Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yau karima ta ke sa'insa da shi. Matar da ta kasance magana daya zai yi ta zauna, babu jayayya ko rashin amincewa amma yau sai ga akasin haka a tsakaninsu? Yace Wallahi kinji na rantse Binta ba zata zauna min a gida ba ke kuma dole ki zauna. Ya karashe maganar cijin bayar da umarni. Sai ta duke ta sunne kai a kasa tana rusar kuka shi kuma yayi am fani da kaifin basisararsa a matsayinsa na jangwarzo ya rarrashe ta da tausar zuciyata. Mata har kullum rauni garemu don haka zuciyarta ta yi rauni ta aminta da ci gaba da zaman gidan mijinta. Wannan ke nan!!!! ***************
************** A kwana a tashi Shuhuda ta shiga aji hudu na sakandire karatu ba kama hannun yaro kowanne malami yana alfahari da ita saboda kwazonta da mayar da hankali akan karatu. Ranar litinin bayan an gama assembly kowanne dalibi ya shiga aji don daukar darasi. Shuhuda na zaune a mazauninta a kujerar karshe ita da abokiyar zamanta mai suna Sa'adatu. Kowanne dalibi ka duba karatu yake kafin malami ya shigo dama haka al'adarsu ta ke ba ka ta6a ji dalibai suna hayaniya irin na sauran makarantu. Amma banda Shuhuda da ta yi tagumi ga dukkan alamu tana cikin yanayin nata. Wani malami ya shigo gaba daya daliban suka mike tsaye don girmamawa a gare shi banda Shuhuda wadda ba tasan da shigowarsa ba. Ya amsa gaisuwarsu ba tare da ya lura da rashin mikewar Shuhuda ba Ya ba su umarni da su zauna. Bayan kowa ya zauna ya gabatar da kanshi a gare su a matsayinsa na sabon malamin da zai dinga daukarsu darasin chemistry. Ya duba littafan wata daliba da ke kujerar gaba ya ga inda suka tsaya a karatunsu sai ya dora da yi musu karin bayani. Ya ji dadin yadda ya same su dalibai masu fahimta suna da rike abu a kansu. Yana cikin bayanin nasa ne ya jefo musu tambaya mai stauri yace; Cikinku wa zai min bayani akan Radioactivity? A cikin harshen Turanci ne ya yi musu tambayar don ka'idar makarantar ne haka ba a baiwa malami damar yiwa dalibai tambaya da wani harshe ba idan ba Turanci ba, sai dai idan Islamic studie ne wanda shi harshen larabci tsagwaronsa ake gabatar da shi ga musulman dalibai kenan. Gaba daya ajin aka yi tsit, wuta ta dauke musu saboda ba a ba su darasin a cikin ayyukan da zasu yi a aji hudu ba su kuma hankalinsu bai kai ga bincikar 6angaren ayyukan da ke gaba ba. ( Dalibai anan tsanyi tsokaci idan kuka shiga makaranta ba dole sai syllabos din da aka ba ku zaku duba ba a'a ana son dalibi ya kasance mai kutse-kutse yana binciko abubuwa da dama a harkar karatunsa yadda idan kun zo gurin komai zaizo da saukiza kuga kamar maimaici ne ma kuke yi). Uncle Hamza ya yi murmushi ganin cewa an rasa wandazai iya yi a gare su bai ce komai ba sai ya koma kan kujera ya zauna yana baza idanu ya ga ta inda zai samu amsarsa. Aka dauki tsayin mintina huudu a haka babu wanda ya ko motsa sai ya girgiza kai yace: Yanzu duk taron yawanku babu wanda zai iya ba ni amsar Radioactivity? Karaf sai ji aka yi daga kujerar baya an soma bayanin cikin zazzakar murya mai natsuwa. Kyam! Ya tsaya tare da tsura mata idanu yarinya karama 'yar fara mai kyawun sura tana ta bayani cikin hadadden turancin ta(Latent English) na kasar Amurka babu tuntu6en harshe ko gwamutsawa da gur6ataccen turanci(Broken English) kuma bayani take akan Radioactivity da tsurar saninta wanda kowanne malami zai saurara sai ya jinjina mata. Haka ma idan a jarrabawa ne babu tantama zata sami maki(scores)mai yawa. Su kuwa dalibai 'yan uwanta ba su yi mamaki ba domin duk wanda ya kwana ya hantse a makarantar nan yasan shuhuda da kaifin kwalwa zai yi wuya a tuntu6eta sanin wani abu a rasa amsa daga gare ta. Shuhuda ke nan mai abin AL'AJAB! Haka dalibai suke mata lakabi. Tana kammala jawabinta ta koma mazauninta ta zauna ta mayar da tagumin alamar ta nutsa tunani. Uncle Hamza ya rasa abin da zai ce wace jinjina zai yiwa yarinyar nan. Wace irin kyauta zai bata wadda zata nuna jin dadin da ya samu kansa a ciki. Lallai ya yarda ya kuma aminta wannan yarinyar 'yar baiwa ce kuma ga dukkan alamu gidansu ana dagewa akan karatun yaro.
ada Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA)¤¤08¤¤
Kai ko da ma dagewar to akwai BAIWA ta musamman dake tare da ita, aiki ne wanda ake yi a aji biyar ya tambaye su akai don kawai ya kafa harsashinsa ga dalibai su san cewa zai iya daukarsu darasin da aka damka masa ba kamar yadda suka yi kuka da wancan malamin ba wai ba su gane darasinsa sosai saboda sauri da yake a dukkan abin da zai koyar da su a takaice yake yi musu. Don haka shugabar ajin ta kai korafi gurin shugabar makaranta aka yi katari da sababbin malamai da suka samu sauyawa(transfer) daga wasu rassan makarantar. To shi ne aka turo shi ajin ya taho da azamar ba su mamaki sa6anin haka sau ga shi daya daga cikin mafi karantar daliban ta ba shi mamaki ba kuwa karami ba mamaki ne cike da AL'JAB da ace dukkan daliban da ke ajin haka suke da budaddiyar kwalwa to tabbas da zai ji dadin kasancewarsa malami a ajin. Uncle Hamza ya sauke ajiyar zuciya ya mike tsaye daga inda yake zaune ya fito tsakiyar ajin yana duban inda Shuhuda take yace: Ke! Mike tsaye? Shuhuda ta dago da kai ta dube shi duba na rashin fahimta wanda ke nuni tamkar ba ta ji abin da ya fada ba. Ya sake maimata maganarsa, sai ta mike tsaye ta rusunar da idanunta kasa. Yace ya sunanki? Ta maimaita maganarsa kamar wadda ke koyon magana amma ita cikin yanayin tambaya da kuma jinjinawa ta yi maganar. Sai ya samu kansa cikin 6acin rai wannan wane irin rainin hankali ne zai tambaye ta sunanta ta maimaita tambayar da ya yi mata, sai kace tana magana da sa'anta? Duk fara'ar da ke fuskarsa ta kau a lokaci daya, yace; Tambayarki nake ya sunanki? Kanta na duke a kas ta ce: Sunana IZRA'EL!!!!! Ya cika da al'ajabin jin amsar da ta ba shi Izra'el? A yanayinta bai yi tsammanin zai ji sunan da ya dangantata da wata kabila wanda ba bahaushe ba. Saboda akwai hijabi karami a jikinta kamar yadda yake duk musulmin da ke ajin zaka samu bambancin kayansa da na sauran kabilu. To ba ma wannan ne al'ajabin ba shi ai sunanta ya tambaye ta mai yasa zata fada masa sunan mahaifinta? Lallai wannan yarinya ta raina shi, in baya da raini ta ya zata ba shi akasin tambayar da ya yi mata? Ya fito da ido waje sosai cikin barazanarwa yace: Sunanki na tambaya ba na mahaifinki ba. Na ce ya sunanki? Ta yi shiru bata ko motsa ba bare ta ba shi amsa. Abokiyar zamanta Sa'adatu ta mike tace: Uncle ka yu hakuri haka take tana da matsala a kanta. Matsala? Ya maiaita kalmar ta ya za a ce wannan yarinyar tana da matsala a kanta? Matsala ko rainin arziki? Idan ba haka ba ta ya yarinyar da ta ba shi amsar da bai ta6a tsammanin samu a ajin ba za a ce tana da matsala? Wato maganar da aka fada masa cewa 'yan ajin suna da rainin arziki abin ya zo kansa? Idan kuwa haka ne shi zai yi maganin abun domin shi ba ya daukar raini ga kowane dalbi. Ya dubi Shuhuda cike da 6acin ran rainin hankalin da ta zo masa da shi yace: Fita waje kika ma kunnan ki. Tayi tsaye tamkar ba da ita yake magana ba.
Suka ce; Uncle ka yi mata hakuri haka ta ke tana da ta6in hankali. Ransa ya kuma 6aci ko kadan ba ya son wannan kalmar rainin hankalin wai tana da ta6in hankali Sai kawai ya ja dogon tsaki ya dauki dan littafinsa ya ficce daga ajin ba tare da lokacinsa ya karasa cika ba. Kowa yayi tsit cike da al'jabi shi ke nan akan mace daya sun yu asarar ragowar lokacin da ya ragewa Uncle Hamza? A take wadanda ke jin haushin Shuhuda a ajin suka kara jin tsanarta a ransu ta zame musu GOBARAR TEKU. Washegari bayan an koma tara(break fast) Uncle Hamza yake da period a ajin su Shuhuda don haka lokacin na cika ya nufo ajin, sai dai yau sam bai shigo da fara'a ba wannan yana daga cikin matakan da ya tsara game da 'yan ajin saboda ya lura wani lokaci sakarwa dalibin fuska yana kawo raini matuka. Abin da Shuhuda ta yi masa a jiya ya zauna masa a rai koda ya koma gida kasa sukuni ya yi yana ta tunanin yadda lamarin yake yarinyar mai kwalwa da hazaka wadda ta bayar da amsar da matsala a kwalwa? Dama ana saun irin wadannan mutanen? Da tunanin ya yi masa yawa akwai wani abokinsa Dr Ishak da ke Ibadan sai ya kira shi a waya ya yi masa tambaya akan kwalwa shin dama a cikin kashe-kashen kwalwa akwai wadda mutu yake kasancewa haziki duk abin da aka tambaye shi ya bayar da amsa sai kuma daga baya a same shi kamar wanda ba shi da hankali? Dr Ishak ya yi kwan-kwance yana yi masa bayani cewa ' ana iya samun mutanen da idan suna da fasaha da hikima wani lokaci ka gansu a hargitse. Uncle Hamza bai gamsu da bayanin Dr Ishak ba sai yake ganin kamar bai gane tambayar bane saboda haka sai ya share ya yi kwance tare da nutsawa tunanin don samun mafita shi dai kam yarinyar ta kwanta masa a rai, rayuwarsa yana son mace 'yar fara mai matsakaicin jiki kamar dai yadda ya ga Shuhuda matsalar dai ita ce fuskanta da ya yi 'yar rainin hankali ce. Wai tun tana karamarta ke nan ina kuma ga ta girma ta zama babbar mace? Da wannan takaicin ya kwana. Washegarin ne ya yanke hukuncin 6illo da sabbin matakai don tsirar da kansa daga rainin dalibai. Daga cikin matakan da ya tsara har da daure fuska da kuma hukunta duk wanda ya kawo masa raini komai girman dalibi ko daliba. Kamar jiya yau ma yana shigowa ajin dukkansu suka mike don girmamawa a gare shi. Yau har da Shuhuda cikin masu isar da gaisuwarsu. Hannu kawai ya daga musu alamar su zauna ba tare da yayi magana ba. Dukkansu suka zauna ya soma yi musu darasi akan Nitrogen it's compound ba laifi suna fahimta domin Turancinsa mai kyau ne kuma a nutse yake musu bayanin yana yi yana nuna musu a aikace. Inda Shuhuda take ma sam bai duba ba bayaninsa kawai yake . Ita din ma ba ta damu da kulata ba ko akasin hakan tana dai saurare da duban bakinsa. Yana kare yi musu bayanin yasa kai ya ficce daga ajin. Haka suka wanzu idan ya shiga ajin ba ya duban inda Shuhuda take har zuwa ranar juma'a wato karshen mako(weekend). Ranar second period yake da ita kuma double period ne don haka ya yi musu bayani sosai game da aiki da ya yi musu bayani sosai game da aikin da ya yi musu. Daga karshe ya ba su aikin aji(class work) ya umarce su yi maza su gama ya tafi da littafansu. Ba musu duk da tambayoyin masu tsauri ne haka suka kukata suka gama. Shugabar daliban ajin (monitor) ta daukar masa zuwa dakin malamai (staffroom). Uncle Hamza ya zauna akan teburinsa ya dauko littafan daliban yana gyarawa yawancinsu duk gajerun bayanai ne(short note) suke yi game da tambayoyin da ya yi musu sai dai ya yaba musu hakan na nuna suna fahimtar abin da yake koyar dasu. Dama haka ne burinsa domin aikin(subject) dinsa babban aiki ne da ake son dalibai da ke fannin ilimin kimiyya(science department) su sanshi sosai saboda Chemistry yana da muhimmanci sosai gare su. Yana gyaran cikin nishadi, wani malami mai suna Uncle Joseph shi ma yana zaune a teburinsa yana gyara takardun gwaji(test) da ya yi a ajin su Shuhuda a jiya, Shine yake daukansu darasin lissafi(maths) kowannensu gyaran yake yana murmushi saboda irin hazakar daliban. Uncle Hamza yana cikin gyaran ya zo kan wani littafin tun daga tsarin rubutun ya isa mai littafin ya samu maki to bare kuma dogon sharhi(long note) da aka yi. Da sauri ya juya bangon littafin ya tsurawa sunan da ya gani akai ido. SHUHUDA SAGIR RABI'U ya gani an rubuta. Ya sanya kan biro a bakinsa yana jinjina kai wace yarinya ce wannan mai kwalwa da hazaka irin haka? Bayananta sun fi na kowane dalibi tsaruwa ina ta samu wannan BAIWA? Daga Allah! Abin da wani 6angare na zuciyarsa ya fada masa ke nan. Lallai kam Allah mai baiwa ne ga wanda yaso lamarinsa ya wuce gaban mamaki domin idan bawa zai tsaya yana mamaki ga lamarin Allah to ba shakka yana iya fita daga musulunci tauhidinsa ya yi rauni. Shi kuwa tauhidi shine babban jigon musulunci. Mikewa tsaye ya yi hannunsa dauke da littafan ya nufi inda Uncle Joseph yale ya dube shi cikin harshen turanci ya yi masa magana. Joseph ko kasan wannan sunan a cikin daliban aji hudu 'yan ilimin kimiyya? Uncle Joseph ya kar6i littafin ya duba sunan sai ya yi murmushi ya zaro wata takarda daga cikin takardun da ya gyara ya mikawa Uncle Hamza. Eh ina jin wannan ma takardarta ce na gama gyarawa ko? Uncle Hamza ya kar6i takardar ya duba da kyau tabbas ita ce tun daga tsarin rubutun zuwa sunannata duk babu tababa a ciki. Kuma a nan din ma babu inda ta fadi har kyautar maki daya da rabi Uncle joseph ya yi mata. Wannan na nuni ke nan shi ma Uncle joseph ya yaba da kwalwar yarinyar? Ya jinjina kansa cikin gamsuwa yace: Lallai yarinyar nan tana da kokari? Uncle joseph ya fadada murmushinsa. Shuhuda? Ai a tarihin makarantar nan ba a ta6a samun mai kwalwa irin ta ba zai fi kyau ace wannan yarinyar jami'a ta ke ba wai sakandire aji hudu. Uncle Hamza yace; Ni ma abinda nake gani ke nan saboda banyi tsammanin samun bayanan da na gani a cikin littafinta da takardar dake hannuka ba.
Ya juya ya koma akan teburinsa cike da AL'AJAB ya kasa ci gaba da yin gyaran ya fada duniyar tunani. Tabbas duk yadda aka juya wannan 'yar rainin hankalin yarinyar ce mai wannan littafin saboda babbar hujjar da yake da ita a ajin ya yi musu tambaya mai tsauri aka rasa wanda zai amsa masa sai ita ta yi bayani gamasasshe. Idan kuwa haka ne zai yi wuya ya kasance yanzu ma a samu wani da zai yi bayanin gamsasshe kamar nata. Lokaci daya ya soma jin zuciyarsa na sanyi akan tsanarta da ya fara yi a kuma lokacin ne ya soma aminta da bayanin abokinsa Dr Ishak cewar akwai irin yaran da idan baiwa ta yi musu yawa sukan koma kamar marasa hankali. Wani sashi na zuciyarshi yana karyata yiyuwar hakan domin masu irin wannan yanayin akan same su cikin rashin shiga mai ta kamala kana ganinsu ba sai an fada maka ba zaka san cewa suna da karancin hankali a tare da su. Ita kuwa Shuhuda kana ganinta ka ga cikakkiyar mai hankali ta yanayin shigarta gami da nutsuwarta . Duk macen da ta samu kanta a irin yanayin da Shuhuda ta ke ciki to tabbas za a iya kiranta cikakkiyar mai hankali amma abin tambayar a nan mai yasa 'yan ajin nasu suke ikirarin tana da matsala a kanta bayan duk ta fi su kwalwa? Ko kuwa hassada ce? Ai idan hassada ce da ya samu akasin haka daga gare su to amma wannan a bayyane yake akawai SHIRME? Cikin kalamanta in banda shirme ta ya mace ke juyewa zuwa jinsin namiji? Ma'ana ta kira kanta da sunan namiji bayan ta kasance mace? Idan ita ce yarinyar da ake magana mamallakiyar littafin dake hannunsa ai ya ga cikakken sunanta Shuhuda Sagir Rabi'u. To me ye hadin sunanta da Izara'el? Waye Izra'el din? Amsar da yake bukata ke nan a yanzu amma bai san ta ya zai same ta ba. Lamarin shuhuda ya daure masa kai matuka tunda yake rayuwarsa bai ta6a samun kansa a cikin dogon tunani akan lamarin wata diya mace ba, sai akan Shuhuda. Me yasa ne ya soma a kanta? Wani 6oyayyen al'amari!! A ranar bai samu komawa ajin na su ba, saboda kwalwarsa da ta dau caji, eh mana ai ko inji ne wannan aiki ya kamata ya huta, bare kuma kwalwa da ke jikin dan Adam wadda a kowane lokaci ake so bawa ya kasance yana saukaka mata wajen yawaita sanya mata abubuwa masu nauyi.=========- ===============
===========- =======BABI NA HUDU========- ---------------
--------------------------- ======MAFARKI KO GASKE======- RANAR litinin kamar yadda a tsarin shigar malamai ya ke a ajujuwa yau ma Uncle Hamza ya shiga nashi ajin a dai-dai lokacinsa(period). Sanye da kananun kaya bakake wuluk da yake fari ne sai kayan suka amshi fatarsa. Idonsa sanye da karamin bakin tabarau shi din ma ya kara masa kyau ainun saboda matashi ne mai jini a jika. Ya aje kasumba a fuskarsa wadda ta sha gyara ta yi luf ba ya da haka ma kana dubansa kasan ya fito daga tsatson RUMAWA don akwai ma tsagen biyu-biyu a gefen fuskarsa. Bayan ya gama kar6ar gaisuwa daga dalibansa sai ya nemi guri ya zauna akan mazauninsa.
Can karshen bango inda kujerar su Shuhuda ta ke ya tsurawa ido yana nazarinta. Amma farat daya baza ka ce ita yake kallo ba. Kanta na sunkuye kasa ta tallabe ha6arta da hannayenta. Akwai abinda ya lura da shi sai ya ga kamar lokacin da dalibai suka mike suna gaishe da shi ita ba ta tashi ba, kuma ba ta dago kai ba har kowa ya zauna. Amma abin ya tsaya masa a rai mai yasa ita ba ta mike don gaishe shi ba? Shin ita wani ne ta fi a ajin da ba za ta iya girmama malamanta ba. Eh to zai iya cewa tafi sauran 'yan ajin kokari to amma kokari babu ladabi ai shirme ne duk nagartar kokarin mutum idan ya kasance bashi da ladabi to ya kan zama FANKO. Ya kyale ta ne bai nemi ba'asin rashin da'ar da ta nuna masa ba saboda mikin farin cikin da ya shigo da shi ajin na samun gamsassun bayanai na amsoshim da ta bayar. 'Yan ajin suka shiga damuwa ganin Uncle Hamza ya shigo ajin har tsayin mintina sun fi goma amma bai fara yi musu darasi ba sai suka dinga tunanin ko don ba su ta6uka wani abin kirki ba ne a cikin aikin da ya ba su ranar juma'a. Suka tattara komai suka tsura masa idanu don jin hukunci ko wani abu da zai iya yi. Uncle Hamza ya yi huci tare da mikewa tsaye ya isa gaban allo (Black board) hannunsa rike da alli(chalk) ya rubuta sunan darasi Chemistry sannan ya rubta kwanan wata da aikin da zasu yi yau akan MAGNETIC FIELD sai da ya rubuta sannan ya juyo zai fara bayani sai ya tuna littafansu na hannunsa. Yace Ku yi hakuri na manta littafanku na hannuna. Ya dubi shugabar ajin yace Je ki kwaso. Ta fita shi kuma ya cigaba da cewa. A yau zamu yi darasinmu ne akan maganet to amma tunda lokaci ya kure zamu tattauna game da aikin ajin(class work)da ya gabata in yaso gobe sai mu dora wannan. Yana rufe baki shugabar ajin ta dawo dauke da littafan ta dora akan teburinsa ya soma kiran sunaye yana damkawa kowacce daliba nata har sai da ya zo kan na karshe sai ya ajiye shi a gefe. Yace An bawa kowa nasa? Suka ce Eh. Saboda ba wanda ya lura Shuhuda ba ta kar6i nata ba sai Sa'adatu ita kuma tayi nauyin bakin cewa Shuhuda ba ta amshi nata ba. Yayin da Shuhudar bata ma san abinda ke faruwa ba. Uncle Hamza ya ci gaba da yi musu bayani game da amsoshin da suka bayar ya dora da basu shawarwari don ganin sun zama Zakaru a kowanne darasi ba lallai sai na sa ba. A haka ya cinye lokacinsa sai da yaga wani malami a waje yana jiransa sannan ya dauki littafin da ya a jiye a gefe yace; Wace ce Shuhuda Sagir Rabi'u a cikin ajin nan? Kowa ya mayar da dubanshi can layin karshe inda Shuhuda ta ke zaune kanta rusune a kasa Sa'adatu ce ta yi saurin cewa. Ga ta nan. Yayin da ta zunguri Shuhuda. Zumbur Shuhuda ta mike tsaye ta nufo gaban allo ta durkusa(kneel down). Uncle Hamza ya cika da mamakin wannan yarinya daga tambayar wace ce ita sai kawai ta fito gaban allo ta durkusa sai ka ce yace ta yi hakan? Ganin rashin isashen lokaci tunda ga wani malamin a waje yana jiransa sai ya mika mata littafin ya girgiza kai ya ficce ba tare da ya iya cewa wani abu ba. Uncle Hamza yana zaune akan teburinsa cikin dakin malamai ta tagar dake ku sa dashi ya hango dalibai na shawagi a farfajiyar makarantar alamar an fito tara (break fast)ke nan dama ya kosa lokacin ya cika saboda yana son ganawa da Shuhuda akwai tambayoyin da yake son ta amsa masa su. Da sauri ya mike tsaye ya nufi ajin su Shuhuda kamar yasan tana can. Ya tarar da ita tana duba littafanta sai ya ja ya yi tsaye daga bakin kofa ba tare da ya karasa ciki ba. Ya tsura mata ido wato dama shi yasa ta kasance mai hazaka tunda idan an yi break ma ba ta fita daga aji karatu ta ke yi? Kamar ance dago kanki ana kallonki sai kuwa ta yi tozali da Uncle Hamza a tsaye yana kallonta. Da yake bai sako bakin tabarau dinsa ba don haka tana kallon kwayar idanunsa. Shi kuwa ganin ta dago ta dube shi sai ya tako sannu a hankali zuwa inda take ya zauna a kujerar da ke gabanta. Yace Shuhuda Sagir Rabi'u. Kanta na sunkuye ta amsa Na'am. Ya yi gajeran murmushi yace Mai yasa baki fita break ba bayan kowa ya fita? Muryarta a nutse cikin zakin nan nata yaji tace: Bana fita break idan na ciyo abinci daga gida bana karaci cin wani sai na koma. Yace amma ko ruwa kin bukata. Sai ta janyo lokar kujerarta ta fito da robar ruwa Swan water ta nuna masa ba tare da ta yi magana ba. Ya jinjina kai yace: Ki ce tafe kike da gidanki? Ba ta ba shi amsa ba haka kuma ba ta dago ta dube shi ba. Ya ci gaba da cewa yana kallonta. Dama wasu tambayoyi nake son yi miki. A wannan karon ba ta iya jurewa ba sai ta dago kai ta dube shi tace: Tambayoyi? Ya tabbatar mata da hakan ta hanyar daga mata gira sama ya ci gaba da cewa. Ke musulmace kuma bahaushiya? Fuskarta ta nuna yanayi na mamakin jin tambayarsa. Ta ce Eh. Yace Na ji ai cewa kika yi Eh ita kuwa kalmar Eh tana nufin DUKA ban san wane matsayi zan ajiye amsar eh dinki ba. Ta yi shiru ba ta tanka ba. Yace: To misali ma ace na ajiye ki a matsayin musulma shin mai ya hada sunanki Shuhuda da Izra'el? Ta dago kai da suri tace; Izara'el? Yace Eh. Ta girgiza kai tace: Ni ban san Izra'el ba ban hada komai da shi ba. Ya cika kwarai da tsananin mamakin jin maganarta amma sai ya daure yace: Idan baki san Izra'el ba sannan ba ki da wata alaka da shi mai yasa idan an tambayi sunanki kike cewa Izra'el? Ta kara fito da ido alamun dai nuna ba tasan zancen ba idan aka dubi kwayar idonta za a tabbatar da haka. Ta ce Ni din kuwa? Ya kara cika da mamaki wai wannan wacce irin yarinya ce mai wadannan halaye? Ya aminta idan ma kwalwa ce ta yi mata yawa to har da raini tsagwaronsa. Yace to na ji bake bace amma

Please Login or Register in order to submit comment