Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai yasa idan malami na cikin aji ba ki mayar da hankali gare shi? Maimakon ta amsa masa tambayarsa sai cewa tayi.........
¤
¤
ko me ta ce, oho!!! Sai ku biyo ni dan jin saura..........
da Hausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤09¤¤
uncle mu dawo kan maganarmu domin gaba daya ka daure min kai ina son gamsasshen bayani daga gare ka. Ya kara cika da tsananin mamaki wannan wace irin yarinya ce da take neman juyar masa da tunani? Bai gaza amsa mata alfarmar da ta nema ba ko ba komai a cikin bayanin da za su tattauna zai iya fuskantar kowace ce ita. Don haka cikin natsuwa yace: Abu ne mai matukar mamaki ga irin yadda kike wasu abubuwa. Ta katse shi da cewa: Uncle am sorry kamar wadanne abubuwa? Kasan komai yana da dalili zai iya yiyuwa idan ka fada min misalin abubuwan da nake yi na gamsu da zargin da nakewa kaina. Ya dube ta cikin ido yace: Kinga kina kiran kanki da sunan namiji alhalin kina mace. Kuma namijin ba wanda ya haife ki ko dan'uwanki ba. Ta yi murmushi tace: Auho! Ai uncle a tunanina ko wane suna mutum zai iya amfani da shi wata kila akwai wata Hoyayyar ALAKA da ta sanya haka. Cike da rudani yace 6oyayyar alaka? Ban gane ba. Tace Ka tuhume ni akan abun da ko a mafarki ba zaka samu amsarsa ba bisa wani 6oyayyen SIRRI mai wata irin YANAH mai duhuwa wadda idan za z kunna dukkan hasken kwan lantarki dake fadin duniya ba zasu haske DUHUN da ke tattare da ni ba. Illa wani muhimmin ABU wanda ko a mafarki bana tunanin kai zaka iya canko shi. Ya rasa yadda zai yi ya fahimci wace ce wannan yarinyar da ke zaune a gabanshi. Ko a kalamanta na yanzu kamar zai iya ajiye ta a sahun marasa cikakken hankali domin da farko kamar akwai hankali a tare da ita amma koda ta kai tsakiyar maganar tata sai sokana da shirme suka ida mamaye hankalin nata. To yanzu me ma zai furta mata? Kafin ya karasa lalubo abin yi ta cike gurbin shirun da maganarta. Uncle wai waye MUTUM? Ni fa har yanzu ban san waye mutum ba ban san mai ya alakanta shi da wasu jinsina ba. Maganarta wani tsani ne har wa yau da ya kara hauhawar da rudaninsa cikin rudanin da rikitarwa ya lalubo abin cewa. Halittar MUTUM halitta ce wadda Allah(S.W.T) Ya yi ta a doron kasa mai girma da daraja domin duk halittun da ke duniya kama daga shi kansa mutum, jinnu dabbobi tsuntsaye da tsirrai to babu ya mutum . Ana kiran mutum 'Yan Adam a jam'insu ma'ana idan za a tara mutane da suka zarce mutum daya, idan mutum dayan ne ana kiranshi dan Adam saboda asalin halittar mutum daga shugaban halitta ne Annabi Adamu (A.S) don haka duk mutum ake kiransa DAN ADAM mutane kuma ake kiransu Bil'adama ko 'Yan Adam. Idan muka koma ga sauran halittun idan kika tsaya kika lura zaki ga dukkan sauran halittu samuwarsu cikar farin cikin dan Adam ne. Ina fatan wannan bayanin nawa ya gamsar dake sanin ko waye mutum? Ta jinjina kai tace: Haka ne, bana son shiga hakki idan na yi tambaya aka amsa min ko na gamsu ko ban gamsu ba to na gamsu din ne, ba kuma don na gamsu ba. Shin uncle, Ni da kai din nan mene ne a cikin halittu? Ko kuma nace ni ko ka fahimci ni eace halitta ve a cikin halittu? Wadanne dabi'o'i ne mutane suke yi????
Yace Ni mutum ne dan Adam ke ma a yanzu kallon halittar dan Adam nake yi miki saboda kina da suffa da tsari irin na halittar dan Adam. Sannan Bil'adama suna dabi'u na tafiya da kafafu biyu yin ayyuka da hannaye biyu gani da idanu biyu shakar kamshi ko wari da hancina biyu. Bil'adama suna dabi'o'i na tunani da fahimta suna da dabi'ar yin karatu ina tunanin haka ma ya gamsar dake? Tace na fada maka kona gamsu ko ban gamsu ba na gamsu din ne. Yace Ai so nake na sani. Tace Watakila na gamsu wata kila ban gamsu ba ko kuma zan gamsu.... Amma dai na gamsu din tabbas. Dole unle Hamza ya shiga rudani domin gabaki daya maganganun Shuhuda ababen rudani ne. Idan banda rudani ta ya mutum zai ce koya gamsu ko bai gamsu ba amma ya gamsu din? Me ye MANUFAR hakan? Ba a gamsu ba ko an gamsu ya zama lallai an gamsu? Wannan tatsuniya ce ko soki burutsu? Yace: Idan kin gamsu ko ba ki gamsu ba zai zama hujjar gamsuwarki. To maimata min abin da na fada domin hakan shi zai ba ni kwarin gwiwar baki amsoshinki. Tayo dariya. Uncle sai ka ce ni yarinya ce 'yar shekaru hudu a duniya? Shekaruna fa sha bakwai ajina hudu a matakin sakandire ke nan zan iya rike duk abin da aka fada min har ma na yi masa fashin baki? Shi ma dariyar ya yi amma tashi gajeruwa ce mau kunshe da takaicin maganganun yace; Na ji maimaita idan da gaske kin riken. Ta kuwa maimaita har ma da karin bayani. Da ta karashe yace; A maganarki kin ce ba kisan ke mece ce a cikin halittu ba to amma na yi mamakin karin bayanin da kika yi min akan halittar dan Adam, me ne gaskiyar lamari? Kai tsaye tace dashi. Idan har ka yi mamaki akan faruwar hakan to kuwa zaka yi mamaki akan yadda dalibi ke fin malaminsa ililmi. Saboda shi dalibi makoyi ne kwalwa kuwa takan taimaka wa wanda aka fadawa ya kara sanin abun da aka sanarda shi. Ya baki zai kara magana ke nan dodon kunnensa suka jiyo masa karar kada kararrawar komawa aji don haka maganar tashi ta katse ya mike tsaye gudun kada dalibai su tarar da shi. Shuhuda akawai sauran tambayoyin da zan miki amma lokaci ya kure don haka sai idan mun sake samun dama. Tac ce; To uncle ammaka shirya min tambayoyi da suka shafu wasu halittu ba bil'adama ba domin shi ne dama ta karshe da zaka yi magana da ni. Ya daina mamakin maganganunta ya ce; Ke ma ki shirya amsa min korafin da kika sjigar na yi miki tambayoyi akan wasu halittu ba bil'adama ba. Ya karashe maganar yana kokarin ficewa daga ajin amma kafin ya kai ga ficewar sai kunnuwansa suka jiyo masa furinta tana cewa. Wannan hirar da muka yi yasa nasan kai MATA'UL HAYAT ne gare ni dama zan budi ido na ganni cikin yalwataccen guri kwatankwacin dokar daji da na samu MATA'UL HAYAT wanda ba ya ta6a yankewa a gare ni. Sai dai abu ne mai wahala na samu MATA'UL HAYAT a wagga Sai dai abu ne mai wahala na samu MATA'UL HAYAT a wagga........ Bai karasa jin furucin nata ba saboda samun nasarar ficewa da ya yi amma kalmarta ta karshe ta zauna daram a kwanyarsa hakan ne ma ya sa lokacin da ya koma dakin malamai ya shiga kogin tunani. Sam ya manta ma'anar kalmar daga ji dai kalma ce ta Larabci musamman idan ya yi la'akari da HAYAT da ta sako cikin jam'in kalmomin wadda ta sako cikin jam'in kalmomin wadda take nufin RAYUWA. To me MATA'UL ke nu fi? Amsar ta gaza samuwa sai da ya dangano ga uncle Tukur Ahmad Sada wanda shi ne H.O.D na Arabic ya isar da bukatarsa ta neman sanin ma'anar kalmar MATA'UL HAYAT ko ya tantance me Shuhuda ke nu fi? Uncle Tukur ya yi murmushi yana duban uncle Hamza yace; Kalmar MATA'UL HAYAT kalma ce da aka samo daga harshen larabci ma'anar gundarin kalmar tana nufin JIN DADIN RAYUWA. To amma wani lokaci ana alakantata da kayan dadin rayuwa. Uncle Hamza ya yi jinjina kai cikin gamsuwa. Uncle Tukur ya ci gaba da cewa. Wani bincike kake yi ne da ya hado da kalmar? Uncle Hamza ya yi takaitaccen murmushi ya ce Eh. Yana kokarin mikewa; Na gode . Ya koma teburinsa ya zauna. Wani tunanin ya bijiro masa idan kalmar MATA'UL HAYAT na nufin JIN DADIN RAYUWA me Shuhuda ke nufi da ta ce shi MATA'UL HAYAT ne gare ta? Wai kuma da zata samu kanta a cikin dokar daji to da ta samu MATA'UL HAYAT wanda ba ya yankewa. Ke nan ta kasance mai son yin rayuwa a cikin dokar daji? Me yasa ta ke da wannan burin? Wannan ma idan aka auna shi a mizani za a tarar da soki-burutsu ne a cikin maganganun nata kamar yadda ta saba abubuwanta a cikin soki-burutsu. To wai duk me ya yi sanadin hakan? Kwalwar ce ta yiwa Shuhuda yawa yasa ta ke wasu rudaddun al'amura ko kuwa tana daga cikin jinsin mutane masu raunin hankali? A'a gaba daya ma ba ta daga cikin jinsin halittun mutane? Aljana ce? Tabbas Aljana ce! Ya ji zuciyarsa na son gasgata masa hakan bisa kwararan hujjoji. To amma ta ya zai aminta cewar Shuhuda aljana ce? Idan ya alakantata da suffofin mutane ma'ana ba ta da kofato a kafarta idan ba ta daga cikin jinsin mutane ko na jinnu a wane jinsi za a ajiye ta? Bai sani ba! Babu wanda zai yi gajen yanke hukunci akan haka! Babu wanda zai iya cewa ga matsayin Shuhuda a rayuwa illa dai Shuhuda wata halitta ce da ke yawo bisa doron kasa don haka yanzu abu mafi rinjaye a tare da shi sanin nasabarta ma'ana asalinta iyayenta da ma sauran wasu al'amura da suka shafe ta! Zuciyarsa ta kalubalance shi mai yasa zai damu kansa a cikin lamarin Shuhuda a matsayinsa na malami wanda alakar karatu ta gada su? Da gaske ke nan abin da yake ji na masa yawo a rai ya zama gaskiya? Ya kamu da son Shuhuda? Ta ya zai kamu da son abin da bai da tartibin sanin ko mene ne shi? Lokaci daya ya kalubalanci wannan hasashen na shi kawai abin da ya dace dashi ya share ta. Ya manta da wanzuwarta a makarantar bare ta dinga caza masa kwalwa a karin banza. ANYA UNCLE HAMZA? DUBA DAI!!!
Shuhuda na kwance a saman gado, inna yadywa ta shigo dakin tana cewa. Ke burkakkiya tashi ga wannan fitinannen yaron ya hanani sukuni wai sai ya yi waya dake. Shuhuda ta dago kai ta dubi inna yaduwa da wani irin kallo mai rikitarwa ta ja dogon tsaki ta mayar da kanta ta kife a filo. Ran inna yaduwa ya 6aci ta janyo Shuhuda tana cewa: Ke ni kike yiwa tsaki don gidanku? Shuhuda ta daga mata hannu tace: Kada ki kara ta6a ni idan ina wanka ki fita ki bar kallona.... Nace ki fita idan ba so kike na yi miki wanka ba? Inna yaduwa ta ture Shuhuda tace: Ja can burkakkiya kawai. Tana karashe maganar ta fita daga dakin. Isah da yake jiyo hayaniyarsu ta cikin wayar yace: Haba Inna bai kamata kina yiwa Shuhuda irin wannan tsawar ba ya kamata ace kina rarrashinta domin wannan matsalar da ta ke fama da ita ba karamar matsala ba ce: Ta katse shi da cewa: Bayan matsalar ma har da shakiyanci don kawai tana ganin ni kakarta ce sai ta dinga raina min hankali. Wai na shiga dakinta amma sai tace wai tana wanka na fita... Oh ni Yaduwa yau na gamu da gamona!! Isah yace: Wane irin wanka? Inna yaduwa ta ce; Shi ne abin da ke ba ni takaici, kwance fa ta ke akan gado sanye da doguwar riga baka amma don tsabar ta dauke ni wata karabiti shine zata ce tana wanka? Isah ya jinjina maganar yace: To don Allah Inna ki dinga hakuri da Shuhuda kuma ya kamata fa ace ya zuwa yanzu an san wane irin ciwo ne da ita. Saboda barinta cikin wannan matsalar ba karamin cutarwa ba ne a gare ta? Inna yaduwa tace To ai magana ba hannuna take ba wannan sai ka tuntu6i mahaifinku. Yace Shi ke nan zan yi masa maganar idan ma ba a samu kwararriyar asibitin da za a magance mata matsalara nan gida Nigeria ba ko nan Senegal sai a kawo ta tunda ba laifi suna da kwararrun likitoci. Inna yaduwa tace: Dada dai ai ni kuma na gama magana kai ni kyale ni haka yara kun zame min karfen kafa. Daga wannan ya yi watandaririya da ni sai wannan ya juyo ni sai ka ce masa a tanda? Tana karashe fadar haka ba ta bari ya tanka ba ta datse kiran. Washegari Alh Ahmad ya zo gidan ya tarar da inna yaduwa a falo tana matse lemon tsami a kofi ya zauna yana gaishe ta. Ta amsa masa cikin sakin fuska. Yace: Me zaku yi da lemon tsami? Ta ce: Sha zan yi kasan yana wanke dattin ciki. Shi yasa yake son zama da tsaffi ko banza zaka samu magungunan gargajiya. Yayi murmushi yace; To ina Shuhuda da ba ku ba ta ta matse muku ba? Ta kya6e baki tace: Wannan burkakkiyar yarinyar wani abu ta iya? Ya ce Kai inna rannan fa na ji kina yabonta akan dambun da ta yi muku? Ta sake kya6e baki ta ce: Ai ranar ma sa'a aka ci. Amma Shuhuda ba tasan komai ba daga kwanciya sai karatu, haka kawai yarinya ta tsiri wata tsurfa ana magana da ita sai ta yi shiru idan an matsa mata ta shige daki ta kudundune cikin bargo sai ka ce mai fama da lalurin basir saboda yawan kasala. Alh. Ahmad ya girgiza kai yace: Yau ma ke nan baccin ta ke? Tace: Ba fa bacci take ba. Kwance kawai take koda yake dazun tace min wai kanta na yi mata ciwo sannan cikinta na yamutsawa na ce ta dauko lemun tsami ta sha ta ce min. Wai ita rabonta da shan lemun tsami tun tana ciki kafin a haife ta don haka yanzu ba za ta sha ba. Wanda ta sha ma a dole ta sha ba don haka ba babu abin da ya hadata da lemon tsami wai ko ganinshi ta yi zuciyarta tashi ta ke ta jita kamar ba mutum ba. Don tsiya ma har da ce min ita ba tasan wace ce ita ba wai tana jin kanta kamar ba mutum ba. Alh Ahmad ya kwashe da dariya. Ya ce: Cewa zaku yi kuna shan durama a gidan nan? Tace Ba wata durama illa tsabar rainin hankali. Ya sauya fuskarsa daga yanayin fara'a ya nutsu yana cewa. Yauwa. Dama maganarta ce ta kawo ni mun yi shawara da yaya za a kaita asibiti a binciki lafiyar kwalwarta saboda mu ma abin yana damunmu. Cikin rashin kula inna yaduwa tace: Da dai ya fi domin ni na gaji da wulakancin yarinyar nan har ma na soma tunanin ta tattara kayanta ta koma can gidanku tunda ni ta rainani. Alh Ahmad ya yunkura ya mike tare da cewa. Bari na dubuta. Ba ta tanka ba. Ya nufi dakin Shuhuda tarar da ita ya yi zaune akan abin sallah tana lazimi shigowarsa yasa ta tsinke lazimin tace: Baba barka da zuwa. Yace yauwa 'yar baba. Bayan ya zauna saman gadonta ya dora da cewa; Akace baki jin jin dadi? Ta dube shi cikin yanayin rashin fahimta, ta ce: Ni? Kai ni yau garas nake, shekaru sha takwas ne dai na dan yi rashin lafiya, ita ma ban wani jima ba na samu sauki sai dai ko a mafarki ne na ji kamar ba ni lafiya? Fuskarta ta bayyanar da yanayi na tuhumar kanta da kanta. Kafin ya yi magana ta dora da cewa. Amma dai lafiya na ke, jina na ke ma kamar ingarman doki saboda karfi bari ma ka gani. Kawai sai ta mike ta kama tsalle. Bai yi yukurin dakatar da ita ba, tabbas Shuhuda tana da ta6in hankali. Abin da ya ayyana a ransa ke nan. Bayan ta yi tsallen ta koma saman gadon ta zauna tana wata irin dariya ya tsura mata idanu can yace; Ki shirya zamu je Asibiti. Tace: Asibiti? Eh, Ya tabbatar mata. Bata musa ba tac: To. Ya tashi ya fita. A falo ya zauna suna hira da inna yaduwa can Shuhuda ta fito daga dakinta. Inna yaduwa ta wurga mata sakon harara, Shuhuda ta ja tunga turus ta tsaya. Ni fa ki daina hararata idan kina hararata sai na dinga ganinki kin koma min kamar wata dodanniya. Dubi yadda idanuwanki suka yi kulu-kulu kamar kuruga, ina jin sai na rage miki girmansu. Inna yaduwa ta ja tsaki. Sai ki maida hankali tunda ke ce sarauniyar wauta. Shuhuda tace: Au ba ki san ni sarauniya ba ce? To wallahi ki sani an bani sarauta tu lokacin da ya shude, yanzu haka idan fadawana suka ganki sai sun hukunta ki. Alh Ahmad yana so ya yi dariya amma ya gumtse don shi abin na su ma dariya ya soma ba shi. Yace Inna zamu je Asibiti. Tace: Sai kun dawo, ya dubi Shuhuda yace: Wuce mu ta fi. Yana gaba tana binsa a baya har inda ya ajiye motarshi. Sun isa asibitin Fancy Clinic Alh Ahmad ya bukaci ganin Dr Ya'u likitan da ya yiwa Shuhuda tiyata shekarun baya. Anan ne ake sanar da shi ai ya jima da rasuwa. Gaban Alh Ahmad ya fadi yaushe Dr Ya'u ya rasu bai sani ba? Koda yake sun jima ba su zo asibitin ba. Dr Ya'u kwararren likitane da ake ji da shi a wannan asibiti. Ya yi musu aiki lokacin da Shuhuda ta ke tsotsar hannu aka tsaga wanda daga lokacin ne ba ta kuma tsotsar hannu ba. (((( Sai dai abin da Alh Ahmad bai sani ba shine; tun bayan sallamar Shuhuda daga asibitin ya yi ta fama da rashin lafiya wadda bata jin magani daga karshe ya rasu. Sanadin ya faru ne sakamakon allurar da yayi a jikin Shuhudan. wanda idan muka duba tun baya mutum biyu Salmai ta rasu bayan ta tsarga hannun Shuhuda da ta yi. Mas'ud shi ma ya rasa ransa sanadin jinin(ruwan nono) da ya fito daga jikin Shuhuda. Don haka zamu iya tantancewa duk wanda ya yi sanadin fitar jini(ruwan nono) a jikin Shuhuda yakan rasa ransa ne. Me ye sanadin haka?)))). Dole sai wani likitan suka samu ganawa da shi ya yi aune-aunensa da gwaje-gwajensa ga Shuhuda daga karshe ya tura su asibitin mahaukata da ke garin Dawanau don yace yana ganin matsalar tata sai an dangano da can.
YAT (JIN DADIN RAYUWA)
¤¤10¤¤
koda suka fito daga wannan asibitin kai tsaye Dawanau suka nufa. A cikin motar Alh Ahmad har lokacin jimamin rasuwar Dr Ya'u yake yi yayin da Shuhuda ta yi lum kamar mai bacci. Suna isa asibitin Dr Ibrahim m Sani suka gani ya yi gwaje-gwaje ga Shuhuda ya dubi Alh Ahmad yace: Na gama bincike ga yarinyar nan abin da binciken nawa ya ba ni, lafiyarta kalau ba ta da wata cuta da ta shafi kwalwarta. Illa iyaka ta kasance daga cikin yara masu kaifin kwalwa (Gifted) don haka za a ga tana bada himma a karatu da sauran al'amura domin ita kwalwar tata ontop ce da an saka mata abu ta ke daukewa. Alh Ahmad yace; Likita ba wai ban aminta da bayaninka ba ne. Ina so ka gane ita wannan yarinyar ba a 6angaren karatu kawai ne ya samu zargin tana da ta6in hankali ba a'a wani lokaci fa idan ana zaune da ita sai ta yi ta sakin maganganu na shirme. Dr ibrahim yayi murmushi; yace: Irin wadannan yara ba su fadar abu na shirme sai dai idan a gaza fahimtarsu amma idan aka nutsu aka yi wa maganganunsu kyakkyawar fahimta za a ga komai suka fada yana akan turba. Alh Ahmad ya jinjina kai cikin sarewa yace; Shi ke nan likita, mun gode. Koda suka taho a hanya Alh Ahmad bai aminta da bayanin da Dr ibrahim ya yi masa ba. Gani yake bai da kwarewa ne akan aikinsa don haka ya yanke shawarar zaije ya fadawa dan uwansa abin da ya wakana inyaso idan ta kama su fita da ita wajen sai a fita da ita don gaskiya duk wanda ya ga abubuwan da Shuhuda ta ke yi yasan tana da ta6uwa a kwalwarta. Baba wai kuna zargin ni mahaukaciya ce? Muryar Shuhuda ta katse masa tunaninsa. Bai bata amsa ba taci gaba da cewa. Ina mamakin yadda ake kallona a matsayin mahaukaciya, shin idan ni mahaukaciya ce da ba a ganni ina shiga bola ba? Ku daina yi min kallon mahaukaciya ni na fi kowa hankali, ko kun manta daga MISRA na fito? Ko kuwa so kuke na koma inda na fito? Ko a yanzu ma ta yi shirmen da zai tabbatar da tana da ta6uwar kwalwa to amma a yanayin da take ciki ba zai nuna hakan ba, gudun kada ya sa ta a wata damuwar. Haka ya kyale ta tana ta zuba surutai na rashin kan-gado har suka isa gida ya sauke ta. Ko shiga cikin gidan bai yi ba ya juya. Yayin da ita kuma ta shiga gida tana gunjin kuka, wai an mayar da ita mahaukaciya bayan kuma an san ta fi kowa hankali. Inna yaduwa tana jinta ta yi kunnen uwar shegun da ita har dai bacci ya dauke ta. Inna yaduwa tana jinta ta yi kunnen uwar shegu da ita har dai bacci ya dauke ta. Ta leko dakin ta ga Shuhuda na sharar bacci ta yi murmushi rac: Ja'irar kawai waye zai ganki yace ba mahaukaciya ba, bayan kina abubuwa na mahukata? Ai ni ba su burge ni ba da ba su sanya igiya sun daure ki ba. Tsalam! Shuhuda ta mike daga kwance idanunta jajur tace: Sai kizo ki daure ni din. Inna yaduwa tace: Au! Ashe ba baccin kike ba? To koma ki kwanta kin fi kowa hankali. Ta karashe maganar tana kokarin juyawa.
Idan ke ba ki daure ni ba, ni zan daure ki domin na ga alama kin soma shiga bola kina tsin-tsince dubi yarga6a66un kayan jikinki kin wani daura dankwalin kaya ..... Hahaha mahaukaciya 'yar larai ku yi mata yeho. Ta saka dariya. Inna yaduwa ta tabbatar dai akwai haukan a tare da Shuhuda ta sa kai ta ficce ba ta kuma saurararta ba, don idan ta biye mata shirme zata yi ta zuba mata. ==========================----
--------------------------------------- ========BABI NA BIYAR=======***
*******BARA DA BANA******* Ina da hujjoji da ya sanya nake tababa da zamantowata cikin irin halittunka na mutane. Wadanda idan ka dube su da kyau zaka gasgata hakan. kaga kamar misali: Ni idan dare yayi nakan samu kaina a wata daula ana kidan kalangu ina rawa tamkar mazari. Sannan nakan sha ruwa a cikin koko har ma na watsa a jikina ana zagaye da ni wasu na hidima a gare ni. Da zarar sanyin asuba ya ratsa gangar jikina sai kuma na tsinci kaina a cikin kasar Misra ina ta ibadu..... Da safe kuwa sai na dinga jina wata iri bana tantance halin da nake ciki na farin ciki ko bakin ciki? Haka nan nake jina sakayau, kuma nannauya har ma na rasa a ina nake......... Shuhuda ke nan da ta ke fadawa Uncle Hamza lokacin da ya sake rutsata a cikin ajin nasu, bayan dalibai sun fita break. Ta daina ba shi mamaki, sai dai maganganunta babu tababa za a ajiye su a matsayin BARA DA BANA idan akayi duba wai tana jinta SAKAYAU kuma NANNAIYA wannan anyi ba ayi ba ke nan. Tunda tana samun kanta a wannan yanayin. Ya kawar da shirunsu da cewa: Kin san me nake so da ke? Girgiza kai ta yi ba tare da tayi magana ba. Yac: Gidanku nake son sani. Ta fito da idanu waje. Gidanmu? Ya daga mata gura alamun tabbatarwa. Tace ; Ayya ka MAKARO domin gidanmu yana da nisa. Yace Eh, duk nisan sa ina son sani. Tace Misra fa? Kasan kuwa nisan da ke da akwai daga nan zuwa Misra? Ya girgiza kai. Tace; Nisa ne mai tarin yawa. Yace: Ke ta ya kike zuwa kina kuma dawowa makaranta?
Ta yi dariya tac: Ai ni akan wani keken doki nake zuwa. Yace; Kinga ni ma sai na hau keken dokin naki ko? Ta sake yin dariya har tana tuntsirawa tac: Ai ba ka iya hawa. Yace: Saboda me?
Saboda ba ka da guri,

Please Login or Register in order to submit comment