Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hannuna , kuma kare mutuncinta yana wuyana ne, dan haka ki kiyaye, sannan idan kin shirya aurena to ki shirya dabarun zama dani lafiya."

Yana fad'a ya fito daga d'akin yayi wa tanti sallama yayi gaba ranshi na quna , wai tun yanzu kenan za'a fara caza masa kai, sai lokacin kuma ya dinga tunano abinda ya fad'a mata akan Khairat, duk da ba sonta yake ba amma yaji dad'i dan ko ba komai dai dole ya kare mutuncin kowace a cikinsu idan har suka zama nasa dukansu.

*****************

Khairat na bacci ka tasheta saboda bak'i na shirin tafiya, sallama suka dinga mata ana sake mata addu'a Allah ya bada zaman lafiya, ita kuma tana yak'e tana amsawa da ameen ameen 😁, har suka gama tafiya ya rage sai Mammie a gidan, bayan sallah azahar suka tafi da Hibba salon aka cire mata akaihun data saka dogaye da kuma gyaran da aka mata aka aka gyara mata aka mata kitso manya, bayan la'asar suka dawo gida tayi wanka tayi sallah taci abinci, ita da kakarta sai farin ciki suna hira cikin nishad'i.



*Bayan sallah magrib* Papa ya tafi masallaci d'aukar karatu, kamar kullum saida sukayi sallah isha'i aka sallami kowa, anan Baba ya tsayar da Papa ya fad'a masa maganar auren Umar faruk, farin ciki Papa yayi tare dasa albarka kuma yace zasu halarci d'aurin aure insha Allah.

Bayan yazo gida ya fad'a ma Mamie da Mammie, Mamie ce kawai tace "Allah ya basu zaman lafiya ya basu hak'urin zama da junansu, a fad'a mata kawai tasan halin da ake ciki."

"A'a." cewar Papa sannan ya d'ora da "ba hurumin mu bane, ki bari mijinta zai fad'a mata da kanshi, shi yasan ta yanda zai tarota."

"To shikenan, amma ni dai wallahi ina son yaron nan sosai, dan nasan shi kad'ai ne zai iya tafiyar da Khairat a matsayin miji, kuma ina ji a jikina zata gyaru ta dalilinshi ne insha Allah."

Papa ne yace "nima yaron ai ya kwanta min a rai sosai, dan ba kowa bane zai iya yin *jihadin* da yayi."

"Sosai kam, dan da yanzu bamu san halin da muke ciki ba dukanmu, nadai tabbatar bama cikin yanayin dad'i." cewar Mammie.

Dariya Mamie tayi tace "ai yaron kirki ne kuma ya samu tarbiya, tunda ba shine karo na farko ba daya taimakemu."

"Kin sanshi dama? wane irin taimako yayi mana?" inji Papa.

"Shine fa yaron daya je asibiti yana son ganinka, wanda ni na fito na ganshi kuma shiya fad'a min inda aka samu masu laifin nan, kaga ba danshi ba da yanzu muna nan tare dasu."

"Allahu Akbar, lallai ya mana taimako, babu abinda zamu saka masa dashi sai dai addu'a da fatan alkairi, Allah kuma yasa kar yarinyar nan ta bamu kunya."

Mamie ce tace "ameen, amma dai nasan zaiyi wuya a samu sauk'in al'amari daga wajen Khairat."

Mammie ce tace "ba zata bada matsala ba insha Allah."

"Allah yasa."

Suka amsa da "ameen."

********************

*Haka* aka dinga tafiyar da rayuwar ba dad'i ba wuya, Khairat rayuwarta take kamar babu auren kowa a kanta, sai dai Mamie ta hanata fita ko k'ofar gida, itama kuma bata damu ba tunda tana sakewa a cikin gidan, zuwan Mammie ya sata farin ciki sosai kullum suna tare suna shirmensu kamar yanda suka saba.


Sai dai kuma har yau basu had'u da Umar Faruk ba, kamar yanda basa da lambar juna bare wani ya kira wani, sau d'aya yazo da sassafe tana bacci, yace agaisheta kawai zai dawo har yau kuma bai koma ba.


*****************

Umar Faruk ma shirye shiryen wani sabon auren yake tayi hakan yasa ma baya da lokacin kanshi sosai, sai dare yayi kuma sai Khairat ta sallamo mishi ta hanashi bacci, tunaninta na takura masa yana hanashi sukuni sosai, wani lokaci har yakan manta da Zuby a rayuwarshi saboda katutun da Khairat tayi a zuciyarshi.

*Kwana hud'u* yau da auren, Mamie ta tura Mamar Hibba da tanti Safiya gidansu Umar Faruk ganin d'akin Khairat, su kad'ai ne ta yarda dasu da kuma hallayarsu shi yasa ma ta turasu su kad'ai, sunje cikin aminci kuma sun dawo cikin farin ciki saboda tarbar da aka musu, sun fad'ama Mamie komai akan gidan dama d'akin inda tanti Safiya ta qara da cewa "gaskiya rayuwa dai ta mai qaramin k'arfi, to wannan d'akin na Khairat ya ishi bawa rayuwa kuma cikin farin ciki."

Sai dai Mamar Hibba tace "amma ko kad'an kayan da aka saka mata a d'akin Muzaffar ba za suyi a wannan d'akin ba."

Hakan yasa Mamie turawa aka d'auko kayan Khairat daga gidansu Muzaffar aka sasu kasuwa, a take kuma aka siyo mata wasu sabbi yan zamani masu bala'in kyau, *ranar alhamis* aka mata jere a d'akinta, masha Allah yayi kyau sosai duk da d'aki d'aya ne amma zai birge, haka yan gidan suka lek'a suka ga d'aki yayi tsaf dashi, ga kayan kallo da aka lak'a mata panka da k'aramar fridge, matasan kujeru ne aka aza a d'an k'aramin farfajiyar kewayenta , sai babbar kujera a cikin d'akin ta zaman mutun uku, saman wradrob kam cike yake da manyan darori da bargo , ciki kuma bayan kayan jiki sai kwanoni da sauran kayan aikin gida, a kusa da taga ma wasu darorin ne aka jerasu har suna kusan tab'a rufin d'akin saboda yawa, haka aka rufe d'akin ana jiran asabar tayi maishi ta shiga.

Duk wani abu da Muzaffar ya kawo saida Khairat ta tabbatar ta mayar masashi a cikin akwatinshi, duk wani abu data d'inka saida tasa aka nemo irinshi sannan tasa aka mayar masa, kamar dai yanda yayi itama motoci ta samu suka kai kayan har gidansu, had'e kuma da makullin motarshi, tunda yaga haka ya tabbatar da aikin Khairat ne ma'ana tayi hushi kenan, bai k'ara tsinkewa da al'amarin ba saida ya bud'e k'aramar motar ya samu goron daya bada da kuma enveloppe, yana bud'awa yaga kud'i ne a ciki kamar yanda ya bada, sai kuma k'aramar takadar data rubuta wasik'a da harshen french cewar,

_"Bani ba kai, ba kai bani har abada, yunk'urin sake shigowa rayuwata a karo na biyu, daidai yake da yak'in duniya na uku, dan ba shakka yak'i ne zai b'arke tsakanin gidanmu da gidanku, *K'ARAMIN MUTUM* kawai._

Hawayen da yaji suna son zubo mashi yasa ya koma cikin gida ranshi b'ace, hamshak'iyar mahaifiyarshi dake zaune a d'akinta tana waya ya fad'a saman jikinta yana kuka, kashe wayar tayi tare da tureshi daga jikinta cikin jin haushi tace "dallah ni dagani shashasha kawai, kasan kana sonta uban wa ya aikeka d'aukar zigar aboki ana daf da d'aura aurenka? kawai saboda rashin tunani da lissafi saika yarda da abinda ya fad'a, yanzu gashi har yau bai sake zuwa inda kake ba, tunda burinshi ya cika."

Ganin mahaifiyar tashi ma ta d'auki zafi yasa ta tashi ya fita ya koma b'angarenshi zuciyarshi kamar zata buga.


****************


Tun ranar Umar Faruk bai sake zuwa gidansu Zuby ba bai kuma kirata ba, shirin d'aurin auren kawai yake yi amma sam ya daina jinta a cikin ranshi, musamman idan ya tuna abinda ta fad'a masa, haka kawai yake jin ba dad'i idan ya tunata yafi farin ciki kawai idan yana tunanin Khairat wacce yake da yak'inin ko sau d'aya bata tab'a tunaninshi ba.


*Yau juma'a* gidan an tashi da shirye shirye da kimtse kimtse, kamar yanda muka sani lokaci na gudu, dan-danan sai aka fara tafiya masallaci, bayan gama sallah kuma aka sake d'aurawa Umar Faruk wani auren, *Umar Faruk Ahmad Adam* da *Zubeida Hamza*, daga masallaci gidan wani abokinshi *Abdul Azeez* suka wuce inda akasha gara tare da tayashi murna, Ishaq dai dariya yake masa duk lokacin da suka had'a ido dashi saboda tamke fuskar da yayi, bidiri sosai abokanshi suka shirya wanda ya kaisu har magrib, suna sallah kuma suka dawo gida inda aka fara shirin walima.

Shiryawa yayi cikin wata sabuwar shadda ruwan toka had'e da takalma sai dai bai d'ora hula ba, yana fitowa ya samu taro harya fara cika, Abdul Azeez ne ya takura masa ya rakashi asibiti yanzu aka kirashi ankai kakarsu ba lafiya, jin uzurinshi kuma tunda bai nemi kowa ba saishi yasa suka shiga mota suka tafi.

****************

*Amarya Khairat* ce zaune a falo a saman qafafun Mammie tana latsa wayarta, kirane ya shigo ta d'auka da "hello macho."

"Gamu a k'ofar gidanku." cewar Rashida.

"Gidan namu kuma mak'abarta ne da ba zaku shigo ba?"

"Kinga kedai ki fito."

"Wai lafiya, meya faru ne?"

"Kai Khairat, kina b'ata mana lokaci fa, asibiti zamu wuce tare da Farida muke."

"To naji ina zuwa."

Mik'ewa tayi daga jikin Mammie ta d'auki kallabin doguwar bleue rigarta ta d'ora a kai tace ma Mammie "su Rashida ne waje wai asibiti zasu, bara naje naji kiran me suke min."

Tana fita Mamie ta fito cikin shirin tarban Papa, zaune tayi tana fad'in "ina ta shiga kuma?"

"Wai Rashida ta kirata suna k'ofar gida."

Zunbur Mamie ta tashi tace "Rashida? na shiga uku, nifa bana qaunar yarinyar nan, wallahi ita ke qara lalata min yarinya."

K'ofa ta nufa Mammie na kiran "ina kuma za kije? yanzu zata dawo fa."

K'ofa ta nufa tana fad'awa mai gadi "kai duba min Khairat, maza ce nace ta shigo ciki."

A cewar mai gadin "a'a Hajia ai har sun tafi."

"Sun tafi ina kuma?"

"Wallahi Hajia ban sani ba, taxi daice suka shiga."

Dafe kai Mamie tayi tace "na shiga, ina zasu je kuma? me zan fad'awa mahaifinta?"

Dawowa tayi tace "Mama kin gani ko? Khairat bata nan wai sun fita."

Kafin Mammie tayi magana ta d'auki wayarta ta fara kiranta, Khairat kuma da tana fita ta samesu a cikin taxi Rashida ce tace "yawwa zo muje."

Ta fad'a tana matsa mata nufin ta zauna, "ina kuma zanje bayan kinsan ba'a barina fita?"

"Kinga asibiti zamu je k'anan Farida ne ba lafiya, dazu aka kaishi ya k'one da ruwan zafi, kizo muje yanzu zamu dawo daga nan sai muyi magana."

Hannunta ta janyo ta fad'a cikin taxi d'in suka ja suka tafi, ba suyi nisa ba kuma kiran Mamie ya shigo wayarta, tana d'auka Mamie tace "kina ina?"

"Mamie ina bisa hanya za muje asibiti ne yanzu zan dawo."

Da sauri Mamie tace "amma kinsan ba kya fita ko ina ko? me yasa zaki fita haka kawai, idan mahaifinki ya dawo ya zance masa?"

"Dan Allah Mamie karki damu, ba jimawa zanyi ba."

Tana fad'a ta kashe wayar ta kalli Rashida tace "wace magana za muyi?"

Kallon juna sukayi kafin Rashida tace "am Khairat, wallahi mutuminki yana cikin wani hali, yana buk'atar taimakonki sosai."

"Wane mutumin nawa?" ta fad'a tana kau da kai.

Farida ce tace "Muzaffar mana, kinga yanda ya koma saboda damuwa, wallahi sai addabarmu yake wai mu taimaka masa."

"Yanzu dama akan maganar waccen banzan ne kuka saka na baro gidanmu ba tare da izinin kowa ba? kinga tsayar da mai taxin nan na koma gida in dai wannan ce maganar."

Rik'eta sukayi suna fad'in "kinga shikenan to, ba zamu sake miki maganarshi ba, yi hak'uri."

Harara tabi kowace a cikinsu tana fad'in "aikin banza kawai, mutumin daya ci min mutunci har zaku wani zomin da maganarsa , shi bai fad'a muku ba komai tsakanina dashi ba, ko sile baya bina bare ya takura min, mak'uddan kud'ad'e na kashe wajen biyanshi abinda ya min."

Babu wanda sake magana har suka isa asibitin suka duba yaron da qafarshi ce kad'ai ta k'one sannan suka tashi zasu koma, bayan mahaifiyar Farida ta gargad'eta akan ta kula da gida da sauran k'annanta, fitowa sukayi suka tsaya a bakin titi suna jiran samun taxi.

*Umar faruk* ne suka fito zasu tafi suma sun shiga mota suka tayar, bakin titi suka tsaya suna so kai kawon motoci ya tsagaita su samu su hau titi suma, a cikin waige waigen da suke sai kuwa Abdul Azeez yace "masha Allah, abokina da alama nima lokacin aurena ya kusa, domin kuwa naga wacce tamin."

Haka kawai sai Umar Faruk yaji gabanshi ya fad'i, daurewa yayi yace "toh , wace mai sa'ar ce wannan?"

"Gatanan gabanka kan gani."

Sai lokacin Umar faruk ya kai kallonshi ga yan mata ukun dake tsaye, hakan yayi daidai da Khairat ta juyo saboda motar dake bayansu ba haskesu sosai, saida ya rintse ido saboda takaici da bak'in ciki, sam fitowa bada izininshi bai dameshi ba kamar rigar dake jikinta.

Duk da bata kamata ba amma da yake tana da 'yar k'iba kuma yadin rigar yadine mai bin jiki, hakan yasa ya hango shatin kwanciyar pants d'inta da kuma bras d'inta, ga kuma kallabin k'aramin hakan yasa gashinta ya fito har ya kusan rufe shatin bras d'inta, duk da dai baida tabbacin gashin kanta ne, ranshi ya b'ace sosai musamman da abokin nashi ya haskesu da mota yana mata kallon k'wak'waf, dan suma k'awayen nata duk shigar tasu babu mai dama dama a cikinsu.

A fusace ya fita daga motar ya tsaya bayanta ba tare da yayi magana ba, jin kamar mutum a bayanta yasa ta juyo dan ganin wane d'an rainin wayone, a take gabansu ya tsinke ya fad'i sai kallon kallo da sukewa juna, kasa magana tayi dan har cikin zuciyarta taji bata ji dad'in ganin daya mata a haka ba, kasa d'auke idonta tayi daga kanshi shima kuma haka.

Rashida ce tace "macho, kin sanshi ne?"

Had'iye yawu tayi ta kalli Rashida, muryarshi ta dawo da ita da yace "wuce muje."

Kallonshi tayi amma wani irin bala'in kwarjini daya mata sai yasa ta nuna su Rashida da hannu, wani sabon kallo daya mata da idonshi fuskar nan ba hasken annuri ya sake cewa "wuce muje gida."

"Amma ai....."

"Nace ki wuce mu tafi ko." tsawar daya mata yasa ta kama hanya ba shiri , ganin haka yasa yabi bayanta ya bud'e mata bayan motar ta shiga, tana kallonsu Rashida suka wuce suka barsu, su kuma mamaki suke ko wanene shi, Farida ce tace "nifa ina tunanin ko shine mijin nata."

"In kuwa shine gaskiya yarinyar nan mai sa'a ce, danni kin sanni fa ina son namiji irin wacce wallahi, da irinsu sunfi dad'in harka.

Farida ce tace "ki daibi a sannu, dan kinsan yarinyar can ta fiki akuyanci, mijinta kuma yafi k'arfinki."

******************

Tunda suka d'auki hanya babu wanda yace tak , tafiya kawai suke Abdul Azeez kuma da kanshi ke kulle bai samu damar magana, dan yasan tabbas akwai wani abu a qasa saboda yanda yaga Umar faruk ya mu'amulanci Khairat d'in yasan ba sanin yanzu bane a tsakaninsu, Khairat kam tayi iya k'ok'arinta wajen ganin gabanta ya daina fad'uwa amma ta kasa, kamar yanda Umar faruk kejin haushinta da takaicin aurenta da yayi, a haka suka isa gida da kanshi ya fito ya bud'e mata k'ofar ta fito babu wanda ya kalli wani, izuwa yanzu kuma Abdul Azeez ya gane kuskure yayi dan ko ba'a fad'a ba wannan itace 'yar Mani Bukar.

Wucewa tayi zata shiga shima yabi bayanta, tana daf da shiga gidan yace "kina haukane da kika da wannan kayan a jikinki, sannan da izinin wa kika fita?"

A hassale ta juyo tace ".....
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


_Bismmilahir-rahman-rahim_

😭😭😭😭😭😭😭😭
_ALLAH KA SHIRYA MANA YARANMU MAZA DA MATA, ALLAH KA BAMU IKON TARBIYANTAR DASU, AL'AMARIN NAN YA FARA BANI TSORO WALLAHI, YARA QANANA SUN D'AUKI D'ABI'A MARAR KYAU, WASU GANI SUKE WASU KUMA YIN KANSU NE KAWAI, ALLAH UBANGIJI KA KARE MANA 'YA'YANMU DAGA B'ATA GARIN ABOKAI, ALLAH KA BAMU IKON KIYAYE DUK WANI ABU DA ZAI HASKU A IDON 'YA'YANMU HAR SUYI SHA'AWAR KWAIKWAYA._πŸ‘πŸ‘
😭😭😭😭😭😭😭😭


2⃣0⃣


"Ban gane ba, me kake nufi, me kayan jikina sukayi, wai ikone zaka min tun ban tare gidan naka ba? ina ruwanka da kayan jikina to? kana da matsala da hakan ne? karfa kace zaka rainani saboda kaji ance an daura mana aure, wallahi ba dauka zanyi ba kaji na fad'a maka, haka kawai zaka wani tsareni harda tambayar wai da izinin wa na fita, bayan a gidan mu nake har zaka min wannan tambayar, ko kana ganin iyayena basu da ikon da zasu bani damar fita? to in dai kai zan dinga tambaya kafin na fita da sai dai karna fita har abada, dan ba zan iya qasqantar da kaina har haka ba, kuma wallahi ka fita idona, kar kace zaka sake min irin tsawar da kamin d'azu musamman a cikin mutane, in kuma ba haka ba."

K'wafa tayi mai k'arfin gaske ta juya zata shiga gida, wata fizgowa ya mata saida ta kai mashi karo a qirji, turata yayi ta kaima bango karo ya mata runfa da faffad'an jikinshi, kafeta yayi da ido sunyi ja saboda zafin maganganunta fuska a d'aure ba alamar wasa cikin dakakkiyar murya yace "waye ni?"

Cike da tsiwa tace "waye fa daya wuce d'aya daga cikin gama garin mutane."

Rufe ido yayi ya sake maimaita "waye ni nace?"

Kallonshi tayi da ido tace "Umar....Faruk mana."

"Nace waye ni a wajenki?" tsawar daya mata har saida mai gadi ya leko, amma ganin Khairat da angonta yasa ya koma, ita kam yanda muryarshi ta daki k'ok'on kanta yasa ta zabura da k'arfi tare da fashewa da qara har wayarta ta sub'uce ta fad'i, hannayenshi yasa a jikin bango kamar zai rumgumeta ya sake tsareta da ido yace "ina jiran amsarki."

A hankali ta daga idonta ta kalleshi amma sai hawaye suka zubo mata, kau da kai tayi ta sauke ajiyar zuciya ba tace komai ba, sake matso da kanshi yayi daf da fuskarta yace "zamu kwana anan in har baki fad'a min ba."

Cikin daga murya da jin zafi tace "to waye kai? me kake so nace? so kake nace *mijina*? to naji kaine *Umar faruk mijina*, shikenan? to kauce min a hanya zan wuce."

Wani d'an iskan murmushi yayi mai kama da kuka tare da fad'in "humm." kafin yace "daga yau ina so na dinga jin muryarki k'asa da tawa, idan kuma kika bari k'uruciya da hauka irin naki yasa kika d'aga min murya, to ki kuka da kanki, dan zan miki abinda kaf a tarihi babu wanda ya kwatanta yi miki shi."

Sunkuyawa yayi ya d'auki wayarta ya dangwara mata a hannu sannan ya juya ya shiga mota tana kallonshi har suka b'acema ganinta, juyawa tayi ta shiga gida kamar zata tashi sama, har Papa na falo suna jiran dawowarta, a tare suka mik'e ganin ta shigo da sauri tana share hawaye, Papa ne ya fara tambayar "shalele lafiya, meya faru kike kuka."

Mammie ma d'orawa tayi da "shalele meya sameki, wani abu aka miki?"

Kallonsu tayi cikin muryar kuka tace "karku damu ba komai."

"Ya zaki ce ba komai? bayan kin fita cikin farin ciki kin dawo kina kuka, kuma an fad'a min wad'ancen yan iskan yaran ne suka fita dake."

Ganin zasu takurata yasa tace "Mamie ba komai fa, tare dashi muke."

"Shi wa?" cewar Papa.

Turo baki tayi gaba tace "Umar Faruk."

Fuska kowa ya saki yana murmushi har Mammie tace "to kuma a waje kika baroshi?"

"Harya tafi." ta fad'a tana wucewa d'akinta.

_Abinka ga manya_ duk sai sukayi tunanin ko zaman da tayi na sati d'aya ne yasa ya gagara hak'uri, shi yasa suka fita ya d'an rage zafi, πŸ˜‚ masu hangen nesa kenan, wannan hasashen naku ba yau ba ba kuma gobe ba.


Cikin b'acin rai da bak'in cikin abinda Umar Faruk ya mata ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin rigar bacci doguwa, dole ta toshe kunnuwanta da abin sauraro danta rage zafi.

*******************

Tunda suka d'auki hanya babu wanda yayi magana, amma saboda ya nuna masa baisan komai ba yasa Abdul Azeez cewa " *wacece ita*?"

Kamar ba zai amsa ba amma kuma ba tare daya kalleshi ba yace " *matata ce*"

Shiru yayi dan duk wata magana da zaiyi yanzu zai iya janyo b'acin rai fiye da yanzu, har suka isa babu wanda ya sake magana, suna zuwa tuni taro yayi taro *ustaz Khalid* nata bada wuta, nan ya fara gaishe da malamanshi da uwaye da kuma kakanni , tare da sake miki gargad'i da nasiha akan rik'e adalci da gaskiya, wuri ya samu ya zauna kamar mai sauraron abinda ake amma a gaskiyar lamarin ba haka bane, harya fara hango irin rayuwar da zaiyi a tsakanin d'akin Khairat da d'akin Zuby, Zuby akwai k'arancin wayo, Khairat kuma da wayonta zata b'ata maka rai, amma dole ya d'auki matakin gyara tun kafin lokaci ya k'ure masa.

****************

Zuby ce tsakiyar aunyt's d'inta guda uku, sun gama zigata tare da hure mata kunne, sun cire mata soyayya da tausayin Umar Faruk a ranta tun kafin aje ko ina, tilasta mata sukayi ta kurashi ta bashi hak'uri akan abinda ta masa, saboda akwai wani magani da suka siya mata, kuma dole aiki dashi sai suna shiri dan suna son ya kusanceta, wayar ta d'auka ta kirashi lokacin yana tsaka da tunani, yayi mamakin ganin kiranta sosai dan abune da bai tab'a faruwa ba suyi fad'a ta kirashi sai dai shi ya kira, dauka yayi baice komai ba, cikin taushin murya tace,

"Amincin Allah ya tabbata a gareka angona yayah Umar."

Nauyayyan ajiyan zuciya ya sauke yace "amincin Allah ya tabbata a gereki."

Cikin shagwab'a tace "kenan ba zan samu ko wane irin suna daga gareka ba?"

Murmushi tayi yace "ina tsoron nace amaryata kuma kiyi hushi ne."

Cike da wayencewa tace "ba komai yayah Umar, ka kirani amarya zan amsa, tunda aunty Khairat ta rigani zama taka."

"A'a, har yanzu fa babu wacce ta shigo hannuna, dukanku dai ina jira ku gama wainani sannan ku shigo gidan."

Haushi ne ya kamata danta lura soma yake Khairat ta shigo gidan bayan yace taimako yayi, shi kuma baya so ne ya bada wata k'ofa da zata sa Zuby ta raina Khairat musamman ace ta dalilinshi, koba komai itama matarshi ce kuma uwar gida, a dak'ile tace "dama na kirane na baka hak'uri abisa abinda ya faru, dan Allah ka yafe min ba zan sake ba."

"Ba komai k'anwata, ya wuce ai."

"Na gode, saida safe, dan naji kana cikin jama'a."

"Saida safe." ya fad'a suka tsinke kiran.


Haka taro ya tashi lafiya bayan addu'o'in da aka zuba musu, dare yayi kowa ya kwanta amma banda Umar Faruk, a qarshema d'akin Khairat ya bud'e ya shiga, fitilar d'akin ya kunna a hankali ya dinga sauke numfashi saboda wani baqaraken k'amshi dake shigar hancinshi, had'e yake da kamshin turaren wuta da kuma turaukan dake zube a saman coiffeuse da mayuka har babu wurin aza wani abun, bin d'akin yake da kallo ko ina yana kallon irin kayan da aka cika d'akin dashi, wai nan danma yana ba'a samu irin wurin da ake so bane, kusan komai na d'akin pink couleur ne hakan yasa yace "da alama shine couleur prΓ©fΓ©rΓ© (best coulor) d'inta."

A sannu yake tunanin ranar daya fara shiga d'akinta yana fad'in "girman d'akinta shine kaso d'aya na bisa ukun gidan nan, girman gadonta kuma d'akin nan ba zai daukeshi ba, duk da banga ban d'akinta ba, amma na tabbata ta kusa girman d'akin nan."

Ajiyar zuciya ya sauke tare da sakin murmushi yace "taya zata iya rayuwa a d'akin nan? bayan gashi tagar dake akwai ma kaya sun rufeta, taya zata iya rayuwa da wannan pankar? bayan acan ac take kunnawa , taya zata iya rayuwa a gidan nan da mutane haka? bayan ita acan ita kad'aice ba k'ane ba k'anwa ba yaya ba aunty."

_Wannan itace rayuwar daya kamata ta fara kota koyi hankali_


********************

*A b'angaren* tunda aka tashi da safe ta tashi jiki ba k'wari, gashi Mamie ta kira mai kitso amma sam tace bata so, ayi juyin duniya tace ba taso dole aka barta, da qyar ta bari aka mata jan lalle tunda waccen ya goge dan jikinta baya da kama lalle, duk da mutanen da suka zo dan rakiyar amarya Papa yace sam bashi ba wannan bidi'a, dan haka da kanshi zai kai yarshi gidanta tare da rakiyar kakanninta.

Abin yama Khairat yawa dan haka tun yamma ta fara kuka, amma sai tace musu kukan rabuwa ne dasu, haka akayi magrib akayi isha'i, ba wani shiri tayi ba atamfa ce ta zabga riga da zane d'inki simple, kasancewar bata tab'a saka zane simple ba saiya mata kyau d'as, Mammie da Hajia *Maryama* ne suka kamata Papa da kanshi ya tuk'a mota suka nufi gidan amarya bayan d'an jan kunne da Mamie ta

Please Login or Register in order to submit comment