Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta6a mata zuciya ba illa zafi da radadi ko na ganowa da ta yi, can baya ta yi soyayya da wani a tubalin sha'awa, ko kuma mutuwa ta gitta ta raba su. Wadannan kuwa ababe ne masu radadi.
Ya mike tsaye ya nufi cikin gidan. Don tarar da shuhuda ya sanyayar mata da zuciya, sai dai yana shiga falon ya tarar da Inna yaduwa zaune akan kujera ya nufi dakin shuhuda.
Ta sanya baki ta kira shi, ya dawo ya zauna a dayar kujerar tace:
Kada ka shiga gurin shuhuda, domin kana shiga zaka sanya ta tayar da hankalin mutane. Haka ta tsiri wannan dabi'ar tun bayan kammala sakandiri dinta, da zarar an 6ata mata rai sai ta shige daki ta yi ta kuka. Ai ka gani abin da ya faru kwanaki ko?
Don haka kyale ta, me ya faru ne a tsakaninku?
Yace: Daga na ce ina sonta shine ta shiga wannan yanayin.
Inna yaduwa tace: Kyale ja'ira kawai ci gaba da son nata, inshaa Allah idan rabonka ce zaka aure ta.
Bayan an gama sallar magriba Isah bai samu komawa gida ba, saboda tun kafin su shiga sallah Alh Rabi'u ya ba shi sakon da zai kaiwa Alh sada(Mahaifinsa) ya saka a mota, saboda haka ana gama sallar kai tsaye can gidan mahaifin nasa ya nufa.
'''''''''''' ''''''''''''' ''''''''''' ''''''
Duk yadda ya so ya koma gida da wuri hakan ya ci tura, saboda kannesa da suka saka masa shagwa6a lallai sai ya zauna sun sha hira tunda tun bayan dawowarsa bai zauna da su ba.
Dole ba don ya so ba ya zauna. Tun yana duba agogo yana tunanin i wannan lokacin yana tare da su shuhuda a dakinsu yana yi musu hira, har tara da rabi ta yi ya tuna dai-dai lokacin yake tofe musu dakinsu da addu'a ya koma dakinsa.
Goma dai-dai ya kissima yanzu su shuhuda sun dade da yin bacci, saboda dama a daddafe ake yin hirar da ita zuwa karfe tara da rabi.
Saboda haka sai ya sare, gwiyoyinsa suka yi sanyi, ya tabbatar ya yi rashin wannan daddadan hira da suke yi musamman ma da yake dokin ta yau zata fi kowacce hira armashi, tunda har ya samu damar furzar da abin da yake cikin ransa.
Sam ba shi da niyyar tafiya, har sai da Hajiya Safiyya tace: Wai kai ba zaka yi harama ka koma gida ba? Ta dubi su Asma'u tace: Ku tashi ku je ku kwanta.
Haka ya mike ya yi musu sallama ya hawo motarsa ya nufo gida. Lokacin da ya iso gida sha daya saura kwata. Kai tsaye 6angarensa ya shiga don yana da tabbacin sun dade da yin bacci.
Bayan ya gama duk abubuwan da suka zamo al'adarsa misalin karfe sha biyu da mintina takwas bacci ya yi awon gaba da shi.
******* ******* *****
Shuhuda ina son!
Nasan haka''
Shuhuda ina kaunarki.
Na fi kowa sanin haka.
Shuhuda tunanina ya zan yi da raina.
Shine abin da ke nukurkusar min da zuciya, yake saka ni damuwa, amma kada ka damu mafita ta zo gare ka.
Ta ya ya?
Mikewa ta yi daga inda suka yi tsugunnon su duka biyun, ta soma taku yana kallonta hat ta isa inda garken kananun dabbobi suke, irin su kaji, Agwagwa, Talo-talo da tantabaru.
Yana kallo ta zama ZAKANYA ta soma taune kananun dabbobi, yana so ya daga baki ya yi magana ya kasa, yana so ya yi amfani da kafafuwansa ya zura da gudu ya kasa.
Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤18¤¤
Yana nan tsayen ta gama taune kananun dabbobin nan tas! Sannan ta koma halittar mutum, ta yi murmushi, tace:
Yadda ka ga na taune dabbobin nan haka zan yiwa 'YA'YAN CIKINKA, HANTA, KODA da ma ZUCIYARKA. Wannan ita ce kadai mafita, idan ba haka ba babu wata mafita da zamu yi amfani da ita, mun riga mun yi SAKACI wanda 'yan magana ke cewa: TUN RAN GINI RAN ZANE!
Firgigit Isah ya yi ya farka daga baccinsa mai kunshe da wannan hargitsattsen mafarki. Ya duba agogon da ke dakin, amma bai iya ganin komai ba, saboda duhun da ke da akwai.
Sai da ya yi amfani da malatsin kunna fitila, sannan haske ya gauraye dakin. Karfe daya da mintina shidda, tabbas tun ran gini ran zane na fadar shuhuda a mafarkinsa. Ai tunda ya dawo ya saba kullum sai ya yi musu hira kafin daga bisani ya yi musu addu'a ya ja musu kofa ya koma nasa dakin.
Idan haka ne an tunatar da shi yau bai yi musu addu'ar ba kamar yadda ya sabar musu. Saboda haka cikin mutuwar jiki da kuma sauran baccin da ke tare da shi ya mike don nufar dakin nasu ya yi musu addu'a tukunna ya dawo ya dora nasa baccin.
Mamaki ya kamashi na hango haske da ya yi ta tagar(window) dakin bayan ya shigo falo, shin me yasa ba su kashe kwai ba kafin su kwanta? Tagar ya fara nufa, ya kai hannu ya yaye labulen tagar a hankali.
Das! Zuciyarsa ta buga sakamakon abin al'ajabin da ya gani, Inna yaduwa na kwance tana ta sharar bacci cikin nutsuwa, ya yin da shuhuda ke gefenta ita ma baccin take.
Amma cikinta na juyawa kamar ana wana wani abu, kwatankwacin yadda idan an harba kwallo ta ke juyawa kafin ta isa ga inda ake so.
Tambayar da ta fara darsuwa a zuciyarshi ita ce, shin dama haka shuhuda ta ke bacci, ko kuwa ba ta da lafiya ne?
Amsar ta gaza samuwa a gare shi ya kuma dauki tsawon lokaci a wannan hali kafin daga bisani ya bar jikin tagar ya nufi kofar shiga dakin.
A nan ma ya dauki lokaci yana ma ya dauki lokaci yana kallon abin al'ajabi, ga shi dai dare ne, kuma a yanayin da shuhuda take kwance zai tabbatarwa dik wanda ya ganta lallai bacci ta ke, hakan ke nan yana nufin haka ta ke baccinta, cikinta na juyawa kamar kwallo? Tunda da ace ba ta da lafiya ne, hakika da ba a haka za a ganta tana baccin ba hankali kwamce. Ya karasa kusa da ita cikin tafiyar sanda don kada karar takunsa ya tayar da su daga baccinsu, ya sani za su tuhume shi me ya kawo shi dakinsu a irin wannan lokacin wanda ya ke da yakinin idan zai kwana dubu yana fada musu addu'a ya zo ya yi musu ba zasu aminta da hujjarsa ba. Idanuwanta a lumshe suke tabbacin dai baccin ta ke yi. Zuciyarsa ta dinga ayyana masa abubuwa da dama, ganin Inna yaduwa ta gyra kwanciya tsoro ya kama shi, kada ta bude ido ta ganshi. Don haka ya yi sauri ya durkushe har sai da ya ji motsinta ya gushe sannan ya mike cikin tafiyar sanda ya koma bakin kofa ya yi musu addu'o'in da ya saba tukunna ya fice ya ja musu kofar a hankali bayan ya kashe musu wutar. Koda ya koma dakinsa kasa kwanciya ya yi, zaune ya yi a gefen gado yana tunani, shin idan haka shuhuda ta ke bacci ya ya ke nan idan ya aure ta? Amsar da ta gaza samuwa ke nan, amma lallai yana cikin zullumin tabbatuwar hakan, domin yana da tabbacin ba zai samu sakewar da yake son samu ga matar aurensa ba matsawar aka ce haka shuhuda ta ke bacci. Har gabatowar asubah Isah bai samu ya runtsa ba, karshe ma sai da ya sallaci sallan asubah sannan ya koma kan gado ya nade. Bacci mai nauyi ya yi awon gaba da shi. ***** ****** ***** Shuhuda! Isah ya kirayi sunanta lokacin da ta ajiye masa abin karin kumallo. Ta juya zata fita ba tare da ko gaisuwa ta shiga tsakaninsu ba. Turus ta tsaya ba tare da ta juya ta kalle shi ba, fuskarta a daure sam babu alamat fara'a, sake cira baki ya yi ya ambaci sunanta, sannan ya dora da cewa: Dawo ina son magana da ke. Ba ta juyo ba, tace: Idan dai akan maganar jiya ce babu amfanin dawowata, tinda na fada maka ra'ayina. Ya yi murmushi, yace da ita: No, ba wannan maganar ba ce, dawo ki zauna. Ta juyo idonta a rusune ta samu kasan kafet ta zauna ta yi shiru. Yace: Dago idonki ki dube ni, sannan na isar da korafin da nake son isarwa gare ki. Babu musu ta dago ido ta dube shi, duban da ya haifar da abubuwan al'ajabi, daga ciki ya ji wani irin tsoronta ya shiga zuciyarshi, ta yi mishi wani irin kwarjini, tambayar da yake son ya yi mata na abin da ya faru a daren jiya bayan mafarkin da ya yi ta koma zakanya ta cinye dabbobi ya shiga dakibsu ya ga cikinta na juyawa kamar kwallo. Ya ji tambayar ta yi masa nauyi a baki, ba zai iya furtawa ba, sam! Da sauri ya rusunar da kansa kasa ba tare da ya iya isar da korafin rashin gaishe shi da ba ta yi ba. Ita kuma ta kasa cire idonta a kansa, kallonsa ta ke, kuma sauraron abin da zai fada ta ke, amma har tsayin lokaci:- Can tace: Ka tsayar da ni, kuma ka ki yin magana. Bayan ina da abubuwan yi.
Da kyar ya cafko abin da zai ce, bayan ya yi takaitaccen murmushi, yace: Dama cewa zan yi ya kamata mu je katsina. Saboda me? Ta bukata a takaice.
Saboda mu gaishe da Goggo Asma'u da kuma mama karima.
Tace: Sai ka fidda lokaci. Ya ji dadin hadin kan da ta bashi, yace: Ina ganin kafin na tafi Ibadan ya kamata mu je ko?
Tace: Duk yadda ka gani.
Yace: Sai muje karshen satin nan.
Tace: Ba matsala..... Shi ke nan?
Ya daga mata gira.
Tace: Allah ya kaimu lafiya.
Ta karashe maganar tana yunkurin tashi, ya ambaci sunanta cikin jarumta, yanason ya yi mata maganar abin al'ajabin, amma ko da ta juyo suka hada ido ya sake jin wani nauyinta ya kama shi. Yana tunanin ta yadda zai furta maganar a gare ta, ai da kunya.
Jin ya yi shiru bai ce komai ba ya sa tace: Yah Isah ka cika matsala, ka ce ka gama magana na mike zan ta fi kuma ka tsayar da ni, to me kake son na yi maka?
Yace: Dama cewa zan yi ki ba ni lambar wayarki? Tace: Waya? Ka manta ba ni da waya?
Fuskarshi ta nuna yanayin mamaki, don a zahiran bai san ba ta da waya ba. Yace: Kina nufin ki ce sam ba ki da waya? Faduwa ta yi ko sacewa aka yi?:
Ta girgiza kai tace: Ko daya, ni ban ta6a rike waya ba. Yace: Saboda me? Tace: Haka nan! Yace: To zan saya miki. Ta girgiza kai a karo na biyu. A'a ka barta.
Ko akwai dalili? Ya bukata. Eh-to, Ni ban iya rike waya. Yanayinsa ya sake bayyanar da damuwa. Me ya samu hannun naki? Maimakon ta amsa, sai ta jefo masa tambaya. Kai me yasa kake son dole na yi amfani da waya?
Ya yi murmushi, yace: Saboda a yanayinki na budurwa zaki bukaci rike waya ko don saurayinki ya kiraki.
Ta hade rai, tace: Me ye kuma haka?
Jan aji irin na mata. Abin da ya ayyana a ransa ke nan, zahiran kuwa cewa ya yi.
Kamar yadda na bukaci yin mu'amala ta soyayya tsakanina da ke, har ta kaimu ga yin aure.
Tace: Bana soyayya. Kuma wannan yana daga cikin sharuddan haduwarmu da kai, muddin wannan jigon ne zai dinga hada mu lallai zan kaurace maka don tsirar da rayuwar mu....." Tana karashe fadar hakan ba ta jira cewarsa ba ta fice daga dakin, amma ya hango lokacin da kwalla suka zubo daga cikin idanunta. Sai ya yi murmushi, ya ci alwashi ko ta ya sai ya ja hankalin shuhuda zuwa gareshi, sai ya dandana mata zakin soyayya a ruhinta. Da daddare da ya shigo dakin nasu domin yi musu hira, shuhuda nadewa ta yi a gado ta lumshe idanunta alamun ba ta bukatar a yi hirar da ita ba wai don tana jin baccin ba. Ta yi bakam tana saurarensu, mafi yawancin hirar duk akan zuwa katsina ne, Inna yaduwa tana cewa ita ma lallai sai an je da ita. Yayin da isa ya jajurce babu inda za a da ita tunda tafiya ce ta matasa sabbin jini ba zasu kwashi kayan tsufa su tafi ana musu wani gani-gani ba. A haka dai suka yi hirar ba tare da shuhuda ba, karshe ya mike ya yi musu addu'a ya kashe musu wuta ya nufi dakinsa. Ya yi duk abin da ya saba, ya kwanta bacci ya sure shi. Tarihi ya maimaita kansa, domin abin da ya faru a daren jiya yau ma shi ne ya faru, mafarkin ya yi shuhuda ta koma zakanya ta shiga daji tana cinye kananun dabbobi. Tana kammalawa da dabbobin ta dawo suffarta ta asali ta tsaya a gabansa tana mai jifarsa da wani yalwataccen murmushi, tace: Kana son hawa keken shanu don zuwa bigirena? Ya buda baki da nufin amsa mata ke nan, firgigi ya farka daga baccin nasa yana raba idanu, yau dai bai baro dakin su shuhuda ba sai da ya tabbatar da ya tofe su da addu'a, da ya dawo daki ya yi duk abin da ya saba yi. Illa abu daya wanda bai san ta yadda aka yi ya manta bai yi ba, wato ADDU'A, shi dai yasan lokacin da ya yi wanka ya saka kayan bacci(pyjames), sannan ya shiga duniyar gizo(internet) ta Lap-top dinsa. Da ya kammala da wannan ya rufe lap-top din ya mayar da ita ma'ajiyarta, sai ya kishingida ya shiga tunanin yadda shuhuda ta yi masa. Daga nan bai san lokacin da bacci ya dauke shi ba. Hakika rashin addu'a ga rayuwar dan Adam wani babban gi6i ne, idan ya yi la'akari da jiya bai yiwa su shuhuda addu'ar da ya saba yi musu ba, ya yi mafarki mai firgitarwa, wanda yake nufin tunasarwa a gare shi na rashin yi musu addu'ar. Yau kuma ya sake mummunan mafarkinsa duk a sanadin rashin addu'a don haka wannan IZNA ce gare shi da ma duk wani wanda ba ya addu'a ga lamuran rayuwarshi. Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa a sarari. Alhamdulillah! Sannan ya mike tsaye bayan zuciyarsa ta ayyana masa ya je dakinsu shuhuda ya kara tofe su da addu'a don nema musu tsari daga shaidanun dare. Daram! Gabanshi ya yanke ya fadi lokacin da ya karasa a cikin falon, ta taga ya hango hasken kwan lantarki. Ya dai san bayan ya yi musu addu'a sai da ya kashe musu wuta sannan ya nufi dakinsa. Abu na farko da ya fara zuwa ranshi shi ne, Inna yaduwa ko shuhuda daya daga cikinsu ya farka daga bacci ya kunna kwan lantarki watakila don yin ibada ko kuma wani uzurin na daban.
Cikin dakiya ya karasa bakin kofa, yana tura kofar sai ya ji ta a bude ba a rufe ba. Yaye labulen da zai yi idonsa ya yi masa tozali da al'amarin da ya faru a daren jiya a irin wannan lokacin, wato cikin shuhuda yana juyawa kamar kwallo. Mamaki, tsoro, fargaba dukka suka durar masa a lokaci daya, wai wannan wane irin rudadden al'amari ne ace mutum yana bacci cikinsa yana juyawa kamar kwallo irin haka? Lallai ko tababa babu shuhuda ba ta sa lafiya, akwai cutar da ke damunta, tunda haka nan ba zai yiwu cikinta ya dinga irin wannan juyawar ba, ko dai tana da cutar kyambon ciki? Cikin sanda kamar yadda ya yi a daren jiya don gudun tayar da Inna yaduwa, gaba daya jikinsa kyarma yake, ji yake kamar wani abu na fizgarshi karasawa inda shuhuda ta ke, duk da cewar ya sani muddin daya daga cikinsu ta farka ba shi da hujja ko kalaman da za su kare shi. Idan jiya yana da hujjar ya zo yi musu addu'ar da bai samu damar yi musu ba, yau kuma mece ce hujjarsa? Zai ce ya yi mafarki shuhuda ta koma zakanya tana cinye dabbobi shi ya sa ya shigo musu daki a dai-dai wannan lokaci? Hujjar ba mai kar6uwa ba ce, illa ya sani tsautsayi ne ke fizgarsa. Idanu ya tsurawa cikin shuhuda har yanzu juyawa yake yi kamar ana juya kwallo. Cikin shakku da rashin sanin fa'idar yin abin da yake yunkurin yi ya daga hannu zai ta6a cikin, har ya kusa kai hannun ya yi saurin daukewa, sakamakon buhum kirjinsa da ya tsananta. A karo na biyu ya sake kai hannunsa da nufin ta6a cikin, saboda zuciyarsa da ta ke azalzalarsa ya ta6a cikin ya ji me ye yake juyawa haka? Wannan karon duk kokarin da ya yi na hana hannun nasa isa ga cikin shuhuda sai da ya isa. Bisa ga tsananin mamaki, hannun na isa cikin ya tsaya cak! Ma'ana ya daina juyawa kamar ace talabijin ce take aiki aka sa hannu aka kashe ta. Da sauri ya dauke hannunsa yana ci gaba da tsura mata idanu, har tsayin wani lokaci babu abin da ya kuma faruwa, cikin bai sake juyawa ba, haka kuma shuhuda ba ta farka daga baccin nata ba. An shafe ya fi mintina takwas babu wani abu da ya faru, don haka ya fice daga dakin ya nufi dakinsa cike da al'ajabin yadda abin ya faru. Washegari da yammaci misalin karfe biyar, rana ta yi sanyi, Isah yana kokarin bude murfin motarsa don shiga zai je cikin gari wajen abokinsa da suka yi za su hadu. Da sauri shuhuda ta karaso gurinsa tana cewa. Yah Isah! Don Allah tsaya!! Ya dakata da bude murfin motar tare da juyawa yana kallonta. Ta tsaya a gabansa tana sanye da doguwar riga ta atamfa mai gajeran hannu, ta daura dan karamin bakin gyale a kanta, kafarta da silifas. Ta sunkuyar da kanta kasa ta kasa magana. Yace: Ya aka yi ne shuhuda? Muryarta a raunane tace: Yah don Allah ka yi hakuri na tsayar da kai ko? Ya girgiza kai. Kada ki damu, me ye matsalarki? Ta sake rusunar da kai kasa. Ni ma ban san abin da ya sa na tsayar da kai ba. Mamaki ya bayyana a fuskarsa, yace: Aha! Ban gane ba kui san abin da ya sa kika tsayar da ni ba?
ada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤19¤¤
.
Tace: eh yaya, shin hakuri zan baka, ko kuwa albishir zan yi maka? Ya yi murmushi, ya jingina da mota yace: Duka. Sai ki fada ina saurarenki. Tace: Ka yi hakuri akan kin kar6ar soyayyarka da na yi, hakan ya faru ne bisa tunanin da na yi kamar ban cancanta da zamowa abokiyar rayuwarka ba a matsayinka na wayayyen mutum, wanda ya rayu a cikin masu jajeyen kunne, ni kuma BAGIDAJIYA, bakar fata, wadda ta rayu cikin 'yan uwanta bakaken fata! Sai na ga yin soyayyar akwai matsala.
Tana karashe fadar hakan ta yi shiru, shi kuwa murmushin ya sake saki, sannan yace: Sai kuma aka yi rashin sa'a duk da kasancewar na rayu a cikin masu jajayen kunne, sai Allah bai sa na ga wata daga cikinsu da zuciyata ta aminta ta zamo uwar tuwona ba kamar ke.
Hasalima tunda nake mace daya ce na ta6a gani, wadda zan ce ta burge ni. Wato SHUHUDA IBN KHADDAB, wadda na fada miki mun hadu da ita a birnin misra, ita ma burgeni ne kawai ta yi ba wai ina son ta zamo mata a gare ni ba.
Saboda haka ke din dai ke ce wadda asalin sona yake a tare da ita, wannan tsinkayen naki raunanna ne, bai isa ya zamo jigon da zai hana soyayyarmu ba.
Ya yi shiry yana sauraren ya ji daga gare ta, amma ba ta tanka ba, ya ci gaba da cewa: Wani albishir ne zaki yi min?
Ta dan dago kai ta dube shi, suka hada idanu ta mayar da idanunta ta rusunar kasa, murya a sanyaye tace:
Na amince da soy.......
Maganar ta makale a kasan makoshinta, yayin da farin ciki ya cika masa zuciya, ya daga hannu sama yana cewa:
Alhamdulillah, godiya ta tabbata ga Allah ubangijin Talikai, masani akan dukkan SIRRIN 6OYE da na BAYYANE.
Ya sake dubanta, yace:
Idan na ce na fi kowa farin ciki a wannan rana ban yi laifi ba, saboda na tabbata duk wanda ya dace da mace irinki, lallai ya yi dace da uwar 'ya'ya ta gari, irin wadda ake son samu, wadda aka yi hasashen idan mutum ya same ta lallai zai yi katari da madauwamin farin ciki.
lokaci daya fara'ar dake fuskarshi ta raunana, sakamakon abin da ya faru SHERAN JIYA, da kuma JIYA na ganin cikin shuhuda yana juyawa kamar kwallo. Ya so ya yi mata magana akan haka, amma suna hada idanu da ita sai ya ji nauyinta ya kama shi, tabbas wannan ba muhallin da zai furta abin ba ne, domin gudun kada ta zarge shi akan yana son fakaitar idanu ya 6ata mata rayuwa......
Shuhuda ta katse shirun da cewa: Yauwa, Yar Isah, wai don Allah ya kamannun shuhudan da kuka hadu da ita yake, ina ganin kamar na ta6a ganinta.
Ya girgiza kai, yace: Bana tunani, tunda ta ce ba ta ta6a zuwa Najeriya ba. Ko ke kin ta6a zuwa Misra bayan tafiyata?
Tace: A'a amma ba ta ta6a zuwa Najeriya ba ya aka yi ta sanni? Yace: Eh, ni ma abin da nake mamaki kenan, tace: wai bincikenta ne ta sanki, wata 'yar fara doguwa, irin matan Misran nan dai.
Shuhuda ta yi dariya, tace: Kai Yaya, su matan Misra har kala daban gare su? Yace: Sosai ma kuwa, domin kina ganinsu kin san su 'yan asalin kasar Misran ne.
Ta jinjina kai, tace: Ni kam zan so na ga wannan shuhuda mai bincike haka. Yace: Nima zan so hakan.......
Ya kawar da maganar da cewa: Jibi ne tafiyarmu katsina ko? Tace: Haka ne. Yace: Ya kamata ki shirya gobe dai mu yo tsaraba ko? Ta narke idanu cikin shagwa6a, tace: Kai Yah Isah ni fa bana son zuwa super market. Yace: Ko akwai dalili?
A'a, haka kawai bana sha'awar zuwa super market. Cewarta.
Yanzu ya kamata ki koyawa kanki sha'awar zuwa tunda ra'ayina ne. Shi ma ya fada yana kallonta. Sai tayi shiru ba ta ce komai ba. Yace: Yanzu ma ba don mun yi alkawari da Salman Alparis zamu hadu ba, ai da yau zamu je, amma yau da gobe duk kayan Allah ne.
Tace: Haka ne, bara na koma tunda fita zaka yi......
Ya katse ta, idn babu takura mu je ki raka ni mana? Tace: Anya? Akwai wani nazari da na ke yi. Yace: Shike nan, sai na dawo. Ai ba jimawa zan yi ba.
Tace: To Allah ya dawo da kai lafiya.
Ya amsa, Amin.
Yana kokarin shiga mota, ita kuma ta juya ta koma cikin gida. A ranar da dare hira suka sha mai tarin yawa, da amfani ga Isah, domin a cikin hirar ne ya kara tabbatarwa kansa lallai ya yi sa'ar samun mata mai kaifin hankali da basira. Wadda ta san makamar rayuwa, ta kuma san yadda zata farantawa wanda ke tare da shi rai.
Saboda dik hirar ta su ta ta'allaka ne akan yanayin da ma'aurata suke kasancewa idan sun sami matsala. Ya dinga dangantawa da su. Misali: Ace ya aureta matsala ta shigo ta karin aure ba tare da ya sanar mata ba, sai ranar daurin auren ko kuma ana gobe daurin auren.
To idan irin wannan matsalar ta shigo ta ya ya zata magance ta?
Murmushi ta yi, tace: Yah Isah ai ita soyayya ta gaskiya wadda ta zamo jigon aure mutumtata ake yi, kuma a yi uzuri tsakanin juna, tare da kar6ar uzuri. Zata iya yiwuwa saboda tsananin kaunar da kake yi min ne yasa ka kasa sanar da ni zaka yi nin kishiya. Kasan a rayuwar aure nagartacciyar kauna da fahimtar juna ake nema, muddin aka samu haka to kuwa dole ne a samu uzuri.
Kuma duk macen da ka gani ko jin mijinta zai kara aure ta tayar da kayar baya, da tasa rayuwar auren na su ta samu tangarda. To ka tuhumi asalin tushen kafuwar tubalin auren. Mai yiwuwa ne dama can ba kaunar mijin ta ke ba, sha'awa ko burgewa ce ta sa ta aure shi. Ko kuma ta kasance daga cikin jinsin mata wadanda suka dauki KISHI dabi'a mai kyau a gare su.
Wannan dogon bayanin da ta yi masa ya sama masa nutsuwa da gamsuwar cewar, lallai ya yi dace da samun mace ta gari.
Inna yaduwada yake babbar mace ce, tuni ta fassara maganganun nasa, ta yi dariya tace: Isah kenan, ga dukkan alamu kana daga cikin mazan da ke sha'awar tara mata fiye da daya.....
Ya yi

Please Login or Register in order to submit comment