Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komawa ta zauna a gidan abokin mahaifinta inda ta soma zama ganiyar karatunta. Suna ta yawon kallon dabbobi, kowanne a cikinsu yana nuna abin da ke burge shi na daga dangin dabbobi. Sun zo layin da ked a akwai zakuna, sun tsaya a dai-dai kejin wani zaki suna kallo, kawai sai sager ya ji an ambaci sunansa. Dago kan da yake suka yi tozali da Izra’el, nan take suka rungume juna cike da jin dadi. Sun dau lokaci a wannan hali kafin daga bisani sun saki juna suna kallo-kallo a tsakaninsu.Sagir ya ga sauyi sosai a tare da Izra’el mamakinsa bai boyu ba, saboda shigar day a yi ba karamar shiga ba ce, shiga ce irin ta wadanda ke jin dadi, duk da dama mahaifan Izra’el masu kudi ne, to amma ga dukkan alamu yanzu sun fi kudi. Izra’el y ace, “mutumina yanzu wane aiki ka ke?” Sagir ya girgiza kai, y ace”bana aiki, na dai gama karatu ina ta neman aiki ban samu ba”. Murmushi Izra’el ya yi y ace “aiki a kasar nan ai wahala ne, idan bad an wane kake ba baza a taba baka aiki ba”. Ya ciro wani kati(comlementory card) daga aljihunsa, yace. “yanzu dai babu isasshen lokaci, amma ka same ni a gida sai mu tattauna”. Ya karashe maganar yana mika masa katin Sagir ya sa hannu ya karba, a haka suka rabu. Kwana biyu a tsakani day a shirya ya yi amfani da adireshin da ke jikin katin ya je gidan Izra’el, gida na alfarma wanda ya kunshi duk wani nau’in abu na shagalta, ko kafin Izra’el ya fito daga daki, said a Sagir ya yi kauyanci. Yana fitowa, tsoron ma hada hannu da shi ya yi don gaisawa, sai zubewa ya yi a kasa yana gaishe shi.
Dariya Izra’el ya dinga yi, sannan ya tayarda Sagir ya zaunar da shi saman kujera, su kadai ne a falon, sai mai aiki da t agama zube nau’o’in ababen cid a na sha, ta fice. Sagir ya gaza hakuri y ace. “kai mutumina, yaushe Bos dinka ya zama hamshakin mai kudi ne haka?” Izra’el y ace. “a’a duk abin da ka gain a gidan nan mallakina ne, ni na hada komai da kudina da kuma gumuna, domin bayan tafiyata karatu mahaifina ya rasu, yanzu haka ni ke rike da duk dawainiyar gidanmu ba kuma da gadon mahaifina ba”. Mamaki ya sake mamaye zuciyar Sagir, ya dinga dube-dube, fuskarsa na nuna matukar kauyancinsa.
Izra’el ya yi murmushi, y ace “to yanzu dai fara cin abinda da aka ajiye maka kafin mu shiga tattaunawa”. Hka ya ci abubuwan da aka jera masa shi kuma Izra’el ya koma cikin wani daki, jim kadan ya dawo hannunsa dauke da wata ‘yar karamar jaka, ya ajiye ta a gafe, ya zauna akan kujera yana kallon Sagir har ya kamala. Sannan suka gaisa tare da tambayar juna bayan rabuwa. Izra’el y ace, 2Sagir na tausaya maka matuka, acebsaurayi kamarka babu ‘yan cnji ko aikin yi akwai fargaba, amma kada ka damu, ni zan taimakeka saboda shakuwar da muka yi da kai, zan sama maka aikin yi ko don abotar da ke tsakaninmu tun kuruciya, sai dai akwai sharadin d azan gindaya maka muddin ka amince shi ken an”.
Cikin zakuwa Sagir y ace da shi “wani sharadi ne?”
Izra’el ya yi murmushi tukunna y ace masa yana kallon kwayar iadanunsa. ‘”a’a ba yanzu zan fada maka ba, ka dai bi ni sannu a hankali”. Haka suka ajiye Magana, da zai tafi Izra’el ya damka masa wannan jaka day a fito da ita, wadda ke dauke da manyan agoguna guda hudu kowacce daya zata kai dubu goma, sai tsabar kudihar na dubu talatin.
Sagir ya rude, ya rasa inda zai saka kansa don dadi, ya shiga zabga masa godiya tamkar an ba shi kyautar aljanna. A takaice sun ci gaba da haduwa a lokuta mabanbanta, da haka har yawon dare suke zuwa, tukunna Izra'el ya bullowa Sagir maganar aiki. Iya kaduwa ya kadu da ya ji irin aikin da Izra'el din yake ikirarin ya samar masa, wannan shi ne dalilin dauke kafarsa ga gidan Izra'el, amma ko da aka dauki lokaci ba su hadu ba, sai ya ji zuciyarsa ta karaya, har ya amincewa kansa zama daya daga cikin 'ya'yan kungiyar safara da shan jinin mutane...." Ko da Abubakar ya zo nan a labarinsa, gaba daya sai gurin aka dauki salati. Inna Yaduwa kam fashewa ta yi da kuka. Abubakar ya ci gaba da cewa, "Tun Sagir yana dari-dari har ya bada kai bori ya hau, ya je ya samu Izra'el ya sanar masa ya amince. Gudun kada a gano shi tunda ba aiku yake ba, kada a ganshi da manyan kudade a zarge shi da wani abu, sai daya daga cikin 'y'yan kungiyar ya sama masa aiki a ma'aikatar kula da tsirrai na jihar Kano. Tashin farko abin da dodon tsafi ya fara bukata ga sagir shi ne jinin Akkina a matsayinsa na wadda ya fi so fiye da kowace mace. A ranar sam bai samu yin bacci ba saboda yana tunanin yadda zai iya sadaukar da Akkina ga dodon tsafi bayan dumbin son da yake yi mata. Sai da ya dauki tsayin kwanaki hudu a halin damuwa da rashin sukuni, sannan ya amince. Ya tsarata akan zasu je Abuja holewa kamar yadda sukan yi, amma ba ya son kowa yasan da tafiyar, don haka ta yi karya a gidan da ta ke zaune cewar zata je can gidan su mahifarta. Wannan shi ne dalilin da ya sa har yau iyayenta ba su san yadda aka yi da gawarta ba. Bayar da Akkina ga dodn tsafi ya kara samarwa Sagir daukaka a kungiyarsu, sannan hakan ne ya sa ba wanda yayi zargin ta ya ya samu wadannan dukiyoyin nasa. A kungiyar tasu akwai Hausawa da yawa a ciki, irinsu Alh. Badaru mataimakin shugaba, Alh. Nuraini da dai sauransu. Alh. Sammani shi ne mutumin da kusan suka shiga kungiyar a tare, shi mutumin jihar Jigawa ne, a shekaru ma za su kusan sa'annin juna. Bisa ga yadda shugabancin kungiyar yake shugaba wanda yake akan karagar mulki shi ne mai alhakin zabar wanda zai maye gurbinsa a lokacin da wani sanadi ya taso, ko mutuwa ko kuma rashin cika ka'idojin shugabancin kungiyar. To tun kafin daya daga cikin wadannan abubuwa biyu su taso yake zabar magaji wanda zai gaje shi. Wanda yake shugabancin kungiyar a lokacin wani inyamuri ne mai suna John, tun lakacin da Sagir ya shiga kungiyar ya kasance yanna kaunarsa, don haka shi ne ya kasance yana kaunarsa, don haka shi ne ya zaba a matsayin MAGAJINSA, wanda hakan bai yiwa da yawa 'ya'yan kungiyar dadi ba, ganin cewa akwai waganda suka shafe Sagir a shekaru, kuma akwai wadanda suka fi shi dadewa a kungiyar, bugu da kari ma akwai wadanda sunfi shi gogewa a harkar tsafin nasu, amma ace Sagir shi ne zai shugabance su?
Wannan dalilin ne ya sa aka yi ta cece ku ce a tsakaninsu,sun manta da cewar muddin shugaba ya fidda Magaji shi ke nan maganar ta zauna, ko da shi shugaban ne ba zai iya kankare abin ba. Wannan tsari ne na abin tsafinsu, don haka ya koma gefe yana kallonsu sai da daya daga cikinsu ya samu nutsuwa ya tuna da wannan tsari, tukunna ya tunatar da sauran. Dole ba don sun so ba suka amince da wannan zabin magaji. Ana ta gudanar da rayuwa ne cikin jin dadi da shagaltar MATA'UL HAYAT (kyale kyalen rayuwa), babu mai tunawa da wani imani a zukatansu. Sagir ya samu sararin bude gidan gona kamar yadda wannan buri ya jima aransa, don shi kam yana sha'awar tsirrai. Shekarar da zai yi aure ne john ya mutu shugaban kungiya, don haka aka hada hidimar aurensa da nadinsa shugaban kungiyar. Isan ba zaku manta ba, akwai mutanen da suka halarci bikin da dorayin kaya ajikinsu a gurin partyn auren, harma aka so yin rigima da wani daga cikinsu shi da wata budurwa da ta nemi cin zarafinsa, wadda ita kuma ta kasance dama yarinyarsa ce, ta gano matsafi ne, ta rabu da shi, da kyar aka samu aka fitar da ita tana cewa jininta ya fi karfinsa. Ina tunanin a lokacin ba wanda ya gane abinda ta ke nufi, shi yasa ba azurfafa bincike ba aka fitar da ita, karshe kuma jinin nata bai fi karfinsu ba, domin sai da aka mikata ga dodon tsafi ya sha jininta. An samu tsayin shekaru uku da auren Sagir, Amma ko batan wata Karima matarsa bata taba yi ba, hakan bai dame shi ba, sai dai ita Karimar ce ta ke cikin damuwa akan rashin haihuwarta. Duk kawaicin da ta ke da shi, sai da wata rana ta shawarce shi da suje asibiti a auna su a gano wanda ba shi haihuwa a cikinsu, ya yi biris da ita, sai ta saka masa kuka tana cewa, ita ta amince idan shi ne ba ya haihuwa zata ci gaba da zama da shi muddin ranta. Yayinda idan aka samu akasin haka tana shawartar shi da ya kara aure, saboda a duk lokacin da aka kawo Isah (lokacin yana dan yaye) gidan hankalinta tashi yake, ta dinga fatan Allah Ya ba ta hauhuwa. Ya yi shakulaton bangari da zancen natam saboda shi bai ga wani abin doki ga haihuwar ba, duka shekaru uku da aure har an isa a soma karafinn rashin haihuwa? Ganin yadda bai damu da damuwarta ta rashin haihuwar tasu ba, ga kuma fuskanta da ta yi a duk lokacin da ta yi maganar ransa na matukar baci sai ta daina yi masa maganar, ta rungumi hakuri tare da rokon Allah ba dare ba rana akan Ya bata haihuwa. An samu shekaru biyar cur da yin auren Sagir babu wani bayani na game da haihuwa, don haka su duka ma sun fitar da rai da samun haihuwa a gare su, suna ganin dama can su din ba masu kwan haihuwar ba ne. Wata ranar litinin ce aka yi zama cikin sirri irin nasu na masu sirri, 'yan kungiya suka taru kamar yadda akasari suke gudanar da taronsu a ranakun littinin domin ta fi kowacce rana muhimmanci a gurinsu, kasancewar a ranar ta littinin ne aka kafa kungiyar, kuma airin ranakun littinin din ne shuwagabannin da suka shude suka hau kujerunsu, don haka sun fi yin taro a wannan rana. Sai dai idan wata bukata ce ta taso musu ta gaggawwa, wannan za a iya gudanar da taron a kowace rana ta kama. Taron na wannan ranar ba shi da armashi, domin sun taru ne akan korafin tun da Sagir ya hau karagar mulki bai fitar da Magaji ba, ga shi har ya shafe shekaru biyar, wanda azahirin fitar da Magaji, domin yadda yake jin dadin Mulkin nasa, yana ganin kamar idan ya fitar da Magaji to wa'adi na iya riskarsa a kowane lokaci. Amma a ranar 'yan kungiya suka uzzura masa har suna ikirarin ya karya doka daga cikin dokokin da kudin shugabancin nasu ya tanadar, wanda bijirewa hakan akwai hukuncin da aka tanadar. Cikin bacin rai ya yi SUBUL-DA-BAKA ya ce. "Tunda kun matsa lallai sai na fitar da Magaji kamar yadda kuka sani, Shugaba ne kadai yake da damar zabar magajinsa, idan kuwa ya zba ko shi bai isa ya ce ya sauya da wani ba. Don haka ni ma a yau zan bi jerin takwarorina, zan fitar muku abin da kuke so, zan fitar muku da Magaji yanzu-yanzun nan. Magajin kuwa shi ne, duk abinda na haifa, ma'ana dan cikina shi ne magajina, shine wanda zai ci gaba da mulki bayan gushewata daga doron kasa".
Dukkansu sai suka kama kallon-kallon, domin dai sun san Sagir bai taba haihuwa ba, amma wai dan da ya haifa shi ne magajinsa. Alh. Sammani shi ne ya soma magana, ya ce. "Honourable, dama kana da da ba mu sani ba?" Sagir ya girgiza kai, ya ce. "Ba ni da ko kwai, amma hakan da na fada shi ne hukunci fakat!"
.
(Wato bai son sauka daga KAZAMAR MULKI!, ni kuma na ce da kyakkyawar mulkin ma ai, MUTUWA BATTA KYALE WANI DAN WANI........(Sadin Mama))
.
Alh. Nuraini ya ce. "Isan kuma ka gushe ba ka haihu ba fa?"
Bai ba shi amsa akan hakan ba, sai ya ce. "Na sallami kowa bana bukatar jin wani cece ku ce daga gare ku".
Shi a tunaninsa wannan karamin al'amari ne, sam bai taba nadama akan wannan hukunci da ya yanke ba. Sai da aka wayi gari Karima ta samu ciki, wannan rana ita ce ta zamo RANAR NADAMA agare shi, ya shiga kuncin zuciya, ya shiga damuwa ainun har Karima ta rasa gane kansa. Yayin da ya kai labarin a kungiya ba karamin dadi suka ji ba, musamman mutanen da suke adawa da shi, dalili kuwa shi ne, suna ganin Sagir ya gina ramin mugunta ne ta zabar abinda ya haifa ya zamo magajinsa a tunaninsa ba zai samu haihuwa ba, sai ga shi ramin ya burma da shi tsulum!
Babu wanda ya jajanta masa bare ya ba shi wata shawara don gujewa faruwar subul-da-bakan da ya yi, shi da kansa ya shiga laluben hanyar da zai magance matsalar abin ya ci tura.
Ya yi tunanin ya fita daga kungiyar, amma gudun abin da zai biyo baya shi ya hana shi fita, daga baya ya yi na'am da wannan BAHAGON HUKUNCI da ya yiwa kansa, ganin cewar ai da bai taba haihuwar ba, hasalima bai yi tunanin zai haihu ba. Tunda kuwa yanzu za a soma akwai alamar za a ci gaba da haihuwar agidansa, shi ba komai yake jiwa tashin hankali ba, sai ganin shi da kansa ya kai abinda ya haifa kungiyar shan jinin mutane, ina zai kai wannan abin kunyar yayin da kwai ya fashe? Dole dai ya hakure rayuwa taci gaba da tafiya har aka samu watanni takwas rannan abib tsafinsu ya bukaci jinin dan Alh Sammani, ai kuwa duk ya rude ya kidime ganin cewa da daya yake da shi, amma yana gani zai rasa shi? Ga shi yana yiwa dan matsanancin so, yayi juyin duniya akan a hakura da jinin dansa, amma ba wanda ya kula shi saboda sanin ka'idojin kungiya.
Daga karshe ma wani da ke kira Madu ya harzuko masa da ruwan masifa cewar, lokacin da dodon tsafi ya bukaci jinin mahaifin Madun waye ya hana? Alh Sammani wani irin bahagon mutum ne, yana da bakar zuciya, sannan ba ya hakuri da daukar fansa. A dalilin bukatar jinin dansa da dodon tsafi ya yi ya sa shi shiga cikin rudu da tunanin hanyar daukar fansa ta ayyana masa ya bi duk hanyar da zai bi ya kawar da Sagir in ya so daga bisani ko ta halin kaka shi sai ya hau karagar mulkin yadda zai fanshe jinin dansa, ya dinga yiwa 'ya'yan kungiyar dauki dai-dai da iyalansu.
Saboda haka shige da ficensa ya yi yawa wurin ma shahuran bokaye duk da kasancewarsa gogaggen matsafi masani sosai a harkar, hakan bai sanya ya san wasu hanyoyi da zai assasa mutuwar Sagir cikin sauki ba, don haka bin bokaye shi ne abin da ya ke dacewa a gareshi.
ada Hausa Book stories
MATA’UL HAYAT(JINDADIN RAYUWA)
¤¤30¤¤
Kafin a samu nasarar abin da yake so, said a aka yi wani gagarumin aiki, wanda ya boye duk wani shiri da Sammanin ke yi bare har Sagir ya gane ya dauki mataki, shi ma shirin kafin yinsa said a aka halakar da mutane uku, don wani shahararren boka ne mai gain har hanji ya yi aikin. Bayan ya tabbatarwa Alh. Sammani cewar, matsawar ana son kawar da Sagir sai an yi wannan shirin. A cikin wannan shiri da aka yi akwai wasu bayin Allah guda uku da suka so tarwatsa shirin, to suma said a bokan ya daure, daurin talala cikin boyeyyen sirri da surkulle irin na mushirikai wadanda Allah ne kadai yake iya karya shirinsu, tunda yasan shi bai isa ya kawar da su daga doron kasa ba. An samu nasarar kowanne shiri da aka yi, wanda ana gobe rasuwar Sagir aka zo gidan gona cikin sirri aka kafa tarkon a dai dai inda yak e ajiye motarasa. Washegari da safe shaukin abin ne ya dinga fizgarsa har yah an masa sukuni, yana son yin kiran gaggawa a kungiya don tattaunawa, amma kasala ta hana shi. A lokacin ne Haj. Karima ta kira shi a waya ta sahida masa Haj. Asmo ta zo daga Katsina. A lokacin kuma ne da zai tafi gida Alh. Sammani ya zo a ofis dinsa, wanda y agama bulbule jikinsa da turarukan da bokan ya ba shi. Ma’anar turaren shi ne, matsawar ya yi tozali da Sagir ya ji kamshin turaren kafin mai afkuwar ta afku, to ba shakka shi ne zai hau karagar mulki sabanin abin da matar Sagir zata Haifa akasin da aka samu bokan y ace kada ya yarda ya yi Magana da wani yayin day a saka turaren, har sai ya je gurin Sagir. To amma day a shigo gidan gonar akwai wadanda suka gaishe shi ya amsa musu, wannan shi ne sanadin day a sa Sagir bai ji kamshin turaren ba. Bayan sun gama tattaunawa game da batun daukar dan Alh. Sammani da za a yi abai wa dodon tsafi, suka rabu lokacin ne Sagir ya fada tarkon da aka kafa masa, ya yi tuntube da kahon LIBHAS wanda aka samo daga kasar Sin, cikin surkullen bokan Alh. Sammani, ya dinga aman jinni har zuwa asibiti…”
Ko da Abubakar ya zo nan alabrinsa sai ya ja baki ya yi shiru, yayin da su kuma duk kasala, damuwa, firgici da komai ma suka lillube musu jiki. Inna Yaduwa kuka ta ke kamar ranta zai fita, shi kansaAlh. Rabi’u kwallan ne a idanunsa, Alh. Sada yace, “Subhan Allahi, tabbasa biri ya yi kam da mutum, akwai lokuta da dama da na dinga mamakin irin dukiyar da Sagir yake da ita, ashe akwai sanadin samuwarta?”
Yakub ya karbi zancen da cewa, “wannan shi ne sanadin duk wata matsala da ta faru, abin al’ajab ko rudani da kuka ga sun faru da Shuhuda duk sanadin hakan ne.kamar yadda na fada muku labarin yana dauke da bangare uku, kuma kowane a cikinmu yana da bangaren da zai bayar, to kun ji bangare daya, sannan muna rokonku da kada ku yi fushi ku yafewa da uwanku, kuma danku abin day a aikata, ko don ya samu sassauci”. Babu wanda ya tanka, shi kuma ya ci gaba da cewa.”kafin wani daga cikin mu biyun nan y ace wani abu zan sanar da ku wani abu day a faru, yayin da Sagir ya zo rasuwa Alh. Ahmad ya ga idanuwansa sun sauya launi daga fari da baki kamar yadda idanunsa suke, zuwa launin KORE, DORAWA da BAKI. Tabbasa hakan yana da nasaba da sirrin tsafinsu duk wanda zai mutu dan kungiyar ko kuma aka sha jininsa ta wannan hanyar to sai anga wadannan launuka a idanunsu” ya karashe maganarsa yana duban Uncle Hamza, ya dora da cewa. “nasan daga kai Hamza har Isah kun yi tozali da abubuwan al’ajab daga ciki hard a sirrin NETWARK, sirrin sauya suffa dama dai sauransu. Tun da zare daya na labarin ya kamala, Shuhuda ita zata kamo zare na biyu wanda ke dauke da sirrin NETWORK da wasu abubuwa da suka faru su ma cikin sirri”. Ya yi furucin yan duban Shuhuda Ibn Khaddab. Ita kuwa ta gyara zama sosai tana fuskantar mutanen da ked akin, sannan cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, ta soma fadin cewa:-
BABI NA SHA TAKWAS
SAKAKKIYA
Yayin da aka haifi Shuhuda ‘ian kungiya sun ji dadi matuka, koda yake akwai alhinin rasuwar shugabansu a tare da su da suka wayi gari bakatantan, to amma wannan bai hana su farin ciki ba. Idan an cire Alh. Sammani wanda tunda ya bar gidan gonar bai zame ko ina ba sai gurin bokansa ya sanar masa ya aikata duk abinda y ace ya aikata. Bokan ya fashe da dariya, sannan y ace. “sammani ka yi kuskure gurin aikata abubuwan da an ace maka tun a gida lokacin da zaka fito ka yi amfani da ruwa, wanda n ace maka kada ka kusanci ruwa yayinda ka fesa turaren. Sannan da ka je gidan gona kafin ka isa gurin Alh. Sager ma’aikata sun gayar da kai, kuma ka amsa musu, ko mantawa ka yi, ko kuwa duk girma da isr ce suka janyo maka? Don haka aiki bai yi kyau ba sam-sam. A bangare daya ne aka sami nasarar wato mutuwar Sagir, domin tabbas ya yi tuntube da kahon dama ka’idarsa na muddin mutum zai yi tuntube dakahon libhas shi lallai babu makawa sai ya tattara inda ba a dawowa. Sai dai an haifi ‘ya mace wadda it ace magajinsa a kungiyarku kamar yadda tsarin kungiyar ta ke, samun galabrka kuwa zai yi wuya”. Tun day a ji wannan bakin labarin hankalinsa ya dugunzuma ya tashi, sun rabu da bokan akan idan wata bukata ta tashi zai dawo masa. A lokacin da aka haifi Shuhuda an ganta tana tsotsar hannu wanda aka yi tunanin sanadin bakunta ne ko kuma tana jin yunwa, wanda a zahiri ba haka ban e, babban makasudin tsotsar hannun Shuhuda shi ne, don nusar da ku akwai wani boyayyen al’amari a tare da ita mai bukatar tallafi, amma ba wanda ya yi tsinkaye da hakan. Idan ba ku manta ba a labarin da Abubakar ya bayar yanzu ya sanar da ku cewa, akwai wasu bayin Allah guda uku da aka daure yayin hada tarkon kawar da Sagir daga doron kasa, hakika su wadannan bayin Allah ba mutane ban e , ALJANNU ne masu alaka da KHASHIM TSAGEM, ai kun gane ko wan a ke nufi ko?” cikin mamakin yadda yarinya karama ke ta lailayo labari Alh. Rabi’u y ace. “Idan na fahimce ki, kina nifin kakana wanda ya haifi mahaifina?” t ace, “Tabbas shi nake nufi, wadannan bayin Allah sun kasance masu yiwa Khashi Tsagem hidima tun zamanin yana mahaifarsa (Tsagem) lokacin da yake haziki kuma hafizi don a gurinsa bayin Allah suke daukar karatu, har ya baro Tsagem suna yi masa hidima. Sun ci gaba da bin tsatson Khashi Tsagem suns bas u kariya daga miyagun aljannu, bas u taba sarewa ba, to lokacin da aka daure su aka gudanar da wannan aiki na kafa kahon libhas, Sagir na mutuwa aka kunce su, iya kuka sun koka, duk da dama can suna kuka akan shigar Sagir kungiyar matsafa. To lamari ne wanda yake rubutacce wanda babu wani mahalukin daga bil’adama zuwa jinnu da suka isa su hana ikon Allah tabbatuwa, don haka suna ji suna gain babu yadda suka iya Sagir ya fada wannan kungiya ta matsafa. Damuwar da suka shiga ta ta’azzara, haka ya sa daya daga cikinsu yayi kaura daga kasar Nigeria ya koma can Misra.daya daga ciki kuma ya assasa tsotsar hannun da Shuhuda ke yi, sannan da ta soma girma wata rana da aka yi yunkurin tsaga hannunta ya samara da rowan nono maimakon jinni, don dai a fahimci matsalar da ke tattare da ita, amma ba a fahimatar ba. A can kungiyar matsafa kuwa sun ci gab da kulawa da karagar mulki, domin bayan Alh. Sammani ya bar gurin boka bai hakura da son hawa karagar mulkin ba, don haka da aka samu shekara daya wata rana kawai yah aye karagar a zuwan ya zama shugabansu kamar yadda burinsa, amma nan take ya daskare suka ga naman jikinsa na zagwanyewa har ya zube kaf sai kasusuwansa. Bayan shi ma Izra’el da kwadayin mulkin ya shiga ransa ya jaraba hawa karagar mulkin ya daskare naman jikinsa ya zagwanye. Hakan ya daga musu hankali matuka, amma da dodon tsafin nasu ya sanar musu babu mai iya hawa karagar mulkin a zauna lafiya face wanda aka zaba ya zama magaji sai hankalinsu ya kwanta, sun san akwai wanda zai shugabance su a gaba. A sirrance suna zuwa ganin Shuhuda amma ba a taba bat a wani abu day a danganci naman mutane ko jinni ba, suna dai zuwa dubata a matsayinta na Mgajiya wadda zata zamo shugabarsu nan gaba. Lokacin da Slmai mai haja ta tsaga hannun Shuhudan ‘yan kungiya ne suka kasha Slmai, saboda ta raunata magajiyarsu su kuma ka’idarsu ken an, ba a taba musu shugsba a

Please Login or Register in order to submit comment