Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba don t agama kaishi bango, kiris ya rage ya fashe don haushi da takaicinta.
Mamaki yake wai yarinya karama kamar Shuhuda ta iya wannan fitsara da cin fuska. Ba don Inna Yaduwa ta yi masa togaciya ba, da sai ya nada mata shegen duka inyaso gobe ma ta kiyaye harshenta. Shi yanzu baa bin da ta yi masa na juyawa soyayyarsa baya yafi damunsa ba, a’a mummunana halin da ta tsira.
Ya sauka Ibadan cikin rashin walwalar zuciya, dama komai ya kammala na muhallinsa, da makullan ofis dinsa, don haka kai tsaye gidan da aka mallaka masa ya nufa, a unguwar Shasha, a layinda yak e gidaje ne jeer masu kyau da kayatarwa, komai na layin a shirye yake gwanin ban sha awa, haka cikin gidajen ma an saka duk wani abu na jin dadin rayuwa.
Idan da akwai abin da zaka nema ka rasa a cikin gidajen, to ba zai wuce na abin da zaka ci ba, wanna hakkin duk mazaunan gidajen ne, kasancewa gidaje ne da masa’antu suka gina, kowace masa’anta idan ta dauki ma’aikaci sai tab a shi gida daya inda zai zauna.
To shi Isah tun kafin zuwansa ma’aikatar da ta dauke shi aiki tuni t agama tanadar masa komai kan abinci, musamman da suka samu tabbacin a kasar da yayi karatu sun san cimar da ta dace da shi. Yana shiga ciki ya tarar da ma’aikatan da aka sanar da shi suna jiransa, ma’ana wadanda zasu yi masa hidima, wanki, dafuwar abinci da sauransu.
Duk da basu sanshi a sarari ba, sai taswirarasa da suka sani a hoto, amma suna ganinsa suka gane shi. Gaba daya suka mike tsaye cike da girmamawa, gaisuwa da kawo kayan sha duk suka yi masa, sannan aka kai masa rowan wanka bandaki. Ya fito ya shiga bedroom ya tarar da duk abin da yake bukata na jin dadin rayuwarsa. Sai dai kash! Baya da jin dadin, hasalima jin kansa yake kamar ba shi ba.
Washe gari ya soma fita gurin aiki, ofis kam yayi kyau, ya kuma matukar dacewa da shi. Kwana biyu yana cikin ayyuka na ofis, ranar na uku da daddare misalign karfe takwas na dare yana tsaye a barandar gidansa, sanye da pyjamas jajaye, don yana gama sallar Isha’I yayi shirin bacci ba don yana da tabbacin baccin zai yi ba, kawai yayi hakan ne don ya san babu inda zai kuma zuwa musamman a matsayinsa na bako, bai da wani wanda ya saba da shi. Kamar an ce ya daga kansa, sai kuwa idanunsa suka hango masa kyakkyawar fuskar dab a zai manta da ita ba, ta fito daga mota har tana kokarin bude wani gida daga cikin jerin gidajen da ke layin.
Daram! Gabansa ya yanke ya fadi.
“SHUHUDA IBN KHADDAB!”
Ya fada a sarari cike da tsananin mamakin yadda aka fara ya ganta a nan. Lallai wannan yarinya shu’umar gasket ce, ba don haka bay a ganta a birnin Misra, ta zo masa a bakuwar fuskar da ta san kanwarsa ba tare da ita kanwar tasa ta sanshi ba.
Ya ganta a Katsina ta nuna bata taba saninsa ba, yanzu kuma aiki ya kawo shi Ibadan ta biyo shi, dama ‘yar Ibadan ce? Wani burin e gare ta game da shi? Abin da bai sani ba kenan, amma mamaki kam ya nunka hauhawa a zuciyarsa.
Kafin yayi wani yunkuri hart a shige cikin gidan, zuciyarsa ta ayyana masa yabi ta zuwa cikin gidan don jera mata gwanon tambayoyin da suka cike masa ruhi, amma kuma sai ya fasa wannan yunkurin nashi, sakamakon tunowa day a yi hakan da yake son yi haramun ne ka shigarwa mutum gida bad a izininsa ba. Wata tambayar ma ta sake zuwar masa, ta dade a gidan tana zaune, ko kuwa ma dai gidan wasu ‘yan uwanta ne? idan gidan wasu ‘yan uwanta ne ai makulli ya ga ta saka ta bude gidan, hakan yana nufin ba kowa, ita dai ce yazu ta bude ta shiga. Tabbas haka ne, sai dai ko iada masu gidan suna da tsarin rufe gidansu a kowane lokaci, idan mutum zai shiga sai yayi amfani da makulli. Wannan tsari ne na wasu mutane da ke kasasjen Turai, amma mu kam a Nigeriar mu ba mu san wannan tsari ba, to ya abin yake? Tsayuwar waata bakar mota kirara Odessy a kofar gidan da Shuhuda Ibn Khaddab ta shiga ta dau hankalinsa. Wani Balaraben matashi ne ya gani ya fito daga cikin motar,sanye da Fakistan a jikinsa, fuskarsa da karamin tabarau. Isah yana kallo shi ma Balaraben ya sanya makulli ya bude gidan ya shiga, haka dai ya tabbatar masa duk wanda zai shiga gidan da makulli yake amfani.
Waye shi wannan matashin Balarabe da ya shiga gidan? Babu amsa gumi ya gama jike shi sharkaf! Duk wata nutsuwarsa tayi kaura ta rabu da gangar jikinsa. Kanwarsa Shuhuda ta tabbatar masa Shuhuda Khaddab 'yar asalin jihar Katsina ce, kuma mazauniyar jihar Katsina, wadda ta yi karatun sakandire dinta a jihar Kano. Wane sanadi ne ya kawo ta birnin Ibadan? Ga shi ba ya shiri da kanwarsa Shuhuda da ya tuntubeta shin ko dama Shuhuda Ibn Khaddab tana zuwa Ibadan ko ta taba zama a can ne? Komawa yayi cikin gida, ya zauna a gefen gadonsa yana tunanin abin yi, shin ko dai ba Shuhuda ibn Khaddab bace ya gani ba? Ta ya ma zai ce ba ita ce ya gani ba? Lallai ita ce to tababa babu. juyawa yayi ya dauko wayarsa da ke kan bedside(gefen gado) wata zuciyar ta shawarce shi kawai ya kira Shuhuda yayi mata tambayoyinsa. Har ya laluba lambar Inna Yaduwa, sai kuma ya fasa sakamakon wani kunci da ya ji ya mamaye masa zuciya. Abin da ta yi masa akan Hamza ya yi masa ciwo, wai har ta iya son bare akan na gida?
Karar kwankwasa kofa yaji, a hankali yace. Alwaye ne?" Daga bakin kofar dakin nasa ya jiyo muryar Beka (daya daga cikin masu yi masa hidima) ya ce. "Ni ne yallabai". Cikin harshen turanci yayi maganar. Isah ya bashi umarni ya shigo, ya ce "Yallabai an kawo wuta za a sauya". "Ok, ba matsala". Isah ya mayar masa da amsa. Beka ya fice daaga dakin. Isah ya maida kai ya kwanta, tunanin ma aka rufe babinsa, amma damuwa da rudani sun kaura daga zuciyar sa. Da yaga abin zai masa tarnakinda zai iya haddasa masa matsala, sai ya janye wani littafi 'lobe sick' ya soma karantawa. Washegari sai misalin karfe takwas da mintina arba'in ya tafi gurin aiki. Bai dawo ba sai yammaci sosai, yau ma a barandar ya tsaya har lokacin magaruba ya yi, da yake akwai masallaci a layin,sai ya fito ya samu jam'I. Ana gamawa ya dawo, bai shiga cikin gida ba, a harabar ya tsaya. Yana kallon motar ta tsaya, Shuhuda ibn Khaddab ta fito, yau sanye ta ke da material mai ruwan sararin samaniya (sky blue) sabanin jiya da take sanye da leshi ja. Da ta fito daga motar ba ta bar gurin ba, jingina tayi da motar tana dube-dube tamkar mai neman wani abu. Zuciyarsa ta ayyana masa kawai ya isa inda take, sai dai yana yunkurawa da nufin haka, sai yaga ta rabo jikinta daga motar ta soma taku tana nufan gidan da ta shiga jiya. Fasa zuwa wurin nata yayi, don yana da tabbacin kafin ya zagaya ya fita tuni ta dade da shigewa gidan. Har tsayin mintina ashirin da uku da shigarta cikin gidan bai ga matashin Balaraben ya shiga kamar yadda ya faru a jiya ba.
Kamar walkiya ya hangota ta fito a sukwane gurinsa ta nufo. Kallo daya zaka yi mata kasan a rude ta ke, sam ba ta cikin nutsuwarta.
Sai da ta karaso daf da barandar maimakon ta zagayo ta get ta shigo ciki sai ta tsaya daga nesa musryarta da dan sauti mai karfi ta ce.
"Don Allah yah Isah ka taimaka min, mijina ne ba shi da lafiya, ba zan iya tuki ba, ka taimaka min don Allah".
Ta karashe maganar cikin raunanniyar murya, kwalla suncika gurbin idanunta. Maganarta ta hargitsa masa tunani tabbas dai Shuhuda ibn Khaddab ce, tunda har ta iya ambatr sunanasa kai tsaye haka. Amma abin tambayar shi ne, dama tana ta aure? Ba mamaki hakan ne tafuya ta kamata ita da mijin nata zuwa birnin Misra, asalinta 'yar Katsina ce, zaman aure ya kawo ta Ibadan. A haduwarsu ta Katsina ta nuna sam ba tasan shi ba, yanzu kuma ta zo ta ambaci sunansa har tana neman taimako, wannan rainin hankali da yawa ya.......
"Ka taimaka min, wallahi zai iya mutuwa!"
.
.
Wata sabuwa........!idan kai/ke ,ne/ce, zaka/ki taimaka?
Hanya, Isah zai taimaka???
da Hausa Book stories
MATA UL HAYAT
¤¤26¤¤
Ta katse masa tunani da fadar haka, hankalinta yayi kololuwar tashi. A matsayinsa na Musulmu, wanda yake son ya kasance mai karfin imani da tausayawa halin da dan uwansa muslmi ya shiga, sai ya ji zuciyarsa ta kare har ma yana kwadayin samun wannan gugguben ladar. Kawai sai ya zagaya ya bi bayanta yana jefa kafafu tamkar wadda zata tashi sama. Ta bude gidan ta zura kai, shi ma ya bi ta bayanta. Yana kwance a falo, magashiyan yake. Usah ya karsa gurinsa da sauri yana taba jikinsa. "Subhan Allah". Ya dago kai ya dube tan ya ce, "Tun yanshe ne bashi da lafiyar?" Cikin yanayi na rashin sukuni ta ce, "Yanzu ne na dawo na tarar da shi a haka, amma lafiya lau ya baro ni gurin aiki". Ya ce, "bari na dauko mota". Ta katse shi, tana mika masa makulli. "Ga tawa, mu je kawai". Ya kama shi suka fito harabar gidan, Ta yi sauri ta bude masa gidan baya ya shiga da mara lafiyan, sannan ya zagaya mazaunin direba ya shiga, itta kuma ta shiga gidan baya, Ya ja suka tafi.
Ba a bata lokaci ba aka karbe su, wani daki na musamman aka saka marar lafiyan, su kuma aka bar su a bakin kofa. Isah yana zaune saman kujera, yayin da ita kuma ta ke zarya daga bakin kofar dakin da mara lahiyan yake ciki zuwa tsakar falon da suke, tana takun tana buga hannunta cikin daya hannun. Shi dai kallonta yake a nazarce don tantance shin da gaske ita din dai ce ko kuwa kama ce? Amma iya duba da nazarinsa bai ga wata alama da ta banbanta da Shuhudar da ya gani Misra da Katsina ba, har yanzu zuciyarsa ta kasa samun nutsuwa a lamarin, idan ya kamo wannan zare kafin ya tufke shi, sai ya gudu, ya sake kamo wani, shi din ma babu nasara. Sun yi shiru su duka na tsayin lokaci babu wanda ya tankawa dan uwansa. Can Isah ya dago kai yana sake dubanta, ya ce. "Ya kamata ki zauna, in shaa Allahu zai samu sauki". Ta dan juyo a kaikaice ta ce masa. "Ina son mijina! Ina mararin zama da shi, kada ya mutu idan na rasa shi ban san da wane namiji zan rayu ba. Wayyo yah Abubakar kada ka mutu ka barni da maraici, kasan kai ne NURUL KALBI dina, kai kadai ne wanda zan kalla na ji sanyi a kalbina". Idanunta suka soma zubar da hawaye. Sai ya ji zuciyarsa ta karaya ya soma rarrashinta da sanyayen kalamai masu kwantar da zuciya da saka nutsuwa. A hankali ta nemi guri a gafensa ta zauna tare da sanya hankici tana share hawayenta. Murya a raunane ta soma cewa da shi. "A rayuwa idan mutum ya dace da masoyi na kwarai, wanda sai iya sadaukar da rayuwarsa don sama maka farin ciki, ya yi tawaya akan komai don kai, ai ka gama samun komai a rayuwa. Irin su Yah Abubakar Ibn Khaddab suna da karanci a duniya, duk macen da ta yi sa'ar samunsa a matsayin miji to ta godewa Allah, domin ba karamin rabo ne ta samu ba". Isah ya tuna sunayen 'yan gidan su Shuhudar Misra da ta lissafo masa a haduwarsu can Misran, daga cikin lissafin nata tace su uku ne mahaifansu suka haifa. Ita kanta Shuhudan, Yayanta Abubakar sai kaninsu Yusif, kuma dukkansu suna lakabi da sunan mahaifinsu IBN KHADDAB. Yanzu wannan Shuhuda da ke gabansa ta ce sunan mijinta ABUBAKAR IBN KHADDAB ke nan ba iata ce Shuhudan da ya tab sani a Misra da Katsina ba, tunda a bayyane yake babu aya ko hadisin da suka halatta auren JINI DAYA.... Ta katse masa tunaninsa da cew. "Akwai wadda nake zargi da ciwon mijina!" Ta mike zunbur kamar wadda aka tsirawa allura, ta ce, "Tabbas na gano sanadin rashin lafiyar mijina!" Ta daga yatsanta sama kamar zata yi masa nini da wadda ta ke nufi, shi dai ya tsura mata idanu kawai yana kallonta da sauraren maganganun da suke fitowa daga bakinta.
"SHUHUDA SAGIR RABI'U ce! Ita ce ta bakunce mu a ofis ta ba wa mijina wani lemo. Da farko bai karba ba, sai da na matsa masa a matsayinta na bakuwarsa bai kamata ta yi masa kyauta ya ki karba ba. Ina tunanin lokacinda ya dawo gidan ne ya sha lemon, shi ne ya haddasa masa rashin lahiya, wata kila wani mugun abu ne ta sanya masa..." Tun lokacin da ta ambaci cikakken sunan kanwarsa ya mike tsaye cikin rudani, musamman da ya ji karashen maganarta. Yaushe Shuhuda kanwarsa ta zo ibadan? Me ye alakarta da garin? Ba ta zo ba, kuma ba ta da alaka da birnin Ibadan, to amman me maganganun wannan Shuhudar ke nufi? Sharri za ta jawa kanwar ta, aminiyarta? Ko kuwa rainin hankalin da suka saba yi masa ne za ta yi masa don dilmiyar da shi cikin rudani? Idan haka ne ba ta yi masa adalci ba, ta zoleye shi da yiwa kanwarsa sharri irin wannan, rai ai ba abin wasa ba ne. Ba tare da ta damu da shi ba, ta ci gaba da maganarta. "Dama tunda na ga kwayar idanunta na zargi wani abu, na dauka ko irin kishin nan ne namu na mata yasa na zargi wani abu, ashe dai akwai wata kullalliyar da ta kullo mana?" Isah ya ske tsintar kansa cikin wani rudanin jin tana tabbatar da zarginta akan Shuhudarsa. Amma sai ya maze ya boye damuwarsa ya ce, "ki yi hakuri, kada zuciya ta sanya ki yi hasashe mara kyau gudun saka rayuwarki cikin rudu"..
Wani murmushin takaici ta yi masa tukunna ta ce, "Mhm! Kai dai ayi sha'ani, maye ya ci dansa. Amma mutum? Mutum?" Ta sake maimaitawa cikin jinjinawa. "Mugun icce ke nan, mutum dan masara kana goyonsa yana fidda kai. Kana kallonsa sumi-sumi amma mugun nifinsa ya wuce misali. Shi ya sa na tsani mutumin da zan dinga kallonsa kamar salihi, na fi son kawai ka zo min a tsayenka sai na fi aminta da nutsuwarka, amma sai su nuna su na gari ne, suna wani sunnar da kai alhalin KATTIN MUGAYE ne!" Daga haka su duka suka yi shiru, Isah yana tunanin hanyar da zai bi ya fitar da maganganun da ke cikinsa, amma yana tuna hakkin aure, bai kamata ya tsawaita zance da matar da ba muharramarsa ba. Bai. San yadda aka yi ba, ya kasa hakuri ya magantu. "Yauwa, don Allah a ina kika san sunana don na ki lokacin da kika zoneman taimako a gurin kin ambaci sunana?" Ta dube shi fuskarta da dan yalwa, ta ce. "Ba mamaki, ai duk mutumin da yake cikin unguwar nan musamman layin nan, mijina ya sanar da ni wanzuwarsa gami da sunansa, don haka nake kiran kowa YAYA saboda na tabbata kowa ya mirme ni". Bai gamsu da amsar da ta ba shi ba, ya buda baki zai kuma magana ke nan, likita ya fito. Da sauri ta mtsa inda yake, ta ce. "Likita ya mutu? Wayyo ta kashe min miji!" Ta soma kuka, liktan ya ce. "Saurara madam bai mutu ba, yana nan da ransa". Isah ya matsa shi ma kusa da likitan ya ce da shi. "Ok, muna iya shiga gurinsa?" Likitan ya girgiza kai, ya ce. "Bacci yake, idan har ba zaku yi masa kwarabniya ba za ku iya shiga, saboda yana bukatar hutu, ciwon ciki ne yake damunsa". Isah ne kadai ya karasa sauraren maganganun likitan, ita kuwa tuni ta shige dakin. Likitan ya wuce, yayin da Isah yayi tsaye yana mamakin wannan MURDADDIYA, ko ta ina zai warware ta?
"Mhm! Hanya mai sauki!"
Wata zuciya ta ayyana masa.
"Idan ka danganta Shuhudan Misra, da ta Katsina da kuma wannan ka samu warwarar labarinka". Zuciyar tasa ta kuma ayyana masa. Da sauri ya ciro wayarsa, ya lalubi lambar Inna Yaduwa ya kira, ta yi kara sau daya, biyu, ana uku aka dauka. Shuhuda ce ta dauka, ko bari ba ta yi ya yi magana ba ta soma magana cikin doki da murna. "Haba Yah Isah, yanzu haka rayuwa ta ke? Zunmunci sai ya yi wuya?" Mamaki ya hana shi magana, yayinda ita kuma ta dora da cewa. "Ai na yi tsammanin ko ba wani abu a tsakaninmu wanda ya danganci JINI, aka nuna maka ni aka ce 'YAR UWARKA ce, ka dinga kirana muna gaisawa, amma saboda Allah tunda ka tafi ka taba tunawa da ni? Yanzu ma ba don wayar Innar na hannuna ba, na tabbata ba zaka ce a baka ni mu gaisa ba". Cikin kasalalliyar murya ya ce da ita "Kuna lafiya?" Ta ce, "kalau waLlahi, ya birnin Ibadan? Don Allah Yah Isah me da me ke da akwai a ibadan wanda babu a kano, wai akwai sanyi, ana barin wuta, matansu farare ne sol, wai ko ina cikin Ibadan akwai cinkoso kamar nan K....." Ya katse ta da cewa. "Ya isa haka, ina Inna Yaduwa?" Muryarta a raunane kamar wadda zata yi kuka, ta ce. "Kayi hakuri Yah Isah, ban san zan takura maka har na bata maka rai ba, ka yi hakuri don Allah.... Inna Yaduwa ta fita unguwa, ni ma Shuhuda Ibn Khaddab ce ta kawo min ziyara daga Katsina shi yasa ban bita ba, ita kuma ta manta wayar".kamar zai tuhume ta abin da yake son tuhumarta, amma jin abin da ta fada sai ya kasa magana ya katse wayar. Komawa ya yi akan kujerar da ya tashi ya zauna. Wani tunani ya darsu a zuciyarsa, wai bakuwa ta yi... Shuhuda ibn Khddab ta kawo mata ziyara daga Katsina... Ke nan wannan ta gabnsa ba ita ce wadda yake nufin ba, wata ce can daban? Lokacin da yana Senegal suna yawan yin waya da kanwarsa Shuhuda a wayar Inna Yaduwa, da ya dawo ya bukaci ya siya mata waya ta kawo masa kabli da ba'adi wai hannunta ba ya iya rike waya, yanzu da wane hannun ta yi amfani ta rike wayar da suka yi magana? Da can da wane hannun ma ta ke rike waya suna gaisawa? Gaba daya yaran nan sun gama raina masa hanka li, fita a sha'aninsu shi ne mafitar MURDADDIYAR da suke saka shi! Sai dai zuciyarsa ta kasa wannan yunkurin, Allah Ya jarabce shi da abu mafi tsauri, wato KINAYAR MATA, abin da ya fi ba shi mamaki kasancewar yaran kanana, amma sai juya shi bai-bai suke kamar waina a tanda. Ya dokantu ya ga an zo karshen wannan wasarere da hankalinsa da ake yi.
* * * * *********
.
Kwana hudu tsakani tun bayan rabuwar Isah da wadda yake ganin Shuhuda Ibn Khaddab ce bai sakata a idanunsa ba, sakamakon aiki da ya rufe masa kofa, sam ba shi da sukuni, idan ya fita tun safe ba shi yake dawowa gida ba, sain gama sallar magruba. Lokacin da zai dawo a gajiye yake, don haka a daddafe ya ke samu ya salaci jam'in isha'I ya shige gida ya yi wanka, sai kuma maganar bacci. Yau ya kama ranar lahadi ce, baya zuwa aiki, tun asuba da ya yi sallah ya koma bacci bai farka ba sai karfe sha daya. Kafin ya fito wanka Beka ya gama hada masa abin karin kumallo. Yana gama karin ya fito barandar gidansa ya tsaya, sanye yake da kananun kaya blue jeanz da red T shirt wadda daga bayan rigar aka rubuta Onlu for you. Rashin sukunin da yake da shi ya sa ya dan rame, amma ramar sai ta kara masa kyau dama ga shi kyakkyawan.. Yana tsaye a gurin tunanin abubuwan da suka faru suka dinga dawo masa a rai. Wato tunani ma lokaci gareshi, hakika ba don aikin da ya sha masa kai ba da damuwar da zai shiga Allah ne Ya yi yawa da ita, amma yanzu dan takaitaccen lokaci da ya samu na hutu tunanin har ya bijiro masa. Sai dai bai yi nisa a tunanin ba ya hango Abubakar yana fitowa da jakunkuna yana zubawa a mota. Mamaki ya kama Isah, lafiya? Ya tambayi kansa. Kafin ya samu amsar tambayar tasa ya ga Shuhuda ita ma tana fitowa da wasu kayan, sannan tana share kwalla da hannayenta. Hakan da ya gani ya tabbatar masa da lallai ba lafiya ba, akwai wani muhimmin al'amari a tare da su. Da farko ya so ya shere da su, amman zuciyarsa ta ki amincewa, makoci ba wasa ba, hakkin da yake kan makoci ba karamin ba ne, shi mutum ne da yasan darajar makocinsa. Idan ya kyale su suka tafi bai san damuwarsu ba, abin zai dame shi, wata kila ma rasuwa ce aka yi musu. Cikin karfin gwiwa ya soma takawa don isa inda suke. Daga can nesa da su kadan ya tsay saboda Shuhuda na kusa da mijinta, yasan ko yaya ne mijin nata ba zai ji dadi wani ya kusanta da ita ba. Ya dan daga murya, ya ce. "Malam Abubakar lafiya dai na ga kuna loda kaya a mota kamar za ku yi doguwar tafiya?" Abubakar yana kallonsa ya ce. "A'aha Haji isah karaso mana, ka toge daga nan?" Cikin karkarfan takunsa ya karasa gurin yana kuma maimaita tambayarsa. Abubakar ya ce masa. "Eh, gida Kaduna zamu je, wata yarinya ce ta yaudareni daga ta zo min bakunta ta zuba min magani a lemo shi ne na sanya aka kamata tana yunkurin guduwa da dalolina, don haka zamu je. Sai munyi tsayin wata daya kafin mu dao shi ne mai dakin nawa ke kuka.
A rayuwarta ba ta son zama Kaduna. Ta fi sha'awar nan ibadan ni kuma ina duba kadaicin da zata shiga kafin na dawo. Isah ya ce da shi. "Akkah Sarki, ashe dai abin da gaske ne? An samu nasarar kamata ke nan?" Shuhuda ta tsoma musu baki, ta ce. "Ai idona idon Shuhuda Sagir Rabi'u sai ta raina kanta, muguwa, azzaluma kawai". Abubaakar ya dube ta, ya ce. "Ai sai ki yi hakuri tunda dai. Ba ta kassara miki rayuwa ta raba ki da ni ba, ba ga shi ba da yake Alla ba Ya barin hakkin wani akan wani ba, tun aduniya Ya toni asirinta ba?" Shuhuda ta ce, "Wallahi Yah Abubakar ba komai nake ji da tafiyar nan ba. Illa dadewar da zamu yi ba ma nan, gida babu kowa akwai matsala, musamman yadda bata-gari suka yi yawa a gari yanzu. Wannan shi ne damuwata kawai ba wani abu ba".
Abubakar ya yi dan takaitaccen murmushi, ya ce. "Ka ji hasashen matan ko? Sai ka ce wadda ta tsauna dukiyar Nigeria gaba dayanta". Isah ya ce, "A'a kada ka ga laifinta, ai ko naira biyar aka sace wa mutum dole ya ji zafi, ba satar ke da ciwo ba, abu mai muhimmancin da aka sace shi ne ciwon". Abubabakar ya ce. "Haka ne, amma an fi so mutum ya saka karsashi a zuciyarsa, babu abin da zai same shi face rubutaccen al'amari ne daga Allah". Isah ya ce. "Idan haka ne, kada ku damu in sha Allah zan saka a dinga kular muku, ni ma idan ina gida zan dinga kula". Abubakar ya ce. "Ai kuwa mun gode da wannan taimako da ka yi mana". Ya dubi Shuhuda ya ce. "Ina makulli? Kawo mu ba shi daya ko da wani abu zai taso na bukatar shiga ciki". Isah ya yi saurin cewa. "A'a ba ma sai na karbi makullin ba, zan dinga kula, inshaa Allahu babu abin da zai faru har ku dawo". Abubakar ya girgiza kai, ya ce. "Idan dai har ka amince zaka yi mana wannan taimakon, to karbar makullin yana da amfani". Bai tsawaita jayayya da su ba, ya karbi makullin tunda ya ga sun aminta da

Please Login or Register in order to submit comment