Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi hakuri,juriya zuwa MATA'UL HAYAT-3 don jin yadda zata kaya.
Shin Hamza ko Isah? Akwai dai sadaukarwa, waye mai sadaukarwar? Kuma ta ya ya?
ada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)Book 3
¤¤21¤¤
.
KUSKURE.
.
Idan aka duba littafi na biyu page na 150 sakin layi na karshe an yi amfani da sunan Abdallah Ibn Khaddab a maimakon Abubakar Ibn Khaddab har zuwa karshen littafin a haka ya kare.
Matsalar ta faru ne daga gare ni ne, da parko Abdallah shi ne asalin sunan, bisa wani dalili na maida Abubakar, na ci gaba da bi ina replace da Abubakar, tuun daga page din da aka samu matsalar gaskiya ban duba ba, lokacin ba ni da lafiya, kuma har aka gama aikin ban ga kuskuren ba, sai da na yi nisa a 3 sannan ma na fuskanta.
.
A gafarceni bisa wannan kuskure.
Zahra u Baba Yakasai.
.
Allah ya jin kanta da rahama ya saka mata da Aljannah.....ameen.
.
Ci gaban labari..
.
Shuhuda ta dan dube shi a kai kaice, tukunna ta ci gaba da cewa. 'Shuhuda tana da mutumci, ta na da kaifiyya da bincike akan abin da ya shafi harkar taimako. Ka ganta dai yarinya ko, amma wallahi idan ka ji irin mutanen da ta binciko ta taimaka musu abin sai ya ba ka mamaki matuka. Shi yasa a rayuwa duk wanda ya kasance yana da kaifiyya ya ji dadi'.
Wannan kalma ce da Shuhuda Misra ta yi amfani da ita a lokacin da ta ke sanar da shi yadda aka yi tasan kanwarsa Shuhuda, ta ce tana amfani da bincike ne gami da kaifiyya. Wannan ma kadai ya isa ya zamo hujja agare shi, Shuhudan Misra ce ya yi tazali da ita a Nigeria.
Ya so ta ba shi lambarta, gami da adireshin gidansu a can Misra ta goce masa, kuma babu amfanin da ba shi lambarta don gudun kada idan sun hadu a Nigeria ta nuna ba ta sanshi ba ya kira wayarta ta yi kara a gabansu asirinsu ya tonu, shirin da suka yi ya ruguje.
Lallai idan haka ne ya ci a jinjinawa wannan kaifin hankali nasu, tunda har suka iya wannan tufkar ba tare da an samu rauninsu ba kasancewarsu MATA masu tarin rauni, da kuma kuruciya. Domin mace mai shekaru sittin a duniya ba ta kai namiji mai shekaru ashirin kaifin hankali ba, su dama mata haka suke, rauni ne da su. Abin da suke tunanin idan sun yi dai-dai ne, amma idan maza suka tace sai aga abin ba dai-dai ba.
.
(Sadin Mama yar Anty, ni dai na ce what a man can do, woman can do far much better )
.
Ku yi hakuri yan uwa na mata, kada kuce na yanke mu, gaskiya ce idan kuwa gaskiya ta zo ana son fadarta komai dacinta.
.
Shiru ya yi bai kuma tanka mata ba domin ta gama yawo da hankalinsa, ta gama kunce masa duk wata jijiya ta tufka da warwarashi.
.
BABI NA GOMA
TABDIJAN!
Shagari low-cost nan ne unguwar da Haj Asmo ta ke, a kofar gidan suka tsaya suna jiran maigadi ya bude musu get. Koda ya bude Isah ya sulala da motar cikin harabar gidan, Shuhuda ta bude kofa ta fita ta nufi hanyar shiga cikin gidan.
Isah ya sanya baki ya kirayi sunanata. Ta juyo tana dubanshi ba tare da ta tako ba.
Ya ce, "ki tsaya mu shiga da tsarabarsu mana".
Cikin shagwaba ta ce masa, "mu tara shiga mana, ba sai a samu wadanda zasu shiga da tsarabar ba?"
Yana kyabe baki ya ce da ita.
"Shi ke nan".
Yara kusan su shida suka tarar a falon suna kallo, da ya ke sun san Shuhuda don haka suna ganinta suka mike da sauri suna mata oyoyo-oyoyo.
Ta dauki Sajida 'yar shakara hudu ta saba a kafadarta.
Hayaniyar yaran ce ta fito da Haj.Asmo daga dakinta. Ita ma tana ganinsu ta washe fuska.
"Ni kam na yi fushi, yanzu saboda Allah Isah sai yau kake zuwar min?"
Yana sosa keya irin na maza, ya ce,
"Ayi hakuri Goggo".
Ta ce "idan ban yi hakurin ba ai da ba zaku ma gane gidan ba, duk da kuwa ka dauko wannan marar son zumuncin. Ta hana min 'ya zaman lafiya, kullum kuka wai ita akaita gurin Aunty Shuhuda".
Su duka suka yi murmushi, Shuhuda ta dora da cewa.
"Ki yi hakuri Goggo, dama karatu ne yake hana ni zuwa, to yanzu kuma an gama kafin a tafi wata".
Haj.Asmo ta ce.
"Idan an daura aure ko? Ai ni an fada min kun hada kanku....."
Kunya ta lullube Shuhuda har shi kansa Isah, aka rasa wanda zai ce wani abu.
Haj.Asmo ta lura da hakan, sai ba ta ja zancen ba, ta dubi Sajida da har lokacin ta ke makale a kafadar Shuhuda ta ce.
"To a sauka a bar Aunty ta zauna ko?"
Ba musu yarinyar ta soma kokarin sauka, Shuhuda ta sauke ta, ta zauna akan kujera. Haj. Asmo ta ce da daya daga cikin matasan matan.
"Nafisa a kawo musu abinci da ruwa ko?".
Nafisa ta nufi kicin don hado musu abinci.
Isah ya dubi sauran yan matan, ya ce.
"Ku taso mu je ku kwaso tsarabarku".
Sun kwaso kayan tsarabar wanda suka ware na gidan, sauran kuma suka barshi a mota.
Sai da suka soma gaisawa sannan suka ci binci, aka shiga hira.
Karfe shida na yamma, Isah da Shuhuda suna zaune a falon Haj. Asmo da ita kanta Haj. Asmon suna hira, Musabahu ya shigo falon hannunsa rike da waya yana murmushi ya ce.
"Afuwa, wani uzuri ne ya tsayar da ni".
Isah ya kawar da kai, ya ce.
"Ba ni zaka bawa hakuri ba, kanka zaka baiwa, domin yiwa wani yiwa kai ne, kuma duk wanda ya gyara ya sani".
Musbahu yana kokarin zama akan kujera ya ce.
"Kin ji shi ko Sister?"
Shuhuda ta kawar da kai, ta ce.
"Ni kyale ni, bani da lokacinka. Bayan tunda muka zo aka sanar maka isowarmu, amma ba ka tashi zuwa ba sai yanzu da ka ga dare ya yi, don kada mu fita zaga gari ko?"
Musbahu ya saka dariya, ya ce.
"Shi yasa ina shigowa na soma neman afuwa, kuma sha kuruminki tunda dai kwana zaku yi ai magana ta kare, gobe idan muka dinga yawo sai kin ce kin gaji".
Haj. Asmo ta saka musu baki.
"Ai sun ce da safe zasu wuce. saboda zasu karare. Kuma a goben zasu koma kano".
Ya ce "shi ke nan, sai a yi min uzuri".
Bayan sallar magariba Isah da Musbahu su ka fito daga masallaci. Wayar Musbahu tayi kar. Yana dubawa ya ga wande ke kiransa, kafin ya duba ya dubi Isah ya ce.
"Ina ji se ka rakani wani guri saboda wannan kiran da aka yi min nasan mafita".
Kafin Isah ya magantu, Musbahu ya kara wayar a kunnansa, yana cewa.
"Ya aka yi ne Malami?"
Ya dan saurara kadan don jin abinda ake fada masa, sannan ya ja fasali ya ce.
"Malami ni a ganina ka baiwa Allah zabi idan Zuwai din ce alkhairi. Allah Ya tabbatar, idan kuma Dodoridon ne.... Don Allah tsaya.... Na daina.. Kana jina? Ba na son ka sanya kanka a cikin taskun rayuwa, ka yi hakuri...."
Ya sake saurarawa na wani lokaci, sannan ya ce.
"Kai kasan yadda ta ke, mu kam ba ka taba nuna mana hotonta ba, don haka maganar musun kyawunta ko kwarjininta bai taso ba.... Kuma yarinyar da aka tabbatar maka da MAYYA ce na me zaka....... No! Wallahi na fi kowa son ka, son da nake maka din ne ma yasa nake nusar da kai tarin kalubalen da kake neman fadawa.... Shi ke nan, zan shigo, baki muka yi ma ai da tuni ka ganni.... To sai na shigo din".
Ya kashe wayar cike da alhini. Isah a tun soma wayar ya tsurawa Musbahu ido, mamakin kalaman da suka tattauna yake, don haka Musbahu na kashe wayar ya ce.
"Me ya ke faruwa?"
Musbahu ya yarfar da kai, ya ce.
"Wallahi wani aboki na ne yake cikin rudani. Wata yarinya ce Allah Ya hada su da ita, yana matukar sonta amma matsalar ne barkatai, ka ga dai na farko wani yayanta Yakub ya same shi ya fada masa auren zumunci za a yi mata, amma shi ya kasa hakura da ita, kuma fa akwai wata kanwar mahaifinsa da ta ce yarinyar mayya ce, shi kansa yana tunanin kasantuwarta jinsin mutane, saboda kana kallonta zaka ga tsabar kyau kamar aljana.
Amma sonta ya makantar da shi kana ji yanzu har an kai fagen da yake tunanin tuburburewa lallai sai ya aure ta".
Isah ya girgiza kai cikin tausayawa.ya ce.
"So ke nan! Kasan idan mutum ya na son abu hankalinsa ba zai taba kwanciya ba har sai ya ga ya mallaki abin"..
Musbahu ya ce. "Ai ko dai, amma wani lokacin yana da kyau mutum ya dinga ragewa kansa kaifin son abu idan har ya soma katari da matsalolin da abin zai saka shi".
A dai-dai lokacin suka karaso gidan.
Sun gama cin abinci, Isah da Musbahu suka mike zasu fita. Tsam! Shuhuda ita ma ta mike tana cewa.
"Ina zaku?"
Musbahu ya yi murmushi, tukunna ya ce.
"Zamu je wani guri ne mu dawo".
Ta ce, "Ai kafarku kafata".
Nusaiba kanwar Musbahu wadda zasu iya zuwa kai daya da Shuhuda, ta ce.
"Yaya ai wannan cingam ce, don haka kada ka damu tunda dai ka dauke mai jan kunne ai ita ma sai ka dauka".
Sukayi murmushi, Isah ya ce.
"Idan dai da ita za a fita, to ke ma sai ki taso mu tafi tare, don ba zamu tafi da mace daya tsikau ba ace maza biyu mace daya".
Musbahu ya dubi Nusaiba ta gafen ido, ya ce.
"Dama abin da ta ke so ke nan, don tasan ni ba zan fita wani guri da ita ba, Amma kin ci arzikin su".
Nusaiba tana dariya, ta ce. "Na dai ji, komai zaka ce ka fada".
Haj. Asmo dai ba ta tanka ba, haka suka tafi su hudu. Musbahu da Isah a gaban mota, Shuhuda da Nusaiba a kujeraa baya.
Suna tafe suna hira irin ta abokan wasa(Dan mace da dan namiji).
Sun isa Kanada Quaters inda gidan Malami yake, Musbahu yayi hon maigadi ya bude kofa suka shiga. Su duka hudun suka fito daga cikin motar, Musbahu a gaba, Isah a bayansa, sannan Shuhuda da Nusaiba.
Yana zaune akan kujera cikin falonsa, sanye da wando (3quater) baki, sai karamar riga(roundneck) ja. Kayan sun kara fito da kyawunsa, duk da dama shi din kyakkyawa ne, don da wahalar gaske ka ga dan asalin Ruma mummuna, yawancinsu farare ne dogaye masu cikar haiba.
Sai da Musbahu ya shigo sosai sannan yayi tozali da wadanda ke bayan Musbahu.
Zumbur! Ya mike cikin RUDANI, ya ambaci sunanata.
"SHUHUDA!"
Ita ma cike da rudanin ta ambaci sunansa.
"UNCLE HAMZA!"
Musbahu, Isah gami da Nusaiba suka kama kallonsu cike da tsananin mamaki, ina suka san juna?
.
Sadin Mama 'yar Anty na ce "WAI! Ni ma na rasa inda su ka san juna".
ausa Book stories
Kyan Alkawari........
.
MATAUL HAYAT
¤¤22¤¤
Saboda yadda suka ambaci sunan juna yanayi ne da ke bayyana sun dade da sanin juna kuma sun dade basu hadu ba.
Shuhuda ta sake dubanshi, tace.
"Uncle Hamza dama zan sake ganinka? Dama kana raye a duniya ka manta da dalibarka, kuma kanwar ka?"
Wannan batu da ya fito daga bakin Shuhuda ya baiwa su Musbahu amsar tambayarsu ta inda suka san juna, kuma kalaman dai ne suka haskowa Musabahu wannan ita ce yarinyar da Malami ya ke so, wadda kuma yake cikin tashin hankali a game da ita.
Shi kam ya san Shuhuda mutum ce tunda a tsatsonsu ta fito, mahaifiyarsa da mahaifinta uwa daya uba daya, sannan ya sani duk cikin tsatsonsu babu MAYE, don haka wannan ma wata hujja ce da zai kafawa Malami, sai dai kash! An makaro. Domin an sanar masa Isah zai auri Shuhuda a yadda ma suka zo Katsina tare shaida ce ta cewa sun aminta su zamo ma aurata.
Abinda ya ke bashi mamaki ma ta yadda akayi duk labarin da ya bashi game da yarinyar da ya ke son suka faru akan kanwarsa Shuhuda.
Uncle Hamza ya kama mustuke idanu, gani yake kamar abinda ya saba faruwa da shi ne na gizon da take masa, yau din ma gizon take masa, ba don haka ba, ta ya zai ganta da Musbahu mutuminda ya kasance abokinsa tun kuruciya, kuma suka san juna sosai?
Isah ya kashe shirun da kuma al'ajabin ta hanyar zaunawa ragwab! Kan kujera yana cewa.
"Ya kamata ku zauna sannan a tattauna duk abinda ya dace".
Ba su bijirewa tayin sa ba, dukkansu suka zazzauna, amma al'ajabin ya ki boyuwa ko wanne ka dubi fuskarsa ka san yana cike da rudanin yadda aka yi hakan ta faru.
Shiru na 'yan mintoci suka gilma kafin daga bisani Uncle Hamza ya dubi Musbahu ya ce.
"Wai Musbahu da gaske ko kuwa a mafarki ne ka zo min da Shuhuda don ka sani a rudani?
Idan da gaske ne, taya ka samo Shuhuda har ka kawo min ita a cikin gidana? Ka yi min gamsasshen bayani da zai fitar da ni daga rudanin da nake ciki, don na gaza fahimtar a matsayin da zan dora wannan rudadden al'amari".
Musbahu ya matsa kusa da Uncle Hamza, ya ruko hannunsa yace .
“Ina tunanin ruko hannunka da na yi ka ji dumin hannuna ya is ya tabbatar maka a ido biyu muka bayyana gabanka. Sai dai kamar yadda ka samu kanka cikin rudani mu ma ka saka mu a rudani.
Amsa day ace wadda zata warware tambayoyi masu yawa a lokaci guda. Shin mai ye alakarka da Shuhuda. Itace yarinyar da kake so a makarantar da ka ke koyarwa can jihar kano? Ita ce yarinyar da kake zrgin aljana ce, wadda kanwar mahaifinka ta kira MAYYA? Wadda kake kokarin yi………..”
Uncle Hamza ya daga masa hannu cikin sarewa, y ace.
“Tsiyar dan Nigeria kenan. Ya ce zai maka tambaya daya,amma saiya jero fiye da goma ba tare day a bari ka amsa masa daya ba”.
Isah yace, “ina ganin manufar hakan warwarar lamari ne ko?”
Ba tare da Uncle Hamza ya bari Musbahu yayi Magana bay a ce,
“Shuhuda it ace dalibata wadda na koyar daita karatu a MARIAMA AJURI reshen jihar Kano. Maganar ina zargin aljana ce bat a taso ba.domin ina da tabbacin mutum ce kamar kowa.
Haka maganar cewa ita mayya ce har tayi sanadiyyar mutuwar wasu bayin Allah ban yarda ba,saboda kwararrun hujjoji na. Da ace Shuhuda zata zamto mayya ba zamu shafe shekaru uku da ita ba tare da ta lashe kurwata ko wani a gabana ba.
Na yarda na amince dukkan wanda ya rasu ake zargin Shuhuda ce sanadi mutuwa ce ta Allah da Annabi.
Wadda ko wane bawa yak e hawa siradinta da zarar lokacin amsa kira yayi.”
Bayan karshen bayaninsa, Shuhuda ta fito da idanu waje, ta ce. “Uncle n ice za ka aura?” ta dafe kirji, ta ce. “Na shiga uku ni Shuhuda, aure kan aure? Aure da ci……” maganar ta makale sakamakon tangadi da suka ga ta na yi alamar za ta fadi.
Nusaiba tayi saurin tallafar ta, idanta biyu tangaram babu alamar suma ko mutuwa a tare da ita, amma tan a cikin yanayi na fitan hayyaci.
Su din ma hankalinsu ya tashi matuka. Sai dai Musbahu ya dauki maganarta akan labarin day a sani na cewar Isah zai aure ta.
Su ma Isah da Nusaiba duk haka su ka fahimta, amma shi Uncle Hamza sam shi bai fahimta ba, abin daya dauka shi ne, har yanzu Shuhuda na nan da SHIRMENTA!
Nusaiba ta soma girgizata tana cewa. “Shuhuda! Shuhud!!”
Ta bude ido fayat tana kallon Nusaiba, hakan ya tabbatar wa Nusaiba ba suma tayi ba, don haka ta sauke ajiyan zuciya tare da jin wani sanyin dadi.
Musbahu ya dubi Uncle Hamza murya a sarke cikin tsananin sarewa y ace.
“Malam ina me baka hakuri ka taushi zuciyarka, ka sa lumana a dukkan komai, ka yi hakuri ka karbi Zuwairiyyah a matsayin matar da Allah ya zaba maka ka rabu da soyayyar Shuhuda tunda a halin yanzu an bada ita ga Yayanta!”
Cikin firgici Uncle Hamza yace.
“Ga wa aka bayar da ita? Yayanta Yakubu? Shi yasa dama y ace min auren zumunci za a mata , ashe shi ne mugun?”
Musbahu ya nuna masa Isah yace.
“Ka ga wannan, shi ne aka bai wa ita, sunansa Isah, bata da wani yaya Yakub”. Uncle Hamza y ace. “Ya za a ce min bat a da yaya Yakub, bayan shi ya fara burbusamin ba za a bani aurenta ba, saboda yasan anyi min katobara?”
Isah da Musbahu suka dubi juna, su dai sun san duk cikin family din su ciki da bai basu da mai suna Yakub, amma ya cije akan wai wani yayanta Yakub ya sanar da shi ba za a ba shi aurenta ba.
Shuhuda t ace.
“Uncle Hamza da gaske kake za ka iya………”
Nusaiba ta yi saurin rufe mata baki, tana gudun kada ayi abin kunya, tun da ta fuskanci tan a son ta aminta da soyayyar Uncle Hamza bayan ga Isah wanda ke sonta tun tana jinjira. GIDA BE KOSHI BA. Ai bai kamata a bai wa DAWA ba. Kuma ko banza Isah shi ne wanda zai riketa bias gaskiya ba tare da ta fuskanci tsangwamar dangin miji ba. Sabanin Uncle Hamza da tun kafin ya aure ta an soma kiran Shuhuda da MAYYA. Duk mutumin da aka kira nasa maye ba karamin bakin ciki zai samu kansa a ciki ba. Wannan babban cin zarafi ne. dan haka koda Shuhuda na son Uncle Hamza kuma tana da burin auren sa, in shaa Allahu zasu ruguza abun, ba zasu bari taje inda za a dinga jifarta da miyagun kalamai ba. Uncle Hamza ya ji wani takaici ya tokare masa a makoshi, wannan wane salon rainin hankali ne su Musbahu suka zo masa da shi? Sai ya dinga zargin mafarkin dai ne yake yi, hakika duk abinda ke faruwa a mafarki ne, yanzunnan zai bude idanunsa ya ga komai ya koma a matsayin mafarki. Don karfin hali hard a rufe idanunsa, ya bude cike da fatan hakan ya zamo a mafarki, amma hakan bai samu ba, domin suna zaune a gabansa kamar yadda ya barsu a lokacin da zai rufe idanunsa. Wannan al’amari da me yayi kama? Shuhudan da yasha mafarki ta zama matarsa har m da ‘ya’ya a tsakaninsu it ace ake ikirarin an baiwa wani ita? Shin meye ribar wahalar sonta da yake sha? Shike nan ya tashi a tutar babu? Ya watsawa Nusaiba harara cike da takaici, y ace. “Ki barta ta fadi abunda zata fada mana”.
.
Ko me zata pada, oho! Sai ku canka!!!!!!!
Taku har kullum Sadiq Halima(Sadin Mama) 'yar Anty lol....
ausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤23¤¤
Isah ma ya harzuka, shi ma ya san Shuhuda niyyar maida masa zance ya kwana take, shi dama tuni yasan ta taba yin soyayya, dama ya yi has ashen wani dalili ne ya sad a yayi mata bayanin soyayyar ta kama yi masa kuka, har tana ikirarin ba zata iya soyayya ba.
To yau dai an yi walkiya ya ga komai tangaram! Babu inda za alayance masa, hakan ma ne ya darsar da kishin nasa wanda yak e da shi na halitta, a harzuke ya dubi Musbahu y ace.
“Ya kamata ka tashi mu koma, don ko da ace ba ni zan auri Shuhuda ba, ba azan bari ta yi aure a inda za a wulakanta tab a. Shuhuda amanita ce, b azan saurarawa duk wanda zaici zarafinta ba”.
Uncle Hamza ya dubi Isah ido tsakar kai yana mamakin yadda Isan ya yake yana wannan cika da batsewa, ya tuna lokacin yaje wurin Alh. Sada ya karbe shi hannu biyu, amma bai ba shi dammar kadaicewa da Shuhuda ba har sai ta kamala sakandire dinta. Haka Yayanta Yakub ya amince masa aurenta da farko. Sai yanzu da kaunarta t agama mamaye masa zuciya sannan za a nemi a tarwatsa masa rayuwa? Ina! Ba zai lamunta ba. Ya dai fahimta Shuhuda na sonsa, wanda dama hakan shi ne ribarsa, saboda haka zai nuna KWANJINSA don karbo soyayyarsa da ke barazana kubucewa.
Muryarsa babu kyawun amon sauti y ace,
“Malam ka taka a sannu, don kana neman aurenta ba wai ka aureta ban e. Shuhuda tana da dammar da zata zabe ni ko kai, don haka ka sanyawa ranka mun yi gamayya akan son abu daya, kowa tasa ce zata fisshe shi, amma b azan juri cin zarafi ba, don ban ma sanka ba, ba zaka ci mutunci nab a, ok?”
Maganar ta batawa Isah rai, y ace,
“Duk abinda ya samu kuda shi ya jaw a kansa, idan kuma hankaka yana yin dan kansa ga fili ga mai doki”.
Hankalin Musbahu ya tashi, saboda yadda ya ga kowanne yana muzurai tamkar zasu rukume da kokawa, da sauri ya mike tsaye ya dubi Shuhuda. Yace,
“Ku tashi mu tafi”.
Ya maida kallonsa ga Uncle Hamza, y ace,
“Malami ka yi hakuri, mu bakinka ne kada kayi fushi dam u”.
Isah ya ja wani dogon tsaki y ace,
“Hkurin me za ka bashi? Kai baka san muna da hakki a gurinsa ba? Ko yanzu bari ganin yana abokin ka idan yakama mu nemi hakkin mu, waLlahi sai mun nema sai muji ta yadda aka yi Shuhuda ta zama mayya”.
To a nan Uncle Hamza bai iya tankawa ba, illa wani mugun kallo day a ke watsawa Isah, ji yake a duniya babu wanda ya tsana sama da Isah, da ace za a bawa wani dammar kashe wani ba tare da zunubi akan wanda yayi kisan ba, hakika da zai iya dauke Isah, saboda shigar hanci da kudundunen daya soma yi masa.Gaba dayansu suka mike tsaye, Shuhuda idanunta taf da hawaye, suka fice daga gidan.
A cikin mota Isah n eke ta yarfa uwar masifa, yana kyamar tsatson Uncle Hamza tunda har suke jifar Shuhuda da miyagun kalamai irin wannan.
Musbahu ne kawai yake tausarsa, a haka har suka isa gida.
BABI NA GOMA SHA DAYA
ANYA KUWA?
Misalin karfe goma da rabi na safiya su Isah sun gama shirinsu, Haj. Asmo da iyalenta su ka rakosu har bakin mota, Musbahu na tsokanar Shuhuda.
“Ke bakauya sai ki shirya ina nan zuwa Kano neman aurenki, tunda nag a kowane tsuntsu ma hawa bishiyar yake”.
Isah ya auna masa sakon harara, y ace.
“Sai ka maida niyya, albishir daya zanyi maka, kafarda ta kaika Kano neman auren Shuhuda, ba ita zata maido ka ba”.
Nusaiba tana dariya, t ace.
“Kai ma yaya Musbahu da taya dora bari kake, ina kai ina wannan yariyar mai shanyayyar kafa? Ai ka wuce ajinta, kana ganin ko iya daura zani bata iya ba”.
“Musbahu ya fashe da dariya, y ace,
“Ai dama ba neman mai saye ake ba”.
Haj. Asmo t ace, “Kai idan zaku tafi ku tafi, kada ku tsaya yi min shirme”.
Ta mayar da dubanta ga Shuhuda t ace.
“Idan kun isa kya gaishe min da Haj. Karimar Allah Ya sauke ku lafiya”.
Su ka amsa mata da ”amen”.
Yayinda suka shige cikin motar suka tafi.
Suna tafiya a motar da farko babu wanda yake Magana, sai daga baya da tunanin ya yiwa Isah yawa, yasan kuma Shuhudan ce kadai zata iya amsa masa tambayoyin da yake da su, don haka ya dago kai ya dube ta.
Kanta a rusune yake a kasa, tana kallon yatsun kafarta. Yace.
“Shuhuda!”
Ta dago kai kadan tana dubansa. Ya ci gaba da cewa.
“Waye Yakub?”
Ya daga mata kai.
“Eh, domin a maganganun malaminki ya ambaci wani yayanki Yakub, ni kuma a sani na duk tsatsonmu bamu da Yakub, sai nake tunanin ko daga dangin mahaifiyarki ne?”
Ta girgiza kai, tukunna t ace,
“A’a, ni sam ban san waqni Yakub ba, ni ma nayi mamaki da na ji y ace waqi wani yayana Yakub”.
Yadda ta yi maganar akwai alamun gamsarwa a ciki, don haka ya yarda haka din ne, soki-burutsu ne da zafin rabuwa da masoyi ya sa Uncle Hamza ambatar sunan Yakubu a cikin maganganunsa.
To amma fa akwai alamar tambaya, kuma akwai aiki ja agabansa, saboda ya lura kamar Shuhudan tana son Uncle Hamza.
“Shuhuda wai da gasket kin san Hamza yana sonki?
Ya jefa mata wannan tambayar a ba zata.
Ta girgiza kai, t ace .
“Eh, ya taba fada min wai ya je gidanmu bayan ya je gurin Babanku ya zo namu gidan ya hadu da wani yayana Yakub ya sanar da shi yana son aure na. Sai dai ni ban dauki maganar da muhimmanci ba, saboda nasan duk gidanmu bam u da Yakub, watakila gidan su wata Shuhudar ce ya je ba niba”.
Ya dan samu nutsuwa kadan a zuciyarsa, ya ci gaba da cewa da ita.
“To ya ni kuma fa?”
Ta ce “ban gane ba?”
Ya dan juyo kadan yana kallonta, yace, “Ma’ana soyayyata a gareki”. Ya karashe maganar yana mai langwabar da kai. Tayi murmushi, t ace, “Ai kai ne masoyina, me kake tantama?” y ace. “Na sani ko za a so wani bare akan na gida?” Sai ta kama dariya, t ace. “Yaya Isah kenan, wani lokaci RANAR NAKA………. Sai naka, wani

Please Login or Register in order to submit comment