Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gida, tun a k'ofar gida yara suka fito suka tarbesu, haka suka shiga cikin gidan ana musu sannu da zuwa, Ruk'ayya ce ta karb'i kayansu da makulli ta bud'e ta shigar musu da kayan, Zuby ce ta fito daga wanka zata shiga d'aki, kallon kallo sukayi da Umar Faruk dan Khairat harta shiga d'aki, "sannu da zuwa."

Ta fad'a kawai tasa kai d'aki, ganin ta shige yasa shima ya wuce d'aki, Khairat ya samu harta shiga wanka dan haka ya fito ya shiga d'aya douche d'in dan yayi wanka, doguwar riga kawai Zuby ta saka ta fito dan tayi alwala dan an fara kiran sallah, ganin yara maza sun fita k'ofar gida suna alwala iyayen kuma sunyi sun shiga d'aki, kusan dai gidan ya d'anyi shiru hakan yasa ta tuna da aikin da malam ya basu, aje butar hannunta tayi ta lallab'a a hankali ta shiga d'aki Khairat, tana shiga idonta ya sauka akan gado, jaka waya da kuma mouchoir (hankciep) ta gani akan gadon, da sauri ta d'auki mouchoir d'in dan a ganinta zaifi zama qaramin abu wanda ba za'a gane ba, sai dai kash, sark'ar da Khairat ta cire ce ta rufe da mouchoir d'in, kuma wajen d'auka da sauri yasa yan kunnai suka fad'i qasa saita had'a da sarqar ba tare data lura ba.


Da sauri ta shiga d'aki ta kira wayar Mama, a lokacin kuma Umar Faruk ya fito ya shiga d'akin Zuby baiko kulata ba yasa kaya ya fita masallaci, saida taga ya fita sannan tace wa Mama "Mama na samo abinda malam yace."

"Yawwa yar albarka, amma tayaya sun dawo ne?"

"Eh Mama." ta fad'a tana warware mouchoir d'in danta kalla, ido ta waro tace "Mama, sarqa ce fa a ciki."

"Sarqa kuma, ita kika d'auko?"

"A'a Mama, ina ga cikin mouchoir d'in take."

"To kinga ki ajesu , zanzo gidan an jima saina kaiwa malam d'in."

"To Mama." daga haka sukayi sallama, kallon sarqar take sosai qarama mai kyan gaske, wani babban dutsi ne ya qawata sarqar, ajewa tayi ta jira zuwan Mama.


Khairat na fitowa ta shirya cikin doguwar riga sannan ta rama duk wata sallar dake kanta kafin ta cire doguwar riga tasa riga da wando, jakarta ta d'auka ta fara cire kayan ciki tana mayar da komai mazauninshi, kan mouchoir ta aza hannu sai taji ba komai, kallon wajen tayi amma dai taga ba komai, wajen dressing miror ta nufa danta duba sai taji ta taka abu a qafarta, "ashhhh." ta fad'a tare da d'auke qafarta ta duba wajen.

Da mamaki tasa hannu ta d'auki 'yan kunnai dake qasa zube, duba gadon ta farayi amma sam bata gani ba, aje 'yan kunnai kawai tayi ta kwanta da littafinta a hannu tana karatu, sai dai tana tunanin yanda akayi abinda ta aje anan ta kuma rasashi.


***************

Bayan sallah la'asar Mama tazo gidan ta karb'a, a lokacin Khairat na d'akinta bata sanma da zuwanta ba, koda Mama taga sarqar tace zata kaita kasuwa ta siyar, dan ba zai yiwu a mayar da ita ba kuma da alama za tayi tsada, dan haka daga nan wajen malam ta nufa takai mishi mouchoir d'in, kasancewar magrib ta gabato yasa ta koma gida da niyyar gobe zata kai sarqar kasuwa ta siyar.

****************

Har Khairat ta fara bacci Umar Faruk ya shigo d'akinta, bai yarda ya tasheta ba dan yasan tana tare da gajiya, a hankali ya lallaba ya sumbaci goshinta sannan ya sake gyara mata rufa, dauke littafin dake qirjinta yayi ya daga hannayenshi ya tofa addu'o'i sannan ya shafa mata a jiki, ficewa yayi ya rufe mata d'akin sannan ya koma d'akin Zuby, da qyar Zuby ta amince da Umar Faruk ta bashi hakk'inshi, abin takaici kuma banbaci ne nesa tsakaninta da Khairat, ba yanda ya iya dole yana da hankalin da zai iya banbace dad'i da akasin haka, yana mamakin yanda yake samun Khairat kullum kamar budurwa kullum, dan kullum saita zubar da hawaye idan zai shigeta, amma Zuby ya kasa tantance meye ma yake ji a tare da ita, koda ya samu ya tsarkake kanshi bai kwanta ba, karatu ya dinga yi har dare ya raba kafin ya kabbara sallah, nanma saida aka kira sallah sannan ya nufi d'akin Khairat, koda ya shiga ya samu har tayi alwala, dad'i yaji sosai bayan ta gaisheshi sannan ya wuce masallaci.

Da safe kuma basu samu damar karatu ba saboda yana d'akin Zuby yana bacci, Ruk'ayya ta samu ta d'ora mata karatun, suna gamawa kuma Mamie ta kirata danta mata ya gajiya, suna cikin magana Khairat tace " Mamie, jiya fa na jefar da sarqata."

"Wace sarqar kuma?" cewar Mamie.

"Mamie sarqata ta *diamond*."

Waro ido Mamie tayi kamar tana gabanta tace "diamond d'inki, garin yaya Khairat, me yasa kike da sakaci ne haka, sarqar milyoyin kudade zaki saki har a d'auke?"

Cikin katse hanzari tace "Mamie, sarqa cefa, kuma ta b'ata, ya zanyi to? dan Allah karki damu kanki, zan siye wata insha Allah."

"Humm, haka za kice mana, dan kinsan kina tambayar mahaifinki ko million nawa ne zai baki shi yasa."

"Mamie, to idan bai bani ba wa zaiba? ni kad'ai ya haifa a duniya, nice mai gadon komai nasa, ai yafi naci tun muna kan lokacinmu."

"To naji, yanzu ki aje yan kunnan, zan kira *Alpha* da *Maiga* na fad'a musu idan sun samu koda mai kama da 'yan kunnan su kawo min, dan nasan halinki zaki iya yin banza dasu."

"To Mamie, amma nidai da baki bawa kanki wahala ba."

"Kiyi yanda nace kawai."

"To Mamie." tana fad'a ta kashe wayar, Mammie ce ta kalli Mamie ta tambayeta meya faru, nan ta fad'a mata abinda ke faruwa, a take Mamie ta kira Alpha da Maiga ta kula tura musu photon sarqar da yan kunnan lokacin da aka siyesu.

****************

Tun Mama nakan hanyar zuwa kasuwa take kiran wayar malam amma yak'i d'agawa, ta alaqanta hakan da yawan abubuwa, shi kuma ya ya kasa d'auka ne saboda sam babu nasara a aikinsu, danya riga daya gama fahimtar indai har Khairat na cikin gidan nan to babu abinda zai iya yi mata, saboda tsaron dake cikin gidan, ana yawan karanta Qur'ani musamman suratul Baqara, dan haka dole dai su sake shawara.


Mama na zuwa kasuwa ta zarce wajen wani babban mai harkar sarqoqi mai suna Alpha πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚, (wallahi dariya take bani), yana ganin sarqar yace "gaskiya Hajia kinzo da babbar harka, amma ki d'an jirani zansa a duba kota qwarai ce ko jabu."

Tana wasar baki tace "ba komai ai, nasan ma ta qwarai ce." kuma ta fad'i hakane ba tare da sanin wace irin sarqar take rik'e da ita ba.

Yana shiga daga cikin shagon ya kira Mamie ya fad'a mata irin sarqarce komai da komai, amma babu yan kunnai "bani minti biyu zan kiraka." cewar Mamie.

Tana kashewa ta kira Khairat ta fad'a mata, shiru Khairat tayi tana tunani, mamaki take sosai ta yanda akayi sarqarta ta fita daga gidan, duk da dai ba tabbaci amma tana so tasan waya samu sarqar, da sauri tace "Mamie, kice ya rik'e matar karya bari taje ko ina."

"To." Mamie ta fad'a tare da kashe wayar, ba b'ata lokaci Khairat ta dannawa *Abdul waid* kira, tare sukayi makaranta abokinta ne sosai kuma gendarme ne, yana d'auka yace,

"Marar mutunci, ashe zaki tuna dani harki kirani?"

Dariya tayi dan indai sun had'u sai haka ta faru, cewa tayi "petit frère, ya kake?"

"Ba zaki daina cemin qannanki ba ko? har yanzu kina nan da shegen san girma, ke mutum koya baki shekara arba'in kina iya kiranshi qannanki."

"Saboda nasan na girmeka ne shi yasa."

"To naji, ya akayi yanzu? kwana biyu kin b'ace."

"Wallahi da dama, amma yanzu akwai matsala."

"Meya faru?"

"Shekara d'aya data wuce akwai wani diamond dana siya, to shine jiya bayan na dawo daga las vegas na ajeshi, kawai na fito ban sameshi ba, amma abun mamaki yanzu Alpha ya kirani wai wata mace tazo da irin sarqar zata siyar."

"Subhanallah, yanzu me kike so ayi?"

"Um , ina so nasan matar kuma ya akayi sarqar taje hannunta, nasan zaiyi wuya ace ba sarqata bace, tunda ga 'yan kunnan a hanuna."

Kamar yana gabanta yace "an gama ranki shi dad'e, za ayi yanda kike so baby."

Da sauri tace "kai bana san iskanci, wannan sunan yanzu mijina kad'ai keda damar kirana dashi."

"Ke tafi can marar mutunci, ai dama jira nake na had'u dake wallahi sai anyi yak'in duniya na uku, wai yarinyar nan dan kin rainani kawai sai dai naji kinyi aure a gari, ba sanarwa ba kira ki fad'awa mutane, amma ba komai nine kika tsana ai, tunda *Ma'aruf* yace da kanki kika kira kika fad'a musu."

"Ai ban kiraka bane saboda baka damu dani ba, wata na kusan hud'u ina jinya amma baka tab'a zuwa ka dubani ba."

Shiru yayi kafin yace "kiyi hak'uri Khairat, wallahi nima labari na samu akan abinda ya faru dake, amma lokacin bana gari."

"Kaga ni ka dameni da surutu, kaje da sauri dan Allah ku qwamuso min matar nan."

Dariya yayi yace "baki da dama, kina nan yanda kike har yanzu."

"Kai wallahi ba kamar da ba, yanzu in fad'a maka inka ganni ba zaka ganeni ba, yanzu fa da hijabi nake fita."

Bushewa yayi da dariya lokacin da suka shiga mota shida jami'ai guda biyu suka nufi kasuwa yana fad'in "Allah ya shirya minke Khairat, yanzu fad'a min adresse d'in mai shagon?"

"Ba matsala zan turo maka, amma fa bana so kayi saurin fad'an sunana."

"No wahala baby, za ayi yanda kike so."

"Kai, zanci..., wallahi ka kiyaye ni fa, mijina zai shek'ek'a idan yaji"

Tana fad'a ta kashe wayar ta tura masa d'Γ  adresse d'in, Mamie ta kira ta fad'a mata yanda ake ciki, tana d'an duba karatun da Ruk'ayya ta d'ora mata Umar Faruk ya shigo d'akin da sallama, tashi tayita tarbeshi suka gaisa, tambayarshi tayi da "ba zaka fita yau ba?"

Saida ya shafi qasumbarshi yace cike da kasala yace "yau kam bana jin dad'in jikina, amma kuma ina so na fita, gashi kuma na makara sosai."

Itama gemunshi ta shafa tace "bara kaga yanda za ayi."

Wayarta ta d'auka ta dannawa manager kira, cike da girmamawa ya gaisheta kafin ta d'ora da "manager ayi mana uzuri nida Faruk, kasan jiya muka shigo."

"Ah haba Hajia, ai girmanku ne, ba komai wallahi."

Kashe wayar tayi ta kalleshi tace "kaje ka sake kwantawa."

Ba gardama ya sake mikewa ya fita ya koma d'akin Zuby, yana tafiya kuma sai taji hawaye sun zubo mata, sharewa kawai tayi taci gaba da karatunta.

***************

Alpha ne ya d'anja Mama da hira yace mata "Hajia saifa kin jira an kawo min kud'i daga banki."

Baki Mama ta bud'e tace "wai dama darajarta har takai haka?"

"Hajia dama baki san darajarta ba."

"A'a ba haka nake nufi ba, kasan mu tsofaffi ba ruwanmu."

Murmushi yayi yace "Hajia diamond kike d'auke da ita fa."

"Diamond?" cewar Mama da ita k'arfinta, hakan kuma yayi daidai da isowar su Abdul Waid, cikin d'aure fuska Abdul Waid ya sauko daga mota yana zarewa Mama ido, "kece wacce zaki siyar da sarqar?"

Mama da jiki ya ya fara rawa ga fad'uwar gaba da tsinkewar yan ciki tace "a'a.....a..a.., ba...b.ni."

Kallon Alpha yayi yace "mun samu rahoton anzo siyar da sarqa nan wajen, shin zamu iya sanin gaskiya."

Sarqar ya bashi tare da fad'a mishi komai, ba sauki al'amarin suka tusa Mama cikin mota suka tafi da ita, suna zuwa suka garqameta suka rufe sannan ya kira Khairat ya fad'a mata, duk da bata san ko wacece ba cewa tayi "kawai ta fad'a muku yanda ta samu sarqar."


_Ma'u ho_πŸ˜‚


***************


Sai kusan la'asar labari ya riski Zuby da mutanen gidan, gaba d'aya Zuby ta ishi gidan da kuka da jiniya , da qyar Umar Faruk ya lallab'ata yace zaije yaji miye matsalarπŸ˜‚πŸ˜‚ (wlh dariya kawai ke sub'uce min), koda yaje kuwa aka fad'a mishi abinda ake ciki, amma kuma Mama tak'i fad'in yanda akayi ta samu sarqar, abu kamar wasa haka labari ta fara karad'e dangi da mutan gari.

Khairat na jin abinda ke faruwa tayi mamaki sosai, to taya sarqarta taje hannun Mama? wannan itace tambayar da take wa kanta, dan haka taci alwashin sai Mama ta wahala ta kuma gane kurenta tare da fad'in yanda akayi sarqarta taje hannunta, gidan babu wanda yayi bacci a daren saboda kukan da Zuby keyi, a haka safiya tayi Zuby ta shirya dan tafiya ganin Mama.

Saida Umar Faruk ya matsa mata ta samu taci abinci, suna shirin fita daga gidan jiri ya d'ebeta ta fad'i, a firgice Umar Faruk ya d'auketa yana kiran sunanta, d'akin Mama ya kaita ya kwanta aka shafa mata ruwa ta farka, bayan qanqanin lokaci kuma zazzab'i ya rufeta, duk da haka matsawa tayi saita tafi dan haka Umar Faruk ya d'auketa suka tafi, koda taga halin da Mama ke ciki ma sabon shafin kuka ta bud'a, da qyar Umar Faruk ya fito da ita daga wajen, suna hanya yaga tana rawar sanyi sosai dan haka ya wuce da ita asibiti.

Ana dubata aka tabbatar mishi tana d'auke da qaramin cikin da ba zai juri wahala ba, ji yayi kamar almara hakan yasa saida suka shiga mota ya rufe ido na d'an wani lokaci, yana bud'ewa ya saki murmushi yana fad'in "Alhamdulillah Allah, Allah kaine Allah, ina godiya abisa ni'imominka a gareni."

Aifa ranar Zuby na jikin Umar Faruk, duk da masifar shagwab'a da kukan da take haka ya taushe ya had'iye, a ranar ko saida safe bata bari yama duka muten gidan ba bare kuma Khairat, Khairat kam ganin shiru yasa ta maida hankali ga tilawar karatunta, amma fa da taga dare yayi sosai kuma ta tabbatar ba zai shigo ba saida ta zubar da hawaye, a haka asuba tayi saida ya samu ya dawo daga masallaci kad'ai ya wuce d'akin Khairat har safiya tayi, yana shiga ya sameta kwance akan kujera da littafin *Hisnul muslim* tana karanta addu'o'i, a wahalce ta tashi zaune tana fad'in,

"Sannu da zuwa."

"Yawwa sannu." ya fad'a yana zaunawa kusa da ita, kallonta yayi yace "kin tashi lafiya?"

"Lafiya lau." ta fad'a a tak'aice, janyota yayi jikinshi yace "yadai, me yake damunki."

"Ba komai."

Tashi tayi zaune ta kalleshi tace "Faruk, da zuciya d'aya nake zaune da kowa a gidan nan, zan iya sadaukar da komai nawa dan taimakawa marar k'arfi, amma duk da son taimakona a gaskiya bana son sata, bansan tayaya sarqata ta shiga hannun mahaifiyar matarka ba, amma dai nasan ta sameta ne da taimakon wani na kusa dani, ma'ana wanda yake cikin gidan nan, ni nasa aka maka wanda ya d'auka min sarqar, amma gaskiya da farko bansan ita bace."

Katse mata magana yayi da "da kuma ki kasan itace me ki kayi?"

"Banyi komai ba."

"Ai kuwa na d'auka za kisa a fitar da ita ne ,kodan matsayinta a gareni."

"A'a Faruk, ina so nasan yanda ta samu, dan nasan b'arawona, hakan na nufin akwai mai son cutar dani, ba kuma zan lamunci hakan ba."

Gyara zama yayi yana kallonta yace "dan Allah Khairat kiyi hak'uri kisa a fitar da ita basai kowa yaji ba, na miki alk'awarin hakan ba zata sake faruwa ba insha Allah."

Tsaye ta mike ta aje littafin hannunta tana fad'in "kayi hak'uri, gaskiya ba zan iya ba, dole nasan meya faru, kuma fa maganar milyoyin kud'ad'e ake, taya kake tunanin zanyi wasa haka."

Shima tsaye yayi yace "kenan kina so kice ba zaki iya fito da ita ba?"

"Eh, haka nake nufi." ta fad'a ba tare data kalleshi ba.

"In kuwa hakane baki cika masoyiyar gaskiya ba, na dauka zaki iya yin komai saboda ni, ashe ba haka bane."

Yana fad'a ya fita ya bar d'akin, ko kallonshi ba tayi ba itama taci gaba da harkokinta, shiryawa tayi bata kula kowa ba itama ta tafi office danta samu salama, taji dad'in tafiya domin ta manta da duk wasu matsaloli, sai dai damuwar d'aya shine rashin zuwan Umar Faruk aiki, da yamma ta fito dan tafiya gida amma motarta tak'i tashi, kiran Umar Faruk tayi a bugu d'aya ya d'auka, nanta fad'a masa abinda ke faruwa, saida ya shiga gida ya d'auko makullin motarshi danya tafi d'aukarta, Zuby ce ta shagwab'e sai dai ya zauna bata so ya fita, ganin ba zata barshi ya tafi ba yasa yace sutafi tare.


Koda suka isa Khairat bata damu ba tunda yau ba itace dashi ba, gidan baya ta bud'a ta zauna lokacin har mai gyara yazo duba motarta, suna fara tafiya tace "sannunku."

Umar Faruk kad'ai yace "sannu, ya aiki? kinga yau banzo ba ko?"

"To ai naga amarci kake ci har yanzu."

Karaf Zuby tace"bai kai yaci amarcin bane kome?"

Ajiyar zuciya kawai ta sauke, tsaki tayi ita kuma tana habaice habaice har tana fad'in "wataqila itama tana kurb'awa kamar gyatuminta."

Murmushi Khairat tayi tace "zanyi farin ciki ace kurb'awa nake, koba komai shan giya sai mai kud'i, amma halin b'era, ina fatan Allah yamin tsari dashi."

Zuby zatayi magana Umar Faruk ya daka mata tsawa yace "karki sake naji bakinki, wallahi idan na sake jin makamancin haka a tsakaninku har takai ga sanya iyaye, wallahi zaku gane kuskurenku."

Qwafa yayi mai k'arfin gaske, shiru sukayi suka ci gaba da tafiya, daf da wani babban shago Khairat tace "dan Allah baby inba damuwa ka ajeni nan zan duba wani abu."

D'an qaramin tsaki yayi yana paka motar yana fad'in "bana so magrib ta sameni akan hanya."

"Ba zan jima ba baby."

Ganin Zuby na kallon shagon yasa yace "ko kema zaki shiga?"

"Eh, madara nake so." ta fad'a cikin shagwab'a.

Hannu yasa ya shafi sumar kanshi sannan ya bud'e murfin yace "fito muje."

Fita sukayi suka rufawa Khairat baya, a tare suke duba kayan yayin da Khairat keta cika kwando da kaya, suna gamawa suka zo wajen biyan kud'i, ana lissafi kayan daga baya sukaji ance,

"Hajia Khairat."

Juyowa tayi amma wanda ta gani yasa mamaki ya bayyana a fuskarta fal, da farin ciki ta nunashi tana dariya tace "Alhaji....
20/08/2019 Γ  14:26 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


_Bismmilahir-rahman-rahim_


4⃣9⃣


"Alhaji Bala, kaine?"

Cike da girmamawa ya matso inda take ya sunkuya yana gaisheta "Hajia ina wuni."

"Haba dan Allah ka tashi mana."

"Haba Hajia, aini ba butulu bane, wallahi uwata kad'ai nafi girmamawa a duniyar nan kafin ke, duk da dai nasan nayi laifi, amma ina neman afuwa Hajia, ke babbace kina bawa komai baya komai girmanshi, musamman ga irinmu talakawanki."

"Alhaji Bala, matsalata dakai fa kenan, wasa mutum da kurantashi, to ya kwana biyu ya iyali?"

"Lafiya qalau Hajia, ya harkoki ya kuma fama damu?"

Bata amsa ba sai nuna masa Umar Faruk da tayi tana fad'in "am Bala, ga mijina nasan baka san nayi aure ba, ga kuma yar uwata abokiyar zamana."

Hannu Umar Faruk ya mika masa amma saiya nemi zube gwiwoyinshi qasa danya gaisheshi, da sauri ya rik'eshi yana fad'in "haba haba, ya haka kuma? kaifa babbane."

"Barni Alhaji na gaisheka, aiko karen Hajia Khairat dole samu girmamawa daga gareni, bare kuma kai mijinta."

Cikin jin haushi Zuby ta juyo danta fita daga wajen, idonta ne ya sauka kan Alhaji Bala, wucewa tayi dan bata sanshi ba shi kuma ya santa farin sani, binta yayi da kallo harta b'acewa ganinshi, hannu Umar Faruk ya ya sake bashi suka gaisa sannan sukayi sallama, ledojin ya d'auka harda na Khairat ya wuce dan yau dad'i yake ji ya mata hidima, kallon Alhaji Bala tayi tace "mu zamu wuce, sai kwana biyu."

"Am Hajia." ya fad'a a hankali.

Kallonshi tayi shi kuma ya d'ora da "Hajia ki kace waccen abokiyar zamanki ce?"

"Eh." ta fad'a a tak'aice.

Shiru yayi yana girgiza kai, da mamaki tace "lafiya ko, kasanta ne?"

Shiru yayi yasa babbar rigarshi ya shafe zufa, d'an hararanshi tayi tace "He Bala, nasanka fa, ka fad'a min gaskiya, kardai itama tana cikin yan matanka."

A tsorace ya kalleta yace "A'a Hajia , wallahi na jima da daina wannan harkar, wannan d'in indai sunanta Zubeida kuma ya ga Asma'u, to tabbas *d'iyata ce*."

"Me, 'yarka fa, tayaya?"

"Kamar yanda kika sani bana iya b'oye miki komai, domin kuwa badan taimakonki ba da yanzu ina bara akan titi, wannan da kika gani 'yata ce ta cikina, kuma bata hanyar aure muka sameta ba."

Bai qara komai ba daga hakan, kuma itama bata tambayi komai ba suka rabu, a mota kallon Zuby kawai take tana mamaki, Zuby kam cikin rawar kai tace "da auranka ma saika nuna halin, wannan jaraba dame..."

Bata qarasa ba Umar Faruk ya taka burki da k'arfi yana harara, cikin zare ido yace "wallahi tallahi zan zubar miki da hoqoran gaba, kinji dai na rantse ko? tom."

Tayar da mota yayi suka d'auki hanya, duk da haka Zuby bata daddara ba suna daf da shiga gida saida ta bangaji Khairat da k'arfi ta wuce, bugu da qari ta d'ora da "yar mashayi kawai, in banda qaddara me zai had'ani had'a kafada dake."

Yanzu kam Khairat takai maqura ba zata iya jura ba, kamar mai tab'in hankali haka ta zubar da kayan hannunta ta shak'o wuyan Zuby, kafin ma Zuby ta fahimci meya faru Khairat ta dasata a qasa tabi kanta da duka , ihu ta fara tana kiran sunan Umar Faruk dake gyara parking d'in mota, sosai Khairat take bugun bakinta harya fara fitar da jini, gashi girman jiki ba d'aya ba ta kasa qwatar kanta, jin kururuwa ne yasa mutanen dake d'aki duk suka firfito, da azama kowa yayi soro ya fara qoqarin rabasu, lokacin kuma Umar Faruk ya shigo, sosai ta rik'e rigar Zuby harta keta mata rigar, janyota Umar Faruk yayi a lokacin Zuby itama ta rik'e rigarta sosai, hakan yasa zip d'in rigar cirewa har rigar ta zame daga jikinta, ganin haka yasa mazan wajen komawa mafakarsu suka bar mata, cike da takaici da b'acin rai Umar Faruk ya fizgi hannun Khairat daga wuyan rigar Zuby yana fad'in "ba zaki saketa ba?"

"Ba zan saketa ba, wallahi saina ci uwar yarinyar nan, akan me zata rainani, ni tsararta ce?" duk tayi maganar nan cikin neman d'aukewar numfashi.

Duk maganganun da mutanen wajen keyi ko jinsu basuyi, da k'arfi ya b'abb'are hannayensu ya nuna Zuby yace "wuce ciki."

Juyawa tayi tana kuka tana d'yangasa qafa tana tofar da jinin dake bakinta, Khairat ma a tsawace yace "maza wuce ciki."

A hassale ta qarasa zame rigarta ta jefar ta wuce nata kewayen, zaune tayi akan kujera saboda makullin na cikin jaka kuma ta jefar da ita, Zuby na kaiwa qofar d'aki ta durk'ushe tana dafa ciki tana qara tsananta kukanta, da sauri kuma sukayi kanta ana tambayar lafiya, Mama ce da Saratu suka kamata danta shiga ciki, sake lanqwashewa tayi tana dafe ciki, Mama Sa'a ce ta kalli Umar Faruk tace "Umar Faruk tana da ciki ne?"

Kai kawai ya d'aga mata alamar eh, Mama Maimuna ce ta qara da "Allah yasa dai ba b'ari za tayi ba."

Jin haka yasa Zuby sake fashewa da kuka tana kiran cikinta cikinta, a hanzarce yace "to Mama mu tafi asibiti mana."

"A'a bari dai mu gani." cewar Mamanshi, d'orawa tayi da "bud'e mana d'akin."


Umar Faruk d'in ne ya bud'e musu d'aki suka kwantar da ita akan gado, duk wannan murqususus da take har yanzu shiru ba alamar jini ko wani abu, da qyar suka rarrasheta tare da bata baki, sannan Mama ta dora "in ki kaji wata matsala kiyi sauri ki fad'a masa kinji."

Bata amsa ba su kuma suka kama bansu, tashin hankali Umar Faruk ya ganshi a daren nan, kuka kawai take tana fad'in cikinta, sam bata barshi yayi bacci ba, kuma duk kururuwar nan da take akan kunnan Khairat dake cika tana batsewa, duk yanda taso tayi banza dasu abin ya gagara saida ta zubar da hawayen bak'in ciki ,itama dai ba tayi wani bacci ba sai karatunta data kwana tanayi.


Tunda asuba Zuby ta fahimci illar da Khairat ta mata, kallon kanta tayi a madubi taga yanda bakinta ya kumbura, ga masifar ciwon da hannunta keyi ko motsashi bata son yi, a haka Umar Faruk ya dawo daga masallaci ya sameta ba tayi sallah ba, nuna mishi hannun tayi yana gani ya kece da dariya yace "wallahi gotaki tayi, kawo na gyara miki."

Cike da jin haushi ta bashi hannu danya gyara mata, amma yana tab'awa ta fara ihu da kururuwa tana qwaqwumeshi, taji jiki sosai yayin da Umar

Please Login or Register in order to submit comment