Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

can 6angaren aka ce:
ABUBAKAR IBN KHADDAB ne, an kira wayata ba ni kusa da wayar na gani kamar a kasar Najeriya ne, wa ke magana? Uncle hamza ya zabura saboda shi sam duk yau bai kira wata lamba ba idan ba yanzu da ya kira Yakub ba. Yana girgiza kai kamar Abubukar din na ganinsa yace:
A'a gaskiya ban kiraka ba, domin duk yinin yau wayata a kashe ta ke. Abubakar ibn khaddab yana dariya ta cikin wayar yace: Amma na yi mamaki, saboda na dauka ko su Yusufa ne suke son magaba da ni. Don Allah kada ka zolaye ni ka fada min waye?
Uncle hamza ya kara cika da tsananin mamaki yace: Abin da na fada haka ya ke, ni ban sanka ba. Babu wani da na sani a wata kasa da ta tsallake Najeriya bare na zolaye ka.:
Abubakar yace: Ni ma cikin makon nan zan dawo Najeriyar idan ma ka 6oye min shike nan na gode. Ka gaishe min da su Alh BABBA.
Yana gama fadar haka wayar ta katse, tsoro da fargaba suka cika zuciyar uncle hamza tabbas duk yadda aka yi akwai SANAYYA tsakaninsa da wanda ya kira kansa da Abubukar. Idan ya yi la'akari da maganarsa ta karshe, wai ya gaishe masa da ALH. BABBA.
Mahaifinsa shi suke kira da Alh Babba, idan haka ne akwai alakar, ta ina? Waye Abubakar ibn khaddab? Yaushe ya kira lambarsa?
Tambayoyin da suka damu kansa ke nan. Suka hautsina masa tunani ya rasa sukuni sat!
Washegarin ma bai samu kadaicewa da Shuhuda a makaranta ba, ana tashi ya neme ta ya rasa, ko motar da ake daukarta bai ga lokacin da ta tsaya har Shuhuda ta shiga ba, bayan tun kafin a tashi ya ke zubawa kofar ajin nasu idanu har ya soma hango dalibai na fitowa daga ajin suna tafiya bai ganota ba.
Wannan dalili ne ya sa shi yanke shawarar zuwa gidan su Shuhudan. Kamar yadda ya shirya zuwa gidan nasu haka ya dauki hanya yana tafe cike da tunanin abin da zuwan nashi zai haifar.
Yayin da ya isa gidan kafin ya tsaya a kofar gidan ya hango Yakub ya fito daga cikin gidan ga dukkan alamu wani guri za shi. Sai uncle hamza ya bishi yana yi masa hon, sai da suka koma can karshen lungun sannan Yakub ya tsaya, ya juyo yana duban uncle hamza da ke kokarin fitowa daga cikin mota.
Don Allah ka yi hakuri, wallahi ban san dani kake ba. Uncle hamza yace: Kada ka damu ab yini lafiya? Yakub yace: Kalau, jiya ina ta magana bana jinka.
Dif! Wuta ta daukewa uncle hamza ya rasa mai zai ce dashi. Yakub yace: Shi yasa nbake tunanin sauya layi saboda matsalar network da MTN suke fama da shi a kasar nan, kullum daga wannan matsala sai wannan matsala.
Kwanakin ba ya ma don wukakanci da mutum ya saka kudi sai su wafce masa, suka 6illo da wani tsari Magic number na yaudara.
Shi dai uncle hamza shiru kawai ya yi yana kallon Yakub da hakikance yana magana ba ya jinsa. Bayab shi yasan da ya kira lambar Yakub din ba shi ya samu ba, kuma ma ai kiransa aka yi bayan ya gama kira ba a dauka ba. Watakila gaskiyar Yakub din ne matsalar daga network ne, lambarshi ta shiga wayar wani daga kasar waje.
Yakub ya yi murmushi, tukunna yace: Hala mutumiyar taka ka biyo? Don tace min kwana biyu ba ku gaisa ba. Murmushin karfin hali uncle hamza ya kirkiro yana shafa kasumbarshi yace: Hakika an yi haka.
Yakub yace: Ai matsalar ba daga gare ta ba ne. Daga gida ne, an yi mata shamaki da kula saurayi, har sai ta kammala sakandire dinta don haka idan ka ga ba ta kulaka ba kada kaga laifinta.
Ina sauri zamuje taron matasan unguwa da muke yi duk karshen wata. Sai ga ni na biyu. Mun gode da kaunar da ka nunawa tsatsonmu. Ya karashe maganar yana kokarin barin gurin. Uncle Hamza ya yi saurin zura hannayensa cikin aljihu ya fiddo kudi yana cewa:
Ga wannan ka sha ruwa.
Yakub ya tsaya yana duban uncle hamza tare da kudin sannan yace:
Ayya na gode amma mu ba ma amfani da irin wadannan kudaden. Yana karashe fadar haka ya yi gaba abinsa.
Mamakin uncle hamza ya sake hauhawa, sam bai gamsu da maganganun yakub ba, me yasa su ba su amfani da irin wadannan kudaden bayan kuma a kasar Nijeria suke rayuwa? Lokaci daya maganar Shuhuda ta dawo masa a rai, lokacin da ya bukaci sanin gidan su.
" Gidan mu?.... Gidanmu da nisa.... Misra fa.... Akan wani keken doki nake zuwa.... Kullum fa na koma gida sai na suma, mamata ta yi ta kwara min ruwan sanyi, sannan nake farfadowa...."
Idan ya tattara maganganun Shuhuda da kuma maganganun da suka gudana tsakaninsa da yakub sun isa su zame masa hujja na cewar yana mu'amala da ALJANU a matsayin MUTANE.
Wani kunci da takaici suka lullu6e masa zuciya kawai ya rufawa kansa asiri ya rabu da lamarin Shuhuda ya sa wa kansa salama ya cire sonta daga ransa shine kawai abin da zai sama masa nutsuwa. Idan ba haka ba kuwa zai yiwa rayuwarsa BARA DA BANA, ma'ana ya hana zuciyarsa samun matar da zai rayu da ita akan son da yake wa Shuhuda, wanda a bayyane yake babu aure tsakanin jinsin mutane da aljannu.
Ko da ma ace zai iya auren aljana, ma'ana an halasta aure a tsakanin jinsin bil'adama da jinsin jinnu, to ba zai auri Shuhuda ba. Tunda bai san manufar da ta ke so da shi ba. Bai san me ye shirinta na kulle zuciyarsa da sonta ba.
a Hausa Book stories
MATAUl HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤13¤¤
Abubuwa da dama sun faru wanda sai yanzu ya samu kakkarfar hujja da zai saka Shuhuda a jinsin jinnu. Alh sada, shi ma ya kasance daga jinsin jinnu, an rike shi ne don kawar da tunaninsa ya aminta shuhuda mutum ce don ya aure ta a kaddamar da shirin da aka shirya.
Tana karatu a makarantar ne don an samu tabbacin zai shigo makarantar koyarwa. Ta ko'ina dai babu hanyar da za a layance masa yace Shuhuda mutum ce ba aljana ba! Idan an bar zuciya da tabo ba a yi mata magani ba. Lallai za a samu rudani. Komawa ubangiji a dukkan tsanani da rudani, ko ma jin dadi shi yake haifar da nagartacciyar rayuwa. A duba.
****** ****** *****
BABI NA SHIDA
ANA ZATON WUTA A MAKERA......
Tun daga wannan rana uncle hamza bai kara shiga shirgin shuhuda ba, sam ya nuna kamar bai san da wanzuwarta a cikin makarantar ba. Ko aiki ya ba su ya ga ta yi kokari ba ya nuna ya damu bare ya yaba mata kamar yadda yake yi a da.
Sai ma ya koma duk lokacin da zai shiga ajin nasu idanunsa rufe da bakin tabarau, wai duk don kada ta ga wallensa bare ta raina shi. Tunda ya gane aljana ce yta ke rayuwa acikin mutane.
Shi ba zai iya tona mata asiri ba, haka kuma ba zai kulata ba. Idan ma tana tunanin zata cimma wani buri ne a gare shi, to ta sha karya, ba zata ta6a samun wannan damar ba.
Idan ya tuna yadda ta dinga yi masa yawo da hankali, sai ya ji haushin kansa. Ai tuni ya kamata ace ya gane shuhudan aljana ce idan ba haka ba ta ya mutum zai ce bai san waye bil'adama ba, bai san shi wane irin jinsin halitta ba ne?
Ai daga ji ma kasan wata kullalliya ce kawai ake kullawa.
An murda an tufka murdaddun al'amura don jefa shi a cikin tarkon da ba zai iya fitar da kansa ba. To amma da yake shi Allah mai taimakon bawansa ne, duk da ratar dake tsakanin jinsin bil'adama da jinnu hakan bai hana yayewar yanar da aka dankara a idanuwansa ba. Ya gane ko wace ce ita.
Wannan ma abin godiya ne ga Allah da ya ni'imta shi da wannan ni'ima, tunda har ya kare shi daga kaidin jinnu. Ya sani ba hikimarsa ko kwarewarsa da dabarunsa ba ne ya ku6utar da shi ba. Illa wata BAIWA da HIKIMA ta Ubangiji.
Wannan hukunci da ya dauka ya dan rage masa zafin da yake hada wa kansa, yanzu sam ba ya irin wannan zaman na dogon tunanin ya ya lamarin shuhuda ya ke? Saboda yasan yadda aka yi masa alayen irin na mutan 6oye (Jinnu).
To kuma ga shi an yi walkiya ya ga komai, saura da me? Tabbas dole ne ya samu nutsuwa, a da kam ya susuce komai ya kunce masa, ba shi da wani tunani sai na yadda al'amuran shuhuda suke har wani kira yake kwalwa ce ta yi mata yawa. Ashe ba kwalwa ba ce tsabar rainin hankali ne da yaudara irin na shiryayyen lamarin da bai san dalilin shiryuwarsa ba.
WAYE UNCLE HAMZA?
""""""""""""""""""""""""""""""
HAMZA A. Babba shine asalin sunan nasa dan asalin jihar katsina a karamar hukumar Batsari. Mahaifina Alh Babba mai lakabin sunan Abdullahi sananne ne a fadin birnin katsina. Domin ma aikacin gwamnatin tarayyar birnin katsina ne.
Ya rike mukamai da dama a ganiyar kuruciyarsa kafin daga bisani ya ajiye aiki saboda girma da ya kamashi. Matansa hudu na aure, ko wacce kuma ta hayayyafa da shi. A takaice dai mutum ne mai yawan iyali saboda yana koyi da sunnar ma'aiki.
Yawan 'ya'yansa bai sa aka samu nakasu ga tarbiyyarsu ba, tsaye yake tsayin daka gurin kulawa da tarbiyyar yaran nasa.
Hamza yayi karatunsa na firamare a nan cikin kauyensu karare da ke cikin karamar hukumar Batsari. Da ya gama ya tafi Technical Mashi, inda ya fito da takardu masu kyau, bugun farko na Jamb dinsa ya samu 258point. Don haka bai samu matsala ba lokacin da ya nemi gurbin karatu a A.B.U ZARIA.
Tunda hamza ya fara karatunsa ba shi da wata matsala har ya kammala lokacin da ya dawo gida yana hutun jiran aiki.
Akawai wata yarinya zuwairiyyah diyar kanin mahaifinsa da ta so shi tun can baya, to amma sai aka samu akasi, zuwairiyya irin shagwa6a66un yaran nan ne, ba ta iya komai ba ga ta katuwar bagidajiya irin dai yaran nan da ake cewa: GIRMA YA RIGA WAYO.
Hakan ne ma ya sa koda ya nunawa mahaifinsa rashin amincewarsa ga lamarin ba su zafafafa ba, amma daya daga cikin kannen mahaifinsa mai suna Binta ta zafafa abin, wai ita don me zuwairiyya zata ce tana son hamza zai ce ba ya sonta. Kuma a biye masa? Wannan salon gur6ata zumunci ne.
Rigima aka yi sosai, dama can hamza ba ya shiri da Gwaggo binta, wata irin masifaffiyar mace ce, haka nan ta bushi iska ta zo gidan ma ta yi ta ruwan masifa.
Da yake Alh Babba mutum ne mai tsananin hakuri da son zumunci ba ya damuwa da halayyar 'yar uwarsa. Ba ma ita kadai ba duk cikin sauran 'yan uwansa shi daban yake bai dauki rayuwa da zafi ba.
Duk hutun da hamza yake dawowa yana zuwa gaishe da dangin mahaifinsa amma ba ya zuwa gidan Gwaggo binta saboda muguwar tsanar da ta yi masa tun yana yaro, har cewa take wai hamza kamar musaya aka yi aka ba wa Alh Babba shi, amma sam bai yi shige da tsatson gidansu ba.
Idan 'ya'yanta sun zo gidan, misali ace an yi katari lokacin hamza ya zo hutu ba ya kula su. Saboda yaran sam ba su da kunya wannan ya sake hura wutar kiyayyar Gwaggo binta da hamza.
A lokacin da yake aji uku a sakandire dinsa wani zuwa ziyarar dalibai da mahaifinsa ya je yake sanar masa dan Goggo Binta ya rasu, ko a kwalar rigarsa bai damu ba. Don haka da ya dawo hutun ma bai je yi mata gaisuwa ba.
Ana haka kuma auren Goggo binta ya mutu, tace: zata dawo gidan Alh BABBA kin amincewa ya yi. Don yasan zama da Binta tashin hankali ne ba karami ba. Sai dai gidan wani dan'uwan ta koma.
Ta yi zaman zawarci na shekaru hudu sannan ta yi aure. A lokacin hamza ya tafi ZARIA. Shi ma auren ba wani dadewa ta yi ba ta fito saboda rashin hakuri da munanan halayenta ba kowane namiji ne zai iya zama da irinsu Binta ba.
Ta koma zaman zawarci har hamza ya gamo karatunsa ya dawo ya fara aiki a nan cikin jahar katsina. A wata makaranta MARIAMA AJURI MEMORIAL SCHOOOL Goggon tasa ba ta yi aure ba.
Albashinsa na farko da na biyu zuwa na uku ya sayi tamfatsetsen filoti a nan cikin katsina unguwar kanada. Tafiya ta tafi ya gina gidansa ya sayi mota sai kuma maganar zuwairiyya ta kuma danno kai don har lokacin ba tayi aure ba.
A wannan karon an so fin karfinsa, to amma sai ya roki alfarma a makarantar da yake koyarwa a mayar da shi wani reshen, tunda makarantar ta kafu tana da rassa da dama a garuruwa daban-daban.
Yayi wannan hikimar ne don ya yiwa su zuwairiyya nisan zango. Idan aka ga ba ya kusa an gaji a bata wani mijin ta yi aure.
Da farko za6i aka ba shi cikin Kaduna, Jos da kuma Bauchi. Ya duba duk cikin wadannan garuruwan babu wanda ya kwanta masa a rai, ya dauki lokaci yana tunanin garin da zai za6a.
Kwatsam aka ce an turo shi Kano dama suna bukatar karin malamai. Ya yi farin ciki da hakan ko ba komai kano gari ne na cibiyar kasuwanci idan yaje kanon zai iya samun wani kasuwancin da zai yi ko ya saka hannun jari a wani kamfanin.
Hakan ko akayi, yana zuwa birnin kano ya fara aiki, a hankali kuma ya fada harkar kasuwanci ya ba wa wani abokinsa kudi masu yawa yana yi musu kasuwanci a nan kasuwar kwari.
A kuma makarantar ne ya hadu da ALJANA! Kamar yadda ya kira SHUHUDA.
WANNAN KE NAN!!!
****** ****** *****
Rashin kulawar da uncle hamza ba ya yiwa Shuhuda ya sama masa nutsuwa na gajeran lokaci ne kawai. Domin lokacin da su shuhuda suka shiga aji shida suna gab da soma jarabawa tsumin abin nan ya taso masa haikan. Ya dinga jin a duniya babu macen da yake son ya aura sama da Shuhuda.
Ta kowane 6angare jinta yake kainarta na yi masa yawa, duk kuwa da a lokacin ya fara tunanin ya komawa zuwairiyya. Saboda hakuri da juriyar jiran tsammanin da ta ke yi dominsa. Tunda har lokacin zuwairiyya ta ki aure ita a cewarta akwai ranar da mafarkinta zai zamo gaskiya. Wato ranar da hamza zai aure ta.
Da farko an so takura mata sai ta tsiro da karatu, tace lallai sai tayi karatu mai zurfi tukunna za su yi aure, wai haka uncle hamza ya sanar da mata, don haka aka zuba mata na mujiya(idanu).
To lokacin da uncle hamza ya daina kula shuhudan sai ya ji kamar ya komawa zuwairiyya saboda shi ma a lokacin Alh Babba ya soma korafin rashin aurensa. Allah ya sa bai yi saurin jefa kansa a ragaya ba sai kuma ga shi ya koma ruwa tsundum! Akan kaunar Shuhuda, yarinyar da yake da hujjojin kiranta Aljana.
Wannan shi ne kwan-gaba-kwan baya, ma'ana yasan abu amma ya kasa aminta da sanin sa. Hujjoji dai sun bayyana a gare shi Shuhuda aljana ce, ba ita kadai ba duk wani wanda ya ra6eta shi ma jinnu ne, to amma kuma ya kasa amincewa kin yin mu'amala da ita. Mu'amalat ma irin wadda yake sa ran zata zamo uwar 'ya'yansa.
Da zarar ya dora idonsa akanta wani irin abu ne yake ji yana fizgarsa, idan ya so sharewa sai ya ji idan ba tsura mata ido ya yi ba, ba zai samu sassauci ba. Don haka ba ya iya hassalawa kansa komai idan ba ya yi kokarin kawar da idonsa daga gare ta ba.
Hasalima gaba daya gangar jikinsa yake ji ta yi masa nauyi, tamkar an daura masa gungumemen dutse, sai dai kuma ya kasa tunkararta, domin a duk lokacin da ya dauki damarar zuwa inda take da maganganun soyayya sai ya dinga jin faduwar gaba.
Yanzu kam shuhuda ta gama rikita masa zuciya da kalbinsa, yanzu haka ma da yake zaune a falonsa, yana tunanin hanyar da zai soma bi domin sake bayyanar da soyayyarsa ga shuhuda.
Uncle hamza ya sauke doguwar ajiyar zuciya. Ya sa hannu ya dauki hankici ya goge gumin da ya jike shi sharkaf Ta kowane 6angare jinta yake kainarta na yi masa yawa, duk kuwa da a lokacin ya fara tunanin ya komawa zuwairiyya. Saboda hakuri da juriyar jiran tsammanin da ta ke yi dominsa. Tunda har lokacin zuwairiyya ta ki aure ita a cewarta akwai ranar da mafarkinta zai zamo gaskiya. Wato ranar da hamza zai aure ta.
Da farko an so takura mata sai ta tsiro da karatu, tace lallai sai tayi karatu mai zurfi tukunna za su yi aure, wai haka uncle hamza ya sanar da mata, don haka aka zuba mata na mujiya(idanu).
To lokacin da uncle hamza ya daina kula shuhudan sai ya ji kamar ya komawa zuwairiyya saboda shi ma a lokacin Alh Babba ya soma korafin rashin aurensa. Allah ya sa bai yi saurin jefa kansa a ragaya ba sai kuma ga shi ya koma ruwa tsundum! Akan kaunar Shuhuda, yarinyar da yake da hujjojin kiranta Aljana.
Wannan shi ne kwan-gaba-kwan baya, ma'ana yasan abu amma ya kasa aminta da sanin sa. Hujjoji dai sun bayyana a gare shi Shuhuda aljana ce, ba ita kadai ba duk wani wanda ya ra6eta shi ma jinnu ne, to amma kuma ya kasa amincewa kin yin mu'amala da ita. Mu'amalat ma irin wadda yake sa ran zata zamo uwar 'ya'yansa.
Da zarar ya dora idonsa akanta wani irin abu ne yake ji yana fizgarsa, idan ya so sharewa sai ya ji idan ba tsura mata ido ya yi ba, ba zai samu sassauci ba. Don haka ba ya iya hassalawa kansa komai idan ba ya yi kokarin kawar da idonsa daga gare ta ba.
Hasalima gaba daya gangar jikinsa yake ji ta yi masa nauyi, tamkar an daura masa gungumemen dutse, sai dai kuma ya kasa tunkararta, domin a duk lokacin da ya dauki damarar zuwa inda take da maganganun soyayya sai ya dinga jin faduwar gaba.
Yanzu kam shuhuda ta gama rikita masa zuciya da kalbinsa, yanzu haka ma da yake zaune a falonsa, yana tunanin hanyar da zai soma bi domin sake bayyanar da soyayyarsa ga shuhuda.
Uncle hamza ya sauke doguwar ajiyar zuciya. Ya sa hannu ya dauki hankici ya goge gumin da ya jike shi sharkaf Zuciyarsa ta jagule, yana son furtawa yana tsoron abin da zai biyo baya. Shin zai amince ya sake saka rayuwarsa a tarkon aljana? So wani irin makahon abu ne, duhu ne da shi wanda yake makantar da zuciya gami da idanu tsinkaye da tarin kalubale.
Idan haka ne so ya taka muhimmin rawa ga uncle hamza tunda ya hana ganin duhun son da zai fada.
Cikin rashin walwala ya mike tsaye ya shiga bandaki ya yi wanka, sannan ya dawo falon, ya dauki wayarsa yaga yana da kiran da aka rasa(missed call) guda sha uku, ya duba duk lamba daya ne aka kirashi da ita. Kuma babu suna ma'ana bakuwar lamba (New number) ce.
Sannan yana da rubutaccen sako guda biyu baki wanda bai karanta ba. Ya buda daya daga ciki ya soma karantawa kamar haka:-
" Wata rana mai dumbin tarihi wadda ta kasance LITININ an yi kullaliya mai kulle kwalwa da tunani. Ranar litinin an rasa an kuma samu . Ranar litinin anyi katari da wani shamaki, bayan wasu al'amura masu murdiya da murde kwalwa. Shin mai yasa wannan rana ta kafu da murdaddun abubuwa? Tambayar ke nan!"
kuma a zahiri karshen sakon ke nan. Yanayin uncle hamza ya bayyanar da matsananciyar damuwa, rudani gami da razana. Bai san ina sakon ya sa a gaba ba, bai san wanda ya turo sakon ba, bai san me yasa aka turo sakon gare shi ba......
Da sauri ya buda dayan sakon don karasa tantance abin rudanin , shin shi aka aikowa ko kuwa dai halin network ne kamar yadda ya dauki lambar Najeriya ya kaita Misra?
" Rayuka cikin kunci ba karamin tashin hankali ba ne, ace dan Adam ya rayu a gurbin da ba wanda ya sani anbin a tausaya masa ne. Shi yasa ta ke ba ni tausayi, nakan ji alhini game da lamarinta. Amma babu komai akwai Allah, shi ne maganin komai. Amma zaluncin ya yi yawa....."
Iya rudewa uncle hamza ya shiga, ya rasa ma yadda zai fassara wannan cukurkudadden al'amari, hakika ko tantama babu halin network ne. Amma saboda ya fita daga wasu-wasin da yake ciki, sai ya kira lambar.
a Hausa Book stories
MATAUl HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤13¤¤
Abubuwa da dama sun faru wanda sai yanzu ya samu kakkarfar hujja da zai saka Shuhuda a jinsin jinnu. Alh sada, shi ma ya kasance daga jinsin jinnu, an rike shi ne don kawar da tunaninsa ya aminta shuhuda mutum ce don ya aure ta a kaddamar da shirin da aka shirya.
Tana karatu a makarantar ne don an samu tabbacin zai shigo makarantar koyarwa. Ta ko'ina dai babu hanyar da za a layance masa yace Shuhuda mutum ce ba aljana ba! Idan an bar zuciya da tabo ba a yi mata magani ba. Lallai za a samu rudani. Komawa ubangiji a dukkan tsanani da rudani, ko ma jin dadi shi yake haifar da nagartacciyar rayuwa. A duba.
****** ****** *****
BABI NA SHIDA
ANA ZATON WUTA A MAKERA......
Tun daga wannan rana uncle hamza bai kara shiga shirgin shuhuda ba, sam ya nuna kamar bai san da wanzuwarta a cikin makarantar ba. Ko aiki ya ba su ya ga ta yi kokari ba ya nuna ya damu bare ya yaba mata kamar yadda yake yi a da.
Sai ma ya koma duk lokacin da zai shiga ajin nasu idanunsa rufe da bakin tabarau, wai duk don kada ta ga wallensa bare ta raina shi. Tunda ya gane aljana ce yta ke rayuwa acikin mutane.
Shi ba zai iya tona mata asiri ba, haka kuma ba zai kulata ba. Idan ma tana tunanin zata cimma wani buri ne a gare shi, to ta sha karya, ba zata ta6a samun wannan damar ba.
Idan ya tuna yadda ta dinga yi masa yawo da hankali, sai ya ji haushin kansa. Ai tuni ya kamata ace ya gane shuhudan aljana ce idan ba haka ba ta ya mutum zai ce bai san waye bil'adama ba, bai san shi wane irin jinsin halitta ba ne?
Ai daga ji ma kasan wata kullalliya ce kawai ake kullawa.
An murda an tufka murdaddun al'amura don jefa shi a cikin tarkon da ba zai iya fitar da kansa ba. To amma da yake shi Allah mai taimakon bawansa ne, duk da ratar dake tsakanin jinsin bil'adama da jinnu hakan bai hana yayewar yanar da aka dankara a idanuwansa ba. Ya gane ko wace ce ita.
Wannan ma abin godiya ne ga Allah da ya ni'imta shi da wannan ni'ima, tunda har ya kare shi daga kaidin jinnu. Ya sani ba hikimarsa ko kwarewarsa da dabarunsa ba ne ya ku6utar da shi ba. Illa wata BAIWA da HIKIMA ta Ubangiji.
Wannan hukunci da ya dauka ya dan rage masa zafin da yake hada wa kansa, yanzu sam ba ya irin wannan zaman na dogon tunanin ya ya lamarin shuhuda ya ke? Saboda yasan yadda aka yi masa alayen irin na mutan 6oye (Jinnu).
To kuma ga shi an yi walkiya ya ga komai, saura da me? Tabbas dole ne ya samu nutsuwa, a da kam ya susuce komai ya kunce masa, ba shi da wani tunani sai na yadda al'amuran shuhuda suke har wani kira yake kwalwa ce ta yi mata yawa. Ashe ba kwalwa ba ce tsabar rainin hankali ne da yaudara irin na shiryayyen lamarin da bai san dalilin shiryuwarsa ba.
WAYE UNCLE HAMZA?
""""""""""""""""""""""""""""""
HAMZA A. Babba shine asalin sunan nasa dan asalin jihar katsina a karamar hukumar Batsari. Mahaifina Alh Babba mai lakabin sunan Abdullahi sananne ne a fadin birnin katsina. Domin ma aikacin gwamnatin tarayyar birnin katsina ne.
Ya rike mukamai da dama a ganiyar kuruciyarsa kafin daga bisani ya ajiye aiki saboda girma da ya kamashi. Matansa hudu na aure, ko wacce kuma ta hayayyafa da shi. A takaice dai mutum ne mai yawan iyali saboda yana koyi da sunnar ma'aiki.
Yawan 'ya'yansa bai sa aka samu nakasu ga tarbiyyarsu ba, tsaye yake tsayin daka gurin kulawa da tarbiyyar yaran nasa.
Hamza yayi karatunsa na firamare a nan cikin kauyensu karare da ke cikin karamar hukumar Batsari. Da ya gama ya tafi Technical Mashi, inda ya fito da takardu masu kyau, bugun farko na Jamb dinsa ya

Please Login or Register in order to submit comment