Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fad'a ba tare data kalleshi ba.

"Ina nufin 'yar uwarki, nasan kin karanta a hadith, cewar idan kazo ka samu mutum a wuri kaine zaka fara gaisheshi."

A wulak'ance tace "ina kwana." tana hararan Khairat d'in.

Khairat da ita kanta haushinta take ji itama a wulak'ance ta amsa da "lafiya lau."

A haka suka fara cin abincin babu mai magana, Khairat kam yau kishinta take ji sosai, haka ma Zuby kamar zata mutu saboda ganin wai yau Umar Faruk ne ya zama nasu su biyu.

Zuby da masifa ke gurgurarta ce tace "idan ba damuwa zan iya magana?"

Kallonta yayi da murmushi yace "Zubeida, a zamanin 'yanci muke fa, zaki iya magana mana kina da damar hakan."

"Sai nake ganin kamar hakan bai dace ba kullum a dinga dafawa ana bamu, me zai hana ka raba mana girki, kaga kenan duk lokacin da kwanan d'aya daga cikinmu ya zagayo itace da girkin ranar."

Tabbas Zuby tayi gaskiya dan abinda ya kamata kenan, saida ya gyara zamansa kafin yace "gaskiya ne Zubeida, kin fad'i abinda dama dole zanyi magana akai koba yanzu ba."

Kallon Khairat yayi yace "abinda ya dace ayi kenan, dan haka yanzu zaku fara girki da kanku."

Waro masa ido tayi tayi magana qasa qasa sai dai baiji me tace ba saboda na kurame ne tayi, ganin Zuby ta tashi tare da fad'in "alhamdulillah, aci lafiya." tana fad'a ta bar d'akin domin kuwa burinta ya cika.

Khairat na ganin haka ta gyara zama da kyau ta cire hannunta daga plate d'in tace masa "me kayi haka Faruk, so kake kaci mutuncina a gaban yarinya qarama, dan kasan ban iya komai ba shi yasa zaka amince da abinda ta fad'a? to kama sake tsari dan wallahi ba zan yarda ba, dan babu abinda zai sani yin girki koda ma na iya."

"Khairat, miye abun d'aga hankali a cikin nan? kinyi sakaci tun farko kasancewarki na 'ya mace kika kasa koyan aiyukan da kinsan dole zaki yisu in dai har kinyi aure, amma duk da haka ba wata matsala tunda zaki iya koya."

"Kana haukane? nice zanje koyan girki saboda kawai waccen yarinyar, nifa ba zan iya wannan wahalar ba ta girki danko a gidanmu banyi ba, kuma kai shaidane."

Kallon da yake watsa mata ba tare da magana ba yasa ta mik'e ta cire rigar baccinta ta shiga wanka, tana fitowa shima ya shiga cikin sauri ya fito ya fara shiri, saida ya gama shi da ita babu mai kula wani harya d'auki jakarshi zai fita ya d'auko makullin motar ya mik'a mata, karb'a tayi ba tare data kulashi ba kafin ya fice daga gidan.


Saida ya fita kuma tana shirin tana tambayar kanta me yasa tayi haka? ita da take burin ganin ta mallakeshi ta hanya mai kyau, ji tayi kuma ta kasa hak'ura kawai ta d'auki wayarta ta danna masa kira, k'in d'aga kiran yayi saboda yana kan hanya cinkoso yayi yawa, har ya kai bata daina kira ba koda yaga itace kawai saiya share yana tunanin me zata fad'a masa, da sauri ya shiga ma'aikatar ya tarar an fara taro, kamar ko wane ma'aikaci shima tsayawa yayi yana sauraron abinda manager ke fad'a, ya jima yana jawabi kafin ya gabatar da abinda ya tarasu.

Nan aka fara duba sunayen mutum uku wanda zanensu yafi na kowa, na farko shine *Umar Faruk Ahmad* na biyu kuma *Abdullahi Salis* ta uku *Surayya Balarabe*, nan aka kira kowa aka bashi kyautarshi tare da musu fatan alkairi sannan aka qarfafa musu gwiwa tare ma da wanda nasu samu nasara ba, damar tafiya aka basu ba tare da sunyi aikin wannan ranar ba.


*****************


Umar Faruk baya raba d'ayan biyu kan cewar aikin Khairat ne, dan shi dai yasan a tarihin masana'antar babu wanda akace an tab'a bawa kyautar mota, wannan mamakin ya hanashi tuk'a motar sai Ishaq ne ya tuk'ota shi kuma yazo a mashin d'inshi, a k'ofar gida aka paka motar su kuma suka shiga ciki Ishaq na shaidawa mutanen, murna dai ba kowa ke yi ba daga ciki harda Umar Faruk, a haka aka kira Khairat da Zuby dansu gani, suma dai babu wacce ta fito da farin cikinta a fili, Zuby tunaninta shine Khairat ce ta bashi motar raina mata hankali kawai zasuyi, Khairat kuma haushin ta kira bai d'aga bane yake damunta.

Sake fita sukayi da Ishaq Umar Faruk ya goyashi a mashin ya mayar dashi ma'aikatar shi kuma ya dawo amma a hanya saida ya tsaya ya s gas guda biyu 5kl kafin ya dawo gida.

_Bara nima na tab'a turancin nan._😜

_I need you prayers fan's._πŸ‘πŸ‘πŸ‘

_Me zai faru to_πŸ€”
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

_Sorry fan's abisa rashin amsa comment d'inku, jikin ne sai a hankali._

_Dan Allah ku tayamu da addu'a Allah ya bawa my *BK* lafiya, ina so ta dawo muci gaba da kodimoπŸ˜‰, my masoyiyar BK nayi kewarki sosai, rashinki yasa nima bana jin dad'i._


_Bismmilahir-rahman-rahim_


3⃣6⃣



Tunda yaga baiga mota a k'ofar gidan ba ya tabbatar ta fita, koda ya shigo Aliyu ne ya tarbeshi ya karb'i tukunyar gas d'in, d'aya ya bawa Zuby d'aya kuma ya aje a kewayen Khairat, shiga yayi ya rage kayan jikinshi sannan ya kwanta akan gado, wayarshi ya ciro ya fara kiran Khairat, Khairat kuma data bar wayar a mota tana cikin babban kanti tana siyayya, hakan yasa Umar Faruk cewa ta rama ne itama.

***************

Har *12:40* Khairat bata dawo ba, ganin haka yasa Zuby girki d'an sassauk'an abinci ta zuba a plate ta rufe da d'aya tare da cokali ta tunkari d'akin Khairat.

😏😏😏humm, zaki jawa kanki.

"Assalama alaikum." tayi sallama cikin taushin murya.

"Wa'alaiki salam, shigo." ya fad'a.

Bud'a labulen tayi ta zura qafafunta ta shiga, ganin Zuby yasa ya tashi zaune dan baiyi tsammanin ita bace saboda murayar daya ji, "Zubeida, kece dama?"

Saida ta tsaya gabanshi tace "eh, kona koma ne baka buk'atar ganina?"

"Ah haba, ni na isa."

Ganin tayi zaune a bakin gadon kusa da qafafunshi tana wani yamutsa fuska yasa ya d'an qara gyara nutsuwarsa yace "ina jinki, magana zamuyi ne?"

"Abinci na kawo maka, dan nasan kana jin yunwa, tunda naga ita har yanzu bata dawo daga walagigin ba." ta fad'a tana bud'a plate d'in.

"Me kike nufi da abinda kika fad'a?" ya tambaya.

Cikin had'e fuska tace "ka fini sani mana."

Qara gyara zama yayi yace "Zubeida, ku matana ne, kuma nine mai alhakin kare mutuncin kowace daga cikinku, ya kamata kisan me zaki dinga fad'a akan Khairat, duk cin zarafin da zaki mata kamar ni kikawa , haka itama idan ta miki ni tawa, tunda kika zo gidan nan kike kiranta da sunan da bai dace ba, na miki shiru ne kawai amma naga baki gani ba, to daga yanzu bana so na sake jin kin kirata da sunan karuwa, dan ita ba karuwa bace kamar yanda kike fad'a, dan haka ki kiyaye, idan kuma abincin kika zo bani zaki iya ajewa ki tafi na gode."

Cike da makirci ta fashe da kuka tana fad'in "ni dama sani baka sona yanzu, wallahi banyi tunanin haka daga gareka ba yah Umar, gaba d'aya ka canza saboda waccen matar, shine ba komai ba anfanin zamana a gidan nan in dai har baka sona."

Tsaye ta mike ta fara tafiya taji ya rik'e hannunta, saukowa yayi daga kan gadon ya rumgumota jikinshi yana shafa kanta, cikin rarrashi ya fara fad'in, kiyi hak'uri, baki fahimceni bane Zubeida, ina so ki gane cewa, ke da Khairat ba zan bari wani ya cutar da d'aya ba, ko itace take fad'a miki haka abinda zanyi kenan, ke da ita duka Allah zai tsayar dani ranar gobe kuma ya tambayeni yanda na shugabanceku, Zubeida na zama mutum azzulumi da baya iya adalci tsakanin matanshi, da farko naci amanar Khairat ta hanyar kusantarki a kwananta, dan Allah ki taimaka karna sake aikata wani laifi, banyi adalci ba idan nayi shiru ina ji kina kiranta da karuwa, amma kiyi hak'uri kinji."

D'ago da kanta yayi yana kallon fuskarta yace "kiyi shiru to, yanzu kije d'akinki ki zauna zanci abincin, bana son mai d'akin ta sameki anan, dan nasan yanzu tana kan hanyarrrr."

Bai k'arasa ba kuma Khairat ta bud'a labulen d'akin ta shigo, daram dam, shine tsinkewar da gaban Khairat yayi ganin Zuby a qirjin Umar Faruk, bugun zuciyarta ne ya qaru ta yanda ba zata iya saisaita kanta ba, sauke idonta tayi akan Zuby ta fara takowa cikin d'akin, itama Zuby d'in ita take kallo harta aje plate d'in hannunta akan center tebur d'in d'akin, ganin yanda suke kallon juna yasa Umar Faruk cewa "Zuby ki wuce d'akinki."

Saida ta gama hararan Khairat sama da qasa sannan taja dogon tsaki ta nufi hanyar fita, aikam dama zuciyar Khairat a wuya take hakan yasa ta finciko rigar Zuby ta shake sosai ta zubar da kayan hannunta harda wayarta ta mata wani jan kallo tace "dawa kike, ni Khairat ki kewa tsaki, ni kike wa tsaki? dake nake magana."

Ta qarashe maganar da d'aga murya, matsowa Umar Faruk yayi da nufin magana Khairat ta daga masa hannu tace "dakata min dallah, bari na gama da ita sannan, kana kallo qaramar yarinya zata nemi taci mutunci na, akan miye zata min tsaki?bayan nice ke daidai nayi mata tunda ni na sameta a d'akina, koda yake ba laifinta bane laifinka ne, da baka kirata ba aiba zata zo, shine har zata dinga min kallon raini da iskanci, wallahi sai naji wanda ya d'aure miki gindi a gidan nan."

Ta qarasa tana jinjigar Zuby dake hannunta, Zuby kam tuni idonta suka fara kawo qwalla, cikin gunguni ta rik'e hannun Khairat tace "dallah sakeni malama."

Wani murmushin rainin hankali Khairat ta mata ta sake shak'ar rigarta ta jinjina tace "ki k'wace mana idan kina ganin k'arfinki yakai, tabbas gata da shagwab'a ne suka raini ne, amma ki sani ina da k'warin k'ashi da tsabagen tsagwaron k'arfi, ta yanda idan na rik'i kamarki wallahi ba zaki iya k'watar kanki ba, amma idan kinyi musu toki gwada ki gani."

Qara qoqarin qwaqwale hannun Khairat tayi amma tajita jim a hannunta, sake maqale murya tayi tace "dallah nace ki sakeni ko."

"Hum, bari kiji na fad'a miki, dama nasan dole za kiyi rawar kai dan tunda naga mahifiyarki na tabbatar da haka, tun ranar da kika shigo gidan nan kike min kallon bi aho amma na miki shiru, to ki sani qyaleki nake ba dan komai ba sai dan canjin da aka samu, idan kuma kika kuskura kika tayar da qwanqwanman Khairat harna dawo asalin Khairat d'ita, tofa akwai matsala dan ba lallai gidan nan su iya dani ba, kashedi na qarshe, karki bari na sake ganin qafarki cikin d'akina dan ban yarda dake ba, kamar yanda ban yarda da mahaifiyarki ba."

Da kai ta mata alamar ta wuce kawai, ficewa tayi da sauri saboda hawayen dake son taho mata, kai tsaye d'akinta ta wuce ta fad'a saman gado ta fashe da kuka, duk da zuciyarta naso ta qaryata abinda take ji, amma dai tabbas ta tsorata da Khairat yau d'in nan, dan tasan gaminta da ita ba zai mata kyau ba, saida taci kukanta ta koshi sannan ta kira Mama ta fad'a mata abinda yake faruwa, fad'a sosai Mama ta mata tare da zaginta gaba da baya kafin ta sake jaddada mata tayi aiki da magungunan nan.

Bud'ar bakinta cewa tayi "ai Mama maganin ne nasa a abinci nakai masa, shine fa tsinannar ta shigo."

"Toki kwantar da hankalinki, nasan ai zaici abinci, da yaci kuma magana ta qare."

"To Mama, sai an jima."


***************

Tana fita Khairat ta wurga masa harara tana hango Zuby a qirjinshi, ta gabanshi taso wucewa amma saiya tareta, kallonshi tayi tace "matsa min a hanya."

"Ba zan iya ba, saboda kina hushi dani."

"Ka matsa min nace ko, inba so kake na huce a kanka ba."

"In dai zaki huce na amince ki huce a kaina."

K'arfinta tasa ta tureshi gefe hakan yasa yayi baya da k'arfi, amma jarumta tasa bai fad'i qasa ba, tsaye yayi sosai a gabanta a hankali ya rik'o hannunta tare da zube gwiwoyinshi a qasa ya marairaice kafin ya fara magana,

"Kiyi hak'uri, nasan ke mai hak'uri ce, ki yafe min domin nasan kin yafe min laifin da yafi wannan ma, kimin uzuri danna fahimci ke mai ilimi ce, my *Khairiri* ki yafewa wannan hamagon mijin naki mana, ke alkairi ce a gareshi kamar yanda fassarar sunanki yake, duk da dai bana da laifi, amma ina neman gafararki matata, idan baki yafe min ba zan shiga tashin hankalin da nake da yak'inin ban tab'a shiga irinsa ba, domin kuwa Khairat ta zama wani b'angare na sassan jikin Umar Faruk, a yanzun yafiyarki ce zata zata tabbatar da ci gaba da farin cikin mijinki ko akasin haka, domin kuwa ba Umar Faruk in dai har ba Khairat, hushinki na second d'aya, tamkar hushin duka mutanen duniya ne a wajen Umar Faruk, ki tausaya kuma agazawa wannan bawan Allah wanda rayuwarsa ta kasance kece mahad'inta, kuma nasan ko Khairat ce ta b'atawa Umar Faruk rai, zata sunkuya har qasa sannan ta nemi afuwarsa, a lokacin kuma Umar Faruk zai rumgumo Khairat jikinsa sannan yace na yafe miki my Khairat."

_Kaji mai wayo, wato ya fad'a mata abinda ya kamata tayi cikin dubara._


Inhar Khairat tace kalaman nan basu shiga sassa da b'argo da jijiyarta suka ratsa zuciyarta ba, to qarya ta fad'a hakan yasa ta sunkuya itama ta rumgumeshi tace "na yafe to, amma me yasa zata shigo min har d'aki kuma ta raina min wayo?"

K'eya ya d'an sosa yace "kiyi hak'uri, abinci kawai ta kawo min."

Sai lokacin ta juya ta kalli plate d'in dake aje, takawa tayi ta d'auki plate d'in ta dauka ta bud'a, tsaki tayi tare da fad'in "aikin banza kawai, inba munafirci ba meye na kawo maka abinci? bayan ba ranar girkinta bace, to ba zaka ci ba danni ban yarda da ita ba."

Tana fad'a ta fita da plate d'in ta aje akan gajerar katangarsu sannan ta dawo ta fara cire kayanta, bayanta ya tsaya ya fara cire mata bras yana fad'in "naji dad'i da kika yafe min, nan gaba zan kiyaye b'acin ranki."

Tana d'aure kitsonta tace "kayi nasara akan Khairat, dama wannan kalaman kad'ai Khairat take buk'ata kuma gashi ta samu maiyi mata."

Da haka ta shiga wanka shi kuma ya nufi masallaci, yana dawowa kuma ya samu tana sallah, kayan data barbaza ya fara tattarewa, wanda ta cire kuma ya ninkesu ya mayar drower, tana gamawa ta taso ta sumbaci goshinshi tare da qarasa addu'arta ta fad'a a fili cewa "Allah ya dawwamar maka da farin ciki a rayuwarka."

"Ameen." ya fad'a yana kallonta yace "addu'a kika min?"

"Eh mana, addu'a nawa mijina." ta fad'a tana cire hijabinta.

Yana kallo ta fara shafe shafe da murje murje, humra kusan kala bakwai yaga ta shafa kafin ta d'auki qaramar riga iya cinya ta saka sai pants, wasu turaren yaga ta dauka tana fesawa har kala hud'u suma kamar dai abun hauka, *pure love*, *Mid night*, *Blue dive* da kuma *love flowers*, amma fa cikin k'ank'anin lokaci d'akin ya gauraye da k'amshi mai dad'in shak'a, a hankali ta juyo tana kallonshi cikin takon d'aukar hankalitana jijjiga qirjinta ta tsaya gabanshi.

Rumgumarshi tayi cikin kunne tace "me kake ji?"

Dogon numfashi yaja ya gagara maidowa saboda ji yake kamar zai mutu, wani irin rikitatacen k'amshi ne mai tafiya da hankali, nanfa suka lula wata duniyar wacce Khairat ce kad'ai ta samu nutsuwa amma banda Umariri πŸ˜‚, dan wata sabuwar sha'awa ce ta taso masa wacce inba fa can yakai ba ba zai samu nutsuwa ba, a haka tafi masallaci sallah asar , yana dawowa kuma ya sameta tasa kayan marmari gaba tana shan kayanta a maimakon abincin rana, zaune yayi kusanta ya d'auki ayaba yana fad'in "me zaki dafa min?"

"Yaushe? wai da gaske kake? shi yasa kenan naga tukunyar gas."

"Eh mana." ya fad'a tare da kai ayabar bakinta.

Bud'a bakinta tayi sosai ta tsotso tana kashe masa ido, shi kanshi abinda tayi wata ma'anar ya bayar ta daban, a take yaji wani abu yana masa yawo dan haka ya rintse idonshi, cire ayabar tayi daga bakinta ba tare data d'iba ba tace "me kake so na dafa maka?"

"Komai ma." ya fad'a numfashinshi na fizgarshi.

Aje tuffan dake hannunta tayi ta mik'e tsaye tace "zaka sha mamaki yau, dan zaka ci abincin shalelen Papa."

Canja kayan jikinta tayi ta saka riga da wando kafin tace masa "to ta ina zan fara?"

Murmushi yayi a zuciyarshi kuma yace "zan kuwa sha mamaki."

Kallonta yayi yace "ki fara tanadar kayan aikin, daga baya sai kiyi tunanin abinyi."

"To ina suke kayan?"

Dariya yayi dan da alama shima yau zai d'ana girki, fita yayi ya kira Ruk'ayya dake fama da nasu aikin, tana zuwa tace "yah Umar gani."

Cewa yayi "kije ki d'auko mata duk wani abu da kika san za'a buk'ata wajen sarrafa doya da k'wai da miyar...."

Sai kuma ya kalli Khairat yayi shiru, itace tace " umm , jus kawai nake buk'ata na mayonnaise da albasa."

"Me zai hana ki had'a da sardines?" cewar Umar Faruk.

"Um um, bana cin kifi da daddare."

Kallon Ruk'ayya yayi yace "jeki kawo, ai akwai komai ko?"

"Akwai yah, doya ma akwai sauran wacce ka siyo."

Tana fad'a ta fito tana dariya dariya murmushi murmushi, qanqanin lokaci ta had'a mata komai a kewayenta ta tafi ta kama nata aikin, tare da Umar Faruk suka fito tana kallon kayan, rik'e k'ugu tayi ta yamutse fuska, satar kallonta yayi ya bushe da dariya ya koma ciki, "humm, dariya ko? zaka sha mamaki."

Tana fad'a ta dawo d'akin wata santaleliyar wuk'a ta d'auka ta fita, d'aya daga cikin kujerun wajen ta zauna ta janyo doya ta gatsa mata wuk'ar, aikuwa sai doya ta rik'e wuk'ar Khairat ta jinjina wuk'a tak'i fitowa, haushi ne ya kamata ta taso cikin shagwab'a ta samu Umar Faruk dake shirin fita.

"Eh, lallai ma malam Umariri, wato ka had'ani da aiki, shine kake qoqarin fecewa daga gidan, to muje idan ka datsa min doyar ka fita."

Bata bari yace qala ba taja hannunshi sai waje, zaunar dashi tayi akan kujerar ita kuma tayi tsaye tace "to fara, dama aikin doya na maza ne irinku masu k'arfi."

Shi dai in banda dariya ba abinda yake, yana tab'a wuk'ar kuma sai yaji ta biyo hannunshi, kai kawai ya girgiza ya fara sara mata ita harya gama sannan ya yunk'ura da nufin tashi, maidashi tayi zaune tana fad'in "kasan me? bara na d'auko wata wuk'ar sai naga yanda zaka fereta , dan ba zan iya ba."

Tana fad'a ta koma d'akin ta d'auko wata wuk'ar, zaune tayi ta d'auki doyar tace "to fara ina kallo."

"Yanzu ina namiji meye had'ina da wannan aikin? bafa wuyane dashi ba."

"Ehe , kaji ka da wata magana, to miye a ciki? naga koda ma na iya ai zaka iya kama min aiki, koka manta ka fara bani tarihin rayuwar *Annabi muhammad (S.A.W)*, kuma kai ka fad'a min yana taya matanshi aikin gida, kaga kayi koyi dashi kenan."

Yamutse fuska yayi yace "Allah ko?"

"Eh mana, d'affak'a sunna." ta qarashe da d'aga mishi gira sama.

Ferewa ya fara yi itama tana ganin yanda yake tana yi, surutu kawai take zubawa yayin da shi kuma a d'arare yake, ya matsu koya tashi dan gidansu ana ganinshi anan duk iliminsu zai tashi a banza, za ace ya zama mijin tace kawai, duk a ciki qwaya biyu kad'ai ta fere shima saida Umar ya d'auka a nuna mata yana fad'in "dubi bata feru da kyau ba."

Suna gamawa ta mik'e tsaye da wuk'a a hannu tana gilmawa da ita ta gabanshi tana fad'in "gashi yanzu harka samu lada, to me zanyi a gaba?"

Qarewa yayi a kujerar yana kallonta da tsoro cikin zolaya yace "wuk'a fa kike nuna ni da ita, zaki yankeni fa."

"To nidai fad'a min me zanyi?"

"Ki kunna wuta saiki d'ora tukunya , saiki wanke doyar ki zuba a ciki bayan kinsa ruwa saiki zuba gishiri."

"Yeeeee, ashe mijina kuku ne." ta fad'a da rumgumeshi.

Yanda ya fad'a tayi amma shiya kunna wutar dan kasawa tayi, suna azawa ta kuma cewa "to saime yanzu?"

"Ki yanka albasa ki b'are tafarnuwa, kinga ni tafiyata zanyi."

Albasa ta d'auka da nufin yankawa amma da qyar ta samu ta fitar da hancin, hannunta ya kasa tsayawa sai rawa yake, shi dai yana kallonta har yaga wuk'ar ta kubce ta daki hannunta, saida ya rigata rintse ido danji yayi kamar wuk'ar ta sauka a qahon zuciyarshi ne, ji yayi ba zai iya jura ba, hakan yasa Umar Faruk cewa "kawo na yanka miki, d'auki tafarnuwa ki b'are."

Dad'i taji sosai nanta fara b'ara tafarnuwa amma fa shima ansha wahala, saboda akaihun dake hannunta duk sun rarraba tafarnuwa gashi ita kanta zafi take ji a akaihun nata, da qyar ta b'ara 'yar kad'an tace ta isa, "to ya zanyi yanzu?" ta tambayi Umar Faruk.

"Ki d'auko turmi ki jajjaga."

"Tu me?"😳

"Ba zan iya daka ba hannuna yayi ruwa." tana fad'a ta shiga d'aki jim kad'an sai gata da blender a hannu cikin kwalinta, bud'ewa tayi ta had'a sannan ta zuba kayan miyar gaba d'aya ta dawo d'aki ta jona a waya ta markad'asu, Umar Faruk kam cewa yayi "dama saboda irinku akayita."

Gama markad'an yayi daidai da dahuwar doyan, nanfa ta d'auko passoire (abin tace macca) da roba ta aje zata sauye doyar, wani k'yale tasa ta kama tasa zata sauke amma tace tsoro take ji karta zubar, karb'a Umar Faruk yayi ya juye mata zai jiyo ya kalleta yaji saukar sumba a kumatu tana fad'in "na gode Faruk."

Aifa buga k'wai a kazo, humm reader's kuzo kusha kallo wajen fasa k'wai.....


_Wai nikam wa yayi girkin nan ne, *Umar Faruk* ne, ko *Khairat*???_


*Ina buk'atar addu'arku masoya.*
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

_πŸ’•πŸ’•πŸ’•Je vous aime tellement.πŸ’•πŸ’•πŸ’•_


_Bismmilahir-rahman-rahim_


3⃣7⃣


Tana bugawa da k'arfinta k'wain ya baje gaba d'aya, kallon Umar Faruk tayi da yake mata dariya yana rufe baki, fashewa tayi da kukan shagwab'a harda turmusa qafafu a qasa, tasowa yayi ya tsugunna kusanta ya dago fuskarta ya fara share mata hawayen yana fad'in "haba babyna, kiyi hak'uri ki daina kukan, kawo na fasa miki."

Karb'a yayi ya fasa k'wain kafin ta zuba kayan had'i yace ta soya, a tak'aice dai haka tayi suyar rabin mai ya zube qasa rabi ya fallatsar mata a jiki rabin kuma ya qone bayan ta kammala, sauce d'in ta had'a shima da taimakon Umar Faruk har suka gama, idan ka ganta saika tausaya mata kuma ta baka dariya, saboda yanda ta had'a zufa ta ko ina biyar jikinta take, amma saboda turarukan dake jikinta yasa zufar ke fitar da k'amshi, sauke kaskon yayi daidai da fara kiran sallah, da gaggawa Umar Faruk ya shiga yayi wanka saboda duk jikinshi ya d'auki odeur d'in abinci kafin ya fito da gaggawa ya nufi masallaci.

***************

Abincin da Zuby ta kawo masa kuma Ruk'ayya ce ta had'a da kayan wanke wanke zata kai wajen da zata wanke, cikin tsautsayi kwanukan suka zube qasa abincin ya b'are, Mama dake zaune saida tayi ta mata fad'a saboda ganin abinci lafiyayye ya zube, hak'uri taba Mama tare da gyara wurin kafin ta fara wanke wanken.


*****************


Kasancewar Khairat yanzu ba abinda take bawa mahimmaci kamar sallah yasa ko wanka bata tsaya yi ba tayi alwala tayi sallah, tana gamawa ta fito ta zuba abinci a wasu shegun kwanukan masu kamar yan shafesu da gold ta zuba, akan tebur ta kai ta aje sannan ta d'auko carap (jug) wanda sukayi daidai da kwanukan ta aje sannan ta d'auko lemu a cikin fridge *chivita* ta juye a ciki, tana

Please Login or Register in order to submit comment