Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

murayr duka yaran dake d'akin ta daki kunnuwanta.

D'an murmushin gefen labb'a kawai ta musu kafin suka juya kan Umar Faruk suka ce "ina kwana yah Umar."

"Lafiya lau, kun tashi lafiya?"

"Lafiya lau." suka amsa.

"Mama kinsha maganinki?" cewar Khairat.

"A'a 'yata, yanzu dai zanci abinci sai nasha."

Juyawa tayi ta kalli Ruk'ayya dake shirin fita tace "har yanzu baku gama bane?"

"Eh aunty Khairat, yanzu ma zan d'ora."

"Me? yanzu fa? kuma Mama ta zauna tana jiranki? me yasa ne wai kuke haka? kamar dai baku damu da ita ba."

Mtsssss, taja tsaki tare da tashi rai bace ta fita daga d'akin har tana karo da Abbakar da Saratu da zasu shigo suma, wayarta ta d'auko ta dawo d'akin tana ci gaba da kira amma ba'a d'auka, saida ta aika kira na hud'u sannan mutumin ya d'auka jiki na rawa, tana jin ya d'auka tace "ka kyauta, amma yanzu bata kai nake ba, ka gaggauta had'a min duk wani abinda kake dashi yanzu, amma karka saka arom (d'and'ano) a ciki na mai tension ne, da zaran ga kama ka kirani."

"To Hajia." ya fad'a ta kashe wayar.

Umar Faruk ta kalla wanda suma dukansu kallonta suke tace "dan Allah ka d'auki makullin motata kaje *riva side* ka karb'owa Mama abinci."

Fita tayi shi kuma yabi bayanta, makullin ta d'auka ta bashi ta bud'a post d'inta ta d'auki kud'i ta bashi, kai ya girgiza mata yace "ki barshi zan biya."

"Kai kayi magana a maka oder koni? kaine ka sani koni nayi niyya? dan haka karb'i kawai."

Karb'a yayi ya cire doguwar rigarshi ya sake kayan sannan ya fita, yana fita ita kuma ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin riga da siket na shadda, kwalliya tayi sosai kafin ta d'ora gyale a kafad'a ta d'auki jaka da takalmi, wayarta ta d'auka da nufin kiranshi sai gashi ya shigo, hannu kawai ta tara masa ya bata makullin sannan ta fita.

Bayanta yabi amma sai yaga ta shiga d'akin Mama, Mama ce kad'ai a d'akin dan haka ta sake zubewa qasa tace "ga abinci nan kici Mama, sannan ki saka min albarka zan fita wajen aiki."

"Allah yayi albarka yata ,daga yanzu har zuwa fitar numfashina na qarshe sanya albarkata ba zai tab'a nesanta dake ba."

"Na gode Mama." ta fad'a tana yunk'urin tashi.

Hannunta Mama ta rik'e tace " 'yata."

Komawa tayi yanda take tace "na'am Mama, akwai abinda kike sone?"

"A'a 'yata, ina so na fad'a miki wani abu."

"Ina jinki Mama."

" 'Yata, wannan kayan na jikinki, bai kamata ki fita dasu ba a matsayinki na matar aure, ki sani Allah ya umarcemu damu dinga rufe jikinmu a duk lokacin da zamu fita daga cikin gidajenmu, kuma hakan nada alfanu sosai, hakan da zaki fita baiyi ba sannan shi kanshi mijinki zaiji ba dad'i, yata, ina so ki zama salihar mace kuma yar aljanna, amma fa ki sani ba'a zama salihar mace a haka, dan Allah yata ki kare mutuncinki ko dan gudun sake faruwar abinda ya faru dake a baya, ki kame kanki ba kowa jaki da alade bane ya kamata ace sunga surar jikinki, idan zai yiwu ki gwada saka hijab ki gani, na tabbata zai miki kyau, dan sutura ce mai rufa asirin mace tare da qara mata kwarjina da haiba."

Murmushi Khairat tayi ta sake makale hannun Mama tace "na gode Mama, kullum mahaifiyata na fad'a min na dinga rufe jikina, yau kema gashi kin fad'a min, hakan na nuna irin soyayyar da kike min."

Tsaye ta mik'e tace "ina zuwa Mama."

Nan ta bar jakarta ta fita ta koma d'akinsu, cikin hijabban da Mama tasa aka d'inka mata ta d'auko kalar aikin shaddarta ruwan qasa, tana saka hijab d'in ta kalli kanta a madubi, wani murmushi ta saki ganin yanda ya d'auki jikinta ga hannayenta da suka fito ya tsaya iya gwiwarta, fita tayi daga d'akin ta koma na Mama, su Mama Sa'a mamaki ne ya kamasu ganin tana safa da marwa a d'akin, tana shiga Umar Faruk da Mama suka sakar mata ido, tsaye tayi gaban Mama tace "Mama haka yayi, nayi kyau?"

"Yata fad'ar kyan da ki kayi ma bata bakine , Allah ya kareki."

"Ameen Mama, na gode saina dawo."

Tana fad'a ta d'auki jakarta ta bar d'akin ko kallon Umar Faruk, tana fita ta d'auki hanya amma saboda rashin sabo yasa taji kamar an d'aureta , kasa jurewa tayi hakan yasa ta cire ta ajeshi saman kujera harta isa ma'aikatar, d'aukar hijab d'in tayi ta saka ta d'auki jakarta sannan ta fito, da gudu massinger yazo ya tareta yana gaisheta, hannu kawai ta d'aga masa tayi gaba, tunda ta shiga idon kowa ke kanta suna gaisheta da mamaki, kowa da abinda yake sak'awa a ransa, Khairat a wajen aiki tunda safe haka gashi ko Umar Faruk d'in bai zo ba, sannan da sabuwar shiga, harta tunkari office d'inta, dago ido Habiba tayi amma saita saukesu ba tare data mik'e tsaye ba kamar yanda ta saba, saida Khairat ta tsaya gaban tebur d'in tana kallonta, k'amshin turaren da taji ya tabbatar mata Khairat ce, a zabure ta tashi tsaye tana fad'in,

"Kiyi hak'uri Hajia, wallahi ban...ban ganeki bane."

"Wato *arniya kafira* yau ta shigo da hijabi, shi yasa har zaki kasa ganeni? dama wad'ancen shashanshun sun bini da ido, shine kema zaki min fitsara."

Wucewa tayi mazauninta tana shiga ta zauna kuma ta cire hijab d'in ta rataye, a gaba d'aya ma'aikatar kuma maganganu aka d'auka, wasu na ganin Umar Faruk yayi namijin qoqari da har ya iya canza Khairat a qanqanin lokaci haka, wasu kuma na mamakin ta yanda ya iya juyata harta zama haka.

_FAN'S ya kuka ce? nifa sai nake ganin kamar qoqarin na Mama ne ba Umar Faruk ba._

Abun mamaki jakarta naga ta d'auka kawai ta fito da littafin da Umar Faruk ya bata, budawa tayi ta fara karatunta a hankali daki daki , dan bata so gobe ya tambayeta ta kasa fad'a mashi, kodan gudun bulala.πŸ€ͺ

_Shin kuna ganin zai iya dukanta idan ta kasa kawo karatun daya koya mata?_
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

_Bismmilahir-rahman-rahim_


2⃣7⃣


Tunda ta fita ya bita da ido, Mama ce tayi murmushi tace "tana da taushin zuciya, cikin sauk'i zata dinga fahimtarka in dai kana binta a hankali."

Shiru yayi shi dai abinda kawai yake ji a zuciyarshi yake so ya gano ko menene, "ka tashi kaje ka shirya karka makara kuma." muryar Mama ta katseshi.

Tashi yayi cikin sanyin jiki ya fara shiri harya gama, tsaye yayi bakin madubi yana b'alla mab'allan rigarshi tare da wani hamshak'in murmushi a fuskarshi, yana gamawa ya makala agogo sannan ya d'auki jakarshi ya rataya zai fice, rigar baccin data cire da asuba ya gani akan gado ya d'auka, rufe fuskarshi yayi da riga yana shak'ar wani tattausan k'amshi da ba zaka tab'a jinshi ba in har ba shak'a kayi ba a kusa, aje rigar yayi amma har yanzu ya kasa daina wannan tsadaddan murmushin, ko kari baiyi ba kawai ya fita saboda ji da yake yana so ya kusanta da ita, wayarshi ya d'auka akan tebur har zaisa aljihun riga kuma saiya k'ura mata ido, tunawa yayi da wajen da wayar ta shiga jiya, wani murmushi ne ya sake sub'uce masa hakan yasa ya mannawa wayar sumba tare da mannata a qirji, haka ya d'auki hanya cike da sabon yanayi a tare dashi da sabon farin ciki, yana shiga yau ma dai haka gaisheshi wasu keyi cike da girmamawa wasu kuma tsabar izgilanci ne kawai, zaune yayi ya fara abinda ya kawo, alk'alami ya d'auka da farar takarda ya fara zana wani sabon sanfirin takalmin, ji yake yana so yaje wajenta amma kuma yana jin fargaba, jin ya kasa samun sukuni yasa kawai ya tashi ya nufi wajenta zuciyarshi na d'ard'ar na abinda zata masa ko zai tarar.


Koda Habiba ta ganshi ta tashi ta bud'e masa k'ofar tare da gaisheshi, shiga yayi cikin sakin fuska amma saiya tsaya cak yana kallon Khairat, chocolat a hannu tana sha sai kuma littafinta data duqufa da karatu, d'ago kai tayi tana ganinshi ta saki murmushi tare da fad'in "yawwa, qaraso mana."

K'arasawa yayi zauna kujera yana kallonta, tasowa tayi daga kujerarta ta zauna kujerar kusa dashi ta aje littafin tace "bara na karanta maka kaji, saika sake d'ora min wani."

"Anan d'in?"

"Eh miye to, ba bureau na bane?"

Basarwa yayi kamar ba ganinta ne ya kawoshi ba ya mike tsaye yace "ba zan iya ba, kuma shine kika cire hijab d'in ko? ai za muje gida saina fad'awa Mama ta janye sawar albarkarta."

Juyawa da yayi zai fita yasa tayi saurin tashi da nufin ta riko hannunshi, sam bata kula da inda ta rik'e ba sai zuba take tana fad'in "dan Allah malam kayi hak'uri karka fad'a mata, wallahi na daina daga yau, kuma rashin saboda ya janyo haka, kaima kasan ai ba zan yaudari Mama ba, dan Allah karka fad'a mata."

Da k'arfi ya fizgota ta fad'a jikinshi yana mata wani kafirin kallo mai kashe jiki yace "to cire hannunki."

Ido ta bud'o tace "a ina?"

Raba jikinsu yayi ita kuma ta kai kallonta ga hannun nata, d'aya hannun tasa ta rufe baki ganin ceinture (belt) d'inshi ne ta cakumo, hannu biyu tasa ta rufe fuskarta saboda kunya, shi kanshi dariya ce ta kubce masa hakan yasa ya juya ya fita, zaune tayi tana mamakin abinda tayi kuma ba tare da tasan tayi ba, shi kuma yana mamakin wasu b'oyayyin halayen Khairat da sai yanzu ne suke fitowa, dan kunyar data nuna taji ma ya masa dad'i sosai, misalin *10:00* Khairat tasa aka tattara kowa dake ma'aikatar suka shiga meeting, saida ta saka hijab d'inta sannan ta fita, anan ta fad'a musu zangon shekara yazo qarshe, dan haka ana buk'atar kowa ya fito da nasa sabon sanfirin domin aga bajintar kowa, sallamarsu tayi sai kuma manager da accountant da suka tsaya suka yi wani lissafi sannan suka tashi suma, tana fitowa jakarta kawai ta d'auko ta kama hanya zata fita, dan dama aikinta ba jimawa take ba.

Tunda ta fito kowa ke kallonta kamar wacce tayi wani mugun abu, ranta ne ya bace harta tsaya ta fara kallon kowa zata fara zazzaga masifa, sai kuma taga kowa yasha jinin jikinshi saboda ganin zata koma musu Khairat d'in ta asali, lokacin ne ta fahimci dalilin kallon nata, hakan yasa ta saki murmushi a fuskarta sannan ta fara takawa cikin rangwad'a ta tsaya bayan teburin Umar Faruk, duk da yaji alamar akwai mutum a bayanshi, duk da turarenta ya bayyana mishi ita amma baisa ya juyo ya kalleta, cike da tsantsar shagwab'a da bubbuga qafafu Khairat tace "shine ma zaka wani kyaleni ko ka juyo ka kalleni, ni wallahi zanyi hushi da kai."

Mamaki ne yasa ya juyo dan ganin dawa take, qara waro ido yayi tare da dage giranshi sama, kasa magana yayi saboda kowa na wajen kallonsu suke, sake shagwab'ewa tayi ta fara kukan sakuwa tace "uhum uhum uhum, wallahi Allah saina fad'awa Mama mana."

Kunyar data fara basa ne yasa ya mik'e tsaye yana kallonta cikin mamaki yace "ya dai, me yake damunki ne?"

"Gida zan tafi wajen Mamie, shine nazo kamin sumbatata ta ban kwana."

"Sumba kuma?" ya fad'a da k'arfi har mutanen suka sake sakar musu ido.

Lab'e baki ta sake yi tana "uhum uhum uhum uhum uhum uhum uhum."

Zaiyi magana kuma saiya d'an kalli mutanen da wutsiyar ido, ganin yanda hankalin kowa ke kansu yasa ya zura hannu ya janyota yana fad'in "oh mon bΓ©bΓ©, meya faru ne waya tab'a min ke?" ya fad'a yana shafar fuskarta.

Kamar zata janye hannunta kuma saita goge ido kamar mai hawayen gaske tana magana cikin shagwab'a tace "toni sumbata nake jira."

Wasu yawu ya had'iye danshi dai ba zai iya ba kome za tayi, kallonshi tayi ta fahimceshi dan haka ta nuna mutanen tana fad'in "wai kunyarsu kake jine? su d'in fa duka yaranka ne, tunda shugabarsu ma a qarqashinka take."

Saida ta d'an d'aga qafafunta ta kai bakinta daidai kunnenshi saboda ya fita tsayi sannan tace "ko ba wannan ne burinka ba? ace Umar Faruk mijin Hajia Khairat."

Sai kuma ta sake tsayawa yanda take tana murmushi tana kallon fuskarshi, ganin zai b'ata mata lokaci yasa ta kalli idonshi tace "wato zaka iya yiwa waccen figaggiyar matar taka sumba a waya, amma ni gani gaka ma ba zaka iya ba ko? to bara ka gani."

Sake d'aga qafafunta tayi ta daidaita tsawonsu tare da d'ora bakinta akan nashi bakin, ji kake muahhhhh😘 ta sumbaceshi, daga cikin wasu mutanen dake wajen ne sai kuwa suka saka tapi tare da shewa, yayin da Khairat kunyar abinda tayi ta lullub'eta, ficewa tayi ba tare da sun had'a ido ba ta bar wajen, ta jima zaune kafin ta tayar da mota ta tafi, tun tana tunanin dalilin da yasa tayi haka, har dai ta fara sakin murmushi da ba tasan dalilin yinshi ba, wannan ce sumbatarta ta farko, dan ko Raj dake ba musulmi ba bata tab'a yarda ya sumbaceta a baki ba, haka ma su Musa da suka keta mata haddi babu wanda ya damu da bakinta, da wani irin sabon farin ciki daya lullub'e zuciyarta ta isa *marina market score*, siyayya tayi mai yawan gaske kayan abinci da kuma kayan mak'ulashe saboda kanta, a bayan mota aka saka mata daga nan kuma gida ta nufa wajen Mamie.

***************

Tunda ta d'ora labb'anta akan nashi ya sandare tare da lumshe ido, ba komai ya tafi dashi ba kamar taushin labb'anta, ga kuma wani sabon k'amshin turare daya baibaye hancinshi, harta fita bai iya zaunawa ba har saida Ishaq ya janyo rigarshi yana dariya yace "sabon shiga kenan, kai yanzu bizou (kiss) ne ya sukurkutar da kai haka? tofa wannan inaga har yanzu ba wani labari tsakaninku ko? dan inaga ranar da kaje bakin boda, tofa sai dai mutanadi makarar da zamu saka gawarka."

Duk da ya zauna amma hankalinshi baya jikinshi, sake tab'ashi Ishaq yayi yace "kai, ko dai ka zaucene, sumbata ce fa."

A hankali ba tare daya kalleshi ba yace "ya danganta dawa ya sumbaceka, wannan ta dabance Ishaq, ba zaka gane ba."

"Wow." ya fad'a tare da dogara hannayenshi akan teburin dake gabanshi ya tusa hannayenshi a cikin sumar kanshi, bakinshi har kunne yayin da hakoranshi suka kasa b'oyuwa, wani irin sanyi ne yake ji yana shigarshi a hankali, zuciyarshi kuma na qara narkuwa akan wani abu da take so sosai, sai dai bai yarda son Khairat bane take.

_Zama kayi magana Umariri_πŸ˜‰

****************

Da sauri mai gadi ya bud'e mata k'ofar ta shiga, tun kafin ta fito kuma yaja ya tsaya gabanta yana fara gaisheta tun kafin ta fito, qafafu ta zuro kafin ta qarasa fitowa, "barka da zuwa Hajia, sannunki da zuwa uwargijiyata, 'yar Alhaji da Hajia, 'ya d'aya tilo kuma farin ciki da sanyin idaniyar gidan mai gidanmu, takawarki lafiya yar albarka jikar arzik'i, sannu da zuwa."

Hannu ta d'aga masa tana kallonshi tace "baka tab'a min irin wannan kirarin ba, halan da wani abu a qasa?"

Kai ya d'an sosa amma baice komai ba, "humm, nasan dama da wani abu, dan banza bata kai zomo kasuwa, ka jira na shiga ciki na fito."

Tana fad'a ta wuce shi kuma ya sake rakata da wasu kirarin, saida yaga ta shige yaja baki yayi shiru yana mamaki Hajia Khairat da hijabi, lallai mijin nan mai sa'a ne, kuma da alama zai juyata yanda yake so.

Mammie ce zaune a falo ita kad'ai tana kallo, da gudu ta qarasa ta rumgumeta tana fad'in "Mammie na."

Rumgumeta tayi itama tana fad'in "lah, Khairat d'ina, ashe kece?"

D'ago kanta tayi tana gyara zama tace "nice Mammie, kema baki ganeni ba saboda nasa hijab?"

"Ah haba, ni na isa na kasa gane 'yar gudaliyata, kawai dai gani nayi kin qara min kyau da haske."

Kumatunta ta kama taja suna dariya tace "kin ganki tsohuwar nan, wato harda haske na qara, bayan duhun da nayi saboda bala'in zafi da cizon sauro."

Dariya Mammie tayi cike da zolaya tace "ba wani nan, kinje kin manta dani kina kwasar amarcinki, yanzu zaki ce wai zafi da sauro , kedai sai dai in kin samo min wani d'an gudaliya ne kawai."

Fashewa tayi da kukan shagwab'a tana fad'in "lah Mammie, d'an gudaliya fa, tun yanzu? wallahi ba dani ba, Mammie yana da mata fa."

"Eh na sani ai, amma ina ruwanki da matarshi? ke daban ita daban."

"Humm, Mammie baki sani ba fa, wallahi ni ba sona yake ba ita kawai yake so."

Hannu tasa ta rufe mata baki tace "bana so, karna sake jin haka daga bakinki, shiya tab'a fad'a miki baya sonki?"

"To Mammie saima ya fad'a, jiya ma fa cemin yayi ba zai tab'a had...."

Mammie ta rufe mata baki, kai ta girgiza tace "Khairat, kefa yanzu ba yarinya bace, kamata yayi ace kina rik'e sirrinki, musamman irin wannan sirrin mai tsada, ki sani duk abinda ya faru tsakaninki da mijinki to bai hallata ki fad'eshi koda ga mahaifiyarki bace bare kuma waninta, dan haka bana so na sake ji kinji yar albarka."

Hannayenta ta matse sosai tace "naji Mammie ba zai sake ba, kinga yanzu nima na fara sauyawa, ina so na zama 'yar aljanna."

Muryar Mamie ce ta katsesu da cewa "nayi hushi dake, tun d'azu nake jiyo muryarki amma kin kasa zuwa inda nake."

Yanda take maganar da shagwab'a ne yasa Khairat yin dariya tace "kiyi hak'uri Mamie, ina nan tare da wannan tsohuwar k'awar tawa."

Hannaye Mamie ta bud'e alamar Khairat ta taho, abinda Khairat d'in ba tayi tunani bane hakan yasa da mamaki ta tashi ta tafi, tana zuwa Mamie ta rumgumeta sosai a jikinta tana fad'in "nayi kewarki sosai 'yata."

"Nima haka Mamie, ina Papa?" ta fad'a tare da tashi daga jikinta.

Hannunta ta kamo tace "Papanki ya tashi *Germany* amma yace ba zai jima ba."

"Ta'bb, yanzu shine har Papa yayi tafiya ban sani ba? lallai gidan nan kun daina sona."

Mamie data qura mata idone tace "Khairat, wannan sabuwar shigar fa?"

Saida ta cire hijab d'in tace "wallahi Mamie mahaifiyar Faruk ce tace na dinga rufe jikina, matar tana da kirki gaskiya ga yiwa mutum addu'a a kullum."

Duk da Mamie ta gano kuskurenta anan take amma bata nuna ba, murmushi tayi tace "Alhamdulillah, ashe 'yata ta kusa zama salihar mace itama."

"Eh Mamie, kuma ma yanzu har karatu na fara, Faruk ke koyar dani, wallahi Mammie baki ji dad'in dake akwai ba idan kana karatu."

"Alhamdulillah, ashe yaron ya kusa canza min yarinta ta yanda ba zan ganeta ba nan gaba? to Allah ya mishi albarka, ke kuma Allah ya baki sa'a ya taimakeki a karatunki."

"Ameen Mamiena." ta fad'a tana sake rumgumeta.

Mamie ce tace "to amma daga ina haka? kina ganin ba kiyi saurin fara fita ba kuwa?"

"Mamie daga wajen aiki nake fa, kuma shima na baroshi acan."

"Amma kin fad'a masa?" cewar Mammie.

"Eh, nace masa zanzo gida."

"To ya mutanen gidan, ba wata matsala dai ko? inji Mamie.

"Eh to, bana shiga sabgar kowa, amma akwai kishiyar mamanshi tana da zakewa, amma ba komai zan gyara mata zama."

"A'a."

"A'a."

Mammie da Mamie suka had'a baki a tare ,Mamie ce ta d'ora da "haba yarinyar kirki, 'yar aljanna, aiba girmanki bane wannan, ki rabu da ita kawai, kinji?"

"Shikenan." tayi maganar tana gyara zama.

Su kuma kallon juna sukayi saboda mamakin canzawar Khairat, magana d'aya tak Khairat tace to ko shikenan, tab', dole ma mu nemi yaron nan mu qara gode masa, saboda wannan namijin k'ok'ari da yayi, a kwana uku rak ya gyara musu 'yarsu cewar Mamie.

Saude da Biba da kuma Baraka masu aikinsu ne suka fito suka gaisheta, ba yabo ba fallasa ta amsa suka koma ciki ana mamakin Hajia Khairat.

Mamie ce ta kira Papa ta bashi Khairat d'in suka gaisa, anan kuma yake fad'a mata lallai lallai ta shirya tare da mijinta zasu zo Germany suma nan da kwana biyar tare dasu Mammie da Mamie, dad'i taji sosai saboda zata keta hazo, anan ta wuni gida sam tama manta da wani gidan aurenta, ji take kamar ta tsaya a inda take ba tare data koma waccen kurkukun ba.

******************

Yamma sosai Mammie ta iza qeyarta zuwa gidanta, haka ta tafi ba dan rai naso ba, tana zuwa ana kiran sallah dan haka koda ta shiga gidan wasu na alwala wasu sun tafi masallaci, sai dai ganin moton Umar Faruk ya tabbatar mata ya dawo, tana shiga ta tub'e ta shiga wanka sai dai bata jima ba ta fito saboda yanzu tana son yin sallah akan lokaci, cikin gaggawa ta shirya amma saboda qananan kaya ne saita dora doguwar riga a sama sannan ta saka hijab, harta kammala sallah bai shigo ba har qaramar kwalliya tayi sannan ta d'auki hula (hana sallah) ta zatsa akai, wata k'atuwar chocolat ta d'auka ta d'auka ta fara sha ga kuma k'atuwar loli pop d'inta a hannu, abin sauraronta ta dasa a kunne ta fara biyar waqar Zaho mai taken *Allo* tare da rausaya.

Da sallama tare da d'aga labulen ya shigo, baiyi mamaki ba saima birgeshi da tayi , bak'in dogon wando da farar riga mai hannuwa sai bak'ar hula itama, kamar ita ta rera waqar ga kuma yanda take tafiyar da kowace gab'a ta jikinta cikin qwarewa, shiga yayi ya zauna dan sunyi ido takwas takwas dashi amma bata nuna ta damu ba, a cikin takon rawa ta bud'a jakarta ta d'auki makulli ta mik"o masa ya karb'a yana kallonta da mamaki, ta jima kafin tace "akwai kaya a mota a deb'osu."

Duk tana maganar ne tana girgiza rawarta, hararanta yayi da fad'in "waye zai d'auko?"

Nunashi tayi da hannu tana ci gaba da abinda take , cilla mkullin yayi a saman gado harya kusan bugeta, cire abin sauraron tayi tana kallonshi tace "ni kake so na kwaso to?"

"Eh, saboda ke kika siyo."

D'aga kafad'u tayi alamar ba matsala, fita tayi daga d'akin ta zura takalmi harta kai k'ofar fita daga kewayen yayi saurin fitowa yace "ke."

Duk da taji amma bata saurareshi ba, wucewa tayi ta kuma yi sa'ar ganin Aliyu da Usman sun shigo, da sauri ta mik'a musu makullin tana fad'in "yawwa karb'i nan, akwai kaya a cikin mota ku fito dasu saiku shiga dasu madafar gidan nan."

Suna karb'a suka fita ita kuma kawai tasa kai ta shiga d'akin Mama dan ganin jikinta, duk da saurin da yake ya rik'ota tuni ta shige, dafe kai yayi yace "duk kaine ka jawo Umar Faruk, da kayi abinda tace daba haka ba."

Mama na zaune duka yaranta suka ga ta shigo, gaisheta sukayi qasa qasa kamar yanda ba wanda ta amsa ma, zaune tayi kad'an tace "Mama ya jikinki?"

"Da sauk'i sosai 'yata, ya kike?"

"To yayi kyau, kinsha magani?"

"Eh nasha." Mama ta fad'a tunda taga ba kowace magana take amsawa ba.

Tashi kawai tayi ta kalli Ruk'ayya dake koyar da k'annanta karatu tace "akwai kaya za'a shigo dasu."

"Mama saida safe, Allah qara lafiya."

"Ameen 'yata saida safe."

Tan a fitowa suka ci karo da Umar Faruk dake sauraronsu, wucewa kawai tayi a lokacin kuma su Aliyu suka fara shigowa da kayan, saida suka gama duka sannan Aliyu yayi sallama ya bawa Umar Faruk makullin, mutanen gidan ne suka fito suna tambayar ina za'a da kayan, Zeinab aka aika ta tambayo tana fitowa ta fad'a musu wai nasu ne, kowa dai yayi farin ciki amma banda Baba.

Umar Faruk yasa aka kira masa, bayan ya fito yace dashi da ita su sameshi d'akinshi, ba b'ata lokaci suka hallara bayan yasa tasa dogon hijab, zaune suke gaban Baba ya fara da " 'yata, munga abin arzik'i da kika mana kuma mun gode, amma sai nake ganin da kinbar bawa kanki wahala haka, tunda cikin ikon Allah muna ci muna sha kuma muna rayuwa cikin rufin asiri, dan haka ba buk'atar ki dinga bawa kanki wahala."

Kallon Baba tayi ido tsaye tace "Baba, karka wahalar da kanka, in har nima d'aya ce daga cikin 'ya'yanka, to inada damar da zan taimaka maka, bawai inayi bane saboda wani abu, haka kawai nake ganin ya dace na taimakawa duk wanda yake tare dani, a shekarunka mune ya kamata ace muna ciyar da kai da d'aukar duk wata d'awainiyarka, dan haka

Please Login or Register in order to submit comment