Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Khairat take da iko akansu, kinsan me yasa? saboda itace ta siyesu, kuma bata tab'a kulasu ba sai ranar dake kika kawo shawarar kowace ta dinga girki da kanta, Zubeida idan akwai wanda akawa rashin adalci to Khairat ce, domin kuwa a lokacin dana siyo miki kayan abincin nan ita ban siyo mata ba, sannan na d'auki kud'i na qara muki dasu, duk da haka sisin kwabo ban bata ba dan nasan ba zata karb'a ba, tunda ta shigo gidan nan zan iya fad'a miki adadin da taci abincin gidan nan, kinga kenan ita akawa rashin adalci, na uku kuma kince sutura, to kijini da kyau Zubeida, ni banwa Khairat lefe ba kece nayiwa lefe, tunda nake da ita zani d'aya na atamfa bai shiga tsakani na da ita ba, kin ganni a matsayin mijin Khairat? wallahi har yanzu idan banda wurin kwanciya da ruwan gidan nan, banga wani abu da Khairat ke anfani dashi ba wanda zan iya cewa nawa ne, sannan atamfar da Khairat ke sawa a jikinta ma kad'ai tafi k'arfin arzik'ina, bare kuma kudin d'inkinta har azo ga shadda ko less, maganar sarka da d'an kunnai ma mu barta, har yanzu babu tsaiyar dana tsinanawa baiwar Allah nan a matsayina na mijinta, hasali ma nine ke qaruwa da ita tako ina, a yanzun burina bai wuce na samu hanyar da zan saka mata da alkairin data min ba, dan duk wanda zai bawa ahalinka abinda zasu ci ya kuma dinga kyautata musu, to tabbas shi masoyinka ne na gaskiya, musamman ita da bata damu da dukiyarta ba, ita dai burinta kawai ta kyautatawa wanda yake tare da ita, ba tayi dan gobe ta fad'a tayi maka, sannan idan tayi ba'a karb'a ba tana jin zafi, domin kuwa ita alheri a cikin jininta yake kamar yanda ma'anar sunanta yake, dan haka ina baki shawara Zubeida, ki cire komai a ranki ki rumgumi yer uwarki, wallahi babu komai a zuciyarta a game dake, ko sau d'aya bata tab'a nuna min kishinta a kanki ba, ina fatan za kiyi anfani da shawarata, kuma ki yafe min idan na fad'i abinda ya b'ata miki rai."

Mik'ewa yayi da fad'in "saida safenku." danshi baiga abinda zai sashi b'ata lokacinshi ba akan banzan shirmen Zuby.

Mama da Baba ma sun gamsu da abinda ya fad'a dan haka sukayi shiru harta tashi ta koma d'akinta, yana shiga d'aki Khairat ya sameta zauna tana tunani akan karatun da Baba ya musu, dan a cikin kyautatawar daya musu magana akai, akwai kyautatawa iyaye, ita kuma tana tunanin yanda ta zauna da nata iyayen, ji tayi tana so ta basu hak'uri akan yanda ta mu'mulancesu a baya, zaune yayi kusanta ya janyota jikinshi yana fad'in "yadai, meya faru."

"Ba komai." ta fad'a tana shafa jikinshi.

"Kin tabbata?"

"Um."

Dago kanta yayi ya kalli fuskarta, turo baki yayi gaba kamar yaro ya langab'e kai yace " ban yarda ba gaskiya, akwai wanda ya tab'a min baby, fad'a min meya faru.?

Qara langab'ewa tayi tace " ba komai fa."

"To indai hakane kiyi dariya na gani."

D'an murmushin yaqe tayi tace "nifa bacci nake ji."

Tana fad'a ta kwanta tare da jan zanin rufa, Umar Faruk a ranshi cewa yayi "baiwar Allah, ko tana tunanin abinda ya faru ne wanda ya tsayar dani? koma dai meye dole nima na saki farin ciki kamar yanda kema kike sakani farin ciki, wannan itace damar da nake da wajen saka miki da alkairi."

Hayeta yayi ya fara mata cakulkuli yana fad'in "ba zan iya komai ba sai naga dariyarki."

Ai kuwa dariya ta fara qyalqyalawa daga haka kuma suka lula duniyarsu ta maji dad'i......

**************


Tunda asuba koda Khairat tayi sallah ta fara shirya musu kayansu tare da shirya kanta , Umar Faruk kuma saida ya shiga d'akunan iyayensu suka gaisa tare da d'akin Zuby, haka yayi sallama har sau uku amma ko qala ba tace ba, sannan ya qara da "kin tashi lafiya?"

Nanma shiru ba amsa, fita kawai yayi daga d'akin, yana zuwa shima shiryawa yayi a lokacin kuma Khairat ta gama abin karyawa, suna gama break suka fito cikin shirinsu, duka iyayen nasu na zaune dan haka suka qarasa suka musu sallama, sun tashi kenan zasu wuce Zuby ta fito tana rufe d'aki itama zata wuce Γ©cole, ganin ko kallon kowa ba tayi ba ta kama hanyar fita yasa Umar Faruk binta da sauri, a soro ya sameta ya rik'e yana fad'in "ki jira mu saukeki."

Fizge hannunta tayi tace "rabu dani bana so."

Ganin Khairat ta taho kuma ko Khairat ba zaiso ta rainashi ba yasa ya wurga mata wata harara, shiru tayi tana sauke numfashi ,wucewa yayi suka bi bayanshi amma abin mamaki, da hanzari Zuby ta zagaya ta zauna a gidan gaba, kallonta yayi zaiyi magana kawai yaga Khairat ta bud'a mazauninshi ta zauna, saida ta daidaita zamanta sannan ta fizgo makullin hannunshi fuskarta a had'e itama ba alamar wasa, jin tayiwa motar key yasa ya bud'a gidan baya ya zauna ya rufe yana fad'in "Allah gani gareka, ashe dama haka mata biyu suke, da zaran sun had'u sai an caza maka qwaqwalwa."

Gyara madubi Khairat tayi ta kalleshi tace "baby ka shirya?"

Gintse dariyarshi yayi ya sunne kai qasa, Zuby kuma qoqarin bud'ewa ta farayi danta fita, Khairat na ganin haka ta fizgi motar da iya k'arfinta a zuciyarta tana fad'in "uban daya kawoki gidan gaba."

Titi suka hau Umar Faruk na kallon kowace daga baya, Khairat na tuk'i hankali kwance Zuby kuma tayi tsaki yafi dubu , amma jin sun qyaleta yasa tace "aikin banza, barewa ai ba tayi gudu ba d'anta yayi rarrafe, an gada wajen uba dole a nuna hali."

Ba tare data kalleta ba tace "na fad'a miki ki daina saka iyaye a maganar data shafemu , bai zama lallai abinda zai fito a bakina ya miki dad'i ba, amma kika b'ata min rai yanzun nan saina had'a motar nan da bango."

Sai lokacin ta kalleta duk da tana tuki tace "bana tsoron mutuwa, dan Mama tace ni yar aljanna ce, bugu da qari ina tare da babyna, zanyi farin ciki mu mutu tare, idan kin shirya biyarmu to."

"To an fad'a miki ina tsoron mutuwa ne? ai gwara na mutu ma da zama dake a matsayin kishiya wallahi, inkin fasa hadamu da bango bakya tsoron Allah daya halicceki."

"Kin shirya mutuwa kenan?" cewar Khairat.

"Shege ka fasa, d'an halak sai yanka."

Da sauri Khairat ta kalleta tace "a'a malama, ki daina sako mana wannan kalmar anan, ni dai 'yar halak ce."

"Kenan nice shegiyar?"

"To ai ba kama garesu ba, kuma ba'a rubuta a goshinki ba bare na karanta, kinga kenan ba zan iya sani ba."

"In haka kike tunani, toki d'auka ni yar babanki ce."

Umar Faruk ne yayi saurin cewa "ya isa haka to, karna sake jin bakinku, inba haka ba rai zai b'ace."

Khairat kuma gani tayi aita kaita qasa, dan haka tace "ina aiki na masu hankali, amma idan haukana ya motsa to akwai matsala, ki kiyaye bakinki kafin kiji abinda zai iya tarwatsa miki lissafi."

Tsaki Zuby tayi ta rumgume hannaye har suka isa ecole d'insu, saida ta juya ta kalli Umar Faruk sannan ta kalli Khairat tace "na gode Allah, ni ba 'yar d'an giya bace."

Tana fad'a ta fita ta bar motar, Khairat binta tayi da kallo lokaci d'aya hawaye suka soma zubo mata, fitowa Umar Faruk yayi ya bud'e inda take zaune, saida ya kama hannunta ya fito da ita sannan ta zagaya ta zauna inda Zuby ta tashi, saida suka fara tafiya jin tana shashek'ar kuka yasa ya fara tausarta da kalamai masu sanyi, ba tayi shiru ba har saida taga yayi parking a k'ofar gidansu sannan, zata fita ya rik'e hannunta suka kalli juna, d'aure fuska yayi yace,

"Ki maye fara'a a gurbin d'aure fuskar nan."

Cikin muryar kuka tace "amma fa kaji abinda yarinyar nan ta fad'a min."

"Naji, kuma kamar yanda ki kace kina da hankali, to ina so ki nuna min ke mai ilimi ce, kuma naji dad'i da kika qyaleta."

Share fuskarta tayi kafin suka fita suka nufi cikin gidan, sun samu Papa da Mamie suna hira a falo, da gudu Khairat ta fad'a jikin Papa tana dariya, saida suka gama murnar ganin juna sannan Papa yace "shalelen Papa, ashe har yanzu baki girma ba? na dauka kin girmi hakan yanzu."

Turo baki tayi gaba tace "Papa wane irin girma kuma, nifa kamar autace a gareku, babu wani gabana kuma babu bayana, to in banyi ba wa zai muku."

Mamie ce ta juyo da fuskarta ta kama kumatunta tana fad'in "banga laifinka ba, kiyi yanda kike so shalelen Papanta."

Murmushi tayi tace "Mamie ina kwana?"

"Lafiya lau Khairat, ina mai gidan naki?"

Kallon kofar da suka shigo tayi danta nuna musu Umar Faruk, ganinshi tayi durk'ushe yana gaishe da Papa, ajiyar zuciya tayi ta tashi ta kama Umar Faruk ta zaunar dashi kan kujerar da dukansu suke tana fad'in "kaifa yanzu d'an gidane, bamu da wani dangi daya fika, yanzu kaine babban d'ansu bani ba, ka d'auka na baro Mama da Babana can gidan, yanzu kuma nazo gidanku ne kaima."

Murmushi Umar Faruk yayi yana jin maganganunta na sake dawo masa a qwaqwalwa, Mamie ce ta dora da "gaskiya ne kam, ya kamata ka saki jikinka, muma iyayenka ne."

Papa ne yace "wai harka shirya kenan?"

Cike da ladabi yace "eh Alhaji."

Khairat ce ta katsesu da fad'in "Alhaji kuma, Baban nawa? ni wallahi ban yarda ba, kace Papa kaima, inba haka ba, tam."

Papa ne yace "dan Allah ki rabu dashi."

Maida kallonshi yayi ga Umar Faruk yace "to amma kuma na ganku tare, kana nufin da ita zaka je?"

Nanma cikin ladabi yace "eh, saboda bansan garin ba shi yasa nace muje tare."

"To, da yake tana da biza ba matsala, amma ai ba jimawa zakuyi ba."

Kwance Khairat tayi akan kafad'ar Papa tace "Papa ba zamu wuce kwana biyu ba."

"To Allah yasa."

Papa ne ya d'ora da "ya kamata ku wuce lokaci na tafiya."

Kukan shagwab'a Khairat tasa tana fad'in "Papa korarmu kake, shikenan idan naje ma ba zan dawo ba, zan zauna acan ni da baby."

Saida Papa ya kama kumatunta yace "da kuwa kin ganmu nida mahaifiyarki, dan kinsan ba zamu iya jurar zama nesa dake ba."


Gyara zama Khairat tayi dama a tsakiyarsu take ta kamo hannayensu ta had'e wuri d'aya tana kallonsu tace "Papa, Mamie, a cikin karatun dana koya a gidansu Faruk, na fahimci girma da matsayin iyaye, iyayena ku yafe min, domin a jiya ne na gane kuskure na, nasan ban saku farin ciki ba, kuma ban zama 'ya ta gari a gareku ba, dan haka ina neman afuwarku tare dasa albarkarku, kuma nayi alk'awari insha Allah zan zama d'iya mai tarbiya a gareku, ba zan sake muku rashin kunya ba, dan Allah ku yafe min iyayena." ta qarashe da fashewa da kuka.

Kusan a tare suka rumgumota a jikinsu, kuka suke sosai yayin da Mamie take kuka tana fad'in "Khairat mun yafe miki, kuma inda mai laifi, to mune iyayenki, munja miki abubuwa da dama a rayuwarki, muma muna neman afuwarki , dan ko kad'an bamu baki tarbiyar data dace ba."

"A'a Mamie, kunyi iya qoqarinku, nice kawai ban maida hankali ba, ku yafe min dan Allah."

Papa ne yasa hannu ya share mata hawaye yace "Khairat ba laifinki bane, komai nine silarshi, nine silar faruwar komai, inada damar da zan iya gyara halina tun lokacin da nake da quruciyata , amma na kasa gyarawa harna auri mahaifiyarki bada son ranta ba, amma kuma duk da haka ban gyara ba, ganin an haifa min 'ya mace ma baisa nayi tunanin komai ba na saduda , a haka naci gaba da shek'e ayata , harsai ranar da aka ci zarafin sannan na gane kurakuraina dana tafka wanda ba zasu tab'a gyaruwa har abada, nasan a baya wasu suna kiranki da 'yar d'an giya ko kuma shugaba marar adalci, wasu ma suna kiranki da 'yar mazinaci , amma ki sani wannan sunayen dane, yanzu na daina komai, siyaya ma ajeta zanyi da yardar Allah."

Da qyar Umar Faruk ya rarrashesu sannan akasa driver ya kaisu aireport ya dawo da motar, ba b'ata lokaci jirginsu ya tashi da ikon Allah kuma suka sauka da izinin ubangiji.....

Mota aka turo ta d'aukesu, kai tsaye babban hotel aka saukesu, wanka suka shiga koda suka fito an kawo musu abinci, suna gama ci kuma aka d'aukesu izuwa compagnie da suka zo dominshi, babban compagnie ne mai dubbanin ma'aikata, d'aki na musamman aka shiga dasu domin tattaunawar, manyan mutane ne guda biyu suke zaune suna zaman jiran zuwansu , suna ganinsu suka mik'e saboda girmamawa tare da bawa Umar Faruk hannu, suna gaisawa d'aya dattijon ya bawa Khairat hannu dansu ba wani abu bane a wajensu, saboda ne yasa Khairat mik'a mishi hannu itama da nufin su gaisa, amma jan kallon da Umar Faruk ya mata yasa yan cikinta murd'awa, tabbas Umar Faruk nada kwarjini kuma tana shakkarshi, da sauri ta janye hannunta a daidai lokacin da mutumin ke neman rik'e hannunta, kallon Umar Faruk sukayi kawai suka basar, da hannu suka nuna musu su zauna, nan suka zauna suka tattauna akan abinda ya kawosu, duk da ya fad'a musu ba zaiyi aiki dasu ba na dindindin amma sun amince, dansu burinsu kawai shima su mori basirarshi, dan qirqirarshi da aka nuna musu yayi matuk'ar birgesu , abinda yaba Umar Faruk mamaki shine, bill da suka bashi kuma sukace ya rubuta adadin kud'in da yake so su dinga biyanshi , da taimakon Khairat ya rubuta adadin da yake bukata, anan suka sallameshi bayan sun bashi sabuwar computer wacce zai dinga musu aiki da ita, sannan aka ce jibi jirginsu zai kuma tashi, kai tsaye aka sake mayar dasu masaukinsu, saida suka huta sukayi bacci sannan suka shirya suka fita ganin gari, Khairat ce ke zagayawa dashi ko ina duk da itama ba wani sanin garin tayi ba sosai, a haka suka dinga shaqatawa har dare yayi sai dai lokacin kowace sallah suka samu wuri Umar Faruk yajasu , taxi suka tare ta kaisu masaukinsu, suna zuwa wanka sukayi suka ci abinci sannan suka kwanta.

*Asuba ta gari*


Washe gari ma koda suka shirya fita sukayi cikin qananan kayan sanyi, wuraren shaqatawa suke je sukayi farin ciki abinsu tare da d'aukar photuna , saida dare yayi yauma suka kamo hanyar masaukinsu, kafin su hau titi akwai tafiya kuma gashi wajen babu mutane, Khairat ce ta qamqameshi tace "baby nifa tsoro nake ji."

"Tsoro, kina tare dani d'in?"

Sunkuyawa yayi yace "hau na goyaki to." ko qarasawa baiyi ba Khairat ta haye bayanshi, tafiya suke a hankali suna hira qasa qasa, dan Khairat gabanta kawai ke fad'uwa tana ji akwai matsala, amma dai bata san me zai faru ba, suna cikin tafiya kawai wasu samari su shida dake gefen hanyar suka fito tare da tare musu gaba, a hankali Khairat ta sauko daga bayan Umar Faruk tana kallonsu cike da tsoro, hannunta Umar Faruk ya kama da nufi su wuce danshi ko d'ar bai jiba a zuciyarshi , d'aya hannu tasa ta rik'e hannunshi tana girgiza kai, kallonta yayi yaga tsoro fal a idonta da fuskarta, fuskantarta yayi ya dafa kumatunta yana fad'in "baby, kalloni nan, kwantar da hankalinki, babu abinda zai faru ina tare dake, ki nutsu kinji, kar kiji tsoro."

Kai ta girgiza da sauri hawaye na zuba a idonta dan duk gani take zasu mata abinda su Musa suka mata ne, qara rik'e hannayenshi tayi tana fad'in "dan Allah Faruk kazo mu canza hanya, wallahi tsoro nake ji, bana son abinda ya faru dani a baya yanzu ma ya sake faruwa, zan iya kashe kaina in haka ta faru, dan Allah kazo mu canza hanya, wannan basu da imani 'yan shaye shaye ne kawai."


"A'a Khairat bab......." bai qarasa ba yaji saukar abu a kanshi, qarar da Khairat tayi yasa d'aya daga cikin matasan ya fizgota a jikinshi tare da rufe mata baki, duk da girman bugun da suka mishi akai bai fad'i ba, sai dafe kai da yayi yana lumshe ido, kallon matashin daya rik'e Khairat yayi yana murmushin takaici, kamar mai ciwon baki yace "saketa, in kana son kanka da lafiya."

Biyu daga cikin samarin sun fahimci me yace a harshen frensh dan haka suka fad'a musu me yace dansu sunfi jin english, wurga Khairat yayi ga d'aya daga cikinsu, shima rik'eta yayi har yana shafar jikinta, ganin haka yasa Umar Faruk yin kukan kura kan samarin , cikin sauk'i yayi nasarar k'wace madakin dake hannun d'aya daga ciki, nan fa ya soma dukansu kamar Allah ya aikoshi , wani ne yayi nasarar dukanshi ta baya ba tare daya lura ba, qara dafe kai yayi yana ganin dishi dishi ga jiri na d'ibarshi, tangal tangal ya ya fara yana shirin fad'uwa, da gudu Khairat ta rik'eshi ya fad'a kanta, tana daddab'ashi d'aya daga ciki ya finciko gashin kanta yana fad'in "ina kud'i suke? kud'i muke so."

Cikin kuka da d'aga murya tace "babu kud'i a jikinmu, mu bak'i ne."

Rigar sanyinta yaja da k'arfi harta fita ya rage sai qaramar rigarta ta ciki, hannunta ya kamo da k'arfi ta mik'e tsaye yayin da Umar Faruk ya qarasa fad'uwa qasa yana fad'in " idan baku da kud'i, ai kina da kadara, dan haka zamu je dake mu fanshe kud'inmu."

Kururuwa kawai take tana qara tana dukanshi, a hankali Umar Faruk ya bud'a idonshi ya kalli inda suke nufa da ita, wani d'aki dake gefen suka jefata a ciki suka rufe, baya baya take ja d'aya na biyanta yana rage kayan jikinshi, qara ta qurma da k'arfi wacce tasa Umar Faruk mik'ewa zunbur, ai kuwa tunkarar d'akin yayi cikin wani sabon k'arfi da yake ji yana zuwa mishi, qafa yasa ya dinga bugun k'ofar, ana uku kuwa ta bud'e, yanzun ma dai saida aka kai ruwa rana kafin yayi nasara a kansu, wanda ya fara fitar da kayanshi ne Umar Faruk ya shak'e mishi wuya cikin zafin rai yana fad'in "me kayi niyyar aikatawa a kanta, fyad'e, shin kasan me iyali yake nufi, kasan me ake cewa mata, kasan me mutum zaiji idan akace an yiwa matarshi fyad'e a gaban idonka, shin kasan me zai ji?"

Ya qarashe da had'a kanshi da bango, zubewa yayi kamar ba rai a jiki, tsorata da Khairat tayi yasa ta kama hannun Umar Faruk da sauri suka fito daga d'akin, Khairat har had'awa take da gudu gudu, yayin da Umar Faruk zuciyarshi ke bugawa da k'arfi yake jin inama yaci naman yaran nan d'anye , dan wani sabon tsumi suka tayar masa tare da tuna su Musa, cikin sauk'i suka samu taxi suka koma masaukinsu , suna daf da shiga Umar Faruk ya lura da rigar dake jikinta, cire rigar sanyinshi yayi ya mik'a mata ta saka sannan suka wuce d'akinsu, cike da tsoro da fargaba Khairat tasa key ta murzawa k'ofar d'akin, tana juyowa taji saukar wani azababben marin daya sa ta fad'i gefe d'aya....


_Tohhhhhh, me kuka ce yan uwa?_
20/08/2019 Γ  14:26 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


_Bismmilahir-rahman-rahim_


4⃣8⃣



Dafe kunci tayi lokacin data kwamtsa qara dan a bazata marin yazo mata, da'gowa tayi ta kalli Umar Faruk ba tare data tashi daga fad'uwar da tayi ba, za tayi magana kuma ya sunkuya yasa hannu ya shako wuyanta rai b'ace ya had'ata da bango yana fad'in,

"Ke mahaukaciyar inace, ke wace irin sakarya ce, au dama haka ake miki fyad'en, ba kya iya kare kanki sai dai kawai ki dinga kuka, me kike tunanin zai faru idan da sun sake maimaita abinda ya faru a baya, ni sakarai saina sake hak'urin zama dake? sam ba zai yiwu ba wallahi, da kin bari haka ta faru dana rabu dake, danni ba sakarai bane da zan zauna ina qarasa ragowar 'yan iskan gari."

Hannun daya shak'e mata wuya dashi ta kam tana so ta kwaci kanta, idonta duk sun fito ta rasa shed'a cikin wahala da fafutukar neman rayuwa tace "Fa...faru.k, ka...k..ka sakeni, zan..... zaka...kasheni.."

Sakinta yayi ya tashi ya fara cire kayan jikinshi ya shiga douche, binshi tayi da wahalallen kallo tana kallon jinin dake bin kanshi, da qyar ta rarrafa ta rakub'e qasan gado tana kuka, tana nan harya fito d'aure da towel ya shirya cikin gajeran wando ko riga bai saka ba, wani hankciep ya d'auka ya d'aure kanshi kafin ya bud'a wata drower ya d'auko paracΓ©tamol, wanda ake ajewa saboda irin haka dama yasha sannan ya zauna akan kujera, matuk'a ranshi a b'ace yake dan haka ko kallonta baiyi ba, kuka take amma babu mai rarrashi sai dai ta juya ta saci kallon Umar Faruk, amma shi ko kulata baya yi, share hawayenta tayi ta tashi ta zagaya inda yake ta tsaya, d'ago da jajayen idonshi yayi ya wurga mata harara, jiki na rawa tayi saurin zube gwiwoyinta qasa, a hankali ta qara satar kallonshi, ganin yanda ya kafeta da ido ba annuri fuskarshi yasa ta sake fashewa da kuka, wani dogon tsaki yaja ya kawar da kai gefe yace "kije ki kwanta bana son kukan nan, idan kuma ba haka ba ranki zai qara b'aci."

Cikin fashewa da sabon kuka tace "dan Allah Faruk kayi hak'uri, wallahi bana da laifi, ya kamata ka...."

Cikin d'aga murya yace "kije ki kwanta nace ko."

Tashi tayi ba yanda ta iya, ko kayan jikinta bata cire ba taja zanin rufa ta rufe tana shashek'ar kuka, kusan minti ashiri babu mai magana sai jiniyar kukanta, cikin dakkakiyar murya yace "ki rufe min bakin nan fa."

Hannu tasa ta rufe bakinta tana fitar da sautin kukan a hankali, jin tak'i yin shiru yasa ya taso yazo gabanta yace "nace kiyi shiru, amma saboda kin rainani kin k'i kiyi shiru ko? to tashi zaune."

Tashi tayi zaune taja zanin rufa ta rufe bakinta tana kallonshi tace "kayi hak'uri na daina."

Kan gadon ya hau ya jingina ya mik'e qafafunshi yaja zanin rufa ya d'auki wayarshi ya fara dannawa, kallonshi take ganin baya kulata daga haka har bacci ya d'auketa daga zaune, jin yanda take sauke numfashi yasa ya d'an juya ya kalleta, ganin tana bacci yasa ya aje wayar gefe ya gyara mata kwanciyarta, kallon fuskarta yake sosai yana jin sonta na qara huda mushi zuciya, wani b'angare kuma tunanin abinda ya faru a baya da wanda yaso faruwa yau ne yake, a ranshi yace "wallahi Khairat zan kashe duk wanda ya sake keta miki haddi, haka kema zan iya kashe kaina danna huta, ki kiyaye kuma ki kare min mutuncinki."


Haka suka tashi suka shirya dan komawa qasarsu amma babu mai magana, Khairat har gaisheshi tayi amma bai amsa ba, kuma a haka har suka hau jirgi, suna cikin jirgi Khairat ta kalleshi cikin taushin murya tace "baby, dan Allah ka daina fushi dani, bana da laifi a cikin al'amarin nan, ba zan iya shiga qasarmu ba alhalin kana fushi dani, dan Allah ka yafe min."

Kallonta yake kamar ba zaiyi magana ba ita kuma tana sunne kai, hannayenshi ya bud'e mata alamar ta taho, saida tayi murmushi kafin ta fad'a jikinshi ya rumgumeta, wasu hawaye ne suka taho mata tace "Faruk ina sonka, dan Allah karka hukuntani ta hanyar nesanta kanka dani, ba zan iya jura ba."

Saida ya sumbaci kanta yace "kiyi hak'uri baby, rai nane kawai ya b'ace, amma nima ba'a son raina nayi ba, amma ba zan sake maimaitawa ba, nima ki yafe min kinji."

D'ago ido tayi ta kalleshi tace "ba zan yafe ba, sai munje gida na rama sannan zan huce."

Kallon idonta yayi yace "kina so na mutu ko?"

"A'a." ta fad'a cikin taushin murya.

"To karki fara ramawa, dan zaki gane mijinki ragone idan ki kayi haka."

"Ba wani nan, bayan jiya ka nuna min zaka iya acting as sadaukin jarumi."

Nanma qwayar idonta ya kalla yace "zan iya komai a kanki Khairat, na fad'a miki zan iya indai akan sonki ne."

"Ina sonka." ta fad'a tana qara qwaqwumeshi.

Sun sauka lafiya kuma taxi ya kaisu gidansu Papa, bayan Umar Faruk da Papa sun tattauna sannan ya d'auki motarshi suka tafi

Please Login or Register in order to submit comment