Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta saci kallonshi ta gefen ido taga yana kallonta ta madubi sannan ta dafe kai da fad'in "ahhhhh, washhh kaina."

Da sauri ya juyo yayi kanta ya rik'ota yana fad'in "baby lafiya, meya faru ne?"

Cikin lumshe ido da kasallaliyar murya hannunta dafe da kai tace "kaina ne kemin ciwo, harna fara ganin jiri."

"Ayya, sannu, zoki kwanta to." ya fad'a yana nufa da ita kan gado, a yamutse tace "karka damu kanka, zai bari yanzu."

"Ke lafiya kike? bana da hankali ne zan barki a wannan halin, kinsan yanda nake jinki kuwa?"

Kafin tayi magana ya nufi da ita kan gado ya kwantar da ita yace "bara na samo miki magani."

Shiru tayi harya bud'a drower ya fito da maganin ya d'auko ruwa ya d'agata yasa mata maganin a baki tare da kai mata ruwa, bata bari ya wuce ba ta maidoshi a jikin Umar Faruk kamar wacce ke aman gaske, rik'e rigarshi tayi ta sake yunquro wani aman kamar gaske, ganin babu abinda ya fito daga bakinta yasa ta koma ta kwanta, kallonta yake harya cire rigar yasa ya goge mata bakinta a tunaninshi amai tayi, fitar da rigar yayi ya dawo da abin gogewa ya goge na kan gado, gefenta ya zauna ya d'ora kanta akan cinyarshi yana shafarta yace "tun yaushe kike jin haka amma baki fad'a min ba?"

Da qyar kamar marar lafiya tace "ban jima da jin haka ba."

Lek'o fuskarta yayi yace " to me yake damunki, kodai akwai ajiyata ne anan?" ya qarashe da dafa cikinta.

Shiru tayi ta rufe ido ta nuna bacci harya d'auketa, jin shiru yasa ya sake kallon fuskarta, ganin tana bacci yasa yace "to, ke kuma naki mai bacci ne."

Tana jin haka ta bud'a ido tayi murmushi tana d'aga ido tana kallonshi dan tasan ba ganinta zaiyi ba, murmushin gefen labb'a tayi a ranta tace "kad'an kika gani Zuby kike ko uwar wa, zaku san dani kuke magana."

Daga haka kuma har baccin gaske ya d'auketa, saida yaga ta jima tana baccin sannan ya gyara mata kwanciya, lokacin dare yayi sosai dan haka ya kabbara sallah...


***************

Ganin shiru yau ma yasa Mama fita tace za taje ta dawo, haka ta bar Zuby ita da Zulfa'u a asibiti, daga nan kuma wajen malam ta nufa.

A gaban malam take ta fad'a mishi abinda ya faru tun washe garin ranar data bar wajenshi har izuwa yau, kwantar mata da hankali yayi kafin ya d'ora da "ke dai kinsan komai game da gidan nan, matsalar da aka samu a game da aikinmu shine wannan tsaron dake cikin gidan, abu d'aya da zakiyi yanzu shine, da zaran yarinyar ta fita daga gidan ki gaggauta kirana ki fad'a min, ta haka zamu samu sauk'in yin nasara a kanta."

"To amma malam aiba gidanmu guda ba, taya zansan ta fita?"

" xYarki ba gidan take ba? ki fad'a mata ita saita fad'a miki idan ta fita."

"To shikenan malam, za ayi komai." da haka ta baro wajen malam ta dawo asibiti, koda ta tambaya yazo akace a'a, masifa ta fara asibitin tana fad'in ya rainata ma.


************

Shi kuma yana gida ko fitar baiyi bama shima mutan gida sai kula da Khairat ake , dan gaba d'aya ya fad'a musu bata da lafiya, kowa na tunanin itama ciki ne a kwasa,shi yasa kowa ke bada gudumuwarshi , sai bayan sallah azahar ta nuna ta warware babu abinda ke damunta, amma duk da haka Umar Faruk bai barta har saida akayi sallah magrib, a lokacin ne Khairat ta buk'aci Zuby ta dawo gida, sai dai tana jin kunyar tama Jamila magana ba tare data tura mata kud'in nan ba, dan haka ta kalli Umar Faruk tace,

"Baby."

"Na'am baby, me d'an baba yake so?"

Murmushi tayi tace "ba komai, maganar kud'in nan ne da zan tura, ina buqatarsu ne kuma bansan me nawa Papa ba ya rufe min asusu na."

Wayarshi ya mik'a mata yace "gashi kisa lambar saiki aika."

Karb'a tayi kuwa ta tura iya wanda tayi niyyar tura mata, ganin hankalinshi baya kanta yasa ta duba lambobin daya kira ko suka kirashi, cikin sauk'i ta samu lambar Zuby a wayar, saida ta d'auka a wayarta sannan ta bashi wayar, fita yayi dan sallah isha'i dan rabon daya dawo irin wannan lokacin harya manta, saida tayi sallah tana zauna ta dannawa Jamila kira tace a sallami Zuby, saboda taji nauyi a lalita yasa yace "an gama hajiyata."

Suna gama waya ta kira lambar Zuby, Zuby na zauna taga baquwar lamba, d'auka tayi ba tayi magana ba, "Hello."

Yanda muryar ta daki kunnanta yasa har saida gabanta ya fad'i, kafin tace wani abu Khairat tace "Zubeida, kiyi hak'uri da rashin ganin mijina a asibiti, kar kiga laifinshi indai kina da wayo, mahaifiyarki ce ta fara tsokanoni, a qarshe kuma sai kika nuna min kina so mu fara siyasa a cikin zaman namu , da wannan nake so na nuna miki cewar, ni jinin siyasa ce kuma na gajeta ne ba kamar ke ba da tsinta kawai ki kayi a hanya, bara na nuna miki kad'an daga cikin ikona, yanzun nan za'a sallameki daga asibiti, dan nasan kuna tunanin an ajeku ne kawai, to nice nan nasa aka rik'eku, zai iya yiwuwa ba ara miki mijina yazo ya d'aukoki, bye bye."

Tana kashe wayar ta tuntsire da dariya tana fad'in "waya fad'a miki barno gabas take, turnuqu fad'an iblisai, yaro bai gani ba balle ya raba, da uwarki ma a shirye nake nayi kishi bare kuma ke."


πŸ€Έβ€β™‚πŸ€Έβ€β™‚πŸ€Έβ€β™‚πŸ€Έβ€β™‚πŸ€Έβ€β™‚πŸ€Έβ€β™‚


Cike da jin haushi Zuby ta buga wayar a qasa ta fashe, a tsorace Mama ta kalleta tace "ke lafiya, meye haka dan ubanki?"

Kallon Mama tayi zatayi magana sai kuma ta fashe da kuka, da qyar ta tsagaita da kukan ta fad'awa Mama abinda tace mata, dafa kafad'arta tayi tace "kwantar da hankalinki, zamu je gidan ai wallahi sai Umar Faruk d'in ya raina kansa."

Tana cikin daddab'ata wani namiji ya shigo shiya sallamesu, tattara kaya sukayi suka fito daga cikin asibitin......


**************

Lambar Jamila ta kira amma kafin ta d'auka saita katse kiran, hakan yasa Jamila maido kiran kuma ta dauka, cewa tayi tayi hak'uri ba ita taje kira ba, *anya ba wani abu a game da kiran nan* suna kashe kiran tun kafin ya shigo Khairat ta kirashi a waya, yana d'auka tayi fuska tace "dama qawar nan tawace ta kirani waina fad'a maka kaje ka d'auko marar lafiyarka, an sallamesu kuma sun kasa samunka a waya."

"Amma ai wayata a kunne take." ya fad'a da d'an mamaki.

"To nidai haka ta fad'a min, kaje kawai saika dawo."

"Ok to, ki kula min da kanki da babyna."

"Ina babyn yake?" cewar Khairat.

Dariya yayi yace "bari na dawo zan nuna mikishi."

"Allah ya tsare, saika dawo."

"Ameen." ya amsa ya shiga mota dan dama da makullinshi a aljihu, ita kuma goge kiran da tawa Zuby tayi da wanda tama Jamila, amma bata goge wanda Jamilar ta mata ba da wanda tama Umar Faruk.

************

A k'ofar asibitin ya samesu suna jiran taxi, tsayawa yayi gabansu harya fito, "sannunku." kawai ya fad'a, kayansu ya d'auka yasa ciki sannan ya shiga ya zauna yana jiran shigowarsu, saida suka gama wainashi sannan suka shiga motar, Zuby ce gaba Mama baya sunyi nisa babu mai magana, shirun ne yayi yawa yasa Mama cewa,

"Umar Faruk, ina kallonka mai hankali, amma gashi kana nuna min ba haka ba, me yasa kake haka?"

"Me nayi tanti?" ya tambaya cike da gadara.

"Yanzu yaushe rabon da kazo asibitin nan? saika nuna mana kai ka auri karuwa, gaba d'aya tabi ta shanyeka ta hanaka komai, inba ka sakar mata fuska ba har tana da ikon da zata kira Zuby tana fad'a mata magana, har za tace wai zata ara mata kai kazo ka d'auketa, shi yasa kazo kenan?"

D'an juyowa yayi ya kalli Mama yace "Khairat d'in ce ta kira Zubeida?"

"Eh mana, ko qarya zan mata?"

"A'a, ni bance ba, amma da mamaki."

"To shikenan, kaimu gidan saika tambayeta a gabanmu kaji."

"To." ya fad'a a tak'aice.


Suna zuwa gida ya shigo da kayansu, nan aka fara musu sannu da zuwa har Mama Sa'a da Mama sukace "shirin tafiya muke yanzu kam, amma gashi an muku sallamar dare."

"Ki tambayi karuwar surukarki, ita tasan yanda akayi tasa aka rik'emu sai yanzu kuma tasa aka sallamemu."

Kallonta Umar Faruk yayi yace "tanti ba karuwa ba dai, Khairat sunanta, idan kuma sunan na miki wuyane zaki iya kiranta da alkairi."

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

"Ubanka." ta fad'a cikin hushi harda mishi da hannu.

Gimtse fuska yayi Mama kuma tace "ka fito da munafukar mana ta fad'a a gabanku kuji."

Juyawa yayi ya nufi d'akin ya sameta zaune tana karatun littafi mai tsarki, daga qofar ya tsaya yace "kizo dan Allah."

Da kai ta masa alamar to, hijabi tasa sannan ta biyo bayanshi, ganin kowa cirko cirko yasa ta tsaya kusanshi tana kallon Zuby tana fad'in "yar uwa, yanzu kuka shigo, ya jikin naki?"

Kallonta Zuby kawai take Mama ce kad'ai ta samu damar yin tsaki, Umar Faruk ne ya kalleta yace "alkairina, akan me kika kira Zuby kika fad'a mata magana har kina cewa zaki ara mata ni."

Da sauri ta bud'e baki tana kallon kowa dake wajen da tsantsar mamaki, cike da rainin hankali tace "baby, nice na kira Zuby, akan me kuwa zan kirata, ina na samu lambarta ma?"

Maida kallonta tayi ga Zuby tace "ni d'in na kiraki, tunda muke na tab'a kiranki ne? wallahi kuji tsoron Allah ku tuna zaku mutu fa."

Mama da Zuby kasa magana sukayi sai Umar Faruk ne yace "kin gani tanti, na fad'a muku dama da mamaki, babu ruwanta da sabgar kowa."

Zuby ce dake dafe da cikinta tace "kece za kiji tsoron Allah munafuka kawai, kina nufin zaki qaryata mahaifiyata ne? ai wayarta nanan a duba kiran za'a gani. "

Ta qarasa da kallon Umar Faruk, kallon daya ma Khairat ne yasa ta nuna mishi d'aki tace "tana d'aki, ka d'auko da kanka ka duba."

D'akin ya nufa Khairat kuma ta kalli Mama tace "da kike cewa mahaifiyarki zata min qarya, ita littafi mai tsarki ce da ba za tayi qarya ba, ta aikata laifin daya fi na qarya ma bare kuma wannan."

Kallon Mama Zuby tayi ta kalli Khairat tace "me tayi? ki daina kwalo kwalo ki fito ki fad'a mana in kina da gaskiya."

Matsawa kusan Zuby tayi tace "Ina ruwanki to da zaki ce ta fad'a, karna sake jin bakinki."

Fitowar Umar Faruk yasa sukayi shiru suna kallonshi, saida ya gama duba kiran sannan ya bawa Zuby wayar yace "duba ki gani, kiran da qawarta ta mata ne ta fad'a mata naje na d'aukoku, sai kuma kirana da tayi ta fad'a min, amma duk da haka kike neman d'ora mata laifi."

Saida Khairat ta maqale hannunshi ta d'ora kanta akan kafad'arshi tana kallon Zuby tace "Allah yasa zata gane idan ba asarar kud'inku ku keyi ba kuna zuba mata ecole d'in."

Mama Ruk'ayya Mama Sa'a Umar Faruk harma da Mama Maimuna dariya suka saka, aida bak'in ciki ya taso mata sai kuwa ta buga wayar qasa itama, a take wayar ta fashe ita kuma ta dora "sai dai dukanmu muyi asara, shegiya kawai."

Juyawa tayi zata nufi d'akinta Khairat tace "wallahi ina rabaki da yawan kiran wani shege, zafa ki iya jin kunya a qarshen al'amarin, kuma waya da kika fasa mijinki ne zai biyani."

Maida kallonta tayi ga Mama tace "ki fad'a mata komai ko zata daina kirana shegiya, inba haka ba wallahi da kaina zan fad'a mata komai."

Itama d'akinta ta shige ta barsu nan, Umar Faruk kuma daukar wayar yayi yaga ta fashe sosai, yanzu dole saiya siyi sabuwaπŸ˜πŸ˜‰, haka dai Mama ta fita ba nasara Zuby kuma wanka ta samu tayi ta kwanta, d'akin Zuby ya kwana bayan ya gargadeta sosai tare da ja mata kunne, nan ta fad'a mishi itama wayarta ta fashe, cewa yayi "ke kika fasa wayarki saboda b'acin rai, kuma kika fasa ta mutane, dan haka karki d'auka zan siyo miki tsadaddar waya ce, wacce kika fasa ita zan siyo miki."

"Kenan itama zaka siyo mata wacce na fasa ne?" ta fad'a tana kallonshi.

"Sosai kuwa, wannan ai shine adalcin da kike cewa bana yi."

A haka sukayi bacci suna nesa da juna, da safe kuma ba wayoyinsu kad'ai ya siyo ba harda kayan d'inkinsu na sallah, dana gaba d'aya sauran mutanen da yasan yana musu....


_Indai Zuby ce nasan yanzu ma za tace wani abun ne_
23/08/2019 Γ  12:51 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


_Bismmilahir-rahman-rahim_


5⃣3⃣


Da safe Umar Faruk ya bawa kowa kud'in d'inki tare da damar tafiya kai d'inki, Khairat kuma yace ta zauna ta huta tunda bata da lafiya karta wahalar masa da babynsa, saida ya fita tace "na shiga uku nikam na jawa kaina."

Zuby ta zuba ido tana so taga Khairat ta fita kai d'inki danta kira ta fad'a, ganin shiru bata da niyyar fita yasa itama ta fita kai nata, kuma harta dawo bata ga alamar Khairat ta fita ba, dole ta hak'ura ta cire rai amma dai tasan dole zata fita koba yau ba tunda uwar yawo ce.


Saida Umar Faruk ya dawo yace Khairat ta shirya ya kaita, cewa tayi ya bari har ranar data karb'i girki saisu tafi, bai mata musu ba ya barta dan tayi tunanin abinda shi baiyi tunaninshi ba.


*Bayan kwana uku* ranar litinin kuma a ranar aka tashi da azumi, a ranar Khairat tasha wahala sosai dan saida ta tafi aiki ta dawo misalin 12:00, wanka kawai tayi da sallah ta fara aiki saboda abinda take sonyi yana dayawa, duk da ta fara da wuri kuma Ruk'ayya dasu Fateema Zeinab duk sun kama mata saida ta gaji sosai, an soya an dafa an motsa haka tayi shirye shirye sosai domin taya mijinta tarban wannan watan, koda suka gama wanka kad'ai ta fito aka sha ruwa, Umar Faruk kuma dama duka mazan sai an gama sallah isha'i suke shigowa dan daga gidan ake fitar musu da wasu daga cikin kayan shan ruwan.

Tunda ya shiga d'akin yaga abubuwan ci da sha zube kala kala ya saki baki, saida ta zaunar dashi ta fara taimaka masa sannan yace "babyna wai duk ke ki kayi wannan abun, yaushe kika zama babban qwararriyar Mai girki ne?"

"Idan ka gama ci zaka san ranar."

Hannunta ya kamo ya zaunar da ita akan cinyarshi yana kallon fuskarta yace "kenan kin wahalar min da babyna ko? gaskiya ni bana son haka, daga yau ba zaki sake aikin nan ba, kibar komai su Ruk'ayya zasu yi."

A raunane ta kalleshi tace "baby nifa bana da komai, ka daina tunanin inada ciki fa, bana da komai."

Ta qarashe da shagwab'ewa, sumbatar kumatunta yayi yace "idan ke baki tabbatar ba ni na tabbatar."

"Tayaya?" ta fad'a tana kallonshi.

"Zan nuna miki anjima." ya fad'a yana kallon tarin kwanukan dake gabanshi.

Azumi ake yayin da abubuwa sukayi dama, sai dai kullum da dramar da za ayi tsakanin Zuby da Khairat, wani lokacin dramarsu tana bawa mutanen gidan dariya, danko Baba ya gani yakan dara saboda yanda Khairat ta bala'in raina qurar Zuby, a hankalce da dubara da salo take fad'a mata magana, a qarshe sai dai ta shiga d'aki tana kuka, kullum cikin waya suke da Mama tana fad'a mata abinda ke faruwa gidan, Mama kuma tana cewa tayi hak'uri watan azumi take jira ya qare suci gaba daga inda suka tsaya, ta mata alk'awarin dole wata rana gidan zai zama mallakinta, a haka kad'ai take jin sanyi a ranta, duk da qoqarin da Umar Faruk keyi akanta bata ganinshi, Allah ya sani ya saba da irin rainon Khairat hakan yasa idan yazo d'akinta yake sa ran samun irinsu, amma sam baya samun damar hakan kuma idan ya buqaci ta bashi jikinta kawai shiya juyata bata yarda, dan haka ya gama lura ita d'in mace ce da bata damu da wasanni ba, ita dai kawai kaje mata lokaci d'aya, abin haushi kuma da an fara haqar rijiyar sai tace ta gaji ko gaba d'aya ba'a haqa ba, zuwa yanzu kam badan haqqinta ne ba daya daina kusantarta , tunda dama ba wani abu yake jiba (πŸ˜‚ a dauri kashi ko a b'ata igiya), ita kanta idan ta zauna tana jinjinawa qoqarinshi, matsalar d'aya shine tana ganin kamar yafi nunawa Khairat soyayya, alhalin Khairat ko bai tab'a jikinta ba ita zata kai ga jikinshi, hakan yasa take ganin kamar yafi sonta ne.

*Kwana sha biyar* da fara azumi Papa yayi aike gidan, mota guda aka aiko ta dinga sauke kayan abinci babu abinda babu, bugu da qari harda shaddodi da atamfofi, saida aka gama shigowa dasu kuma driver ya ciro enveloppe ya bawa Mama yace abawa malam inji mai girma baban Khairat, godiya dai kan anshata kuma shima yaji tukuici sosai, Khairat ma na d'aki bata san me ake ba, tana can tunanin bayin Allah da take taimakawa ya dameta, bata san a wane hali suke ba yanzun, gashi yanzu mahaifin nata na mata wuyar samu ko a waya saboda waya da harkoki suka masa, sai lokacin Fateema ta shigo ta kirata, fita tayi taga kayan ta tayasu murna.


*A gurguje fan's*


Haka suke tafiyar wa rayuwar, idan yana d'akin Khairat yana farin ciki, idan yana d'akin Zuby qorafi da fad'a suke takura masa, haka kuma har yanzu zaman na Khairat da Zuby ba dad'i, yayin da Khairat keta qunsawa Zuby baqin ciki kala kala, kullum da sabon tuggun da take zuwa mata dashi, kuma har yanzu sun kasa samun nasara a kanta saboda sau d'aya ta fita taje gida wajensu Papa tare da Umar Faruk, har yanzu bata sake fita ba har Umar Faruk d'in kanshi yana fad'in taje takai d'inkinta amma tak'i takai, kuma tak'i tafiya ne saboda tana da d'inkin da zata iya sakawa ranar sallah, gashi kuma Zuby har yanzu ta kasa sakewa da Umar Faruk kamar ba mijinta ba, (mutan da).

Alhamdulillah rayuwa sauyawa take, Umar Faruk alert kawai yake ji hankali kwance, ga kuma albashin aikinshi shima yana samu, da wannan yanzun haka ya fara qoqarin kafa kanshi ta hanyar kama wani babban shago yana zuba takalma da jakunkuna wanda ake bugawa a wannan compagnie dana Khairat, duk da dai burinshi shine shima ya samu nashi ma'aikatar da zai fara buga nashi takalmin, komai na tafiya daidai saboda yana samun albashi mai tsoka sosai, da wannan arzik'in Umar Faruk ya fara bunqasa.

*RANAR JAJIBIR*

Saniya Umar Faruk ya yanka ya rabawa masara qarfi, bayan ya wadatan gidan da kajiπŸ˜‹da zabi, bayan sallah la'asar ya shiga d'akin Khairat ya samu tana kuka abinda ya jima bai gani ba a tare da ita, bayan rarrashinta da yayi ya tambayi me yake faruwa, cikin muryar kuka ta fara magana "Faruk bansan ya zanyi ba, bansan me nawa Papa ba ya hanani samun kud'i tako ina, Faruk ina jin kunyar su Mama saboda na kasa musu komai a bikin sallah, akwai mutane da dama wanda nice ke taimaka musu a wannan lokacin, nasan wasu zasu je gida nemana su samu bana nan, wasu kuma kirana a waya amma kunya ta kasa na d'auka dan babu abinda zan iya yi musu, dan Allah kaje ka bawa Papa hak'uri ka fad'a mishi ya taimakawa duk mutanen da yasan ina taimakawa, wallahi bana jin dad'i."

Rumgumeta yayi jikinshi yace "yanzu akan haka kike zubar min da hawayenki? nifa na tabbatar babu abinda kika yiwa Papa, wataqila wani horo ne yake so ya miki, amma karki damu zan bashi hak'uri insha Allah, yanzu ki fad'a min nawa zai isheki biyan duk buqatun nan da kika zayyana?"

Girgiza kai tayi tace "a'a Faruk, ka barshi kawai, ba zan yarda ka tauyeni ba akan me zan yarda ka tauye wata, da ni kad'ai gareka zan iya fad'a maka haka tun tuni, kuma kud'i ne masu yawan gaske dani kaina bansan nawa nake kashewa ba a kowane wata, ka barshi kawai."

"Kenan har yanzu bamu zaman d'ayan da komai nawa naki ne, kuma komai naki nawa ne?"

"Ba haka nake nufi ba, amma dai..."

"Amma me? dan haka dole ki fad'a min."

"Wallahi ni ban sani ba, kawai ka barshi kamar yanda na fad'a maka, zanfi jin dad'i idan ka gano min laifin da nawa Papa."

Tabbatarwa da yayi ba zata fad'a ba yasa ya tashi ya bud'a wradrob d'inshi ya d'auko daurin kud'i yazo ya mik'a mata, kallonshi tayi ta fara girgiza kai hakan yasa ya d'aure fuska yace "ranki fa zai b'ace."

Turo baki tayi gaba ba tare data karb'a ba, d'aga hannu yayi kamar zai mazgeta yana fad'in "zan gabjeki wallahi."

Da sauri taja baya tana fizgo kud'in daga hannunshi, "nifa wallahi bana ssss.." bata qarasa ba Yusuf ya shigo d'akin da sallama cikin murya irinta yara, amsawa sukayi Umar Faruk ya d'aukeshi yana fad'in "babban mutum ya dai, ya azumin?"

Baiko kulashi ba sai Khairat da yake kallo yana fad'in "aunty Mama na ciyanki."

Cikin dariya ta aje kud'in hannunta akan gado ta tara hannu ta amsheshi duk da ba qarami bane tana fad'in "Mama ke kirana?"

"Eh." ya fad'a, hanyar fita ta nufa tana fad'in "to muje."

Umar Faruk ma bayansu yabi shima, suna fita suka samu Papa ne yanzu ma yayi aike, naman jajibir ne mai tarin waya da kuma kud'in cefane na sallah, yaron da aka aikone ya kalli Khairat ya bata enveloppe biyu yace "Alhaji ne yace abaki keda yar uwarki."

Bata tankasa ba harya fita su Umar Faruk yabi bayanshi dan bashi tukuici, kallon enveloppe d'in tayi taga d'aya sunanta ne a baya da signature d'in mahaifinta, d'aya kuma sunan Zuby ne nanma da sa hannun Papa, tasan akwai dalilin da yasa ya saka suna, ba kuma zai wuce adadin kud'in ne ya banbanta ba shi yasa ya raba musu, da Yusuf a jikinta ta qarasa inda su Zuby ke aiki ita dasu Saratu ta mik'a mata ba tare data mata magana ba, a wulaqance ta kalleta tace,

"Miye wannan d'in?"

Itama a daqile tace "ki karb'a mana saiki duba ki gani."

Saida taja tsaki ta karb'a tana kallon sunan da aka rubuta, kallonta tayi tace "wai miye wannan iskancin?"

A hassale Khairat tace "ba iskanci bane, mahaifina ne yace a baki, kuma na tabbata yayi hakane saboda yana kallonki a matsayin 'yarsa kamar ni."

Wani tsaki tayi kafin tayi dariya irinta daba tace "kiji wani rainin hankali, to an fad'a miki bana da hankali ne ko kuma sakara ce ni? to bari kiji wallahi asirinku ba zaiyi tasiri a kaina ba, kuma koba komai Allah ya kiyayeni naci kud"'in haram kud'in da bansan ta wace hanya aka samesu ba."

Muryar Umar Faruk ce ta katsesu yana fad'in "waike me yasa baki da hankali ne, le kullum inba tsokano abinda za ayi tashin hankali ki kayi ba hankalinki baya kwantawa, gidan nan sai kace ni kad'ai ne mai mata kullum a masifa nake kuma duk saboda ke, ko kad'an ke baki d'auki iyaye a wata tsiya ba shi yasa baka jin kunyar aibata na kowa, to wallahi na gaji da wannan iskancin naki, nakai maqura ta qarshe dan haka ba zan sake yarda ba, ya zama karo na qarshe da zan sake jin kina mata rashin kunya, ke inma banda raina mutane da ki kayi ba itace gaba dake ba a komai, amma kuma tana hak'uri dake bata miki cin kashin dake kike mata, to wallahi kashedi ne na qarshe wannan, in baki ji bari ba zaki ji a jikinki ma ba hoho ba, yar rainin hankali kawai."

Yana fad'a ya juya ya fita daga gidan, Khairat ma da yau takai maqura matsowa tayi kusan Zuby tace "ina da yaqini akan mahaifina cewa baya tab'a anfani da dukiyar daba tasa ba, sanin kowa ne da arziqinshi ya shiga siyasa, bawai yayi kud'i bane bayan ya fara siyasa, kin jima kina cin zarafina amma ina d'aga miki qafa, ki sani yau kin kaini qarshen da ba zan iya hak'ura ba, ya zama dole na nuna miki kuskurenki Zubeida, dole ki gane baki da wayo a duniyar nan, wallahi saina nuna miki banbancin dake tsakanina dake, Zubeida inhar bansa kinji kunyar mutanen gari ba ki canza min suna, Zubeida

Please Login or Register in order to submit comment