Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai yi mana karamabani
Dama mun dade muna burin shan jininka , tunda kuwa ka kawo kanka faduwa ta zo dai –dai da zama . sannan za mu hada da tsoho rabi’u don kun ci kuin jini, kun sha kudin jinni, kun ji dadi da kudin jinni dole mu kaddamar da ku jiniku ya yi kuka
Cikin tsananin jarumata isah y ace
“ allah ya fi ku , do domin kuidn jinni ba mu da masaniya a kansu , allahi bay a kama bawa akan lain da bai sani ba .
Ina rokon allah kariya a bisa sharrinku, saboda ku mushirikai ne, ina mai tabbatar muku da ku tuba ga allah , don ka sha jini domin samun kyalen rayuwa me ka yi ? me kuka dauki rayuwa ne ?
Akwai fa tsufa, idan hisabi”
A fusace mataimakin shugaba ya yiwa Isah wata razananniyar tsawa bakinsa na fidda yahaki, idanusa na awalkiya suna sauya kaloli KORE, DORAWA zuwa BAKI.
Isah dai ya budi idan ya ganshi a daure, sun zagaye shi yayin da shuhuda ke faman rabsar kuka tana ba su hakuri, tana fada musu matsayin Isah da muhimmancinsa a rayuwarta.
Sun tabbatar mata cewa, yau za su sha jinin Isaha yanzu kuma ita zata yi jagorancin kisan nasa kasancewarta shugaba kuma sarauniyar matsafa.
A hankali ta tako gaban Isah idanunta dauke da wasu sirrika, amma zuciyarta na kuka akan abin da tasan yanzu ya zamar mata dole ta kasha Isah, anya zata iya bayar da jinin Isah wasu can su sha?
Isah da ke kallonta a ci kin zuciyarsa yana karanto ayoyi daga cikin alkur’ani bakinsa ya furta.
“Allah ga bawanka kada ka bar wadannan bayin naka su halaka ni, Ya Allah, Ya Ubanjigin Jibrilu da Mika’ilu da Israfilu, mai kaga halittar sammai da kassai, masanin fake da sarari. Kai ne kake hunkunci tsakanin bayinka cikin abin da suka kasance suna sabawa a gare ka na gaskiya.
Ina rokonka ka shiryar da su don su kasance masu saba maka, Allah idan ka so kai ne mai shiryarwa, Allah ka shiryar da su izuwa tafarki madaidaici.
Idan kuma ba masu shiryuwa ba ne, Allah bayinka ne na barka da su, ka tsare ni daga sharrinsu, ka kuma kwato min baiwarka shuhuda wadda azal ta fadawa ba ta ji ba ta gani ba, tunda tun tuna da kuruciya suka sanyata hanyar halaka. Allah ka tserar da mu daga sharrinsu”.
Ya yi kabbara mai karfi, y ace.
“Allahu akbar! Allahu akbar!! Allahu akbar!!! Walhamdu lillahi kasiran! Walhamdu lillahi kasiran!! Walhamdu lillahi kasiran!!!.
Take ya sake karanta suratul Waki’a sai ga daurin jikinsa duk ya zube. Cikin zafin nama ya janyo hannum shuhuda, amma sai ta soma togewa.
Ya sake yin kabbara, ya kuma maimaitawa sai kawai ya ji ita ma ta dauka, suka soma gudu.
Ba su dade suna gudun ba sai suka tarar da miyagun mutanen a gabansu. A yanzu zuciyar Isah ta soye bay a shakka, kuma bay a fargaba bakinsa dauke da Ayatul Kursiyyu yana karantunta a fili yana karanto surorin karshe na Suratyl Bakara a fili.
Tsoro tare da firgici ya shiga cikin zuciyoyin matsafan, don suna mamakin irin barnar da Isah ya yi musu, suna kuma ji suna gani gas hi yana neman samun galaba a kansu.
Cikin tsirkewar zuciya mataimakin shugaba ya kwo hannu da niyya shaker Isah, sai hannun ya kama da wuta, ganin haka sai gurin ya yi tsit, babu su duk sun bace.
Isah da shuhuda gudu suke bas u yi aune ba ga su jikin dutsen nan na kasar Sokoto, wato Dutsen Kwatarkwashi, suka fadi yaraf.
Shuhuda ta zabura ta kankame inna yaduwa ta ce.
“Don Allah kada ku bari su sake tafiya da ni, suna wahalar da rayuwata, sun takura min, ni dai wallahi ban yafe masa ba, cuce ni!”
Inna yaduwa tana kuka tana rika da shuhuda tana tuno rayuwar da ta yi, lallai akwai sakayya, shi yasa Hausawa suke cewa wata shari’ar sai dai Allah.
Ita ma addu’a aka ci gaba da tofa mata har bacci ya yi awon gaba da ita.
Zuri’ar Alh. Rabiu sun shiga fargaba da tarin tsoro saboda halin da suka tsinci kansu na samun jinisu cikin matsafa.
“Ina zargin kaina a bisa lalacewar Sagir, saboda tun farko shi yaro ne mai son kyale-kyalen rayuwa, a gaskiya na taka rawa wajen shigarsa kungiyar matsafa”.
Gaba daya suka zubawa tsohon ido, ya ci gaba da cewa.
“Abin da yasa na fadi haka shi ne, me yasa lokacin da Sagir ya soma tashen kudi farad daya ya zam mai arzikin gaske ban bincike shit a ya ya same su ba, wannan yan faruwa bag a ni kadai ba, al’umma baki daya. Me yasa ba zamu ringa bibiyar rayuwar ‘ya’ yanmu ba tare da sun sani ba mu gano su waye abokansu, ko a ofis ko kasuwar, amma idan yaro ya taka matakin balaga shi ken an sai mu zuba masa ido ba zamu san me rayuwarsa ta ke ciki ba.
Anya mun son samawa rayuwar iyalanmu jin dadi? Wai me muka dauki MATA’UL-HAYAT (kyale-kyalen rayuwa) ne a wannan zamani? Me muka dauki rayuwar kanta ma? Mu yi gida, mu sanya suture na alfarma, mu shiga motoci na gani a fada, mu auri mataye, me yasa kyale-kyalen rayuwa ya fi tasiri a cikin al’umane?”
Kuka sosai Alh. Rabi’u yake yi yana jin ciwon abin da dansa ya aikata.
Ya dago idanunsa fal da hawaye, ya ci gaba da cewa.
“misali akan Sagir, ya dauki shuhuda ya bayar da ita cikin matsafa, tun farkon rayuwarta cikin kunci ta taso, cikin maraici, ana yi mata wasarere da hankali, da muna yin kafi a gidajenmu irin wadannan shu’uman mutane da bas u shigo ba.
Ita shuhuda ya addinta ya ke? Ya karatunta ya ke? Amsar it ace, an birkita rayuwarta, an hanata jin dadin rayuwarta, an hana ta zam mutum. Ni abin da ya fi daure min kais hi ne, su matsafan bas a tsoron yadda rayuwa ta ke juyawa, ma’ana shin suna ta salwantar da jinin al’umma ya rayuwar bayansu zata kasance a lokacin da su suka mutu? Ba sa tsoron abokan huldarsu su yi ta dauki dai-dai cikin iyalansu?
Lallai wannan toshewar basira ne babba, kuma ba su tsoron Allah sun tabbatar ko tsafinsu bai kasha sub a lallai ne za su mutu tunda kuwa fadar Allah ce, kowance rai sai ya dandani mutuwa.
Saboda haka ya zamar wa iyaye dole su gano su wa ‘ya’ yansu ke abota da su, idan danka ya yi kudi ka sanya idanu ka gona ta ya ya same su, a kuma sanya tsoron Allah a zuciyar iyali, a bas u ilimi musamman ilimin islama, don tsoron Allah ya shigi mutum, ya gano tsafi abu ne na SHIRKA, ka yi arziki ta hanrtar halal, kuma idan Allah ya rubuto kai mai arzikin ne dole zaka yi shi, amma iyaye su ne mafi’ala su gano inda dansu ko ‘yarsu ta sa a gaba, domin ‘ya’ yanka ababen kiwo ne a gare ka.
Da ace ma mu iyaye muna kokarin samawa yaro sana’ar yi, misali ko a kasuwa zai yi kasuwanci ya kasance mune jagoransa, ko aiki ne mu zamu nema masa, lallai da an samu ragowar bara gurbi, saboda wasu yaran daga neman abin yin ne ake batar da su, ake jefa rayuwar cikin gurgataccewa duk saboda MATA’UL-HAYAT (kyale-kyalen rayuwa)”.
Alh. Rabi’u ya saurara yana sharer hawaye da gefen babbar rigarsa.
Inna yaduwa ta ce.
“Ni kam Sagir ya cuce mu, haihuwarsa bat a yi mana komai ba sai bakin ciki”.
Alh. Rabi’u ya daga mata hannu, y ace.
“Kuskuren da wasu iyayen ke yi ken an akan yaransu, ba ma iya dannar zuciyarmu dan ‘ya’ yanmu suka yi mana wa, ni abu, bakin iyaye ko masifa ne ga yaro”.
Ta ce, “to ina ranar haihuwarsa, ya mutu ya bar baya da kura?”
Alh. Sada ya ce.
“Ku yi hakuri, mun sha jin jita-jita game da hakan, to amma kun san yanzu rayuwa ta lalace, yawamnci hassada ta shiga zukatan al’umma , daga an ga mutum ya fara samun kudi ma sai ku ji an ce dan mafiya ne”
Alh. Ahmed shi ma ya magantu, ya ce.
“wannan abu dai ya riga ya faru, addu’a zamu dinga sanyawa ana yi masa, mu ma mu ringa aika Masada tamu don nema masa rahmar Ubangiji”
Shuhuda ta yi tsagal cikin bacin rai ta ce.
“B azan yafe masa ba, ya cuce ni, ya shafa min bakin fenti, na yi wata bahaguwar rayuwar, kullum tambayar da name yiwa kaina, wai ni mutum ce ko aljana, ko wata dabba ce daban. Amsar da na kasa ganewa ke nan”
Gaba daya shiru ya bakunci falon, Isah ya ce.
“shuhuda dukkan mai rai yana kuskure a rayuwarsa, ki yafewa mahaifinki, ki yarda da kaddara domin ke kika fi cancanta da ki yafe masa”
Ta ce, “To ko na yafe masa jinin al’umma da ya sha fa? Kun san abin da nake ji ace ka kasance dan matsafi, kuma ya sanya ka a hanyar tsafi, shi ke nan ni mai son MATA’UL-HAYAT ce? Shi ke nan…”
Sai ta sanya kuka.
.
Allah Sarki Shuhuda, hakuri ya zama dole...
Hada Hausa Book stories
MATA'UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA)
¤¤33¤¤
.
Karshe....
BABI NA ASHIRIN DA DAYA
GARIN BANZA..
Washegarin da abin ya faru, alh. Ahmad ya samu waya ake sanar masa gidan gonar alh. Sagir ya kama da wuta. Inaalillahi wa’inna ilaihi raju’un kawai yake karewa”
Wani irinci ciwon shuhuda ta kwanta bahu ci babu sha, kuma iyayenta bas u son su fita da ita zuma asibiti saboda tsoron azzaluman da ke bibiyarta.
Yakub ne ya zo da wani mani malami, don tunda suka dawo das u isa gida ya wucw zuwa birnin g taron fararen aljannu da sukan gudannar a irin wanna lokaci.
Har dakin da shuhuda ta ke kwance ma Islamic, masu bayer da magani na gargajiya don kauceuwa tarkon jinn.
Ya dubi isah bayan ya gama duba shuhuda ya ce.
“ga wasu magunguna nan da zata dinga amfani da su, sunnan ga addu’o’ in da idan tashi zata ringa yi ba ita bag a duk wanda matsafa ko aljannun suka dame shi, idan dai zai bi ka’. Ida zai raba das u.
Ayutul kursiyyu 30 bayan kowace sallah, amma sallar ish’I 40. La’ilaha illallahu wahadahu lasharikalahu lahul mulku wa lahul hamdu wahuwa ala kulli shai’in kadeer, kafa 100 bayan sallar asuba da sallar isha’i. idan ta zo kwanciya bayan adduo’in yau da gob eta karanta Ayatul kursiyyu 1 ta hura daya a damanta, daya a hagunta, daya a kafarta, daya a kanta. Sai ta hada hanneyenta ta karanta surorin farko aya biyar na Bakara, da Ayatul kusiyyu da ayoyi guda na karshe na Bakara amanar rasulu, sai ata sha ajikinta ta kwanta.kada ta tashi ta je ko’ina idan tasan da wata bukatar da zata yi, to kafin ta yi bukatar zata yi, in shaa Allahu ta fi karfin abin sharri mutum ko aljan.
DOKOKIN DA ZATA BI DON KAUCEWA MATSAFA DA SHAIDANUN ALJANNU.
Ta dinga yawan zama da alwala. Ta dinga yin bismillah akan duk abin da zata yi. Ta kaura da kallon finafinai hart a warke. Ta daina jin kide-kide. Ta daina zama babu riga ko dankwali. Idan da hoto a dakin a cire ko na tsuntsaye ne. ta dinga yawaita zikiri, irin wanda ya tabbata bakin manzon Allah (S.A.W).
MAGANI
Man habbatus sauda dan saudiya,itiliti garin babbar roba guda daya, shayin shaidanu guda 12, jan miski.
Wadannan su ne magungunan da zata yi amfani das u, ga ga ita kadai ba har ga wanda shaidanu suka dame shi, irin masu yin aljannu”.
Bayan sun tafi ne, sako ya iso gidan ganar ya karasa kamawa da wuta, yak one kurmus, duk abin da yake ciki ya zama toka. Sam Shuhuda bat a damu ba, amma dangin mahaifiyarta sun fi damuwa kwarai saboda sub a su san wainar da aka toya ba, su Alh. Sada su dama sun yi has ashen hakan.
*********
Uncle Hamza tun day a ga Isah ya juyo zuciyarsa ta karaye, ya sani yana son Shuhuda amma ba zai iya kassara rayuwarsa ba, (IRI DAYA DA OGA MUHSEEN )ya sha jin labarin shu’umancin matsafa ko jinnu, tabbas ba zai iya ba, dole ya turje ya dawo baya. Suka hadu da Yakub, ya kale shi yana murmushi, y ace. “haba Hamza, kada ka zama ragon maza mana, ko ba kasan mace ta fi son namiji sadauki, gwarzo a? mace bat a son namiji soko, hakika duk da haka na yaba da kwazonka, kasancewarka malamin makaranta sai nag a kana da iya mu’amalada kowa, kasan cewar malamin makaranta babban mutum ne a cikin a’umma mai iya mu’amala da kowa, malamin makaranta mutun ne mai juriya mai kwazo, mai himma amma duk da tarin baiwar da Allah ya yi maka sai gas hi ka karaya. Dama haka rayuwa ta ke, komai himmarka akan abu idan ba ka da rabo akansa sai ka samu sarewa”
Uncle Hamza ya yi shiru dai bai iya cewa komai ba, ya san dai zuciyarsa ba zai iya ba, kuma dama komai na rayuwa bay a tabbata said a niyya, idan har ka samu karfi a zuciyarka to kana saka ran samun nasara, shi kam ba zai iya ba.
Haka Yakub ya dauke shi ya dawo das hi inda ya dauke shi, ya yi alwala ya yi sallah ya fuskanci alkibla yana addu’o’ in da suka sauwaka a gare shi don samun sauki, yana rokon Allah ya karbi uzurinsa ya cire masa son shuhuda, tunda alamonin su nuna ba zai same ta ba har abada, koda Isah yana son shuhuda ba sai iya barwa wani ita ba.
Labarin da Uncle Hamza ya samu na rashin lafiyar shuhuda shi ya sanya ya nufo gidan su don ya je ya yi mata sannu da jiki.
Ya same ta a zaune a falo, amma tana kishingide jikin inna Yaduwa, ya ce.
“tun yaushe ne bat a da lafiya”
Ta yi murmushi, ta ce.
“Ai Hamza ta kwana biyu, yanzu kam sai ta samu sauki ma kwarai”
Ya kada kansa alamar gamsuwar, muryar Isah suka jiyo yana sallama, suka amsa masa ya shigo.
Uncle Hamza ya ji wata matsananciyar kunya ta kama shi, amma sai ya mazance saboda kada ya bayar da kansa.
Isah ya dube shi, ya ce.
“Ai ta ji sauki”.
Hamza yana son ya tambayi Isah yadda aka yi ya kwaci shuhuda, amma bai sami fuska ba, ya dake ya ce.
“Ina godiya ta Allah day a baka nasarar kwato marainiyar Allha. Ina yaba maka bias kokarinsa na amince ka fini juriya, ka fini karfin hali. Saboda haka Isah kai ka fi cancanta ka zamo abokin rayuwar shuhuda.
Kai ka fi cancanta ka zam miji a gar eta saboda haka ni na janye na bar maka ita.
Ina rokon Allah barku tare har karshen rayuwarku”
Inna yaduwa cikin zolaya, ta ce.
“Kai Hamza ya zak yi saurin karaya? Kasan ba a san mace tuwo ba sai miya ta kare”
Ya ce. “Inna, Isah ya fi ni cancanta”.
Ta yi murmushi, ta ce.
“Mun gode da kaunar da ka nunawa shuhuda duk da kasancewar ta cikin wani yanayi lallai soyayyarka gar eta ba kadan ba ce. Ina fatan zumuntarmu zata dore”
Ya ce, “Insha Allah”
Isah da Hamza sun zam abokai tunda har sukan kaiwa juna ziyara, shuhuda ta samu sauki kwarai tana fita tana yawo, duk inda ta ga dama babu yadda matsafa zasu yi da ita, saboda ko inda ta ke bas a iya karasowa.
Shi ma Isah ya fi karfinsu saboda mutum ne ABIDI, ma’ana mai yawan ibada.
Cikin dare shagunan shuhuda da ke cikin kasuwar kwari suka kama da wuta, hankalin Alh. Rabi’u ya tashi kwarai, amma ita shuhuda ko a jikinta, don da zasu bi shawararta ma da an sadaukar da dukiyar gaba dayanta tasan kuma dole zata kare, domin kyalkyal banza ce, kuma dama GARIN BANZA a farau-farau banza yake karewa.
Mabiya kungiya sun tashi da tashin hankalin mutuwar mataimakin shugaba, sun damu tun daga nan wasu suka soma yiwa kungiyar tawaye tunda dama babu wanda ke gundanar da mulki kamar mataimakin shugaba, sai suke gudu wasu kuma suka yi gamayya da wata kungiyar saboda sama akwai abota a tsakaninsu.
Wannan dalilin ya tashi hankalin tsafinsu inda ya bas u tabbacin jinin shuhuda da Isah ya zam dole a sha shi, amma an rasa ta inda za a kama su, hakan ya sa Yakub da ke kallonsu ya sanar da Isah da shuhuda suka nufi kasa mai tsarki don yin umra, suka yi dawai don samun rinjaye akai.
Allah ya bas u nasara gaskiya ta fi karya, alkur’ani waraka ne, sun ce gaba da karantun alkur’ani a masallacin Makka, sanna suka ziyarci Manzon mu a can Madinatul Munawwara.
Cikion kudirar Ubangiji dakin tsafin nasu ya kama da wuta, duk wasu manyan bokayensu da suka yiwa biyayya Allah ya karya su, duk abin da suke tinkaho das hi ya lalace, wasu daga cikinsu Allah ya ganar da su, sun shirya, wasu sun mutu, wasu sun samu tawaya ta rasa wani bangare na jikinsu, wasu kuwa hauka tuburan suka dinga yi, haka komai ya lalace musu.
Shuhuda ta kubuta daga sharrinsu, ta samu lafiya, ta samu jin dadin da ta rasa.
BABIN KARSHE
RAI DA RABO
Jin dadin rayuwa ya samu ga shuhuda Sagir Rabi’u, yanzu ta gano Isah Sada abi’u shi ya sama mata jin dadin rayuwar da ta rasa. Yanzu shuhuda ta zam mutum kamar kowa. Dama can ita yarinya ce mai nutsuwa ga kaifiyya, a yanzu ma abin haka ya ke, ta samu gurbin karatu a B.U.K Kano, yayin da ta tsunduma neman ilimi ka’in da na’in, a yanzu ta dawo baya saboda samun waraka ma’ana tun farko ta soma karatun alkur’ani ta dantsama a sira don sanin tarihin manzannin Allah, kawa ‘idi, Ahlari, Ishmawi, Izziya duk cikin kankanin lokaci ta yi nisa, dama can ita yarinya ce mai kwalwa.
Idan ta samu hutu tana kai wa mahaifiyarta Haj. Karima ziyara can karare.
Dama an bat a dama ne saboda ta samu ilimi cikakke domin a da tana rayuwa ne ga ta nan ga ta nan, shi kuma Isah yana can Ibadan a ma’ikatar da yake aiki, yana samun dudi sosai a rayuwa, domin Allah ya yi masa nasibi.
Ya samu dauka kwarai da gaske, ya kuma fantsama harkar kasuwanci, samun kudin Isah ya tada hankalin Alh. Rabi’u ta inda ya yi kiran mahaifin Isah Sada ya fada masa abin da ke cikin zuciyarsa. Hausawa sun ce, idan maciji ya sare ka to idan ka ga bakin tsumma zak tsorata.
Sun sanya masa ido sun bi komai daki-daki, kuma bas u same shi da wata badala ba, hakika dukiyarsa wankakkiya ce, a yanzu an maida shi Abuja kuma ana ta shirye-shiryen yi masa biki da shuhuda.
Shuhuda kwance idanunta na zubar da hawaye. Inna yaduwa ta shigo ta samu gefenta ta zauna, ta ce.
“Anya shuhuda rayuwa zata samu haka?”
Ta daga idanunta dubi inna yaduwa ta ce mata.
“dole ne na yi kuka inna, da ban san komai a rayuwarta ba, duk abin da ya faru gare ni wai-wai nake ji, nasan dai ina rayuwa ne tare da matsafa, ina kuka ne don ina jin tsoron haduwata da Allah”
Inna yaduwa ta ce.
“haka ne shuhuda, amma ina so ki sani Allah ba ya kama bawa da laifin da bai aikata ba, sun juyar miki da tunani ne tun kuruciya”
Sallamar Haj. Karima ta katse ta, ta shigo Inna yaduwa ta yi mata lale marhabin, bayan ta zauna inna yaduwa ta ce.
“Gwanda da Allah ya kawo ki, yarinyar nan taki ta dauki abin nan da ya faru ta saka a zuciyarta, kowane mai raid a irin kaddararsa, ki yi hakuri kinji shuhuda”.
Ta sanya hannu tana goge idanunta da suka yi jijir saboda kuka.
“Ni ina jin haushin Baban ne, ina ji a raina ban yi sa’ar mahaifi ba, in jin haushin Ummata da aure shi, saboda kila don yana da kudi ne ta aure shi, me yasa bat a nema min uba na gari ba?”
Murmushi kawai Haj. Karima ta yi, tana jin radadin kalaman ‘yar tata, tasan auren soyayya suka yi da Sagir duk cewar lakacin da ta aure shi yana da abin hannunsa, amma dukiyarsa ba ta rufe mata idanu ta so shi ba, kuma har yanzu tana jin soyayyarsa a ranta, ba don Alh. Jamilu ya yi mata rukon mutumci ba, kila da har abada ba kuma wani auren ba, tana kuma yi masa addu’ar Allah ya yafe masa kura-kuranse.
Ba karamin rudewa ta yi ba a lokacin da inna yaduwa da Isah suke kora mata bayanin abin day a faru ba, saboda sam Sagir a mu’amala mutumin kirki ne, kila da ya yi TSAWON RAI za ta iya gano illar halin day a sanya kansa.
Hawaye na bin kumatunta ta dubi shuhuda, ta ce.
“shuhuda ke yanzu ba yarinya karama ba ce, domin aure ne a gabanki, ke yanzu kina shirin zam uwa, shin kina irin wannan halin wace tarbiyya za ki ba wa ‘ya’ yanki? Kin san kaddara kuwa? Kin san me ake nufi da kaddara? Shin kin yi imani da Allah kuwa? Ina da ja a kan ki shuhuda, ni mahaifiyarki ce zan sanar da ke abubuwan da har yanzu nag a tunaninki bai zo kai ba.
Kin yi imani da Allah kuwa, ko har yanzu tsafin na cikin kwanyarki ne? ko har yanzu ba ki zam cikakkiyarki mutum kamar mu ba? Bari ki ji abin da ake nufi da imani.
IMANI DA ALLAH
Abin da ake nufi da imani da Allah shi ne, ki yi imani da Allah da kyakkyawar zuciyar, ki shaida cewa akwai Allah, kuma Shi ne mai kowa mai komai, Shi ne wanda Ya kagi duniya da lahira da duk abin da suke a cikinsu. Idan hakan ta samu, toh lallai za ki so Allah, domin son Allah wajibi ne, idan kin so Shi za ki girmama Shi Zuciyarki. Ya zamar wad an adam wajibi ya so Allah, ya kuma girmama Shi, idan mutum ya kasance haka zai guji sabawa Allah da manzanSa, zai kuma nisanci abin da Allah Ya hana idan haka ta samu mutum zai samu jin dadin rayuwa a nan duniya da lahira, kamar fadin Allah (S.W.T) a cikin alkur’ani mai girma.
“wadna ya aikata aiki na gari mace ko namiji a halin yana mumini wallahi zamu rayarda shi rayuwa mai kyau, kuma wallahi zamu saka musu ladarsu da mafi kyawun abin da suka kasance suna aikatawa”.
IMANI DA MALA’IKU
Kuma idan kana son zama cikakken mai imani dole ka yi imani da Mala’ikun Allah (S.W.T), Shi Ya halicce su, Ya sanya su su dinga gadinka a matsayinka na dan gatan bawanSa. Idan mai imani ya tuna haka zai dada son Ubangiji har ya ji yana da GIRMA sosai, saoda kulawar da Yake bas hi, hakan kuma zai sad an Adam ya godewa Allah.
IMANI DA LITTATTAFAI
Amfanin imani a zuciyar dan Adam zai sa kasan HIKIMAR ALLAH da kulawarsa ga bayinsa dalilin littattafan da Ya saukar wa kowace al’umma. Hakan zai samu gane hikimar Allah cikin abubuwan da Ya shr’antawa kowace al’umma, domin su fuskanci littattafan da suka dace da zamaninsu, sai Ubangiji Ya maida karshen wadannan littattafai shi ne ALKUR’ANIL KAREEM, wanda ya dace da halukan kowa kamar yadda kuma ya dace da kowanne zamani, kuma kowanne bigiri har ya zuwa ranar kiyama. Kai mun godewa Allah da Ya yi mana ni’ima da saukar mana wannan littafi mai tsarki.
IMANI DA MANZANNI
Dole ne mu so manzannin Allah (SWT) domin Allah Ya aiko mana da Annabawa masu daraja da girma don su zama shirya a gare mu, ya kuma aiko mana da fiyayyen halitta don ya zama cikimakin Annabawa. Hakan zai sa mana son Annabawa ya sa kuma mu girmama su, mu yaba musu domin su ne Manzannin Allah, su ne kebabbun bayinSa da suka tsaya akan bautar Allah da isar da sakonsu da yiwa bayin Allah nasiha suka yi matukar hakuri abisa duk wata cuta da ta su a cikin wannan aiki nasu.
IMANI DA RANAR LAHIRA
Dole ka yi imani dar ranar lahira hakan zai kwadaita wa mutum bautar Allah Ta’ala t inda zaka yi kwadayin samun ladan lahira, zai kuma sa mutum ya nisanci sabawa Allah a cikin ranar lahira ne wadda ya guji MATA’ULHAYAT (kyale-kyalen rayuwa) zai shakata da ni’imar Allah, ya ji dadin ladan aikinsa”
Shuhuda jikinta ya yi sanyi da jin bayanin haifiyarta, ta yi sa’ar uwa wacce ta ked a ilimi, sai dai ba ta yi sa’ar uba ba, da ace yana da ilimi kila da bai shiga kungiyar matsafa ba.
Kamar mahaifiyarta ta karci zuciyarta, ta ce.
“Zan miki bayani akan IMANI DA KADDARA, domin na sanar da ke kowanne rai bay a tsallakewa akan abin da Allah ya kaddara masa.
IMANI DA KADDARA
Idan kin dauki kaddara kin yi imani da Annabawansa, dole ki yi imani da kaddara mai kyau ko mara kyau. Idan ka yi

Please Login or Register in order to submit comment