Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

and lovely *Heenat*, kin tuna min da wannan had'uwar nima, ba zan tab'a manta ranar nan ba, soyayya hadin Allah ce kuma shi yake sakata a zuqatan bayinshi a sanda yaso, *My HEENAT* kin tambayi me nake so ko? to abinda *Meera* take so shine ganin kyakyawan murmushinki a koda yaushe, soyayya kuma *Meera* ta samu daga Heenat, dan haka kisha zamanki ki huta, Allahn daya had'a shine zai raba da izininshi._ 😘❀😘


_Bismmilahir-rahman-rahim_


5⃣7⃣



"Umar Faruk, mun maka farin sani shi yasa muka shirya da kyau kafin shiga jikin matarka."

Suna fad'a da iya k'arfi aka fizgi Khairat aka bugata ga bango, take ta fad'i gurin kamar babu rai, da sauri Umar Faruk yayi kanta ya rik'eta, "Khairat, Khairat."

D'aukarta yayi ya aje kan gadon ya d'auko cup d'in ruwa ya shafa mata, numfashi ta sauke da nauyi amma bata bud'a ido ba, ajiyar zuciya ya sauke saboda ganin tana sauke numfashi a hankali, a zuciyarshi kuma yana tunanin hanyar da zaibi wajen magance matsalar, danya lura suna son cutar da Khairat ne kawai da abinda ke cikinta, duk da ance babu shi amma bai yarda ba, yana shafar kanta yana kallon fuskarta data fita tayi fiyau da ita duk ta rame ta fice, qwaqwasa qofa yaji yasa ya tashi ya fita, Mama ce tsaye tace "Umar Faruk har yanzu jikin nata?"

Saida ya juya ya kalleta daga qofar d'akin yace "har yanzu Mama,amma ta samu bacci yanzu."

"To kazo mahaifinka nasan ganinka."

"To Mama." ya fad'a yana saka takalmanshi.

D'akin malam suka shiga da sallama suka zauna a tare, Baba ne yace "Umar Faruk mahaifiyarka ta fad'a min abinda ya faru yau d'in nan, nayi mamaki sosai tare da jimami, amma abinda nake so ka sani shine, babu abinda ya samu cikinta, kuma yana nan cikin qoshin lafiya kuma da yardar Allah za'a haifeshi/ta, dan haka ba sai na fad'a maka abinda za kayi ba, nasan kasan abinda ya dace da ita, amma idan kaga akwai cutarwa ga lafiyarta ko abinda ke cikinta saika sassauta kabi a hankali, kaji ko?"

"Naji Baba, kuma nima abinda na fahimta kenan, kamar suna sob cutar da ita ne saboda yanda suka bar jikinta a yanzun, amma dai insha Allah basu fi k'arfin addu'a ba."

"Allah ya kyauta." cewar Mama da Baba.

Kallon Mama yayi kallo na tsanake yace "komai muqaddari ne daga Allah, ciwon Khairat kuma yana da sila kamar yanda ko mutuwa akance ga sila wani lokacin, zuciyar Khairat fara ce Mama bata qullatar kowa, amma tanti ta kasa fahimtar hakan har tana so taga ta cutar da ita, bai zama lallai na iya yin shiru ba Mama, amma dai zan qoqarta naga mun rabu da lafiya da shed'anun aljanu da kuma shad'anun mutanen, amma wallahi sukayi taurin kai, to Mama sai dai kiyi hak'uri, dan gaskiya zansa su koma kan wanda ya turosu, ba wai zargin tanti nake ba a'a tabbas ne nake da itace." duk da dai ranshi a b'ace yake, amma baya jin zai iya cutar da yayar mahaifiyarshi, kawai ya fad'i haka dan ya bada tsoro.

Baba ne yace "Umar Faruk, ina kasan haka, me yasa kace itace?"

Baba ya kalla yace "da bakinta kuma a gabana ta furta kalamai marasa dad'i akan Khairat, ban damu bane saboda nasan gidan nan na cikin kariyar ubangiji, kuma Khairat d'in yanzu bata da bace, kullumtana cikin karatu ne da kuma ibada, saboda ta gyara halayenta marasa kyau domin son rabauta, kuma tun ranar da tanti tayi wannan maganar ban tab'a kwanciya bacci ba ba tare dana tofa mata addu'ar bacci ba da kaina, koda kuwa ba'a d'akinta ba nake, hakan daya faru ya sake tabbatar min lallai sihiri gaskiya ne kuma zai iya shafar kowa idan Allah yaso hakan."

Ajiyar zuciya Mama ta sauke wacce ke sairaranshi gabanta na fad'uwa, shirun da iyayen sukayi yasa ya tashi yana fad'in "saida safenku iyayena."

D'akin Zuby ya fara shiga ya sameta kwance tun d'aurin qirjin daya sameta dashi da rana, tuhumammen kallon da yake mata yasa ta tashi zaune tana kallonshi itama, ita ba tace komai ba shima kuma baiyi magana har tsawon minti biyu, da qyar ya iya cewa "kin samu labarin abinda ke damun 'yar uwarki?"

Cike da rashin kulawa tace " a'a, meya sameta?"

Gyara tsayuwa yayi yace "da kyau tunda baki sani ba, na d'auka kina da labari ne danna miki hannunki mai sanda, amma duk da haka ina fad'a miki da kuji tsoron Allah Zubeida, kusan zaku koma gareshi kuma wallahi zai mumu hisabi, baya kuma yafe haqqin wani akan wani bare ka samu alfarma, lahirar nan da kika gani mai kad'aita Allah ne kad'ai ke shigarta ba wanda yake neman biyan buqata ga waninsa ba, kuma nine Umar Faruk kin samu, bai kamata a cutar da wani ba saboda kawai ana so a rabamu ko *d'aukar fansa* a kanshi."

Matsawa yayi kusanta ya sunkuya yasa hannu ya shafi cikinta yana kallon idonta yace "ina fatan yana lafiya, kinci abinci?"

Kai kawai ta d'aga masa, d'agawa yayi ya shafi kumatunta ya manna mata sumba a d'aya kumatun yace "ki kula da kanki, saida safe."

Fita yayi kai tsaye ya nufi d'akin Khairat, yana so ko da Zuby nada laifi ya lallab'ata saboda cikin dake jikinta, kuma koba komai addini ya nuna ka rabu da mace da kyautatawa, tunda baya da hujja akan lallai da hannunta ba zai matsa mata ba, kayanshi ya cire yayi wanka yazo ya shirya duk Khairat na bacci, saida ya zauna ya d'auki littafi mai tsarki zai fara karatu kawai ta farka tana dafe qeyarta data bugu sosai, fashewa tayi da kuka tana shirin sauka daga kan gadon, tasowa yayi ya hau gadon yana so ya lallab'ata, kuka take sosai tana fad'in ya kaita gida ita ba zata zauna nan ba.

Yayi rarrashin duniya amma tak'i shiru kuma gashi dare yayi, duk iyayen gidan babu wanda ya ritsa saboda rigamar da Khairat keyi, saida suka ga abin bana qarewa bane suka samu suka kwanta, amma babu inda suka kai aka kira sallah asuba, rana ta farko a tarihin rayuwar Umar Faruk da yayi sallah a gida, hakan yasa yaji abin ba kan gado saboda rashin sabo, yana gamawa yace mata ta tashi tayi sallah idan ta gama ta shirya ya kaita gidan, tashi tayi ta shiga douche ta kama ruwa ta d'auro alwala, fitowa tayi daf da zata shiga d'aki taji anyi sama da ita an buga qasa, qara ta saki wanda tasa Umar Faruk fitowa da gudu gudu, taimaka mata yayi suka shiga ciki, ganin yanda take dafe bayanta yasa yace "baki ji ciwo ba ko?"

A marairaice ta kalleshi tace "akwai zafi mana, bafa santsi ne ya kayar dani ba, amma dai ina mamaki."

"Karki damu kinji, je kiyi sallah ki shirya muje."

Hijabi tasa a matuqar galabaice saboda babu komai a cikinta, da qyar ta gama sallah ta tashi zata shiga wanka, ganin yanda take yasa Umar Faruk zaunar da ita ya d'auko fresh milk ya bata, ji tayi har yawunta na tsinkewa tana so tasha, da azama ta daga ta fara sha ba qaqqautawa, saida ta gama ta tashi Umar Faruk yace "muje na miki wankan."

Tare suka shiga ya fara mata wankan, suna cikin yi sai kuwa amai, saida ta amaye fresh milk d'in kad'ai aman ya sarara mata, haka suka fito kafin ya shiryata ya sake d'auko wata madarar da ayaba da kankana ya bata, da qyar taci ayaba guda biyu bata sake cin wani abu ba bayan ita.

Fitowa sukayi ya shiga da ita d'akin Mama, da sallama ta shiga ta zauna tana d'ora kanta a qafar Mama tace "ina kwana Mama."

"Lafiya lau Khairat, antashi lafiya?"

"Lafiya lau Mama."

"Ya jikin naki da dama?"

Saida ta tashi zaune tace "da dama Mama."

Ruk'ayya ce ta sallamo ta aje kwano gaban Mama tana fad'in "auntyna kin tashi lafiya?"

"Lafiya lau Ruk'ayya." ta fad'a tana bud'a kwanon, ganin d'umamen tuwo sai qamshin man shanu ke tashi ya birgeta sosai, kallon Mama tayi tace "Mama ina so naci amma."

"Indai kina so kici yata kici kawai, idan kina sawa ranki komai ki kaci zakiyi amai to da kinci kuwa sai kinyi."

Kallon Umar Faruk tayi tace "baby bara na d'anci kad'an saimu tafi."

Shi kam farin cikine ya kamashi tare da mamakin wacce ke kuka sai an kaita gida, hannu tasa tana d'an qwalbatar tuwon tana kaiwa baki, ji take kamar taci ta qoshi amma yanzu haka zuciyarta ce ke tashi, cire hannu tayi suna kallonta harta wanke ta dawo d'akin ta kalli Ruk'ayya tace "ki bani dabino dan Allah."

Ledar dabino Ruk'ayya ta bud'e ta ciko hannu ta bata, karb'a tayi tana fad'in "ke qaro min malama."

Da dariya Ruk'ayya ta qaro mata sannan sukawa Mama sallama suka tafi, tafiya suke a hanya tanata gwaigwayar dabinonta harta fara d'an b'ata rai saboda aman dake taso mata, hannunshi ta rik'e da yake tuqi ta kalleshi, alama kawai ta mishi ya tsaya, kai ya girgiza mata shima ba tare daya tsaya ba, tafiya suke ba mai magana har wayarshi tayi qara.

D'agawa yayi suka gama hirarsu duk tana jinshi, saida ya gama ta kalleshi tace "akan me kake magana?"

Ajiyar zuciya yayi ya kalleta yace "har yanzu muna kan magana ne bamu tsayar ba, dan haka ban fad'awa kowa ba."

Kallon titi yayi yace "ina sone na tashi nawa compagnie nima."

Murmushi tayi tace "naji dad'i kuma na maka murna, Allah ya sanya alkairi."

"Ameen, yanzu ciniki ya fad'a, biya kawai zanyi kafin muje mataki na gaba."

Da wannan tattaunawar suka isa gida, har ciki ya shiga suka gaisa sannan ya musu sallama ya tafi, kwance tayi akan kujera Mamie tayi saurin cewa "kije d'aki mana ki kwanta za kifi sakewa."

Zaune ta tashi tana yamutsar fuska, Mammie ce tace "me kike so a dafa miki kafin ki tashi?"

A yamutse tace "dambu zanci."

"An gama shalelen Papa." cewar Mamie.

Tashi tayi zata nufi d'akin Mamie kawai qafafunta suka kasa d'aukarta, zubewa tayi qasa kamar wasu kayan wanki, Mamie ce ta tashi ta kamata tana salati, zaunar da ita tayi tana kallonta da mamaki, matsa qafafunta tayi tace "Mamie, kamar ba qafafuna ba, wallahi ciwo suke min sosai."

Kallon juna sukayi da Mammie, kafin kace kwabo kuma sai ciwon ciki mai tsananin gaske, Papa suka kira yazo gida yaga halin da take ciki, tausayi ta bashi sosai harya kira likita yace yazo ya sameshi gida, koda likita ma yazo shi cewa yayi baiga wani abu dake damunta ba, amma su kaita asibiti a duba lafiyar d'an cikin nata, Mamie ce tace ya tafi kawai sunji, yana tafiya ta kira Umar Faruk yazo, ruwa suka bashi a cup a mata addu'a, zai bata tasha tace ai ina bai isa ba, saida su Mamie suka kama mish suka d'ura mata ruwan tasha sannan taji sassaucin ciwon kamar an cire mata qaya, daga nan kuma bacci ya d'auketa.


****************

Tunda Zuby taji fitarsu ta kira Mama duk da yanzu ba wani sosai suke waya ba, kira ta dinga yi amma ba'a d'agawa harta gaji ta daina, amma maganganun Umar Faruk na mata yawo har yanzu a qwaqwalwa, tana haka Ruk'ayya ta kawo mata nata abincin, gyara zama tayi ta handami abinta ta qoshi sannan ta d'auki kayan karatunta ta fara tilawa dan suna daf da fara jarabawa kwanaki suka rage musu.


******************


Koda yaje daukarta ma ya sameta kwance ranga ranga, Mammie na gefenta tana share qwalla, zaune yayi yana tambayar "Hajia lafiya kike kuka, meya faru ne?"

Cikin kuka Mammie tace "wannan wane irin laulayi ne yarinyar nan take, tunda ka kawota gidan nan har yanzu wallahi ko ruwa tak'i sha idan ba ruwan addu'a daka bata ba, taya mutum zai rayu to a haka bare d'an cikinshi, gaskiya nidai abin ya fara bani tsoro."

"Hajia dan Allah kuyi hak'uri ku daina kukan nan, insha Allah babu abinda zai faru sai alkairi, ku tayi mata addu'a kawai ita take buqata daga gareku."


Ganin tana bacci yasa yace "ni zan tafi Hajia, tunda ta samu bacci ba sai an tasheta ba."

"To shikenan, saida safe."

A haka ya tafi gida rai ba dad'i ya fad'awa su Mama abinda ake ciki, d'akin Zuby dole ya kwanta amma baiyi bacci ba, yana cikin tsayuwar dare Papa ya kira wayarshi......


😭😭😭😭

Yana d'auka Papa yace "Umar Faruk jikin yarinyar nan fa yayi tsanani, koda wani abinda da kuke bata ne?"

"Subhanallah, Papa ku d'ora mata wayar a kunne."

D'ora mata yayi shi kuma cikin taushin murya yace " Khairat, me yake damunki?"

Cikin matsannancin kuka tace "Faruk mutuwa zanyi, mutuwa zanyi Faruk, ciwo nake ji tako ina a jikina, ba zan iya cewa ga abinda yake damuna ba, amma dai bana jin dad'i ko kad'an, Faruk ka taimaka min dan Allah bana son cikin nan wallahi, dan Allah ka taimaka ka cire minshi kafin na mutu."

Saida taji numfashinshi cikin kunnenta, a hankali ya lumshe idonshi daga inda yake tsaye, wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mishi, tsantsar tausayinta ne ya lullub'eshi, saida ya saita nutsuwarshi yace "haba baby, ya kike fad'an haka? komai yayi farko yana da qarshe, kowace uwa da kika gani a duniya da kalar nata wahalar da tasha kafin ta haifi abinda ke cikinta, kema kamar hakane Khairat, ki sani wannan d'anki ne ko 'yarki kike d'auke dashi, ki daina cewa ba kya sonshi hakan zai iya tasiri akan abinda ke cikinki koda yazo duniya ne, yanzu kinsan me nake so dake?"

"Ina jinki Faruk." ta fad'a cikin kuka da sake kama cikinta sosai tana matsewa.

"Ina so ki sake neman gafarar iyayenki, wala'Allah ki samu sassauci, wataqila mahaifiyarki tasha fiye da wahalar da yanzu kike sha, sannan karki bari anbaton ubangiji ya fita daga bakinki inba bacci kike ba, kinji ko baby?"

Sassauta kukanta kawai tayi ba tare da tace komai ba, d'orawa yayi da "kinsan me?"

"A'a." ta fad'a cikin muryar kuka.

Saida ya kalli Zuby dake bacci hankali kwance yace "duk abinda kika haifa na bakishi kyauta, kisa a ranki d'anki ne ba nawa ba, kece zaki zab'ar mishi sunan da kike so, ni nawa kawai hidima ne gareshi da kuma ke."

Duk da bala'in ciwon da take ji bai hanata jin dad'i ba har cikin zuciyarta, su Papa dake tsaye mamaki ne ya mamayesu ganin murmushin da tayi, cikin ikon Allah sauqi saiya samu hakan yasa da Umar Faruk yaji bacci na shirin d'aukarta sai yace ta rufe ido zai mata addu'a, tun tana jin sautin muryarshi yana mata addu'a har bacci ya d'auketa ba tare daya daina ba, ganin bacci ya d'auketa yasa Papa d'auke wayar a kunnenta ya mayar a nashi, Papa ne yace

"Ikon Allah Umar Faruk, kaga yarinyar nan tayi bacci, meka mata ne haka?"

Murmushi yayi yace "ba komai Papa, sai dai Papa dan Allah kar kuyi sake da addu'a musamman idan tana irin haka, sannan na fad'a mata ta sake jaddada neman afuwarku, hakan nada anfani musamman ma Mama, dan zai iya yiwuwa tasha wahala fiye da wacce take sha yanzu."

Papa kam kallon Mamie yayi yace "bansan komai ba game da wannan lokacin Umar Faruk, dan haka ba zan iya cewa komai ba, kuma insha Allah zamuta yi mata addu'a."

"Shikenan Papa saida safenku."

"Allah sadamu da alkairinsa."

*Asuba ta gari*


Ko abinci bai tsaya ci ba suka fita tare da Zuby ya ajeta makaranta, daga nan kuma wucewa yayi wajen da zasu had'u da mutanen da zabawa kudin tsohon store d'in daya siya danya tayar dashi, suna gamawa ya wuce gidansu Khairat, zazzab'in data tashi dashi shi kanshi saida ya bashi tsoro saboda zafin jikinta, amma saboda dauriya data ganshi haka ta tashi zaune tana gaisheshi, ya jima gidan yana hira da ita harya tashi tafiya, koda ya mata maganar yaushe zaizo ya d'auketa su koma gida, take yanayinta ya canza dan haka kawai ya rabu da ita......


Daga nan kuma yaje wata harkar, koda lokacin tashinsu Zuby yayi ya wuce ya d'aukota, suna isa gida koda suka shiga suka samu tanti zaune da alama zuwan Zuby take jira, kallonta Umar Faruk keyi saboda ganin wata sabuwar shiga ga tantin , duk da dama ba ma'abociyar saka hijabi bace, amma kuma siket d'in daya gani a jikinta da kwalliya a fuskarta ne yafi d'aga mishi hankali, kamar yanda ya samu suma mutanen gidan mamakin da sukeyi kenan, d'aki Zuby ta bud'a tanti tabi bayanta suka shiga ko magana, shi kuma juyawa ma yayi ya bar gidan saboda b'acin rai.....
29/08/2019 Γ  14:33 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


_Bismmilahir-rahman-rahim_


5⃣8⃣


Tana kallon Zuby harta cire kayan jikinta ta d'auka za tayi wanka ne sai taga tasa wasu kayan, tab'e baki tayi ta kawar da kanta tana kallon d'akin, saida ta gama ta zauna kusan Mama, Ruk'ayya ce ta sallamo ta shigo ta aje mata abincinta dan yanzu sun daina saboda rainon ciki, saida ta fita Mama tace "naga kiranki jiya, meya faru?"

Kallon Mama tayi da kyau kafin tace "Mama wannan sabuwar shigar fa, da quruciya ba kiyi ba sai yanzu kawai saboda ki zubar mana da mutunci, waime kike so ki zamane Mama?"

"Ke, karki fad'a min maganar banza, ki fad'a min abinda kika kirani jiya kawai na tambaya, kece zaki fad'a min abinda ya dace."


Kallon qofar d'akin tayi sannan ta kalli Mama tace "Mama, me ki kawa Khairat?"

"Mtssss, dama akan haka kika kirani, to me tace miki na mata?"

"Ba ita tace min kin mata wani abu ba, amma dai naga kwanan nan tana wahala sosai bata da lafiya, nasan kuma ba zai wuce da hannunki ba."

Gyara zama Mama tayi tace "aina fad'a musu ba zan bari haka ba saina d'auki fansa, kuma yanzu ma ta fara gani, dan yanzu haka nima inada mutane kamar yanda take taqama tana dasu, kuma yanzu haka daga nan zan wuce wajen wata matace da akace tsohuwar karuwar ubanta ce, zanje mu cika aikinmu na gaba."

"Mama, Mama, wallahi babu ruwana idan ki kayi abinda za'a qara d'aureki, nidai in dan saboda ni kike haka to na yafe bana so, ki barni zan zauna da ita a haka, kawai ki cire hannu a al'amuran gidan nan dan Allah Mama."

Kallonta tayi tace "tun kafin ki mallaki hankalinki nake shiga na fita akan lamarin aurenki da Umar Faruk, daf da kaiwa ga gaci wallahi ba zan zubar da makamaina ba, dole na d'auki fansa tare da mallaka miki Umar Faruk a hannunki."

Kafin tayi magana ta d'auki jakarta ta bud'a ta fito da qullin magani ta bata tace "karb'i nan, a abinci zaki zuba mishi yaci, wannan kuma kije qofar d'akin waccen hatsabibiyar ki zuba mata, ba zata sake sha'awar qara koda minti d'aya ba a gidan nan."

Rumgume hannaye tayi tace "bana so Mama ki koma da kayanki, kuma meya rage a yanzun tunda gida ta kwana jiya."

Wata yar dariya tayi tace "da kyau, hakan ya tabbatar min aikin malamin nan yanayi fiye da waccen na baya."

"Mama sabon malami kika samu kuma?"

"Eh yarinya, ai ban fad'a miki ba sabon malami ne wannan, kuma kinga shekaranjiya ne kad'ai na fara zuwa wajenshi, amma gashi aiki yayi."

Da kyau ta kalli Mamanta tace "wallahi Mama yah Umar ya fara zargina akan haka, dan Allah ki daina duk abinda kike ki tuba ga Allah Mama, niko a haka ma zan zauna dashi tunda ina sonshi, ina jiye miki tsoron ranar da zaki sake jin kunya akan abinda kike aikatawa Mama."

Tab'e baki tayi tace "humm, shi yasa ma na taho miki da maganin matsalar nan, idan ki kayi anfani da wannan maganin na hannunki komai zai yaye."

Ta fad'a tana bata d'aya qullin maganin, ganin tana hararanta yasa ta karb'a tana turo baki, d'ora mata tayi da " ki tabbatar kinyi aiki dasu kamar yanda na fad'a miki, idan ba haka ba ki sani, wallahi wata rana saikin zubar da hawaye, dan ina tabbatar miki hankalinshi zai koma kan wacce bata da lafiya ne, in ba kiyi sa'a bama ya tare da zama acan gidan sai dai kawai yazo ya ganki ya koma, ni kinga tafiyata ina da abinyi."

Bata jira komai ba ta wuce gyalenta najan qasa sai yan mazaunanta dake motsawa, da takaici ta bita da kallo tana jin kamar ba tayi sa'ar uwa ba, qarqashin gado ta jefa maganin ta d'auki abincinta ta fara ci.


***************


Fitarta daga nan gidan wata qawarta ta wuce, koda taje kuma suka wuce kamar yanda ta mata alk'awari, wani matsakaicin gidane sai dai yana da kyaun gaske da kuma tsari, bayan sun gaisa hamshaqiyar matar tasa aka kawo musu ruwa, qawar ta Mama wacce ake kira da *'yar fara* ce wannan hamagiyar matar ta kalleta tace " xyar fara ina jinki."

Nuna tanti tayi tace "kamar yanda na fad'a miki a waya tun kafin muzo, wannan itace matar da take neman taimakonki."

Murmushi tayi da bakinta kad'ai ya motsa kafin tace "ta fad'a min komai a waya duk abinda ya shiga tsakaninki da 'yarsa, na yarda zan taimakeki ne a zahiri saboda kin samemu tsakiya da shirye shiryen zab'e, kuma akwai wani aiki da mai neman kujerar Mani Bukar ya biyani kud'ad'e danna kai Mani Bukar qasa kamar yanda ina d'aya daga cikin wanda suka sakashi yayi sama, dan haka karki damu zuwa gobe zan gama shirya komai, kuma zakisha mamakin abinda na shirya, tabbas Khairat zata ji ba dad'i itama."

Da farin ciki tanti tace "na gode sosai Hajia da wannan taimakon, kuma insha Allah Hajia za kiji babban biya."

D'an b'ata rai matar tayi ta kalli yar fara tace "yar fara ina fatan kin fad'a mata ba'a min wasa da maganar data shafi kud'i ko?"

"Ai karki damu Hajia, na fad'a mata komai a game dake, ba za'a tab'a samun matsala ba." cewar 'yar fara.


"To yayi kyau, zaku iya tafiya." tana fad'a ta tashita shiga wani d'aki ta barsu nan, tashi sukayi Mama na yaba matar tana ji inama ta zama ita, har saida 'yar fara tace "to ai matsalar kin tsufa ne, amma badan haka ba ai zaki iya hawa network kema."

Hararanta tayi tace "karki cimin mutunci mana, me kika d'aukeni?"

"Ba komai." cewar 'yar fara.


*Mamienmu amin afuwa*πŸ‘πŸ™‡β€β™€

****************


Umar Faruk na zaune daf da Khairat yana bata magani zazzab'i tana sha, Mammie na gefen Khairat sai Mamie da Papa dake d'aya kujerar suna kallonsu, duk da dare yayi yana so yaje gida amma ganin jikin nata ba sauqi yasa ya kasa tafiya, tana shan maganin ta koma ta kwanta tana sake dunqulewa cikin bargon da Mamie ta d'auko mata, a hankali take lumshe ido alamar tana so tayi bacci, a haka har baccin yayi gaba da ita, tashi Umar Faruk yayi ya musu sallama zai fita, da k'arfi sukaga Khairat ta fad'o daga kan kujerar, a zabure ta farka itama tana kallon mutanen wajen, da sauri Umar Faruk ya qarasa wajenta ya kamata ta tashi ta koma ta zauna, fuska ba annuri yace "kalleni nan."

Kallonshi tayi ya sake had'e rai yace "wallahi ku daina wahalar da ita haka in kuna son zaman lafiya, kunga ina binku a hankaline saboda ina so mu rabu lafiya daku, tab'ata da kuke shine kuskuren da kukeyi."

Qwafa yayi ya mik'e zai nufi hanyar fita Papa yace "Umar Faruk, me yake damunta ne?"

Juyowa yayi yace "karku damu Papa, komai zaiyi daidai na baku tabbacin hakan."

Yana fad'a ya juya ya kalli Khairat, hararan sama da qasa ta masa taja dogon tsaki, fita ranshi a b'ace ba tare daya damu da abinda tayi ba, sam yau ma basuyi bacci ba ko kad'an, daga wannan ciwo sai waccen a haka suka kwana.


**************

Tunda Zuby taga shiru bai dawo ba sai ranta ya fara b'aci ta fara tunanin abinda Mama ta fad'a mata, ta kuma yarda tabbas wata rana zaice zai tare can tare da Khairat indai har ana haka tun yanzu, ganin Ruk'ayya ta kawo abincinshi ta aje kawai saita tashi ta d'auko maganin data jefa qasan gado ta duba wanda zata saka a abinci ta mayar da sauran, tsautsayi ya kawo Umar Faruk a lokacin da take zuba maganin a abinci, komawa yayi da baya ya saita kansa tare da had'e

Please Login or Register in order to submit comment