Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hakuri? Wannan kalami ya sake tunzura Binta tace Kin sa Alhaji ya bugi Mas'ud to idan dai ni na haifi Mas'ud har aban abada ba zai ta6a gayar da ke ba. Duk wani ahali nawa ba zai ta6a yin wata mu amala da ke ba, idan kina so ki burge ni kisa Alhaji ya sa wuka ya yanke kawunan duk wani ahali nawa akan ba sa gaishe ki sannan zan tabbatar da sunanki karima matar so. Ta ja wani dogon tsaki tace Shi kuma Alhajin yayi na farko ya yi na karshe don bashi ya sha min wahalar daukar cikin ba bare ya kama min 'yaya da duka akan wata banzar bazara ruwan kaka, juya wadda tun da ta shigo gidannan komai ya ta6ar6are. Tana karashe maganar ta sa kai ta fice daga kicin din ta bar karima nan tsaye sororo cike da takaici don halayen Binta ba su ba ta mamaki, sai dai tsoro. Ta tabbatar da ace za a bata umarni ta kashe ta ko jinkiri Binta ba zata yi ba zata iya kashe ta saboda wannan zafin kishin nata yayi yawa. Cikin rashin sukuni ta kammala miyar ta dawo daki da nufin ta huta kafin a dawo daga sallar azahar ta zubawa kowa nashi. Tana nan zaune ta jiyo sallama a falonta ta shaida muryar dattijuwa ce mai YAKANAH wadda ta nuna mata halacci ta sota a lokacin da take tare da ita wato Inna Yaduwa. Ai kuwa da sauri ta fito falon ta na lale marhabun da zuwanta. Bayan Inna yaduwa Shuhuda da Isah sun zauna Karima ta je ta zubo musu tuwon shinkafa miyar agushi ta kawo musu gami da ruwan sanyi. Ta zauna suna cin abincin suna gaisawa har suka kammala Inna yaduwa tace: Karimatu ki yi hakuri don Allah da jinkirin da aka samu na kawo miki Shuhuda tsayin watanni tara. Kinsan lamarin zaman gidan wani wuya gare shi musamman ma yadda na lura halayen abokanan zamanki ba ya da kyau. Karima tacr Lah! Wallahi Inna ba komai ai ana kawota don wannan karon an samu jinkiri sai ya zama wani abu? Wallahi ba komai. Shuhuda ta mike tsaye Inna yaduwa tace Ina zaki? Tace Fitsari zan yo? Ta fita Inna yaduwa ta dawo da dubanta ga karima ta ce; Ga fa danki kin san dul cikin satin nan ba zancen da yake sai naki yau dai ya takura sai na zo. Karima ta yi murmushi tace Isah ke nan? Ai shi kam da Mamansa sai Allah. Inna yaduwa ta dan saka nutsuwa tace. A nan zamu bar Shuhuda za ta yi miki sati biyu saboda mako mai kamawa zata soma zuwa Makarantar boko kuma kin san yaro idan ya na karatu baya da wani sukuni bare ga kuma Islamiyya.
Karima taji dadi har cikin ranta da jin wannan batu saboda a yau zata kwana da gudan jininta 'ya daya tilo ta mallaka a duniya. Wadda in baci ita da sai ta aminta da maganar su Binta ke fada akanta cewar ita din juya ce to amma kasancewar ta san ta ta6a haihuwa sai zancen na su bai dauke ta ya nana da kasa ba. Ta san cewa tsawon shekaru biyar data shafe a gidan Alh jamilu Allah ne bai hukunto haihuwar da shi ba idan lokaci yayi zata haifa din. Kukan Shuhuda da suka jiyo ne a tsakar gida ya sa gaba daya suka mike tsaye a zabure suka nufo tsakar gidan. Mas'ud yaro dan shekaru sha tara suka hango ya kama Shuhuda yana jibga kamar wata tsaran shi. Sai dai suka ja tunga suka tsaya, Inna yaduwa ta dubi karima cike da tsananin mamaki ita karimar Inna yaduwan take kallo. Isah kam tuni ya kaiwa 'yar uwarshi dauki ya cakumi wuyan rigarshi ya yi wurgi da shi tare da kai mishi wani irin wawan naushi. Rigima ta raku6e tsakaninsu Shuhuda kuwa tana kwance. Karima ta yi saurin shiga tsakanin su ta raba su amma Mas'ud ya tattakura ya kaima ta naushi a gefen cikinta ba arziki kuwa ta ja baya. Inna yaduwa ita ta raba fadan yayin da Binta ta fito daga dakinta dama duk abinda yake faruwa akan idonta ne abinda yasa tun dazun ba ta fito ba tasan Mas'ud yana da taurin rai mawuyaci ne ayi fada da shi bai samu galaba ba amma yau sai ga shi zance ya sha bam-bam. Duk girman jiki irin na Mas'ud amma Isah ya fi shi zafin nama da karfi domoin ba don Inna yaduwa ta raba fadan ba wata kila sai dai a dauki Mas'udin ranga-ranga. Binta na fitowa daga dakinta ta balbale Inna yaduwa da masifa har tana kiranta tsohuwar akwala wai tana shiga fadan yara. Inna yaduwa ta rike ha6a kawai tana karewa Binta kallo mamaki take yi 'yar da ta haife ta a cikinta amma ita ce take yi mata wadannan munanan furucin. Binta jin ba wanda ya tanka mata sai ta kama hannun Mas'ud tace: Mu je ciki Alhajin ya dawo Ni na gaji da wannan masifa mata kin zame min ciwon ido mai wuyar magani a gida? To wallahi ba zata sa6u ba bindiga a ruwa yau alo tsiya alo danja sai an san mai yiwyuwa. Inna yaduwa suka karasa inda Shuhuda take kwance duk ya farfasa mata jiki, amma a madadin a ga JINI a gurin da ya farfasa mata sai suka ga RUWAN NONO fari kal yana zuba. Wannan lamari ya hargitsa tunanin karima don bata da masaniyar wancan al'amari da ya ta6a faruwa. To ita kanta Inna Yaduwan da Isah abin ya kara hautsina masu kwanya shin ita Shuhuda wacce irin halitta ce da gaba daya jikinta babu jini sai Ruwan nono? Dama akwai mutumin da jikinsa yake dauke da ruwan nono sa6anin jini kuma yana rayuwa? Amsar data yi musu wuya kenan suka taitaye ta zuwa daki. Kwallah ne kawai ke zuba a idon karima yayin da Inna yaduwa tace. Karima shin dama baki zaman lafiya da matan gidan nan ne? Sam ta kasa magana zubar hawaye kawai take. Inna yaduwa ta jinjina kai tace; To Allah ya sauwake tunda abin haka ne bazamu bar shuhuda a gidan nan ba.
ada Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA)
¤¤07¤¤
Karima ta girgiza kai da sauri amma ba ta iya cewa komai ba Inna yaduwa tace; A'a ba za mu barta ba ba zan so sanadinta ki sake samun rashin jituwa tsakiniki da abokan zamanki ba har yayi sanadin mutuwar aurenki. Idan dai an kwana biyu za a dinga kawota ta yinar miki a koma da ita amma don Allah kici gaba da halinki na hakuri, shi dama zaman aure gaba dayansa hakuri ne jigonsa, da zarar aka ce babu hakuri to babu zaman aure. Ba yadda yi haka ta hakura sai dai abin na damunta a rai ganin ruwan nonon da ya zuba a raunikan Shuhuda amma ta yi alkunya ba ta tanka ba saboda kasancewa Shuhuda 'yar fari ce. Ita din ma Inna yaduwa ba ta maida kai kan al'amarin ba ta sa ruwa ta wanke wa Shuhuda raunukan. Da yammaci su kayi bankwana suka ta fi cike da alhinin abinda ya faru. Bayan sallar magruba Alh Jamilu ya dawo gida a gajiye saboda aiki da yayi masa yawa. Kai tsaye bandaki ya shiga yayi wanka. Yana fitowa ya tarar da Binta zaune akan kujera sai huci take tamkar kububuwa. Yana ganin yanayin ta ya san korafi ne ya kawota dakin don haka ya gumtse fuskarsa ya zauna gefen gado yana murza mai a jikinsa. Binta ta kara kulewa ganin yadda ya banzantar da ita cikin 6acin rai tace: Gaskiya Alhaji na gaji wannan matar ko 'yar gwal ce sai haka bare kuma ba abinda ta fi wani cikin gidan nan. Ya dago kai ya dube ta. Mai kuma ya faru? Cikin isa-isa tace; Kawai ta gayyato gayyar danginta sunzo sun kama Mas'ud da duka ba don na fito ba kila da kashe shi za su yi. Domin na lura wannan tsohuwar kwararon so tayi ta shake masa wuya ya mutu? Yace Shikenan a saurare ni zan bincika lamarin. Tace Ni fa gaskiya duk laifinka ne domin kai ka nuna iyalanka ba su da gata a gurinka.... Ya daga mata hannu ransa a dan 6ace yace: Kinga ya isa haka, kin fada min nace zan bincika ba shikenan ba? Ta mike tsaye. Ai don ka sani ne bazan lamunta da dik wani iya shege ba. Duk wanda ya ta6a min 'yaya sai na ji dalili. Ta karashe maganar tana kokarin fita. Ya bita da kallo kawai batare da ya tanka ba su dai korafi shine abin yin su inda yake jin dadin karima kenan. Sam bata kawo mishi korafin wani, duk abin da zata yi wanda zai sanya shi farin ciki shi take yi. Yana kokarin saka jallabiya ne karima ta shigo hannunta dauke da kofin ruwa a hannunta. Fuskarta dauke da fara'a amma idonta kadai zaka kalla kasan ta sha kuka. Tayi sallama ya dago kai ya dube ta shima fuskar tashi dauke da fara'a ya amsa mata. Don Allah ka yi hakuri na tsaya yin sallah ne. Yace Kada ki damu nima sallar zan yi. Ya gama zura rigar ya hau sallaya ya gabatar da sallah. Sai da ya gama tsaf ya zauna yana murmushi. Me aka tanadar min ne? Ta tsiyaya mishi ruwa a kofi tace: Ga ruwa dai ka fara jika makoshi, ai sai kayi Isha'i zaka ci abinci ko? Ya daga mata gira yayin da ya kai kofin ruwa a bakinsa. Ya sauke kofin yace; Yauwa yau su waye suka zo gidan?
Sai taji gabanta fadi ya fadi tana da tabbacin an sanar dashi abinda ya faru. Tace: Su Inna ne suka zo kawo wagga mu gaisa. Ya gane wadda take nufi saboda ba zaka ta6a jin bakinta ya ambaci sunan Shuhuda ba. Yace Okay har sun koma ne? Tace Eh. Yace Mai yasa ba a bar mana Shuhudan ta yi mana ko dan kwana biyu ba? Sai tayi shiru, a ganinta idan ta fada masa kamar ta rura wuta ne do haka ta za6i yin shirun. Yace; Binta ta ce min an dan samu rashin fahimta don Allah karima ku zauna lafiya da junanku ku daina daga min habkali. Rashin zaman lafiyarku yana dagula min lissafi da hana min sukuni, ko fita na yi kullum da fargaba nake dawo wa. Cikin kwantacciyar murya tace; Inshaa Allahu komai ya wuce. Yace: Na gode na sanki mace ce mai biyayya idan don take za a yi tashin hankali to an dade ba a yi ba. To amma halin su Binta yana iya sauya miki hali don haka don Allah kada ki yi koyi da halayensu, ki dinga kawar da kanki garesu. Tace: To amma ni ma ina rokon alfarma. Don Allah kada ka kara yiwa wani iyalinka wani abu daga gare ni. Idan sun gaishe ni kan su ba kara min lafiya gaisuwar tasu zata yi ba haka rashinta ma ba zai rage ni da komai ba. Yace; Shikenan Allah yayi miki albarka. Tace Ameeen. Karfe Uku na dare wani irin mummunan ciwon ciki ya murde MAS'UD ihu kawai ya ke zabgawa. Sunusi kaninsa da yake kwance yana bacci shine mutumin da ya fara jin ihun yayansa. Cikin tashin hankali ya tashi ganin halin da dan'uwansa yake ciki ya daga masa hankali. Da sauri ya nufi cikin gida yana kwankwasa kofar mahaifinsu. Alh jamilu da yake bacci ya tashi a firgice yazo bakin kofa yana tambayar; Waye ne? Sunusi yace; Abba ni ne. Yace; Sunusi lafiya? Kafin ya bude kofar Sunusi yace;; Abba ya Mas'ud ne bashi da lafiya. Da sauri Alh Jamilu ya bude kofar suka nufi dakin. Kwance shame-shame suka tarar da sunusi jini yana madodawa. Iya tashin hankali Alh Jamilu ya shige shi ya rasa abinda zai yi. Yanzu wane asibiti za su nufa? Dare ne karfe uku na dare da wuya a samu asibitinb da za a tarar da likita. Ya tuna yana da wani aboki likita don haka da sauri ya dubi sunusi yace; Maza je ka dakina ka dauko min wayata. Sanusi ya nufi dakin, tare suka dawo da karima wadda a lokacin ta farka saboda girkinta ne tana dakin Alh jamilun. Sunusi ya mikawa mahaifinsa wayar ya kar6a ya soma lalubar lambar yayin da karima take sallallami ganin halin da mas'ud yake ciki. Bugun farko dr Musbahu ya dauja saboda a lokacin yana kan na'ura mai kwalwa(computer) yana binciken wasu cututtuka. Suka gaisa Alh jamlu ya sanar da shi halin da ake ciki. Dr musbahu yace; ga shi nan zuwa. Amma kafin dr. Musbahu ya karaso gidan tuni Mas'ud yace Ga garinku nan. Anin da ya daga hankalin Binta ke nan ta dinga kwarara ihu cikin daren shi kam Alh jamilu daukar gawar Mas'ud yayu ya kai dakinsa zuwa safiya a suturce shi don sadar da shi makwancinsa. ****** ***** ********
BABI NA UKU ------------- ------------ ------------- AL'AJAB ---------------
-------------------------- Shuda ta soma zuwa makaranta inda ta ke a firamare(primary) Yarinyar Allah ya zuba mata kwalwa da fahimtar gane abu zai yi wuya a fada mata abu ba ta hardace shi ba. Matsalarta daya wani lokaci kamar gidi-gidi(marar hankali) take. Tana samun kulawa ga dan'uwanta Isah wata irin shakuwa ce a tsakaninsu ta yadda idan daya ya yini ba tare da daya ba to lallai zaka samu dayan cikin rashin sukuni. Tun lokacin da abin nan ya faru wato dukan da mas'ud ya yi mata ba a sake kaita gidan mahaifiyarta karima ba, to ita ma yarinyar sai Allah ya sa ba wani damuwa ta yi da akai ta gidan ba. Sai dai ita kariman ta kan zo duba ta shima ba sosai ba, don ma dai hakkin uwa. A haka ta shiga aji shidda na firamare a lokacin ne kuma Isah ya kammala karatun sakandire(secondry) dinsa don ma ya samu matsala ne a sanadiyyar wata rshin lafiya da yayi kamar ba zai rai ba. Sai da ya share wata daya a kwance sannan ya warke don haka aka maido shi baya tinda bai zana J.S.C.E ba. Mahaifinsa Alh sada ya sama masa gurbin karatu a kasar senegal san Isah bai si hakan ba domin yaso ace a nan gida Nigeria ya yi karatu saboda ya dinga ganin gudan jininsa Shuhuda, amma ina! Hakabsa ba zata cimma ruwa ba lokacin da ake shurye-shiryen tafiyarsa, ba shi kadai ba ita kanta Shuhudan hankalinta a tashe yake duk ta zabge ta ramr sau an yi da gaske take iya cin abinci. Suna zaune su uku a falo Inna yaduwa ta dubi Isah tace: Ni fa wannan rama da kuke tana ba ni tsoro daga zuwa karatu duk zaju bu ku tayar da hankalinku haka. Isah yae Wallahi Innada za a bi tawa ni dai a fasa tafiyar ma sam bana sonra. Ta dube shi cike da mamaki tace; Ko akwai dalili? Yace Eh Inna kinga na farko a ra'ayina na fi son ba yi karatu a kasarmu Nigeria, sannan abu na biyu...... Ya dubi Shuhuda tare da nunata da dan yatsansa. Ina so na zauna jusa da 'yar uwata. Inna yaduwa tayi dariya tace; Ka kai su dai in kaya ne. Idan ma don wannan kwailar yarinyar ne zaka damu kanka ka bari domin ko kana nan ba zan bari ka aure ta ba, gwara ma ka tafi kayi karatunka. Shima ya dan yi takaitacciyar dariya yace. Haba dai aike ma ba kya fara ba. Kuma bari ganin zan bar kasar nan ni na tabbatar har naje na dawo ina nan cikin zuciyar Shuhuda ko ya kika ce tawan? Shuhuda da ba tasan inda maganarsu ta dosa ba ta gyada kai. Isah yayi dariya yace: Aha ni dama nasan ba mai shiga tsakanina da tawan. Inna yaduwa tace To na ji amma don Allah ku sabya hakuri da nutsuwa a zukatanku ka dai ga inda zaka je kuma ba don komai zaka je ba sai don karatun nab don haka ka mayar da hankali ga abin da ya kai ka. Isah yace: Inshaa Allahu Inna zan yi karatu har sai na ga karshen biro da mai jan kunne. Ya karashe maganar yana dariya ita ma dariyar ta yi tukunna tace: Sannan kuma don Allah ban da kula masu jajayen kunne don ba ma zamu bari ka dauko mana jikanyar paparoma ba. Dariya ya sake yi ya mike tsaye: Mhm kaji Inna tana tsoron mai jan kunne ta kwace mata miji, ke shuhuda tashi muje gida Baba na kirana. Suka fice suka bar Inna Yaduwa tana tunanin yaran sun hada kansu Allah yasa su dore a haka har zuwa girmansu. Tayi musu kwadayin zama ma'aurata. A ranar da Isah zai tafi Senegak da kyar aka 6am6ari Shuhuda daga jikinsa yana kuka ya hau jirgu dole aka sakata a mota aka juya zuwa gida ba tare da sun ga dai-daituwar jirgin a sararin samaniya kamar yadda suka sa tsara ba, Tun bayan tafiyar Isah kasar Senegal Shuhuda ba ta da sukun sai anyi da gaske ta ke cin abinci. Sai da aka samu ta saka dangana a ranta, ta dinga cin abinci da walwalarta, sai dai wannan matsalar ta rashin wadatuwar hankali na nan har yanzu a tare da ita. Yadda abin nata yake idan ka dube ta ba zaka ce tana da wata matsala ba saboda a hutse ta ke, amma wani lokaci da ta yi magana zaka fahimci akwai shirmr a cikinta. Jarrabawarsu ta fito ta ci makarantar kwana ta shekara. Amma sam Alh Sada yaki don haka ya samo mata gurbin karatu a makarantar kudi mai suna AJURI MEMORIAL SCHOOL. Ta fara karatun ka'in da na'in dama can dai Shuhuda yarinya ce mai kwanya, to har yanzu din ma dai tana ta6ukawa. Mace ce mai nacin tambaya shi yasa malamai suke sonta saboda nagartar yaro makaranta ya kasance mai yawan tambaya da naci akan komai. Hutunsu na farko Shuhuda ita ta yi na goma cikin su talatin da biyar dake ajin. Kasancewarta bahaushiya kuma wadda bata da cikakken hankali kamar yadda 'yan ajin nasu suke gani, sun sha mamaki matuka ganin cewa wannan karamar yarinyar ce tayi na goma. Ba su sake samun wani mamakin ba, sai da aka sake yin jarabawa, a wannan karon na uku Shuhuda ta dauka. Kwalwar Shuhuda tana da ban mamaki joda yake babu mamaki ga lamarin Allah. ********** ******** ********** Haj. Karima tana ci gaba da zaman hakuri a gidan mijinta amma dai abinn da sauki don ma sai da Alh Jamilu ya tsawatar sosai. Binta cewa tayi Karima mayya ce ita da 'yarta sun lashe mata kurwar da. Da farko habaice-habaice ne take yi har dai daga baya ta fito fili ta bayyana manufarta. Ai kuwa duk yadda Karima ta ke da hakuri sai da maganar ta kai ta bango ta shiga daki ta soma hada kayanta, a dai-dai lokacin ne Alh Jamilu ya dawo gidan. Tambayarta yake abinda ya faru ya ga tana kuka ga kaya kuma tana hadawa amma ta kasa magana kukan kuma ya ki tsayuwa yi kawai take zuciyarta na kuna. Da yaga bata da niyyar tanka masa sai ya samu gefen gadonta ya zauna ya zuba mata ido har ta kammala shirya kayan ta saka hijabinta ta janyo jakar zata fice daga dakin. To a lokacin ne ya yi zumbur ya mike ya sha gabanta yana kallonta ido cikin ido yayi karfin hali yace: karimatu tun da na aure ki ban ta6a samun ki mai yin wani abu ba tare da izinina ba. Shin ina zaki da kika hada kaya wani ne ya rasu? Ta girgiza masa kai Yace; To mai yasa kika za6i datse zamanki a gidana? Wani laifi na yi miki? Ta sake girgiza kai yace: Ki fada min damuwar ki ta dai yi shiru ta kasa cewa komai ya ja hannunta ya zaunar da ita akan gado yace;
Jirani ina zuwa. Ya fice zuwa dakin Hassu matarsa ta biyu. Tana zaune a dakinta tana zaune a dakinta tana karatun wani littafin Hausa yayi sallama ya shigo yace:
Hassu me ya faru a cikin gidan nan bayan ba ni nan? Ta tashi zaune daga kwancen da take akan doguwar kujera ta yatsina duska tace: Eh rigima ce ake yi wai Binta ce tace: Karima mayya ce, su suka lashe mata kurwar Mas'ud.
Yace Subhanallahi. Sai ya mike tsaye ya nufi dakin Binta. Kwance take akan gado yace. Binta kin kyauta shi dai jaki duk yadda aka yi da shi sai yaci kara. Ta yunkura ta tashi zaune fuskarta a daure tace: Kana nufin ni ce jaka?
Yace Eh ai abin da kika yi ko jakar ma ba zata yi ba. Banda jahilci da duhun kai ta ya Allah ya amshi ran Mas'ud zaki ce Karima mayya ce sun lashe miki da? To bari ki ji wallahi na gaji da munanan halayenki baki isa ki ja min surutu da bakin jini ga al'ummar gari ba.
Ta watsa mishi wani mugun kallo tace:
Dole ka zoi ka yi ta yi min hargowa tunda an ta6a 'yar gwal mowar mata. Karya ake mata ba mayyar ba ce? Idan kai ba ka sani ba ni na samo cikakken tarihinta karima mayya ce ita ta lashe mijinta haka wata mata daga ta tsarga hannun 'yarta ta lashe ta saboda muguwar maita, don bakin cikin zata yi mata lahani a jininta, sannan ta lashe Mas'ud. Sai a hana ni fada? To na fada karima mayya ce a yi yadda za ayi da ni....'
Ba tasan ya aka yi ba sai dai ganin wasu taurari ta yi suna walainiya a cikin idanunta sakamakon kyakkyawan marin da Alh jamilu ya dauke ta da shi. Yana huci ya cigaa da cewa;
Maza ki fice min daga gida, zama da ke annoba ne har kullum ba za a ta6a jin alkhairi a bakin ki ba dai sharri. Ba tayi mamaki ba domin ta lura mijin nata ya zauce akan wannan afiruwar matar tasa. Ita kam ba inda zata kuma ba zata ta6a barin jinin danta ya tafi a banza ba.
Alh jamilu ya cigaba da cewa; Kuma wallahi kika sake furta maganar nan ga wani sai na sa an kulle ki, mutumiyar banza marar hankali. Cikin dakewa tace da shi:
Idan kasa an daure ni ka jefa mukullin cikin kogin maliya zama daram kuma a cikin gidan nan ban ga 'yar isakar macen da ta isa ta fitar dani ba.
Yaja wani dogon tsaki ya fice daga dakin ya barta tana kananan maganganu.
Ya tarar da Haj karima har lokacim kuka ta ke. Ya zauna kusa da ita ya soma share mata hawayenta yace:
Don Allah ki yi hakuri karima an fada mim duk abin da ya faru.
Ta yi shiru bata tanka ba. Zaman gidansa ya fice mata a rai saboda tunda ta shigo gidan ba ta da kwanciyar hankali. Yau dai hakurinta ya kai gaci a ganinta gwara ta kauce masa ko matansa sa samu sarar tunda dama tunda ta zo gidan ba ta nasa ko kwai ba bare dan adam. MAITA? Ai kalmar ta yi mata nauyi ba ko a kai ba. A'a a dukkan sassan jiki da ma rayuwarta gaba daya. Ta matse hawaye tace dashi; Alhaji ka yi hakuri amma na hakura da zama gidanka ka yi hakuri. Ya tsura mata ido cikin tsananin tausayi yace: A'a karima kar mu yi haka dake. Ki fahimce ni, ni nake aurenki , zamana kike..... Karo na farko yana magana ta katse masa hanzari tunda take da shi. Zamanka nake amma kuma zaman matanka tunda suna juya ni kamar waina a tanda. Yace: Hakane ban ce kin yi karya ba amma ki yi hakuri komai yazo karshe tunda na sauwakewa Binta. Dama ita ce matsalar gidana don ta Hassu za a iya zama da ita. Da sauri karima ta mike tsaye maganarshi ta dakar mata zuciya sosai ta soma girgiza kai. A'a Alhaji ka maido Binta, tare na tarar da ku ni na fi dacewa da wannan hukuncin domin zuwana ne ke neman hargitsa zamanku. Yace Ba zuwanki bane karima dama can Binta 'yar butsu ce hakuri kawai nake da ita. Karima tace Yanzu din ma hakurin zaka ci gaba da ita. Yace Hakurina ya kare. Tace Ni ma nawa ya kare don haka ina so ka maido matarka. Ya cika da mamakin yadda

Please Login or Register in order to submit comment