yasa suka yi amfani da wannan salon gare shi? Shin kowaccensu sonsa ta ke yi ne shi yasa suke son juyar masa da kwalwa? A'a ba sonsa suke ba, so suke su juya shi kai-kai ce, su rikita shi, su sanya shi cikin RUDANI, Su kuma tsotse ruwan kansa bisa jagorancin shuhuda kanwarsa, don ita din ma ta nuna masa abubuwan RUDANI da yawa, saboda ranar da ya ce yana sonta kin amincewa tayi, daga baya kuma ta zo masa da amincewarta.
Tunda ya gane manufarsu kamata ya yi ya bi su da yadda suka zo masa. Murya a taushe kuma yana murmurshin da yake kara masa kwarjini, murmushin da yake fito da cikar HAIBARsa( Asalin sunan littafin)
Yace: Kada ki damu shuhuda ibn khaddab, haka nake na kasance mai binciken duk wata mace mai sunan kanwata, don haka ne ma zan iya cewa na sanki, na san yayanki Abdallah Ibn Khaddab.
Yanayinta ya nuna bata gamsu da bin da ya fada ba, amma jin karar hon din da ake ta doka mata wanda ke nuni ta tsarewa na bayanta hanyar fita, sai ba ta samu damar tankawa ba. Ta dubi shuhuda, tace: Don Allah minti daya na dai-daita tsayuwar motata.
Kafin ta amsa mata tuni har ta shige mota, Isah ya lura da zoben da ke yatsanta, wanda iri daya ne sak da wanda ya sa yowa shuhuda kanwarsa da shi lokacin da ya tsaya a kasar Misra.
Da sauri ya dubi yatsan shuhuda kanwarsa inda ya saka mata zoben, yana nan daram, saboda haka kama ce, ita ma ta sayi irinsa. Sai ya koma motarsa ya matso da ita, ya kasance motoci biyu ne yanzu a gabansa.
Kafin ya baro jikin motar har an sanyawa daya daga cikin motoci biyun da ke gabansa mai, saboda haka sai bai yi garajen barin gurin ba, ya tsaya. Cikin sa'a kuwa ita ma motar dake gaban tasa ba wani mai yawa aka zuba mata ba, sai shi. Ya fadi adadin yawan da yake so, aka zuba masa sannan ya iso gurinsu da motarsa.
Yana isowa shuhuda ibn khaddab ta cewa shuhuda.
To takwara sai gani na biyu, da fatan zaki cika alkawari idan bikin ya tashi ki kawo mana katin gayyata, da dai nace bazan kara zuwa bikin class mate dinmu ba, amma tunda ke ce da yayanmu ba ji, zan zo.
Shuhuda ta rusunar da kanta kasa saboda kunya, tunda Isah na tsaye a kanta.
Shuhuda ibn khaddab ta dubi Isah tana murmushi tace:
Yayanmu Allah ya sa yadda ka binciko ni saboda ina da sunan kanwarka, idan lokacin aurenku ya yi ka iya binciko ni ka kawo min katin gayyata. Kuma idan na koma gida zan sanarwa Yah Abdallah na hadu da abokinsa ISAH SADA RABI'U.
Tana kammala fadar haka ta bude murfin mota ta shige.
Isah tsaye ya yi sararo yana kallonta, ya kasa koda motsin kirki ne, ambatar cikakken sunansa da ta yi ya kara jefa shi cikin rudani.
Koda yake a wani 6angare bai kamata ya yi mamakin jin haka ba tunda ya ba su dama wata kila a cikin lokacin shuhuda ta samu sararin fayyace mata cikakken sunansa, ko kuma dama ta dade da saninsa,idan ya yi la'akari da maganganun da suka tattauna, wai makaranta daya suka yi.
Ta gabansa ta zo ta wuce yana kallonta tana kallonsa, tamkar tana son fada masa wani abu amma ba ta tanka ba, illa murmushin da ya ki 6acewa daga fuskarta.Shuhuda tace: Yaya mu tafi ko?
Ajiyar zuciya ya soma yi, kafin daga bisani ya girgiza kai ya nufi mota.Ta bi bayansa, duk suka shiga cikin motar ya soma jansu zuciyarsa ta gaza nutsuwa, haka kuma ya kasa daurewa, yana son cikakken bayani game da alakar da ke tsakanin shuhuda kanwarsa da shuhuda Ibn Khaddab, don haka yace
Amma kun sakani a RUDANI sosai. Ta dube shi tace: Wane irin rudani kuma yaya?
Yace: Wannan shuhudar ita ce muka hadu fa da ita a birnin Misra na tambaye ki kika ce baki santa ba, ita ma ta ce ba ki santa ba, amma ita ta sanki ta hanyar bincike a dalilin sunanku ya zamto daya, sai ga shi na ganta a Najeriya wanda a can ta tabbatar in ba ta ta6a zuwa Najeriya ba, a yadda na lura na kuma fahimta a cikin kalamanku kun dade da sanin juna, kamar ma a makaranta daya kuka yi, to mutumin da yace bai ta6a zuwa Najeriya ba ta ya kuma ya yi karatu a Najeriya har yasan wasu mutane da ke rayuwa a cikinta? Thats my question (wannan ita ce tambayata)
Shuhuda tace: Kai yaya anya kuwa ita ce wadda kuka hadu kuwa? Ita fa wannan a nan katsina ta ke, karatu ya kaita kano ta zauna gidan yayan mahafinta. Da farko ba ma shiri, saboda lokacin da na yi karatu ina rayuwa da hankali ne na awa biyu, sai gab da zamu soma jarabawa muka soma shiri har ma muke zama mu yi hira. A nan ne ma ta sanar da ni ita 'yar katsina ce, su uku mahaifanta suka haifa, daga ita sai yayanta Abdallah wanda yake karatu a Misra, sai kaninta Yusufa su ke nan mahaifinsu suka haifa. Mafarin ke nan suke samun ingantacciyar kulawa daga mahaifan nasu...
Har muka gama makaranta ba tasan gidanmu ba, ni ma haka dama kuma ba zuwa bikin kawaye nake ba, shi yasa tun da muka gama makaranta ba mu sake haduwa ba sai yau.
Ya gama sauraronta ne kawai, amma bai gama fahimtar inda kalaman nata suka sa gaba ba, shi dai ya yarda ya kuma amintar ma kansa, wannan shuhudar da suka hadu a Misra ce, wadda ke bin kasashe yawon majalisin malamai, shuhudan da ta sanar da shi iyaye da kakanninta dukkansu 'yan asalin Misra ne. Ya fi amincewa lokacin da suka hadu a Misra wani sanadi ne ya kaita, amma ta 6oye masa saboda sun shirya hakan da kanwarsa shuhuda, wannan shi ne hakikanin abin yarda.
Tammat bihamdillah
Gare ku fa makaranta? Kun yarda? Anya kuwa? Kai ko ni ban yarda ba, akwai dai yadda akayi.
Shin ina Uncle Hamza da zuwairiyyarsa?
Kada fa a yi danyen kasko mana? Ai kun fahimci labarin MATA'UL HAYAT ko? Idan ma ba ku fahimta ba, zaku fahimta ne idan kuka ji muhimmin sakon da ya kunsa.
Kada dai ku manta da tarin abubuwan da suka faru tun daga littafi na farko zuwa na biyu. Musamman rayuka uku da aka rasa saboda shuhuda, da sauran abubuwan da suka biyo baya?
Izra'el,Libhas,Tanzif me ye alakarsu da shuhuda? Ina aka samo keken doki da ta ke zuwa Misra kamar yadda ta fawa uncle Hamza?
Yakub, Abdallah ibn khaddab, da shuhuda ibn khaddab duk me ye alakarsu da shuhuda.
Kai-kai-kai!!! Akwai fa yawa abubuwan, amma dai mu

Please Login or Register in order to submit comment