Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wai ka mantani ne da kake fad'a min haka, ko dan kaga ana kiranka da mijina shi yasa, to bana so wallahi kaji na fad'a maka."

Fizge hannunta tayi zata wuce yayi saurin tare gabanta yace "kinga saurareni, kiyi hak'uri ki shiga nan kiyi wankan , daga baya zansa a gyara miki tunda ba kya so, kinji?"

Zuyawa tayi ta kalli douche d'in sannan ta kalleshi tace "idan ma baka gyara ba wallahi ni zansa a gyara, kawai douche sai kace gidan b'eraye."

Wucewa tayi ta fad'a douche d'in ta cire kaya ta cillo kamar yanda ta saba, rigar data jefo qarshe sai a fuskar Umar Faruk da zai shiga d'akin, a hankali ya janye rigar ya kalli sauran kayan pants bras da zanin, sunkuyawa yayi ya kwashesu ya shiga dasu d'akin ya aje mata, ruwa ta makama jikinta ta d'auki sabulu ashe bata d'auko ba ta d'auka douche d'inta ce wacce ke akwai komai da komai, cikin d'aga murya tace "ka d'auko min sabulu."

Shirun da taji yasa ta sake bud'a murya tace "ka d'auki min sabulu, kona fito na d'auka."

Tun maganar farko ya jita ya kuma tashi d'auka, jin abinda ta fad'a a qarshe yasa yana fitowa daga d'akin yana b'are sabulun a cikin kwalishin yace "kizo ki d'auka mana."

Yana daf da kaiwa bakin douche d'in ita kuma ta zuro da kai za tayi magana, da sauri ta dage qirjinta saboda bayyanar da yayi tare da komawa ciki tayi shiru, yana ganin haka ya juya bayanshi ya mik'a mata sabulun yana fad'in "gashi."

Amsa tayi sannan ta fara wankan shi kuma ya fita daga gidan, Ruk'ayya ya turo ta d'auki kwanunan ta wanke sannan ta zubo musu wani abincin ta kawo ta aje, duk lokacin Ruk'ayya na mamakin irin wankan da take data jima haka, amma a b'angaren Khairat fad'a da guna guni kawai take rusawa daga cikin douche d'in, sai gashi ta fito ba tare da tayi abinda ta saba yi ba, ta fito daga wanka cikin minti sha biyar zuwa ashirin, d'aki ta shiga ta fara shiri tana ci gaba da masifa akan douche d'in.

K'aramar riga ce mai siraran hannaye ta kamata sosai duk ta fito mata da mamanta , sai kuma jan siket data d'ora a saman rigar har kusa da qirkinta, a bud'e yake siket d'in sai dai iya gwiwa ya tsaya mata, raba gashinta tayi gida biyu tasa k'ananan chouchou (ribom) ta d'aureshi, bata wani kwalliya ba sai turare data shafa ta kuma fesa sannan ta d'auki wayarta tasa takalma ta fito farfajiyar gidan.

Wata kujerar ta d'auka ta aza 'kofar kewayen nasu ta zauna dan zafi ya isheta, daga yaran har iyaye satar kallonta kawai suke babu wanda yayi magana, mahaifiyar Umar Faruk kuma tana so tayi magana amma tana jin tsoron wulak'ancin da zata mata, waqa tasa a wayar ta fara biyarta tana rausaya daga zaune, mak'ota da yan uwa suka fara shigowa ganin amarya, amma duk wanda ya shigo saiya nufi wajen mahaifiyar Umar Faruk ya zauna yana tambayar ina amarya, da an nuna masa Khairat saiya tashi yana addu'a Allah ya kyauta, a qarshe da taga kowa ita yake kallo, aje wayar tayi ta zuba tagumin rainin hankali tana bin kowa da ido itama, hakan yasa gidan yayi shiru sai magana qasa qasa.


Baba da Abbakar ne suka taho zasu shigo gidan ganinsu yasa Umar Faruk ya biyosu suka shigo, da sallama suka shigo amma ta Umar Faruk saita tsaya saboda ganin Khairat da wannan kayan a jikinta, Abbakar ma dai duk'e kai yayi qasa ya nufi inda mahaifiyarsu take zaune ya tsugunna, Baba ma haka ya k'araso jiki ba k'wari saboda ya riga daya shigo, kamar wanda k'wai ya fashema a ciki Umar Faruk ya tako ya nufi wajenta, yana kaiwa cikin zafin nama ya finciko hannunta yayi cikin d'akin da ita.

Qarar da tayi lokacin daya fizgi hannunta yasa Baba ya kalli Mama yace "kinga, tashi dan Allah kira minshi, sai yayi b'anna yaron nan kin sanshi da bak'ar zuciya, karya lahanta 'yar mutane."

Da sauri ta tashi ta nufi d'akin nasu, suna shiga ya jefata saman gado cikin b'acin rai, zaiyi magana ta rigashi da cewa "meye haka wai, kana haukane? ni sa'arka ce da zaka min wannan pigar kazar mahaukaciyar."

"Mtssssss." tsaki tayi ta fito daga d'akin zata sake komawa inda take, shi kuma dama tsakin yafi bashi ma haushi, da azama ya biyota ya cakumo hannunta ya juyo da ita da k'arfi, wani irin zafine daya ratsata saboda rik'on daya mata yasa ta janye hannunta daga gareshi hawaye fal idonta, kasancewar shima yayi niyyar sakinta yasa ta fad'a saman kujerun dake wajen, kuma bata fad'a da kyau ba kawai sai kujerar ta wuntsila da ita ta fad'i qasa, qara ta saki mai k'arfin gaske hakan yasa Baba dake can tsaye hankalinshi ya sake tashi, Mama kuma ta karasa danno kai ciki, samu tayi Khairat na kokarin tashi tsaye hakan yasa ta kamata ta tashi tana kallon Umar Faruk, "meye haka Umar Faruk, kana lafiya kuwa?"

Kallon matar Khairat tayi tace "kece mahaifiyarshi?"

Kai kawai Mama ta d'aga mata, kallon bayan hannunta tayi da har gurin ya karce jini ya fara fitowa saboda hannun ya had'u da bango, maida hawayenta tayi ta fizge hannunta daga Mama kawai ta koma d'aki, Mama kuma harara ta bishi da ita tace "ai saika fito mahaifinka na nemanka."

Juyawa tayi zata fita ya kamo hannunta ya rik'e ya marairaice yace "wallahi Mama ban mata komai ba, dan Allah ki fad'awa malam."

Wucewa tayi ta barshi kawai dole ya biyo bayanta, da hannu Baba kawai ya masa alama ya boyoshi d'akinshi, cikin sanyin jiki ya bishi d'akin suka zauna, cikin hikima Baba ya dinga mashi nasiha da gargadi har a qarshe ya dora da "ba haka ake ba Umar Faruk, a matsayinka na namiji, dole akwai bukatar kafi matanka hak'uri, saboda su matane kuma masu rauni , mace zata iya yin abu, kai a ganinka waouta tayi amma ita sai tace kuskure ne, dan haka dole ka dinga hak'uri wannan zuciyar taka ka dinga tausarta, musamman kai daka fara da mata biyu, duk ranar da Allah ya had'aku zama gida d'aya, dole zaka gane ba kada wayo dan dole sai sun gwara maka kai, nasan ka sani dan kai shedane akan zaman da nake da iyayenku, dan haka dan Allah bana son wannan yawan hushi da zafin zuciya, ka rage kaji ko?"

"To Baba, insha Allah zan gyara."

"To Allah yasa, yanzu kaje ka bata hak'uri dan Allah, sannan ka mata godiya akan d'awainiyar da tayi, dan mahaifiyarka ta fad'a min, tashi kaje Allah ya maka albarka."

"Ameen Baba, na gode ."

A haka ya tashi ya tunkari b'angaren nasu yana tunanin ya bata hak'uri kamar yanda Baba yace, ko kuma dai ya shareta kawai.

_Ya kuka ce? kuna ganin zai bada hak'uri, ko kuma zaiyi taurin kai?_😎😏


*Ina barar addu'arku yan uwa, Allah yaba mahaifiyata lafiya, tana jin jiki, yer uwata ma na fama da tasku na rayuwar aure, gidan miji da tsangwamar kishiya , plss ku tayamu da addu'a.*

_I love you sis Alawiyya._😘❀
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

*ALLAH KA KYAUTATA MAKOMARMU*πŸ‘πŸ˜­


_Bismmilahir-rahman-rahim_


2⃣2⃣


Da sallama ya shiga ya sameta zaune a tsakiyar gado tana share hawaye, har ga Allah har zuciyarshi yaji ba dad'i kuma yaji bai kyauta ba, bata amsa sallamar ba harya zauna kan kujera yana kallonta, hannunta na dama da yake fitar da jini ya gani, shi kanshi baisan lokacin daya zaburo ba yayo kanta yana fad'in "subhanallah, kinga jini kike fitarwa."

Zai kama hannun tayi saurin janye hannunta ta d'aga masa hannu tana fad'in " karka kuskura ka tab'ani, mugu kawai azzalumi, wallahi Allah saika sakeni na koma gidanmu, ba zan iya zaman wannan takaicin ba."

Wani tafarfasa yaji zuciyarshi nayi tare da bugawa da k'arfi, wajen kayanshi ya nufa ya bud'e ya d'auko wani magani pommade ya bud'e ya lak'ata a hannunshi ya matso zai shafa mata, tsaye ta mik'e akan gadon tana fad'in "nace karka tab'ani ko, ko ana dole ne? ban son taimakon naka."

Danya nuna mata ba damuwa yayi da ita ba kawai ya cilla mata maganin a jiki yace "idan kinga dama ki shafa da kanki, yarinya sai taurin kan tsiya."

"Nice yarinyar? Umar Faruk ni kake fad'ama yarinya? lallai *zaka gane kurenka* wallahi."

Zaune tayi akan gado shi kuma ya matso kusanta yace "yaushe aka haifeki to?"

Sama da qasa ta wurga masa harara tare da jan tsaki, bata daidaita bakinta ba ya kama labb'an nata ya matse sosai wanda yayi silar sake fito da wasu hawayen daga idonta saboda masifar zafi, duk da idonta daya ga sunyi ja saida ya qara murd'e bakin yace "zaki sake min tsaki?"

Rintse idonta tayi sosai hawaye na zuba, sake murd'ewa yayi yana fad'in "za kiyi magana ko saina cire bakin? fad'a min naji zaki sake hararata ko tsaki?"

Kasa magana tayi saboda ya rik'e bakin sosai, cikin fashewa da kuka ta girgiza masa kai a hankali cike da takaici, shima harara ya dalla mata ya saki bakin yana fad'in "marar kunyar banza kawai, wallahi ki yarda na sake gani kiga yanda zamu kwashe dake."

Zaune yayi akan kujera ya fara zuba abincin da Ruk'ayya ta kawo ta aje, ita kam hannu tasa ta dafe bakinta gam tana kallonshi, had'a ido da sukayi yasa ta sake banka masa wata hararar, danya tsorata yasa ya taso da azama yana fad'in "baki daddara ba kenan? bari kiga yanda zanyi dake."

Da gudu ta wuntsila daga kan gadon tayi d'aya b'angaren tana nunashi da hannu tace "wallahi ka matso kusa dani zan illataka."

Murmushi kawai yayi ya koma ya zauna ya gama zuba abinci ya kalleta har yanzu tana tsaye yace "kizo kici abinci."

"Ni ba komai nake ci ba, ina da tsari na."

Tab'e baki yayi ya fara cin abincin, amma bai kai ko ina ba sai wata zuciyar tace masa "da safe ma bata ci komai ba, a hakane Umar Faruk zaka tafiyar da iyalinka? kai kaci ita kuma baka damu da taci ko karta ci ba."

Ajiye cokalin yayi ya kalleta yace "ki fad'a min me zaki ci?"

Sai lokacin ta zauna bakin gadon tana fad'in "karka damu dani, ka d'auka zamana a gidan nan kamar naje k'auyen kakanni na ziyara ne, dan haka zan kula da kaina."

" *Khairat*."

Saida taji gabanta ya buga tare da sanyin jiki saboda yanda ya kira sunanta, bata kalleshi sai dai tana sauraro taji me zaice, ganin bata kallonshi yasa kawai ya qyaleta shima, saida ya gama cin abincinshi sannan ya tashi ya fita ko kallonta baiyi ba, ita kuma tana ganin ya fita ta sake kama bakinta saboda har yanzu zafi yake mata sannan ta bishi da harara tace "mugu kawai." sake haye gadon tayi ta kwanta, taso tayi bacci amma ina zafi da matsatsi sun hanata, dole tashi tayi ta sake fitowa farfajiyar gidan, lokacin wasu na d'aki wasu na tsakar gidan, zaune tayi dan har yanzu kujerar na nan inda take.

Usman ne ya doso cikin gidan, da matuk'ar mamaki yake kallonta ganin bak'uwar hallita a gidansu, ko kad'an baya tunanin matar Umar Faruk ta kasance haka, cike da fara'a yace "sannu ko."

Da hannu ta masa alamar yazo, ba musu kam kamar sakarai ya nufi wajenta, tsaye yayi gabanta yayin da mutanen dake wajen kallo ya koma kansu, rik'e hab'a tayi ta tangale hannu da kujerar tana kallonshi tace "kana da abin hawa?"

"Eh, ina da moto."

"Da kyau, aikenka zanyi restaurant ka siyo min abinci."

"Ke kuma awa?" ya fad'a yana mata tuhumammen kallo.

Mik'ewa tayi tsaye tace "ka bari idan wanda nake zaune dominshi yazo ya fad'a maka koni wacece, amma yanzu ka fara zuwa aiken nawa."

D'akin data nufa ya tabbatar masa matar Umar Faruk ce, kuma wannan itace Khairat, kai kawai ya girgiza ya juya ya kalli mahaifiyarshi da yasan sarkin surutu ce amma tayi shiru, tunkararta yayi ya tsugunna gabanta yana fad'in "Mama, ita kuma haka take?"

"Kai, tashi kaje abinda ta saka bana son surutu, kuma kayi sauri ka dawo." cewar Mama Sa'a tana yi tana kallon k'ofar da Khairat zata fito.

Fitowa tayi amma ganinshi gaban wacce take tunanin mahaifiyarshi ce yasa tayi zaune saman kujerar tana jiranshi, da k'arfi Mama Sa'a ta turoshi ya dawo gaban Khairat ya tsaya, jikka goma guda uku ta bashi ta fad'a masa abinda take so, wucewa yayi yana tsananin mamaki akan abincin da zata ci zaka kashe duk wannan kud'in, lallai yaran nan iyayensu sun kwashe mana kud'i suna facaka yanda suke so😎 inji Usman faπŸ˜‚.


Ta jima tana jiranshi amma bai dawo ba, har saida ranta ya gama b'acewa taji abinda take so d'in ya fita a ranta, ta tashi kenan zata shiga d'aki Usman ya danno kai cikin gidan, wani wawan tsaki taja tare da nunashi tace "saika zauna kaci ai, ni bana so."

Shigewa tayi d'akin shi kuma ya tsaya da leda a hannu yana kallon k'ofar, da gudu gudu Mama Sa'a ta taso ta karb'i ledar zata shiga d'akin Usman yace "canjin fa."

Dawowa tayi ta karb'a ta wuce d'akin Khairat mahaifiyar Umar Faruk na kallonta tana jin tsoron abinda zai biyo baya, da sallama ta shiga cike da ladabiπŸ€” sau hud'u tayi sallama ana biyar ne Khairat tace "ki shigo."

Da murmushi ta shigo tana k'arewa d'akin kallo tana ji kamar ace d'akin tane ko kuma na 'ya'yanta mata masu aure, aje wayarta tayi tana kallonta cike da tsana da wulak'anci amma ita bata damu ba, ledar ta mik'o mata tana fad'in "gashi 'yata , kiyi hak'uri kici kinji, kinsan yaran yanzu sai hak'uri, inka aikesu sai sun b'ata lokaci kafin su dawo, amma na miki alk'awarin ba zai sake ba daga yau."

Gatse gatse Khairat tace "baki ji me nace mishi bane? nace yaci idan kuma ba zai ci ba, ke kici ko kuma ku zubar a shara, amma ni na gama da babin wannan kuma, zaki iya tafiya."

Ba tare data damu ba ta sake murmushi ta mik'o mata kud'in tace "to ga canjinki."

"Suma ku rik'e bana so." ta fad'a tana maida abin sauraronta a kunne.

Da dariya cike da farin ciki ta juya ta fita, amma abin mamaki saita d'auki kwano ta juyo abincin ta zauna Usman da sauran yaran dake nan suna kallo da mahaifiyar Umar Faruk ta fara ci tana fad'in "harkar arzik'i aida mutanen arzik'i ake yinta."

Usman da haushi ya kamashi ficewa yayi daga gidan, ita kam ko a jikinta cin abinta tayi tasha ruwa saura ta bawa yara, amma kasancewar sun samu tarbiya sai basu karb'a ba suka ce sun k'oshi, masifa ta fara tana fad'in "yara an koya muku bak'in hali tun kuna k'anananku, to ku aje kar Allah yasa ku ci d'in ."

Kud'inta kuma bata bari ma kowa ya gani ba, ko abokiyar cin mushen nata dan dama tana d'aki tana bacci.


******************

Mamie da Papa sosai suke cikin damuwar rashin 'yar gudaliyarsu, haka duk suke zama shiru kowa da abinda yake tunanin a kanta, haka ma ma'aikatan gidan suna damuwa ta b'angaren kyauta da taimako, amma ta b'angaren wulak'anci da yawan aiki kuma suna farin ciki da hakan, amma dai kam tabbas suna kewarta saboda ita kad'aice 'ya a wajensu.

*******************


Ana gama sallah isha'i Umar Faruk ya shigo gidan danya shirya saboda yace ma Zuby yana nan zuwa, da sallama ya shigo tare da leda a hannunshi, bata amsa ba kuma bata kalleshi ba sai ayabarta data d'auko a fridge take ci tana korawa da fresh milk, aje ledar yayi saman tebur ya d'auki maclean da brush ya shiga wanka, ya d'an d'auki lokaci kafin ya fito sanye da dogon wando fari da kuma towel ya rufe jikinshi dashi, ya jima tsaye yana shafawa yana fesawa kafin ya fara k'ok'arin saka kaya, ganin yana zame wandon daga jikinshi yasa Khairat saukowa daga kan gadon da duk ta ya mutseshi ta fito a d'an kewayen nasu ta zauna, saida ta daidaici ya gama shiryawa sannan ta shigo, gaban madubi ta ganshi yana daidaita hularshi, da kuma waya a kunnenshi ya danneta da kafad'a.

Muryarshi taji qasa qasa yana fad'in "to ki shirya min kanki, dan gani nan zuwa yanzu, kinga tunda aka d'aura mana aure bamu had'u ba."

Shiru ya d'anyi sannan yace "ok to, sai nazo."

Juyowa yayi yaga Khairat tsaye tana kallonshi, wuceta kawai yayi yana sa wayarshi aljihu sannan yasa takalmi ya d'auki leda d'aya a cikin wanda ya aje ya kalleta yace "wannan taki ce."

Juyawa da yayi zai fita yasa Khairat tayi saurin cewa "wannan fa ta wacece?"

"Zubeida, amaryata."

Kai tsaye kuma ya fita daga gidan ba tare daya sake kulata ba, tab'a ledar tayi taji kaza ceπŸ˜‹(ina sonki kaza), a hankali ta fara d'aga qafafunta harta koma kan gado, sai dai ta rasa meke damunta da taji zuciyarta na mata k'unci duk taji ba dad'i, haka ta rasa me za tayi gaba d'aya kalmar Zubeida amaryata ta tsaya mata a rai, daga ta dafe baki saita dafe goshi ko kuma k'ugu, a hankali ta lumshe idonta amma sai tayi saurin bud'ewa saboda jin hawaye sun zubo mata, hannu tasa ta share ta tashi ta shiga 'yar k'aramar douche d'in ta cire kayan jikinta ta jefosu kamar yanda ta saba ta fara wanka, saida ta gama ta fito kuma ashe babu towel, kamar yanda tayi da rana haka ma yanzu tayi, da gudu ta fito ta shigo d'akin sannan tayi shirin bacci, rigace mai 'yan hannuwa sai wandon dogo har qasa amma bai kamata ba sannan ta kwanta, bacci ne ya gagareta saboda zafi fitowa tayi farfajiyar gidan, kowa yayi shinfid'arsa ya d'aura gidan sauro ya kwanta, kewayenta ta koma ta zauna akan kujera tana sauraron waqoqi daga nan kuma bacci ya d'auketa zuciyarta na tsananta bugawa, gashi tunanin Umar da Zuby ya kasa barin qawqwalwarta.

****************

Tunda yace zaizo tanti Ma'u tayi farin ciki Zuby kuma ta shiga wanka, tun kafin ta fito kuma Umar yazo, koda ta fito mahaifiyar tata harta had'a mata 'yan tame tame da tsarabe tsarabe, saida tayi kwalliya sosai ta shirya cikin riga da siket na shadda sannan Mama ta zaunar da ita bakin gado ita kuma tana tsaye ta mik'a mata roba mai cike da nono da magunguna masu k'arfin gaske ta shanye, wani farin magani ta bata tace "tashi ki matsashi a gabanki."

Tashi tayi kamar yanda tace haka tayi sannan ta aje mata kaskon wuta ta zuba wani turaren tace ta sake tsugunnawa, gyara jikinta tayi sannan Mama tace "kina jina ko? kiyi duk abinda kika san zaija hankalinki ya kwanta dake, dan wannan abinda kika gani bana wasa bane, nasan dai duk gaggawarshi bai riga ya kusanci waccen karuwar ba, dan haka kar kiyi wasa da wannan damar."

Ganin Zuby tayi qasa da kanta alamar kunya yasa tace "to kuma miye na kunya? nifa uwarki ce dan haka karki damu."

A sanyaye ta kalleta tace "wallahi Mama tsoro nake ji, gabana ma fad'uwa yake."

"Saboda me? mijinki ne fa, kasheki zaiyi? keni nama ci uwaki idan kika b'ata min rai, to in banda abinki kowace mace ba saida tazo wannan gurin ba kafin nan ta wuce, muma duk bata haka muka sameku ba."

Shirun da tayi yasa tace "maza wuce kije yana jiranki."

Lemon da Mama tasa aka siyo mata ta d'auka ta fito ta shiga d'akin da aka gyara mata ta zauna kafin lokacin tariyarta, zaune yake akan k'atuwar katifar dake tsakiyar d'akin, k'ura mata ido yayi harta zauna kusa daf dashi duk da irin ruwan da take jin gabanta na fitarwa, sosai ta masa kyau kasancewarta siririya kuma kayan sunbi jikinta, ga kwalliyar da tayi sosai hakan yasa ta masa kyau.

Wani kashe ido ne da tayi yasa jin tsikar jikinshi ta tashi had'e da fad'uwar gaba, itace tayi k'arfin halin cewa "sannu da zuwa angona, na barka kana ta jirana ko? kayi hak'uri to na tsaya maka shirine."

Cikin wani irin yanayi da shi kad'ai yasan me yake ji yace "ba komai, ai girmanki ne."

Lemon ta d'auka ta bud'e sannan ta kai masa a baki tana sake rikirkitashi da wani sabon kallon, kurb'a d'aya yayi ya kau da kansa gefe tare da d'auko ledar daya shigo da ita mai d'auke da kaza da kuma lemuka masu sanyi, bata yayi ta karb'a tana fad'in "meye kuma?"

"Ki diba ki gani mana, kazar amarcinki ce."

Ya fad'a yana dariya, ita kam gabanta ne ya fad'i dan haka tace "na shiga uku, nifa bana son cin kazar nan."

"Me yasa?" ya fad'a yana kallonta.

Cikin tsoro tace "wallahi ina ji k'awayena suka fad'a wai duk wanda yaci kazar nan, to shima dole sai an...." kuma sai tayi shiru.

"Ina jinki, kina tunanin na saka wani abu ne a ciki?"

"A'a, kawai dai ance idan kaci kaima zaka biya."

Cike da zolaya yace "ke kuma biyanne kike jin bak'in ciki ko?"

Tuna abinda Mama ta fad'a mata yasa ta fad'a jikinshi tare dasa hannunta ta shafo qirjinshi amma ba tace komai ba, tunda ta fara shafarshi ta kwance masa lissafi ido ya rufe yana sauraronta, bata daina ba saima botir d'inshi data b'alle ta zura hannu tana shafoshi, cikin wata rikitaciyar murya ya kira sunanta da,

"Z..u....beid...a."

D'ago kan da tayi ta kalleshi tana marmad'a ido yasa ya sake fita hayyacinshi, a hankali ya had'a bakinshi da nata ya fara tsotsa, tun yana aika sak'on a hankali harya fara da sauri sauri, sai kuwa ya kwantar da ita akan katifar ya hau samanta ya cire hularsa da riga da.....πŸ™ŠBK za tace waya aikeni.



Umar Faruk dai ya manta da ina yake sai faman aiki yake, rana ta farko daya fara sanin 'ya mace kenan, shaye shayen da Zuby tayi yasa Umar Faruk bai sarara mata ba ko kad'an, hakan ya janyo ya mata babbar k'ofaπŸ˜‚shiga gari, wacce ba lallai Khairat nada ita ba, ya jima sosai kafin ya d'agawa Zuby k'afa , kwance yayi yana kallon sama yana sauke numfashi duk da gumin daya had'a, Zuby na ganin haka ta yunk'ura ta tashi zaune ta d'auki rigarta ta yab'a tare da saka siket d'inta ta mik'e zata fita, da sauri ya tashi ya d'auki wandonshi qarami ya saka ya rik'ota yana fad'in "ina zaki je haka Zubeida, miye haka?"

Cikin layi da shan wahala tace "dan Allah ka k'yaleni na tafi, wallahi ciwo nake ji, zanje wajen Mama ta taimaka min."

Tare gabanta yayi yace "haba Zuby, ya kike nema ki tona min asiri? ki bari dan Allah ki gyara jikinki, karki fita haka."

Zip d'in rigarta ya saka mata tare da bata d'an kwalinta ta d'aura sannan ya saka nashi kayan shima, sallama ya mata ya bar gidan dan ba zai iya had'a ido da Mama ba, haka ya bar gidan gabanshi fad'uwa kawai yake kamar bai samu nutsuwa ba, a haka harya isa gida.

Zuby na shiga d'aki ta fad'a saman gado, da sauri Mama ta d'auko babban roba da ruwan d'umin data d'ora musu tunda ta kara kunne a k'ofar d'akin taji nishi da sambatun Umar Faruk da kuma kukan Zuby ta dafasu , da taimakonta ta samu ta gasa jikinta sannan tayi wanka kafin baccin wahala ya d'auketa.πŸ˜‚

******************

00:30 ya shigo da mashin d'inshi a cikin gidan bayan ya kasheshi yanda Baba ba zaiji ba, yana daidaita zaman mashi d'in yana sad'af sad'af zai shiga ciki muryar Baba ta daki kunnuwanshi da kiran sunan "Umar Faruk."

Rintse ido yayi sosai yana jin bugu zuciyarshi na qaruwa, a hankali ya juyo ya kalli Baba dake qofar d'akinshi, kallon da yake masa yasashi zubewa k'asa ya durk'usa yana sauraran Baba.

"Umar Faruk, ya ina yabanka sallah zaka kasa alwala, kai da kanka Umar Faruk, yanzu ka kyauta kenan? to waima daga ina kake?"

Yana shafa kai cikin rashin gaskiya yace "kayi hak'uri Baba, daga gidansu tanti Ma'u nake."

"Au, yanzu acan kayi dare kenan haka? Umar Faruk yanzu yarinyar mutane daka bari fa? ya kayi da ita?"

Shiru yayi ba magana dan haka Baba yace "to kaje ka bata hak'uri, dan kamar ka d'auki kwananta ne ka kaiwa wata, ko ban tambayeka ba nasan akwai abinda ya shiga tsakaninka da Zubeida,

Please Login or Register in order to submit comment