Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne ba zaka sake had'awa ba?"

Sakinta yayi yace "daga wannan ba zan sake ba."

Har zai wuce tace "baka ji mena fad'awa mahaifiyar matarka ba kenan? idan naso Faruk zaka zama nawa, idan nayi niyya zaka zama kamar raqumi da akala sai yanda nayi da kai, ka daina cika baki."

"Hummm, ba wani cika baki, ina da yarda da kaina ne shi yasa."

"Ka tabbata?"

"Qwarai ma kuwa."

"Ok, zamu gani, ni kuma zan ruguje wannan yarda da kai d'in."

"Kinga maganinki nan ki d'auka kisha yafi miki mahimmanci."

Juyawa tayi inda ya nuna mata ta kalla, maido kallonta tayi gareshi tace "ina ka samu magani na?"

"Matata ce ta bani."

Wani irin murd'awar kayan ciki taji lokaci d'aya kuma zuciyarta ta turnuk'o, a dake tace "wace matar taka? ba dai wannan d'iyar masifafiyar matar ba?"

Dariya ce ta kama Umar Faruk, karo na farko da Khairat taga dariyarshi, kafeshi tayi da ido harya tsagaita yace "wannan ta dabance , duk cikin matan nawa babu mai qaunata kamar ita, shi yasa nima na mata waje na musamman a zuciyata."

Duk da Khairat ta fahimci Umar faruk zaiyi dad'in zama kuma kamar yanda Ruk'ayya tace ta fad'a ne, amma kuma wani bala'i da taji ne a zuciyarta yasa ta rasa meke damunta, haka kawai taji bata so yana danganta kanshi da kowace mace a duniya, ba tare daya ankara ba Khairat ta kai masa duka a qirji harda fad'in "aisai kaje gaka gata ku cinye junanku."

Juyawa tayi zata haye gado tana fad'in "aikin banza kawai, ni gidanmu ma zan koma."

Da k'arfi taji ya janyota har saida ta fad'a qirjinshi, kafe juna sukayi da ido na d'an lokaci kafin yayi k'arfin halin cewa "meye wannan nake gani a idonki?"

Tsaki tayi mai k'arfi ta janye kanta daga jikinshi, fizgota yayi niyyar yin sai kuma,
"Assalama alaikum." sallamar Ruk'ayya ta katsesu.

"Shigo Ruk'ayya." cewar Umariri😁.

Shigowa tayi tana aje kwanukan Khairat tace "kina zuwa a lokacin da bai dace ba fa."

Ruk'ayya dai sakin ido tayi tana kallonta, har zata fita kuma tace "kina ji? ki dafa min."

A hankali Ruk'ayya ta tako ta zo ta d'auki indomien inda ta d'auka d'azu sannan ta fita tana guna guni, kwance tayi akan gado ta d'auki wayarta ta fara kiran lambar Mamie, muryarshi taji yace "ki daure ki dinga suturta jikinta koda gaban mace ne 'yar uwarki."

Hannu d'aya ta rumgume a qirji ta mike qafafunta tana girgizawa tana murmushi tace "to meye a ciki, naga jikina ne ba bana ka ba, kuma kace baka qaunarshi ba zaka tab'a had'ashi da jikinka ba, to miye na damuwa?"

Muryar Mamie ta daki kunnuwanta dan haka tace "Mamie ya kike, shine kun manta dani ko kirana ba kuyi ba?"

Shiru tayi kafin tace "ba wani nan, kudai kuna can kuna soyayyarku da Papa, tunda yanzu babu kowa a gabanku, dama nice kuma kun kawar dani."

Turo baki tayi cikin shagwab'a tace "wallahi Mamie nayi kewar Papa, nan fa gaba d'aya ba dad'i, yau fa har zazzab'i ya kamani, amma dai da sauki."

Nan suka dinga hira har Ruk'ayya ta shigo ta kawo mata sannan ta kashe wayar, sauka tayi daga kan gadon ta zauna kujerar da Umar Faruk ke cin abinci harda turashi take da k'ugu tana fad'in "duk kabi ka matse waje kai kad'ai."

Plate d'in imdomin ta ta aza ta fara ci itama, satar kallon hannunta yake wanda suka sha jan lalle, tana ci tana kallonshi ta wutsiyar ido tana kuma tunanin abubuwan da matar nan ta fad'a mata, alwashi taci saita saka matar nan tayi nadamar abinda ta mata, to amma tayaya? dole saita samu kusanci da Umar Faruk, to shima tayaya? abu mai sauk'i, namiji neshi ke kuma macce, kawai ki samu kusanci dashi, a hankali ta juya ta kalleshi, caraf idonsu suka had'u, kallon baka da hankali ta masa yayin da shi kuma ya bita da harara, tunawa da plan d'inta yasa ta turo baki gaba cikin sigar shagwab'a ta d'an mangareshi da kanta, hannu tasa ta debo lomar indomie ta nufi bakinshi da ita, ganin yana mata kallon rashin fahimta yasa ta sake langab'e kai tace "bud'a bakinka mana."

Kai ya gurgiza mata alamar a'a, a bakinta ta saka lomar ba tare data kallesa ba tace "hum, kama daina kallona haka."

Wata sallamar ce ta katsesu daga k'ofar kewayen nasu, Umar faruk ne ya fita jim kad'an ya dawo, tsaye yayi a kanta yace "ki canza kaya Baba nasan ganinmu."

"Meya faru?" ta tambaya.

"Ki tashi, duk litinin ana zama wajenshi da wannan lokacin."

"Me ake tattaunawa?"

"Oh, Khairat, kiyi abinda nace mana."

"To bari na gama cin abinci na."

Ba yanda ya iya saida ta gama sannan ta wanke hannu ta d'auki doguwar riga tasa ta d'auki kallabi ta yafa, yana kallonta yace "hijab zaki saka."

"A'a, nifa bana iya zama dashi, kuma ba kace wajen Baba ne zamu ba."

Hijab d'inta da take sallah ya d'auka ya matso kusanta ya gyarashi , bai b'ata lokaci ba wajen saka mata, k'ok'arin 'kwacewa tayi ya mata wani jan kallo dole ta tsaya, gaba ya sata suka fita daga d'akin bayan ya rufe, suna daf da shiga d'akin Baba inda gaba d'aya mutanen gidan suke, hannunta Umar Faruk ya kama ya gyarawa yatsunsu waje d'aya tare da murzawa har suka shiga yayin da yayi sallama, amma suna shiga ya saki hannunta suka samu wuri suka zauna, tunda ya rik'e hannunta taji wani *baqon yanayi* a tare da ita da bata tab'a jin irinshi ba, kamar yanda shima abubuwan da yaji sunfi k'arfin wasa, dan saida ya tuna da maganar Ishaq cewar *wataqila yanzu ne ya fara soyayar gaskiya.*

Kallon kowa take yayin da su kuma suke sauraran nasihar da Baba ke musu akan rik'o da zumunci, sun jima sosai kafin Baba yaba Zeinab damar rufe musu taron da addu'a, sosai yarinyar ta shiga ran Khairat saboda ganinta bata fi yar shekara bakwai ba, amma sink'i sink'i addu'o'i na fitowa daga bakinta, haka suka tashi suka fito, kowa makwancinshi ya nufa sai Umar Faruk daya kalli Khairat yace "muje kiga Mama."

Binshi kawai tayi suka nufi d'akin Mama, da sallama ya shiga ita kuma tun k'ofar d'akin take kalle kalle har suka shiga, zaune yayi kusa da Mama dake kwance amma ganinsu tare yasa ta tashi zaune tana fad'in "ah, ashe tare kuke da 'yata."

Sai lokacin ta d'anyi zaune akan kujera tana kallon d'akin da kyau, k'aramar panka take kallo a ganinta ba zata musu komai ba, muryar Umar Faruk ce ta katse yana fad'in "ya jikin Mama?"

Kallon Mama tayi tace "dama baku da lafiya ne?"

"A'a 'yata, ai nama ji sauk'i."

Umar Faruk ta kalla dan haka yace "hawan jininsu ne ya tashi, amma sunsha maganinsu."

"Wane irin magani, kuma baku kaita asibiti ba?"

"Eh, akwai maganin da aka rubuta musu, to shine suke anfani dashi." cewar Ruk'ayya dake gyara shinfid'a.

"Amma ai hakan bai dace ba, me zai hana ku dinga kaita asibiti duk lokacin da bata jin dad'i? amma zama da ciwo ana shan magani barkatai."

Tsam ta mik'e daga kujerar ta durk'usa kusan Mama ta tallabota ta zauna daidai, kallon Ruk'ayya tayi tace "ki bani hijab d'insu."

Ba tace komai ba sai hijab d'in data mik'o mata, saka mata tayi sannan tayi tsaye tana ciccib'ar Mama tana fad'in "muje asibiti Mama, lafiyarki tafi komai mahimmanci, kuma suma kansu yayanki nasan sun san da haka, amma babu mai fasahar kaiki asibiti, sai sun rasaki kuma za kiga sunfi kowa damuwa da kuka."

Kallonta kawai Umar Faruk da Ruk'ayya da sauran yaran suke, tsaye yayi yana fad'in "ba wai bamu damu bane, muma muna...."

"Dan Allah kayi shiru, ni ba tambayarka nayi ba."

Mama ce tace "'yata dama kin barshi wallahi, naji sauk'i ai da dama jikin ba kamar d'azu ba."

"A'a Mama muje kawai, sai dai kuma ko kina so ki nuna min ni ba 'yarki bace."

Suna fitowa farfajiyar gidan ta kalli Umar Faruk tace "ka rik'e Mama, zan d'auko makullin mota."

Tana fitowa kuma da makullin da post d'inta ta kuwa haka ta rik'e Mama har suka fita inda Baba ya fito da su tafi tare amma Khairat tace kawai yayi zamanshi, tare da Umar Faruk suka tafi suna gaba ita dashi tana tuk'i, Mama na baya in banda addu'a da qaunar Khairat babu abinda take ji, bata san kuma me yasa ba amma taji daga haka son sarakuwar tata ya kamata, suna zuwa asibitin da taje da safe docteur Sadiya ta tafi sai wani docteur d'in, cikin qwarewa ya duba Mama kuma ya fad'a musu jininta ya hau, allura aka mata na saukar da hawan jinin sannan aka rubuta wasu magunguna masu matuk'ar tsadar gaske, ita ta biya kud'in sannan suka kamo hanyar gida, saida ta tsaya babban pharmacie ta siyo duka magungunan sannan suka tafi gida dare yayi sosai lokacin.

Har d'aki suka kai Mama ta kwanta Khairat taja zanin rufa ta rufeta, gefen fuskar Mama ta shafa tace "kiyi bacci Mama, dan Allah banda damuwa da tunani, ki more baccinki babu mai takuraki."

Mik'ewa tayi tana fad'in "saida safe Mama."

Hannunta taji ta rik'e hakan yasa ta koma ta durk'usa tana kallonta, cike da jin dad'i da tsantsar qauna Mama tace "na gode yata, ubangiji ya saka miki da mafificin alkairinsa, Allah ya kareki daga sharrin masharranta, Allah ya baki abinda kike so, Allah ya saka miki da gidan aljanna, Allah ya albarkaci rayuwarki da zuri'arki baki d'aya, Allah ya sakawa iyayenki da alkairi, Allah ya kareki daga bakin duniya, Allah....."

Rufe bakinta Khairat tayi ta fashe da kuka ta fad'a jikin Mama ta rumgume, saida tayi mai isarta ba wanda ya bata hak'uri kafin ta d'ago ta share hawayenta ta rik'e hannun Mama sosai tace "Mama, kin kusa kasheni da farin ciki saboda wannan addu'ar taki, tunda nake a rayuwata ban tab'a jin addu'a irin wannan ba, ko mahaifiyar data haifeni bata tab'a kwatanta yimin irin wannan addu'ar ba, Mama nice da godiya bake ba, ina da yak'inin wannan addu'ar taki ba zata fad'i k'asa banza ba, a yanzun nan sai nake ji kamar ni 'yar aljanna ce kuma zan gama da duniya lafiya, Mama Allah ya bar mana ke, kuma nayi alk'awarin zama a gidan nan har qarshen rayuwata in dai har zan dinga samun irin wannan addu'a a wajenki."

Tana fad'a ta bar d'akin tana kuka, Umar Faruk ma bayanta yabi bayan sunyi sallama da Mama, yana shiga ya sameta kamar ba ita bace mai kukan nan harta murje idonta tayi kwance, sai dai abinda Umar Faruk bai sani ba ta rufe ido ne amma addu'a Mama ce ke yawo a qwaqwalwarta, kashe wutar d'akin yayi bayan yayi shirin kwanciya sannan ya kwanta a saman kujera, zunbur ta tashi zaune tana lalubar wayarta ta kunna haske, a daqile tace "malam nifa bana bacci a cikin duhu, ka kunna fitilar mana in dai ba wani abu bane a ranka."

Wayarshi ce a hannunshi yana duba kiran da Zuby tayi bai d'aga ba, ba tare daya kalleta ba yace "ni kuma gashi bana bacci a cikin haske, ya kenan za ayi?"

_To fan's ne zasu bamu shawara, ya kuka ce akashe ko a barta kunne?_

_Idan an kashe akwai d'an dannau mai taushe mutun cikin dareπŸ˜ŽπŸ˜‚, idan an bari kuma shed'anun aljanu na anfani da hasken su cutar da bil'adama._
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

*_MasoyanaπŸ’–, kune abin alfahari na, ina matuk'ar ji daku fiye da tunaninku, fatana Rabbi ya bar qauna tare da soyayya, nasan ba zamu iya had'uwa daku ba dukanku, amma ina fatan Allah ya sadamu da alkairinsa sannan ya taramu a aljannatul-firdausi._*πŸ‘πŸ‘

_Bismmilahir-rahman-rahim_


2⃣6⃣


Wajen makunnin ta nufa tana shirin kunnawa yayi saurin tare gabanta, d'auke idonshi yayi daga nata saboda masha Allah akwai girma kamar idon Barbie ga kuma kyau da yalwataccen gashi, "dan Allah ka matsa min na kunna, bana iya bacci a cikin duhu, tsoro nake ji."

Da kanshi ya nuna mata gado yace "kije kiyi addu'a saiki kwanta, babu abinda zai sameki da yardar Allah."

"Ba zaka gane ba, dan Allah..." bata qarasa ba saboda hannunta data kai ta kunna wutar shi kuma ya rik'e.

Janye hannunta tayi tana sauke ajiyar zuciya tace "shikenan, kar Allah yasa ka kunna, amma wallahi naji hannun mutum a jikina ana lalubata, to zaka sha mamaki dan saina fasa maka kai wallahi."

Dariya ce ta subece masa komawa yayi kawai ya kwanta, harta kwanta itama amma data rufe ido saita ga su Musa a idonta, sosai ta rintse ido amma duk da haka bata daina gani ba, bud'e idon tayi taga duhu sosai, zaune tayi ta kalli wajen da Umar Faruk yake tace "malam nasan ba kayi bacci ba, dan Allah ka taimaka ka kunna ko hasken fitalar wayarka ne."

"Wayarki fa?" ya fad'a cikin taushin murya.

"Haka kawai zan kunna harsken wayata har safe, ai tunda ka hana a kunna wallahi na wayarka zaka kunna."

"To zan gani, wayata ce kota wani."

"Kaji kamar mai wata wayar million d'aya, wallahi saika kunnata ko kuma."

Ta fad'a tana saukowa daga kan gadon, jin tahowarta yasa ya tashi zaune yana fad'in "ko kuma me?"

"Gani nan ai a aikace zan nuna maka."

Da hasken wayarta taga wayar tashi akan qaramin teburin dake tsakanin gadon da kujerar da yake, tunkararta tayi gadan gadan tare da kai hannu zata d'auka, da sauri ya d'auki wayar tare da ajeta bayanshi ya rumgume hannaye yace "ki d'auka idan ke jan wuyace."

"Dan Allah ka bani, wallahi bana iya bacci a duhu, kuma gashi dare keyi har yanzu banyi bacci ba, zanfa maka kuka wallahi ko kuma na fad'awa Mama."

"Wace Mamar?" ya tambaya.

"Mamank...." kuma kawai sai tace "Mamana."

Kallonta yayi dan ya mata tambayar ne dan yaji me zata ce, a hankali ya zura hannu ya d'auko wayar ya mik'o mata kamar sakarai, hararanshi tayi tace "ka kunna mana, meye saika wani bani a hannuna."

Baiyi magana ba kuma bai bar mik'a mata ba, cike da haushi tasa hannu ta karb'a ta kunna fitilar, murmushi tayi ta kalleshi tace "kaga tasirina ya fara aiki a kanka, tun ma ba'a je ko ina ba kenan."

Zaune yayi yana fad'in "ke bani wayata, tasirin me? kin d'auka dabararki ce tasa na baki?"

Juyowa tayi tana kallon qwayar idonshi ta soka wayar a cikin rigarta tsakiyar mamanta sannan ta rik'e k'ugu tace "kazo ka d'auka idan ka isa."

Murgud'a baki tayi ta koma gado ta haye tare da fitowa da wayar ta aje gefenta, baki sake ta barshi yana kallonta har bacci ya d'auketa, saida ya tabbatar tayi nisa sannan ya taso zauna bakin gadon yana kallon fuskarta, baisan menene asalin abinda yake ji ba, sai dai yana ji kamar a yanzu haka baya so ta masa nisa, to amma me yasa? *my aunt Aishan Umma* ce zata baka amsa a gaba, wata irin nutsuwa ce yake ji tana sauko masa, ga kuma taimakon da tawa mahaifiyarshi wanda yafi komai faranta masa rai, ya jima a wajen sosai yana tunani akanta kafin ya tashi ya koma wajenshi, ko bacci bai d'aukeshi ba yaji Khairat ta farka a tsorace.

Da sauri ya dawo kanta yana kallonta, numfashi kawai take saukewa kamar wacce tayi tseren gudu, a hankali ya furta "Khairat, lafiya? meya faru dake?"

Kallonshi tayi a firgice sai kuma ta rufe bakinta da hannu tana fashewa da kuka, wata nauyayyen ajiyar zuciya ya sauke ya kau da kansa danya lura tana da saurin kuka akan komai, sake cewa yayi "Khairat, meya faru?"

Share hawayenta tayi tana kallonshi tace "ba komai, kaje ka kwanta kawai."

"Ya zaki ce ba komai? bayan ga komai nan ya faru."

"To me kake so nace? na fad'a maka bana son duhu, sune ke sake zuwa min duk da qoqarina nasan ganin na manta komai, fyad'e ba abu bane mai sauk'i, amma duk da haka ina so na manta dan nayi rayuwata ba tare da damuwa ba, naso na zama marar tsoro da fargaba, amma su sun saka na zama mai tsoro, sunsa min fargaban da bana iya sakewa a kowane lokaci, kullum ji nake kamar zasu qara dawowa gareni ne."

Hawaye ta goge tace "ka kwanta kawai." tana fad'a ta koma ta kwanta ta bashi baya.

"Tashi zaune." yanda ya fad'a yasa ta tashi ba tare da gardama ba.

"Kiyi addu'a kafin ki kwanta."

Kallonshi tayi kuma lokaci d'aya ta dauke idonta, a hankali yace "baki iya bane?"

Nanma shiru tayi kawai sai yace "to ki d'aga hannayenki, saiki dinga fad'ar duk abinda na fad'a, kinji?"

Yanda yace tayi, *ayatul kursiyu* ya fara karantawa sannan *ammana rasul*, kafin suka karanta *falaq* da *nas* sannan ya karanta mata *Allahuma aslaftu nafsi ilaikh, wa fawadhatu amri ilaikh, wa wajahtu wajhi ilaikh, wa aljahtu zahri ilaikh, ragabatan wa rahabatan ilaikh, lamalja'a wala manja minka illa ilaikh, amantu bi kitabikal-lazi anzalta wabi nabiyikal-lazi arsalta.*

"Ki shafe jikinki." ya fad'a.

Shafawa tayi sannan ta koma ta kwanta, a hankali ya tashi yana sake nanata kalmar fyad'e a bakinshi, karo na farko daya ji haushin masu laifi kuma yaji inama shiya d'auki mataki akansu , wutar d'akin ya kunna tare da komawa shima ya kwanta, ganin haske yasa ta kashe na wayarsa sannan ta sake rufe ido sai bacci.


******************

Koda tanti ta koma gida tasa Zuby ta kira mata sauran 'yan uwanta a waya kasancewar duka matane 'ya'yanta guda hud'u, nan fa ta fad'a musu matar Umar Faruk taci mutuncinta tare da fad'a musu qudirin Khairat, nan fa suka fara zaginta suna aibatata tare da cin alwashin fitar da ita daga gidan, sannan suka qara kitsama Zuby wani sabon shiri a kanta tare da alk'awarta mata sabon had'in magani na musamman domin yaqar Khairat.

Sai dai tanti ita burinta ya wuce nasu dan haka safiya ma take jira kawai tayi, danta lura yarinyar dole sai an had'a da malamai.

******************

Tunda Khairat take a gaba d'aya tsawon rayuwarta, bata tab'a bacci mai dad'in na yau ba, bata tab'a jin natsuwa da farin ciki ba a cikin bacci kamar yau, gashi kuma ubangijinta ya nuna mata wani abu da ko kad'an bai firgitata ba saboda nutsuwar data farka da ita, a baccinta Allah ya haska mata tanti Ma'u tana matuk'ar biyarta da sharri , sai dai ta rasa waye kuma me yasa ya fad'a mata cewar ta rik'e addu'a tafi komai mahimmanci, koda Umar Faruk ya tasheta tayi sallah zaune tayi ta murje idonta kafin yace mata "ki fad'i abinda zan fad'a."

Kai ta jinjina alamar tana sauraro, *Alhamdulillahi lazi ahyana, ba'ada ma'ama tana wa'ilaihir-nushur.*

Nanma fad'a tayi kafin ta shafa ta sauka daga kan gadon shi kuma ya nufi masallaci, har tayi alwala tazo ta kabbara sallah tana tunanin akan me matar nan zata nemeta da sharri, shin akan yarta ne ko kuma akan abinda ya faru tsakaninsu? da qyar ta saita nutsuwarta ta samu tayi sallah tana gamawa kuma ko hijab bata cire ba ta zauna bakin gado, a hankali take tunano addu'a da Umar Faruk ya fad'a mata jiya, tana haka kuma ya shigo d'akin.

Kayanshi ya bud'a ya d'auko duk litattafan daya fad'a jiya sannan ya zauna akan kujera, kallonta yayi yace "dawo nan ki zauna."

Ba musu tayi yanda yace, littafi mai tsarki ya bata sannan yace ta bud'e, a farko ta bud'e sannan ya fara biya mata daga qananan surori har guda goma, kallonshi tayi jin daga nan yake tsayawa yasa tace "to wai meka d'aukeni, iya haka zaka tsaya min? kaga ni qara min kawai ai zan iya."

"Da farko dai ina so ki d'aukeni a matsayin malaminki, dan ta hakane za kiga haske da albarka a karatun, sannan ki girmamani domin samun sauk'i, sai kuma jin maganata a duk lokacin dana miki, kin fahimta?"

"In dai sai nayi haka zan samu albarka a karatuna, to na shirya zama dalib'a 'yar shekara biyar a gaban malaminta."

"Da kyau." ya fad'a kafin yace "idan kina so na qara miki, ki fad'a min wanda na fad'a miki sannan."

Gyara zama tayi kamar zata kwanta jikinshi sannan ta d'ora yatsarta a littafin ta fara biya masa, duk da a cikin salon koyo take karatun, amma abin abin birgewa da sha'awa, bakinta yake kallo wanda take motsashi a hankali tana biya karatun domin gudun kar tayi sauri tayi b'ata kuma, sosai Umar Faruk ya girgiza domin kaf a cikin waje d'aya kawai ya mata gyara, shima kuma ta fad'a ne ba daidai ba, murmushi yayi har hak'oransa suka fito fili yace "kinyi qoqari sosai, kuma ina fatan zaki kasance haka, har ranar da zaki hardace al'Qur-ani a kanki."

Wata irin lallausan dariya tayi data tafi da imanin Umar Faruk dan bai tab'a ganin irinta ba a fuskarta, cike da jin dad'i tace "nima zan hardace a kaina, na zama kamar k'anwar nan taka?"

"Zama ki fita in har kika saka kanki."

"To shikenan qara d'ora min wani." ta fad'a cike da zumud'i.

Nan ya sake dora mata har suka kai suratul *Qari'a* sannan yace ta rufe littafin tare da cewa "ki tabbatar kin kawosu gobe, idan ba haka ba kuma."

"Idan ba haka ba me?" ta tambaya tana kallonshi.

"Zaki sha bulala ne, saboda ke dalib'a ce."

Wata dariya ta kece da ita mai qarfi kafin tace "ai bama zaka fara ba kaima, dan kasan zamu iya dakuwa da kai."

Kunnanta ya kama ba zato ba tammani ya murd'e fuska a had'e yace "ni kike fad'awa haka? anya kina neman albarka kuwa?"

Hannayenshi ta kama duka biyu tana rokon ya saketa tana fad'in "dan Allah kayi hak'uri wallahi ba zan sake ba malam, dan Allah kasa min albarka ko nayi saurin fahimta."

Sakinta yayi yana tunanin ya samu hanyar da zaibi da ita cikin sauk'i dan haka yace "idan akayiwa malam laifi har qasa ake duk'awa a bashi hak'uri, dan haka ki fara in dai har da gaske dalib'a ce mai neman albarka."

Ita kuma yanzun nan taji a ranta bata da wani buri daya wuce na karatu, musamman da taji wai yau itace take karatun littafi mai tsarki haka, shaukin abin ya shigeta sosai dan haka bako tunani ta zube qasa ta kamo hannunshi ta rik'e tana murzawa ba tare dama tasan me take yi ba tace "naji to kayi hak'uri dan Allah, ba zan sake ba, nidai ina sonna samu albarkar karatuna."

Shima biye mata yayi ya dinga murza tattausan hannunta yace "ba albarkata kad'ai kike buqata ba, akwai ta iyayenki, dama mutanen da kike zaune dasu."

Cikin mamaki tace "wai har suma?"

"Eh, basu cancanci saka miki albarka bane?"

Cikin turo baki tace "toya zanyi?"

Mik'ewa tayi yace "yanzu zaki fara ai."

Ta qasan ido ta harareshi kafin tace "toya zanyi yanzun?"

Wani shu'umin murmushi yayi ya tashi tsaye yace "biyoni muje."

Saida suka fita sun nufi d'akin Mama Maimuna yace "za muje ne mu gaida iyayenmu, sai kice kina neman albarkarsu."

Kallonshi tayi kamar zata fashe da kuka tace "zafa ka rusa min jiji da kaina, gaskiya ba zan iya ba."

"Shikenan, koma ki zauna, amma ki sani za kiyita karatu bakya fahimta, saboda ba albarkar manya a ciki."

Bubbuga k'afafu tayi cikin shagwab'a ta kutsa kai d'akin Mama Maimuna, ganinta kawai tayi ta fad'o mata dan haka ta tsorata, da sallama ya shiga sosai ya gaisheta duk idonshi na kan Khairat da har yanzu ta b'ata rai, da ido ya mata alama kafin ta fahimta ta kalli Mama Maimuna tace "ina...kwana, an tashi lafiya, ina neman albarka dan Allah ki saka min."

Mama Maimuna mamaki ne ya hanata magana, saida Khairat ta sake cewa "ba zaki samin bane kome?"

Kai ta girgiza da sauri tace "a'a 'yata, kin tashi lafiya? Allah ya miki albarka."

"To na gode, sai an jima." tana fad'a ta tashi ta fita shi kuma ya mata sallama ya fita.

Kewayensu ta nufa shi kuma ya janyo hijab d'inta ya nuna mata kewayen Mama Sa'a, ciki suka shiga amma Mama Sa'a harda rumgume Khairat tanata wasar baki tana gaisheta, haushi ne yasa Khairat yin shiru ta kasa gaisheta, danta lura irin mutanen nan ne masu shishigi, Umar Faruk kad'ai ya gaisheta kuma yanawa Khairat alama da ido akan tarbiyar gaisheta amma tak'i, fitowa sukayi suka shiga d'akin Mamanshi, suna shiga da sauri ta qarasa ta durk'usa gaban Mama tana rik'o hannunta da fad'in "Mama ya jikinki?"

Cikin sakin fuska tace "da sauk'i 'yata, kin tashi lafiya."

"Ina kwana aunty Khairat."

Please Login or Register in order to submit comment