Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'aya hannu kuma tana shafa qirjinshi tace "ya isa haka baby, ka rabu da ita mana, yarinya ce fa."

Tureta Umar Faruk yayi daga jikinshi cikin jin zafi ya cabko Zuby da k'arfi ya fara magana "wacece ke Zubeida da har nake magana kina katseni, yaushe aka haifeki da har zaki d'aga murya akan yawa, fad'a min ina jinki akan me? yaushe wuyanki yayi kauri haka?"

Sakinta yayi ya nuna mata kujerar yace "maza zauna malama."

Jiki na rawa ta zauna kowa ya zauna wajenshi sannan yace "abinda ki kayi yanzu hauka ne, kuma bana d'aukar irin wannan, akwai kishin da zan iya yiwa mace uzuri a kanshi, amma banda irin wanda ki kayi yanzun, dan haka a kiyaye nan gaba, bana buk'atar tashin hankali da qananun maganganu, zan sab'ama duk wacce ta tayar min da tarazma a gida ba tare dana d'aga qafa ba, dan haka ku had'a kanku shine zaifi muku alkairi dani kaina, dan saida had'in kanku zan iya samun farin ciki, kwantar da hankalinku shine zai zama silar nasarata a rayuwa, da wannan nake mana fatan samun zaman lafiya."

Addu'a ya dinga kwaranyowa ta fatan zaman lafiya tare da neman tsari daga shed'an daga garesu, kafin daga bisani ya d'ora da "akan maganar kwana kuma, kamar yanda muka sani ne, zan dinga yin kwana bibbiyu a d'akin ko wacce."


Yana fad'a ya fita ya bar d'akin ranshi a b'ace yana tunanin abinda Zuby tayi, Khairat ma ta bishi a sannu bare kuma ita k'aramar alhaki banza a banzaπŸ˜‚inji ni fa ba Umar Faruk ba.


Juyawa Zuby tayi zata fita Khairat ta rik'e mayafinta ta tako a hankali gabanta ta tsaya, kallonta tayi sosai kafin tace "hum, wai kishiyata , kinyi wasu maganganu d'azu amma bansan ko zaki iya maimaitawa ba? nasan ma ba zaki iya ba domin karyaki zanyi, amma bari kiji in fad'a miki, ni *karuwa* ce kuma ta Umar Faruk, dan haka zan baki shawara kamar yanda na bawa mahaifiyarki, ki koyi karuwaci kema ko zaki iya samun wani kaso a zuciyar Umar Faruk, idan kuma ki kayi wasa, to ki sani kin rasashi kenan har abada, sai dai kiyi rayuwar k'unci a gidan Umar Faruk ko kuma kiyi rayuwar 'yanci a gidanku a gaban mahaifiyarki, ma'ana zawarci."

Da hannu ta mata alama tace "zaki iya tafiya, idan kin fita ki turo min baby na rarrasheshi, dan kin b'ata masa rai daga zuwanki gidan."

"Dama Mama ta fad'a min baki da kunya, amma ni zan koya miki hankali." cewar Zuby tana shirin fita.

Rik'ota tayi tace "au, dama kuna tunanin samun karuwa da kunya ne? ai kawai ki tanadi maganin hawan jini dana ciwon kai, domin daga yau salon bugun zuciyarki zai canza."

Tana fad'a ta haye gado ta kwanta ita kuma ta fita daga d'akin ta koma nata, ko kayan jikinta bata cire ba ta kwanta tana kuka saboda bak'in cikin abinda ta gani da idonta.

_Ni kam nace zaki wahalar da kanki a banza._


D'akin Mama ya nufa ya samu abinci yaci kafin ya mata sallama ya komo d'akin sahibaπŸ˜‰, tana ganinshi ta sauko daga kan gado ta sake rumgumeshi kafin ta d'ago ta kalli fuskarshi cikin shagwab'a tace "kayi hak'uri baby, ta b'ata maka rai, muje na maka wanka to."

Sake rumgumata yayi a jikinshi murya can cikin mak'oshi yace "zaki iya yimin wanka?"

"Me zai hana? kaifa nawa ne."

Kafeta yayi da ido harta rabashi da kayan jikinshi ta d'aura mishi towel, hannunshi ta kama dan zuwa douche ya rik'e hannunta ya fizgota ta fad'o kanshi, kallon juna suke sosai kafin ya fara magana cikin sigar tausayi kamar zaiyi kuka yace,

"Khairat, dan Allah ki fad'a min me yasa kika canza daga yanda na sanki? Khairat me yasa kike min duk wannan kyautatawar? bayan nasan ba sona kike ba, Khairat dan Allah ki fad'a min me kike shiryawa a kaina? dan ina ji zuciyata zata iya bugawa idan har kika gujeni daga baya, ni kaina bansan me nake ji ba, ban kuma san me zance yake damuna ba a kanki, amma dai ina jin bugun zuciyata yana qaruwa idan ina tare dake, sannan ina shiga farin ciki idan na ganki a kusa dani, Khairat nakan ji daban a tare dani idan jikinmu ya had'u wuri d'aya, Khairat ina jin matsanancin kishi a kanki, kuma ina yawan tunaninki kamar yanda kike yawan zuwa min Γ  qwaqwalwata, tunaninki na hanani sukuni, fuskarki takan hanani shak'at saboda yawan ganinta da nake a idona, Khairat, wasu na tunanin na kamu da sonki ne, amma ni kaina na kasa tantacewa sonki nake ko kuma ba haka bane, kinsan me yasa na kasa tantacewa?"

Kai kawai ta girgiza masa shi kuma yace "domin ban tab'a shiga irin wannan yanayin ba har saida na had'u dake, a sanadinki ne na fara jin komai na canza min, Khairat, a yanzun in har zan iya fad'in gaskiyar abinda yake raina, to zan iya cewa *ina sonki*, tabbas Khairat *ina qaunarki*, bana jin zan iya rabuwa dake a yanzun, dan Allah kema karki gujeni, nasan ni talaka ne kuma ba zan iya d'aukar nauyinki ba, amma Khairat zanyi iya qoqarina wajen ganin na samar miki duk abinda kike buk'ata, Khairat zan iya bada rayuwata dan ganin walwala da farin cikinki, yanzu abu d'aya nake so naji shine, kema kina sona?"

Rarraba ido ta shiga yi tare da had'iyar yawu tana k'yabta mishi ido, abinda za tace masa take tunani, koda bata sonshi tasan dai taji dad'in abinda ya fad'a yanzu, idan kuma ta fad'a mishi bata sonshi to zata rasa duk wani abu da take shiryawa, dan haka mafita d'aya ta nuna itama sonshi take, maye murmushi tayi a gurbin da mamakin kalamanshi suka bayyana sannan ta riko hannunshi sosai ta sumbata kafin tace...

"Na d'auka ni kad'ai nake jin abinda nake ji a game dakai, bansan wani irin farin ciki zan nuna ba, Faruk, kayi min abubuwa da dama wanda babu wanda ya tab'a min har iyayena ma, tun daga ranar na fara jin abubuwa daban a game da kai, amma dayake shashasha ce ni, saina kasa fahimtar halin da nake ciki, sai yanzu da naga wata zata shiga tsakanina da farin cikina, naga ba zan iya hak'ura ba zaifi nima na tashi tsaye na nuna maka soyayyata a zahiri."

Ajiyar zuciya ta sauke tace "Umar Faruk."

Amsawa yayi ta hanyar sake kafeta da ido, dorawa tayi da " *ina sonka*, ina qaunarka, ina sonka so mai tsanani , son da babu wanda zai iya ganin qarshensa sai mahallicin sammai da qassai."

Qasa yayi da kanshi yana dariya saboda wani kuntumemmen farin ciki daya tokare zuciyarshi, tabbas ya yarda yanzu ne ya fara soyayya, kuma da Khairat, hannayenta tasa ta tallabo kanshi , abin mamaki ba dariya bace kad'ai harda hawayen farin ciki, ita kanta wani farin cikin ne taji yana nuk'urk'usarta a zuciya, rumgumeshi tayi sosai suka mak'alewa juna kowa kuma hawaye yake zubarwa.

_My Khairat ki yarda kawai, kema kin fad'a tarkon guy nan, auntyna Aisha, ina ga maganar team tazo qarshe, mu nemi 'yan adawa mu sasanta kanmu, dan muji dad'in farmakar Hajja Zuby._πŸ˜‰

Tare sukayi wanka kai kace shekararsu arba'in suna zuba love, haka suka fito a towel d'aya kowa ya shafa na shafawa ya murza na murzawa, Umar Faruk na kallon Khairat tana shafa humra takai kala bakwai wacce ta shafa, ta bayanta ya rumgumota ya shinshina wuyanta ido lumshe kafin yace "miye sirrin turarukan nan? danna lura akwai al'ajabi a tare dasu."

"Ni kuma ba zan iya fad'an sirrinsu ba wa kai."

"Me yasa to?" ya tambaya yana qara tusa kanshi a tsakiyar wuyanta yana shak'ar daddad'an k'amshin.

Juyowa tayi da nufi d'auko kayan baccinta ta saka kawai ya sureta yayi kan gado da ita, saida ya kwantar da ita sannan ya sauka ya kashe wutar d'akin ya dawo tare da zame towel d'in jikinshi ya wurgo mata, kan jikinta ya kwanta ya fara lagudarta yana sarrafata son ranshi, to itama fa ba kwance kawai tayi ba aikin ta tayashi yi, duk da ita kanta tasa takai mak'ura kuma tana buk'atar tallafi domin gabanta ya nuna hakan, amma ba zata bari ya shigeta tun yanzu ba, tana jin ya fara bud'e mata qafafu ta tashi zaune a firgice.

Janyota yayi jikinshi yace "Khairat, wallahi taimakonki kad'ai nake nema, dan Allah ki barni nayi."

Cikin kukan shagwab'a tace "um um, gaskiya ni tsoro nake ji, wallahi ciwo zanji."

Da sauri ya rik'ota yace "a'a Khairat, na miki alk'awarin ba zaki ji ciwo ba, wallahi a hankali zan biki."

"Ka manta meya faru ne, ba qaramin rauni suka min ba fa, gaskiya ba zan yarda na sake kai kaina mahallaka ba."

Janyeta yayi daga jikinshi rai b'ace ya sauka daga kan gadon, kayanshi ya bud'a ya samu doguwar riga ya zura da qaramin wando ya kwanta akan kujera, ranshi kam in yayi dubu ya b'ace dan wani irin kishin bala'i ne yaji ya taso mishi akan su Musa, kawai saiya dinga haskota kwance su kuma suna juyata son ransu, tunani yake yanzu nan wasu sun rigashi isa bakin bodar, tuk'uk'i kawai ke taso masa a zuciya har Khairat ta d'auro towel d'in tazo kusanshi, zata sunkuya kenan ya tsayar da ita ta hanyar d'aga mata hannu yace "dan Allah ki rabu dani, kije ki kwanta."

Yanda yayi maganar yasa bata da wani zab'i daya wuce ta koma kan gadon tayi zaune sai kuma ta fara kuka, yana jin shashek'arta kuma duk sai hankalinshi ya watse, alk'awarin daya d'auka na ba zai bari ta zubar da hawaye ba yasa ya koma kusanta ya fara rarrashi, a cikin rarrashin yace "ke kika tsokano min kishina Khairat, dan Allah idan zai yiwu? bana so na sake jin wannan kalmar a bakinki, ina so ki manta nima kuma zanyi qoqari naga na manta, kinji ko shalelen Papa."

Murmushi tayi tace "kayi hak'uri to , insha Allah ba zan sake ba."

Kwanciya ya gyara mata a qirjinshi ya tofeta da addu'a sannan ya dinga daddab'ata har bacci ya d'auketa, shima ya jima kafin bacci ya d'aukeshi.

_To me kuka ce fan's?_
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

πŸ’•πŸ’•πŸ’• *My Meelat*πŸ’•πŸ’•πŸ’•

_Ina tayaki murnar zagayowar ranar haihuwarki, fatan Allah ya qaro shekaru masu albarka, *jouyeux anniversaire* My mentor._πŸ’–

_My sweet and lovely *Hawwer* , ina miki fatan qarin wasu shekarun domin sai dake bugun zuciyar Sameera ke tafiya daidai, *Happy Birhtday* my Hawwer._πŸ’–

_Bismmilahir-rahman-rahim_


3⃣3⃣


Kiran sallah asuba ne ya tashesu, alwala yayi ya nufi masallaci bayan ya biya ta d'akin Zuby ya tasheta, sallah sukayi bayan ya dawo kuma ya d'orawa Khairat karatunta, kamar kullum yau ma jinjina mata yayi sannan ya sake ninka mata wani, suna gamawa wanka ta fara yi bayan ta fito ya shiga, harya fito bata saka kaya ba hakan yasa da kanshi ya shiryata cikin riga da zani mai kamar siket na shadda, d'inkin yayi sosai gashi ya zauna mata a jikin, d'an kwali ta d'aura sannan ya saka mata sark'a da yan kunnai na zinariya kafin ta juyo ta kalleshi tana murmushi tace "nayi kyau?"

Saida ya sumbaci goshinta kafin yace "ai fad'a ma b'ata lokaci ne, kin ganki kuwa? kamar k'yank'yasar yau."

Dariya tayi ta rumgumeshi tare da sumbatar kumatunshi tace "ka saka min albarka to."

"Allah ya miki albarkar baby." ya fad'a yana dariya.

"Sakinshi tayi tana d'aukar hijab d'inta tana fad'in "yaufa ba zanje wajen aiki ba, yanzu haka salon zanje amin kitso da kuma gyaran jiki."

Shima kayanshi ya fara sakawa yace "wane irin gyara kuma, kina so sai kin fara haukatani da kyawunki ne?"

"To ai ba kyawu zan qara ba, gyara ne kawai."

Yana gama shirinsa Ruk'ayya ta kawo masa abinci, har zata fita yace "ki kira min Zubeida."

"To yaya." ta fad'a tana ficewa daga d'akin.

Da kanshi ya zaunar da Khairat a gefen hagunshi jim kad'an kuma Zuby tayi sallama, da hannu ya mata alama data zauna kusanshi , saida ta duk'a har qasa tace "ina kwana yah Umar."

"Lafiya kalau Zubeida, kin tashi lafiya?"

"Lafiya lau."

"Ya kwanan bak'unta kuma?"

Sai lokacin kad'ai ta tashi daga durk'uson ta zauna inda ya nuna mata tana fad'in "yah Umar ai gidan nan ba bak'ona bane."

"Kuma fa hakane."

Jin shiru yasa yace "banji kin gaishe da ita ba?"

D'an karatun tanutsun da tama kanta ne a daren jiya taji yana neman sub'ucewa saboda b'acin rai, cikin harare harare tace "ina kwana." ba tare data kalleta ba.

Khairat kam data fita iya karatun zaman duniya saita saki fuska duk da irin k'uncin da take ji da kishin dake taso mata tace "lafiya lau yer uwa, kin tashi lafiya?"

Shiru ta mata hakan yasa Umar Faruk cewa "a gaskiya ba haka nake son gani daga gareku ba, akwai bukatar ku canza tun kafin lokacina ya fara aiki."

Yana fad'a ya kalli Zuby yace "kece qarama , ki zuba mana abincin."

"Ruk'ayya takai min nawa a d'akina." ta fad'a a daqile.

"To zan fad'a mata daga yau tare zamu dinga ci, yanzu ki zuba mana."

Khairat ce tayi saurin cewa "lah baby, ka barshi ni zan zuba, ya zaka saka amarya aiki daga zuwanta." tana fad'a ta janyo kayan ta had'a musu tea kamar yanda taga Umar Faruk yayi jiya, sannan ta bud'e plate d'in soyayyan k'wai da dankalin turawa, sai kuma miyar dake cikin kwano ta naman rago, tana gamawa ta dafe qirjinta tare da sauke ajiyar zuciya, kallonta Umar Faruk yayi yace "gajiya ki kayi?"

Cikin dariya ta dafa kafad'arshi ta rad'a masa cewa "wallahi na zata ba zan iya ba, na gode daka koya min jiya."

Shima dariyar yayi Zuby kam ta gefen ido ta kallesu, shiya fara saka hannu kafin yace "to bismillah."

Nan suka fara ci ba mai magana har suka gama, Zuby ce ta fara tashi ta fita dan zuciyarta barazanar tarwatsewa take, shima dai jakarshi ya dauka haka ma Khairat kafin suka fito a tare, saida suka shiga d'akin iyayensu suka gaishe dasu kafin suka fito suka tafi, yauma a motarta suka tafi yana tuk'awa , saida ya ajeta salon sannan ya wuce bayan tace ya bari zata koma gida a taxi.


Kitso akan fara mata yayin da tasa aka makala mata sabbin akaihu, sai dai wannan karan ba masu tsayi bane sosai yan madaidaita, tasa aka lullub'esu da jan lalle mai ja sosai, bakin lalle tasa aka mata ga hannuwa kawai saboda har yanzu wanda aka mata bai gama zubuwa ba, gyaran fuska aka mata tare da gyaran gira, masha Allah kamar balarabiya ta fito, dogayen riguna ta gani masu kyau da kwalliya ta siyo har kala shida, sannan ta d'auko hanyar dawowa gida.


*************

Tun fitarsu Zuby suka shiga d'aki ita da Ruk'ayya tana sank'ama mata tambayoyi ita kuma tana kakkaucewa wajen bata amsar, a qarshe kuma cewa tayi "itama tana girki ne?"

"A'a, tunda tazo bata tab'a girki ba." cewar Ruk'ayya.

"To kenan me take? sai dai a dafa a bata taci."

"To ai kusan yanzu itace ma ke ciyar damu, tunda da kayan abincin data siyone muke anfani dasu."

"Me? wai kina nufin abincin da naci ma d'azu a cikin wanda ta siyo ne?"

"Qwarai kuwa." cewar Ruk'ayya cike da mata kallon baki da tunani.

"Tabb', bari yah Umar d'in ya dawo, wallahi ba zan sake cin abincin wajenku ba, kayan abinci kawai zai siyo min na dinga dafa nawa nima."

Cike da iya shege Ruk'ayya tace "amma da ice zaki dinga dafawa ko?"

"Kawai ma bayan naga harda gas gareku." ta fad'a tana hararanta.

"Toshi gas d'in dashi kika taho jiya? ai shima ita ta siyoshi, dan haka ki sake tunani ma dan wannan ba mafita bace."

"Keni dallah tashi ki bani wuri." korarta tayi daga d'akin ita kuma ta kira Mama ta fad'a mata halin da ake ciki.

Nan Mama tace "to bari kiji in fad'a miki, wallahi saikin tashi tsaye sosai, inba haka ba kin shiga uku a wannan gidan, kuma abinda za kiyi yanzu shine, da zaran ya dawo ki fad'a mishi ya siyo miki kayan abincinki da qaramin rechau wanda zaki dinga aiki dashi, tunda kinga nan da kwana biyar zaki fara zuwa ecole (school), kuma wallahi karki yarda ya fad'a miki wasu maganganu, ki dage saiya siya miki, kuma ki tabbatar kinyi aiki da abinda na baki jiya."

"To Mama, amma ai ita bansan yanda zanyi na bata tasha ba."

"Saboda ke ba mace bace? kisan duk irin dubarar da za kiyi tasha, inba haka ba wallahi data fara haihuwa kafin ke, kin shiga uku."

Da haka sukayi sallama tana tunanin hanyar da za tabi wajen saka ma Khairat wannan maganin.

**************


*12:15*, Khairat ta shigo gidan ba tare da sallama ba kamar yanda ta saba, ganinta da babbar leda a hannu yasa Ruk'ayya taje da sauri ta karb'i ledan tana fad'in "sannu da zuwa aunty Khairat."


Saratu da Zuby na zaune waje d'aya ko kallonsu ba tayi ba,
yaran ma duk suna zaune da sannu suka bita , jakarta ta bud'a ta fito da d'an qaramin kwalin chocolat taje inda yaran suke zaune duk rabawa kowa harta qare, godiya suka mata Zuby kuma ta bita da kallon banza, ita kuma ta wuce d'akinta saboda iyayen duk suna d'aki, Ruk'ayya ce ta bud'e k'ofar ta shigar mata da ledar har ciki, aje jakarta tayi tare da hijab tana kallon d'akin an kitsashi ba kamar yanda suka barshi ba, kallon Ruk'ayya tayi tace "Ruk'ayya waike ba kya gajiya da aikine, naga ko ecole ba kya zuwa sai d'ora girki da shara, a haka zaki qarene?"

Cikin dariya tace "aunty kenan, ai wannan aikin shine aka saba mana dashi, duk 'yan uwana mata wanda sukayi aure saida sukayi wannan aikin, kuma karatu na gama ne shi yasa bana zuwa, na addini kad'ai Baba yake qaramin wani lokaci yah Usman ko yah Umar, amma yanzu dai mun daina da yah Umar."

"Me yasa?" ta tambaya lokacin da take b'alle bras d'inta.

"Tunda yayi aure ne."

Towel ta d'aura a qirji ta nufi k'ofar fita tana fad'in "ki bud'a ledar nan dogayen rigunane ki d'auki wacce ta miki."

"Wayyo aunty Khairat na gode sosai, Allah ya saka da alkairi."

Bud'awa tayi sai dai bata tsaya zab'eba kawai ta d'auka ta fita cikin farin ciki, Zuby na ganinta taja dogon tsaki tace "aikin banza, ashe dai gulma ce tasa daga ganinta kika tashi harda wani karb'an abun hannunta kamar uwar data haifeki."

B'ata rai Ruk'ayya tayi tace "Zuby, ki fito idona na rufe, ba ruwana dake baruwanki dani, kar kisa muyi abinda za'a mana dariya, tom."

"Nak'i d'in marar kunya, kenan nice za kima rashin kunya dan kinga daidai muke dake? to ko kina so ko ba kya so nima matar yayanki ce, kuma na tabbata ni ya fara sani dan haka na fita kusanci dashi."

Wani dogon tsaki Ruk'ayya taja kafin tace "kishin ne haryake neman haukataki , ya muna magana zaki canza mana maudu'in da muke kai."


Tana fad'a bata tsaya sauraranta ba tayi d'aki ta nunawa Mama rigarta, godiya tama Khairat tare da saka albarka, dan tasan kyauta ce ta bata ba rok'a tayi ba.

****************


Koda ta fito daga wanka kwalliya sosai tayi sannan ta shirya cikin d'aya d'aga cikin rigunan data siyo, nanfa ta d'auki k'yali da shek'i ga gyaran data sha, gama shirinta ba wuya kuma taji dumin Umar Faruk a tsakar gidan, d'an kwalin rigar ta yane kanta dashi ta feshe ko ina da turare sannan ta tsaya tana jiran shigowarshi.

Shi kuma yana shigowa yaji wani sanyi ya ratsashi saboda ganin d'akin bud'e ya tabbatar da sanyin idaniyarshi ta dawo, Zuby ce tace "sannu da zuwa yah Umar."

"Yawwa,sannu da gida." ya fad'a tare da yin sama da Fateema.

"Ango kasha k'amshi." cewar Saratu.

Yana kallonta yace "ke ko ba kya gajiya da tsokana, to wane k'amshi kuma?"

"Au, nice zan fad'a maka wane iri? ai kai kafi kowa sani."

"Kinga da surutun nan, ki tashi ki kaimin ruwan wanka zafi miki ki samu lada."

Hararanshi tayi tace "bana so, sai yaune ka tuna dani kenan?"

Waro ido yayi yace "lah, ladar ce ba kya so? lallai ma matar nan, gaba d'aya ba kya kula dani yanzu."

"Haba Ummaru, 'yan aljanna biyu ne fa a tsakiyarka, ai kuwa kaga ba buk'atar na zama ta uku a bayansu."

Wani shu'umin kallo yama Zuby wacce itama shi take kallo yace "ga d'aya nan a kusanki ma, amma ya banga d'ayar ba?"

Da hannu Saratu ta nuna mishi d'aki tace "to ai kasan basan fitowa take ba, ina jin tana ciki tana shirin tarbanka, dan naji qarar ruwa alamar tana wanka kenan."

Cike da zolaya yace "toke me kike anan? baki je kiyi shirin tarban naki mai gidan ba."

"Ni! rufa min asiri, mu ai tsohine mun barma 'ya'ya da k'annanmu."


*Irin wannan tunanin shi ke kashe mata dayawa ta hanyar nakasasu, kice ke kin tsohuwa saboda kawai kinyi haihuwa uku hud'u, mijinki kuma yana buk'atar ganinki cikin kyakyawan yanayi da shiga, koda ke kika haife duniya, wallahi saimun gyara sosai idan har muna son ganin daidai, a duniya karki yarda namiji ya rainani saboda rashin tsaffa da kama jiki, daya rainaki ta wannan hanyar kin gama shiga tara.*

Wucewa kawai yayi bayan ya aje Fateema, tashi Zuby tayi tabi bayanshi hakan yasa ya juyo ya kalleta, cikin jin kunya tace "magana nake so muyi."

Baice mata komai ba sai sauya akalarshi da yayi ya nufi d'akinta, yana shiga ya zauna a bakin gado ita kuma ta tsaya, kallonta yayi ganin bata zauna ba kuma ba tace komai ba, kammo hannunta yayi ya zaunar da ita akan cinyarshi d'aya tare da zura hannunshi ta bayanta ya rumgumota, d'aya hannunshi yasa ya rik'o hannunta yana wasa da yatsunta ya qurawa fuskarta ido yana kallo, ita kam kunya ce ta rufeta hakan yasa tayi qasa da kanta ta kasa had'a ido dashi, cikin taushin murya yace "ina jinki, kince za muyi magana kuma kinyi shiru."

Wala-wala ta fara da ido tana tunanin yanda zai fahimceta idan ta fad'a masa, tasan halin Umar Faruk sarai, zai iya baud'ewa ya kuma bita da masifa, sumbar daya watsa mata a wuya yasa ta dawo daga tunani, hannunshi yasa cikin rigarta ya fara wasa da cinbiyarta, sake maimaita mata yayi "ki fad'a mana ina jinki."

Hannu tasa tana shafa wuyanta tana fad'in "yah Umar dama, nan da kwana biyar ne zan fara zuwa ecole, to kuma ni ba wani cin abinci ba nake sosai, shine nace da zaka siyo min nawa kayan abincin saina aje."

Shiru tayi tana d'an satar kallonshi dan ganin yanayinshi, shi kuma shiru yayi yana tunanin abinda ta fad'a, tabbas yasan wannan ba tunaninta bane, amma kuma ba matsala bane tunda ko Saratu itama wani lokacin ita kad'ai take abincinta, dan haka zaiyi yanda take so kodan gudun magana.

Fuskarta ya shafa yace "hakan ya miki?"

Kai ta d'aga alamar eh tare da fad'in "eh yah Umar."

"To karki damu, an jima zan siyo miki kayan abincin, abinda ban siyo ba kuma saiki fad'a min saina baki kud'in ki qarasa siyowa."

Ko kad'an ba tayi tunanin haka ba hakan yasa tayi murmushi tace da cewa "na gode yah Umar."

D'agata yayi daga jikinshi ya mik'e tsaye yace "ba komai."

Matso da ita yayi kusanshi yace "ba kiyi kewata ba ko?"

"Kai yah Umar." ta fad'a tana rufe fuska wai ita kunya.

Janye hannayen nata yayi yana kallon fuskarta yace "to naji, in dai ba kiyi kewata ba karki sumbaceni, amma idan kinyi ki sumbaci bakina."

Zuro mata fuska yayi yana jiran yaji saukar sumba, a tunaninta ta ballagazar da kanta sau d'aya dan haka ba zata qara ba, dan haka kawai ta fito daga d'akin ta baroshi tana dariya, dan gani take ya fad'a tarkonta, yana ganin haka ya fito shima kai tsaye d'akin habibiya ya wuce.



Da sallama ya shiga kamar yanda ya saba, amma saiya kasa shiga ciki yana kallon Khairat dake tsaye tana sakar masa tsadadden murmushi, ganin ya tsaya yasa ta karasa ta janyo hannunshi ya k'arasa shigowa ciki, saida ta sakar masa kyakyawar sumba a baki tare da wata a goshi kafin tace,

"Ya kake kallona haka?"

Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi kafin ya lumshe idonshi ya kuma bud'e a kanta yace "dole na kalleki, a gaskiya baby dana rasaki da nayi asara babba, sai yanzu nake qara fahimtar sa'ata a rayuwa."

Wani murmushi zaka

Please Login or Register in order to submit comment