Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ina zata kaishi ba, a hankali yake takawa harya riski lambun dake bayan gidan, jingina yayi a bishiyar daya fara gani cikin taushin murya ya mayar da martanin abinda Zuby ta fad'a masa,

"Ina sonki, ina qaunarki , na matsu ranar nan tazo domin a ranar burina na gidan duniya ya cika, na gaji da mafarkinki a kullum, ina so mu fara rayuwar gaske."

Khairat dake sauraren wak'ok'i bata jin me yake fad'a, amma shi duk da yana magana ne amma yana jin wata siririyar murya na tashi a kusa dashi ana rera waka , juyawa yayi ya kashe wayar yasa aljihu tare da rumgume bishiyar ya lek'a kanshi a hankali dan ganin me wakar, yanda ya rumgume bishiyar yasa hannunshi ya d'an shafi kafad'arta hakan kuma yasa ta juyo da sauri, manyan idanunsu ne suka sarke dana juna suna kallon kallo, babu wanda baiji fad'uwar gaba ba a cikinsu amma sai suka basar.

Babu wanda yace wani abu kuma babu wanda ya d'auke kanshi, Khairat ce taja tsaki tare da maida kallonta ga wayarta ta ci gaba da abinda take, yana ganin haka ya tab'e baki shima ya koma hanyar daya fito, Biba ce ta masa izinin zama sannan taje ta sanar da Mamie bak'onta ya zo.

Yana cikin kallon hadadden falon yaji bud'a k'ofa, maida kallonshi yayi ga nutsatsiyar matar mai dattako, tsaye ya mike yana murmushi ita kuma ta masa izinin zama, cike da girmama juna suka gaisa kafin Mamie ta kalleshi a tsanake.


Hakika Umar Faruk ba zaka kirasa da kyakyawa ba ajin farko, amma dai dole ka kirashi kyakyawa na farko a aji na biyu, manyan idanunshi masu firgita mai kallonsu da kuma saka kwarjini, haka kuma bak'i kuma yalwataccen sajenshi ma ya k'ara masa kyau, kana ganinshi zaka san jarumin namiji dan suffarshi ma ta zaratan maza ce, daga tafiyarshi kuma zaka gane ingarman dokine mai tashen k'uruciya a jika.

Murmushi Mamie tayi tace "Umar Faruk, ranar ka taimakemu amma kuma saika tafi ba tare da mun maka godiya ba, kome yasa kayi haka?"

D'an murmushi yayi yace "Hajia ni na taimakeku ne saboda Allah, bana buk'atar ku gode min."

"Duk da haka Umar Faruk muna godiya sosai da irin taimakon daka mana, amma dan Allah tayaya akayi kasan da mutanen nan?"

Kallonta yayi yace "Hajia da mun bar duk wannan maganar, tunda dai masu laifin sun shiga hannu."

"Hakane, amma zan iya sanin meke tsakaninka da Khairat?"

Murmushin gefen labb'a yayi yace "ba komai Hajia."

"In tambayeka mana idan ba damuwa?"

"Uhum, ba damuwa."

"Dan Allah kana da aure?"

"A'a, amma dai nakusa insha Allah."

"Allah yasa alkairi."

Ya amsa da "ameen, na gode."

Kallonshi tayi tace "amma misali, idan nace zan da Khairat, kana ganin zaka yarda ka aureta?"

Kafeta yayi da ido da tsananin mamaki, ba zai iya yi mata qarya ba kamar yanda ba zai yarda ya lalata rayuwarshi ba ta hanyar auren Khairat, ko kyauta za'a bashi ita to ba zai karb'a ba, shima da ido ya kalleta yace "kiyi hak'uri Hajia, amma gaskiya ba zan iya ba, kiyi hak'uri idan abinda na fad'a ya b'ata miki rai, ina da wacce nake so kuma hutu kawai muke jira a d'aura mana aure."

Murmushin takaici tayi tace "karka damu raina bai b'ace ba, dama tunda abun nan ya faru na sawa kaina dole haka zata fara faruwa damu, nasan a yanzu ba kowa bane zai iya yarda ya aureta, amma ba komai zamu ci gaba da hak'uri har komai ya zo qarshe, kuma ina so ku sani Khairat bata da laifi, duk laifin namu ne iyayenta musamman ma ni uwa."

"Shari'a ta nuna mana yanda zamu samu yaya na gari tun kafin aure, amma sai kaddarata ta zo da tangarda na kasa samar mata uban daya dace, ba komai karka damu kanka kaji."

Tsaye ta mik'e tace "na gode yaro Allah ya maka albarka."

Shi dai baice komai ba yana kallo ta fara tafiya kuma ta tsaya ta juyo tace "bansan ko kana buk'atar kuyi ban kwana da Khairat ba, dan baifi awa d'aya daya rage mana ba mu koma India da zama tare da mahaifiyata."

Tana fad'a ta juya saboda hawayen da suka taho mata, yau gashi *halin rayuwa* yasa harta yiwa namiji tayin 'yarta a cikin wasa amma yace baya so, shi kuma jikinshi ne yayi sanyi duk yaji ba dad'i, amma kuma baiyi nadama dan ba zai yarda koda a misaline ba a dinga had'ashi da Khairat.

Tashi yayi shima ya bar gidan dan baiga wani ban kwana da za suyi ba da ita, haka ya d'auki hanya yana tunanin maganganun mahaifiyar Khairat, uwar mutuniyar kirki ce amma diyar da uban sai a hankali kam , inji Umar Faruk.
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

πŸ€ΉπŸ»β€β™€πŸ€ΉπŸ»β€β™€πŸ€ΉπŸ»β€β™€πŸ€ΉπŸ»β€β™€πŸ€ΉπŸ»β€β™€πŸ€ΉπŸ»β€β™€πŸ€ΉπŸ»β€β™€πŸ€ΉπŸ»β€β™€
*MARAYU MA 'YA'YANE*
πŸ€ΉπŸ»β€β™€πŸ€ΉπŸ»β€β™€πŸ€ΉπŸ»β€β™€πŸ€ΉπŸ»β€β™€πŸ€ΉπŸ»β€β™€πŸ€ΉπŸ»β€β™€πŸ€ΉπŸ»β€β™€πŸ€ΉπŸ»β€β™€

_A gaskiya littafin nan ya ilmantar sosai, kuma da za'a dinga yin labari irinshi to za'a samu ci gaba, my Lissa na tayaki murnar kammalashi, ubangiji ya yafe miki kurakurenki ya baki ladar fad'akarwar da ki kayi._ sai mun had'u a labari na gaba.



_Bismmilahir-rahman-rahim_


1⃣1⃣


Lokaci nayi suka fito cikin shirin tafiya, Papa na ganin Mamie ya janyeta gefe cikin rad'a yace "wai me kike shirin yi ne Na'ima, da gaske tafiya za kiyi?"

Fizge hannunta tayi tace "ka rabu dani, aina fad'a maka babu abinda zai hanani tafiya wallahi, kaji na rantse."

Jinjina kai yayi yace "naji, tunda kince dole zaki tafi to ki tafi, amma ki barmin 'yata zan kula da ita."

Dariya tayi tace "'yarka, wallahi idan kaga nabar Khairat a hannunka to ka tabbata aure zaka mata, amma in ba haka to wallahi ba zan bar maka ita ba."

Wucewa taje yi ya sake rik'eta yace "naji tunda haka kika ce, ki bar Khairat anan, na miki alk'awarin samo mata miji na gari na had'ata dashi."

Kallon sama da qasa ta masa tace "idan ka samu mijin saika kirani ka fad'a min, ni kuma zan kawo maka ita da kaina."

Tana fad'a tayi gaba, haka suka tafi tare ya rakasu babu mai magana har jirginsu ya tashi yana kallonsu, haka suka tashi yana ji kamar ya bisu amma tunda bai shirya hakan ba dole ya hak'ura, haka ya juya ya koma gida zuciyarshi na tafasa kamar zata fashe, yana son Na'ima kuma yasan ba zai samu mace kamarta ba, amma hallayarshi taja mashi rasata a lokacin daya fi buk'atarta.

Ita kanta Mamie saida jirgi ya tashi sai taji kamar bata kyauta ba , kamata yayi ace ta hakura su rumgumi 'yarsu su maida hankali kan tarbiyarta, ba kuma wannan ne yafi d'agawa Mamie hankali ba shine ji da tayi kamar itama ta kamu da son Papa ba tare data sani ba, haka dai har suka sauka a india Mamie na hawaye, Khairat kuma na ganin haka saita dinga jin haushin Mamie saboda tana ganin ai farin ciki ya kamata tayi data rabu dashi na d'an wani lokaci, to amma ta rasa kukan miye take.


*SOYAYYA KENAN*😁


Tunda suka sauka abokan arzik'i da aka saba suka fara zuwa musu sannu da zuwa, kuma sai lokacin suke ganin halin da Khairat ke ciki, haka dai ake ce musu hatsari tayi nan zasu mata addu'ar samun lafiya sannan su tafi.

Haka ma dai masoyin nata Raj ba'a barshi a baya ba, a sukwane yazo domin ganin Khairat cikin farin ciki tare da shirinshi na neman aurenta a yau d'in, amma ganinta a wannan hali saiya sare masa gwiwa dole ya hak'ura, amma yayi niyyar bayyana mata k'udirinshi bada dad'ewa ba koda tana cikin wannan halin ne dan yana sonta so mai tsanani.

*Daga* wannan rana sai Raj ya fara taimakawa su Mamie wajen jinyar Khairat, duk da Mamie bata so ko kad'an amma da yake mutum ne mai barkwanci da son mutane gashi da aiki ko ba'a sashi ba, hakan yasa ya shiga ran Mammie kuma ya qara girma a idon Khairat, kowace safiya saiya zo gidan ya tayasu had'a abin kari kuma da kanshi yake bawa Khairat nata , haka kuma da dare zai zo su jima suna hira da Khairat saboda kusan unguwa d'aya suke, Khairat najin dad'in haka hakan yasa yanzu harta fara canzawa yanzu tana magana sosai tana dariya in dai Raj na nan.

A haka sai shakuwa ta sake shiga tsakaninsu fiye da baya, duk da raunin dake jikinta tare da rashin tafiya hakan baya hana Raj fita da ita wuraren shaqatawa, kuma hakan na mata dad'i tana d'ebe kewa sosai.


*A b'angaren* Papa kuwa an duk'ufa an maida al'amura ga ubangiji, sallah kan lokaci tsayuwar dare yana neman gafarar ubangiji, azumi kullum sadaka da taimakawa marasa galihu duk wannan yanzu shine aikinshi, damuwar rashin iyalinshi na damunshi musamman Na'ima wacce yake ganin ta tafi kenan, duk kiran da yake mata bata dauka Khairat kad'ai da Mammie suke waya dasu amma banda ita, idan ka ganshi yanzu yayi kalar tausayi sosai kana ganinshi za kasan yana rayuwar kad'aici, sai ma'aikata kawai dake hidima da gidan.

_Allah ya karb'i tubanmu ya yafe mana kurakurenmu._


*Bayan wata uku* Umar Faruk ne a tsakar gidansu Zuby suna hira, Zuby ce ta nunfasa tace "yaya Umar, a gaskiya kaban mamaki sosai daka iya b'oye min abu mai mahimmanci haka."

Gyara zama yayi yana kallonta sosai yace "uhum, ina jinki, me nayi kuma?"

Cewa tayi "yaya Umar, jiya da naje gida wajensu Mama nake jin abinda ya faru a wajen aiki, wai matar da kuke aiki a qasanta ta mareka, a gaskiya raina ya bace sosai, ganin duk kwarjinin nan naka ace mace ta daga hannu ta mareka, ai sai dai mai zarra."

Shiru ya d'anyi na wani lokaci dan sai yanzu da tayi maganar ya tuna da wata Khairat, a hankali ba tare da sanin maganarshi ta fito fili ba yace "ko ya jikinta yanzu?"

"Wacece?" tambayar da Zuby ta jefo masa kenan.

Da sauri ya kalleta yace "a'a...ba...bb..ba komai."

Dorawa tayi da "amma ai kamar itace na gani a Whatsapp ana magana akai, wai in dai har za'a dinga keta haddi yayan manya ma to ina ga talakawa da marasa 'yanci."

Kallonta kawai yayi da ido, dan haka ta sake cewa "kuma naji ance har mutum hud'u ne ko, gaskiya ta ban tausayi, nikam yaya da zaka kaini gidansu ma na ganta wallahi."

"Keeee." tsawar daya mata tasata zabura da k'arfi.

Tsaye ya mike yana masifa "ita d'in cinema ce da za kice na kaiki ki ganta, wani abun dad'i ne ya sameta da har zaki dinga magana haka cikin shauki , to ba zan kaiki d'in ba kije da kanki saiki ganta, hada wani wai mutum hud'u, to sai akayi me dan mutum hud'u ne? zata fasa rayuwa ne ko kuma zata rasa mijin aure ne?"

Yana gama fad'a kuma ya koma ya zauna yana huci, ruwan dake kusa dashi a cup ya d'auka ya kai bakinshi , kamar dirar mikiya ya tsinci muryar Zuby tace "zata rasa mijin aure, dan a mahawarar dana gani a Whatsapp, kowane namiji yana cewa shi ko kyauta ba zai aureta ba, wasu kuma suna cewa idan za'a had'a musu da kud'i da mota da gida to zasu amince, watak'ila kaine kake ganin ba komai bane, amma wannan ba k'aramar matsala bace."

Kasa shan ruwan yayi ya qura mata ido, ita kuma tashi tayi ta shige d'akinsu wai ita ya d'aga mata murya akan wata banza.

_Lallai ruwa sun daki babban zakara , Khairat d'in ce banza?_

Ai baiko bi ta kanta ba ya fita daga gidan shima ya hau mashin d'inshi, bai zame ko ina ba sai majalisar da manage ke zama bayan an tashi daga aiki, zaune ya samesu wasu akan tabarma wasu akan benci, gaidasu yayi cikin girmamawa dan duk ba sa'anshi, manager ne yasa takalmi ya tashi suka keb'e.

"Umar Faruk lafiya na ganka cikin wannan daren?"

"Eh to, lafiya lau."

Shiru ya d'anyi shi kuma yana kallonshi kamar mai nazartarshi, kai ya shafa yace "manager wai dan Allah ya jikin Hajia Khairat ne? naga har yanzu babu wani labari tunda suka tafi basu dawo ba."

Manager daya kafeshi da ido murmushi ne ya bayyana a fuskarshi ya dafa kafadarshi yace "Umar Faruk kenan, irin wannan damuwa haka? to ka kwantar da hankalinka, Khairat na nan lafiya dan mahaifiyarta tace min ma harta fara takawa da taimakon wani saurayinta Raj, kuma da zaran ta samu sauki sosai zata turota ta dawo gida."

Da mamaki ya kalleshi yace "ta turota kuma, ita fa?"

Ajiyar zuciya ya sauke yace "wannan sirrin gidan Alhaji Mani ne, bai kamata na fitar dashi ba, amma dai ka sani mahaifiyarta ba zata sake dawowa ba sai dai wani iko na ubangiji kuma."

A tsanake ya kalli manager yace "hakan nada alak'a da abinda ya faru da 'yarsu kenan?"

"Sosai ma, faruwar hakanne ya jawo komai."

Kai Umar Faruk ya girgiza ya bawa manager hannu yace "na gode manager, ni zan wuce."

Harya tafi manager ya kira sunanshi, juyowa yayi yace masa "ko dai na baka lambarta ne saika kirata kaji."

Kamar wanda aka ba tsoro saiko yace "a'a a'a, ni kuma me zanyi da lambarta."

Yana fad'a ya juya ya hau mashin d'inshi yana fad'in "ina ruwana da ita, tana can fa ita da masoyinta."

Tafiya ya fara amma ya rasa dalilin da yasa ranshi b'acewa, da k'arfi sake fizgar mashin d'in tare da jan dogon tsaki yace "Raj d'in banza da wofi, miye matsalata dashi da zai dameni."

πŸ˜›πŸ˜›πŸ˜›πŸ˜›πŸ˜›πŸ˜›πŸ˜›

*A wannan* lokacin Khairat jiki yayi dama sosai tafiyarta ma lafiya lau, da taimakon Raj ta fara takawa dan kullum shike rik'e da hannayenta yana koya mata tafiya harta fara sosai, yanzu dai da kaga Khairat to ta baya ce dan ba zaka tab'a cewa tayi wata larura ba.


Mammie Mamie da Khairat duka suna zaune a falo suka ji ana buga kofa, Khairat ce ta tashi ta bud'e, da farin ciki ta rumgume Raj wanda ya shirya cikin pink d'in riga da bakin wando, sosai yayi kyau dan dama akwai kyau d'in, sakin juna sukayi ya shigo ciki ta rufe kofar, hannun juna suka rik'e cikin yaran india take cewa,

"Yaufa kayi kyau, da wani abu ne dake faruwa?"

Murmushi kawai ya mata ya mik'a mata flowers daya taho da ita ja mai kyau, karb'a tayi tace "na gode."

Mamie da tunda ta ganshi ta had'e rai dan ko kad'an bata san ganinshi tare da Khairat, bata musa akan cewar yaran kirki ne ba,amma tafiyarshi da Khairat bata dace ba, saboda shine namiji kuma ba musulmi ba, d'aya bayan d'aya ya sunkuya ya tab'a qafafun Mammie da Mamie d'in dan neman tabarruki, Mammie ce tace ya zauna, kallon kallon aka shiga yi har saida Khairat tace,

"Ya dai Raj?"

Kai kawai ya girgiza mata alamar ba komai, Mammie da Mamie ya kalla cikin harshenshi yace "ina neman izininku akan ku bani damar neman auren Khairat."

Khairat ce ta kalleshi da mamaki, kai ya jinjina mata dan haka ta taso ta dawo wurinshi ta zauna murya qasa qasa tace "kana haukane? nifa ban shirya aure ba yanzu."

Hannunta ya kama ya rik'e yana mata shu'umin kallo yace "me yasa Khairat? baki sona ne?"

Cikin sanyin jiki tace "ba haka bane Raj, amma ba...."
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


_Bismmilahir-rahman-rahim_


1⃣2⃣



Bai bari ta k'arasa ba ya rufe mata baki yana fad'in "shiiii, Khairat, in dai har kina sona, to ki tabbatar min da hakan yanzu ta hanyar saka wannan zoben, alamar munyi baiko dake." ya fad'a tare da fito da zobe daga aljihun rigarshi ya bud'e mata.

Da mamaki ya kalleta tana tunanin mafita, hak'ik'a Raj shine namiji na farko da take jinshi a ranta, ganin bata da wani dalili na kin amincewa yasa tayi murmushi ta mik'a masa hannunta tace "eh, na amince."

Cikin farin ciki ya fito da zoben jiki na rawa ya fara k'ok'arin saka mata, "Khairat!"

Kira da Mamieta mata yasa suka kalleta a matuk'ar razane, tsaye suka mik'e suna ci gaba da kallonta, d'orawa Mamie tayi da "ashe baki da hankali Khairat, ke yanzu amince masa za kiyi ki aureshi kike nufi kome? kinsan hukuncin kuskuren da kike shirin aikatawa kuwa?"

Maida kallonta tayi ga Raj da bai fahimci komai ba ta fara masa magana a harshen india duk da yanzu indiancin nata yayi rauni sosai amma haka ta dage tace masa,

"Kaga Raj, kai yaron kirki ne, amma ka sani alak'arka da Khairat ba mai dorewa bace domin kuwa ita musulma ce kai kuma ba musulmi ba, addininmu kuma ya haramtawa mace musulma auren namiji da ba musulmi ba, dan Allah ina so ka fita a harkarta ka manta da ita a rayuwarka, kaje ka samu mace yar uwarka ka aura, dan Khairat ma an fitar mata da miji fad'a maka ne ba tayi ba."

Duk da ta fad'i hakane danya rabu da ita, amma dai bata ji dad'in abinda ta fad'a ba saboda ba gaskiya bane, had'e hannayenta tayi tace "na rok'eka da ka tafi, ka tafi dan Allah karka sake dawowa, dan Allah."

Tunda Mamie ta fara magana ya zama kamar gunki, jin ta gama fad'an abinda take son fad'a yasa ya juya ya kalli Khairat, gefen fuskarta ya shafa yayi murmushi wanda yasa hawayenshi suka fito, da qyar ya iya furta mata "zanyi kewarki Khairat, naso na sameki, amma dole na barki, ba zanso ki sab'a umarnin addinninki ba a kaina, kibi zab'in iyayenki."

Yana fad'a yayi hanyar fita, da sauri Khairat tabi bayanshi, fizgowar da Mamie ta mata tasa ta fad'a saman kujera, a hassale ta tashi cikin harshen zarma (zabarmanci,😁inji k'anwata zamarmanci) ta fara magana,

"Wai meye haka, me yake damunki ne, kinsan me kika aikata kuwa? aurena fa ya nema a gabanku, akan me zaki masa haka?"

"Khairat, kin manta ke musulma ce, bai halatta gareki ba auren wanda ba musulmi ba."

"Mamie saime, nifa zan zauna dashi bake ba, me yasa zaki min haka?"


_WAI'IYAZU BILLAH_😭


A fusace ta shige d'aki ta barsu, Mamie kuma fad'awa tayi saman kujera ta fashe da kuka sosai har saida Mammie ta taso ta zauna kusanta ta dafata tace,

"Na'ima kiyi hak'uri, kici gaba da yiwa Khairat addu'a, insha Allah zata canja."

"Yaushe, Mama sai yaushe Khairat zata san mu iyayen tane, Mama munyi kuskure da bamu d'ora Khairat a tafarkin ilimin addini ba, yafi kowane ilimi a rayuwa, na tabbata da tayi karatu da zata san girman hukuncin iyaye sannan zata san girman zunubin da take shirin aikatawa."

"A gaskiya Mama ba zan jure ba, aure kawai nake so Khairat tayi Mama, akwai matsala zamanta anan dan haka gobe zamu koma wajen mahaifinta, na gaji da ganinta a gabana Mama."

Tana gama fad'a itama ta tashi ta nufi d'akinta, kwance tayi tana tunanin rayuwa da kuskurensu da kuma kuskuren da 'yarta ke cikin aikatawa, Khairat ma na d'akinta tayi kiran wayar Raj harta gaji, ganin ta aika sak'o ba amsa yasa kawai ranta ya b'ace ta fita harkarshi shima, abin sauraronta tasa a kunne tasa sanyayyen waka domin d'ebe mata kewa.


*Tunda gari ya waye* Mamie taje ta ciro musu ticket kuma tayi sa'ar samun jirgin da zai tashi da yamma, tana zuwa ta shirya kayanta dana Khairat dake bacci a d'akinta, tana gamawa ganin lokaci ya fara tafiya yasa Mamie tashin Khairat.

Da mik'a ta farka tare da hamma, ganin Mamie tsaye yasa ta gyara zamanta tana kallonta, "ki tashi ki shirya zamu tafi."

"Ina kenan?" cewar Khairat tana saukowa daga kan gadon.

"Gidan mahaifinki zamu koma?"

Dariya tayi tace "kije kawai idan kinyi kewar mijinki ne, ni nafi jin dad'in zamana anan tare da kakata."

Gabanta Mamieta tare tace "Khairat tare zamu tafi dake, kiyi sauri ki shirya ki fito ki sameni."

"Bansan me yasa kike so ki bawa kanki wahala ba, na fad'a miki ba zanje ba."

Da sauri Mamie ta fita daga d'akin ta koma falo ta bud'a jakar kayan Khairat d'in ta d'auko wata doguwar rigar atamfa ta dawo d'akin da zafinta, tana zuwa zaune ta samu Khairat akan kujerar dake gaban madubi tana kallon kanta, da k'arfi Mamie ta kamo hannunta ta tsayar da ita gabanta ta cire mata qaramar rigar dake jikinta, ganin tana kare qirjinta yasa Mamie tayi tsaki taci gaba da abinda take, saida ta barta da silip kad'ai sannan ta rataya mata wannan rigar, wani irin d'auri ne Mamie ta mata mai ban dariya sannan ta d'ora mata gyale a kafad'a dan tasan haka tafi so.


Hannunta ta fizga zasu fita daga d'akin Khairat ta tirje tace "wai Mamie miye haka, nifa ba yarinya bace?"

"Amma ni na haifeki, muje." ta fad'a tana janyota har suka fita.

Mammie na zaune taga sun fito kamar ankorosu, tsaye ta mike tace "ku kuma lafiya, miye haka kike janta kamar yarinya?"

"Fad'a mata dai kakata." cewar Khairat tana so ta kwaci hannunta.

"Mama kiyi shiru, zamu tafi ne saina dawo."

Jakunkunansu Mamie ta d'auka zasu fita Mammie tace "saikin dawo kuma, ina kuma yaushe, ki zo kiyi me?"

Saida Mamieta bud'e k'ofar fita tace "idan na dawo za muyi magana, sai kinzo bikin gimbiyarki."

Dariya Mammie tayi lokacin da taji Khairat tace "biki kuma, aure zaki min?"

Haka suka fita suka shiga taxi d'in dake jiransu a k'ofar gidan, Mamie bata saki hannunta Khairat ba har saida suka shiga jirgi sannan.


*Dare ya fara tafiya* suka shigo garin, suna cikin taxi Khairat na kallon gefen titi kwatsam ta hango Papanta zai shiga wani super market tare da wata wayayyar mata sun shiga ciki, da sauri Khairat ta daddab'a kafad'ar driven taxi tace ya tsaya, tsayawa yayi Mamie kuma tambayarta ta fara yi ko lafiya, fita tayi daga motar da sauri ta fita ta rufe motar ta lek'o kai tace wa Mamie "kije gida, zanje na taho miki da mijin naki."

Da gudu ta tsallaka d'aya titin, zata tsallaka na biyu wani mai mota da bata kula dashi ba ya danna mata wata irin oder da saida ta zabura, cak ta tsaya tana kallon motar, ganin mai motar ya tsaya yasa ta kwada tsaki zata wuce kawai taji yace "yan mata lafiya, da matsala ne?"

Hararanshi tayi tace " dallah gafara can, wai kai mai mota sai iya oder tsiya, hamago yanzu haka ma motar aro ce."

Umar Faruk ne a d'aya b'angaren data tsallako zai wuce yaga kamar idonshi na mishi gizo, amma daga ganin kayan jikinta da yanda takewa mutumin nan magana yasa yasan Khairat ce da kanta ba mai kama da ita ba, tsallakowa yayi ya tsaya daga gefe yana kallonsu kamar wasu mutanen da suma har sun fara kallonsu, mai motar nan ne yace "da alama baki da tarbiya, amma tunda kika had'u dani kin gama, wallahi daga yau ba zaki sake wulak'anta wani ba."

A zabure ta matso kusanshi tace "me za kayi, dukana za kayi, ko kuma kaima za kayi abinda kuka iya ne, to ka sani ba kaine farko ba?"

Zaiyi magana ta mashi wata irin kyara tace "tafi dallah ni bana da lokacinka."

Zata wuce ya tari gabanta ya zaro mata ido yace "ke har kin isa kice zaki ci mutunci na, kinsan ko waye ni? ke yar gidan uban waye? da alama fa karuwanci kika fito amma har kike so ki rainani, to yau sai naga uban daya d'aure miki gindi a garin nan."

Waya ya fito da ita da alama kamar wata lamba yake nema, Umar Faruk ne yaga al'amarin zaiyi tsamari dan haka ya matso tare da rik'e hannun mutumin yace "sannu abokina, dan Allah kayi hak'uri ka rabu da ita, qwaqwalwarta ce ta samu matsala tunda ta samu wani hatsari."

A hassale mutumin yace "ina so ne naga uban daya d'aure mata gindi a garin nan da har take wa mutane rashin kunya, ka bari kawai na koya mata hankali."

"Ka koya

Please Login or Register in order to submit comment