Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

titi, tana tunanin me zai faru, shima baice da ita komai ba suka d'auki hanya......

_Bara muji meya faru bayan fitarsu_

*************


Abdul waid ne yayi irin durk'ushin nan nakan tafikan qafafu da kulki a hannunshi yana zarewa Mama ido, a nutse yace "Mama, Mama, Mama, sau uku ko? ina ganin girmanki shi yasa ban dakeki ba tunda kika zo nan, amma yanzu kin kaini bango mafita d'aya itace nasa a lallasa minke, in kuma baki son a dargajeki to ki fad'a mana yanda akayi kika samu sarqar tunda kince bake kika d'auko ba."

Cikin rawar jiki da tsoro dan ganin ba sauk'i a al'amarin yasa tace "a'a yi hak'uri zan fad'a, wallahi zan fad'a maka gaskiya."

"Ina jinki Mama."

Cikin kuka tace " 'yata ce, sunanta Zubeida, wallahi ita ta d'auko bani ba."

Zunbur ya mik'e tsaye yace "bani adresse d'inta?"

Had'e hannaye tayi tace "dan Allah kamin rai yaro karka tona mata asiri, wallahi tana da aure kuma tana da kishiya, idan maganar nan ta fita wallahi aurenta zai iya mutuwa, nima kuma zan iya mutuwa."

A tsawace yace "tasan da auren nata kuma tayi sata, mu aurenta bai damemu ba, aikinmu kawai mukeyi, ki bani kwatancen gidanta." ya fad'a da sake d'aga murya.

Cikin kuka ta fad'a musu takwacen gidan malam, fitarsu Khairat ba wuya motar jami'ai tazo gidan, guba biyu daga ciki ne suka kutsa kai cikin gidan, a lokacin Zuby na zaune tana gurgurar tsamiya, saida gabanta ya fad'i data gansu, idon jami'in akan Mama Sa'a yace "sannu ko, dan Allah Zubeida muke tambaya a gidan nan?"

Ba Zuby ba har Mama Sa'a saida kayan cikinta suka murd'a, a duburbuce take kallonshi tana kallon Zuby da ido ya raina fata , cikin d'aga murya yace "Hajia dake muke magana kinyi shiru."

"Gata nan, wallahi gata nan, bani bace." cewar Mama Sa'a cikin harshen zarma, dan dama shi tafi iyawa.

Ganin sun tunkari inda Zuby take yasa Mama Sa'a tashi da dugu ta shige d'akinta, tun basu qarasa wajenta ba ta fashe da kuka tana kiran sunan Mama ta fito ta taimaketa, Saratu Mama da Mama Maimuna ne duk suka fito, Mama kad'ai tayi k'arfin halin tambayar "bayin Allah lafiya, me tayi?"

Shirun da sukawa Mama yasa dole taja baki tayi shiru, tsawa d'aya suka mata ta tashi ta d'auki hijabi tasa suka wuce, cikin qanqanin lokaci sai gata a prison (cell) tare da Mama, hannu ta d'ora a kai tana fad'in...

"Na shiga uku Mama kin cuceni, yanzu da wane ido kike so na kalli yah Umar, haka kawai kinja mana abin kunya, akan me zaki fad'i sunana kamar ba 'yar da kika haifa ba?"

Tsaye Mama ta mik'e tace "wallahi ubanki zaki ci idan baki min shiru ba, mahaukaciya kawai, dan ubanki ke ba banza ki kayi dani ba anan d'in kina can kina iskanci, shine ni kuma saina rufa miki asiri, to mu shirya d'aukar hukuncin da za'a mana, danna gama lura yarinyar nan 'yar akuya ce, ba zata tab'a sawa a fitar damu ba."

Kuka ta sake fashewa dashi tana fad'in "haka kawai na jawa kaina, yanzu ya zanyi da cikin dake jikina? kina nufin zanyi rainon cikine a magarqama kome? wallahi ni dai ban yafe ba."

Kwaf, Mama takai mata bugu a baki tana fad'in "ubanwa kike cewa baki yafe ba, ni Zubeida, ni?"

Murgud'a baki tayi ta kawar da kanta, suna haka Khairat suka qaraso, nan ta samu Papa ya hakimce yana jiran zuwanta, masu tsaron lafiyarsa ne suka sara mata alamar gaisuwa kafin ta zauna, bayan sun zauna Abdul waid yace "Khairat dama yanzu nake tunanin kiranki , saboda an samu wanda ta d'auki sarqar."

Kallon Umar Faruk tayi ta maida kallonta ga Abdul waid tace "an sameta, wacece, tana ina?"

Papa ne ya katsesu da "bana kiraki bane danna saurari haka, ina baki umarni da ki janye qarar nan sannan kisa a rufe qarar, wannan ba girmanki bane."

Kallon Papa tayi tace "amma P..."

"Amma me, kiyi yanda nace kawai."

Furzar da iskan bakinta tayi ta kalli Abdul waid da ido kawai ta masa alama, kai ya d'an jinjina yace "an gama."

Da mamaki Umar Faruk ya kalleta, shi girma da ikonta ne kawai ke qara bashi mamaki, wata takarda ya bata tasa hannu sannan ya kalli wani jami'i yace "ka fito dasu."


Da mamaki duka suke kallonsu kowa da abinda yake ayyanawa a ranshi, har suka tsaya gabansu cike da kunya dan sun kasa d'aga kai su kallesu, da qyar Umar Faruk yace "Zubeida, dama da ha...."

Papa ne yace "tunda kun sansu , kuyi hak'uri ku koma gida, bai kamata kuyi magana anan ba."

Kai kawai Khairat ke girgizawa yayin da Ruk'ayya ta rik'e baki, tsaye ta mik'e ta nunasu da hannu tace "na tabbata izuwa yanzu kun gama fahimtar abin kunyar da ku kayi, kunci albarkacin mahaifina wallahi, badan haka ba da sai kun gane shayi zalla ruwane, amma duk da haka nasan kun gane wacece ni, kuma in halinku ne nasan zaku koma, a wannan lokacin kuma zan muku d'aurin da goro ma saiya fiku kyan gani, daga qarshe kuma dole za'a shiga tsakanina daku, danna tabbatar ba alkairi kuke nema dani ba, kamar yanda jikina ke bani ba kun d'auki sarqar bane dan kawai ku siyar, ina fatan zaku gyara halinku in kuma hakan yaci tura to da fatan zaku kiyaye qara yiwa Khairat sata a karo na biyu."

Da harara ta bisu tare da tsaki ta fice daga wajen, Abdul waid ne ya bawa Umar Faruk sarqar yasa aljihu, bin bayanta sukayi shi da Ruk'ayya, Papa ma tashi yayi ya wuce da qyar suka rarrafa suka fita daga wajen, tun a bakin titi Zuby ta fad'awa Mama abinda ya faru bayan tafiyar Khairat gida, a wahalce Mama tace "muje gidana."


Taxi suka hau ta ajesu gidan Mama, suna shiga sukayi zaune kamar kayan wanki suna jajantawa kansu, Mama ce tace "ashe haka yarinyar nan take?"

"Humm, ai bata da mutunci ko kad'an."

Kafin Mama tayi magana Zuby tace "bama wannan ba, nifa akwai wasu maganganu da yarinyar ta fad'a min a ranar sun d'aure min kai sosai, amma nasan ke zaki sansu."

"Wace magana?" cewar Mama tana neman cire riga dan tayi wanka.

Maganganun da Khairat ta fad'a mata ta maimaita mata, cak Mama ta tsaya da cire rigar da take, da sauri ta juyo ta kalli Zuby ta kafeta da ido, ta kasa d'auke idonta kuma ta kasa magana, saida Zuby ta d'aga murya tace "Mama."

Zabura tayi ta sake kafeta da ido, "lafiya Mama?"

A hankali ta girgiza kai tace "ba komai, bara na fito daga wanka saiki tafi gidanki."

Harta d'ibi ruwa ta shiga bayi jikinta ba qwari, saida ta fara kwararawa kanta ruwa ta dawo hayyacinta, *wacece Khairat, ya akayi tasan sirrin dako 'yan uwanta basu sani ba, taya tasan wannan sirrin? shine dai kad'ai nasan abinda na aikata wanda nake tsoron duniya ta sani, inba shi ba me Khairat take nufi???* wannan sune tambayoyin da takewa kanta harta fito daga wanka, Zuby ma tattarawa tayi ta kama hanyar gida, da sand'a ta shiga gidan dan ba zata iya had'a ido da kowa ba, d'akin Mama ta nufa kai tsaye ta samu ta kwanta.


Khairat kuma daga nan gida suka dawo saboda takaici da zulumin abun, Ruk'ayya da Umar Faruk kuma babu wanda ya fad'i maganar a gida, d'aki take kwance tana karatu dan yanzu shi kad'ai ne ke cireta damuwa.


Ana sallah magrib kuma Mama tasa Zuby ta shirya tace ta koma d'akinta, ba gardama ta shiga ta hakimce tana sabgar gabanta, Umar Faruk na shigowa bayan sallah isha'i yaga d'akin bud'e da alama qarara tana ciki, wata shegiyar qwafa yayi ya cire belt d'inshi ya tunkari d'akin........


_Wallahi nima gidana zanje, wannan hushi haka Umar Faruk_πŸ˜‚

*Kuyi hak'uri da rashin cika alk'awari da nayi jiya, hakan ya faru ne saboda daukewar da wata tayi ina cikin typing.*
23/08/2019 Γ  12:51 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


*Allah Ka qara mana tsoronka*


_Bismmilahir-rahman-rahim_


5⃣1⃣


Daf da zai shiga d'akin Mama ta kira sunanshi, juyowa yayi yaga Mama tsaye a k'ofar d'aki, b'oye belt d'in yayi ya nufi wajen Mama, sunkuyawa yayi har qasa yana fad'in "gani Mama."

Saida ta shiga d'aki yabi bayanta daga tsaye tace masa "na mayar maka da matarka, dan Allah bana son jin wata hayaniya, kayi hak'uri da duk abinda ya faru, kaji?"

Jim ya d'anyi kafin yace "shikenan Mama."

Tsaye ya mik'e zai fita ta sake cewa "azumi ke tahowa,amma banga kana shirin tarbansa ba kamar yanda kake kowace shekara."

Ajiyar zuciya ya sauke yace "ina tune Mama, insha Allah za'a fara gudunar da komai kamar yanda ake kullum."

"To shikenan, Allah yayi albarka."

"Ameen, saida safenku." ya fito daga d'akin.

Saida ya harari d'akin ya wuce d'akin Khairat, tunda ba za'a barshi ya mata shegen duka ba, gwara ko hukunci ya mata wanda zata san ta b'ata masa rai, tsakiyar gado take ta mike qafafu ta jingina bayanta ta rufe da zanin rufa tana karatu ya shigo, bayan amsa sallamarshi ta bishi da "sannu da zuwa."

"Sannu." kawai ya fad'a ya fara cire kayan jikinshi, douche ya shiga yayi wanka sannan ya fito, wando iya gwiwa yasa ya feshe jikinshi da turare ya haura kan gadon, computernshi dake gefe ya d'auka ya fara aikinsa, ganin shiru babu mai magana yasa Khairat cewa "baka jin yunwa ne?"

"Ya zanyi idan ma ina ji, wa nake da da zai bani abinci naci?" shine abinda ya fad'a ba tare daya kalleta ba.

Jaye zanin rufan tayi ta fita daga d'akin, tununya ta d'ora a gas sannan ta shigo ta d'auki indomie ta dora mishi, ba jimawa ta gama dafawa ta juye a plate ta kawo masa, saida ta janyo tebur d'in har gabanshi ta aje masa, ruwa ta d'auko da lemu mai sanyi ta aje masa, kallonshi tayi ganin ko kallonta bayayi tace "bismillah yallab'ai."

Abinda bata sani ba, kaf kai da kawowarta a idonshi tayashi, ya kuma kalleta ne da idon rahama da qauna, aje computer yayi ya sauko da qafafunshi, cokalin ya d'auka yana kallonta yace "kefa?"

Kai kawai ta girgiza alamar a'a, fuska a d'aure ya janyo hannunta ya zaunar da ita akan cinyarshi, kafeta yayi da ido yace "me yasa ba zaki ci ba?"

"Naci abinci tare da Ruk'ayya." ta fad'a tana kawar da kai.

Hannu yasa ya juyo da hab'arta yana kallon fuskarta yace "Khairat, bansan da wane baki zan baki hak'uri ba, amma ina baki hak'uri daga gaba d'aya zuciyata."

Kallonshi tayi cike da yanga tace "manta kawai ya wuce, hakan da sukayi aiya nuna nice a samansu."

D'an lumshe ido yayi kafin ya bud'e ya fara cin indomien ba tare daya d'agata daga cinyarshi ba, yana ci tana shafar qasumbarshi kamar daga sama sukaji qarar Zuby.......


Tsakin da Umar Faruk yayi yasa Khairat kallonshi tace "yadai, kasan meya faru ne? kaje ka duba."

"Meye fa idan ba iskanci ba." ya fada yana ci gaba da cin abincinshi, itama sherewa tayi saida yaji hayaniyar mutane sannan ya d'auki singlet yasa ya fito, ganin mutane a k'ofar d'akin nata yasa ya qarasa cike da takon izza, Mama na ganinshi tace "ka d'auko makullin mota ka kaita asibiti, ina jin fa tayi b'arine."

Ba zaice yaji dad'i ba amma dai yasan baiji zafin barewar cikinta, dan a halin yanzu baya ma buqatar had'a zuri'a da Zuby, juyawa yayi a kasalance ya koma d'akin Khairat ya sanyo doguwar riga ya d'auko makulli ya fito, Khairat ma dai lek'owa tayi taga tanata birgima tana dafe ciki, sosai taji tausayinta lokacin da Mama Sa'a da Mama suka kamata zasu fita taga jini ya b'ata mata jiki, cike da rashin jin dad'i ta girgiza kai ta koma d'akinta, tana komawa d'aki ta kwanta ruf da ciki ta janyo computer Umar Faruk tana kallon aikin daya fara, kamar da wasa saita fara dora mishi tata fasahar zanen, bata daina ba har saida ta gama, kallon sabon sanfurin zanen takalman tayi tayi dariya, dan a ganinta babu abinda zaiyi dashi, bacci ne ya fara fizgarta har tana gwara kai ga computer, sulalewa tayi ta aza kanta daf da computer yayin da hannunta ke saman ceybor d'in, cikin kuskure saiko Khairat ta aika da sakon a shafin yanar gizo na compagnien da yake ma aikin.

*************

Koda suka je ma wankin ciki aka ma Zuby dan ciki kam ya b'are, duk wasu kudade da aka caza saida ya biya sannan yace zai koma gida, tunda dai ance saida safe a sallmeta, Mama bata hanashi ba tunda babu abinda ya rage Zuby kuma bacci take, amma koda aka kira Mama aka fad'a mata ta garzayo tazo, abin mamaki ko kallon Mama ba tayi ba wai ita tana hushi saboda bata je ta ganota ba, haka ma Umar Faruk bata kulashi ba kamar yanda shima bai kulata ba, Mama Sa'a kad'ai ta tambaya yanda ake ciki, ana fad'a mata tace su tafi gida ita zata zauna wajenta, hakan kuma ba qaramin dad'i ya musu ba, dan haka Umar Faruk ya dawo dasu.

*****************

A hankali ya shiga d'akin da sallama d'auke a bakinshi, da murmushi ya qarasa wajenta ya zura hannu zai gyara mata kwanciya, cak ya tsaya yana kallon computer dake gabanta da tsananin mamaki, d'aukar computer yayi danya tabbatar da abinda idonshi ke gane mishi, ai kuwa dai gaskiya idonshi ya nuna mishi, sanfurin daya aika an karba kuma ana tayashi murna, tare da turo mishi adadin wasu manyan kud'ad'e a account d'in daya bud'e bada dad'ewa ba, da sauri ya janyo sak'on daya tura ya gani, nan yaga sanfurin da aka tura, shi dai yasan bashi bane kallon Khairat yayi dake bacci abinta, dariya yayi ya aje computer kamar daga sama Khairat taji an d'auketa sama, cikin dubara ya azata bayanta yana juyi da ita tsakiyar d'akin,

"Wai miye haka Faruk?"

Fad'a mata yayi abinda ake ciki, itama murna ta tayashi kafin yasa tayi alwala suka dinga jera nafilfili har zuwa sallah asuba, yau kam sunyi karatu kuma yayi mamakin yanda bakinta ya fad'a sosai akan karatun, qara mata yayi sannan suka shirya dan tafiya wajen aiki, amma shi dole zai fara biyawa asibiti, suna hanya ya kalleta yace "saina biya asibiti fa."

"Ba komai." ta fad'a tana kallon gefen hanya.

Ba b'ata lokaci suka isa asibitin, a tare suka shiga ciki kafad'unsu na gugar juna, da sallama Umar Faruk suka shiga sab'anin Khairat data d'auke kai, tsaye tayi kofar d'akin ko kallonsu ba tayi ba, Umar Faruk d'in ne kad'ai ya zauna bakin gadon suna gaisawa, gaba d'aya sama sama suke gaisuwar dan kowa da abinda ke ranshi, Zabba'u ce tazo shigowa d'akin, ganin Khairat a k'ofar yasa ta shirya ta taqarqare ta bankad'e Khairat har saida ta fad'a bayan Umar Faruk dake kusanta, yar qaramar qara tayi tare da maqale wuyanshi sosai, jin a jikinshi ta fad'a yasa ta canza rik'on da tayi masa dΓ  salon shafa, kanta ta zuro ta wuyanshi tana kallon Mama da Zuby da suke fuskantarta, kashe musu ido d'aya tayi kafin ta d'ago tana kallon Zabba'u wacce ke tsaye Umar Faruk ma kallonta yake, murmushi ta mata tace "sannu."

Kamar jira take sai kuwa ta shak'i wuyan hijabin Khairat ba tare data shirya ba, kamar Umar Faruk ta shaka sai kuwa yayi zunbur ya mike tare da qwaqwale hannunta ya nunata da yatsa yace "karki sake dora hannunki akan matata, marar kunya kawai, meta miki to? bayan turowan da ki kayi mata bai isheki ba saikin ci mutuncinta a gabana, to ki kiyaye ni wallahi."

Juyawa yayi ya kalli Zuby dake zaune tana kurb'an pure water yace "nasan ai kinsan laifinki, kiyi qoqari kada ki bari wani ya sake jaza miki sabon laifin."

"Kai Umar Faruk, kana cikin hankalinka kuwa, dama abinda kazo fad'a mata kenan, kuma dan wulak'anci shine saida wannan zaka zo ganinta? kawai dan kana so kaci zarafinmu." cewar Mama.

A kaurare yace "hmm , Tanti, naci zarafinku fa ki kace? ai kune kuka gama cin zarafina."

"Mu kuma, wai yaushe ka zama marar kunya fitsararre ne? nidai ba haka na sanka ba."

Saida ya rik'e hannun Khairat cikin nashi yana murmushi yace "tun ranar dana samu soyayyar gaskiya, ranar na fara banbance tsakanin qarya da gaskiya, kuma ranar na fara sanin asalin masoyiyata, ranar dana samu wacce ta dace da rayuwata, matsayina, mafarkina, da kuma burina."

Hannunta Umar Faruk yaja zasu wuce ta juya ta kalli Mama ta sake kashe mata ido, wayarta ce ta sub'uce daga hannunta ta fad'i qasa hakan yasa Umar Faruk sakinta ta sunkuya ta d'auka, da murmushin mugunta ta sunkuya ta d'auki wayar tana d'agowa ta d'ora wayar a kunne kamar da gaske tana fad'in " Hello, Bala , ka sameni office za muyi magana da kai, eh akan maganar nan ba, ok saika zo."

D'auke wayar tayi tare da juyawa ta kalli Mama data sake baki da kunne tana saurarenta, wata kafirar dariya tayi ta juyo tare da gimtse bakinta dan kar Umar Faruk ya gani, bakin k'ofar kuma suka had'e da wata matashiyar likita mai sunan *Jamila* , da farin ciki suka mik'awa juna hannu ita da Khairat suka rumgume juna, sosai suka gaisa ana gaisuwar yaushe gamo saboda an jima ba'a had'u ba, saida sukayi musayan lamba sannan suka fita, dariya na takura mata saboda yanayin da taga Mama, suna cikin tafiya Umar Faruk yace "waye Bala kuma?"

Gimtsewa tayi tace "ba komai." ta fad'a.

"Ban yarda ba." ya fad'a yana kallonta.

A tak'aice tace "wannan Alhajin da muka had'u dashi ranar."

"Waye shi?" ya sake tambaya.

Cikin qosawa tace "ba komai fa, idan da wani abu ma ai lokaci zaiyi da zaka ji."

Wayarta ta fiddo ta fara aikawa Jamila sak'o kamar haka " k'awata naso na miki magana tun acan, amma muna buqatar sirri."

Maido mata tayi da fad'in "k'awata baki da dama, ina fatan dai ta samu?"

"Sosai kuwa, wata alfarma nake nema a wajenki idan zan samu?"

"Fad'i kawai, kinsan umarninki abin bine."

"Na gode, aiki nake so kimin akan yarinyar nan dake qarqashin kulawarki."

"Ina jinki."

"Ina so ne ki rik'esu har nan da kwana biyu."

"Me yasa, meye tsakaninki da ita?"

Maida mata tayi da "ita d'in kishiyata ce, kuma tana min kallon raini, ni kuma bana so, ina so tasan wacece ni."

"Shegiya qawata, ashe zaki iya zama da kishiya? aina d'auka baki da ra'ayin auren mai mata, amma karki damu ba zai gagara ba insha Allah."

"Na gode qawata, zaki ji nauyi a lalitarki."

"Da kyau qawata, shi yasa nake sonki wallahi."

Suna gama message Khairat ta fara qoqarin tura mata da kud'i, ganin an nuna mata ba zata iya cire kud'i ba yasa tace "ban gane ba, wannan wane salon iskancin ne kuma?"

Kallonta Umar Faruk yayi yace "meya faru?"

"Kud'i zanyi transfert yanzu ana nuna min ba zan iya fitar dako sisi ba."

"Wataqila kin cinye wajen siyan sweet da kayan jiki." cewarshi ba tare daya kalleta ba.

"Haba dai, kasan nawa ke cikin asusu nan kuwa?"

Wayarshi ya fito da ita ya kalleta tare da bata wayar yace "ki turawa duk wanda kike so kuma ko nawa ki kayi niyyar turawa."

"A'a ka barshi kawai, zanje bankin naji meye matsalar."

Murmushin gefen labb'a yayi yana kallonta yace "wane banki kike ajiya?"

"Bank centrale." ta bashi amsa.

Nanma wani murmushin yayi ya fara danna wayarsa , 'yan daqiqu ya fara magana " mutumina ya kake?"

Jim yayi yana sauraro kafin yace "lafiya lau wallahi, dan Allah kana aikine yau?"

Nanma shiru kafin yace "zan turo maka da lambar wani asusu ina so nasan nawa ne a ciki, dan ana so a cire kud'i bayayi, ina so nasan meye matsalar."

Jim ya d'auke wayar daga kunnanshi ya bata wayar yace tasa lambar asusun, tura mishi yayi bayan wasu mintina ya sake kira, nan ya fad'a masa mai girma Mani Bukar ne yasa aka rufe asusun, take ya fad'awa Khairat yanda ake ciki, waya ta ciro tana dannawa Umar Faruk yace "me za kiyi?"

"Papa zan kira." ta fad'a a tak'aice.

Fizge wayar yayi yace "ba yanzu ba, tunda ki kaga sunyi haka to da dalili, ki sarara musu dan Allah."

Dole ta hak'ura badan taso ba, da haka suka isa ma'aikatar, kowa mazauninshi ya nufa amma Khairat ta kasa samun sukuni saboda abinda Papa yayi, bata tab'uka komai ba har lokacin tashinsu yayi, tare da Umar Faruk suka koma gida, alwala yayi ya wuce masallaci, saida yayi sallah isha'i ya dawo kai tsaye wanka ya shiga, tunda Khairat taga haka tayi niyyar babu inda zaije, dan haka yana gama shiryawa ya rumgumeta yace "zanje asibiti na dawo."

"Saika dawo." ta fad'a a qasan maqoshi.

Zai tafi ta rik'e hannunshi......

_Anya kuwa zai tafi?_
23/08/2019 Γ  12:51 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


_Bismmilahir-rahman-rahim_


5⃣2⃣


Ta had'e bakinsu waje d'aya, salonta ta fara masa wanda yasa ya manta komai dake gabansa ya biye mata, take ta lula dashi wata duniya har suka fad'a kan gado, nan dai naji ya fara karanto wannan addu'ar mai kayar min da gaba, da gudu na fito daga d'akin na barosuπŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€.

***************

Tun bayan fitarsu Khairat Mama tasa gyalenta ta goge gumi, a ranta kuma tace "nifa nayi mamaki, tabbas yarinyar nan tasan Alhaji Bala, to amma meye tsakaninsu da ita da har take kiranshi da Bala haka ba girmamawa? kodai itama karuwarsa ce, wata zuciyar ta fad'a mata."

Zuby ce ta katse mata tunani da "ni dan Allah suzo su sallamemu naje gida, wanka ma nake so nayi."

Kallonta tayi amma ba tace komai ba, Zabba'u ce tace "kiyi hak'uri mana zasu sallameki ai."

Sai lokacin Mama tace "nima dai na matsu, dan yanzun haka akwai abinda ya taso min mai mahimmanci."

Zuby ce tace "Mama badai wajen malam zaki koma ba?"

A fusace tace "eh wajenshi zan koma saime? ba dole naje ba, ke baki ga abinda ya faru bane kuma yake shirin faruwa."

"Kamar me kenan?" cewar Zuby.

"Mtsssss." tsaki kawai tayi ta shareta Zabba'u ce tace "to ai qwara aje wajen malam, dan ina tsoron kar karuwar can tasa miki hannu a cikin zubewar cikin nan."

Kallonta Zuby tayi tace "kuma fa hakane, gaskiya kam."

"Ah to fad'a mata." cewar Mama.

Jamila ce ta shigo ta fad'a musu tana buqatar sake murmurewa , dan haka sai nan da kwana biyu zasu sallameta , da farko fad'a Mama tayi saboda ba zata iya zama waje d'aya ba haka, amma da Zabba'u tace "ku kwantar da hankalinku mana, wannan ma ai hanyar samun kud'i ce a hannun yah Umar."

"Shegiya, kuma fa hakane wallahi." cewar Mama tana dariya.


_Allah ya shiryeku_

Zuba ido suke da dare suka Umar Faruk amma shiru, sai Saratu da Abbakar Baba dasu Mama ma duka sunzo amma banda shi, tun lokacin Zuby ta fara damuwa tare da kuka tana fad'in Khairat ce ta hanashi zuwa, haka dai su Uwani da suka zo suma aka rarrasheta.

_Tukunna ma Zuby, ke kika tsokano min qawata._


****************

Da safe ma saida Khairat tayi abinda yasa suka makara, hakan yasa dole suka wuce wurin aiki ba tare daya biya asibiti ba, a ma'aikatar ma bata barshi ba, basu fi minti talatin da zuwa ba tasa Habeeba ta kira matashi, yana shigowa ta taso tasa makulli a k'ofar ta zaunar dashi akan kujera, qafafunshi ta zauna ta b'alle masa botir d'in riga, yanda ta rikirkitashi yasa ya cire mata tata rigar itama, duk da a tsorace take dan bata manta wahalar da tasha ba, amma haka ta daure suka dinga....duk da komai bai faru ba amma anji jiki sosai kuma ankai maqura.

A daddafe suka kai yamma suka koma gida, kamar kullum alwala yayi ya tafi masallaci sai bayan sallah isha'i ya dawo, wanka yayi cike da kasala ya fara shiri, tun bai qarasa ba Khairat ta sauko daga kan gado ta nufi hanyar fita, yana kallonta ta madubi yana b'alla mab'allan rigarshi, saida

Please Login or Register in order to submit comment