Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zauna lafiya. Maganar kwalwa da Shuhuda ta ked a ita, hakan Allah Ya yita ita din mai kwakwalwa ce, sai dai akwai abubuwan da ta yi wanda daya daga cikin bayin Allah nan guda uku ne ya yi jagorancin yinsu. Misali lokacinda tana aji hudu ranar da aka kawo wannan………”
Ta nuna Uncle Hamza ta cigaba da cewa.
a Hada Hausa Book stories
MATA’UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤31¤¤
“a matsayin sabon malami, ya yi musu tambaya akan RADIOACTIVITY ta bayar da amsa, amma a zahiri ba it ace ta bayar da amsar ba, saboda a duk lokacin da hankalinta ya gushe bat a ma inda ake tsammaninta. Sannan irin haka tta sha faruwa da Shuhudan, a dauketa a samara da wata. Mas’ud ya bugi Shuhuda a lokacinda suka je Katsina har ya ji mata rauni don huce haushin dukan da mahaifinsa ya yi masa saboda mahaifiyarta Karima, shi ma yan kungiyane suka halaka shi. Dr Ya’u ma ya rasa ransa net a sanadin kungiya saboda su a ka’idarsu shugabansu bay a rashin lafiya ya je asibiti kai tsaye,suna da likitocin da ke kula da wannan bangaren, kai yawa ne fa da su ta kowanne bangaren ma’aikata da ke Nigeriyar nan, abin kunya ne matuka a garesu ace wani ya fitar da jinni ga shugabansu, sun bar shi da rai Shuhuda ta yi amfani da sunan Izra’el a wajen Uncle Hamza, da nufin sunanta ken an a lokacin ba it ace ta furta hakan ba,BAWAN ALLAH ne ya furta kamar yadda na fada muku a duk lokacin da hankalinta ya gushe bat a a muhallin, sai an samara da wata, shi yasa lokacin da Uncle Hamza ya sake tambayarta me yasa take amsa sunan Izra’el a matsayin sunanta ta nuna bat a san ta yi hakan ba, tabbas din bat a da masaniya. Hikimar yin hakan shi ne, tun lokacin da bawan Allah ya lura da Uncle Hamza ya shigo rayuwar Shuhuda sai ya yi tunanin ta hanyarsa za a samu a gano matsalar da Shuhudan ked a ita, shi yasa Hamza ya dinga katari da abubuwan rudani game da Shuhudan. Amma sai ya dauki abin kwalwa ce ya yi mata yawa kamar yadda wani abokinsa Dr Ishak ya sanar masa ana samun irin yaranda ked a kwalwa irin tata su kuma kasance da irin abubuwanda yake ganinta da su. Ko kuma yana dubanta a matsayin burkakka mara hankalibkamar yadda Inna Yaduwa itama ta ke ganinta a hakan. Wata rana Inna Yaduwa ta zo dukan Shuhuda hannunta ya srke, bawan Allah ne da alohakin hakan, duk dai akan turbar haska mata akwai babban al’amari a tare da Sahuhuda……….” Alh .Ahmad ya katse Shuhuda Ibn Khaddab da cewa. “wai shin duk a ina kukasami wadannan labaran? Idan dai kun kasance mutane ne ku, to muna bukatar Karin bayanin ta yadda aka yi kuke da sani na abubuwanda zai yi wuya ku iya sani kai tsaye sakamakon karancin shekarunku”. Yakub ya yi murmushi, y ace. “ai cikin sharadinmu da ku, ba zaku yi mana tambaya ba har sai mun gama sanar da ku labaran da muke son sanar da ku. Idan kuma kunce lallai sai mun sanar da ku yadda aka yi muka samu wannan labaran, hakika abin da ake gudu zai faru, zaku rasa Shuhuda ‘yar ku, rasawa ta har abada, wanda hakan ba karamin barazana ban e a gareku ba, domin laifin wani ne ya shafeta”. Sai aka yi shiru, Shuhuda Ibn Khaddab ta ci gaba da cewa bayan ta fasali.
*****
“idan dare ya yi maji dadin kungiyar mai suna Mandus yakan zo ya dauki Shuhuda ya kai ta guraren da ake shakatawa ake casu don girmamawa a gareta. Wannan tsarinsu ne ma ji dadi shi ked a wannanaikin. Wani lokaci Shuhuda ta taba fadawa Hamza takan ganta a wata daula tana rawa tana shan ruwa a cikin koko, bawan Allah ne ya yi hakan duk a cikin abin da yake faruwan na gushewar hankalinta a samara da wata, ya yi hakan ne domin haskawa Hamzan, amma bai gane ba sai ma ya dauki abin a BARA-DA-BANA, saboda an yi amfani da kalmomin sakayau da kuma nannauya. Mu koma sirrin Network wato sabis ken an, lokacin da Inna Yaduwa ta so dukan Shuhuda hannunta ya sake, ta shiga daki ta dauki waya don ta kira wani ta sanar masa halin da ake ciki, amma sai wayar ta mutu. Abin day a faru shi ne, idan har Inna Yaduwa zata yi tunani daga ta zo dukan Shuhuda sai hannunta ya sake haka kawai? Ai dole akwai sanadi, ita ba sanadin ta ke tuhuma ba, a’a burinta ta sanar a zo a dauke mata Shuhuda daga gidanata ba jikanyarta b ace. Wata rana tunani ya yiwa Hamza yawa game da Shuhuda, ya kira lambar da mutumin day a kira kansa da Yayanta ya ba shi, ya kira maimakon ya ji sautin tiring-tirin irin na Mtn, sai ya ji tiring sau daya wanda hakan ke nuna wani layin ne ya kira bayan shi kuma yasan MTN ne. ba a dauka ba, har sau biyu yana kira ba a amsa kiran ba. Can aka kira shi da bakuwar lamba, daga kasar waje aka sanar masa Abubakar Ibn Khaddab ne daga Misra, wai ya kira lambar ne shi a tunanin Hamza matsalar network ne, wanda duk kadan ne daga cikin hikimomin bayin Allah da za a gane akwai wani sirri dangane da Shuhuda”. Ta dan saurara da bayar da labarin tana kallon Uncle Hamza fuskarta cike da murmushi. Y zuwa yanzu ko ba a fada musu ba sun gano ko su waye wadannan bayin Allah wato dais u ukun nana sun e aljanun!
*
(kun sani typing cikin dare ina yi ina hawaye :’( :’( :’( ……………)
Ko da yake J ALLAH na tare da ni don addu’a it ace takobin mumini ALHAMDULILLAH Sadin Mama)
*
Dukkansu matsanancin tsoro ne ya dirar musu, domin bas u taba tunanin hakan ba, Shuhuda= Ibn Khaddab ta ci gaba da cewa “Hamza an turo maka rudadden sako wand azan iya cewa ya juyar da tunanika, da ka kira lambar kuma sai ka yi katari da samun kanwarka kuma wadda ta ke son ka aureta ZUWAIRIYYA. Alal hakika Zuwairiyya ta fi ka gaskiya, domin itama ta turo maka sako a lokacin tana Magana game da irin son da take yi maka kai kuma ka yi watsi da hakan, shi yasa ta yi mamaki da ka nemi juyar da tunaninta. Ranar littinin ne suke yawaita yin taron kungiya. An hasasa maka Shuhuda tana rayuwa cikin kunci saboda azal din day a fada mata shi yasa wanda ya turo maka sakon yake jin tausayinta. Hikimar juye suffer Shuhuda a hotoin da kuka dauka a library lokacin yin candy dinsu, don ka gane akwai boyayyen sirri, matsalar kasancewarka mai zurfin ilimin addini. Amma sai hakan ya sanya ka rudani, ka rasa wace ce aljana a cikin su biyun, Shuhudan ko Zuwairiyya? Karshe kai kanka said a ka dinga tabbatar zamowarka bil’adama”.
Shuhuda Ibn Khaddab ta mayar da dubanta ga Isah, sannan ta ci gaba da cewa tana dai murmushi. “mun hadu da kai a birnin Misra ranar da ka baro Senegal, sannan mun hadu da kai a Katsina, mun sake haduwa da kai a Ibadan har ka samu budaddiyar wasika, koda yake kafin haduwarmu da kai a Katsina da Ibdadan, wasu murdaddun abubuwa sun faru, masu SARKAKKIYA, misali, furtawa Shuhuda da ka yi kana sonta ta ki amincewa, a ranar ne ka yi mafarki Shuhuda ta kima Zakanya tana cinye kananan dabbobi. Da ka je dakinsu ka tarar cikinta na juyawa kamar kwallo wannan duk aikin bawan Allah ne. washegari kan son yi mata maganar amma ka rasa yadda zaka furta a haka har kwanaki biyu, ka taba cikin a cikon kwanaki na biyun, wanda daga lokacin ne ba ka kuma mafarki da Shuhuda ba, kuma a washe garin ta amsa soyayyarka. Dalilan da suka sa Inna Yaduwa ta dinga jin tsoron Shuhuda a dukblokacin da ta so furta wani al’amari shi ne, an shirya kasha Inna Yaduwa a can kungiya, saboda dodon tsai ya bukaci hakan, har aka bai wa Shuhudan wani kaho wanda zata zuki jinin Inna Yaduwar hakan bai samu ba.wannan shi ne sanadin da bawan Allah yayi kafi a gidan hatta Shuhuda said a aka neme ta a kungiya sama ko kasa bas a ganinta muddin dai a gidan za a zo daukarta to ba za a ganta ba. Wannan mataki da bawan Allah ya dauka ya samo shi ne daga sarakunan fararen aljannu na lardin kasar Misra. Shekara da shekaru bawan Allah na neman hanyar da zai kubutar da Shuhuda daga halaka, amma bai samu ba, sai wannan lokaci day a soma samun nasara ta batar da gidan nan daga idanun masu sirri, wannan rufaffiyar robar it ace sirrin batar da gidan. Wannan shi ne karshen labarina wanda ya hattama zare na biyu”. Yakub ya yi saurin magantuwa tun kafin wani ya tanka, y ace. “zare na biyu ya kamala, ni zan ba ku labari na karshe”. Kowa dai ya zuba masa ido ya ci gaba da cewa.
BABI NA SHA TARA
WARWARA
“ba wasu ban e bayin Allah da ke hidima da Khashim Tsagem illa mu ukun nan!!!!!!! Tabbas mun kasance daga cikin jinsin jinnu, kada ku tsorarta domin lamarin yanzu ya wuce matakin tsoro, idan kuka yi la’akari da sanin sirrin da muka yi, kai tsaye dama bai kamata ku danganta mud a bani ‘adama ba”. Alh. Sada mai dakakkiyar zuciya y ace. ”idan ba zaku damu ba, zan so kai tsaye ku fada mana yanzu abin da ke tare da Shuhuda, da kumja abinda za a yi a cireta dag kungiyar matsafa, tunda kun ce ku masu taimako ne a gare mu, kuma kuna da sani na sirrin masu sirri, sai nag a mafita kawai ya kamata ku kawo mana!” yakub yayi gajeren murmushi, sannan y ace. “tunda kuka yi hakurin sauraren labarin da aka ba ku a baya, yanzu ma hakurin ya kamata ku sake yi, garaje ba shi da amfani, musamman kasancewar saura zare daya ne labarin ya kamala. Sannan mu kai matakin WARWARA. Rashin hakurin sauraren karshen labarin ba zai kawo samun WARWARAr labarin ba. Don haka ku yi hakuri da juriya a karasa”. Alh. Rabi’u ya magantu.
“Babu matsala, kuna iya ci gaba da labari”. Inna Yaduwa kam ta yi duru-duru, tsoron su Ykub ya ci gaba da tsirga mata jiki. Yakub ya dora da cewa. “Rashin ganin Shuhuda a kungiya ba karamin damuwa suka shiga ba, koda yake sun dauki mataki akan haka duk lokacin da Shuhuda ta fita zuwa wani guri suna samun nasarar dauketa su kai ta kungiyar. Sun yi iya bincikensu don gano sanadin da yasa bas a samun nasarar ganin Shuhuda yayin da take gida, hakan ya ci tura, sun kasa gano komai, babu abin da suke gain a cikin madubin tsafinsu face DUHU dun-dum! Idan sun kai ta kungiya suna tuhumarta abubuwa da dama, sai dai ta kan manta abubuwan da ta sani yayin dab a ta cikin kungiya, don haka bat a iya bas u amsa game da tambayoyin da suke yi mata. Ganin wannan yanayi da suka samu kansu ya sa Alh. Nuraini wanda yak e da mukamin kujerar SANIN SIRRIN KUNGIYA wato DANMASANIN KUNGIYA ya yi gagarumin shiri na daukar mataki……..
Koda ya ke ku yi hakuri ban gabatar muku da zaren d azan kama ba, hakan ya faru sakamakon dokantuwa da na yin a karashe muku labarin tun kafin ya gundure ku kamaryadda na gain a kwayoyin idanun wasunku labarin ya soma gimsarku. Ni zan ba ku labari game da kungiya da abin da shafi Shuhuda a zamanta na kungiya, zuwa samuwar ciki da halin da Shuhuda ta ke ciki a halin yanzu, da yadda za a bi a warware matsalar idan Allah Ya nufa hakan mai yiwuwa n eke nan”. Babu wanda ya tanka, ya ci gaba da cewa “ Alh. Nuraini ya dauki matakin sanin sirrin day a sa ba a ganin Shuhuda akai-akai a kungiya, matakin day a dauka kuwa shi ne. yana da wani kaskon wuta, wanda babu komai a cikinsa sai garwashi yana sirrin wuta, ya samu wannan kaskon wata ne bayan shekaru shidda da mutuwar Sagir wani kasurgumin matsafi ne dan wata kungiya da suke abota ya ba shi kaskon wutan a wani zama da suka yin a gamayyar wasu ‘yan kungiyoyi don kare kansu daga kalubalen da suke fuskanta na barazanar wasu mutanen.Dama sukan yi irin wannan zama ta hakan ne yasa wasu ‘ya’yan kungiyoyin suka hadu da wasu ‘ya’yan kungiyoyin suna mu’amala. To a irin wannan zama da suke yin e Alh Nuraini ya fadawa abokinsa halin da kungiyarsu take ciki, shi ne ya bashi wannan kasko, ya umurce shi day a dinga kadaita a daki shi kadai ya sanya wani garin magani day a ba shi a cikin kaskon wutar, zai ga komai. Hakan kuwa ya yi, sai dai bai iya ganin sirrin da zai faru a gobe ba, tunda a lokacin Shuhuda na zuwa kungiya, kuma ana komai yadda ya kamata da ita. Duk wasu shirye-shirye danake yi bana tunanin ko sau daya Alh Nuraini ya sani,harzuwa lokacin da aka daina ganinta a kungiya, sai idan ta fita daga gidan kawai ake samun nasarar daukarta. Shima saboda a wajen babu magungunan da muka saka a cikin gidan.wata ranar liyyinin suka sami nasarar daukar Shuhuda lokacin suna cikin mota a hanyar su ta zuwa Katsina………….”
Da ya zo nan, sai ya tsaya ya dubi Isah, y ace masa. “Zka iya tuna hirarrakin da suka gudana a tsakaninku?” Isah day a kasa kunna yana sauraren rudadden al’amarin nan ya gyada kai, tukunna ya labarta musu hirar da suka yi da Shuhuda tun daga lokacin da suka bar gida garin Kano har zuwa Katsina, da kuma lokacin da suka tafi Karare,kauyen karamar hukumar Btsari gurin Hajiya Karima. Yana karashewa Yakub ya yi murmushi, ya ci gaba da cewa. “watakila zaka yi mamaki idan n ace ba Shuhudar da ka sani a matsayin kanwaraka b ace kayi hira da ita hart a ce zata yi maka kyautar dan mutum, wadda kuna karashe hirar ka juyo ka gat a bingire da bacci”.
Mamakin said a ya bayyana karara a fuskar Isah, Yakub bai bari Isah ya tanka ba, ya ci gab da cewa. “to Shuhudar da kuka yi hira ba it ace Shuhdan da ka sani ba, wata ce aka samara musamman, ita Shuhudar ku tun lokacin da kuka fito waje aka dauke ta zuwa kungiya, wanda kafin ranar an kwashi tsayin kwanaki buyar ana son samun wannan dammar bat a samu ba. Shi yasa ana samun dammar aka dauke ta, wanda dai-dai lokacin lira ne ba ka yi ba babu ita har muka kawo wata a zuwan it ace. A ranar an tattauna matsaloli da suka shafi kungiya na rashin halattar Shuhuda a kungiya, wanda suka yi ta bincike, amma bas u samu dammar sanin wani abu ba. Hakan yasa aka yanke hukuncin ba zata koma gida bat a dawo kungiya ken an.
Sai dai maji dadin kungiya ya karya wannan batu bias karanto dokokin kungiya day a yi, babu shafin day a nuna cewa a tsare shugaba a hana shi harkokinsa nay au da kullum koda kuwa hakan na nufin zai bar kungiya ne. sannan ya kuma karanto dokokin kungiya ga wanda ya yi yunkurin barinta, aka yanke hukuncin cewa, za a dinga daukarta a duk lokacin da ta fita daga gida.
Haka kuwa suka ci gaba da yi, a ranar da Isah zai tafi Ibadan Shuhudar da ke cikin daki ba ita b ace, saboda ta fita da safe bias kaddara zata siyo sabulun wanki aka dauketa, a lokacin dukkanmu muna wani taro na bita akan addini can kasar Saudiyya, shi yasa ma bat a fito sun yi bankwana ba. Duk abin day a faru da Shuhuda izina ce ga wanda ya dauki kyale-kyalen rayuwa ya gane cewar bayan kura ta lafa akwai daru, ma’ana bayan shuka sharran zai iya bibiyar bayanka(iyalinka). Yau kwanaki takwas ken a Shuhuda bat a cikin gidan nan, tana can wani tsuburi da ke Sokoto an daure sakamakon wani laifi da ta yi, kamar yadda na fada muku an taba bat a wani kaho wanda za ta zuki jinin Inna Yaduwa bat a yi hakan ba,
shi ne aka kuma son ta zuko jinin saboda abarakar da muka saki suka yi tunanin su ne suke hana shuhuda halartar kungiya, shi yasa suka yanke shawarar kawar da inna yaduwa da Isah daga doron kasa.
A matsayin Shuhuda na shugaba ta nuna bat a amince da hakan ba, shi ne aka yi mata caa! Daga cikinsu akawai wanda ya nuna dama bai dace ace Shuhuda ce shugabarsu ba, tunda bat a taba shan jini ba a iya tsawon zamanta a kungiyar.
Don haka aka kai ta tsuburin aka duare ta ana azabtar da ita bisa laifin karya dokar shugabanci da ta yin a son bada wasu ga abin tsafi da ta nuna rahsin amincewarta, a shafi na tare cikin kundin tsarin mulkinsu ya bayyanar da wannan hukunci a gare ta .
Sannan an yanke shawarar ranar da aka gama hukuntata wato bayan kwanaki goma sha hudu ke nan za a bata jini ta soma sha, don tabbatuwarta shugaba a gare su.
Shuhudar da ke tare da ku wannan…….
Ya nuna daya Shuhuda da yatsa, ya ci gaba da cewa.
“Ba asalin Shuhudarku b ace, wata ce muka samar. Cikin da kuke zargin tana da shi ba ciki ba ne, anyi haka ne bisa mataki na karshe da muke ganin zamu iya bullo muku da shi ku gane cewa Shuhudarku na bukatar tallafi daga gare ku.
Wannan shi ne cikamakon zaruruwan labarin da muke son ba ku
Yanzu kuma sai a ba ku zabi da shawar akan lamarin. Da farko dai Shuhuda tan a da matukar amfani a tare da ku kasancewarta tsatsonku, zabin da zamu ba ku shi ne, kuna sonta a cikinku ko ba kwa so . ba ruwanmu ba ne mu tursasaku ku so ta, sai dai zamu karfafa muku gwiwa akan ku so ta.
Shawara kuwa, idan har kuna son ta ci gaba da zama da ku, dole sai kun kawar da komai na abin da ya faru, kun rungumi kaddara bisa azal din da ya fadawa shuhuda tunda ba don ra’ayin kanta ta shiga kungiyar matsafa ba.
Sannan ko da ta ke a kungiyar har yau ba ta sha jinin wani dan adam ba, bare nata. jinin mutum yana halatta ne yayin da kasace mushiriki mai shan jinin yan uwansa mutane
(ALLAH SHI NE MASANI).
Idan muka yi amfani da wannan batu za mu ga cewa, wanda yak e shirka don Karin kansa, yak e kuma shan jini shi ne jininsa ya halatta , idan kuma ya tuba ya daina jininsa bai halatta ba.
Kun ga ke nan har yanzu akwai sauran dama a grace ku ta yin jihadi ku ceto tsatsonku daga halakar da ta ke ciki
I dan kuka yi watsi da lamarinta hakika kuna da hakki, Allah (SWT ) sai ya tuhume ku a ranar gobe kiyama
Yakub yana zuwa nan a labarinsa ya yi shiru, kowa da abin da yake kissimawa a ransa
Alhaji Rabi’u ne ya kawar da shirun nasu da cewa .
“ lallahi mun tafka kuskure da muka dauki kowace cuta akwai maganinta a asibiti mun manta cewar duk inda aka bar Alkur’an i sai an samu ba dai -dai ba, domin shi Alkur ‘ani shi ne zuciyar kowace irin ciwo.
Amma mun gode wa Allah da ya kawo mana ku cikinm rayuwarmu , shin yanzu ta wace hanya zamu kubutar da Shuhuda?
Yakub y a ce, “ gaskiya kubutar Shuhuda daga tarkon da ta ke ciki yana da matukar wahala, amma da yake Allah yana tare da mu, da izininsa zamu samu nasara.
Shuhuda kam na cikin wani mawuyacin hali na azabtarwa, idan har ana son kwatota daga hannun matsafa akwai SADAUKARWA, ma’ana a fita da zummar za a dawo da rai ko akasin haka
Kuma ba lallai ne a samun nasara ba, sai dai addu’a bat a bar komai ba, rubutaccen al’ amari kuma ba wanda ya isa ya kankare shi
Tsuburin da Shuhuda ta ke yana can jihar sokoto a can kungurmin daji, dole sai an yi tattaki daga nan Kano zuwa Sokoto sannan za a sadu da inda ta ke , kuma tafiya ce da za a yi a cikin sirri ba tare da idanun masu sirri sun san da ita ba.
Daga ban garenmu za mu dauke nauyin tafiyar har kusa da tsuburin , sannamn za mu bada wata addu’a ta makantar da makiya daga ganika
Mu ba zamu iya tunkarar tsuburin bas hi yasa tun tuni ba mu kwatota daga hannun masu sirri ba, hakan kuwa ya biyo baya ne akan wani sinadari da saka a tsuburin da zarar jinsin jinnu ya ratsa gurin to kuwa zai soye ne rumus`
Karmar yadda na fada muku a baya masu sirri suna tunnanin isah da inna yaduwa suke hana shuhuda zuwa kungiya, shi ne suke ganin a kowane lokaci su isah za su iya sanya malamai su tura jinsinmu (jinnu) a dauko ta, don haka suka yi wanna surkulle amman bani’adam yana iya keta tsubrin har ya isa inda shuhuda ke duare ba tare da wani abu ya same shi ba.
Matsawar idanun masu sirri bas u san da zuwan bani’adamu din ba, ma’ana bas u ga wanda yatunkara guri ba
Idan an samu nassar isa inda ta ke , hannu ba zai iya kunce daurin talalar da aka yi mata ba, akwai surar WAKI’A, karantata a koda yaushe yana kawo tsari, ita za a karanta a dai-dai inda shuhudan ta ke, idan Allah ya yarda daurin zai kunce hart a dawo hayyacinta da ta rasa tun lokacin da aka daureta a tsuburin.
Ina mai tabbatar muku da cewa, daga lokacin da daurin ya kunce, dukkan wadandan ke kungiya sai sun ji a jikinsu, don haka za su yi saurin zaburowa domin sun dauki matakin gaggawa.
To a wannan lokacin Allah ne masanin yadda zata kasance, ko a mutu ko a yi rai, fatan ma dai a yi ran ga godiyarmu.
Idan har aka samu nasarar fitowa da shuhuda daga tsaburin komai zai iya faruwa ga kungiyar, imam ta tarwatse ko kuma ta ci gaba da wanzuwa ana farautar rayuwar shuhuda da duk wanda ya shafe ta.
Idan bat a fito daga tsuburin ba, shi ma wanda ya yi jarumtar zuwa tsuburi ba zai fito ba, kuma dukkan su zasu zamo kyautarwa fa abin tsafi.
Fitowar su daga tsuburin na tafiya bisa kalubalen tarwatsewa kungiya ko akasin haka!”
Yakub ya yi shiru da ya karashe maganarsa. Alh. Ahmed ya karbe da cewa. “Idan aka samu nasarar fitowarta daga tsuburin kungiya bat a tarwatse ba, wane irin taimako za ku ba wa lamarin?”
Abubakar ya magantu.
“Allah shi ne masanin yau da gobe, don haka shi ya bar wa kansa sani. Shi yasa aka ambaci SADAUKARWA a cikin lamari. Ma’anar da muke nufi da sadaukarwa shi ne, ku sadaukar da rayuwarku don yin jidadi.
Amma ki sani mu ba mu isa mu ba ku kariya ba facea bin da Ubangiji ya tsara, idan ya nufe mu da ci gaba da ba ku kariya za mu ba ku kamar yadda ya nufe mu da sanin sirrin da wayonmu ko kasantuwaru jinsin jinnu ba mu isa mu sani ba.
Tun a nan za ku gane shi (Allah) gwani ne, mai hikima ne a dukkan lamuransa, kamar yadda suratul Ikhlas ta bayyana tsarkin Ubangiji.
Abin da muke so ku sani shi ne rayuwar dan Adam da dukkan abin da yake bisa doron kasa na sarari da na boye, da abin da yake a kiyama duk Allah (S.W.T) ne ya yi su, kuma Annabi Muhammadu (S.A.W) dan gatansa ne!
Idan kun yarda da hakan babu tababa a cikin duk rokon da zaku yi, shi roko ana son yinsa da tsarkakkiyar zuciya, madamar ana son Ubangiji Ya karba, don shi (Allah) mai tsarki ne, ba ya karbar ibadar marar tsarki.
A cikin suratul Bakara aya ta 186 an bayyana yadda bawa ya kamata ya yi roko da tsarkin zuciya.
Duk zuciyar da ta kasance cikin wasi-wasi akan tabbatuwar Ubangiji, ko kin amincewa da Annabi Manzon Allah ne, lallai ba za a taba amsa rokon mai zuciyar ba”.
Shahuda Ibn Khaddab ta dora da cewa.
“An karbo daga Abi Hamzata anas bn Malik (R.A) hadisi na sha

Please Login or Register in order to submit comment