Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kalli Khairat ta gefen ido sannan ya rage sautin murya yace "ina asibiti."

"Subhanallah, wake asibiti yah Umar?"

Wannan karan kallon idon Khairat yayi wacce take latsa wayarta sai dai zuciyarta bugawa take da k'arfi, haushi take ji yana taso mata tana ji kamar ta bugeshi tare da wayar, sannan yace "auntynki ce ba lafiya, amma yanzu zamu koma gida serum d'in ta kusa qarewa."

Zaro ido tayi ta kalli Mama sai kuma tace "tana kusanka ne?"

"Eh, wani abu ne?"

"A'a, ka gaisheta."

"Zata ji."

"Yah Umar. " ta kira sunanshi.

"Na'am." ya amsa yana kallon Khairat.

"Sumbata nake so kamin wacce baka min ba jiya ka tafiyarka, kuma na d'auka zaka kirani amma baka kira ba."

Umar Faruk kam mamaki ne yasa yace "sumbata kuma?"

Da sauri Khairat ta d'ago ta kalleshi, sai kuma ta mayar da kanta k'asa.

"Eh, ko ban cancanci sumbar bane duk da jiya ne darenmu na farko?"

Qasa yayi da murya yace "kinga zan kiraki anjima."

"Wallahi ban yarda ni saika min." ta fad'a cikin shagwab'a harda kukanta.

A hankali ya tashi ya fita bakin k'ofar d'akin ya danna mata sumbar sannan ya kashe wayar, sai dai kuma Khairat tajishi hakan ya qara harzuk'ata.

Tana aje wayar tace "shikenan Mama, na shiga uku, wallahi harta fara laulayi."

_KeπŸ‘€πŸ‘€πŸ‘€ laulayin lafiya._

"Meya faru, meya ce miki?" cewar Mama kamar zata had'eta.

"Waifa suna asibiti bata lafiya, kinsan dai ba haka kawai za tayi rashin lafiya ba, gashi abinda muke gudu ya faru, kuma ni na riga na bashi kaina tun ban tare ba."

πŸ˜›πŸ˜›πŸ˜›πŸ˜›πŸ˜› _FAN'S JIHADI sukace ke kika jiyo_

Ajiyar zuciya Mama ta sauke tace "to kin gani, wallahi ba zan iya wannan kayan takaicin ba, dan haka shiryawa za kiyi kawai ki tare gidansa kema, in yaso duk abinda suke ayi a gabanki, dan zai iya mantawa dake anan d'in, yana can ya samu mai kud'i kenan ya fita harkarki, dan haka ki koma can ki zauna duk abinda suka ci kema kici wanda sukasha kema kisha, kinji ko?"

"Amma fa Mama ba...."

"Amma me? dan ubanki ana nuna miki annabi kina rintse ido, duk abinda nake yi ba saboda ke bane nake yinshi, dan haka ki fara shiri wallahi kin kusa komawa gidanki."

Tashi tayi ta barta ita kuma ta koma ta kwanta dan har yanzu ba dad'in jikinta take ji ba, dan ba qaramar wahala tasha ba abinka ga sabbin shiga.

******************

Ran Khairat a matuk'ar b'ace ba tare data kalleshi ba tace "ka kira min *Sadiya* tazo ta cire min na koma gida."

"Ki bari ta qarasa mana." ya fad'a yana kallon ruwan.

Bata san me yake damunta ba amma bata kosan had'a ido dashi, a zafafe tasa d'aya hannun ta janye sirinjin daga hannunta hakan kuma yasa jini ya fito tunda bata cire yanda akeyi ba, kallonta kawai yake ita kuma ta d'auki mayafinta ta laga a kafad'a tasa takalmi tayi hanyar fita, da kallo ya bita yana k'ok'arin kiran sunanta.

"Khai...k.k..." tuni ta fita dan haka ya biyota da sauri, har zai tari gabanta saiya tuna lokacin data maresa,😁( ba kyau), cak ya tsaya sai kuma ya fara binta a baya har suka fita, Sadiya ce taga fitarsu a ranta tace "Allah ya had'aka sai hak'uri."

Tana fita farfajiyar ta tsaya saboda ganin motarta, juyowa tayi ta kalleshi lokacin daya tsaya gabanta, hannu ta tara masa tace " bani makullin motata."

D'ago hannu yayi zai mik'a mata sai dai kuma baya so ya bata, da k'arfi ta fizgi makullin tana fad'in "ka bani nan, ko taka ce?"

Tana karb'a ta dalla masa harara tace "inma kanayi ne dan naji haushi to ba zanji ba, da kai da matarka baku isheni kallo ba, kana k'ok'arin kaci mutuncina a gaban k'aramar yarinya saboda kaga damata, to kaje ka had'iyeta mana iyakar sumba , ba shikenan ba saiku huta."

Motar ta nufa ta bud'e ta shiga ta tako da k'arfinta tayi kwana domin ta hau kan titi, saida ta tsaya inda yake ta zuge galss tace "ka tari taxi ta mayar da kai inda ka fito."

Rik'e kugu yayi da hannu d'aya d'ayan kuma ya rik'e wuya, yana so ya fahimci wani abu amma ya kasa, to duk miye na wannan harzuk'ar? qarasawa yayi gaban titi ya tari taxi yace ya mayar dashi ma'aikata, abin mamaki shine baijin komai dan gane da abinda ta masa, ranshi bai b'ace ba kuma baijin haushinta, to me yasa?πŸ˜‰ka tambayi Hasfat A A, haka ya koma jiki ba k'wari wata zuciyar na raya mishi ya dinga taka tsantsan ya daina waya da Zuby a gabanta, wata zuciyar tace masa to akan me? ai matarka ce, haka dai har yamma tayi ya tashi ya nufi gida yana tunanin yau kuma wacce zai isko.

***************

Da qyar takai kanta shagon wani *Saminou* saboda jiri dan dama ba'a tashi lokaci d'aya idan aka gama sΓ©rum, kuma gashi ba wani abu bane a cikinta, tana zuwa ta paka motar anan, fad'a mishi da tayi bata jin dad'i yasa ya shiga motar ya tukata ya kaita gida, tare suka fita ya bata makullin motar a shiga gida shi kuma ya hau acaba ya mayar dashi, ganin layin da take yasa suka fara tunanin ko shaye shaye take, Ruk'ayya ce ta taso da Umar Faruk ya bata makullin d'akin ta bud'e mata sannan ta shiga, da k'arfi ta fad'a saman gado ta fashe da kuka tana fad'in "wayyo Mamie, zuciyata zafi take, ji nake kamar zata fasa qirjina ta fito, dan Allah Papa kazo ka d'aukeni mu kuma gida."

Ruk'ayya da taji haka yasa ta shigo a hankali ta fara cewa "aunty Khairat, lafiyarki k'alau? me yake damunki? ko baki da lafiya ne?"

Da qyar tayi zaune tana kallonta hawaye na ci gaba da zuba mata tace "ki bud'a fridge akwai madara a ciki ki d'auko min nasha."

Da sauri ta juya ta d'auko ta kawo mata saida ta bud'e murfin sannan ta bata ta kifa kai, saida ta shanye duka sannan ta jefar da kwalin , Ruk'ayya kuma d'aukar kwalin tayi ta rik'e ta sake tsayawa gabanta tana kallonta tace "aunty kina buk'atar wani abun?"

Saida ta goge hawayen dake fuskarta cikin shagwab'a tace "kin iya dafa indomie?"

_Ko dai kin manta ba Umariri bane?_

"Eh, aunty Khairat na iya." ta fad'a cikin ladabi.

Nuna mata tayi da hannu tace "ki bud'a coffre d'in nan akwai indomie, ki d'auki guda biyu ki dafa min, idan akwai k'wai ki had'a min dashi guda uku."

"Ai kuwa aunty babu k'wai, sai dai in za'a siyo ne?"

"Yanzu babu kwai a gidan nan? to jeki dafa hakanan kawai."

Tana fad'a ta kwanta saboda jiri, d'aukar indomin tayi ta fita nan ta fara dafa mata, cikin k'ank'anin lokaci ta gama ta kawo mata kuma taji dad'inta sosai, hakan yasa ta kalli Ruk'ayya tace "ke ba kamar yayanki ba, kina da kirki."

"Shima yana da kirki aunty Khairat, kawai dai baki fahimceshi bane."

"Ke mugu ne fa, k'etar tsiyace dashi."

Yar qaramar dariya Ruk'ayya tayi tace "ba zance miki a'a ba, yaya kam akwai zafi kuma akwai salon k'eta, amma kuma in dai har zaka dinga jin maganarsa sannan baka rainashi ba, to gaskiya zaku zauna lafiya dashi."

Cike da basarwa tace "ok, kije, idan na fita zan siyo k'wan saiku aje."

Tashi tayi tana fad'in "to aunty Khairat, an gode."

****************

Yana shigowa gidan tanti Ma'u ya samu tare da Mama suna hira, har qasa ya tsugunna ya gaishesu sai dai bai bari sun had'a ido da tantin ba, dan yasan tasan me yayi kuma tana kallonshi da abun, Mama ce tace masa "akan maganar tarewar Zubeida ne, ta yarda ta dawo gidan mijinta ta zauna itama tayi karatunta."

Kallon Mama yayi ya kuma kalli tantin, tanti Ma'u ce ta katseshi da "ko dai baka shirya tariyarta bane, kafi son ka dinga zuwan can gida kana....."

"Na amince tanti, yaushe ne?" ya katseta dan yaga zata tona mishi asiri, ita kuma dama ba ruwa bane a idonta, dan haka ba komai bane a wajenta danta fad'a kowa yaji.

"Nan da kwana uku ne." ta fad'a a kausashe.

Tashi yayi ya nufi kewayen nasu yana mamakin canzawarsu, tunda ya tunkari d'akin yaji kid' na tashi, can cikin mak'oshi yayi sallama dan haka ma bata ji ba, shiga kawai yayi tare da tsayawa k'ofar d'akin yana kallonta tana tiqar rawarta, kayan jikinta su suka d'aga masa hankali tare da tayar masa da wata kafirar sha'awa da bai tab'a jin irinta ba a rayuwarsa, iya cinyoyinta wandon yake sai rigar da ba za'a kirata da bras ba haka kuma bata fi bras girma ba, rintse idonshi yayi sosai ya cije labb'enshi , bud'e ido yayi ya sake saukesu a kanta, da k'arfi ta juyo hakan yasa gashinta dake sake saida ya tashi sama shima ya juya sosai, duk da ganinshi da tayi ba tayi wani yunk'urin kare jikinta ba sai dai dakatar da rawar da tayi, gumin data had'a yasa ta fara takowa itama da nufin fita, tsaye tayi saboda ya tare hanyar fitar kuma har yanzu idonshi na kanta ya kasa d'aukewa , hannayenta ta d'aga tana tattare gashinta tana kallonshi tace,

"Ka bani hanya zan wuce."

Ganin ya kasa gusawa kuma har yanzu kallonta yake yasa ta matso daf dashi ta d'aga kanta tana kallonshi saboda ya fita tsawo sosai, wani mayan kallo ta masa tana murmushi tace "yadai, kana jin wani abu ne?"

Da sauri ya dawo hayyacinshi hakan yasa girgiza kai, wani murmushin ta sake yi tace "hakan yafi maka."

Saida tayi kamar zata fad'a jikinshi kafin ta samu ta wuce saboda ya kasa matsawa a hanyar, takalmi tasa ta shiga douche tayi wanka duk da ta d'auki lokaci hakan yasa ma Umar Faruk tafiya masallaci saboda idan ya tsaya jiranta zai b'ata lokaci, harya dawo bata shirya ba sai d'aurin qirji daya sameta dashi tana shirin saka kaya, bai sake kallonta ba harya saka doguwar rigarshi zai shiga wanka tace "kayi hak'uri fa, d'azu na baroka acan wajen." ta fad'a tana dariya.

Kallonta yayi kawai yace "hmmmm, ya jikin naki?"

Saida ta nufo wajenshi ta bud'e fridge ta d'auki ruwa sannan ta fara bud'ewa tana fad'in "da sauki, amma dai ba zaka sake bari na kwana a cikin sauron nan ba ko? dan nan gaba nasan mutuwa zanyi."

Sallamar tanti Ma'u ce ta katsesu ta shigo ganin amarya, Umar Faruk ne ya leko yana fad'in "tanti shigo mana."

Khairat kuma wajen kayanta ta nufa ta fara neman wanda zata saka har tanti Ma'u ta shigo, Umar Faruk ne ya bata wajen zama amma Khairat ko kallo, cikin taushin murya yace "Khairat, wannan itace magajiyar Mama kuma mahaifiyar Zubeida."

"Oho , ina wuni Mama, ya Zubeida? fatan tana lafiya?"

"Um , lafiya lau."

Tana fad'a ta tashi tace "Umar ni zan wuce, zaka zo ganin matar taka?"

Saida ya kalli Khairat yace "eh tanti zanzo."

Tanti Ma'u kam mutanen nan ne da bakinsu baya da linzamin, kawai sai cewa tayi "da alama karuwancin harya fara tasiri a kanka, tunda gashi har saika kalleta kafin ka yanke hukunci."

Labule ta bud'a zata fita Khairat ta rufe wajen kayanta ta matso tana fad'in "yadai tsohuwa, me kika ce? sai naji kamar kince karuwanci ko?"

"Eh, haka nace, ko k'arya nayi ba karuwar bace ke? me ake kiran mace irinki inba karuwa ba? ke kar kice zaki min fitsara dan wallahi ba mutunci ne dani ba, ba zan duba cewa ke sarakuwata bace ko kuma kishiyar 'yata, tsaf zan kwab'e kayana na dakeki son raina."

Dariya kawai Khairat tayi, kasancewar ba mai son hayaniya bace hakan yasa kawai tace "bansan me kika sani akaina ba da har kike kirana da karuwa, amma ga dukkan alama 'yarki kike tayawa kishi tunma bata shigo gidan ba, to ba komai kije, amma ki sani ni Khairat da karuwa ce, wallahi da Umar Faruk bai kusanci 'yarki ba a daren jiya, ki dinga sanin me kike fad'a dan baki san me za'a fad'a miki ba idon kin b'arota da zafi, Umar Faruk kuma gashi nan ki d'auka ki kaiwa 'yarki, amma nasan saiya dawo gareni, koba haka ba...... *Faruk*?"

Ta fad'a tana fad'awa jikinshi tare da shafo fuskarshi, tsikar jikinta ne ta tashi haka shima, a take yaji zufa na tsattsafo masa, ba abinda ya masa dad'i kamar kiransa da tayi da *Faruk* dan babu wanda ya tab'a kiranshi da haka sai yau, bai iya cewa komai ba saboda mamaki, tanti Ma'u kuma cewa tayi "ke dai wallahi anyi tsinanniya marar kunya, yanzu a gabana kike rik'eshi haka kamar wata uwarki ce ta haifeshi."

"To wace kunya kuma? mijina ne fa, nan da qananin lokaci ma cikinshi zaki gani jikina." duk tayi maganar ne tana sake cukwikuye Umar Faruk.

"Mtsssss, Allah ya wadaranki 'yar iska kawai, wato kinzo kin samu wuri harda mik'e qafa, kamar ba kece yar d'an siyasan nan ba da ba'a fadanshi da alkhairi , ke da gani nasan baki samu tarbiyya ba daga wajenki uwarki, kuma nasan hakan ba zai rasa nasaba da tasu rashin tarbiyyar suma iyayen naki."

D'agawa tayi daga jikin Umar Faruk tace "ke tsohuwa, kifa kama girmanki, ba mutunci ne dani ba wallahi saina zubar miki da...."

Yayi saurin saka hannunshi ya rufe mata baki yana kallon tanti yana fad'in "dan Allah tanti kiyi hak'uri ki tafi, nace zanzo."

"A'a, saketa ka barta ta fad'i abinda take son fad'a danta nuna min ita yar zamani ce, da wallahi nima saina nuna miki ni tsohuwar zamani ce, wai har wani cika baki kike zaki raba Umar Faruk da Zubeida ko? to bismillah, idan kika fasa raba tsakanin nasu ke ba *'yar halak* bace, baki haihu cikin uwarki da ubanki ba, shed'aniya kawai marar kunya."

Jin abun na tanti wuce ya gona da iri yasa ya dafa kafadunta ya fitar da ita daga d'akin, Khairat kuma kanta ne taji yana sarawa da k'arfi sosai ga qirjinta da take jin yana d'an zafi ga kuma dukan da yake mata, hannu biyu tasa ta dafe kanta sosai ta rintse ido dan kamar saukar guduma take ji a cikin qoqon kanta, da qyar Umar Faruk ya fita da tanti daga gidan ya had'ata da Aliyou dake kofar gida yace ya rakata ta shiga taxi, wannan masifa data dinga yi yasa mahaifiyar Umar Faruk itama kanta ya fara sarawa saboda hawan jini ne da ita, ko kad'an bata qaunar hayaniya koya take.

Mikewa tayi da qyar badan tana ganin gabanta ba ta fara bud'a duk wani abinda take ganin za'a aje abu ciki mai mahimmanci kota samu taga maganinta, tana cikin dubawa Umar Faruk ya dawo d'akin, binta yake da kallo saboda ganin tana abu kamar makauniya dan ba daidai ba ma take tafiya, ganinshi a bayanta yasa ta dago hannunta dafe da kai tana ganin dishi dishi ta fara masa magana cikin yanayin matukar shan wahala,

"Dan....Allah ka tai ....maka min, a cikin kayan nan ka ....duba min...ma...ga...maga."

Bata qarasa ba tayi luuu ta fad'i kasa, da gudu Umar Faruk yayo kanta ya zube qasa ya fara kiran sunanta, shiru bata amsa ba, cike da damuwa yace "na shiga uku, tanti ta kwanto min bala'i, yanzu gashi bansan meye matsalar ba, ya zanyi da ita?"

Tashi yayi da sauri ya d'auki ruwan data aje akan fridge yazo ya zuba a hannu ya fara shafa mata a fuska, da qyar ta farfad'o sai dai da wani sabon ciwon kan, da kuka ta farka tare da saka hannaye biyu akai tana fad'in,

"Kaina zai fashe, ka taimaka dan Allah ka d'aure min, zai fashe, kaina zai tarwatse, ciwo yake min sosai, dan Allah ka d'aure minshi *Faruk*."

"Kanki ne ke ciwo?" ya tambaya cike da tausayi.

Itama cikin kuka tace "qirjina ma fashewa zaiyi, amma nafi jin ciwon kan nan, dan Allah ka taimaka min ka samo abu ka d'aure minshi."

Rufe ido yayi lokaci d'aya kuma ya bud'e ya saukesu a kanta, tsaye yayi tare da sungumarta ya rumguma a jikinshi, yanda ta kwantar da kanta a qirjinshiya yasa hankalinshi ya sake tsananta tashi, domin kuwa tsaf yake jiyo yanda jijiyoyin kanta ke harbawa, a hankali yake takawa da ita harya direta akan gado, ya qura mata ido yana ganin jijiyoyinta duk sun fito, alamu ne qarara suka bayyana masa irin wahalar da take ciki, haka kawai sai yaji inama ciwon ya koma kansa, koba komai zai fita juriya da hak'uri, gyara zamanshi yayi a kan gadon yasa hannayenshi biyu ya fara shafa kanta daga farkon inda take aza goshinta wajen sallah, har zuwa inda gashinta ya tsaya kusa da kunne, ya jima yana shafa mata kamar yana wasa jin haka kuma yasa Khairat shako wuyar rigarshi cikin azaba da rad'ad'i ta bud'e ido danta masa magana amma sai taga dishi dishin ma har yafi d'azu, dan haka ta d'ago kanta ta kai bakinta har saman hanshinshi sannan tace "ka d'aure min kaina nace, ko so kake na mutu? mugu kawai azzalumi."

Shidai baice qala ba harta saki wuyan rigarshi, yana cikin shafa mata ya matse daidai inda gashinta ya tsaya sosai da yatsa biyu, wata siririyar qara tare da zabura ta cakumi rigarshi ta shige qirjinshi tana rik'e hannunshi daya matse mata kai da k'arfi sosai, k'ok'arin k'wace hannunshi take dan ba qaramin matsa ya mata ba, shi kuma ya rik'e sosai hakan yasa ta kasa k'watar kanta, turmutsutsu kawai take a jikinshi tana zubar da hawaye, gashi tana rok'on ya saketa amma bata jin muryarta na fita, da qyar yayi dauriya ya k'arasa addu'o'in da yake karanta mata saboda yanda take had'a jikinshi da nata tana murzawa, ba tare daya d'auke yatsunshi ba yaja yatsun nashi da k'arfi har saida ya diresu akan inda take aza goshinta wajen sallah sannan ya saketa, tana jin wani sauk'i ya zirnyarceta ta fad'a saman pillow tana sauke numfashi amma idonta rufe, sai lokacin taji kan yana mata sauk'i sosai sai kuma taji qirjinta kamar zai tsage, hannaye ta d'ora akai tana murzawa, ganin haka yasa ya d'auke hannayenta yace "bara na taimaka miki, shima zai bari da yardar Allah."

Kallonta yake yana tunanin yanda zaiyi wannan taimakon, kiran sallah isha'i ne ya riske kunnuwanshi, a hankali ya fara k'ok'arin sauka daga kan gado amma sai yaga ta dunk'ule waje d'aya tana dafe qirjinta sosai, wani sauk'ak'ak'en numfashiya sauke sannan ya dawo ya zauna, gyara mata kwanciyarta yayi ta mik'e sosai kamar wata gawa sannan ya d'auke hannayenta daga qirjinta, "um um, Umar faruk, karka fara." cewar wani b'angare na zuciyarshi.

"Ba komai, matarka ce ai, ka d'auka yanzu ma wani *Jihadi* ne za kayi, domin tana cikin halin rayuwa ne da mutuwa."

"Hummmmmmm." cewar Umar Faruk.

A hankali ya kai hannu ya sab'ule d'aurin qirjin dake jikinta, wata 'yar k'aramar numfashi yaja tare da saka tafikan hannayenshi ya rufe fuskarshi, ba k'aramin rikita mashi lissafi sukayi ba, kasancewar Allah ya horesu gasu kuma b'ul b'ul dasu kamar na mai k'aramin ciki, jawur suke har sunfi fatarta haske uwa uba kuma kan😎, kamar wani abu ya cijesu saboda yanda suke jawur dasu kamar an sulb'esu, gasu giri giri suke babu alamar kunya a idonsuπŸ˜‰πŸ‘€, bud'e idonshi yayi ya sauke a fuskarta sai dai idonta a rufe suke, da alama bata ma cikin hayyacinta, "k'uk'ut." ya had'iye yawu kafin ya kai hannunshi da tuni suka fara karkarwa ga gumi dake tsattsafo masa, dan tuni ya shiga masifa network kuma ya kawo service, awazarta duka biyu ya soka hannayenshi a qarqashi ya tallabosu, wata irin bank'arewa tayi ta tusa masa qirkinta a nashi qirjin saboda masifar zafin da taji, kwantar da ita yayi saita kuma tasowa tana kara 'kwak'umeshi, sake mayar da ita yayi yana fad'in "ki tsaya mana, bana son mugunta fa."

_To wai fan's, me Umar Faruk ke nufi da baya son mugunta, mema aka masa na muguntar?_

Nan ma dai addu'a ya mata ya tofa mata sannan ya rabu da ita yana ji yana gani jam'i ya wuceshi, sauka yayi daga gadon ya bud'a wajen kayanta ya d'auko wata rigar bacci da wandonta silip ya aje mata yana fad'in "ki tashi ki saka."

Sai dai bansan Khairat azabar ciwon kai yasa ji da ganinta sun d'auke ba na wucen gadi , ko alamar taji ma ba tayi ba hakan yasa ya d'auki kayan ya warware rigar yana kallo........



_Me kuka ce?😁 zai saka ne ko kuma dai yaya zaiyi?_πŸ’


πŸ’‹luv u my Meelat.πŸ‘„
06/08/2019 Γ  00:06 - Meerahgee❀: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*JIHADI*
_Umar faruk_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

_NA_

_SAMIRA HAROUNA_


_DEDICATED TO_

*MA FAMILLE*

πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

*Sadaukarwa ga*

_Fateema_ momyn Dady
_Maman tasleem_

_Bismmilahir-rahman-rahim_


_Allahumma antas- salam, wa minkas-salam, tabarakta ya zuljalali wal-ikram._

*Astagfirullah wa atubu ilaikh.*

2⃣5⃣


Kamar zai fita daga d'akin kuma saiya kashe wutar d'akin ya dawo da rigar a hannunshi, duk da ba'a gani amma haka ya lalabata ya qarasa zame towel d'in, wandon ya d'auka ya fara saka mata sannan ya zura mata rigar, saida ya tabbatar komai yayi daidai sannan ya kunna hasken d'akin, daga inda yake ya kalleta ganin kayan sun mata d'as gwanin kyau, fita yayi daga d'akin danya tafi masallaci sai dai kuma yasan alwalarshi ta karye dole saiya d'anyi wankaπŸ˜‚ ko sama sama neπŸ˜›, haka kam akayi saida yayi wanka ya fito ya bud'a kayanshi zai ciro wasu kayan ya saka kawai yaga maganin da kakarta ta bashi, a hankali ya fara tuna maganganun iyayenta dama kakarta d'in, hakan yasa ya ya fad'a a fili "kenan wannan ne abinda ke damunta? to me yake janyo mata shi?"

Maganar kaka ya sake tarowa baya kawai sai yace "uhum, kenan b'acin rai da damuwa ne kamar yanda mahaifinta ya fad'a? ikon Allah."

Maida kallonshi yayi gareta tana bacci hankali nutse, shiryawa yayi ya aje magungunan kusa da ita ya fita ya nufi masallaci, shi kad'ai yayi sallah shi sannan ya hau mashin d'inshi ya d'an fita, baifi awa d'aya ba kuma ya dawo, har yanzu bacci take dan haka ya fito da clΓ© USB daya siyo ya mak'ala a tv ya jona ya fara sauraren k'ira'o'in, wannan karatun ne ya tasheta yana ganin haka ya taso zunbur yayi kanta, tana dafe da kanta ta fara k'ok'arin bud'e idonta, a kanshi ta saukesu tana kallonshi, saida ta saisaita kanta sannan ta kalli d'akin da kyau ta kuma kalli jikinta, da sauri ta dafe qirjinta ta kalleshi a tsorace.

"Ba wannan kayan bane jikina, waya canza min kayana?" ta tambaya tana kallonshi.

"Dank'ari." cewar Umar Faruk.

Da sauri ta sauka daga kan gadon tana fad'in "waya canza min kayan jikina, ka fad'a min gaskiya Faruk, kaine? yanzu kenan ka kalleni saboda kaga bana cikin hayyacina? kamin adalci kenan? saboda kawai kana mijina."

"Kinga dan Allah, bafa abinda kike tunani bane, ba..ni ba...bane ba sauya miki kaya."

Kafeshi tayi da ido tace "kalleni."

Kallonta kam yayi sai dai gaba d'aya gabansu dukan uku uku yake, a hankali tace "ka rantse ba kai bane, ni kuma saina yarda."

Shiru ya d'anyi kafin yace "kiyi hak'uri, ni na canza miki, amma...."

"Amma me? baka kalleni ba za kace?"

Kuka ta saka da k'arfin gaske harda bubbuga qafafu tana fad'in "shikenan ya gama dani wallahi, ace kamar wannan yaron ne zai saka min kaya a jikina, shikenan ta qare miki Khairat, baki da bakin magana kuma tunda haka ta faru, nan gaba kuma kusantarki zaiyi daga nan kuma saiki d'auki cikinshi sannan ki haifeshi , bayan nan kuma saiya...."

Da sauri Umar Faruk ya janyo k'ugunta ya had'e da nashi ya d'ora yatsarshi akan labb'ata suna kallon juna, wani yanayi yake ji dashi kad'ai yasan me yake ji, dakewa yayi ya kama gashinta ya fara wasa dashi kamar gaske harda murmushi kafin yace mata "kiyi shiru, bana so mutanen dake waje su d'auka wani abu ne nake miki, dan haka kuskure ne, ki cire wannan tunanin a qwaqwalwarki dan haka ba zata faru ba, ni Umar Faruk ba zan iya had'a jikina da naki ba."

"Saboda me? ni karuwa ce? kaima haka kake gani? amma me yasa ka aureni to?"

Ganin hawaye sun cika idonta sai kuma ta bashi tausayi sosai, a hankali ba tare daya raba jikinshi ba yace "ni ba haka nake nufi ba, kawai dai ba zan iya had'a jikina da naki bane, saboda ina da matuk'ar kishi."

Qasa tayi da idonta tace "kenan yanzu da ice ka had'a jikinka? ko kuma kana nufin daga wannan had'awar da kayi yanzu

Please Login or Register in order to submit comment