Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da *KHAIRAT MANI BUKAR* Papa da kanshi ya wakilci Umar Faruk, anan ango ya tattara duk abinda yake da aka biya sadaki, malam kuma ya wakilci Khairat.

_Farin ciki_πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ€barkanmu 'yan uwa, musha biki lafiya.
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

*ALHAMDULILLAH KASIRAN, ALHAMDULILLAH ALA KULLI HAL*


_Bismmilahir-rahman-rahim_


1⃣8⃣


Ana gama d'aurin aure sai kuma labari yasha bam bam, amma a wajen Papa farin cikine zalla yake saboda faruwar hakan, Papa ne ya keb'e da ango da Abbakar da kuma Baba yana tambayar lokacin da zata tare, Umar Faruk dai cewa yayi duk lokacin da suka shirya, amma Baba yace a basu sati d'aya, sosai Papa yaji dad'i ya kuma ce ya bawa Umar Faruk kyautar gidan da zasu zauna da kuma mota, murmushi Umar faruk yayi yace "wallahi bana buk'atar komai, shi yasa ma na fad'a maka koni waye dan matsayinmu ba d'aya bane, ba zan bar gidanmu ba, kuma ina da wajen da zan ajiyeta, idan kuma taga hakan bai mata ba, toni banda matsala tun kafin tafiya tayi nisa zan iya sss..."

Bai k'arasa ba saboda taushe mishi baki da Abbakar yayi, Papa ne yace "ba komai Umar faruk, ai ba sai ankai ga haka ba, ko rumbu ka ajeta dole ai zata zauna, mudai muna godiya sosai."

Papa ne yama Umar faruk iso a cikin gida yaga sauran iyaye da kakannin Khairat ya gaishesu, abinka ga idan Allah ya aiko abu, duk uwayen masu hankali idan suka kalli Umar Faruk sai suji ya kwanta musu a rai saboda hankali nutsuwa da kunya, haka suka kamo hanyar komawa gida yana wasi wasi yana ji kamar yayi kuskure hukuncin daya d'auka.

******************

*Khairat* na d'aki tare da k'awayenta tanti (aunty) Safiya ta shigo ta fita da ita bayan ta rufeta ruf da daren amare bleue wacce ta mata kyau, babban falon da Papa ke sauke manyan bak'inshi suka shiga, duk da kanta na qasa kuma cikin dara amma saida taga yawan mutanen dake d'akin, gaba d'aya kannan da yayun mahaifinta ne, Mamie kuma dama ita d'aya ce ga iyayenta, hakan yasa sai Safiya da *Ramlatou* itama cousine d'inta ce, sai kuma matar margayi babansu Papa da kuma Mammie, zaunar da ita tayi a tsakiyarsu sannan itama ta zauna.

*Nan fa* aka fara sambado ma Khairat nasihoji ta ko ina bayan sun fad'a mata yanzu ita ba budurwa bace mai aure ce, kuma ita ba matar Muzaffar bace, matar *Umar Faruk ce*, an jawo mata ayoyi hadisai da kuma karatun *duniya*, sosai nasihar ta shiga jikin Khairat sai gata da kuka tare da bawa kowa dake wurin hak'uri na ayafi juna, dan duk rashin kunyarta bata kai tama mutanen dake wajen ba saboda girma da matsayinsu gareta, haka suka bita da sa albarka bayan ta musu alk'awarin bin Umar Faruk sau da qafa, tanti Safiya ce ta mayar da ita d'akinta.

Tunda ta zauna ta fara wani sabon kuka dan babu yanda za tayi ne kawai ta amsa musu, amma ko kad'an Umar Faruk baya da tsari irin na mazan da take so (a cewarta fa)😎, gashi kuma baya da komai hasalima a qarqashinta yake samu, to tayaya zata rik'eshi a matsayin miji, gaskiya zata hak'ura taje gidanshi danta musu biyayya, amma dole zata dawo dan rainine ma a had'ata da wani wai Umar Faruk, haka dai bayan 'yan d'aurin aure sunsha lagwadarsu wasu har sun tafi da guziri, aka fara biki gadan gadan aka sha casu sosai.


Tun yamma mutane suka fara watsewa zuwa dare kuma babu kowa sai bak'i da suka zo, kowa ya kwanta dan yayi bacci ya huta gajiya amma banda Khairat dake tunanin yanda rayuwar aurenta zata kasance, yanda taga safe haka taga rana ba tare data rintsa ba, kiran sallah asuba kad'ai yasa ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan ta kwanta rama baccin da bata samu tayi ba.

******************

*A b'angaren* Umar Faruk kuma suna shiga gida yanda duk suka shiga da kazar kazar amma banda shi yasa mahaifiyarshi ta fara tambayar lafiya, fad'a mata yayi ita da yan uwanta (matanshi guda biyu) su sameshi d'akinshi, ba b'ata lokaci suka hallara tare da Abbakar da UmaririπŸ˜‚, nan Baba ya fad'a musu abinda ya faru sannan ya d'ora da "wannan na tabbata itace k'addarar yaranku, kuma wannan abun *rubutatten al'amarine* da ubangiji ya rubutashi tun kafin a samar dashi kanshi Umar d'in, dan haka ku shirya tarbar sarakuwarku ban da rana irin ta yau insha Allah, sannan ku saka musu albarka."

Saida suka gama jimami sannan mahaifiyarshi ta sauke ajiyar zuciya tace "gaskiyane malam, kuma insha Allah ba za'a samu matsala daga garemu ba, kuma muna musu fatan alkairi Allah ya basu zaman lafiya."

"Ameen ameen." cewar malam kafin ya kalli sauran yace "ku kuma me zaku ce?"

Tab'e baki *Sa'a* tayi tace "ah to me zamu ce, tunda kun riga da kun gama yanke hukuncinku."

Mik'ewa tayi ta kama hannun *Maimuna* tana fad'in "nifa ba zan iya zama wajen nan ba."

Itama Maimuna saida suka mike ta kalli Umar Faruk da kanshi ke qasa shi abin duniya ma ya dameshi tace "wallahi dai kayi abin kunya, in banda kwad'ayin dukiya ta uban yarinyar nan, ince kaine nan kazo kwanan baya kana huci akan ta mareka kuma ka rama, shine yanzu dan tsabar rashin zuciya wai kai uban taimako ka taimaketa, kai yanzu ba abin kunya bane a wajenka ace ka auri macen da wasu garada suka raga?"

Sa'a ce tace "ke rabu dashi dan Allah, yana tunanin zai samu abin duniya shi yasa, amma ka sani ba lallai ka mori abinda za'a baka ba, dan cutar da waccen ya guje ma kai zata sama, wannan itace k'addararka."

Bushewa sukayi da dariya suka tafa hannu suka wuce abinsu, ba sabon abu bane wannan dan haka babu wanda ya dama a cikinsu, Baba ne yace "Umar Faruk."

D'agowa yayi ido jawur kamar zai fashe da kuka yace "na'am Baba."

"Kayi hak'uri kaji, wallahi Allah ba zai barka haka kawai ba saiya dafa mata, kuma ni nayi farin ciki da abinda kayi, kuma nayi alfahari da kai a matsayin D'ana, Allah ya maka albarka."

"Ameen Baba."

Mama ce tace "to a ina zasu tare?"

Baba ne ya kalli Umar Faruk d'in shima kallonshi yayi, cikin muryar tausayi yace "Mama ba zan iya barin gidan nan ba, idan sunga nan ya musu, to su kawota idan kuma ba haka ba, to gaskiya sai dai mu rabu, danni dama kawai saboda na fitar dasu daga halin da zasu shiga nayi."

Mama ce tace "haba Umar Faruk, me yasa zaka fara maganar rabuwarku tun yanzu, bana so ka daina, kuma ba komai ai sai a qarasa gyara abinda ya rage, idan har ya musu saisu kawota nan d'in."

Abbakar ne yace "Mama, saida fa mahaifinta yace zai bashi gida da mota, amma yaron nan da taurin kai yak'i amincewa."

Umar Faruk ne yace "idan na amince na amsa kenan me nayi? me kake so al'umma suce a kaina? na aureta saboda dukiya? to wallahi babu abinda mahaifinta zai bani a duniyar nan na amsa, ni taimako nayi *jihadi* nayi na auri 'yarsa, dan haka bana buk'atar komai daga gareshi."

Tashi yayi ya fita daga d'akin Baba kuma ya kalli Abbakar yace "nifa naji dad'i da bai karbi komai ba, dan yanayin haka jama'a za suce dama abinda yasa yayi taimakon kenan, duk da bansan yarinyar ba nasan dai tana da rawar kai, kana ganin idan ya amshi wani abu daga mahaifinta zata yarda ya tank'warata a matsayinshi na mijinta?"

A hankali Abbakar yace "kuma hakane gaskiya, zata rainashi ne ma."

Mama ce tace "nidai wallahi a tsorace nake, dan zamanshi da yarinyar nan fa akwai matsala."

"Wace irin matsala kuma?" cewar Baba.

"Kaifa kasan halin Umar Faruk da zuciyar tsiya, ina jin tsoron yanda zasu zauna gaskiya ba tare da sun samu matsala ba."

"Kinga dan Allah, ki cire tsoro a ranki sannan ki bishi da addu'a, insha Allah komai zaiyi daidai."

"To Allah ya yarda."

Baba ne ya sake cewa "yanzu to me zaku shirya? biki za kuyi ko walima."

"Kuma dai?" inji Mama.

Cikin dariya Baba yace "ban gane kuma dai ba? kina ganin zamu zauna hakane ba muyi komai ba bayan amaryar da muka samu a sauk'ak'e, kema kinsan dole za muyi koda walima ce mu godewa Allah."

Abbakar ne yace "ina ga ayi walimar zaifi, kunga sai ayi wa'azi ma tare da musu addu'ar zaman lafiya."

Mama ce tace "gaskiya kam shawarar tayi, to yaushe kenan?"

Baba ne yace "ayi ranar juma'a, tana gobe zata tare."

"To Allah ya nuna mana."

"Ameen." Baba da Abbakar suka amsa.

Suna fitowa Abbakar yaga matarshi a tsakar gidan tana shirin d'ora abincin rana , saida ya tsaya gabanta yace "ashe haka bakinki keda k'arfi, lallai Allah ya miki baiwa, tunda gashi abinda kika fad'a ya faru."

Duk da gabanta ya fad'i dan bata fahimceshi ba haka tace "lafiya, meya faru, mena fad'a kuma?"

Murmushi yayi yace "da zamu fita ba kince Umar faruk zai sace amarya ba ko a d'aura dashi?"

Dafe qirji tayi da k'arfi tace "me Umar d'in yayi?"

Dariya yayi ya nufi kewayensu dake kusa da d'akin amaryar Umar ZubyπŸ˜‚yana fad'in "dashi muka d'aura auren."

Wata irin bud'a ta rangada data sashi tsayawa cak yana kallonta, wato ita farin cikinta ma harya kai haka, wucewa yayi ita kuma da gudu ta lek'a d'akin Umar daya cire kayan jikinshi ya kwanta, amma ganinshi ba riga yasa ta dawo baya ta koma ga aikinta.

Umar Faruk kuma in banda tunanin irin kuskuren da yayi babu abinda yake, ji yake kamar fa ya sauke ma kanshi nauyin daya d'auka ya aza ba tare da an tilastashi ba.


Tunda kannanshi suka dawo daga islamiyya aka fad'a musu suma dai murna suke yayansu yayi aure, nan kuma Mama ta siyo goro ta bawa yaran suka dinga rabawa makota ana fad'a musu Umar ne yayi aure, haka ma a waya Mama tasa Rukayya da Ali suna kiran yan uwa suna fad'a musu, wani yaji dad'i wani yaji haushi, dan ma ba'a fad'a musu wacece amaryar, duk da a kurarran lokaci ne amma zama lafiya da mutane da Mama keyi yayi tasiri sosai a yau, dan gidan turuwa aka dinga yi ana zuwa tayasu murna, Umar Faruk kuma ganin ba za'a barshi ya huta ba yasa ya sake shiri ya fita zuwa gidansu Ishaq dake kusa dasu.

*****************

Tunda Ruk'ayya ta kira tanti *Ma'u* (Mamar Zuby) ta fad'a mata ta fara bala'i tun a waya, ganin haka yasa Ruk'ayya kashe wayar taci gaba da kiran wasu, duk da haka bata hakura ci gaba tayi da masifa ita kad'ai Zuby kuma da taji meya faru kuka ta fashe dashi, Mama ko nata bala'i ko sauraronta ba tayi ba, jin kukan nata yayi yawa yasa tace,

"Dan ubanki rufe min baki kafin inci uwaki , yar banza kawai duk bake kika jawo ba, Umar Faruk wace irin jaraba ce baiyi ba ki bari ayi aurenku amma kika k'i yarda, waike sai kin gama jarabawarki, to yanzu gashi nan ya samu dama kuma yayi anfani da damarsa, yanzu kafin wata biyu yayi a d'aura aurenki dashi ita lokacin ta fara laulayin ciki, kinga ta riga ta tsere miki."

Zaby na jin haka ta sake fashewa da kuka tace "na shiga uku Mama, yanzu Umar faruk saiya had'a jikinshi da wannan tsohuwar kilakin."

"To me zai hana, macece fa kuma shi namiji, namijin ma rik'akk'e.

"Wayyo Allah, dan Allah Mama ki taimaka min wallahi ba zan iya jura rasa Umar Faruk ba, Mama kinsan ina sonshi sosai, bana so wata ta rab'eshi ma bare harya had'a jikinshi da wata."

"Uwarki ma, yo wane irin taimako zan miki? ai kin riga da kin cuci kanki."

"Dan Allah Mama kiyi hak'uri." kwance tayi tana kuka hakan yasa taji ba dad'i, tadata tayi ta zauna tace "kwantar da hankalinki kinji, Umar fa d'an uwanki ne kuma naki ke kad'ai, sai kinso ne zaki bashi dama harya kusanci wacce karuwar sauran sojawa (da yake Zuby ta fad'awa Mama komai akan Khairat d'in tun ranar da Umar ya d'aga mata murya akanta.)."

"Kamar ya Mama, ban fahimta ba?"

Murmushi tayi tace "idan da zaki yarda da sai nace a d'aura aurenki dashi ranar juma'a da za ayi walima, to daga nan fa sai labari ya fara shan bambam."

Murmushi ne ya bayyana kan fuskarta tace "da gaske Mama, kina ganin Umar zai yarda ya aureni ranar juma'a?"

"Umar Faruk d'in banza, ni uwanshi nake iko dasu, dan haka kwantar da hankalinki tsaf za'a d'aura aukenku."

"Wallahi Mama na amince, danni bana so na rabu dashi."

"Ba zaku rabu ba, amma fa ki sani ba zaki tare a gidansa ba har sai munga kamun ludayinshi a matsayinshi na me mata biyu, kinga zaki samu damar raba tsakaninsu ta zaman da za kiyi anan, sauran karatun kuma na biya miki shi daga baya."

Alk'awari ta mata gobe za taje gidan ta sanar dasu halin da Zuby take ciki, dan haka kawai a d'aura musu aure.

πŸ€”πŸ€”πŸ€” _Mata biyu_

*********************

*Muzaffar* manyan duniyaπŸ˜‚ wallahi dariya yake bani,😎 abokananshi na zuwa gidan suka fara balbaleshi da masifa, wannan bai dameshi kamar da wani yace "dallah ku rabu dashi, tunda shi bai aureta ai wani ya aureta ko."

Da firgici ya kalleshi yace "me kace, wani fa ya aureta?"

"Kwarai, wani ne a cikin taron auren yayi *jihadi* ya rufa mata asirin da kai kake kokarin tona mata, kuma yanzu Khairat ta zama *matar Umar Faruk*, dan haka zaifi maka kaje ka samu mahaifinta danya biyaka duk abinda ka kashe a kanta."

"Kutumar uba, wane dan haune ya auri *matata*? wallahi k'aryane , babu wanda ya isa ya auri Khairat ina raye, na riga dana tsara rayuwata da ita kuma ita kad'ai nake tunani, dan haka dole a kwance wannan auren."

Ire iren irin wannan magnganun yake tayi duk suka watse suka barshi yana sambatu, bai tab'a tunanin yana son Khairat haka ba sai yau daya rasata, dafe kai yayi da hannu yace "na shiga uku, Basta ka cuceni, gashi banma san ina kake ba yanzu, Allah ya tsine maka albarka shege tsinanne."πŸ˜›

Yan uwa da iyayenshi takaicine ya hanasu zuwa inda yake, haka baki kowa ya tattara kayanshi ya koma inda ya fito rai a b'ace, shi kuma damuwa ta mishi yawa saida ya zubar da hawaye kad'ai yaji dama dama, haka ya wuni cikin d'akinshi bai fita ba bai kuma cire kayan jikinshi ba har yayi bacci dasu tare da daukar dangana da komai daya kashe akan Khairat amma ba da ita kanta ba, dan har yanzu yana ji zai iya samunta tunda a tunaninshi tana sonshi.

_A banza man kare_😏

******************

Umar Faruk na baccin da bai jima da d'aukarshi ba k'aninshi *Sa'ad* ya shigo ya tasheshi wai tanti Ma'u na kiranshi, gabanshi ne ya shiga fad'uwa dan sai lokacin ya tuna wata aba wai ita Zuby, haka ya tashi ya sanya doguwar riga ya fito yana tunanin idan aka daura aurenshi da Zuby ya zama *mijin mace biyu* kenan, zaune ya samesu a d'akin Mama tare da Baba, wata harara masa tace "sannu ango."

K'asa ya zauna yana shafa kansa yace "ina kwana."

"Humm." cewar tantin tana kallonsa.

Gyara zama tayi ta kalli su Baba tace "to ni dama ba wani abu bane ya kawoni sai maganar Umar faruk da Zubeida."

Rudududu yaji kayan cikinshi sun kada , yawu ya had'e ya daga kai ya kalleta, ci gaba tayi da "tun jiya da Zuby taji abinda ke faruwa ta daga hakakinta da nawa, har yau kuka take tak'i ci tak'i sha, daren jiya da zazzabi ta kwana gashi yau ma tak'i hakura, maganarta d'aya shine zata rasa Umar Faruk, shine nace to da a tsaya haka me zai hana a daura musu aure? tunda dai dama an gama komai lokaci kawai ake jira, hakan zaisa ta samu tabbacin ba zata rasashi ba, amma shawara ce ya kuka gani?"

Mama da Baba tausayin Zuby ne ya kamasu saboda dole za taji ba dad'i saboda shak'uwar dake tsakaninsu, da firgici ya kalleta yana tunanin girman maganar data zo da ita, a ranshi ne yace "ni kum gidan uban wa zan kai mace biyu a wannan qarnin, a zanyi dasu?"

_Umariri kenan,πŸ˜‚kafi kowa sanin yanda za kayi dasu idan ka gansu gabanka._

Baba ya amshi tayin data zo dashi yace ba matsala, kuma za'a d'aura auren ranar juma'a, ita kuma tace ba yanzu zata tare ba sai bayan ta gama karatun, haka tanti ta koma gida cikin farin ciki Umar kuma ya kalli Baba yace "amma Baba, mata biyu a lokaci d'aya, duka ni d'in nawa nake da zan auri mace biyu, kuma idan suka tare ina zan ajesu? gaskiya Baba nauyin yamin yawa ba zan iya ba."

"Haba Umar faruk, da jarumta fa akasan mai wannan sunan, karka bari mana mata su baka tsoro da wuri haka, zaka iya da yardar Allah, kuma Allah zai baka yanda za kayi dasu insha Allah, zai dubi zuciyarka ya taimaka maka wajen d'aukar nauyin ko wacce."

"Maganar wuri kuma da kake, ai abune mai sauki, tunda itama Zubeida ba yanzu zata tare ba, kaga ita Khairat d'in dake uwar gida saika ajeta acan b'angaren daka gyara, d'akinka na yanzu kuma da muke tunanin saka k'annanka a ciki idan ka tashi, sai a gyara Zubeida ta shiga ciki, abinda zasu ci kuma wannan Allah ba zai hanasu ba, nasan za kayi k'ok'arin yin adalci a tsakaninsu, kuma zamu maka addu'a Allah ya baka ikon yin adalci a tsakaninsu."

Mama ce tace "Allah ma ya yardar maka kafin lokacin da Zubeida zata tare ka mallaki naka gidan na kanka."

Kallon Mama yayi yace "mallakar gida a wata biyu Mama?"

"Eh mana, kana wasa da yin Allah ne?"

"A'a." yana fad'a ya tashi jiki ba kwari ya shiga wanka ya fito ya shirya cikin qananan kaya, fita yayi ya gidansu Ishaq ya sameshi kwance yana bacci, ware hannu yayi ya kai masa duka, a tsorace ya farka yana ganinshi yace...
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


_Bismmilahir-rahman-rahim_


1⃣9⃣

"Umar Faruk! miye haka dan Allah?"

"Dallah malam tashi, wato kai duk girgizar qasarnan da ake baka ji kana nan kana bacci, ni ina can cikin ibtila'i kai kuma hutawa ma kake."

Gyara zamanshi yayi yana murza ido yana fad'in "lafiya, meya faru?"

Saida ya zauna shima akan katifa sannan yace "akwai matsala fa mutumina."

"Matsala tame kuma?"

Kallonshi yayi yace "maganar yaran nan ne mana."

Bushewa da dariya Ishaq yayi yace "ai koda kace yaran nan na fahimci da matarka da kuma budurwarka kake, dan kasan mu maza ko mace ta girmemu muna so muce mata yarinya."

Harara ya cilla masa yace "toni fad'a min a cikinsu wacece ta girme min? ka daina ganin wannan da kabri ga kuma tsayi, wallahi ba zata wuce ashirin da uku zuwa da biyar ba."

"Humm, nidai yanzu fad'a min me yake faruwa da kace akwai matsala? danni bana tunanin abin nan zai fara damunka tun yanzu, tunda Zuby nanan tafe."

"To ai akan Zuby d'in ne, tanti fa tazo gida kuma sun gama magana akan za'a sake wani d'aurin auren ranar juma'ar nan."

"Juma'a kuma? amma me yasa zasu mai dashi juma'a? bayan wata biyu ne nan gaba."

"Kaima kasan halin tanti, wallahi ni nasan dagangan tayi haka, kawai akwai bala'in da suke so su kunno min shi yasa tayi haka."

"Ai kuwa in hakane wallahi saika tashi tsaye, ka nuna musu kai namiji ne na gaske, dan inba haka ba sai kazo ka rasa yanda za kayi, wata rana ka kwana d'akina wata rana kuma kaje wajen Mama kana hawaye."

"Wa? ni Umar zanyi kuka akan mace tamin wani abu, ai kaima kasan halina, duk wacce tamin ba daidai ba wallahi daidai nake da ita, tsaf zan zane yarinya."

Dariya Ishaq yayi yace "sai dai Zuby, amma Khairat ba zata daku a hannunka ba."

"Wai wasa kake dani ko? gani kake tafi k'arfina ne? ai kuwa za kasha mamaki, dan sai nasa yarinyar nan tayi laushi fiye da tunaninka."

"Allah yasa, dan in haka ta faru kaine za kafi kowa cin moriyar hakan."

"Kai, karfa ka d'auka wata rayuwar jin dad'i zanyi da ita, taimak...."

Ishaq ya katseshi da "bana son cika baki mutumina, bari ya shigo tukun muga iya gudun ruwanka, nasan mata kuma zata iya canza maka tunani cikin qanqanin lokaci, dan haka bari har naga tafiyar taku sannan."

"Ai kuwa zaka gani."

Tashi Ishaq yayi ya d'auki doguwar rigarshi yasa ya d'auki maclean da brush zai fita yace "ka jira na fito saina rakaka wajen amarsu."

Dan k'uwa ya masa yace "amaryo ba amarsu ba."

Yana ganin ya shiga shima ya fito zai tafiyarsa ya had'u da Baban Ishaq zai fita shima, har k'asa ya zube ya gaisheshi ya amsa cikin sakin fuska tare dasa masa albarka, sannan ya d'ora "jiya sai mu kaji abin alkairi, gaskiya ka kyauta Allah ya maka albarka ya taimakeka a duka al'amuranka, saura wannan sakaran shima kasa ya samu mata yayi aure."

Dariya kawai yayi ya tashi tsaye shima tsohon ya wuce, saida ya koma gida ya d'auki mashin d'inshi sai dai bansan ina ma zashi ba, yau *lahadi* yau ne dama suke hutu a wajen aiki, mashin d'inshi ya tuk'a bai zame ko ina ba sai gidansu Zuby.


Taji dad'in ganinshi amma kishi yasa ta kasa bayyanawa, d'aki ta shige ta barshi zaune gaban tanti, ganin haka yasa tantin tace "tashi ka wuce ka sameta mana, gidan ai ba bak'onka bane."

Yana wucewa ta bishi da harara, zaune ya sameta a bakin gado ta had'e hannaye, zaune yayi kusanta yana kallon fuskarta, sun jima a haka kafin ya sake kallonta yace "amaryata hushi take dani?"

Da mamaki ta kalleshi tace "lallai ma yaya Umar, yanzu daga d'aura auren naka shine harka kaini matsayin amarya tun ma bata tare ba a gidanka? lallai da matsala."

Shima dai da mamakin ya bita da kallo, taushe zuciyarshi yayi yace "ko da ita ko ba ita, ke amaryata ce kuma kinsan haka."

Hawaye ne suka ciko idonta ta kalleshi tace "wallahi yaya Umar ni dama tun ranar daka d'aga min murya akan banzan yarinyar nan nasan kana sonta, kawai raina min hankali kayi ka nuna ba komai, shine yanzu wai za'a ce ta zama matarka ta farko bani ba, bayan lokacin da muka d'auka muna tare da kai, wallahi kaci amanata yaya Umar, tunda muke da kai ban tab'a kallon wani a matsayin saurayi ba na kare maka kaina,amma shine kai ka kasa hakan, dama ku maza h......"

"Dakata dan Allah." ya katseta.

"Mu maza me? mayaudara ko maciya amana? kinga ki hukuntani ni kad'ai saboda ni miki laifi, amma karya shafi kowa, sannan ni kaina bana jin abinda nayi laifine, saboda ni namiji kuma *mijin mace hud'u*, saboda nayi ta farko kuma zan aureki a matsayin ta biyu ni banga wani aibu a ciki ba."

"Sannan kinsan abinda ke tsakanina da ita, so bashi ya sani nayi abinda nayi ba."

Cike da rashin wayo tace "ba wani nan wallahi, idan da gaske taimakonta kake son yi, meya hana ka rok'i yaya Abbakar ya aureta, ko kuma shi Baban ya aurrr."

Qamewa tayi ta rintse ido tana jiran taji saukar hannun, Umar faruk kam daya d'aga hannu zai wanketa da mari tsayawa yayi saboda tunawa a cikin gidansu yake, nunata yayi da hannu yace "maganar data shafi ni dake, karki sake saka iyayenmu a ciki, idan ba haka ba ranki zai dinga b'acewa."

D'orawa yayi da "karki kuskura kice zaki raina min mata bare iyayena, ita ke gaba dake kuma dole ki bita in har kina son zama dani, in kuma ba haka ba to mu hak'ura da junanmu, dan duk abinda zai shafi mutuncina bana k'aunarshi, a yanzu kuma itace tabbas d'ita tunda ta shiga

Please Login or Register in order to submit comment