Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

samu 258point. Don haka bai samu matsala ba lokacin da ya nemi gurbin karatu a A.B.U ZARIA.
Tunda hamza ya fara karatunsa ba shi da wata matsala har ya kammala lokacin da ya dawo gida yana hutun jiran aiki.
Akawai wata yarinya zuwairiyyah diyar kanin mahaifinsa da ta so shi tun can baya, to amma sai aka samu akasi, zuwairiyya irin shagwa6a66un yaran nan ne, ba ta iya komai ba ga ta katuwar bagidajiya irin dai yaran nan da ake cewa: GIRMA YA RIGA WAYO.
Hakan ne ma ya sa koda ya nunawa mahaifinsa rashin amincewarsa ga lamarin ba su zafafafa ba, amma daya daga cikin kannen mahaifinsa mai suna Binta ta zafafa abin, wai ita don me zuwairiyya zata ce tana son hamza zai ce ba ya sonta. Kuma a biye masa? Wannan salon gur6ata zumunci ne.
Rigima aka yi sosai, dama can hamza ba ya shiri da Gwaggo binta, wata irin masifaffiyar mace ce, haka nan ta bushi iska ta zo gidan ma ta yi ta ruwan masifa.
Da yake Alh Babba mutum ne mai tsananin hakuri da son zumunci ba ya damuwa da halayyar 'yar uwarsa. Ba ma ita kadai ba duk cikin sauran 'yan uwansa shi daban yake bai dauki rayuwa da zafi ba.
Duk hutun da hamza yake dawowa yana zuwa gaishe da dangin mahaifinsa amma ba ya zuwa gidan Gwaggo binta saboda muguwar tsanar da ta yi masa tun yana yaro, har cewa take wai hamza kamar musaya aka yi aka ba wa Alh Babba shi, amma sam bai yi shige da tsatson gidansu ba.
Idan 'ya'yanta sun zo gidan, misali ace an yi katari lokacin hamza ya zo hutu ba ya kula su. Saboda yaran sam ba su da kunya wannan ya sake hura wutar kiyayyar Gwaggo binta da hamza.
A lokacin da yake aji uku a sakandire dinsa wani zuwa ziyarar dalibai da mahaifinsa ya je yake sanar masa dan Goggo Binta ya rasu, ko a kwalar rigarsa bai damu ba. Don haka da ya dawo hutun ma bai je yi mata gaisuwa ba.
Ana haka kuma auren Goggo binta ya mutu, tace: zata dawo gidan Alh BABBA kin amincewa ya yi. Don yasan zama da Binta tashin hankali ne ba karami ba. Sai dai gidan wani dan'uwan ta koma.
Ta yi zaman zawarci na shekaru hudu sannan ta yi aure. A lokacin hamza ya tafi ZARIA. Shi ma auren ba wani dadewa ta yi ba ta fito saboda rashin hakuri da munanan halayenta ba kowane namiji ne zai iya zama da irinsu Binta ba.
Ta koma zaman zawarci har hamza ya gamo karatunsa ya dawo ya fara aiki a nan cikin jahar katsina. A wata makaranta MARIAMA AJURI MEMORIAL SCHOOOL Goggon tasa ba ta yi aure ba.
Albashinsa na farko da na biyu zuwa na uku ya sayi tamfatsetsen filoti a nan cikin katsina unguwar kanada. Tafiya ta tafi ya gina gidansa ya sayi mota sai kuma maganar zuwairiyya ta kuma danno kai don har lokacin ba tayi aure ba.
A wannan karon an so fin karfinsa, to amma sai ya roki alfarma a makarantar da yake koyarwa a mayar da shi wani reshen, tunda makarantar ta kafu tana da rassa da dama a garuruwa daban-daban.
Yayi wannan hikimar ne don ya yiwa su zuwairiyya nisan zango. Idan aka ga ba ya kusa an gaji a bata wani mijin ta yi aure.
Da farko za6i aka ba shi cikin Kaduna, Jos da kuma Bauchi. Ya duba duk cikin wadannan garuruwan babu wanda ya kwanta masa a rai, ya dauki lokaci yana tunanin garin da zai za6a.
Kwatsam aka ce an turo shi Kano dama suna bukatar karin malamai. Ya yi farin ciki da hakan ko ba komai kano gari ne na cibiyar kasuwanci idan yaje kanon zai iya samun wani kasuwancin da zai yi ko ya saka hannun jari a wani kamfanin.
Hakan ko akayi, yana zuwa birnin kano ya fara aiki, a hankali kuma ya fada harkar kasuwanci ya ba wa wani abokinsa kudi masu yawa yana yi musu kasuwanci a nan kasuwar kwari.
A kuma makarantar ne ya hadu da ALJANA! Kamar yadda ya kira SHUHUDA.
WANNAN KE NAN!!!
****** ****** *****
Rashin kulawar da uncle hamza ba ya yiwa Shuhuda ya sama masa nutsuwa na gajeran lokaci ne kawai. Domin lokacin da su shuhuda suka shiga aji shida suna gab da soma jarabawa tsumin abin nan ya taso masa haikan. Ya dinga jin a duniya babu macen da yake son ya aura sama da Shuhuda.
Ta kowane 6angare jinta yake kainarta na yi masa yawa, duk kuwa da a lokacin ya fara tunanin ya komawa zuwairiyya. Saboda hakuri da juriyar jiran tsammanin da ta ke yi dominsa. Tunda har lokacin zuwairiyya ta ki aure ita a cewarta akwai ranar da mafarkinta zai zamo gaskiya. Wato ranar da hamza zai aure ta.
Da farko an so takura mata sai ta tsiro da karatu, tace lallai sai tayi karatu mai zurfi tukunna za su yi aure, wai haka uncle hamza ya sanar da mata, don haka aka zuba mata na mujiya(idanu).
To lokacin da uncle hamza ya daina kula shuhudan sai ya ji kamar ya komawa zuwairiyya saboda shi ma a lokacin Alh Babba ya soma korafin rashin aurensa. Allah ya sa bai yi saurin jefa kansa a ragaya ba sai kuma ga shi ya koma ruwa tsundum! Akan kaunar Shuhuda, yarinyar da yake da hujjojin kiranta Aljana.
Wannan shi ne kwan-gaba-kwan baya, ma'ana yasan abu amma ya kasa aminta da sanin sa. Hujjoji dai sun bayyana a gare shi Shuhuda aljana ce, ba ita kadai ba duk wani wanda ya ra6eta shi ma jinnu ne, to amma kuma ya kasa amincewa kin yin mu'amala da ita. Mu'amalat ma irin wadda yake sa ran zata zamo uwar 'ya'yansa.
Da zarar ya dora idonsa akanta wani irin abu ne yake ji yana fizgarsa, idan ya so sharewa sai ya ji idan ba tsura mata ido ya yi ba, ba zai samu sassauci ba. Don haka ba ya iya hassalawa kansa komai idan ba ya yi kokarin kawar da idonsa daga gare ta ba.
Hasalima gaba daya gangar jikinsa yake ji ta yi masa nauyi, tamkar an daura masa gungumemen dutse, sai dai kuma ya kasa tunkararta, domin a duk lokacin da ya dauki damarar zuwa inda take da maganganun soyayya sai ya dinga jin faduwar gaba.
Yanzu kam shuhuda ta gama rikita masa zuciya da kalbinsa, yanzu haka ma da yake zaune a falonsa, yana tunanin hanyar da zai soma bi domin sake bayyanar da soyayyarsa ga shuhuda.
Uncle hamza ya sauke doguwar ajiyar zuciya. Ya sa hannu ya dauki hankici ya goge gumin da ya jike shi sharkaf Ta kowane 6angare jinta yake kainarta na yi masa yawa, duk kuwa da a lokacin ya fara tunanin ya komawa zuwairiyya. Saboda hakuri da juriyar jiran tsammanin da ta ke yi dominsa. Tunda har lokacin zuwairiyya ta ki aure ita a cewarta akwai ranar da mafarkinta zai zamo gaskiya. Wato ranar da hamza zai aure ta.
Da farko an so takura mata sai ta tsiro da karatu, tace lallai sai tayi karatu mai zurfi tukunna za su yi aure, wai haka uncle hamza ya sanar da mata, don haka aka zuba mata na mujiya(idanu).
To lokacin da uncle hamza ya daina kula shuhudan sai ya ji kamar ya komawa zuwairiyya saboda shi ma a lokacin Alh Babba ya soma korafin rashin aurensa. Allah ya sa bai yi saurin jefa kansa a ragaya ba sai kuma ga shi ya koma ruwa tsundum! Akan kaunar Shuhuda, yarinyar da yake da hujjojin kiranta Aljana.
Wannan shi ne kwan-gaba-kwan baya, ma'ana yasan abu amma ya kasa aminta da sanin sa. Hujjoji dai sun bayyana a gare shi Shuhuda aljana ce, ba ita kadai ba duk wani wanda ya ra6eta shi ma jinnu ne, to amma kuma ya kasa amincewa kin yin mu'amala da ita. Mu'amalat ma irin wadda yake sa ran zata zamo uwar 'ya'yansa.
Da zarar ya dora idonsa akanta wani irin abu ne yake ji yana fizgarsa, idan ya so sharewa sai ya ji idan ba tsura mata ido ya yi ba, ba zai samu sassauci ba. Don haka ba ya iya hassalawa kansa komai idan ba ya yi kokarin kawar da idonsa daga gare ta ba.
Hasalima gaba daya gangar jikinsa yake ji ta yi masa nauyi, tamkar an daura masa gungumemen dutse, sai dai kuma ya kasa tunkararta, domin a duk lokacin da ya dauki damarar zuwa inda take da maganganun soyayya sai ya dinga jin faduwar gaba.
Yanzu kam shuhuda ta gama rikita masa zuciya da kalbinsa, yanzu haka ma da yake zaune a falonsa, yana tunanin hanyar da zai soma bi domin sake bayyanar da soyayyarsa ga shuhuda.
Uncle hamza ya sauke doguwar ajiyar zuciya. Ya sa hannu ya dauki hankici ya goge gumin da ya jike shi sharkaf Zuciyarsa ta jagule, yana son furtawa yana tsoron abin da zai biyo baya. Shin zai amince ya sake saka rayuwarsa a tarkon aljana? So wani irin makahon abu ne, duhu ne da shi wanda yake makantar da zuciya gami da idanu tsinkaye da tarin kalubale.
Idan haka ne so ya taka muhimmin rawa ga uncle hamza tunda ya hana ganin duhun son da zai fada.
Cikin rashin walwala ya mike tsaye ya shiga bandaki ya yi wanka, sannan ya dawo falon, ya dauki wayarsa yaga yana da kiran da aka rasa(missed call) guda sha uku, ya duba duk lamba daya ne aka kirashi da ita. Kuma babu suna ma'ana bakuwar lamba (New number) ce.
Sannan yana da rubutaccen sako guda biyu baki wanda bai karanta ba. Ya buda daya daga ciki ya soma karantawa kamar haka:-
" Wata rana mai dumbin tarihi wadda ta kasance LITININ an yi kullaliya mai kulle kwalwa da tunani. Ranar litinin an rasa an kuma samu . Ranar litinin anyi katari da wani shamaki, bayan wasu al'amura masu murdiya da murde kwalwa. Shin mai yasa wannan rana ta kafu da murdaddun abubuwa? Tambayar ke nan!"
kuma a zahiri karshen sakon ke nan. Yanayin uncle hamza ya bayyanar da matsananciyar damuwa, rudani gami da razana. Bai san ina sakon ya sa a gaba ba, bai san wanda ya turo sakon ba, bai san me yasa aka turo sakon gare shi ba......
Da sauri ya buda dayan sakon don karasa tantance abin rudanin , shin shi aka aikowa ko kuwa dai halin network ne kamar yadda ya dauki lambar Najeriya ya kaita Misra?
" Rayuka cikin kunci ba karamin tashin hankali ba ne, ace dan Adam ya rayu a gurbin da ba wanda ya sani anbin a tausaya masa ne. Shi yasa ta ke ba ni tausayi, nakan ji alhini game da lamarinta. Amma babu komai akwai Allah, shi ne maganin komai. Amma zaluncin ya yi yawa....."
Iya rudewa uncle hamza ya shiga, ya rasa ma yadda zai fassara wannan cukurkudadden al'amari, hakika ko tantama babu halin network ne. Amma saboda ya fita daga wasu-wasin da yake ciki, sai ya kira lambar.
da Hausa Book stories
MATA UL hAYAT
¤¤14¤¤
Bugu daya kuwa ta shiga amma har sai da ta gama ringin ba a daga ba, ya sake kira a karo na biyu shi ma ba a dauka ba.
Kamar ya share, sai da aka dauki tsawon lokaci sannan ya sake kira. A wannan karon an dauka, muryar mace ce ya ji: kuma kamar ya ta6a jin muryar. Bayan ta gaishe shi yace: Yauwa don Allah wa ke magana? Cike da tsananin mamaki aka amsa masa.
Wake magana fa ka ce? Amma wallahi Yah hamza ban san me ka dauke ni ba. Wai don Allah me ye aibuna da ba ka damu da ni ba? Ya ji tsau! A dukkan sassan jikinsa, idan dai idanunsa biyu ne yana a farke to zai iya cankar sunan wadda ke magana, amman ta yaya hakan ta faru? Ko dai mafarki ne? Da ta ji ya yi shiru bai tanka ba, sai ta ci gaba da cewa:
Ace wai ko arzikin ajiye lambata a wayarka ba ni da shi a gurinka? Haba don Allah, aiko ba ka so ni don kyauna ba, ka so ni don arzikin alakar da ke tsakanin mu ta 'YAN UWANTAKA.
Idan ba ka so ni don haka ba, ka so ni ko don saboda shekarun da na share ina jiranka. Ka dai san ba rasa samari na yi ba, amma na jure ina zaman jiranka, karshe sai ka saka min da haka?
Har yanzu bai tanka ba, har sai da ta dure da maganganun nata ta kuma sanya masa kuka, sannan ya samu karfin gwiwar cewa: Na ji dai na kukan ki nutsu ki min bayanin wadannan sakonnin naki, don kwata-kwata ban fahimci inda kika dosa ba.
Ta tsagaita da kukan tana cewa:: Kawai na turo maka ne ganin cewa ba ka damu da ni ba, ka manta da babina a rayuwarka, ko dan kiran da kake yi min a da muna gaisawa yanzu sam ka daina. Yace: To layin waye wannan? Tace: Wai da gaske da ba kada lambata din ke nan?
Shi kansa sai yaji ba dadi kuma ta ya aka yi ya rasa lambarta a wayarsa bayan yasan yana da ita? Bai sani ba! Don haka sai yace mata : Wayar ce ta samu matsala shi ne cire layin na saka a wata wayar. Lambar ki tana a cikin waccan wayar, don a waya (phone) nake ajiye lambobi.
Sai ta dan washe kadan tace:
Sai ta dan washe kadan tace: Shi ke nan, amma don Allah Yah hamza ka daina yi min abin da kake min, ka tuna irin dumbin son da nake maka......
Ya katse ta, kada ki damu.....
Ita ma ta katse shi, Ya zaka ce kada na damu bayan kai baka damu da ni ba? Yace: Duk da haka, ai nace kada ki damu ko? Ki bari karshen watan nan zan zo, tunda 'yan jarrabawa sun kusa kammalawa.
Tace: Shike nan Yah hamza sai ka zo. Ya kashe wayar yana kallon fuskar wayar(screen).
Zabura ya yi ya mike tsaye sakamakon sunan ZUWAIRY da ke yawo akan madubin wayar, lambar da ya kira ce ta koma haka. Ko kuwa dai bai sani ba hannunsa ya lulubo lambar zuwairiyya har ya kirata.
Sai ya shiga neman lambar har kundin ajiyar rubutaccen sako(inbox) sai da ya shiga, amma dai sunan ZUWAIRY ya gani dauke da wannan sako. To ya haka?
A da yana zargin shuhuda ce aljana to yanzu ma ya dora alamar tambaya ga Zuwairiyya, domin yadda al'amuran suka faru ba su da maraba da aikin jinnu, ko kuwa shine ma aljanin bai sani ba? Ya shiga tuhumar kansa.
Cikin kwana biyu uncle hamza ya rame, ya susuce saboda tsananin damuwa da tunani da ya sakawa kansa. Sam ba ya cikin nutsuwarsa, ko abinci ba sosai yake ci ba. Illa kayan gwangwani ko na kwali. Hatta abokinsa zaharaddeen Lawan ya fahimci halin da yake ciki. Sai dai ko da ya tambaye shi amsar da ya ba shi ita ce.
" Ba ni cikin nutsuwa, ban san kuma yadda zan kwatanta damuwata ba". Don haka zaharaddeen ya tsura masa idanu, dama yasan hamza mutum ne mai zurfin ciki, sai ka ce bafulatani.
An fito daga jarrabawar Biology, daliban ilimin kimiyya(science) sun taru a lab. Saboda malamin Biology yace za su yi hotuna, tunda wannan shine karo na karshe na shigarsu lab din Biology.
Uncle hamza yana daga cikin malaman da suka tsaya kai da fata gurin gudanar da jarrabawar, don haka shi ma yana cikin jerin malaman da suka nufo lab din daukar hotunan.
An shirya kowa aka soma dauka, kowane dalibi cike yake da farin ciki, suna ganin darajarsu ga malamai, tunda har suka bukaci yin hotuna da su.
A 6angaren uncle hamza zan iya cewa ya fi kowa farin cikin daukar wadannan hotuna ko ba komai akwai HASKEN ZUCIYARSA a ciki. Tunda dama yana son mallakar hotonta, amma ya rasa ta ina zai fara, sai ga dama ta zo masa, don haka cikin doki ya kosa a dauki hotunan, wanda ya tsaya a bayan Shuhuda yana murmushi.
Bayan an gama daukan hotunan bai samu yin magana da shuhuda ba, sakamakon aikin hada takardun da ya tsare shi.
Lokacin da ya samu sarari sai nemanta ruwa a jallo bai gan ta ba. Yana da tabbacin tuni ta dade da komawa gida. Don wannan al'adarta ce, tun ma kafin soma jarrabawar da zarar an tashi ba ta tsayawa jinkirin komai ta ke tafiya, to dama ita ba kawaye ba bare ace sun tsare ta.
Yayi takaitaccen murmushi, tare da lasar busassun la66ansa tukunna ya wuce izuwa mota.
Ko a cikin motar ma kafin ya tafi ya dauki wani lokaci yana jin dadin daukar hoton. Wannan dama ce da zai yi amfani da ita gurin kwantarwa da Alh Babba hankali, zai nuna masa hoton shuhuda a matsayin matar da zai aura. Inyaso an shafa masa lafiya akan zuwairiyyah, tun da shi dai Allah bai saka masa sonta ko kadan a cikin ruhinsa ba.
Shi kuwa ingancin zaman aure yana ta'allaka ne da ingantacciyar kauna. Da zarar aka ce anyi aure daya ba ya so, dayan ma musamman namiji to kuwa za a yi katari da abubuwa marasa dadi, to bare kuma shi da zuwairiyya wanda akwai karfaffen zumunci a tsakaninsu.
Da wannan tunani ya tayar da motar ya nufi gida.
Washegari aka wanko hotunan, a ranar kuma bau jarabawa, Mr philips ya kira shi a waya ya sanar masa an wanko hotunan. Don dama tunda aka gama dauka yace a wanko masa duk wanda shuhuda ta ke ciki. Har Mr. Philips yana dariya yana cewa: " ko dai ita ce Lobi din ne?"
¤¤¤
.
A lokacin da wayar ta same shi yana kauwar kwari inda zaharaddeen yake gudanar da kasuwancinsu, kaya ne aka kawo daga MALAYSIA, don sun jefa hannun jarinsu da wani kamfanin Material da ke Malaysia shi yasa suke kawo musu kaya akai-akai.
Babu laifi kuma wannan ya kara janyo musu daukaka, don ba karamin abin mamaki ba ne daga fara kasuwancinsu a kasuwar kwari duka-duka shekaru biyu da watanni, amma suin shahara irin haka. Wanda ga wadanda suka share shekaru aru-aru amma ba su yi irin wannan shaharar ba.
To shi da ma kasuwanci ribarsa saukaka abu, da zarar mutum ya yi hakuri da riba kadan, sai ya tarar da tarin alkhairai. Amma muddin za a tsauwala to kuwa akwai ragee kwarjini da kuma dakusar da kasuwancin.
( Don Allah 'yan kasuwa mu duba wannan lamari, barin ma idan Sallah ta zo ko Maulidi sai ka ga an dauki dogon buri an dora a lokacin. Wanda babu wanda ake cuta sai talaka. Shi kuwa talaka abin tausayi ne akan komai na rayuwarsa).
Zaharaddeen ya dago kai ya dube shi da yaga ya mike tsaye yace: Ina kuma zaka je? Uncle hamza ya juyo da kansa yana dubansa, yace: Zan je na dawo ne, ba dadewa zan yi ba.
Yana karashe fadar haka bai jira amsar zaharaddeen ba ya sa kai. Sauri-sauri, gudu-gudu har ya isa inda ya ajiye motarsa ya shiga ya tayar da ita. Nan da nan ya isa gidan hoton Mr. Philips, suka gaisa, mr philips yana dariya ya dauko hotunan yana cewa:
Gaskiya yarinyar nan tana da kyau duba ka ga yadda tayi kyau a dukkan hotunan nan, duk fa ta fi kowa yin kyau. Cikin harshen turanci yake maganar uncle hamza ya kai hannu ya kar6a. Idanunsa suka kai ga abin al'ajab! Tashin hankali aka ce wanda ba a saka masa rana.
Ya gigice ya kuma razane duk a sanadin abin da ya gani a jikin hoton. Maimakon ganin shuhuda sai ya ga taswirar zuwairiyya.
Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤15¤¤
Mr. Philips ya dube shi cike da tsananin mamakin yanayin da ya gani a tare da hamza, yace: Lafiya? Uncle hamza sam wuta ta dauke masa. Abin da yake damunsa shine: ta ya aka yi zuwairiyya ta shigo a cikin hotunannan da suka dauka a makaranta? Ina inuwar shuhuda ta shiga a cikin hotunan da bai ganta ba?
Shuhuda ce ta yi wannan kullalliyar tunda ta kasance aljana. Su kuwa jinnu sukan yi fiye da hakan! Abin da zuciyarsa ta ayyana masa ke nan. Bai san yadda zai yiwa Mr. Philips bayani ya gamsu ba, don haka sai wayancewa ya yi da yin murmushi yace: Kyawun da ta yi ne ya firgita ni.
Mr. Philips ya dan daki kafadarsa yace: Kai mutumina zaka fa more idan ka mallaki wannan zukekiyar yarinyar. Murmushi kawai uncle hamza ya yi ya dauko kudinsa ya bashi, tukunna ya masa bankwana ya tafi.
Travelling bag dinsa ya saka hotunan bai kuma bin ta kansu ba. Haka bai kuma bi ta kan shuhuda ba, don ko da suka dawo yin jarrabawa yana kallonta amma ba ya kulata. Wannan yana daga cikin matakan da ya dauka na kauracewa abin da zai saka shi da-na-sani.
Ranar asabar yana zaune a falonsa yana lissafa wasu kudi da zaharaddeen ya kawo masa na ribar da suka samu a wasu kaya da suka shigo dasu. Wayarsa ta yi kara, yana dubawa lambar yayansa Alh Mukhtar ya gani akai.
Cikin girmamawa ya dauki wayar suka gaisa, Alh Mukhtar yace: Dama Abba ne ba shi da lafiya yana asibiti, sun ba shi gado shine na ce bara na sanar maka. Hankalin uncle hamza ya tashi, cikin rudani yace: Mai yake damunshi?
Alh Mukhtar yace: Ciwon hanta ne, mu ba mu san yana da shi ba, wai ashe dama ya dade yana fama da shi yana zuwa ganin likita a 6oye. Uncle hamza yace: Allah ya ba shi lafiya, ina nan tafe anjima. Suka yi sallama ya tashi ya soma shiri.
Karfe uku na yammaci ya isa birnin katsina, a gidansu ya fara sauka ya tarar da su Goggo binta duk suna gidan har zywairiyyah. Suka gaisa ya ajiye jakarsa ya nufi asibiti.
Ya tarar jikin da sauki, don har ma ya samu bacci, saboda haka ya dawo gida. Ya tarar da tashin hankalin da ya hautsina masa kwalwa a lokacin da ya shigo gidan.
Goggo binta ce rike da hotunansa da ya saka a jakarsa, tana kururuwa wai hamza zai janyo musu MUGUN IRI a zuri'a, tunda yake yawo da hotunan MAYYA a jakarsa! Zuwairiyya kuwa sai kuka take ana rarrashinta, tana kuma rusa ihu barin ma da ta ga uncle hamza ya shigo gidan.
Cikin sanyin jiki da takaicin binciken da aka yi masa ya karasa ya kar6i hotunan ya ga ba ZUWAIRIYYA? to ya haka? Ko kuwa dama idanuwansa ne a wancan lokacin suka yi masa gizo, suka nuna zuwairiyya a maimakon shuhuda?
Muryar Goggo binta ce ta katse masa tunani, inda ta ke cewa: Wallahi ita ce ta lashe MAS'UD, diyar fa KARIMA kishiyata ce, wadda ta yi sanadin mutuwar aurena! Yarinyar nan muhun iri ce, domin ta lashe ma wata mata daga ta tsarga yatsanta. Gadon mugun abu ta yi, kuma na tabbata tunda na ga hotunanta a tare da hamza shi ma so take ta lashe kurwarsa.......
Haj Mardiyya ta katse surutun da cewa: Ya isa haka binta, ya kamata mutuna halin da muke ciki. Uncle hamza bai ce komai ba, ya saka hotunan a jakarsa ya fice zuwa dakin kaninsa salisu.
Koda ya shiga dakin tunani ya sha masa kai, ya auna maganganun Goggo binta, sannan ya daura al'amuran da suka faru gare shi, shin da gaske mayyar ce? Ko kuwa aljana dai? A'a wata halitta ce daban! Ya rasa inda zai dorata a matsayi, mutum-mayya ko kuwa aljana-hatsabib
iya?
.
****** ******* *****
.
BABI NA BAKWAI
.
.
TSAUTSAYI KO KADDARA?
.
Daya ga watan satumba, wanda ya kasance ranar litinin jirgin Egypt air ya sauka a birnin Egypt bayan da ya taso daga senegal don sauke wasu fasinjoji(pasingers)kafin daga bisani ya yi hutun awa daya da rabi, sannan ya dage zuwa birnin kano.
Kamar yadda yake a bayyane masu Transit visa wucewa zasu yi, idan jirgin nasu ya huta ba tare da ko airpot din sun fita ba.
bare ganin yanayin gari, ko yin wasu mu'amaloli nasu abinsu.
Da yawan mutanen da ke cikin jirgin dalibai ne, wadanda suka kammalo digiri dinsu a kasar senegal, wasu kuwa 'yan kasuwa ne da ke zuwa siyayya, don haka mafiya yawan mutanen ciki kabilu ne farare, dai-daiku ne bajkaken wadanda sauyin gari, cima, yanayi da kuma kwanciyar hankali ya sanya suka saje da fararen fatan, amma dai kana kallonsu kasan asalinsu bakar fata ne.
Bayan jirgin ya sauka, fasinjoji suka soma saukowa, ISAH SADA RABI'U yana daya daga cikin masu saukowa daga jirgin. Amma shi zai shiga cikin gari ne saboda yana son ganawa da wani malaminsa da yake mazauni a kasar Misra, aiki ne ya jai shi can kasar senegal daga baya kuma ya dawo kasarsa ta haihuwa.
To sun yi da Isah idan zai koma

Please Login or Register in order to submit comment