Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi, bai kamata shi ya ki aminta da kansa ba. Yana kallo suka ja mota suka tafi suna daga masa hannu, shi ma yana daga musu nasa hannun. Har yanzu dai kwakwalwarsa ba ta gama wartsakewa da yadda lamarin ya gudana a tsakaninsu ba. A yadda dai suka nuna masa su din wadansu mutane ne na daban wadanda ba su da alaka da wadancan da yake hasashen su ne. Abu daya ne ya fi aminta da shi, wannan Shuhudar ko tantama babu Shuhuda Ibn Khaddab ce, amma ta ya ta ke auren dan uwanta na jini? Ko kuwa zakin soyayya ce ta sanya ta alakanta sunanata da sunan mahaifin mijinta (surukinta), ko shi mijin nata ya alakanta nasa sunan da sunan mahaifin matarsa (surukinsa)? Lamarin dai akwai matukar rikitarwa da juyar da hankali har ma mutum ya soma lalubar hanyar WARWARA!
An samu tsayin makonni biyu da tafiyar su Abubakar Kaduna kamar yadda suka sanar da Isah, a tsugin babu wata damuwa da ke tare da Isah, ya kawar da kai da kokarin cusa harkokin ofis a cikin ransa a kowanne lokaci don samawa kansa zaman lafiya da nutsuwar zuciya. Yau ya taso aiki da wuri, ya kuma iso gidan nasaa da wuri. Ya fito harabar gadan yana shan iska, haka kawai zuciyarsa ta ayyana masa ya je gidan su Abubakar don kewaya. Bai yi kasa a gwiwa ba kuwa ya tunkari gidan, ya kewaye shi tsaf ya ga komai lahiya, tukunna ya koma gidansa ya dauko makulli ya zo ya bude gidan.yan zura kafarsa cikin falon gidan yayi katari da wata farar takarda, mai dauke da rubutu. Ya durkusa tare da kai hannu ya dauka. Abu na farko da ya fara gani an rubuta shi ne:-
"BUDADDIYAR WASIKA
Daga Shuhuda Ibn Khaddab
Zuwa ga Isah Sada Rabi'u.".
.
Gabansa ya yi wani irin yankewa ya fadi, ya shiga matsanancin rudani, anya kuwa sunansa ne a jikin wasikar? Idan dominsa aka rubutata me yasa ba a damkata a hannunsa ba? Me ma wasikar ta kunsa wanda har aka sanya mata suna da "budaddiyr wasika"? Ya kalli rubutun da kyau kananan rubutu ne matuka wanda kana gani ka san da biro mai karamin kai aka yi rubutun,kuma falle biyu kowanne gaba da baya an cika shi. Cab! Aiki ja, sai ya soma dube-dube cikin falon. Shirye yake da manyan kujeru sabanin nasa kala ce kawai, amma yanayin tsarinsu iri daya ne. Sannan akwai kayan kallo nau'in duk da ke da akwai a nasa gidan, sai dan karamin firij daga can gefen kusuruwar yamma. Center table a gaban kujerun. Ya jijuna kai, sannan ya nemi daya daga cikin kujerun ya zauna ya tsurawa takardar idanu, tare da soma karanta abin da ta kunsa a sarari.....
.
.
BABI NA GOMA SHA HUDU
Budaddiyar Wasika
"Na san lokacin da zaka sami wannan wasika tawa hankalinka zai tashi, ranka zai dagule, zuciyarka zata shiga kissama maka abubuwa da dama. Misali, me yasa na zabi rubuta maka abin da nake son sanar da kai a wasika sabanin na same ka kai tsaye na yi maka maganar da nake son yi maka? To akwai dalili mai karfi, ida kuwa aka ce dalili ana nufin abu mai girma da muhimmanci. Dalilin kuwa shi ne, ba zamu samu isasshen lokaci ba, tunda nasan idan na fada maka maganganun zaka so na amsa wadansu tambayoyi daga gareka.
Ture wannan gefe daya, mu dora akan makasudin wasikar, don sji ne abu mai muhimmanci a gare ka da gare ni. Wasu matsaloli sun faru da tsatsonku wadanda suka rudar da tunanin duk wanda yasan kanwarka Shuhuda. Musamman hasashe da mafi yawancin ku suke yi na cewar, ALJANA ce, ko kuma MAHAUKACIYA ce! A cikin jinsin bil'adama akwai wadanda Allah ya horewa kaifiyya gami da yakana ta fahimtar abubuwa da dama. Akwai kuma wadanda a rayuwarsu MATA UL HAYAT (Jin dadin rayuwa ko ince kyale kyalen rayuwa) ke rudarsu har yasa su assasa wani gagarumin laifi wanda zai buwayi al'umma ba tare da tsinkaye da sakamako ba. Baya da haka akwai wadanda laifin wasu ke shafar wasu ba tare da su suka aikata laifin ba. A cikin wani boyayyen sirri ne kadai za a iya fahimtar badinin Shuhuda, har a iya kawo tallafin samun jin dadi da nutsuwar zuciya a gareta.
.
(Allah Sarki Shuhuda)
Sadin Mama.
.
Yi hakuri Isah, na rasa hanyar da ya dace na yi mak maganganun da nake son sanar da kai, illa wannan da nake ganin zata fi cancanta. Sai dai idan ka bini sannu a hankali ne kadai zai sa ka fahimtar, idan kuwa ka rudar da tunaninka ba zaka tab fahimtar tawa ba. Shuhuda tana cikin wani hali na rashi tun wani lakaci da ya shude, don ko lojacinda muka yi karatu da ita a makaranta ba ta da nutsuwa, awa biyu ta ke da hankali, idan hankalinta ya gushe kahin ta dawo dai-dai sai ta samu awa biyu, ke nan gaba daya rayuwarta ta makaranta yini cur tan yinsu na awanni uku da hankali, wanda in bacin da Allah Ya sa ita din mai kaifin kwalwa ce babu inda iliminta zai kai. Kada ka yi mamaki akan duk abin da nake zayyana maka, domin nasan sirrikan Shuhuda da dama wanda babu wani mahaluki da ya sani.
Ba Shuhuda kanwarka kadai ba, idan ba ka manta ba a haduwar mu Misra na ce maka nasan adadin Shuhuda da ke da akwai a birnin Kano ciki da wajenta, saboda bincike na mai sunana. A haduwarmu da kai Misra na ji dadin samunka da saukin kai, har na yi tunanin kai ne mutumin da DUHu zai yaye ta sanadinsa, sai aka samu akasin haka.
Munhadu da kai a birnin Katsina na nuna maka ban sanka ba, ba wai don ban gane ka din ba ne, a'a saboda wani dalili wanda idan da a lokacin na bayyana maka kaina Shuhuda zata Shiga rudani matsananci, watakila ma har numfashinta zai iya fita daga gangar jikinta. Ka ga kuwa amatsayina na musulma bai dace na yi abin da zan firgita dan uwana Musulmu har ya rasa ransa ta sanadina ba. Shuhuda ba tasa na je Misra ba, ba tsan kuma ina zaman aure a garin nan ibadan ba, hasalima akwai abubuwa da yawa da suka shafe ni wanda ita ba ta sani ba.
Amma duk wani motsi nata na sani, nasan da a gabanka nake zaka tambaye ni ta ya na sani?
Kamar dai yadda na fada maka a Misra na kasance mai zurfin bincike akan mai sunana, duka da wannan bai isa ya zamo hujja a gareka ba, illa kawai ka share duk yadda zuciyarka ta kissama maka game da yadda aka yi na sani ka dauke shi a hakan. Maanufar dai itace ka fahimci RUFAFFEN SIRRIN da na ke so ka gane. Lokacin da Shuhuda ta shiga aji hudu a makarantar sakandare an yi wani zama na sirri aka shirya wani shiryayyen sirri mai MURDADDIYA da daure kai.
Matsayi mai girma ya wanzu a gare ta, ta kuma zama hazika a wani bangare bisa wani boyayyen sirri kamar yadda wasu rayuka suka shude bisa boyayyen sirri. Abin tambayar anan shi ne, wannan wane irin boyayyen sirri ne haka? To sirrin yana tattre da sirrantaccen sirri kwatakwacin sirrin haduwarmu. Kwatankwacin sirrin tsotsar hannun da Shuhuda ta ke yi. Kwatankwacin sirrin fitar ruwan nono a jikin Shuhuda sabanin jini. Kwatankwacin wani abu mai kama da almara da ya faru a tsakaninku bisa wani boyayyen sirri. Isah zan so matka ka saita kwalwarka da tunaninka wajen fahimtar maganganuna duk da dai kai tsaye ban fito fili na sanar maka ba, gudun dai abin da na fada maka, 'MATSAYINA NA MUSULMA bai dace nayi wani abu da zai razana dan uwana musulmi ba har ya rasa numfashinsa".
Idan aka ambaci kalmar SILA tana nufin SANADI, Shi kuma sanadi yana nufin faruwar abu ta dalilinta wani......
(Shin WAYE MUSABBABI na padawar Shuhuda cikin wannan boyayyen lamari?) Ku biyo ni dan jin karshen BUDADDIYAR WASIKA. Sadin Mama.
Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
27
.
CI GABAN BUDADDIYAR WASIKA………………
Zan iya ce maka dukkan rudadden al’amarin day a rudaka da ma duk wanda yasan Shuhuda ya faru ne sanadin ABOKI, shi ya sa ake so mutum yasan abokan da zai yi mu’amala da su, koda yake faruwar sanadin ma rubutacce ne da ga Lillahi, duk hikima da wayon zillewa ba zasu yi tasiri ba, duk gudun Rago ba zai hana a dora masa wuka don yin layya da shi ba. Hamza yana son Shuhuda har cikin ransa, sai dai ba shi da kwanjin zamowa miji a gareta, idan aka yi la’akari da kasancewarsa akan matsalolinta. Haka kai ma akwai kasawarka, shin wa ya dace da wannan muhallinta? Amsar it ace ZABIN ALLAH domin Shi Yake da SANIN GOBE. Daga karshe zan diga DANBA akan tunatarwa. ‘a duk lokacin da aka manta da mayar da lamari ga Ubangiji akwai tarin da na sani.Addu’a aba ce ga duk musulmi ya dimanci yenta ba wai sai wata matsala ta faru ba. Sannan akwai cutuka wadanda likita bai isa gano makasudin samuwarsu ba bare yasan magungunansu. Shawarar d azan baka, ka kasance mai yin addu’a ba dare ba rana, ko me kake ka yawaita neman tsari daga:-
MIYAGUN MUTANE
MIYAGUN SHAIDANU.
Allah Ya taimakeka ka tsallake siradin da kake a kai, Allah Ya taimakeka ka zamo mutum mai himma wajen SADAUKARWAR da rayuwa akan tafarkin addinin musulnci. Akwai zobenka da yake hannuna wanda ka ba wa Shuhuda lokacin da ka dawo daga Senegal, watakila kaga irinsa a yatsana a haduwarmu burnin Katsina? To na hannunta ma ya dawo hannuna bias wani boyayyen sirri. Wassala! Sai Allah Ya yi mana dawowa idan da rabon ganawa!
Tun kafin ya karasa karanta wannan zungureriyar takarda mai taken ‘Budaddiyar wasika’ gumi ya jike Isah, ya yi sharkaf, idanunsa sun sauya launi, zuciyarsa ta jagule.
Bat a yi karya ba kamar yadda ta fada, dole ne ya shiga rudani akan wannan takardar, ba ma shi kadai ba dak wanda zai karanta takardar dole ne ya shiga rudani. Idan zai iya tace abubuwan day a karanta a cikin wasikar to abu na farko da zai kissima, wannan wani labari ne day a fito daga hannun AJJANA SHUHUDA IBN KHADDAB, bias hujjojin sanin wasu abubuwa da ta ked a su, wanda ya fi karfin sanin bil’adama, koda ace ma wani bil’adama zai zansu, to sai dai ya kasance mai yawan shekaru, kuma wanda yake da alaka da wanda abin yake faruwa akansa. Ita kuwa wannan a yadda ta ke din nan ba zata wuce shekaru ashirin ba, idan ma ta kai ken an. Kuma ba ta zaune da Shuhuda koda yaushe bayan makaranta da ta hada su, bare tasan komai na rayuwarta wanda ita kuma Shuhudan ba tasan wasu abubuwa da suka shafeta ba. Isah mutum ne mai kwanji, amma bai ga alamar yana da kwanjin da zai iya jure wannan sha’ani ba.
Nadama ta zo masa a karo na biyu na dawowars kasarsa ta haihuwa, wato Najeria tunda tun lokacin day a dawo bai samu nutsuwar zuciya ba. Abin day a lura da shi matsawar yana bukatar zaman lafiya da fita daga tarin rudanin da yake ciki game da wannan murdaddiyar al’amari to kawai ya yi kaura da Najeria ya koma Misra ya yi aiki a karkashin kamfanin da malaminsa Dr. Outhman Ibn Abdulfatah ya so ya yi tun da farko.
Sai dai inda yake hangen matsalar bay a wuce ta bangaren mahaifinsa, tunda a farko ma ya so hakan amma mahaifin nasa ya kiya masa, yanzu day a fara aiki a Nigeri zai kuwa yiwu ya amince masa aiki a Misra? Shirme, hauka gami da tsabar rainin hankali shi ne muraran abin da yake ganin su Shuhuda na yi masa. Tunda yasan kauracewa zamansa Nigeria ba abu ne mai yiyuwaba, to kawai ya dauki matakin fatattakar duk wani lamari da zai sada shi da Shuhuda tundabai ga wani abun anfanu a hakan ba. Ya ja wani dogon tsaki yana yarfe gumin day a jike shi, tukunna ya mike tsaye ya tunkari kafar fita daga falon.
Tsau! Yaji wani abu ya ratsa ta dukkan sassan jikinsa, kamar tsoro n eke dirar masa.
Cak! Ya ja tunga ya tsaya tare da waigawa da sauri, ya duba ko’ina bai ga wani abun da zai tsoratar da shi ba, illa dai haka nan ya samu jininsa da tsinkewa ya yi tsururu tamkar ruwa. Ya dau mintina biyu a haka, sai ya ji kamar zuciyarsa na yin shakulaton bangaro (sharewa) da lamarin Shuhuda, musamman la’akari da abinda budaddiyar wasika ta kunsa. Sai dai a wani bangaren yana karfafawa kansa sharewa da Shuhudan, domin budaddiyar wasika babu abin da ta kuma sanya shi illa wani firgici. Sam bai hango wata hanya da zai shawo kan matsalar rudanin da yake ciki ba. Da azamarsa ya sake ‘yunkurin ficcewa daga falon, amma kamar an daure shi, domin ji ya yi gaba daya babu wata gaba da ke iya motsi a jikinsa. Hatta kansa ya kasa juyawa zuwa bayansa, illa gabansa kawai da yake kallo. A bayan nasa kuwa yana jiyo kamar ana motsi, kamar ma taku yake jiyowa. Da sauri ya ambaci…..
‘INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN, LA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAH……’
Kafin ya karasa ma tuni ya ji wani irin kuzari ya zo masa, ya kuma fice daga falon yana mai takaicin shigowarsa hurumin dab a nasa ba. Cikin rudanin ya yi saurin rufe gidan da makulli ya koma gidansa, ya zube a falo tare da rafka tagumi.
Hakika duk abin day a faru da shi a cikin gidan su Abubakar lamari ne na sihiri, ko kuma gaba daya ma y ace jinnu idan haka ne kuwa daga Shuhuda Ibn Khaddab har mijinnata Abubakar Ibn Khaddab duk jinnu ne? idan hasashensa ya zama gaskiya ta ya suka samu wannan gida da suke ciki? A matsayinsu na jinnu zasu iya zama a gidan, to amma ina asalin mutanen da ke zaune a gidan? Ko kuwa sun z one a sigar mutane an dauke su aiki har aka bas u muhalli kamar yadda shi ma kamfanin da yake aiki suka yi masa wannan gatanci? Hakika akwai boyayyen al’amari mai matukar rudani da daure zuciyar tunanin duk mai tunani.
(nima n ace, Isah ba kasan dawn garin ba, Shuhuda Ibn Khaddab ta baka haske sosai ta yadda zaka warware lamarin cikin saukakar hanya, (sadin mama)).
BABI NA GOMA SHA BIYAR
TARIHI YA MAIMAITA KANSA
An wayi gari yau laraba, Inna Yaduwa na kishingide a falo idanunta a rufe, ta kara ‘yar karamar radiyo (kachbo) a kunnenta tan a sauraren wani shiri ‘Ku karkade kunnuwanku’ wanda Aisha Bello Mahmud ke gabatarwa a tashar FREEDOM RADIO wanda suke karanta wani littafi mai suna MACE BAIWA na jinjirar marubuciya mai tasowa Naja’atu Haruna Sale.
Tana jin dadi labarin, saboda yadda aka dauko rayuwar da mata suke a karkara aka rubuta, duk wasu tarin matsalolin mata sun kunshi wannan hadaden labari. Da yake yau din it ace rana ta farko da aka soma karanta littafin, sai Inna Yaduwa ta ke ji, ina ma kada lokacin da aka dibarwa shirin ya cika ba tare da an kamala karanta littafin ba?
Kusan da gudu-gudu, sauri-sauri Shuhuda ta fito daga daki da nufin isa bandaki, sai dai kafin ta isa tuni ta soma kyelaya amai, wanda yunkuri da karar sautin zubar aman ne ya farkar da Inna Yaduwa abin da ke faruwa, hart a hanzarta mikewa zaune daga kishingiden da ta ke tana ambaton.
“lafiya”
Amma Shuhuda shiru ta kasa Magana illa ci gaba da kyelaya aman da take yi kamar zata amayar da duk abin da ke cikinta. Hankalin Inna Yaduwa ya tashi matuka, ta isa gaban Shuhuda a rude tana tambayarta abin day a same ta tare da tattaba jikinta. Sai da kyar aman ya tsagaita, amma duk ta galabaita ta fita hayyacinta. Inna Yaduwa ta kamata zuwa bandaki, tab a ta ruwa ta kurkure bakinta, sannan suka dawo falon, Shuhuda ta kwanta akan doguwar kujera, yayin da Inna Yaduwa ta goge gurin da aman ya bata ta dubi Shuhuda cikin tausayawa, t ace “sannu” bat a amsa ba, Inna Yaduwa ta mike ta nufi kan dan karamin firij da wayarta ke ajiye a kai, ta dauko ta duba lambar Alh. Sada wadda ta sanya wa alamar mota, don duk wanda ke cikin wayar akwai alamar da ta ke gane lambarsa da ita. Kasancewar ba ilimin book ta yi ba. Tana kiran wayar yayin da take dawowa don zaunawa kan kujera. Ya dauki wayar cikin ladabi ya isar da sakon gaisuwarsa tukunna t ace masa. ”Shuhuda ce ba lafiya, tana ta amai, idan kana da hali ka zo a kai ta asibiti” y ace “ina direban gidan ne?” t ace, “sun fita da Alhaji”, y ace, “to ni yanzu na yi nisa sosai, amma bari na turo Nuruddeen sai ya kai ku” t ace, “ba damuwa”, Ta kasha wayar tare da tsurawa Shuhuda idanu cike da jin tausayinta. Ba jima sosai ba Nuraddeen ya shigo gidan yana kada makullin mota, fuskarsa a sake y ace,”yar tsohuwa ke bakin cikin shan gumba zaki yi mana, an ce na zo na kai ki asibiti?” ya fadi maganarsa cikin sigar wasa na kaka da jika, fuskarta a daure t ace,” da yake ba ka da idanu shi yasa ka gaza gane ba nice ba ni da lafiya ba…………. Yayarka ce Shuhuda gat a nan bat a da lafiya, it ace za mu kai asibiti”. Sai lokacin ya lura da Shuhuda da ke kwance akan doguwar kujera y ace,”A’a Aunty Shuhuda me ya same ki”? Inna Yaduwa t ace masa. “ka ga muje asibitin tunda ka ganta a kwance ai kasan akwai matsala”. Ta fada tana kokarin tallafa Shuhuda, suka fita su ukun zuwa inda ya yi fakin, ya bude musu gidan baya ta saka Shuhuda. Nuraddeen ya ja motar cikin azama suka isa ZAHTY MEMORIAL HOSPITAL, aka shiga da ita emergency, Tashin farko likitan day a dubata ya bukaci fitsarinta, aka shiga da ita wani ban daki tayi, sannan ya basu magungunan taimakon gaggawa tare da cewa a dawo anjima a karbi sakamako. Bayan sun dawo daga asibitin gidan ya dinga daukar harami, nan da nan ya cika da ‘yan dubiya. Karfe hudu da rabi Alh. Ahmad da Nuruddeen suka je karbo sakamako. Likitan ya tsayar da su kafin ya basu sakamakon, ya dubi Alh. Ahmad fuskarsa cike da fara’a y ace. “Alhaji ina taya ku murna, da fatan Allah ya raba su lafiya. Amma zan so nab a ku sahwara, duk macen da take da farkon ciki kafin ya yi kwari ana bukatar ta rage yin ayyukan da za su wahalar da ita gudn zubewar cikin…………………..”
Zai ci gaba da dogon sharhin nasa Alh. Ahmad ya daga masa hannu fuskarsa a turbine yana cewa, “Dakata don Allah doctor! Ban fahimci mai kake nufi ba fa?”
Ran likitan ya dan baci sai ka ce bad a yaren Hausa yake masa bayani ba?
Yanzu haka irin mutanen nan ne da suke auren yara kanana amma bas a son haihuwa. Don haka sai ya dauki sakamakon gwajin ya mika masa. Alh. Ahmad ya sa hannu ya karba cikin zumudi, ya duba abin da takardar sakamakon ta kunsa. Ba wani abu ba ne face Shuhuda tana dauke da danyen ciki na wata daya da kwanaki biyar.
“INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN!” Alh. Ahmad ya ji gabansa ya soma faduwa, idanunsa suka sauya launi, cikin wata rikitacciyar murya y ace. “Shuhudan ce da ciki? Mun shuga uku! Ina zamu kai wannan tarin abin kunyar?”
Jin kalaman da ke fitowa daga bakin Alh. Ahmad ya sa jikin likitan yayi sanyi, da farko ya dauka Shuhuda mat ace ga shi Alh .Ahmad din, amma yanzu ya fahimci ‘ya ce a gareshi. Sai ya shiga kwantar masa da hankali cikin sanyayan kalamai. Alh. Ahmad y ace cikin dafe kai. “Likita anya ba a samu akasi an sauya sakamakon Shuhuda da na wata ba? Wallahi budurwa ce ba matar aure ba, ta ya kuma za a ce tana da ciki?”
Likitan y ace cikin nuna tausayawa. “Wallahi ba wani akasi da aka samu, hasalima duk yau ita kadai aka yiwa awon ciki a asibitin nan, shi ma dalilin da yasa aka yi mata, lokacin da aka kawo ta yanayi na mai shigar ciki duk sun bayyanar da kansu a tare da ita, hakan ce ta san a bada umurnin a yi mata awon cikin, sai kuma shi hakan ya tabbata”. Nuruddeen wanda tun fadr cikin ya sandare, sai yanzu y ace. “Abba idan dai har cikin ne da mamaki, saboda kowa yasan tarbiyya ta gidanmu”.
Alh. Ahmad ya dafe kansa, ya nutsa tunanin yadda abin ya faru, iya tunaninsa bai hango wata baraka da zata sa Shuhuda fadawa wannan rayuwar banzar ba. Lokaci daya ya ayyana a ransa, duk yadda aka yi Isah ne yayi mata cikin, musamman idan ya yi la’akari daga kasar waje ya dawo, wata kila dama abinda yake aikatawa ke nana tun zuwansa kasar. Likitan ya girgiza kai, y ace, “Alhaji wannan duk baa bin damuwa ban e, kawai ku kawo ta sai a zubar da cikin asiri a rufe”. Nuradden ya yi saurin cewa. “Haka kawai ma ya dace”.
Alh. Ahmad y ace da Nuraddeen, “muje”.
Suka yi sallama da likitan suka nufo gida kowanne zuciyarsa cike da kunci, wai Shuhuda da ciki na wata daya da kwanaki biyar?
Kafin su isa gidan Alh. Ahmad ya kira yayansa Alh. Sada ya ce su hadu can gida. Suna isa harabar gidan shi ma Alh Sadan ya karaso gidan. Gaba daya suka karaso falo. A cike falon yake, don haka aka wuce dakin mahaifinsu Alh. Rabiu. Dattijon yana zaune akan sallaya yana lazimi, suka zube a gabansa suka kwashi gaisuwa. Alh. Rabi'u ya dubi dansa Alh. Ahmad ya ce. "Ahmadu ya aka yi na ga duk kun shigo gaba daya?" Yayi shiru yana tunanin ta inda zai yanko maganar abin kunyar da Shuhuda ta tafka muusu. Alh. Sada ya magantu ganin shirun ya yi yawa, ya ce. "Ahmadu kai muke saurare, ka kirani a waya ka ce mu hadu nan, kuma ka yi shiru". Ya dago kai cikin dauriya da shanye damuwarsa, ya ce, "Sakamako ne bai yi kyau ba, domin Shuhuda ciki ne da ita na wata daya da kwanaki biyar!" Gaba daya dakin suka dauki sallalami har shi kansa Alh. Amad din. Bayan sun dure sallalamin, Alh. Rabiu ya dora da cewa "Lallai yarinyar nan ba ta kyauta mana ba". Alh. Sada mutum ne mai zafi, idan aka bata masa rai bai iya daukar hukun ba. Yanzu ma cikin matsanancin bacin rai ya nufi falo, kira yake, "Ina Shuhuda???"
Ganin yadda ransa yake a bace yasa Inna Yaduwa tasan da walakin, akwai gagarumin laifin da Shuhuda ta yi wanda yake nemanta, a yadda kuwa ta gani a kwayar idanunsa idan ya damku Shuhuda watakila shi ne sanadin ajalinta. Ta ce. "Tana daki, lafiya?" Bai tsaya bata amsa ba, yana huhhutai ya nufi dakin. Da sauri Inna Yaduwa ta bi bayansam. Yana shiga Shuhuda na kwance akan gado ya wani damko wuyanta, ya daga hannu ke nan zai kifa mata mari Inna Yaduwa ta buda muraya da karfi ta ca, "Idan har ka sake ka daki yarinyar nan ban yafe maka ba!al Cak! Jininsa ya tsaya, Inna yaduwa. Ta ci gaba da cewa. "Abin da nutsuwa bata yi shi ba, daga jijiyar wuya ma ba zai yi shi ba. Komai ta yi maka yadda bata da lafiyan nan karbar hukunci ba nata ba ne". Dalilin Inna Yaduwa kuwa na dakatar da shi daga dukan Shuhudan bai rasa nasaba da tuna halin da ta riski kanta a ciki lokacin da ta jaraba dukan Shuhudan din ba, hannunta ya sankare, abin da har yanzu kuwa babu wanda yasan da faruwarsa. Sai ya saki wuyan Shuhudan ya fice, ita ma Inna yaduwa ta bi bayansa. Ya shiga dakin mahaifinsa ya kifa kai a bango kwallan da ke makale a gurbin idanunsa suka samu damar zubowa. Inna Yaduwa da ta shigo dakin ta gansu sun yi jugum-jugum ta shiga tambayar abin da ya faru, Alh Ahmad ne ya yi karfin halin fada mata komai.m Itama kukan ta fashe da shi, Alh. Rabi'u ya ce. "Kinga daina kukan haka,ku nutstu mu tunkari kalubalen da ke gabanmu". Duk suka yi shiru zuwa wani loka ci, sai can daga bisani Alh, Sada ya dago kai ya ce. "Cikin mutane biyun nan dole a samu daya wanda ya yi mana

Please Login or Register in order to submit comment