Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan muguwar ta'asar, don haka a kira yaron nan a tambaye shi ko shi yayi mata ciki". Alh Rabi'u ya dube shi, ya ce, "Wane yaro ke nan?" Ya ce, "Malaminta, wanda ya same ni da maganar yana son aurenta. Hamza sunanasa, shi ma Isah zan kira shi a waya duk abinda yake ya bar shi ya zo domin sanin gaskiyar lamari". Alh. Rabi'u ya girgiza kai, ya ce, "Ba haka za a yi ba, kuu bar min komai. Zan tuhumi yarinyar idan yiwuwar kiransu ya kama sai dai a bari sai lahadi don kada abin ya shafi aikinsu". Inna Yaduwa ta sharce kwalla, sannan ta ce, "Malam ni a ganina kawai a zubar da cikinnan asiri a rufe ba sai wasu sun ji ba". Alh. Rabi'u ya girgiza kai ya ce. "Ko day ban yarda da wannan gurguwar dabarar ba, mutane suna daukar zubar da ciki wani abin rufin asiri, bayan kuma babban tonon asiri ne, kuma budewa yaro kofar shiga bariki ne. Ciki dai an sameshi, kuma ko mun so ko mun ki dale ne mu yarda da kaddarar da ta fada manam Saboda haka maganar ma zubar da ciki ba ta taso ba, ku dai saurareni".
Da wannan shawarar suka tashi, Alh. Ahmad da Alh. Sada kowa ya kwashi zugar iyalinsa da suka zo dubiyar suka koma gida bayan gargadin da suka yiwa Nura ddeen akan kar ya sake ya fasa zancen ko da ga mahaifiyarsa ce. Alh.Rabi'u bai samu ganawa da Shuhusa a ranan ba, sai washegari da safe ya sa Inna Yaduwa ta yi masa kiranta.
Shuhuda ta shigo dakin ta durkushe. A agabansa, kanta asunkuye ta gaishe da shi, ya amsa. Shiru na wani lokaci ya biyoo bayan gaisuwar, can ya daga harshe ya ce, "Shuhuda wani mummunan labari ne ya zo min game da rashin lafiyar ki, wanda ya daga min hankali, shin me ye gaskiyar lamarin? Da gaske wai kin siyar da mutmcinki har kin samu ciki ba tare da aure ba?" Ba ta dago kai ba bare yaga wani yanayi na tsorata ko razani game da jin furucinsa ba. Ta dai yi bakam kamar an dasa dutse. Ransa ya baci ya dan daga murya cikin barazanarwa ya ce. "Magana nake miki, ki ba ni amsa". Har yanzu dai ba ta tanka ba, sai shi ma ya yi shirun yana ci gaba da tsare ta da idanunsa. Ganin ba ta da niyyar tanka masa ya sa ya ci gaba da cewa. "Shuhuda ba ki kyauta ba, kin kuma zubar mana da mutumci duk da cewa kkanki kika yiwa illa. A matsayinki na marainiya maimakon ki rungumi maraicinki da kyau, amma sai kika yi watsi da kyakkayawar rayuwa. Shin wane rudin soyayya ne ya kai ki ga aikata wannan mummunan abu wanda ko a fada ma akwai muni?" Har yanzu dai bat tanka ba, duk yadda ya so ta tanka amma dai shiru. Ya kwantar da murya cikin tausayawa ya ce. "Isah ne?" Ta yi shiru, ya ce. "Ko Hamza ne?" Nan ma tayi shiru, ya ci gaba. "Shi ke nan,Tashi ki je, amma na baki daga nan zuwa gobe duk abin da ake ciki ki sanar min da wanda yayi miki wannan aika-aika”. Tayi shiru bat a mike ba, kuma bata da alamar tashin, y ace, “Cewa nayi ki tashi ki tafi”. Kamar bad a ita yake Magana ba, a’ah sai ya dan leka kansa ga fuskarta ya ga idanunta a rufe. Ya yi tsammanin kuka ta ke, nan take tausayin maraicinta ya tsirga masa jiki.
Inna Yaduwa ta shigo dakin hannunta rike da kofin ruwa, ta ajiye a gabansa tana cewa, “Ta fada maka?” Y ace “A’a amma abi a hankali, kamata ku tafi”.
Inna Yaduwa ta nufeta zata kamata da sauri Shuhuda tad ago kai tare da daga hannu. “Kada ki taba ni, za ki kone idan kika taba jikina!” Inna Yaduwa ta dubi mijinta, shi ma ya dube ta cike da mamaki, sai ta ja tsaki t ace.
“Wallahi ba hauka ba, kowace irin burkewa ce ba ki isa ki bata mana suna ba”.
Murmushi Shuhuda ta yi tun kafin ni tuni sunanku ya baci ko dan abu yana boye? Mhm, kuma ku sani nib a tsatsonku b ace, ban hada komai da ku ba, taimako ne yasa na shigo cikinku, kuma kun ki fuskanta. To amma masha Allahu tunda har wannan matakin ya sosa ranku har kuka yi tunanin taron gangami, abin d azan muku matashiya da shi anan shi ne, tarkonku da zaku yi don gano wanda ya yi min ciki said a taimakona don gudanar da taron a cikin sirri, gudun idanuwan masu sirri kar su fuskanci sirri har su yi wani abu a cikin sirri kwatan-kwacin yadda suka aiwatar da wani sirri a cikin sirri mai murdaddiya da tsuke tunanin duk wani mai tunani.
A rayuwa ana so komai a yi shi cikin sirri, domin sirri abu ne mai matukar amfani” Gaba daya daga cikin maganganunta babu daya na kamawa, illa tsabar rainin hankali da rashin kunya da suke ganinta da su.
Alh. Rabi’u ransa y abaci, sai ya nuna musu hannu cikin daure fuska, y ace, “Na ce ku fice min ko?” Idanuwan Shuhuda suka kawo kwalla rau-rau, ta durkushe a gabansa tana cewa, “Alhaji don Allah, don Annabi ka yafe min idan maganganuna sun bata maka. Wallahi ni mai taimakonku ce, ba kuma zaku yi nadamar taimakon da na ke muku ba”.Ta mike cikin azama ta nufi kuskurawar dakinsa inda gadonsa yake, ta durkusa daga shi har Inna Yaduwan idanu suka bita da su. Jim kadan tad ago tare da juyowa gaba dayanta dauke da wata roba wadda su duka sun yi mamakin samuwar tata.
Ta durkusa a gaban Alh. Rabi’u t ace, “Ka ga wannan robar na tabbata ba kasan da ita ne a cikin sirri, saboda kawar da idanun masu sirri. Wannan kadai zai iya zama shaida a gareku da zaku aminta zamowata a cikinku RAHAMA ne, kuma taimakon rayuwarku ne”. Har yanzu ba wanda ya fuskanci abin da ta ke nufi, illa zargin da suka dade suna yi akanta ya bijiro musu, wato dai lokacin da aka haifeta jinnu sun yi musaya sun dauke asalin wadda aka Haifa sun ajiye musu tasu ‘yar jinsun jinnu!
Shuhuda ta ci gaba da cewa, “Zan mayar da robar nan a inda ta ke don ci gaba da zama cikin sirri gudun idanun masu sirri, sai dai ku sani duk iya duba idanunku ba zasu taba hango muku inda take ba, tunda ita din an samara da ita ne a cikin sirri. Tunda ya kasance kun tsayar da ranar taron gangami, ina ji it ace RANAR NADAMA! RANAR YAMMA!
Wato ranar da kasuwa t agama ci, wadanda ke cikin kasuwar zasu waste!”
Su duka suna son yi mata Magana, amma sun kasa. Mamaki, tsoro, firgici, rudani gami da damuwa duk sun mamaye sansanin zukatansu. Haka suna gain Shuhuda ta maida wannan rufaffar roba inda ta daukota tukunna tga sa kai ta ficce daga dakin tana sharer kwalla a gurbin idanunta. Bayan fitar Shuhuda sai aka shiga kallon-kallo tsakanin Alh. Rabi’u da Inna Yaduwa, kowannensu da abin da yake son cewa dad an uwansa, amma sun kasa furtawa, sai dai kallon. An kira Isah a waya cewar duk abinda yake ya tabbatar ya zo Kano karshen mako, hankalinsa ya tashi ya shiga kiraye-kirayen lambobin kannansa don jin abin da yake faruwa, amma ba labari. Nuraddeen ne dama yasan labarin shi kuma an gargade shi, don haka Isah ya kosa matuka karshen makon ya zo ko ya je Kanon ya ji abin da kiran ya kunsa, yana addu’a kada ace sanar masa za a yi an ba wa wani auren Shuhuda ba shi ba.
Shi kuma Uncle Hamza takanas Alh. Sada ya je har makarantar da nufin saduwa da shi, amma bai tarar da shi ba, domin an ba shi labarin mahaifin Uncle Hamza wato Alh Babba ne ciwonsa ya tashi a lokacin ma suna birnin Misra don nema masa magani. Haka ya baro makarantar jiki a sanyaye ya dawo gida jiran zuwan karshen mako.
The end
.
To bari mu gani me karshen makon zai haifar, da gasket din ne ranar taron zata zamo RANAR NADAMA? RANAR YAMMA?
.
Ina shirye-shiryen makaranta, shi isa ban cika samun chance din typing ba, da patar zaku cigaba da hakuri.
.
Sai ku biyo ni don jin karshen yadda zata kaya, taku har kullum Sadin Mama me kaunarku har kullum
Ainihin marubuciyar wannan littapi Allah ya jink anta da rahama ya kara mata hasken kabari, (ZAHRA’U BABA YAKASAI)
Hada Hausa Book stories
MATAU’UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA) BOOK 4
¤¤28¤¤
BABI NA SHA SHIDA
Tunda Isah ya shigo gidan ya ga wani sauyi, amma dai bai magantu ba, ya gaishe da Inna Yaduwa ta amsa masa ba kamar yadda ta saba amsa gaisuwarsa ba. Sai yayi tsammanin ko itace bata da lafiya aka yi masa wannan kiran gaggawan. Yayi murmushi yana dubanta y ace “Yar tsohuwa mai ran karfe, hala hala lokaci ya yi ki ke neman yin gardama?” Ta yi masa shiru illa wani irin kallo da take auna masa. Sam bai ji dadin hakan ba, y ace. “Wai don Allah Inna mai yake faruwa ne/. ni fat un da Abba ya kirani hankalinaya gaza kwanciya, ga shi na iso na tarar da sauyi atare da ke. Shin wani ne ba shi da lafiya? Ko kuwa na yi laifi ne b an sani ba? Idan ma akan rashin zuwana net un bayan tafiyata Ibadan, wannan ai bai isa zama laifi ba, idan aka yi duba ni sabon ma’aikaci ne”. Cikin kufula t ace da shi. “Idan don rashin zuwanka new a zai damu? Je ka ma hakan dinne, asabar da lahadi suma ranakun aiki ne?..... Ture wannan, laifi kam ai ka fi kowa sani tunda ka nemi tarwatsa farin cikin mu”.
Hankalinsa ya kuma tashi, idanunsa a waje y ace, “Ni din Inna? Me ya yi zafi haka shi ba wuta ba?” sai tag a kamar ma ya raina mata hankali, ta ja baki ta tsuke bat a ko kara kallon inda yake ba. Shi kuma abin day a sa shi shakku ken an, can ya nisa y ace, “Ina Shuhuda?”
Ta ce “ban sani ba, mugu kawai wanda ba shi da tausayi bare tsinkaye da maraici”.
Wannan gugar zana ce ta yi masa, atunanintsa ken an, duk yadda aka yi akan Shuhuda ne aka yi masa wannan kiran gaggawan, yanzu haka akan ya katse mata waya ne duk ta bi ta tayar da hankalin mutane, ashe dai tana sonsa, yawo da hankali ne yasa ta wulakanta shi a gaban wani bare? Ganin yadda Inna Yaduwa ta ke amsa masa maganganunsa sai bai kara cewa da ita kanzil ba, ya nufi sashensa, don lokacin Alh Rabi’u baya gidan. Amma zuciyarsa fal ta ked a damuwa na rashin sanin tartibin kiransa. Da daddare bayan sallar Isha’I Alh. Rabi’u ya kira Isah adakinsa, sai dai ya rasa ta inda zai kamo zancen. Isah ya shiga laluben laifinsa da har yasa dattijon ma ya kasa cew da shi komai, anya kuwa laifin na katse waya ne? suka yi shiru tamkar kurame, can da Isah ya ga shirun bai zai haifar dad a mai ido ba, sai ya magantu.
“Baba ko shakka bana yi, wani gagarumin laifi ne na aikata mafi muni tunda har kai ma ka gaza ce min komai, amma don Allah ina rokon ku afuwa akan aikata laifi bias kuskure”. Alh. Rabi’u ya jinjina kai y ace, “Lifi kam ka aikata, sai dai na kasa furta abin da na ke son furtawa duk da cewar ga abin a raina, bakin ne yaki furtawa. Amma gobe idan Allah Ya kaimu lafiya za a yi wani taro akan laifin da ka aikata da misalign karfe tara na safe”. Isah ya dube shi a kai-kaice y ace “Allah Ya kaimu lafiya”.
Alh. Rabi’u ya kawar da hirar da cewa, “ya gurin aikin naka, da fatan dai babu wata matsala?”
DANKARI!
Ya ayyana a ransa, matsala kam akwai ta, sai dai ba zai so fadar wannan labari na al’ajab din day a faru a zuwansa birnin Ibadan, don bai ga fa’idar fadar ba. Suka dan zanta tukunna ya koma sashinsa.
Tun day a dawo bas u hadu da Shuhuda ba, hakan kuma bai dame shi ba.
.
Karfe takwas da mintina sha uku na safiya, Alh. Ahmad da Alh. Sada sun hahllara a gidan, yayin da su Inna Yaduwama duk sun gama shirin day a dace na Karin kumallo. Shuhuda sai wani irin farin ciki ta ke, sai ka ce ranar sallah, abin day a bai wa kowa mamaki kenan. Au shidda suna a dakin Alh Rabi’u an ci an sha, ana shirin soma maganganun da suka assasa tarin, maigadi ya doka sallama daga bakin kofar dakin. Alh .Ahmad ya leka yana lekawa yana amsa sallamar, maigadi y ace, “Wani ne ya zo ya ce a fada muku Hamza A. Babba ne ya iso”. Ya bi maigadin zuwa harabar gidan, Uncle Hamza yana jingine a jikin motarsa, sanye da farin boyel day a sha dakakken aiki, fuskarsa na fitar da annuri. Alh. Ahmad ya ba shi hannu suka yi musabiha, tukunna y ace. “Mu shiga daga ciki”.
Ya yi gaba, Uncle Hamza na binsa a baya, zuciyarsa na cike da farin ciki. Tunda ya samu sakon nemansa da ake gidan su Shuhuda ya samu kansa cikin farin ciki, saboda tunaninsa magar aurensu ce ta taso, don haka ya zabi zuwa gidan cikin farar shiga.
Koda suka shiga dakin, kowa ya bishi da kallo, gaban Isah ya soma dukan tara-tara ba ma uku-uku ba, shi ken an zargin da yake ya zamo gaskiya, yasan an bawa Uncle Hamza auren Shuhuda tunda yaga fuskarsa cike da annuri an kira shi ne domin a ba shi hakuri, a kuma kunsa masa bakin cikin dab a zai gushe gare shi bs abadan abidina. Wato shi kadai ne yake cikin kuncin zuciya, tunda ga Shuhudar ma sai washe baki ta ke tana jin dadin za a aura masa wanda take so. Take ya ji kamar ya tashi ya fice kada a hauda jininsa.
Yayinda shi kuma Uncle Hamza ya sake jin wani nishadi ya mamaye masa zuciya, musamman ma ganin yadda aka tara mutane da yawa, ciki kuwa hard a Alh .Sada mutuminda ya san alakr Shuhuda shi wato mahaifi gareta, ganin Isah yana hada rai ma yasa shi jin nishadi ko babu komai yasan yayi masa kub daya, ma’ana ya kasa shi.
Bayan Uncle Hamza ya gaisheda su Alh.Sada y dube shi tare da cewa. “Na je makarantarku nemanka an ce min kun fita Misra kai Mahaifinka asibiti, ya jikin nasa?” kansa na sunkuye a kasa y ace ”da sauki, sun ma wuce Saudi-Arabia shi da yayana”. Alh. Sada yace. “Allah Ya kara masa lafiya, amma ta ya ka samu labarin neman da ake maka?” a wannan karon said a ya dago kai cike da mamaki, y ace. Yakub ne ya je har asibitin da muke ya duba mahaifina, sannan ya sanar min sakonku”.
Sai aka shiga kallon-kallo tsakanin iyayen, Alh Rabi u ya ce "wane Yakub ke nan?" Mamakin Uncle Hamza ya sake bayyana, ya ce. "Yayan Shuhuda!" Alh Sada ya maimaiita maganar, tukunna yace. "Ai mu nan gidan ba mu da mai irin wannan sunan ma Yakub". Jin wanna batu, sai Uncle Hamza ya yi tsuru tsuru, ya tuna can baya da ya fadawa Shuhuda ya je gidansu har ya hadu da Yayanta ta nuna mamaki, to ya lamarin yake? Alh Ahmada ya ce. "Yaya kawai agabatar da abinda ya assasa taron". Alh Sada ya dubi Shuhuda ya ce, "Ga Isah, ga Hamza dukkan su suna ikirarin samarinke ne, don haka sai ki fada mana wanda yayi miki ciki a cikinsu idan kumma babu daya sai ki fada mana wanda ya aikata wannan aika-aikar" da ga Isah har Hamza ko wanne ya zabura ya mike tsaye cikin kaduwa, suna girgiza kai Alh Sada ya daka musu tsawa yace. "Kun ga ku zauna". Suka zauna jiki a sabule, Isah ya ce "Wallahi ba ni ba ne".
Shi ma Uncle Hamza ya ce. "Na rantse da girman zatin Ubangiji ba ni ba ne". Kafin wani ya yi magana a cikinsu, Shuhuda ta mike tana murmushi ta ce "Baba ku yi min afuwa, zan je na shigo da baki gasu can harabar gida".
Ran kowa ya baci, wato su zata mayar abokan wasanta, yaushe aka aiko ga bakin bare ta ce haka? Sai dai kafin wani ya tanka tuni ta kai bakin kofa. Alh Sada ya biyota da hanzari yana kira, har sai da suka fito harabar gidan. Lalle kuwa ya ga baki su uku, mace daya maza biyu, turus! Ya ja tunga ya tsaya cike da tsorota ya Shuhuda tasan da zuwan bakin?
Bai ga lokacinda aka kira a waya bare kuma turo mata sako ta duba ba. Yayin da ita kuma Shuhudar ta rungume macen suna fara'a. Daya daga cikin mazan ya mika wa Alh Sada hannu ya ce, "Baki ne daga Misra akan zaman da kuke yanzuu muka iso, kada ku damu, ku aminta da mu". Alh Sada ya tsayar da zuciyarsa ganin yadda suka zo musu cikin salama, ya ce. "Ba damuwa". Ya yi musu jagoranci zuwa cikin dakin. Uncle Hamza ya mike tsaye da sauri yana nuna daya daga cikin bakin, ya ce. "Yauwa ga Yakub din". Shima Isah ya mikke yana nuna sauran bakin biyu, ya ce. "Abubakar, Shuhuda me ya kawo ku nan?"
Alh Rabi u, Alh Ahmad, Alh Sada da Inna Yaduwa suka dinga kallon juna cikin mamaki.
a Hada Hausa Book stories
MATA’UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
29
Yakub y ace, “ku kwantar da hankulanku, sannu a hankali”
Yana fadar haka suka zauna, sannan su Isah ma suka zauna, sai dai gaba dayansu suna cikin rudani. Bayan sun zauna Yakub din ne ya soma Magana.”Dan Allah ku yi hakuri da bakuncin da muka kawo muku katsaham, akwai babban dalili na yin haka, dalilin kuwa ba zai rasa nasaba da boyayyen sirri ba wanda muke bukatar nutsuwa daga gare ku. Da fatan fahimtarmu bias kyakkyawar fahimta”. Ya mayar da dubansa ga Inna Yaduwa, y ace. “Inna ke mace ce, muna bukatar idan ba zaki damu ba ki fita domin gudun razani a gareki. Idan kuma har zaki dake, ki yi hakuri da kaddarar da ta faru, ba matsala”. Inna Yaduwa ta dubi Yakub cikin takaici, a ganinta ya raina ta, yaushe a matsayinta na babbar mace yaron da a haife ta haife shi zai ce ba zata iya dauke dafin da zai fada ba? Ta ce, “Shekaruna sittin da uku, a haife na haifeka, kuma dukkan zafin kalma ba zata wuce ta rashin ba, ni kuwa na rasa mahaifana da dana Sagir, kuma na yi hakuri, sai sanadin gurbata rayuwar jikata ne b azan dauke dafin ba?” Yakub ya yi malalacin murmushibtukunna y ace. “ki yi hakuri Inna, ba nufi na ke nana ba, amma babu komai tunda nag a alamar zaki nuna juriya ai shi kenan”.
Ba ta tanka ba shi kumja ya ci gaba da cewa. “wani labari ne za mu baku bias yarjejeniya, da kuma alkawari”. Alh. Sada gwanin zuciya, y ace. “kun ga don Allah su waye ku? Kada ku zo kukawao mana raini”.
Alh Rbi’u y ace, “ka ga Sada saurara”. Ya dubi Yakub ya ce “muna saurarena”. Yakub ya gyara zama, sannan ya dora da cewa, “Ni sunana Yakub, wannan kuma Abubakar, macen it ace Shuhuda. Mun kasance tare da ku tsayin lokaci….. koda yake ba wannan ke gabanmu ba, muna a gabar sanin wani sirri da ke lillube a cikin sirri”. Ya dora idanunsa akan Alh Rabi’u y ace. “Alhaji yarjejeniyar da zamu yi da ku it ace, ku amince zaku sauraremu har sai mun gama ba ku labarin da zamu ba ku tukunna zaku tambaye mu abin day a shige muku duhu. Sannan alkawarin, za ku yafewa wanda ya assasa komai laifinsa”. Alh Rabi’u y ace, “zamu amince da yar jejeniya, amma maganar alkawari babu ita, tunda bam u san mai laifin ba…….. Hasalima dai babu yafiya ga mutumin day a kunsa mana bakin ciki ba tare da yayi nadama ba”.
Abubakar ne wannankaron ya magantu, inda y ace. “Tunda harm u muka nemi hakan kun san akwai babban dalili. Na farko dai shi mai laifin bay a cikin duniyar nan bare ya iya neman afuwa, kuma a matsayinku na iyaye dole zai kasance kun e mutane na farko da zasu yi fatan ‘ya’yansu su sadu da rahamar Ubangiji”. Babu wanda ya fahimci inda maganganun suka dosa, kuma gaba daya yanayinsu ya nuna rashin fahimtar. Yakub ya ci gaba da Magana da cewa muna rokarwa Marigayi Alh Sagir gafara a gurinku iyayensa bisa wani boyayyen sirri da ya assasa”.
Inna Yaduwa tayi tsagal t ace, 2wani ne y ace muku muna fushi da shi? Ko salon ku bata masa gawa ne? kai ni fa ban yarda da ku ba”. Alh .Rabi’u ya girgiza kai y ace, “Yaduwa idan ba zaki iya saurara ba kina iya fita”. Ya kareshe maganar yana nuna mata hanyar fita daga dakin. Sai ta yi mucus! Alh. Rabi’u y ace, “mun yafe masa, Allah Ya yafe mana baki daya.
Suka ce
“Amin”
Yakub y ace,
“ina so hakan ya zamo alkawari ne, kada daga baya dokin zuciya ya sa ku sauya shawara”.
Alh. Rabi’u y ace. Mun yi alkawarin”. Yakub ya dubi Abubakar y ace, “wannan shi zai fara ba ku labarin, saboda labarin ya kasu kashi uku, kowanne mud a bangaren da yake jagoranta, Abubakar bismiLlah”.
Abubakar ya gyara zama ya soma da cewa.
BABI NA SHA BAKWAI
MAFARI
MATA’UL HAYAT
(JIN DADIN RAYUWA KO KYALE-KYALEN RAYUWA)
“Kamar yadda kuka sani Sagir ya taso da hazaka, uwa uba nutsuwa da yake da ita, wanda hakan ne ya ja masa farin jin a gurin al’umma.
Da yake labarin a takaice ne zan baku shi, kun san lokacin da yake aji hudu a sakandire kun sauya masa makaranta zuwa ta kudi, to a can ne Allah Ya hada Sagir da wani aboki IZRA’EL, wanda tasu ta zo daya sosai don gurin zamansu daya ma, haka idan ana maganar kokarin daya to za a sanya dayan. Wannan shakuwa tasu da hazakarsu ya sa malamansu ke kiransu 2 Effect, duk da wannan tarayya tasu Izra’rl bai taba taka kafarsa gidansu Sagir ba, hakan kuwa daga Sagirun ne don yana tsoron mahaifansa, sanin Musulmai ne shi kuma Izra’el Krista, yana ganin kamarbza a kalubalanci tarayyarsu. Sai dai shi Sagir ya je gidan su Izra’el wanda zuwan nasa ya tayar da hankalin mahaifansa har said a suka hukuntashi akan don me zai yi mu’amala da musulmi, dalilin haka yasa abotarsu ta soma ja baya, amma dai bas u rabu ba. Lokacin da suka gama sakandire, sai ya kasance, suna haduwa a cikin gari. Tsutsayi mahaifan Izra’el suka gano har wannan lokacin bas u rabu ba, don haka suka tura dansu karatu, can kudancin Najeria. Wannan ya sa suka daina ganin juna, kuskure na farko da aka soma samu a rayuwar Sagir shi ne, gidannan ba a tsaya sosai ga ilimin addinin musulunci ba, ita kuwa duki rayuwar da aka bar ilimin addini akwai nakasu a tattare da ita. Shigar Sagir poly ta sauya masa rayuwa, ta hanyar yin mu’amala da mutane daban-daban, na banbanta addinai, daga cikin mutanen day a yi mu’amala da su akwai wata yarinya mai suna Akkina, wadda ta kasance daga addinin Yahudawa. Akkina ta so Sagir, shi ma ya so ta it ace ma mace ta farko da aka soma SADAUKARWA da ita, a wani bangare na sirri………..”
Inna Yaduwa ta katse Abubakar cikin daukar zafi. “ka ga malam dukkan mu nan ba yara ban e, idan kun z one domin ku ci zarafinmu ku bata mana gawar da, to ku fice ku bam u guri”.
Alh.Rabi’u y ace, “kafin a soma bada labarin said a aka nemi shawarar idan ba zaki iya saurare ba ki fita, don haka yanzu ma kofa a bude ta ke”. Jin abin da ya fada yasa ta yi shiru amma tacika fam!
Abubakar ya jinjina kai yana kallonta tukunna ya dora da cewa, har Sagir ya kamala diplomarsa suna tare da Akkina, yana ta neman aiki bai samu ba, rannan da yammaci ya je gidan zoo shi da Akkina, wadda ta kasa komawa mahaifnta tun kamala karatunta, saboda tunaninta idan ta koma Sagir ba zai bi bayanta ba, ita kuwa a rayuwarta babu wanda ta ke so irin Sagir, don haka ta ki

Please Login or Register in order to submit comment