Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suke so, Khairat ce ta zaba Umar Faruk kuma yace abinda take so shi zaici, cikin k'ank'anin lokaci aka wadata gabansu da kayan tab'awa, suna ci suna hira kamar masoyan tun a ranar farko, suna daf da gamawa ma'aikacin ya dawo ya basu bill d'insu, ganin kudin da zasu biya yasa Khairat kallon Umar Faruk, shima kallonta yayi saita bawa ma'aikacin takardar ta nuna Umar Faruk tace "kaba baby zai biya." tana fad'a ta bud'a post d'inta ta d'auko kud'i ko dubawa ba tayi ba cikin dubara ba tare da kowa ya gani ba.

Nufa wajen Umar Faruk ma'aikacin yayi amma sai Khairat ta rigashi isa ta sunkuya kamar ta mishi sumba ta kamo hannunshi ta dank'a masa kud'in kafin ta dago ta kalli ma'aikacin cikin harshen frensh tace "dan Allah ina zan samu douche?"

Kwatanta mata yayi ta nufi wajen Umar Faruk kuma ya kalli a hannunshi yaga kud'i, karb'ar takardar bill d'in yayi sai yaga kud'in da aka rubuta ko kasheshi za ayi ba zai iya biyansu ba, sai lokacin ya fahimci abinda Khairat tayi, murmushi kawai yayi yayi kamar ya fito da kud'in daga aljihunshi ya bawa ma'aikacin, godiya yayi ya wuce Umar Faruk kuma ya maida kallonshi ta inda habibiyar zata fito.

Ai kuwa sai gata dama ba abinda taje tayi kawai dan tabar wurin ne, tana zuwa ya mik'e itama post d'inta ta d'auka sannan suka wuce, suna fita waje ya kalleta yace "me yasa zaki biya? bayan nine ya dace na biya."

"Ni kuma? biyan me?"

Kallonta yayi yaga raina masa wayo kawai za tayi dan haka yace "daga yau bana so ki sake shiga aikin daba naki ba, wannan ba huruminki bane, yin hakan kamar kina nuna ba zan iya d'aukar nauyinki bane."

Saida suka hau mashin d'in tace "duk da bana da ilimin addini, amma nasan abune mai kyau mata ta taimakawa mijinta, nice nace muzo nan badan kana so ba, taya zan bari kayi asarar mak'odan kud'ad'e har haka."

Jin yayi shiru yasa ta bishi da wata kissar ta hanyar rumgumeshi ta baya tana sauke numfashi tace "kayi hak'uri to idan ranka ya b'ace, zan kiyaye anan gaba, amma ban maka alk'awari ba."

Hannu ya zura ya shafi fuskarta yace "Allah ya miki albarka."

Da sauri ta d'aga daga jikinshi cikin daga murya kamar ta manta inda suke tace "wayyo Allah, yau mijina ne yake saka min albarka, gaskiya na gode baby, dan Allah kayi min alk'awarin kullum zaka dinga saka min albarka, kaji?"

"Nayi alk'awari." ya fad'a yana rik'e hannunta dake kan cinyarshi.

A haka suka kai gida cikin nishad'i da farin ciki, saida suka shiga wanka suka fito kafin ya saka doguwar riga ya shiga yiwa iyayensu saida safe, d'akin Zuby ne ya shiga qarshe ya tarar da ita kwance tana chat a wayarta, ko kallonshi ba tayi ba saboda ta nuna masa ranta a b'ace yake, shi kuma domin ya nuna mata yana farin ciki sai yace "ni zanje na kwanta, ina fatan dai ba wani abu ko?"

"Um um." ta fad'a a cikin mak'oshi.

"Ok, saida safe to." yana fad'a ya wuce ya barta, ta d'auka zai rarrasheta ne koya tsaya tab'a jikinta, hakan kuma ya mata zafi sosai dan haka ma ta fara matso wasu hawaye masu zafi.

Shi kam yana komawa can Khairat tasa ya manta da wata Zuby soyayya da salo ta dinga kasheshi dasu, har saida ya goge hawayen dake idonshi ya k'amk'ameta sosai yace "dan Allah Khairat ki bani dama na shiga rayuwarki shiga ta har abada, Khairat ki amince ki bani kanki mana ta hakane kad'ai zamu sake zama d'aya, dan Allah Khairat ki taimakeni , ina kusa da kaiwa k'adamin da ba zan iya rik'e kaina ba, ki taimaka ki bani kanki kafin kwananki ya qare daga gobe."

Shiru tayi a qirjinshi dan sam ta manta da wani rabon kwana, basarwa tayi ta fara shafar kanshi tana fad'in "kayi hak'uri baby zan baka, d'an lokaci kad'an zaka qaramin."

"Yana iya to , dole nayi hak'uri, na riga dana saba da wannan jikin naki Khairat da salonki , zaiyi yuwa na iya *rayuwa ba tare dake ba*." duk yayi maganar nan yana shafar qirjinta kamar zai ciresu.

Ita kam wani murmushin gefen labb'a ta masa dan kuwa hak'arta ta cinma ruwa, kuma ko iya haka aka tsaya, to tayi nasara akan Umar Faruk.

_Me kuka ce ne my fan's.???_
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

*Jan hankali*

_Akwai wani kuskure da nayi amma ba kowa ya fahimta ba, sati d'aya Umar Faruk zai yiwa Zuby itama, amma na manta nake cewa kwana biyu, tun farkon labarin dama Umar Faruk ba zasuyi tafiyar nan da Khairat ba, kawai dai na kawo maganar tafiyar ne da Umar Faruk saboda ita Khairat za taje, ina fatan zaku fahimceni._

*Tunatarwa*

_Akwai wasu da naji suna cewa Umar Faruk baya adalci a tsakanin Khairat da Zubeida, dalilin kuwa shine ya amince zai tafi tare da Khairat da kuma fad'an da yake yiwa Zuby, ni kuma a sanina sau biyu yawa Zuby fad'a, lokacin da tazo yana magana ta katseshi wanda kuma banga hakan a matsayin laifi ba, sai kuma daya zo mata da maganar tafiya shima ya gargad'eta ne kawai, wasu na ganin Zuby bata da anfani a labarin dan haka inda ban sakata a ciki ba._

*To kuji da kyau dalilina nayin wannan rubutun.*

*1* _Ba budurci bane mace kawai._

Khairat ta rasa budurci a lokacin da namiji hud'u suka mata fyad'e, amma hakan baisa ta cire rai da rayuwar farin ciki ba, ta alk'awartawa kanta ba zata saka damuwa ba, kuma tayi nasarar hakan, bata nuna cewar ita yanzu ta zama wata daban ba kamar yanda al'uma ke kallonta.

Sanin kanku ne idan akace anyiwa mace fyad'e har rasa mijin aure take, badan komai ba sai dan ana ganin kamar ta rasa kima da darajar ya mace, Eh, tabbas ta rasa budurci, amma bata rasa kima ba, domin kuwa har yanzu tana nan a sunan mace kuma mai daraja, budurci abun tattaline garemu domin mu kaishi inda ya dace, amma ba'a fad'a ba ko a *_Littafi mai tsarki_* cewar idan suka rasashi a zubar dasu ba, wannan shine manufata kuma tunanina , bai zama lallai ko dole ba maganata ta shigi kowa, amma nidai abinda na yarda dashi kawai shineπŸ§˜β€β™€ _Dan mace ta rasa budurci bata rasa kima bane da zaisa a kalleta qasqantaciya_


*2* _Ba budurcinki zaisa miji ya soki ba_

Biyayya, Hak'uri, Kissa, Salo, sune matakalar farko da zata janyo miki martaba da soyayyar mijinki, *Na yarda* duk macen da bata kawo budurci gidan mijinta kimarta tana raguwa a wajenshi, amma idan kika rik'e abubuwan dana fad'a a baya, to tabbas zaki sha mamaki, qaramin misali ga wanda suke cewa Zuby bata da matsuguni a cikin labarin.

Tana tink'ahon ita budurwa ce Khairat kuma akasin haka, amma meya faru? Khairat ce a zuciyar Umar Faruk, meya kawo haka? salo da kissa ta shigo dasu a al'amuranta, duk da dai da kanshi ya amshi budurcin Zuby amma yanzu ba zai iya tuna meye amya faru a wannan ranar ba, kunsan me yasa? saboda ba cikin nutsuwa hakan ta faru ba yana gidan sarakuwarshi ne , bai kuma shirya hakan ba, kawai taja hankalinsa ne, kuma yana biyan buk'atarshi ya tafi ya barta, baiga asalin miye ma budurcin ba bare gobe ya fad'a, to tambayarga da zan muku, *wa zai fad'a min me Umar Faruk zai iya fad'a a game da budurcin Zuby???*, masu ganin jan ran da Khairat takewa Umar Faruk ya isa haka a'a, ina so Khairat ta gama kama zuciyarshi da salonta sannan ya kai maqura wajen sha'awarta ta yanda zai kusanceta cike da nishad'i da son isar da sak'onshi a kanta yanda ya kamata, a ranar da zai haukace yaji ita kad'ai yake buk'ata kuma zai iya k'watar hakk'inshi koda ta k'arfi ne, a ranar ko baiga budurcinta ba ba zai d'aga hankalinshi ba, saboda ya samu nutsuwar da yake buk'atar samu a matsayinshi na namiji, dan haka 'yan uwa ku fahimci me nake son isarwa a labarin *Jihadi*.


*3* _Kissa ita ke tafiya da kishiya dama miji kanshi._


Duk da Khairat najin kishin Umar Faruk amma hakan baisa ta fito da kishinta a fili ba, ko Umar Faruk d'in bata bari ya fahimci tana kishinsa ba, me yasa haka? a ganinta bai dace da ita ba kuma ba girmanta bane, da kissa take tafiyar dashi da ita kanta Zubyn.

Wannan yawan tab'awa da sumbatarshi da kuka ga ina yawan sakawa yana da anfani, miye anfanin? anfanin shine, hakan zaisa ko baya tare da ita yaji kamar tana kusanshi, k'amshin jikinta zai dinga tsayawa a jikinshi ta yanda zai dinga bibiyarshi, ko bacci yake kuma zaiji tamkar ta sauke masa sumba mai kyau a kumatunshi, wannan shine dalilina na saka haka.

Saboda rashin iya kissar zama da miji da kishiya , shi yasa Zuby take kasa b'oye abinda ke ranta, a qarshe kuma hakan zai iya haifar mata da matsala, ita a ganinta tunda ya karb'i budurcinta da hannunshi kuma tana da malaman tsibbu, to ta gama dashi alhalin kuma ba haka bane.


*4* _iyaye sune tushen tarbiyar yaronsu._


Tun farko laifin na iyayen Khairat ne, ai a littafin *Akhdari* an fad'a cewar _"babu biyayya ga ababen hallita wajen sab'awa mahalicci."_

Na'ima (mahaifiyar Khairat) tana da damar bijirewa iyayenta saboda ta samu labarin munannen halin Usman, amma saita musu biyayya saboda gudun b'acin ransu, sanadiyar haka ta samu mijin dako addu'ar saduwa bayayi idan zai kwanta da ita, saboda kusan kullum a maye yake.

Sun haifi Khairat an sakata islamiyya, amma saboda an daketa mahaifinta ya hanata zuwa gaba d'aya, mahaifiyarta kuma ta fara koyar da ita, itama kuma saboda ta daketa sai yace ta daina shiga sabgar 'yarsa , me tayi a matsayinta na uwa? saita fita harkar yarinyar da bata san meke faruwa ba.

Khairat ta shiga damuwa sosai ta yanda ta zab'i zaman d'aki akan waje, bata sakewa bata fira da kowa daga tunani sai jiyo hayaniyar iyayenta a lokacin da mahaifinta ke saduwa da mamanta ko kuma yana dukanta ko kuma suna fad'a.

Yarinya ce dole hakan zai tab'ata sosai, hakan ya janyo mata ciwo a qarshe aka fitar da ita wajen kakarta, itama kakar me tayi??? shagwab'a tayi ta hanyar samar mata da duk abinda take so.

Duk da ta dawo kuma ta girma amma Mamie bata shiga sabgar 'yar tata saboda halinta, hakan yasa yarinyar ta tashi tsagera kuma marar kirki, amma yanzu nasan kun fahimci ainihin hallayar Khairat, *waccen hallayar dama aransu tayi ta yab'a a jiki* yanzu kuma data samu nagartaccen miji da 'yan uwa, saita fara dawowa asalin Khairat d'inta.

_Ina fatan zaku fahimci sak'ona, kuma ku nutsu kuga miye zai faru a gaba, kuji ku qara ji *Ni Sameera Harouna* ban tab'a tsayar da labari ba saboda maganganun makaranta, kuma ban tab'a canza akalar labari ba saboda makaranta._

~FATAN ALKHAIRI~ πŸ€πŸ‘


_Bismmilahir-rahman-rahim_


3⃣5⃣

*ZAIZO MUKU INSHA ALLAHU.*
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

_Shi yasa ban tab'a tunanin tsayar da rubutu ba saboda maganar wasu, domin kuwa akwai dubbanin masoya da suke biye da kai, muna mugun tare daku insha Allah._

😘😘😘😘😘😘😘


_Bismmilahir-rahman-rahim_


*My Amnoor, wannan kyautarki ce* Ina sonkiπŸ’•

_My dotana *Khadija* Allah ya saka miki da alkairi, ina alfahari dake kuma ina qaunarki._


3⃣5⃣


Dare yayi sosai Khairat ta farka da matsananciyar qara cike da tsoro, a kunnen Umar Faruk qara ta ratsa hakan yasa suka mik'e zaune a tare, da sauri ya janyota jikinshi yana fad'in "shiiiii, Khairat, ya isa haka, ya isa kinji, ki kwantar da hankalinki ba komai anan."

Kallonshi tayi ido a kafe tana ganinshi ta fad'a jikinshi ta fashe da kuka, kanta ya dinga shafawa yana fad'in "ya isa, ya isa kiyi shiru kinji."

Cikin kuka tace "sune, sune suke zuwa min a cikin bacci, Faruk ina jin tsoro, ina so na manta amma na kasa."

"Kiyi hak'uri Khairat, ba zasu sake zuwa miki ba insha Allah, kar kiji tsoro, ina tare dake, kuma ba zan tab'a bari wani ko wata ya sake cutar dake ba, kinji ko? ki nutsu muna tare."

A hankali ta d'ago kai ta kalleshi tace "kayi alk'awari."

Saida ya sumbaci labb'anta yana murmushi yace "nayi miki alk'awari."

Qara shigewa tayi jikinshi tana qara qamqameshi, ajiyar zuciya kawai take saukewa tare da shashekar kuka, bayanta yake ci gaba da shafawa har bacci ya sake d'aukarta, gyara zamansa yayi tana rumgume a jikinshi shima har baccin ya fara d'ibarsa, amma kiran sallah daya shiga kunnuwansa yasa ya bud'a ido, kallon fuskar Khairat yayi ganin yanda ta turo leb'en qasa cike da shagwab'a, a hankali ya daddab'a bayanta kafin ta bud'a ido.

"A tashi, lokacin sallah yayi." ya fad'a tare da shafa kumatunta.

Tashi tayi zaune shi kuma ya fita yayi alwala, kai tsaye d'akin Zuby ya nufa, saida ya bubbuga kafin ta bud'e k'ofar, tana bud'ewa ya shiga d'akin yana kallonta, itama kallonshi take kafin yace mata "kin tashi ashe?"

"Eh, na tashi."

"Ok, ni na tafi masallaci."

Binshi kawai tayi da kallo dan ita haushi kawai yake bata, gaba d'aya sallah sukayi Umar Faruk kuma koda ya dawo d'akin Zuby ya sake komawa, kwance ya sameta akan gado hakan yasa ya haura kan gadon ya rumgumota jikinshi, duk da dai ba komai ne keda dad'in shak'ar k'amshi a jikinta ba, haka ya matseta har yana sauke numfashi kafin yace "ya kika tashi?"

"Ina kwana." ta fad'a tana turo baki gaba.

"Lafiya k'alau." ya fad'a yana zura hannunshi a cikin rigarta.

Rik'e hannunshi tayi tace "dan Allah ka bari, bana so."

"Saboda me?" ya fad'a yana kallon fuskarta.

"Kawai bana jin dad'i ne."

Tashi yayi zaune tare da d'agota itama tayi zaune yana kallonta yace " hushi kike dani Zubeida?"

Saida ta qara had'e fuska tace "akan me zanyi hushi da kai? kawai dai bana son abinda kake min."

"To me yasa ba kya so?"

"Saboda bana son kana tab'a jikina kamar yanda kake tab'a waccen karuwar."

Sosai kalmar karuwar nan ta shiga zuciyarshi ta fasata, bud'e idonshi yayi daga lumshewar daya musu ya kalleta yace "k'yamata kike kenan?"

Wani kallon bakin cikine ta masa dan ita ba haka taso ba, kau da kanta tayi tace "ashe ma kana kusantarta, aina d'auka za kace min wallahi babu abinda ya shiga tsakaninmu ne, ashe dai ba haka bane."

"Amsar tambayata?" ya fad'a a dake ba alamar wasa.

"A gaskiya in dai har." kuma sai tayi shiru.

"In dai har me?"

"In dai har kana tab'a jikinta itama kamar yanda kake tab'a nawa, to gaskiya ina qyaqyaminka, da ba zan yarda kaje ka d'auko wata cutar da banji ba ban gani ba ka qaqaba min."

Sam bai tab'a tunanin haka Zuby take ba, a yanda ya santa da ilimi na addini ya d'auka zata iya fahimtar komai cikin sauk'i, amma saiga akasin haka, ya zaiyi da ita ita haka nata salon kishin yake, janyota yayi jikinshi yana murmushi yace "ban tab'a tunanin haka ba, aina d'auka ko kina da tabbacin Umar Faruk d'inki yana da wata cutar da zaki iya d'aukarta a jikinshi, ina tunanin zaki amince ki zauna dani saboda soyayyar dake tsakaninmu."

"Zan iya, idan har cutar Allah ne ya jarabeka da ita, ba wacce kai ka siyo da kud'inka ba."

"Naji to, yanzu kiyi hak'uri ki yafe min laifina."

D'ago kanta tayi dan dama jinta take a takure tace " ba zan iya ba, saboda har yanzu kana tare da ita, ga kuma sabon rainin wayon daka zo min dashi, waina baka kwana na kuje qasar waje, humm."

Taushe zuciyarshi yayi yace "Zubeida, na d'auka zaki iya ara mana kwana uku a cikin kwanakinki, idan ki kayi duba da rayuwa yau gareka gobe ga d'an uwanka , wata rana kema buk'atar hakan zata iya taso miki, kuma ta miki alfarma."

"Tabbb', Allah ya kiyaye wallahi, kenan gadin gidan zan zauna yi muku? bafa zai yiwu ba wallahi, sai dai kuma in amanata za aci kawai."

Dariyar baki da hankali ya mata yace "to idan anci amanar taki saime? aiba yau na fara cin amana ba, ko kin manta ne? to idan kin manta bari na tuna miki, a kanki aka fara cin amana, domin kuwa a ranar dana kusanceki aiba kwananki bane, kwanan waccen baiwar Allah ne, amma kinsan meya faru data fahimci naci amanarta? cikin gargadi tace min, na yafe maka a yanzu, amma idan ka sake ba zan yafe ba, ke yanzu wannan matar ce ba zaki iya bawa aron kwanaki biyu zuwa uku ba?"

"To ina ruwana? itama tayi ne dan neman gidin zama a wajenka , kuma lokacin da akayi ai bana gidan bare tamin kallon banza."

Kallon mamaki ya mata sosai kafin yace "kenan ke ba kya neman gindin zama a wajena? ba kya fatan qara samun matsayi fiye da wanda kike da? abinda kika fad'a yanzu sai yasa naji cewar ba zaki damu da darajar mijinki ba, kinsan me yasa nace haka?"

"Alk'awari na d'aukarwa Khairat cewar zamu tafi tare kuma tun kafin kizo gidan nan, nasan kinsan mahimmanci cika alk'awari da kuma alamar mai karyashi, idan na sab'a mata ban kyauta ba, kuma a matsayinta na matata ba zata iya kallona da mutunci ba, zata iya kallon mijinta mutum mara cika alk'awari kuma maqaryaci sannan munafiki, yanzu Zubeida a matsayinki na masoyiyata duk zaki so hakan ta faru, kuma ma ki rasa wacce zaki bari tawa mijinki wannan kallon sai abokiyar zamanki, hak'ik'a ina so na cika alk'awarin dana d'auka saboda tun ina qaramin yaro Baba yake fad'a mana, Babban mutum ba yana nufin girman jiki bane ko matsayi , ainihin abinda yake nufin shine, magana d'aya kuma abisa gaskiya, cika alk'awarin daka d'auka, hakan zai qara martabar addininka."

Jikinta ne yayi sanyi yayin da wannan hadithn ya dinga mata yawo a qwaqwalwa, *alamomin munafiki guda uku ne, idan zaiyi magana sai yayi qarya, idan yayi alk'awari ya sab'a, idan aka amince mishi yayi ha'inci.*

"A gaskiya badan tunawa da hadisin nan ba, da ba zan yarda ba, na amince ku tafi, amma da sharad'i."

"Ina jinki." ya fad'a ba tare da nuna ya wani ji dad'in abinda tayi ba.

"Idan kuka dawo zaka cika min sati na nima kamar kowace mace."

Janyota yayi jikinshi yana sumbatarta yana fad'in "saima kin fad'a, kinsan yanda nayi kewarki kuwa?"

Raba jikinta tayi da nashi tana nok'ewa, cike da karsashi yace "nifa bana son wannan kunyar, zaifi miki ki cireta dan ranar da kika shigo hannuna fa ba sauk'i."

Wata kunyarce ya sake bata hakan yasa ta juya mishi baya ta kwanta tana sauke numfashi, sauka yayi daga kan gadon ya koma wajen da take ya sunkuya yace "bani sumbata a kumatu, kuma harda ta jiya zaki min."

Bud'a idon tayi ta kalli qasunbarshi luf da ita, sake rufe ido tayi, haka yayi juyin duniya amma tak'i koda bud'a ido harya fita daga d'akin, yana fita ta juya ta kalleshi duk da ya fita, ajiyar zuciya ta sauke ta gyara kwanciyarta.


Yana shiga d'akin Khairat ya sameta zaune bakin gado tana waya, da mamaki yake kallonta yana tunanin dawa take magana a muqu muqun safiyar nan, duk da waya take saida ta mik'e tsaye ta rumgumeshi da hannun d'aya tare da bata kumatunta alamar ya sumbata, manna mata sumba yayi ta koma ta zauna inda ta tashi, tsaye yayi gefenta ya fara bin kowace kitsonta yana tab'awa, abinda ta fad'a a wayar ya tabbatar mishi da manager ne,

"Eh, idan angama had'awa kawai ka fitar mana da guda uku wanda nasu yafi na kowa, na farko za'a bashi kyautar mota da qara masa albashi , na biyu kuma za'a bashi sabon moto da qarin albashi, na uku kuma zamu bashi kayan abinci da kuma kud'i, hakan yayi ai?"

Jim tayi alamar tana sauraro kafin tace "yau kam ba zan fita ba, idan ka had'a komai kayi abinda ya dace, kawai dai kana kirana a waya dan insan meke faruwa."

Jim nayan dak'ik'u kafin tace "ok, saina jika."

Aje wayar tayi a gefenta tare da janyo Umar faruk da har yanzu yake wasa da gashinta ta zaunar dashi, sai data dafe kumatunshi ta sumbata kafin tace "ina kwana baby, ina ka shigene haka inata jiranka?"

Yana kallonta yace "na shiga wajen k'anwarki ne, kinyi kewata har haka?"

Duk da taji wani abu ya soketa amma basarwa tayi tace "sosai ma, nifa bana son kana nisa dani sosai, sai naga kamar zan rasaka ne."

Tana fad'a ta janyo kanshi ta kwantar a saman cinyarta ta fara shafar kansa har zuwa qasumbarsa tana fad'in "yau ba zan fita aiki ba, amma zanje na siyowa su Mamie kayan da zasu tafi dashi, kaga daga nan nima saina siyo namu, dan nasan yanzu a Germany akwai sanyi, dan haka ina buk'atar ka bani aron motarka."

Shiru yayi yana kallonta yayin da zuciyarshi ke antayo mishi sink'i sink'in tambayoyi _"wai me yasa Khairat da Zubeida suka kasance ba d'aya ba? bayan kuma dukansu mata ne, me yasa Khairat tafi bashi farin ciki? sab'anin Zuby da sukayi soyayya, me yasa Khairat take son kusanci dashi sosai? ba kamar Zuby ba da bata ma son yana tab'a jikinta a koda yaushe, me yasa Khairat ta iya komai kuma cikin salo tare da iya takonta? shin wayewa ce tafi Zubeida? ko kuma ilimin bokon data fita ne? ko kuma bud'ewar ido?"_

_Bara na fan's Jihadi su baka amsar_😜

Jin yayi shiru yasa ta shafi kumatunsa tace "baby." ta fad'a cikin shagwab'a.

Kallonta yayi yace "ina jinki."

"Au du baka ji me nace ba? me kake tunani?"

Tashi yayi daga cinyarta yace "naji, amma ai naji baki nemi izinin fitar ba."

Hararan wasa ta masa tana fad'in "wato kai mai iko ko? dama an fad'a namiji ko ka girmeshi in dai har aure ya shiga tsakaninku, to ka zama abin tausayi, dan iko kuke nunawa harna fitar hankali."

Da murmushi a fuskarsa yace "kuma hakan yayi ko?"

Gira ta d'aga sama tace "sosai ma, tunda hukuncine da yazo daga sama yankakke."

Kafin yayi magana ta gyara zama tana fuskantarshi tace "to naji zan nemi izinin."

Harda gyaran murya tayi kafin ta langab'e kai tayi kalar tausayi tace "baby, dama ina neman izininka ne ina so zan fita dan na siyowa su Mamie kayan tafiyarsu, idan da hali ina so ka bani izini tare da aron makullin motarka?"

Janyota yayi jikinshi yana fad'in "kaji neman izini mai kyau, gaskiya daga yanzu haka zaki dinga yi idan zaki fita."

D'aga kanta tayi ta kalleshi amma wani kallo daya watsa mata yasa a hankali ta zura harshenta cikin bakinshi ta lumshe ido tare da kama harshen tana tsotsa......... saida ta gama rikirkitashi sannan ta mik'e tana gyara jikinta tace "bara na d'auko kayan karatu."

Hannunta ya rik'e hakan yasa ta juyo ta kalleshi, wani marayan kallo daya mata irin kizo ki taimakeni d'in nan yasa tayi murmushi ta matso kusanshi, kasancewar yana zaune hakan yasa ta manna kanshi a qirjinta a tsakiyar mamanta tana shafa kanshi, a hankali ta d'ago dashi ta kalleshi idonshi sunyi ja tace,

"Malam, lokacin karatu fa yayi." tana fad'a ta wuce d'auko litattafanta, ba yanda ya iya haka suka fara karatunsu kamar kullum.


Ruk'ayya ta kawo musu abin kari kamar yanda ta saba kuma yace ta kira Zubeida, da sallama ta shigo fuskar nan a had'e ba annuri, dogon hijabi ne a jikinta yama rufe kayan dake jikinta, zaune tayi inda tasan nan zaice ta zauna, ganin sun gaisa da asuba yasa ba tayi magana ba, Umar Faruk ne ya kalleta yace "ba gaisuwa?"

"Amma ai mun gaisa d'azu."

Please Login or Register in order to submit comment