Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan aikin da kake neman watsarwa a yanzun, to ka sani akwai dubbun nan mutanen dake qaunarshi kuma d'aruruwan mutane ne zasu so da burin samun kujerar daka tashi, dan haka kayi tunani kafin ka yanke hukunci."

Barinshi yayi tsaye yana tunanin abinda ya fad'a, ganin baida wata mafita data wuce ya zauna yasa ya ajiye jakar cikin sanyin jiki ya koma sale d'in bak'in, a hankali ya bud'e kofar yayi daidai da har sun gama tattauna abinda ya tarasu, kallonshi take sosai da mamakin abinda ya maidoshi, saida ta bawa bakin nata hannu sukayi musabaha sannan suka wuce, saida ta gama kallonshi shi kuma ya kasa cewa komai, wayarta ta dauka Habiba ta biyota da jakarta suka fita daga wajen, acessaire (lift) suka shiga Habiba na shirin rufewa ya kutsa kai ciki, tana ganin haka ta fito cikin zafin rai ta nufi matattakalar bene da sauri ta fara sauka, da sauri shima ya fito harda gudu gudu ya tari gabanta ya soma sauka ta baya yana kallonta yana fad'in "magana zamuyi dan Allah ki saurareni."

Bata saurareshi harta sauka suna kaiwa tsakiyar ma'aikatar ya sake tare gabanta yana fad'in "dan Allah ki saurareni, hak'uri zan baki...."

Marin daya sauka a kunci ne yasa yayi d'uf, dafe yake da kunci yana kallonta, itama shi d'in take kallo haka kuma duk mutanen wajen ita su suke kallo, kafin wani abu ya sake faruwa sai kuwa Faruk ya zabgeta da marin da yafi wanda ta mishi.

Dafe kuncinta tayi baki bud'e tana kallonshi saboda mamaki, kasa motsawa tayi daga wajen yayin da shi kuma ya d'ora mata da wani sabon bayani "wallahi ke baki isa ba kisa hannu ki mareni, akan me? saboda kawai muna k'asanki."

D'aukar kayanshi yayi ya bar ma'aikatar gaba d'aya, cikin fushi da ba zata iya misaltashi ba ta bar wajen, gudu take sosai a mota ba tare da tunanin wani abu ya sameta ba.

Tana shiga ko rufe motar ba tayi ba ta wuce cikin gidan da gudu, daf da k'ofar shiga ta fad'a saman mutum, kallon kallon suka tsaya yi tana gama gane waye ya rik'eta ta fizge jikinta tana tureshi baya, shi kuma murmushi kawai yake mata, cikin masifa da son sauke bala'inta a kanshi ta fara magana,

"Meye haka, kai mahaukacin ina ne? baka ganine da zaka bigeni harda wani tab'a jikina? to bari kaji wallahi yau duk uban daya tsaya maka a garin nan saika bar gidan nan, tunda bana ubanka bane."

Duk da maganganunta sun masa zafi amma daurewa yayi yace "bake kika kawoni ba, ba kuma zaki fitar dani ba idan banyi niyya ba."

Cike da gatsali tace "saboda uban kane ya gida gidan?"

Cike da hassala ya fizgo hannunta kamar zai had'ata da jikinshi yace "wai ke me yasa baki da wayo ne, me yasa duk abinda ya zo bakinki fad'inshi kike? ke dai kinsan ubana ba matsiyaci bane bare kice zaki min gorin da kike wa wasu."

Sake fizge hannunta tayi ta tureshi iya k'arfinta tace "banza kawai, wani arzik'i mahaifin naka yake da da har zaka fad'a min, to bari kaji yau dole ka bar gidan nan, dan ba zai yiyuba ka zauna kana kawo mana mata a gida ba bayan kasha giyarka."

Muryar Mamie ce suka ji tace "Khairat dama rashin mutuncin naki har ya kai haka? waike wace irin yarinya ce marar ganin girman na gaba da ita? me yasa kika zab'arwa kanki wannan kakkaussar rayuwar da ba zata kaiki ko ina ba a matsayinki na mace?"

K'arasa shigowa tayi cikin falo tana kallon uwar tace "nice ai ya kamata na miki wannan tambayar, me yasa kika auri mutumin da kinsan baya da hallaye masu kyau? sannan karki sake cemin bana da mutunci, dan inma hakane to gadone nayi"

Kafin tayi wata magana ta d'ora da "kinga, wallahi yaron nan ya bar gidan nan yau, idan kuma ba haka ba zansa Papa yayi rashin mutunci a gidan nan, idan kuma shiya kasa saboda yana tsoronki, toni da kaina zanyi kuma zaku sha mamaki."

A fusace ta rab'a uwar tayi d'akinta ta barsu nan, hawayen da suka fara taho mata ne tayi saurin saka hannu ta share tana kallon Mujahhid, murmushin yak'e ta masa tace "kana ji ko yarona, kayi hak'uri dan Allah k....."

Katseta yayi ya matso kusanta da sauri yana fad'in "karki damu Mamie, ba komai wallahi, zan tafi, amma ni ke nake tunani yanda zaki ci gaba da rayuwa a gidan nan cikin kad'aici."

Kallonshi tayi tace "a'a, karka damu dani, aini na saba, zan ci gaba da zama a haka, har lokacin da Khairat zata fitar da mijin aure, dan aurenta ne ya tsayar dani gidan nan."

"Shikenan Mamie, zan tafi, bara naje na had'a kayana."

Tana shiga d'aki ta jefar da jakarta ta k'arasa gaban coiffeuse tasa hannu tayi watsi da kayan dake wajen, matuk'a ranta a b'ace yake kuma tana so tayi abinda yafi wanda aka mata ciwo, a hankali ta fara zamewa a jikin bango tana sulalewa har takai qasa, fashewa tayi da kuka sosai, ta jima a gurin tana kuka har saida mai aiki ta bud'a d'akin zata shigo, cikin daka tsawa tace "ki fita ki bani wuri, bana son ganin kowa."


Abinda ba'a so ne ya faru, saboda tsananin damuwa da kuka yasa qirjinta ya fara matsanancin ciwo haka kuma kanta ya fara mata bala'en'en ciwon da tafi fatan mutuwarta a kanshi, jin haka yasa ta rarrafa ta bud'a coffre ta d'auki maganinta, duk da dishidishi take gani hakan ta duba amma bata ga ruwa ba ba a d'akin , k'arfin hali tayi ta tashi ta nufi k'ofa danta samu ruwan, tana kusa ga kaiwa kawai ta fad'i a guri numfashinta kad'an yake fita, hannayenta ne duk bisa kanta saboda yanda yake fizgarta, daga haka kuma bata sake sanin meya k'ara faruwa ba a gaba.


*Da misalin* 16:30 Papa ya shigo gidan, Mamie na zaune akan kujera cikin damuwa da tunanin halin da Khairat take ciki, ba tare da sallama ba kawai ya zauna kusa da ita yana fad'in "sannu da gida."

Cikin sanyin jiki da tabe baki tace "yawwa, sannu da shigowa?"

"Ba dai Khairat bata dawo ba?" ya fad'a yana cire hular kanshi.

Saida ta sauke ajiyar zuciya tace "bata wuce awa d'aya ba da fita ta dawo, tana d'akinta."

"Bacci take?"

A sanyaye tace "gaskiya ban sani ba, ta shigo kamar ranta a bace yake, harma suka samu matsala da Mujahhid wanda yayi sanadiyar komawarsa gida, amma tunda ta shiga d'aki bata fito ba, kuma mai aiki taje ta dubo halin da take ciki ta korota."

Jin tayi shiru yasa ya kalleta yace "ina jinki, sai akayi yaya?"

"Ba komai, har yanzu tana ciki."

Tsaye ya mik'e yana girgiza kai yace "ban san me yasa kike nuna mata rashin kulawarki ba kamar ba 'yar da kika haifa ba, da bake kika haifeta ba sai nace ba kya sonta, kinfi kowa sanin duk baccin da Khairat za tayi ba zata kai wannan lokacin tana bacci ba, amma ki kasa duba halin da take ciki."

Yana bud'e k'ofar ya k'arasa a guje yana fad'in "oh mon Dieu, Khairat, Khairat!!!."

Maida kallonshi yayi ga Mamie wacce ta shigo yanzu, cikin b'acin rai yace "kin gani ko, kin gani abinda kika jawo mana, wai me yasa kike nunawa yarinyar nan rashin kulawa ne? ki dubi sakacinki abinda yake nema yaja mana."

Mamie da bata san meya faru ba itama cikin fad'a tace "to miye anfanin kulawar da zan dinga nuna mata, naga kaima da kake nuna mata kulawar ba wani girmanka take gani ba, bare kuma ni Γ  banza...."

Duk da ta kai k'arshen aya amma saida ta dire kalmar ba daidai ba saboda tsawar daya mata, cikin d'aga murya yace "dallah ki min shiru, zaki kama min ita ne ko kuma burinki ta mutu?"

Qafafunta ta kama shi kuma ya d'auki duka rabin jikinta suka nufo da ita waje, ma'aikatan gidan na ganin haka suka fara tambayar lafiya meya sameta, biyarsu suke a baya har chauffeur ya bud'e musu k'ofar mota suka kwantar da ita a baya sannan suka shiga suka bar gidan, ma'aikatan kowa jini kan akaifa , ba zasu ce suna jin dad'i ba saboda rashin lafiyarta , amma dai sun san sun d'an samu hutu na wani d'an lokaci.

********************

*Faruk* ne zaune akan taburma shi da abokinshi *Ishaq*, yayin da wata dattijuwar mata mai kamala ke gefensu akan kujera yar tsugunno, sai kuma babban malamin dake tsaye ya tisasu a gaba yana fad'a akan aikinshi daya baro, cikin fad'a ya sake cewa,

"Kai yanzu badan baka da hankali ba, daga k'aramin abu sai kawai kayi hushi, kai gaka uban zuciya ko? to bari kaji wallahi wannan aikin idan har ka bari ya kubuce maka, to wallahi za kayi nadama da daka sani, kai kafi kowa sanin kaine kusan rabin k'arfin gidan nan, to idan kace ka daina aikin kenan duk yayanka ne zai had'a ya d'auki har nauyinka.?"

D'ago kanshi yayi yace "Baba bafa k'aramin abu bane, marina fa tayi a fuska, wallahi ko k....."

Tsawar da Baba ya masa yana fad'in "ta mareka d'in, nace ta mareka saime? idan baka rama ba mutuwa za kayi, kuma tun farko ai kai kaja komai."

"Dan haka ka jini da kyau, ka tashi yanzun nan ga Ishaq nan ya rankaka kuje ka sameta ka bata hak'uri, karka yarda ka rasa wannan aikin, in kuma kayi sake to ka sani, wallahi abincin gidan nan ma ka daina ci tunda kai sarkin zuciya ne, waika gaka *Umar Faruk* ko?"

Sake d'ago kai yayi yace "Baba, cewa fa kake naje na...."

"K'warai haka nake nufi, dole sai kaje ka bata hak'uri, in kuma ba haka ba to duk matakin dana d'auka kanka, kai ka siyo da kud'inka."

Sai lokacin mahaifiyarshi tace "in banda abin Umar faruk ma, kaida maganar aure ka keyi amma kake k'ok'arin aje aikin da shine gatanka."

"To, fad'a masa dai, tunda naga shi baya da hankali zuciya ce kawai yasa a gaba."

Ishaq ne yace "kaga, ba wani abin damuwa bane, yanzu ya tashi mu tafi mu koma service d'in mu samu manager, nasan insha Allah zai taimaka mana kamar yanda ya taimaka mana muka samu aikin nan da farko."

Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi kafin ya kalli Baba yace " kuyi hak'uri Baba, insha Allah zanje na bata hak'uri kamar yanda kuka ce."

Addu'a Mama ta bishi da ita da fatan samun dacewa, Baba kuma na sake jaddada masa ya tabbatar ya bata hak'uri sosai harta hak'ura, haka suka fito da niyyar tafiya ma'aikatar wajen manager.


Sun samu manager kuma Ishaq ya fad'a masa komai daya faru, yayi mamaki sosai dan baisan wainar da aka toya ba, yayi jimami sosai tare da k'ara tsorata Faruk akan karma ya fara tunkararta ya jira hukuncin da mahaifinta zai d'auka a kanshi ko kuma ita da kanta, baiji shakka ko d'ard'ar ba akan matakin da zasu d'auka, matsalarshi d'aya shine yanda mahaifinshi ya d'auka da zafi sosai, ganin baice komai ba yasa manager cewa,

"A gaskiya *Umar Faruk* ba zan yarda a dalilinka na rasa nawa aikin ba, kayi hak'uri, amma taimakon da zan iya maka na riga da nayi maka shi, shawara d'aya da zan baka kawai shine, idan har ta dawo d'aukar fansa to ka qasqantar da kanka, ka nuna mata kayi nadama kuma a bisa kuskuren rashin sanin ko wacece ita ka mareta, idan kayi sa'a ta iya yafe maka, amma gaskiya bana tunanin zata hak'ura, dan wallahi yarinyar nan rashin mutuncinta ya kai mak'ura, bata kallon kowa da idon daraja babu tausayi ko imani a zuciyarta, kuma tun ranar da mahaifinta ya mallaka mata masana'antar nan na fad'a muku dukanmu sai munyi hak'uri da ita, saboda kaushinta yayi yawa."

A sanyaye Umar faruk yace "zan jaraba na gani, bara naje bureau d'in nata."

Murmushi manager yayi yace "ta yaya kake tunanin zata zauna a wajen nan, ina jin a lokacin da naga tafiyarta to a lokacin ne abun ya faru."

"Kenan yanzu tana gida?" cewar Faruk d'in.

"Ina tunanin haka."

"Shikenan, zamu je har gidan, watak'ila ma tafi saurarenmu." cewar Ishaq

Faruk ne yace "a'a fa Ishaq, gaskiya bana so naje gidansu, idan taga haka zata san nadamu sosai, zata d'auka gaba d'aya na bada rayuwata wa aikin nan, hakan kuma zaisa ta qara wani rashin mutuncin."

"Muji ta d'auka a hakan in har ba zata koreka ba, meye a ciki?"

Kai Faruk ya girgiza yace "waiku me yasa ne kuke shakkarta har haka? mutum ce fa kamarku kuma mace mai rauni a kanku, me yasa zaku dinga tsoronta har haka, nifa wallahi bana son irin haka gaskiya, dan wannan ai bayar da maza kuke, yarinyar da da zaku bud'e mata ido sau d'aya dole zata fara shakkarku itama, amma duk kubi kuna wani tsoronta kamar ita ta halliceku."

Fuskar manager d'auke da murmushi yace "bawai muna jin tsoronta bane, sai dai ka sani kowane d'an adam a rayuwa yana buqatar ci da sha kafin ya rayu, to tamu k'addarar ta damka cin mu da shanmu ta sanadiyarta ne, ita kuma bata da kirki duk da bata jima a garin nan ba, amma na samu labarinta sosai kamar wanda yayi rayuwa a gidansu, dan ba tun yau muke tare da mahaifinta ba, kaga dole mubi a sannu."

Faruk ne ya tashi tsaye yace "zamu je gidan, ina fatan ta amince kodan saboda Baba."

Cikin tsokana Ishaq daya mik'e shima yace "da kana so amma kake wani nuna baka damu ba."

"Amma ai kaji me nace, ina fata ta amince saboda Baba." ya fad'a ba tare daya kalleshi ba.


Suna fita akan mashin d'in Faruk suka kama hanyar zuwa gidansu Khairat......

_Shin kuna ganin za suyi nasara kuwa? to wai zama su samu ganin Khairat d'in ko kuwa dai...???_

*********************


Suna zuwa k'ofar gidan suka tsaya suka sauka akan mashin d'in suka nufi k'ofar gidan, mai gadin gidan ne mai sanye da kaki irin na sojawa ya taresu yana fad'in "yadai malamai, daga ina, wa kuke nema?"

Ishaq ne yace "sannun ko, dan Allah munzo ganin Hajia Khairat ne."

Kallon tuhuma ya musu yace " Hajia Khairat? to tasan da zuwanku ne?"

Kallon juna sukayi tare da yin shiru na 'yan dak'ik'u kafin Ishaq ya sake cewa "gaskiya bata san da zuwanmu, mu daga service d'inta muke, manager ne ya turo mu saboda wani aiki daya d'an taso."

Kallonshi Faruk yayi saboda jin abinda ya fad'a , mai gadin ne yace "kuyi hak'uri mazaje, duk wanda ku kaga ya shiga gidan nan to an san da zuwanshi koda kuwa d'an uwane, kunsan gidan manyan mutane."

"Yanzu kenan babu wata dama da zata saka mu ganinta?" cewar Faruk.

"Gaskiya babu, dan Hajia Khairat ko tasan da zuwan mutun ma zata iya tsayar dashi a k'ofar gidan nan na tsawon awa uku, idan na barku kuka shiga zan iya rasa aikina."

Faruk ne yace "yanzu dan Allah to ya zamuyi muganta?"

Mai gadin ne yace "in dai abu mai mahimmaci ne, to zan iya fad'a muku wurin da zaku sameta, yanzu dai kunga ta shiga gida, kuma da alama ranta a b'ace ta shigo."

"To kenan ina zamu sameta?"

"Duk kwana uku takan je wajen casu, amma takamaimai wajen da take zuwa kuma wannan kuma ban sani ba, dan tana zuwa club da dama daga manya har qanana, yau kuma nasan zata fita saiku had'u acan."

Da mamaki Faruk ya kalleshi yace "malam, mufa a ma'aikatarta muke aiki, ba wani abu bane a tsakaninmu da ita ba, amma ta yaya zamu sameta a wannan wajen kuma fa sai cikin dare."

D'aure fuska mutumin yayi yace "kunga dan Allah kubar nan, taimako kuka ce kuma shi nayi muku."

Yana fad'a ya koma mazauninshi ya barsu tsaye, mashin d'insu suka hau akan hanya suna tunanin wata shawarar, amma Faruk yace shi bai tab'a zuwa gidan rawa ba ba kuma zai fara zuwa yau ba.


Suna zuwa gida suka fad'awa Baba yanda ake ciki, fafur Baba ya rufe ido yace bai yarda su tashi su koma, ganin basu son tafiya yasa Baba ya tisa k'eyar Umar faruk gaba yace su tafi, haka kuwa akayi akan mashin d'inshi suka tafi, amma wannan karan suna zuwa mai gadin yace musu an tafi da ita likita babu lafiya, da alama ma kamar babu rai a tare da ita, tabbas Umar faruk yaji ba dad'i kuma yana tsoron ace abinda ya faru tsakaninsu ne ya janyo faruwar hakan, likitar aka fad'a musu suka nufi can shi da Baba.


_Faruk ni dai a ganina da kun hak'ura da son ganinta kawai._πŸ˜‰


Cikin sa'a kuwa suna zuwa sukaga masu tsaron mahaifinta a kusa da d'akin da aka shigar da ita cikin gaggawa, kusa da d'akin suka tsaya amma ba suyi magana ba saboda ganin mahaifin nata nata kai komo a wajen ya gagara nutsuwa, duk da baisan mahaifiyarta ba amma da gani yasan ita ta haifeta saboda tsananin kamar da suke, kuma dama tun daga fatar jiki zaka san uwace tayi ba mahaifinta ba dake tillik'ik'e kuma bak'i wulik dashi,🀣 had'in gambiza ba, duk da akwai damuwa sosai a fuskarta amma dai babu alamun hawaye a tare da ita.

D'auke kai sukayi kamar ba wajensu suka zo ba, amma abin mamaki shine muryar Baba da sukaji yace "kina zaune hankali kwance, da alama so kike ta mutu ki huta ko? to ta Allah ba taki ba wallahi."

Tsaye ta mik'e cikin jin zafi tace "eh, so nake ta mutu na huta, kai a ganinka idan ta mutu ba zan samu salama ba? idan da abinda ya janyo mata wannan halin bai wuce kai ba, wallahi duk kai kaja mana halin da muke ciki saboda bak'in halinka, yarinyar nan tun tana k'arama ta fara fahimtar halayenka, amma hakan baisa ka daina ba, me kake so ta zama? wallahi ka sani alhakin lalacewar rayuwarta yana wuyanka ne, addu'a d'aya nake mata yanzu shine, kar Allah yasa ta fara shaye shaye da bin maza kamar yanda kake lalata 'ya'yan wasu."

Fizgota yayi daf dashi cikin hassala yace "ke ya isa haka, ke me yasa baki da kunya ne? a cikin mutane zaki nime tozarta ni, kuma ni ai nasan 'yata, wallahi ba zata tab'a bin maza ba."

Fizge hannunta tayi tasa gyalenta ta share hawayen idonta tayi murmushin takaici tace "kenan baka so ta fara bin maza ko, ka manta da fad'ar Manzo (S.A.W) ne, _cewar duk abinda kayi sai an maka_? kayi gaggawar aurar da ita, idan kuma ba haka ba to wallahi ni zan barka na koma wajen iyayena, dan ba zan iya supporter naji kona ga wani abu ya sameta ba."


"Ke marar mutunci, wallahi zai karyaki a warin nan, shashashar banza kawai."

Duk maganar nan yayita ne da d'aga hannu kamar zai mareta, zaburowa tayi tace "ka dakeni mana, ina jin tsorone ? dukanka wane irine ban gani ba ai sai dai kuma na gaba."

Hannu ya d'aga kam da nufin kai mata mari sai kawai ya tsaya cak saboda ganin Khairat d'in da aka shiga da ita ranga ranga amma ta fito da k'afafunta, kamar dai yanda suka taho da ita haka ta fito babu takalmi ba kallabi, kallon iyayen nata kawai take sai huci take saukewa, takowa ta farayi gabansu docteur kuma ya biyo bayanta yana neman ta tsaya dan farfad'owarta kenan taji hayaniyar iyayenta, saida ta tsaya gabansu ta kallesu da kyau sannan ta kalli drivensu tace "muje ka mayar dani gida."

Wucewa tayi mahaifin nata ya rik'e hannunta yana fad'in "gimbiyata, ina kuma zaki je ya jikin naki?"

Da iya k'arfinta ta fizgo hannunta tana mashi jan kallo tace "lache moi ma main." ta k'arashe da d'aga murya.

Wucewa tayi suka bi bayanta Papa na kiran sunanta harta shiga mota ta rufe, haka suka shiga motar ba tare da kowa yayi magana ba har suka kai gidan.

Faruk kam da Babanshi mutuwar tsaye sukayi, mamaki ya gama kashesu a wurin, tabbas akwai wasu abubuwa a cikin rayuwar gidan, da alama arzik'i ne Allah ya musu amma babu kwanciyar hankali.


_Wallahi da auren wani mai kud'in gwara auren talaka in dai da kwanciyar hankali, Allah ka k'ara mana kwanciyar hankali da ni'ima a qasarmu dama sauren qasashe baki d'aya._

*********************

Gida suka koma dan sunga babu alamun nasara, amma duk da haka Baba bai hak'ura ba yace koma da safe ya shirya ya tafi gurin aikinshi kamar yanda ya saba, watak'ila idan da rabo ma ba zata masa magana.


*Luv you guy's*😍
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_

_My BK, kiyi sauri ki dawo fa._

_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


_Bismmilahir-rahman-rahim_


*Manzo Allah tsira da amincin Allah su tabbata a garesa yace* " _Kaji tsoron Allah a duk inda kake_"
*Rawahu muslim*


3⃣

Tunda ta shiga d'aki wanka tayi ta saka kayan data saba sakawa wato k'aramin wando iya cinya da k'aramar riga, zaune tayi akan gado tana tunanin abinyi, har akayi sallah magrib da isha amma bata tashi daga in da take ba, wani tunani da tayi yasa ta tashi ta fito daga d'akin, duk da duka iyayen nata na zaune a falon amma babu wanda ta kula bare ta masa magana, farfajiyar gidan ta fita, masu tsaron mahaifinta ne zaune a kusa da mai gadi suna hira, tsaye tayi nesa dasu cike da raini tace "kuzo nan."

Kallon juna sukayi cike da raini suka tashi a kasalance suka nufi wajenta, tsaye sukayi kowa ya d'auke kai babu mai kallonta, cikin jin haushi ta daka musu tsawa "kai, ni kuke wa wannan kallon? to ku saurareni da kyau kuji aiki zan saku."

Shirun da sukayi yasa ranta ya sake b'aci , a harrzuk'e ta shak'o uwan rigar d'aya daga cikinsu tana fad'in "kai matsiyacin banza, ku har kun isa ina magana daku kuna wani d'auke kai, ko kun manta k'ark'ashin mahaifina kuke, kufa ba komai bane face maqasqanta wanda suke wuni dare da rana a bayan iyayenmu domin tsare lafiyarsu, yaushe kuka fara tunanin kuna da matsayi da har zaku rainani?"

Mai sauk'in cikin sune yace "kiyi hak'uri Hajia, ki fad'i aikin da zamu miki."

Tureshi tayi yayi baya baya kamar zai fad'i sannan ta kalli wanda yayi maganar tace "ku nutsu ku jini da kyau, akwai wani saurayi da nake so ku d'auko min shi gobe, ina so ku kaishi d'aya daga cikin gidajen Papa, idan kun d'aukoshi saiku kirani zan sameku acan, amma kafin nazo ku tabbatar kun canzamin kammaninshi ta yanda ba zai iya gane kanshi ba bare kuma wani."

Da hannu ta nunasu tace "kun fahimta?"

D'aya daga cikine yace "amma ta yaya zamu iya ganeshi kenan?"

Sai lokacin ta tuna da hakan, a wulak'ance ta kallesu tace "ku jirani anan, yanzun nan zan samo photonshi."

Binsu tayi da harara tare da fad'in "banzaye kawai marasa anfani."

Tana wucewa wanda ta shak'e ma wuyan riga yayi wani huci tare da rik'e gudu yana kallonta, a hassale yace "wallahi saina ma yarinyar nan rashin mutunci ta yanda gobe ba zata sake sha'awar wulak'anta wani ba, dan muna aiki qasan mahaifinta bashi ke nuna maqasqanta bane kamar yanda take d'auka, wallahi na gaji dan abinda take mana ko wannan banzan mashayin uban nata bai isa ya mana ba bare kuma ita banza."

D'aya daga cikine yayi dariya yace "toya zamuyi tunda Allah ya d'orasu akanmu, kuma da kake cewa zaka mata rashin mutunci, ita fa 'yar akuya kai kasan haka, kenan me kake tunanin yi mata?"

Da sauri ya bashi amsa da "dukan tsiya zan mata wallahi har saina sab'a mata kammaninta."

Shak'iyin cikin ne ya lashe baki tare da d'an cije leb'e yace "ku naku duk wasa ne, irin yaran nan ai duka baya gyarasu, karfa ku manta gatane ta gani shi yasa take abinda take so, ni wallahi ban tab'a jin wai na daketa ba, dan duka ba shine mafita ba."

"Miye mafita to? danni dai na gaji da rainin hankalin yarinyar nan."

Saida ya kalleshu yana murmushi kafin yace "kona fad'a ma ba zaku iya ba, dan haka ku barni kawai ni zanji da komai."

"Kamar ya ba zamu iya ba? ka fad'a in dai har za muyi maganinta wallahi za muyi."

Sake kafesu yayi da ido yace

Please Login or Register in order to submit comment