Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan yanayinka ya nuna hakan, ka tashi ka ka b'ace min da gani, kuma wallahi ka kiyaye shiga hakk'in matanka, dan mugun kamu Allah zai maka." yana fad'a ya shiga d'akinshi ya barshi.

Jiki ba k'wari haka ya tashi yana k'arewa kanshi kallo dan baya so ya shiga da wannan yanayin da Baba yace ya gani a tare dashi, kallon ahlin nashi yayi da sukayi nisa a bacci, k'ofar kewayen nasu a bud'e take haka ma wuta ba'a kashe ba, yana dosa kai ciki ya tsaya cak saboda ganin Khairat zaune akan kujera harta langab'e kamar zata fad'i, ga abin sauraronta a kunne wayar kuma ta fad'a a d'aya saman kujerar, abinda ya d'aga mashi hankali shine yawan motsin da take saboda sauron dake ta cizonta sai sosar jiki take, a hankali ya sunkuya daf da ita ya saka hannayenshi ya .....

_Kuna ganin d'aukar zaiyi, ko kuma me zai mata.?_
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


_Bismmilahir-rahman-rahim_


2⃣3⃣


Hannu yasa ya zare abin sauraron daga kunnenta ya d'auki wayar ya kashe, a hankali ya daddab'a hannunta kafin yayi na biyu kuma ta bud'a ido, zunbur ta tashi tsaye tana zare ido sai kuma ta fara sosar jiki kamar mai k'yaya, jin gaba d'aya jikinta ya d'auki rad'ad'i na cizon sauro yasa ta lab'e baki kamar jaririya ta fashe da kuka tana ci gaba da sosar duk inda take jin kyaikayi, Umar Faruk kuma mutuwa yayi da kallonta cike da birgewa yanda tayi kalar yara, wani murmushi ya saki ya nufi kayanta data jefo lokacin da za tayi wanka ya d'auke ya shiga dasu d'aki, jim kad'an ya fito ya fad'a douche danya tsarkake kanshi, kallon juna sukayi ita kuma ta wurga masa harara da tsaki dan sai lokacin ta tuna rabuwarsu dashi, douche ya shiga ita kuma ta shige d'akin amma ta kasa komawa ta kwanta.

Fitowa yayi cikin doguwar riga ya sameta zaune tana kukan shagwab'arta, zaune yayi akan kujerar yana kallonta, ganin har yanzu sosar jiki take yasa ya taso a hankali ya zauna bakin gadon tare da sauke ajiyar zuciya, waigawa yayi ya kalleta cikin taushin murya yace "Khairat."

Cikin kukan shagwab'a ta fara magana "wallahi Allah ni dai ka mayar dani gidanmu, ba zan iya zama anan ba sauro ma kasheni zaiyi, dan Allah ka taimaka ka bani izini na tafi gidanmu."

Ta sake fashewa da wani kukan, "Khairat." ya sake kiran sunanta.

Kallonshi tayi dan haka yace "tashi kiyi alwala kizo."

"Ni ina maganar ka kaini gida, kai kuma kana maganar naje nayi alwala." ta fad'a a matuk'ar harzuk'e.

"Ki tashi kiyi abinda nace." ya fad'a yana komawa kujerar.

Saboda ibada ne yasa ta tashi ta fita ta d'auro alwala ta dawo ta sameshi, tunda ta fita ya duba ledar daya aje tana nan yanda take, yana ganinta ya tashi ya shinfid'a sallaya yace "kisa hijab d'inki ki tsaya bayana."

"Meye kuma haka?" ta tambaya tana kallonshi.

Kallon daya mata yasa ta d'auki hijab d'in ta saka ta tsaya daga gefenshi a bayanshi, kabbara sallah sukayi, raka'a biyu sukayi tare da jimawa zaune Umar Faruk yana jero musu addu'a, suna sallamewa zaune yayi sosai tare da juyowa ya kalleta, cikin nutsuwa da hikima ya fara magana,

"Khairat, da farko na d'auka labarina dake gajeran labari ne, amma daga ranar da zuciyata ta yanke min hukuncin na amince da aurenki, saina yarda labarinmu dogone, hak'ik'a aurena dake Allah ya qaddara faruwarsa bamu ba, idan har za ayi maganar gaskiya, to kin wuce tsarin aurena, matsayinki da nawa ba d'aya bane, amma duk da haka sai kuma Allah ya hukunta aure tsakanina dake, hakan na nufin akwai abinda Allah ya tsara mana a rayuwarmu, dan haka zaifi mu jira hukuncin ubangiji, amma maganar saki ki daina ba kyau, sannan ina so kiyi hak'uri dan nasan na b'ata miki sosai saboda aurenki da nayi, amma dan Allah Khairat ki bani dama na cika alk'awarin dana d'aukarwa iyayenki ta hanyar samar maki ingantacciyar ruyuwar da suke miki fata da kuma burin samu."

"Khairat akwai tambayoyin da nake son yi miki a game da addininki , kuma ina fatan zaki amsa minsu kamar yanda suke, ina so na d'ora miki daga inda kika tsaya, dan haka ina son fara sanin yanda kike tsarkake kanki, domin kuwa saida tsarki ne zaka fuskanci ubangijinki, idan har kina wankan tsarki kamar yanda aka koyar to alhamdulillah, dan haka ina jinki ki fad'a min."

Hannu ta zura a cikin hijab d'inta ta d'an sosa damtsenta da duk k'urajen sauro suka fito mata, shiru tayi kamar bada ita yake ba, hakan yasa yace "Khairat dake nake fa."

"Toni me zance maka? kana ganin sauro duk ya b'ata min jikina, ya kake so nayi."

Tsaye ta mik'e ta cire hijab d'in tana shirin hayewa gado taji ya rik'e qafarta, juyowa tayi tace "dallah sakeni malam."

"Ki dawo magana muke." ya fad'a ya matuk'ar tsaurare.

Tana turo baki gaba ta koma ta zauna shi kuma yana bin hannayenta da kallo, saiya ji tausayinta saboda duk fatarta tayi ja sai shatin cizon sauro a jikinta.

D'orawa yayi da "ina jinki."

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallonshi tace "bansan me zance maka ba, zan fad'a maka rabona da islamiyya tun ina 'yar shekara bakwai, ko kuma zan fad'a maka ni bansan komai ba, abinda na koya daga wankan tsarki a wa'azi naji a gurin malamai da dama, duk da sunce wankan akwai wanda zaka iya zuba ruwa tun daga samanka har qafafunka tare da cud'a jikinka ma ya hallata , to amma ni hankalina yafi kwanciya ga wanda yake tare da alwala, dan haka ni shi nake yi."

"Ina so nasan yanda kike yinshi."

Kallonshi tayi tace "wai dan Allah ba zaka bari harda safe ba, yanzu bacci nake ji ga wannan masifar sauron."

"Ina jinki." yayi maganar ba wasa.

Hararanshi tayi taja tsaki, da sauri ya kalleta ya kai hannu zai kamo bakinta ta tuno da karonsu da rana, da sauri ta jaye daga wajen tayi baya tana fad'in "to naji zan fad'a maka."

"Nakan fara da niyyar yin wanka sannan na tanadi ruwana masu tsarki da tsarkakewa, sannan na wanke gabana da kyau ta yanda duk wata qazanta zata fita har izuwa gwiwoyina zuwa cibiya, sannan nasa sabulu na wanke hannayena da kyau, sannan na fara d'aura alwala sau d'aya d'aya har saina zo shafar kai, ana so ya samu ruwa sosai sannan na k'walk'wale kunnuwana, daga nan kuma zan fara wanke barin damana tun daga sama har qasa, sannan na koma barin hagu shima tun daga sama har qasa, sannan na wanke qafar dama sai kuma ta hagu, wankana ya kammala kuma idan lokacin sallah yayi ma zan iya yin sallah dashi in dai har banyi wanka da sabulu ba, to yanzu zan iya kwantawa *malam Umar Faruk mai tambayar wankan tsarki*?"

Yaji dad'i sosai da har wankanta ya zamana yanda sunna ta koyar ne, dan haka ya dinga mata tambayoyi tun daga lokacin daka gama alwala har lokacin da zaka shiga sallah, kuma cikin ikon ubangiji ta amsa saboda tambayoyi ne masu sauk'i, abu d'aya shine ko hizib d'aya ba zata iya karanta maka ba daga farko zuwa qarshe, dan haka Umar Faruk yace "karki damu, in dai har zaki bani goyon baya, to kema zaki samu hasken qwaqwalwa dana zuciya, ina so zan fara miki karatu daga gobe daga inda nake ganin ya kamata a d'oraki, kuma ina so kisa abin a ranki ta yanda ko bana nan zaki iya tambayar wani ko wata, a cikin gidan nan Khairat ko *Fateema, da Alqasim* kika tambaya zasu iya d'oraki daga hizib d'aya zuwa talatin, dan haka kije ki kwanta gobe insha Allah zan fara miki da littafin *AL'AKHDARI, HUSNUL MUSLIM, KHAMSUNA HADITH, DA KUMA LITTAFI MAI TSAKI DAGA HIZIB D'AYA ZUWA GOMA*, idan har kika saka abin a ranki to Allah zai taimakeki cikin sauk'i ki dinga fahimtar abinda kike koya, saida safe."

Ya fad'a yana tashi tsaye tare da kabbara wata sallah, duk da taga sallah yake amma bai hanata cewa ba "na d'auka ba zan tab'a samun hasken rayuwa ba, ina son sanin addinina sosai, amma duk lokacin da nayi yunkurin zuwa inda za'a koyar dani, sai k'awayena da zuciyata su nuna min na wuce wannan wurin ko kad'an ba ajina bane, kuma ma ai ina da ilimi na zamani ga wayewa ga kuma kudi, sai dai na manta dashi ilimi ba'a tsufa da nemanshi, kuma wannan ilimi saida shine zan samu tsira ranar gobe qiyama, insha Allah zan koya kuma lokacin ya kusa zuwa da zanje gaban Mamie na karanta mata sura mai tsayi wacce za tasa tayi mamaki harma ta saka min albarka."

Tana fad'a ita kuma tayi kwance a gado sai dai ina bacci bai samu ba, kiran sallah ne ya daki kunnuwansu dan haka Khairat taji wani sabon shauk'i a game da son ibada ya shigeta, tun kafin ya sallame ta tashi ta fita tayi alwala, zata shigo d'aki shi kuma zai fita masallaci, tsaye tayi ta fita sannan ta shigo saida ta fara da *salatul fijir* sannan tayi sallah, tun bata tashi ba bacci ya fara fizgarta daga nan, jingina tayi da gado kawai ta dunk'ule cikin hijab ta fara gyangyad'i, a haka Umar Faruk ya shigo ya sameta, zaune yayi yana tasbihi yana kallon fuskarta, murmushi kawai ke bayyana a fuskar tashi saboda tuna tambayoyin daya mata kuma ta amsa, ga kuma abinda yaji tace a game da son karatun, a cikin ranshi yace "taya zan bata hak'uri kenan?"

Bai samu amsa ba kuma bai daina kallonta ba har gari haske yana kallon yanda take bacci kuma ko motsawa ba tayi ba, a sama sama yake iya jin hayaniya a tsakar gidan, dan haka ya d'auka ko masifa ce dasu Mama Sa'a suka saba da ita, hayaniyar ce ke sake yin sama ga kuma kuka da yake ji wanda yake tunanin na *Yusuf* ne d'an Abbakar, wannan kukan ne yasa Khairat bud'a ido ta sauke akan Umar faruk dake kallonta, zaune tayi da kyau tana mike qafafu tana murza ido shi kuma tuni ya d'auke kai daga kallonta, jin kukan da hayaniyar mutane yasa ta kalli Umar Faruk tace "waiku gidanku ba kwa baccin safe ne? suna damuna fa."

Kafin yayi magana ta mike tsaye ta cire hijab zata kwanta kenan taji ana kiran sunan Umar Faruk, da sauri ya fita daga d'akin tana binshi da harara da jin haushin mutanen gidan da basa barin bacci, da azama ya sake shigowa taga yana lalabar aljihun rigarshi daya cire jiya, yana d'aukar makulli yace "zanje na dawo."

"Ina?" ta fad'a dan taga tashin hankali a idonshi.

Yana barin d'akin yake fad'in "zamu kai Yusuf asibiti."

Jin haka yasa Khairat biyo bayanshi da sauri itama ko kallabi bata d'ora a kai ba bare takalma, Yusuf na rik'e a hannun Abbakar sai kuka yake Umar Faruk kuma yana gaba danya fitar da moto, duk kowa yayi cirko cirko Ruk'ayya ce Khairat ta dafa tace "meya sameshi."

Saida ta kalli kayan jikinta sannan tace "wallahi wata 'yar k'aramar lula ce mai kamar ball ya samu yake wasa da ita, shine ya saka a hanci ta shige masa, kuma gata ana gani amma tak'i fitowa."

Jin haka yasa Khairat rugawa a guje ta tari gaban Abbakar ta finciko Yusuf daga gareshi ta zaune dashi a qasa ba tare data damu ba, ganin haka sai kowa ya matso inda take duka suka rufesu suna kallon ikon Allah, Umar Faruk ma zai fitar da moto yaga kuma an taru dan haka ya dawo shima, amma abin mamaki da bai tab'a tunanin ko a mafarki ya faru bane ya faru, Khairat ya gani duk da hawaye da miyo ga majina data b'ata fuskar Yusuf bai hanata saka bakinta a hancinshi ba a inda babu lular tana busawa, sosai take busawa kafin ta d'ago kai ta kalli Abbakar tace "ace duk yawankun nan kun kasa taimaka mishi, sai wani maganar asibiti kuke."

Sake maida bakinta tayi da k'arfi tana busawa, sai kuwa lular nan tayi b'ul ta fito daga hancin Yusuf, wata irin sa'ida da salama da yaron yaji yasashi saurin rumgume Khairat ya manna kanta a qirjinta dake k'yam dashi yana hararan Umar Faruk daga nanπŸ˜‰, d'an shafa kanshi tayi sannan ta mik'awa Abbakar shi yana amsa ya kalleta sosai yace "mun gode sosai k'anwata."

Mik'ewa tayi amma sai Saratu ta rik'e hannayenta duka biyu ta had'e tana kuka tace "na gode sosai yer uwa, tashin hankalin dana shiga yasa na manta ta yanda zan fara taimaka masa, na gode sosai."

"Ba komai." ta fad'a kamar dai wacce aka saka dole, kakkab'e wandonta tayi ta juya ta nufi kewayenta kowa kuma na binta da kallo saboda abinda tayi babu wanda yayi tsammanin yinshi, saida kowa ya kama harkar gabansa Umar Faruk na tsaye, daga baya yaji an dafa kafad'arshi, juyawa yayi sai yaga Mama ce, murmushi yayi zai wuce yaji Mama tace "zuciyarta mai kyau ce, tana da abinda ba kowa yake dashi ba, wato *tausayi da taimako*, duk wanda yake da wannan halayen to mai imani ne shi, d'an duhun dake cikin rayuwarta nake so naga ga yaye matashi ka mayeshi da da haske , kaje Allah ya muku albarka."

Wucewa Mama tayi shima kuma ya nufi kewayen yana jin wani irin nishadi da farin ciki na lullub'e zuciyarshi, yana shiga ya ganta ta d'ibi ruwa tanata wanke baki wai ita majina, murmushi kawai yayi ya shiga d'aki, tana shiga itama tayi zaune tare da d'aukar wayarta tana aika kira, ba jimawa aka d'auka a daqile tace "ka kawo min mota ina jiranka."

Duk da wanda ta kira yaso ya tambayi gidan nata, amma ta riga data kashe wayar, Umar Faruk kuma tashi yayi ya shiga wanka, koda ya fito ta tashi zata shiga itama tace masa "aiki zanje, idan ka rigani zuwa kace Habiba ta share min bureau (office)."

Tana fad'a ta wuce abinta shi kuma yayi shiru yana tunanin kuma ta yanda zaiyi ya dakatar da ita, harta cire kayan jikinta sai kuma taji wani irin sanyi ya lullub'eta, dafa wuyanta tayi sai taji zafi ruf, tsaki tayi dan tasan sauron nanne kawai ya zuba mata zazzabi dan haka ta d'auko kayanta a hannu ta manta da inda take rayuwa yanzu, duk da ta raumgume kayan amma dai kallo d'aya zaka mata kasan babu komai a jikinta, tana dosowa zata shiga Umar Faruk ya bud'e labule zai fita gaida iyayensu, da sauri ta durk'ushe qasa ta rintse ido tare da rufe fuska da kayan, kasa gaba yayi sai baya da yayi ya dawo cikin d'akin ya fad'a saman kujera kamar an turashi, yana hangenta ta labule bata tashi ba yasa ya tashi ya d'auki towel d'inta daya gani rataye ya bud'e ya cilla mata a jiki, sai lokacin ta mik'e ta d'aurashi sannan ta shigo, zaune tayi ta sake d'aukar waya ta danna wani kiran, kasalance tace ,

"Kina asibiti ne?"

Shiru alamar tana saurare kafin tace "wallahi zazzab'i ne ke son rufeni, zanzo yanzu."

Aje wayar tayi duk yana kallonta amma baice komai ba, tashi tayi ta bud'a kayanta ta d'auko doguwar rigar atamfa ta saka tabi jikinta sosai kuma ta mata kyau, d'an kwali ta d'aura sannan ta d'auki qaramin mayafin daya dace da kayan ta aza a kafad'a, poshet (post) d'inta ta d'auka ta bud'a wata jakar ta d'ibi kud'i ta zuba a ciki sannan ta d'auki wayarta tasa takalmi ta d'auki turare ta feshe jiki dashi, takowa tayi har gabanshi ta tsaya tace "idan driver Mamie ya kawo min motar ka karb'a ka aje min ni zan hau taxi."

Zata fice yace "ki saka hijab d'inki."

Juyowa tayi tace "iko? wai iko kake so ka min? to ban tab'a fita dashi ba ba kuma zan fara yau ba."

Tsaye ya mik'e yana fad'in "kuma dole kisan cewa da dah da yanzu ba d'aya bane, wallahi ke baki isa ki zubar min da mutunci ba, idan kika fita a haka to mamaki da zulumi ne zasu hana mutanen unguwar nan samun shak'at, ace surukar malam Ahmad a haka, ina ba dani za ayi wannan fitsarar ba."

"Wato ma nice fitsararriya ko? to ba zanyi ba naga me za kayi, idan kuma zaka tursasani ne na gani."

Sallamar Ruk'ayya ce yauma tasa ya amsa tare da bata izinin shiga, yau ma gaishesu tayi sai dai Umar Faruk kad'ai ya amsa kamar dai jiya, aje kwanukan tayi ta fita abinta Khairat kuma ta juya har zata fita kuma ta tsaya ta sake kallonshi tace "idan iko kake so kaima a matsayinka na namiji, toka bari har figaggiyar matarka ta shigo gidan saika mulketa, amma bani ba *Hajia Khairat*."

Gyara tsayuwa tayi tace "duk da bana da ilimin addini, amma ka sani na kare mutuncina, kuma duk da bana da sani akai amma nasan abinda kayi jiya baka kyauta ba, ka raba dare a wajen amaryarka, kuma daga yanda ka shiga wanka a wannan tsohon daren ya tabbatar min da wani abu ya faru, amma karka damu na yafe maka badan komai ba saboda ni ba sonka nake ba, kuma bana qaunarka kamar yanda ba son auranka nake ba."

Bakinshi ne ya mutu dan haka dole yayi shiru yana kallo harta fita daga gidan, mutanen dake tsakar gidan kuma kowa kasa motsi yayi yana kallonta harta fita, sai dai Mamar Umar Faruk tayi niyyar fad'a mata gaskiya dan wannan ba abu bane mai yiwuwa, malam ma dake k'ofar gida suna tattaunawa da mak'otanshi yana ganinta ya d'auke kai dan karya nuna ma ya santa, amma dai shima dole yaji a ranshi zai tsawatar mata da kanshi, bata sha wahalar samun taxi ba ta d'auketa kai tsaye sai asibitin kud'i asibitin da suke da familly docteurn su, *Clinique d'an magori* kai tsaye bureaun docteur d'in ta shiga, kasancewar suna ganema juna sosai yasa ta kwantar da ita ta saka mata sΓ©rum (drip), tana kwance amma suna hira baka ce Khairat ce ba mai ganin dama kafin tayi magana.

*****************

Tana fita shima ya fito ya fara shiga d'akin Mama Maimuna ya gaisheta saboda shine farko, kuma an nuna musu duka iyayensu ne dan haka d'aya ne, yana fitowa kuma ya shiga na Mama Sa'a, abin mamaki shine cewa da tayi "Umar Faruk ya 'yata, da fatan dai ta tashi lafiya?"

Kallonta ya d'anyi a fakaice sannan yace "da sauk'i Mama, dan yanzu haka ma ta tafi asibiti, zazzab'ine ya rufeta."

"Ayya, Allah sarki yarinyar kirki, Allah ya bata lafiya."

"Ameen Mama."

"Ai Umar Faruk kayi dacen mata wallahi, Allah dai ya baku zaman lafiya."

"Ameen Mama." ya fad'a a d'arare.

Yana fita daga nan ma d'akin mahaifiyarshi ya nufa, bayan sun gaisa ne tace "Umar Faruk ina ne matarka ta fita tunda safe haka? kuma kana kallonta ta fita da wannan kayan, kuma naga duka yaushe ne tazo da har zata fara fita."

"Kuyi hak'uri Mama, duk ni naja muku, amma insha Allah zan d'auki mataki akan hakan."

"To shikenan, amma dai banda duka ko wannan muguntar taka ka kama bakin mutum ka murd'e ko mintsini, ka mata cikin ruwan sanyi harta fahimta."

Cikin dariya yace "to Mama."

Daga nan kuma yayi d'akin Baba kuma ya sameshi yana karin kummalo, kuma Abbakar da Aliyu ma duk sunje gaisheshi, a tare ya musu nasihar daya saba na suji tsoron Allah su kyautata ibadarsu, sannan su guji d'aukar hakk'in wanda Allah ya had'asu zama dashi kona minti d'aya ne, daga nan kuma ya sallamesu suka tafi Umar faruk yayi tunanin sai Baba ya masa magana amma yaji shiru, yana fitowa yaga motarta a k'ofar gida, fita yayi suka gaisa da driver wanda Mamie ta fad'a masa unguwar shi kuma yayi tambaya, makullin ya amsa driver kuma ya koma dan ya hau taxi, shima d'aki ya dawo ya aje mata makullin sannan ya zuba abinci ya ci, Ruk'ayya ya tura ta gyara d'akin ta kuma d'auko kwanuka da kazar da bata ci ba.

_Kuna wulak'anta min kaza faπŸ˜’_

Tunda ya nufi wajen aiki yake tunanin yanda mutane zasu kalleshi, kuma kam hakane ya faru dan yana shiga suka dinga zuwa suna masa wai barka, da qyar ya zauna mazauninshi Ishaq ya zuro kai yace "mutumina ina amaryar, ba dai ka hana ta fito ba?

Wata harara ya wurga masa yayi banza dashi, dan tunaninshi na gareta yana so yaji ya take a yanzun, gashi kuma baya da lambar wayarta, dubara ce ta fad'o masa daya tuna manager, kai tsaye bureaunshi ya nufa, yana bashi izinin shiga ya shiga ya samu wuri ya zauna, kai fa fara sosawa ya kasa magana.

Ganin haka yasa manager cewa "angon Hajiarmu, ya kuma kayi shiru? ina Hajiar tamu take? ko dai har yanzu baku gama cin amarcin bane?"

Wani tarr yayi da ido yace "kai manager, amarci fa? da Hajiar taku ? kamar dai ka mantata, nifa kaga ba wannan ne ya kawoni ba, lambarta ma nazo ka bani ina so zan kira."

"Me!? lambarta fa? kwananka nawa a matsayin mijinta? amma kace baka da lambar wayarta? anya Umar faruk."

Shiru yayi kawai yana jira ya bashi, ba yanda ya iya shima dole ya bashi lambar sannan ya fito yana doka mata kira, tunda taga lambar ta shigo wayarta taji gabanta ya fad'i ba gaira ba dalili, gashi kuma lambar sassauk'a hakan yasa ta birgeta, saida ta tsinke ya sake kira sannan ta d'auka, shiru dukansu sukayi kafin shi yace,

"Hello."

Lumshe ido tayi saboda yanda muryarshi ta daki kunnuwanta cikin nutsuwa, "hello." tace a matuk'ar sanyaye.

Shima dafe qirji yayi saboda wani irin bugawa da yaji yayi, da qyar yace "kina ina?"

"Mai gida kenan, ina asibiti har yanzu, sΓ©rum aka saka min."

Cike da nuna kulawa yace "subhanallah, amma kuma shine baki kira ba?"

"Dame zan kira? bana da lambarka ai, kuma kaima nasan yanzu ka samu tawa."

"Amma ai na samu, ki fad'a min inda kike yanzu zanzo."

"Ina Clinic d'an magori." tana fad'a ta kashe wayar, shi kuma yabi wayar da kallo.

Fita yayi ya hau mashin d'inshi ya koma gida sannan ya d'auki motarta ya tafi da ita dan ba zai dawo ba sai tare da ita πŸ˜‚kasan kuma ba zata hau *Utu utu* ba.

_Kuna ganin zata yarda ta taho tare dashi a motarta, ko kuma shi zai dawo a qafane ya kai mata motar kenan?_πŸ˜‚

_Luv u sis Alawiyya_😘
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


_Bismmilahir-rahman-rahim_

```My Meelat, wannan page taki ce ke kad'ai, i love you.```


2⃣4⃣


Saida ya kirata ta kwatanta mishi wajen da take, yana kaiwa kofar d'akin docteur d'in ta fito danta basu wuri, gaisawa sukayi kafin ta fice tana yaba mijin na Khairat, koba komai a yanda ta ganshi tasan zaiyi wuya Khairat ta rainashi, kallon juna sukayi lokaci d'aya kuma suka d'auke idonsu, zaune yayi bakin gadon ita kuma ta nad'e qafafunta, kallon ruwan yayi yaga harma sun kusa qarewa, shiru sukayi babu mai magana har wayarshi tayi qara, yana ganin Zuby ce sai yaji wani haushi ya kamashi, tunawa da yayi abinda ya faru, amma kuma sai yaji tausayinta a wani b'angaren ganin yanayin daya barota, muryar Khairat ce ta katse masa shiru da "ka d'auka mana, ko sai tayi hushi, zaifi maka ka lallab'ata dan ita kad'ai gareka."

D'auka yayi baice mata komai ba, a daqile yake amsa gaisuwarta, da qyar yace mata "ya kike, da fatan kinji sauk'i?"

Zuby dake gaban Mama tana kallonta tace "da sauk'i dai, amma fa har yanzu ina jin ciwo."

"Ayya, sannu kinji, zai bari insha Allah, yanzu ki kashe waya zan kiraki ina wani wuri ne."

"Ina kenan yah Umar?"

Saida

Please Login or Register in order to submit comment