Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kima da daraja ta 'ya mace, inba haka ba babu ta yadda zaku fara min maganar aure ba tare da sanina ba.:

Wucewa tayi ta barsu nan Papa kuma ya kalli Mamie cikin b'acin rai yace "....😁
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

_Wallahi har qasan raina ina jin dad'in addu'arki sister Alawiyyah, gaskiya ke ta dabance, samun fan's irinki abin alfahari ne kuma burin kowace marubuciya, duk da soyayyar da kike nuna min bata isa ba saida kika nunawa my Heenat d'ina itama tata soyayyar, lallai muna yinki over, luv u dear.😘_


_My aunty *Aishan Umma* ina mik'a godiyata sosai a gareki, kinsa naji cewar ni mai sa'a ce a rayuwa😊 muna alfahari dake a matsayin shugabar k'ungiyarmu._


*Welcome Back my πŸ…±K.*πŸ€œπŸ€›


_Bismmilahir-rahman-rahim_


1⃣6⃣


"Wai me yasa kike wa yarinyar nan haka, akan me zaki dinga d'aga mata murya, me yasa kika cika b'acin rai ne Na'ima?"

"Au, nice ma na daga mata murya kenan? kai yanzu baka ga abinda tayi ba? wai me yasa kake hakane? Khairat fa 'yarmu ce mu muka haifeta ba ita ta haifemu ba, to akan me zata dinga tsaya gabanmu haka tana fad'a mana abinda ranta yake so?"

Tsaye ya mike yace "koma dai miye kinsan muna da laifi, kamar Khairat ace mun tsayar da maganar aurenta ba tare da saninta ba a wannan qarnin da muke ciki, kinga dole ranta ya b'ace."

D'akin Khairat d'in ya nufa yana ci gaba da mita, tundada ta shiga d'aki ta kwanta kan gado tana kuka, jin kanta na sarawa yasa tasan yanzu zai fara mata azababben ciwon daya saba, tashi tayi da nufin d'auko magani tasha amma bata kai ga wajen ba jiri ya d'ebeta ya yadda, rintsegudu ido tayi ta dafe kanta sosai tana fad'in "wayyo Allah kaina, kaina zai fashe, kaina Papa ciwo yake, dan Allah kazo kai kad'ai ke sona, Papa kaina zai fashe, wayyo, ahhhh, wash."

Papa na shigowa ya ganta kwance a qasa, da gudu ya k'arasa wajenta yana tambayar "shalele lafiya, meya faru, kanne ke ciwo halan?"

Kamata yayi ta tashi ya taimakata ta zauna akan gado yana fad'in "wallahi shi yasa bana qaunar abinda zai b'ata miki rai saboda irin haka."

Da sauri ya nufi wajen maganinta ya d'auko ya kawo mata tare da ruwa ya taimaka mata tasha, kwantar da ita yayi yana fad'in "kwanta ki huta kinji."

Kai ta girgiza har yanzu hannunta na saman kanta tana matsewa tace "dan Allah Papa ka d'aure min kaina fashewa zaiyi, ka taimaka ka d'aure min dan Allah."

Ya tashi kenan zai bud'a kayanta Mamie ta shigo d'akin, wata harara ya dalla mata dan ranshi ya b'ace sosai, kayan ya bud'a ya d'auko wani qaramin gyalenta ya dawo ya zauna kusa da ita ya d'aure mata kan sosai, sake cewa tayi ya d'aure mata sosai, shi kuma yana ganin ya d'aureshi qwarai haka ya sake tamke mata kan, duk da haka ba sauk'i Mamie dake tsaye tana kallon yanda jijiyoyin kanta suka fito sai harbawa suke kai kasan ba qaramar azaba take ji ba, cikin muryar kuka tace "dan Allah Alhaji ko zamu fita da yarinyar nan waje ne, kasan fa babu kyau ciwon kai ga 'ya mace? gaskiya ni ina jin tsoro."

Wata tsawa Papa ya daka mata ba tare da saninshi ba "dallah rufe min baki, duk waya janyo yanzu in ba ke ba, ke wai har abada ba zaki iya mu'amulantar yarinya da kyakywar mu'amula ba, sai hushi kawai na banza da wofi, to idan kika kasheta ai kinga saiki huta, kinsan dai ba zaki sake haihuwa ba har abada dan mahaifar ma baki da ita, ni kuma wallahi aure zanyi da ba zan zauna ba magaji ba."

Kasa hak'ura tayi da abinda ya fad'a saida tace " to kayi auren mana saime? nace saime idan kayi aure? namiji goma aiba uba goma bane, wato ka lalata min rayuwa yanzu kuma burinka kenan na rasa 'yar tawa guda d'aya kai kuma kayi aure, to wallahi baka isa ba, yanda ka b'ata min rayuwa kaima a haka zaka tabbata ba d'a ba jika."

Tsaye ya mike "ni kike fad'awa haka Na'ima, waike me yasa baki da kunya? yanzu a gaban 'yarki kike fad'a min haka? kenan tarbiya ce kike so ta d'auka a haka?"

"Kai tarbiyarce kake so ta d'auka daka fad'a min abinda ka fad'a min, kasan kaine silar lalacewar mahaifata, to miye na fad'a min wai zan kashe 'yata?"

"Dallah ni kimin shiru a wajen nan kona tattakaki."

"Naki nayi shiru, kayi abinda za kayi mana, an fad'a maka tsoronka nake ji? aini dama nasan ba tuban gaske za kayi ba, kawai dai parpaganda ce irin taku 'yan siyasa."

Tatsssss, Papa ya d'auketa da gigitancen mari yana fad'in "ke har kin isa kici mutunci na, wallahi bari gani ina d'aga miki qafa, ruwane suka daki babban zakara wallahi, idan kuma kinfi son in dawo Mani na nada to mu zuba dani dake."

Dauke hannu tayi daga kunci tace "ka dawo Mani mana dama ai baka canza ba, kuma da kake maganar mutunci, kai har mutuncine da kai da za'a ci? kuma wallahi ka sake dukana ramawa zanyi, tunda ni ba jaka bace."

Nunata yayi da hannu yace "kici albarkacin 'yarki dake kwance a wurin n...." bai k'arasa ba saboda ganin Khairat zaune tana kallonsu kamar ba mai ciwon kan nan ba.

Kunya ce ta tureshi dan baiji dad'in abinda ya faru ba ko kad'an, kawai ta kaishi bangone, zai zauna a kusa da ita kenan ta fashe da kuka tace "karka zauna, dan Allah ku fitar min daga d'aki, ku barni zanci gaba da ratuwata a haka, ba zaku tab'a sauyawa ba saboda ya riga daya zama jikinku, ba zan iya zama daku na minti d'aya ba ba tare da kun samu sab'ani ba, ku fita dan Allah, zan kula da kaina ko bakwa nan."

Papa ne ya sake marairaicewa yace "shalele ki saurare ni kiji."

"Bana son jin komai, ku fita kawai."

Jiki a sanyaye suka fita, amma tana jinsu ko nisa ba suyi ba Papa ya fara tuhumar Mamie akan ita ta janyo komai, haka suka jima suna wannan fad'an harya fita ya bar gidan, Khairat kam turmutsutsu ta dinga yi saman gado tana tusa kanta pillow saboda rad'ad'in da yake mata.


*Wallahi yan uwa akwai iyayen da basa iya rik'e b'acin ransu, ko a ina ko a gaban waye idan ransu ya b'ace sai suyi musayar yawu, wallahi iyaye muji tsoron Allah, dan dole zamu tsaya a gabansa kuma mu amsatambayoyi.*

*Yana da kyau ace ke uwa mace kina da hak'uri fiye dana namiji , domin kece mai tarbiyar yara maza da mata, idan ranshi ya b'ace ke kiyi hak'uri ki taushi naki b'acin ran, yara tun suna qanana suna lura da zamantakewar iyayensu kuma hakan nada tasiri a rayuwarsu sosai, wannan d'an qaramin jan hankali ne, Allah ya bamu ikon kiyayewa, ameen.*


*****************

Umar Faruk ne da Zuby suke waya, amma shirunshi yayi yawa ba kamar kullum ba, tunanin Khairat da lokacin data rik'e hannunshi kawai yake yi, ga kuma tuna abinda Ishaq ya fad'a, a hankali ya saki wani tattausan murmushi daya bayyanar da kywunshi, sannu sannu ya bud'a bakinshi ya furta kalmar " *shalele*".

Wani murmushin ya koma saki, muryar Zuby ce ta katseshi da tace "yau kuma sabon sunan na samu?"

Dawowa yayi tunaninshi, cikin rashin gaskiya yace "e..e...eh mana."

Shi kuma harga Allah sunan daya ji Papa y kira Khairat dashi ne ya maimaita, cikin sauri yace "am kina ji? zan sake kiranki."

Yana fad'a ya kashe wayar tare da fad'awa duniyar tunani, ya jima a wannan halin kafin ya fara magana da kanshi "haba Umar Faruk, ka dawo hankalinka mana, wannan fa bata dace kai ba ko kad'an, me yasa kake damun kanka a kanta? ko ka manta wacece ita? kai da ita fa kamar mota da jirgin sama ne."

"Kai kana son mace mai kunya, ita kuma bata da kunya, kai kana son mace mai kamun kai da aji, ita kuma sai ajin amma ba kamun kai, kana son samun mace wacce zata kula maka da mutuncinta ko bayan idonka, amma ita ko a gaban idonka ma zata zubar maka dashi bare kuma bayan idonka, kana son mace mai ilimin addini, amma baka da tabbacin sahihancin addininta, kai namijine mai kishi, ita kuma ta riga da tayi tallar surar jikinta a waje kowa ya gani, bugu da qari baka da tabbacin ita d'in saliha ce tun ma kafin a mata fyad'e, dan haka ka fita a harkarta daga tunaninta ma haka."


πŸ€Έβ€β™‚πŸ€Έβ€β™‚πŸ€Έβ€β™‚πŸ€Έβ€β™‚πŸ€Έβ€β™‚πŸ€Έβ€β™‚πŸ€Έβ€β™‚


Sai dare ciwon kan ya lafa mata amma kuma bata fito ko falo ba bare farfajiyar gidan, tana d'aki zamanta tana sauraran waqoqinta, Papa ma yayi yayi ta fito taci abinci amma tak'i, dole sai nan aka kawo mata shima bata ci wani mai yawa ba sosai kamar yanda ta saba, daga nan kuma bacci ya d'auketa.

*Washe gari* gidan an tashi anata qoqarin shirin tarbar bak'i, Khairat na bacci Papa yasa Mamie ta tasheta, dan dole tasan halin da ake ciki, tana bud'a ido taga Mamie kawai ta tashi ta shiga ban d'aki tayi wanka, ta jima kafin ta fito ta shirya cikin rigar shadda dan fita take so tayi daga gidan, falo ta fito da gyalenta a kafad'a da jakarta a hannu, tana shirin kaiwa k'ofa Mamie ta fito daga d'akin Papa, a hanzarce tace "Khairat."

Tsayawa tayi amma jiyo ba, Mamie ce tace "Papanki ke kiranki?"

Saida ta sauke ajiyar zuciya sannan ta juyo bata yarda sun had'a ido da ita ba kawai ta nufi d'akin Papan.

Kamar yanda bata saba ba haka yanzu ma ta shiga d'akin ba sallama, zaune tayi bakin gado saboda Papa na zaune a d'aya daga cikin kujerun d'akin, kallonshi take tana jiran taji me zaice Mamie itama ta shigo ta zauna gefenta, babu wanda ya kalli wani bare suyi magana har Papa ya gyara murya yace....

"Khairat."

Jin yanda ya kira sunanta kuma yayi shiru yasa dole ta amsa da "na'am."

Kallonta yayi yace "waye ni a wajenki?"

Da mamaki ta kalleshi tace "mahaifina."

"Da kyau."

Nuna Mamie yayi yace "wannan kuma wacece ita?"

Kallon Mamie tayi tace "mahaifiyata ce."

Nan ma jinjina kai yayi yace "yayi kyau."

Sannan ya d'ora da "a tunani da hankalin da Allah ya miki Khairat, nasan kinsan iyaye suna da daraja sosai, hakane?"

"Hakane."

"Shin kina ganin mun kai matsayin da zamu iya yanke miki hukunci daya shafi rayuwarki ba tare da saninki ba, ko kuwa dai dole sai mun nemi izininki kafin mu nuna mu iyayenki ne?"

"Zaku iya mana, idan ba zai tauyeni ba."

"Ba wannan nake son ji ba Khairat, zamu iya ko ba zamu iya ba?"

"Zaku iya."

"To Alhamdulillah."

"Khairat, yau za'a kawo kayan lefenki daga gidansu Muzaffar, mun amince a matsayinmu na iyayenki, kuma muna da yak'ini akan ba zaki bamu kunya ba."

Tsaye ta mik'e tayi wata dariyar yan daba tace "nasan dama za ayi haka, yanzu me kuka daukeni da har zaku yanke wannan hukuncin a kaina? taya zaku had'ani da mutumin da tsarina da nashi ma daban ne? ni bana son Muzaffar kuma ba zan aureshi."

Jakarta ta dauka zata fita Papa ya daka mata tsawar da tasa ta tsaya wuri d'aya "ke Khairat, ina magana kina magana, maza wuce ki zauna magana nake dake."

Sum sum sum ta koma ta zauna Papa ya dora da "a tunani mummunar kalma bata tab'a shiga tsakanina dake ba, amma ki sani Khairat idan har kika shirya bani kunya da tozartani, to hakika zaki fara jin kalma marar dad'i ta fara fitowa daga bakina kuma a kanki, bana fatan na tsine miki albarka, amma dai ba zaki ji dad'in abinda zai fito daga bakina ba, ke ba yarinya bace kin isa aure har kin wuce ma, burinmu shine mu kaiki d'akin mijinki kema."

"Khairat, dubi mahaifiyarki ki gani."

Kallon Mamie tayi ta kalli Papa shi kuma yace "burinta kawai taga aurenki, kullum cikin fargaba take a kanki, saboda yanda take son taga kinyi aure Khairat har rabuwa tayi dani kuma ta dawo, yanzu haka mahaifiyarki wata d'aya ta bani dan na aurar dake, idan kuma ba haka ba to zamu rabu kuma rabuwa ta har abada, yanzu ki fad'a min Khairat."

"Shin kina son muci gaba da zama ni da mahaifiyarki, ko kuma kinfi son mu rabu?"

Shiru tayi tana tunanin mafita, tabbas bata son Muzaffar saboda basu dace ba, amma kuma ba zata yarda iyayenta su rabu ba saboda maganar aurenta, dan haka ta samawa kanta mafita, a hankali ta kalli Papa tace "in dai wannan shi zai saku farin ciki, tona amince."

Tana fad'a ta sake d'aukar jakarta zata fita Mamie tace "da gaske kike Khairat?"

Kura mata ido tayi tana kallon tsantsan farin cikin dake fuskar Mamie kafin tace "eh Mamie, na amince."

Juyawa tayi Papa yace " ina zaki je kuma?"

Danne zuciyarta tayi ta qaqaro murmushi tace "yau fa za'a kawo kayana Papa, ai bai kamata na zauna gida ba har sai kowa ya ganni."

Dariya suka saka mata dukansu itama ta wuce tana dariyar, yayin da suka bita dasa albarka, tana fita motarta ta shiga ta fara tuk'i kuma Mamie ta kirata, tana d'auka tace mata "shalelen Papa, dama cewa nayi me zai hana kije gidansu *Hibba*, kinga saiku zauna acan tunda mahaifiyarta ma nanan zuwa nan d'in."

"Ok, zanje." tana fad'a ta kashe wayar Mamie kuma tayi murmushi.


A hanya ta kira k'awayenta *Rashida, Sarina, Farida, Mamy* akan su sameta gidansu Hibba, duka suka amsa kiranta dan sun san akwai labari, hannun riga sukayi da Mamar Hibba hakan yasa basu gaisa ba, kafin su Rashida suzo ta fad'a mata abinda ke faruwa, dan ita kad'ai ke bata shawarar data dace, yanzu ma sake jadadda mata tayi tabi iyayenta, sannan ta nunawa Muzaffar kamar tana sonshi har tayi nasarar samun soyayyarshi ta gaskiya, tunda shi ya fad'a da bakinshi ko da ranar darensu na farko ne bai damu ba dan sun rabu, haka ta bata shawarwari masu kyau, sannan su Rashida suka zo.

Tana fad'a musu za'a kawo kayanta suka saka shewa da murna dan sun san babban bidiri ne, nan suka wuni har Muzaffar ma ya kirata yana tambayarta abubuwa da zasu shirya, kamar yanda Hibba ta bata shawara akan tayi dan ta b'oye sirrin zuciyarya sosai, ta fad'a mishi bata gida za suyi shawara da k'awayenta idan taje gida saita fad'a masa yanda sukayi dasu, a haka sukayi sallama su kuma suka ci gaba da shirye shiryensu.


*A gida* kuwa Mamie farin ciki take sosai hakan yasa suke ta kujuba kujuba, 'yan uwa mak'ota da mutanen arzik'i tuni suka cika gidan, hada hada kawai ake an soya na soyawa , an gasa na gasawa , an dafa na dafawa , an motsa na motsawa haka ma na jik'awa an jik'a.


*16:35* unguwar ta shaida bak'i sun shigo cikinta, jiniya kawai kake ji na motocin matan manya uwa uba ga mahaifiyar Muzaffar da kanta tace ba za'a barta a baya (abinka ga 'yan bariki.😁), motoci ne ba adadi suka tunkaro k'ofar gidan kama daga na matan manya da abokan arzik'i, sai kuma na abokan Muzaffar duk da baya gari amma sun masa kara, abinfa ba'a cewa komai ba'a kuma ga komai ba, saida masu tsaron lafiya suka fara bud'e motoci manyan mata na fitowa daga ciki.

Dala tayi kuka a wajen harka ta girma ce akayi sosai, sai dai wata matashiyar mota kyakyawa wacce aka shiga da ita har farfajiyar gidan, masu tsaronne suka dinga fito da akwatina kowace mak'il da kaya d'aya d'aya har dozin biyu da rabi, ga kuma wannan mota da aka azo akan lefan.

Ciki aka shiga masu gulma nayi masu saka albarka na sakawa masu d'aukar photuna suna d'auka, acan kuwa na hango muku Mamar Mujaheed 🀣ta rumgume jakarta tana kallon manyan mata suna yagar kaji da qafafun rak'umi 😁, haka dai aka ga abin arzik'i tari guda sannan aka sake tsayar da ranar kwana ashirin da biyar ya rage.

**************

Tunda Khairat ta dawo gida taga kayan ita kanta taji dad'i, dan burinta kenan ta samu babban mutum ta aura, bata wani kalli kayan duka ba kwai ta shiga d'aki tayi wanka tasa kayan bacci sannan ta kwanta dan bacci take ji.


*Washe gari* da safe kiran Muzaffar ne ya tasheta, cikin magagin bacci ta d'auka ta aza a kunne da fad'in "hello."

"Amaryata, kuma uwar gidana, ina fatan kin tashi lafiya?"

Sai lokacin ma ta tuna shine fa wanda zata aura, zaune tayi tace "lafiya lau, ya kake?"

"In dai kina cikin k'oshin lafiya, to ai nima haka nake."

Tashi tayi ta fara rage kayan jikinta tace "ok, to yanzu zaka min uzuri na shiga bayi, dan tashina kenan."

Cikin shagwab'a yace mata "amma fa muryarki nake so naji."

A hassale tace "muryar lafiya, tashina fa kenan, so kake nayi fitsarin anan? haba nifa bana son irin haka."

Ji tayi ya fashe da dariya yana fad'in "ashe fitsari kike ji, kinga kuwa da zaran munyi aure, da kaina zan dinga jaye miki fitsarin nanπŸ˜›."

Da sauri ta wani qaqaro amai tana fad'in "kai, wannan qazamtar fa? kaga sai an jima."

Kashe wayar tayi ta cilla saman gado tayi bayin da gudu, ko wanka ba tayi ba ta fito kai tsaye falo ta nufa, binsu take da kallo ganin mata zaune suna kallon kayan lefen, cikin risunawa suka ce "sannu da fitowa Hajia."

Kai kawai ta daga musu ta nufi madafa, had'uwa sukayi da Mamie da kula abinci a hannunta, "yawwa dama yanzu zanje na tasoki , zo muje to ga abincinki."

Hannunta ta kamo suka dawo falo suka zauna, buda kula tayi wani b'ata rai Khairat tayi tace "wannan fa? Mamie karfa zaki fara min wannan tashin hankalin ne? wallahi ba zan iya ba."

Dariya sukayi Mamie kuma tace "kwanciyar hankali dai Khairat, wannan shine gudumuwar da zan iya baki, dan nima shi kakarki ta bani."

Diba Mamie tayi tasa mata a baki, da qyar ta had'e tana b'ata rai sannan tace "haba Mamie ba dad'i ba."

"Yi hak'uri kinji shalelen Papa, ki saba da cinta kullum, kuma wannan fa had'in tattabaru ne, sai an jima zan miki na kaza."

Haka Mamie ta dinga bata tana rarrashinta har saida ta cinye wanda aka zuba mata sannan ta tashi ta shiga wanka.


*Tofa daga wannan rana* Khairat aka shiga sahun masu kurbe kurbe da tamne tamne, duk abinda Mamie zata had'a mata baya wuce na kayan itatuwa saboda sunfi lafiya, wannan kazar da tattabaru namiji da mace kad'ai ake hadawa da wasu sinadarin wajen dahuwarsu, abinka ga lafiyayya sai hakan ya d'an fara damunta saboda wasu itatuwa sun k'ara mata k'arfin sha'awa wanda da bata da ita, wasu kuma suna saukar mata da ni'ima.

Kowace safiya take jan foyer wajen gyaran jiki cikin k'ank'anin lokaci ta koma kamar sabuwar haihuwa, kuma haka ake kullum ba'a daina ba, yan mata da samari sun had'u sun tattauna abinda zasuyi, daga ciki akwai arabian night wanda ango yake bala'in son partyn , sai indian night wato b'angarenmu ba yan india😁, sai kuma party wanda za'a gayyaci kowa da kowa, sai cocktail daya zama kamar al'ada.

Kasancewar Khairat ta karanci zane hakan yasa ma ta zana kalar abayar da zata saka a arabian night d'in, amma kayan indian night Mammie tawa magana aka fara aiko mata da photuna ta zaba sannan Mammie zata taho dasu.


*Shirye shirye sunyi nisa sosai, kuma ango ya dawo sai dai Khairat tak'i yarda su had'u, hakan kuma ya dameshi dan haka ya fara tunanin ko da matsala ne.

Yau ta kama ranar *Asabar* kwana bakwai ya rage a daura aurensu, shiryawa yayi kawai yace shi zai tafi ya gant, mamarshi ce tace "Allah ya kiyaye hanya, amma dan Allah banda saurin hushi."

"Haba Mama, ina kusan zama angonta kuma zanyi hushi."

Yana fad'a yasa kai tare da rakiyar masu tsaron lafiyarsa sai gidansu Khairat....


_FAN'S JIHADI, ku kawo kud'in ankonku , dan yau zan siyo tawa, kuma babu wanda za muma alfarma ya shiga idan baya da anko musamman 'yan team d'in Umar Faruk, dan zasu iya b'ata mana taro.😊😁😎_
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


_Bismmilahir-rahman-rahim_


1⃣7⃣


Babu kowa a falon kasancewar sanyin safiya ce, Mamie yau bata fito wajen girki ba, sai masu aikin kad'ai suke abinsu, ganin babu kowa yasa shi sallama da k'arfi, da sauri Saude ta fito ganin ko wanene yasata zube qasa tana gaisheshi, saida yayi qaramin tsaki sannan yace "ina Mamie?"

Murya na rawa tace "tana d'akinta bata fito ba."

"Khairat fa?"

"Itama bacci take."

Kamar mai ciwon baki yace "ok, jeki."

Tashi tayi ta nufi madafa tana fad'in "ikon Allah kenan, sai kuma Allah ya had'ata da daidai ita."

Shima sama ya haura d'akin Khairat, a hankali ya bud'a k'ofar yana kallon gadon da yake da tabbacin tana nan, (kunsan mutuniyar dama ba kwana take da manyan kaya ba) hakan yasa Muzaffar ya kusa kallon rabin sadakinshiπŸ˜‚, saboda wata irin riga ce bata da maraba da bras, sai kuma wandon rigar kad'an ya wuce mazaunanta, takowa yayi harya tsaya gaf da ita yana had'iye yawu masu nauyin gaske, da qyar ya lumshe idonshi sannan ya sake bud'ewa ya saukesu a kanta, hannu ya kai zai daddab'ata ta bud'e ido tare da juyawa, karaf idonsu suka sark'e dana juna, a zabure ta tashi zaune taja dara ta rufe jikinta tana mashi kallon tuhuma.

"Wannan wane irin jahilci ne, miye haka Muzaffar, ya zaka shigo min har cikin d'aki kana tab'ani?"

K'ara matsowa yayi yana fad'in "kinga Khairat dan Allah kiyi shiru, karki tara min jama'a, wallahi bada wata manufa na tai tab'aki ba."

"Dallah ni kamin shiru, ka fice min daga d'aki."

"Haba Khairat w...." katseshi tayi da fad'in "dallah ni nace k...." kuma sai tayi shiru saboda tuna abinda Hibba tace mata.

Hararanshi tayi ta turo baki gaba tace "to dan Allah kawai ka shigo min haka duk ka bani tsoro."

Ajiyar zuciya ya sauke yace "kiyi hak'uri kinji. "

"To naji, wai mema ya kawoka nan? bayan nace maka ba zamu had'u ba har sai an fara shirya shiryen bikinmu."

"Kiyi hak'uri my Khairiri, wallahi na kasa hak'ura ne shi yasa, matuk'ar so nake na ganki sosai."

"To naji ni dai yanzu ka fita ka jirani falo zanyi wanka na fito."

Cikin wani shu'umin kallo yace "to muje na miki wankan mana."

Pillow ta dauka ta jefa masa tare da masa kallon kai shashasha kuma hamago ne, amma da yake hamagon ne na gaske saiya kasa fahimtar kallon, hannu ya mik'o mata tare da sake fad'in "kizo na rakaki to idan ba zaki yarda na miki wankan ba."

Saida ta had'e fuska sannan ta mik'a masa hannunta ta sauko daga kan gadon, ci gaba yayi da k'arewa surarta kallo ita kuma ko a jikinta, har saida ya kaita bakin ban d'akin sannan yayi murmushi yana cewa "insha Allah nan da rana kamar ta yau kin zama tawa, kuma daga wannan ranar ni zan dinga miki wanka."

Itama murmushin tayi tace "zaka dinga min, ko zamu dinga yi tare?"

Sunkuyawa yayi yace "yanda kike so gimbiya."

"To ka jirani falo ina zuwa."

Tana shiga shima ya bar gidan gaba d'aya ba tare daya jirata ba dan akwai abubuwa gabanshi, itama kuma ta jima bata fito ba bayan ta shirya ta fito falo, bata sameshi ba kuma bata damu ba, harkokin gabanta ta shiga yi bayan Mamie ta had'a mata kayanta tasha nasha taci naci, foyer ta nufa wajen gyaran jiki kamar kullum.

***************

Cikin farin ciki ya fito daga gida zuwa wajen aikinshi, tunda ya shiga yaga gungun su Ishaq sunata hira, saida ya tsaya bayanshi bai sani ba ya kai masa duka yana fad'in "iskancin banza, wajen neman kud'in naku kuka mayar kamar kasuwa?"

Dariya Ishaq yayi lokacin daya juyo ya

Please Login or Register in order to submit comment