Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

me and i want to sleep" wani kallo ya mata,da sauri kamar wanda aka tsikarama abu ya tashi yana kallon idanunta yace "Roohii get up,tashi muga" ta bud'e ido da sauri jin yanayin kiran da yayi mata,tana yamutsa fuska tace "what else?" Yana yi mata wani irin kallon k'urillah yace "anya baby.?" K'uresa tayi da kallo tana harararsa tace "me wai?" Yayi murmushi yace "I'm thinking,but koma dai mene ne ki daure please muje muga Dr yau" saurin bud'e ido tayi tana kallonsa,ko me ta tuna kuma sai tayi murmushi tace "Uhn! Za ka fara ko?" Yace "What shall i do again?" Cikin shagwab'a tace "wancan lokacin ma ciki na na farko haka kace,muna zuwa shi kuma Dr Paredes d'in nan ya wani kama ya tabbatar da maganar" yayi murmushi yana d'ago fuskarta idanunsu a sark'e yace "I will be happy idan hakan ya tabbata" murmushi tayi masa bata sake cewa komai ba ta mayar da idanunta ta lumshe,forehead d'inta daya sumbata yasa a hankali tana tura baki tace "Just let me sleep,anjima sai muje ko?" Yace "an gama,sleep tight" tana kwance a jikinsa bacci mai dad'i ya d'auketa,ba ita ta farka ba sai yamma,har Nuraz d'in ma ya fita ya dawo,but kuma tun daga maganar da suka yi na zuwa hospital ranar sai taji bai sake yi mata zancen ba,for almost two days taga ya daina fita ko ina they were always together at home,Maysam kuwa tun ranar da tayi mata ta'adi da ya fita da ita bata sake ganinta ba,data tambayeshi yace tana gurin Lolly,she didn't bother to ask again because she knew where she was,za ta samu kulawar da ko tana gurinta iya abunda za ta iya yi mata kenan,da taga cikin kwanakin sai dai yayi aiki a computer,ta kalleshi lokacin yana zaune saman bed da safe ya mik'e k'afafu sanye da wani crazy white jean da farar sleeveless,ta kwantar da kanta a jikin kafad'arsa tana kallon abunda yake yi a computer tace "wai kwana biyu baka jin fita ne? Na ga sai dai kayi aiki a gida,ko fita muka yi ma bama wuce apartment d'in Hajiya ko su Mom daga can kuma ni banga kana fita ba" murmushi yayi mata then yace "ina ne mutum zaije,ana batun pandemic na virus a wasu sassan na duniya?" Saurin kallonsa tayi tana bud'e ido tace "kamar yaya?" Ya d'an rufe computer half yana kallonta yace "wai baki san me yake faruwa ba dama?" Ta bud'e ido tace "ni ina zan san wani abu da yake faruwa?" Murmushi yayi yana kallonta da mamaki yace "ba kya hawa social media ne?" Tana yamutsa fuska tace "ni fa kwanakin nan kawai nayi bacci shi ne karatun da nafi iyawa,wayar nawa ma ko ina nasa shi Ohoo" ya bud'e ido yana kallonta intently yace "lallai matar nan,anya ma ba baby za ki bani ba this soon kike bacci?" Bud'a hannu tayi tana dariya tace "ni dai kayi shiru ba ni da komai" da sauri ya ajiye computer saman couch yace "ban yarda ba gaskiya sai na duba" ta zaro ido da sauri tace "me za ka duba?" Yace "ni dai Allah sai na duba" da sauri ta tashi za ta bar kusa da shi yayi maza ya rik'o ta yana cewa "yi a hankali kada ki fad'i" ta kyalkyale da dariya tana kallonsa tace "ni fa ba ni da komai" murmushi yayi yana kallonta yace "Let's not argue akan hukuncin ubangiji,mu jira lokaci zai nuna mana" ta fara dariya ta hauro saman thighs d'insa ta zauna,ta rik'e kansa da duka hannayenta suna fuskantar juna tace "I just have nothing" ya daga gira had'e da tab'e baki yace "alright! Tunda kince haka,sai muyi deal kawai,idan akwai dama tunda kika yi musu yau sai na cinye ki,na cinye komai" yadda yayi maganar yana bud'a baki kamar wani carnival,ta sake kyalkyewa da dariya then tace "then,what if i don't have?" Yana d'aga mata gira yace "shi kenan sai ki cinye ni" ya fad'a and giving her a beautiful smile,dariya ta dunga yi masa yana kallonta,sai da tayi mai isarta ta dakata tace "then?" Ya bud'e ido yana kallonta yace "what?" Ta sake yin dariya tace "Mmm! U made this deal cleverly,and ban yarda ba ni sai dai a canja wani" yana sakin murmushi yace "wanne kike so ayi?" Tace "sai dai idan za muje Nigeria,because ina son ganin su Afaf da dangin Mammana" murmushi yayi da wuri yace "already done! Whatever u say" tayi k'ara ta rungume shi tana cewa "Yay! Nima na yarda",hugging d'inta yayi back yana sakin murmushin mugunta,da ya samu ta sauka akan k'afafunsa ya ci gaba da aikinsa yana satar kallonta yana dariya k'asa²,yana nan a zaunen ya jiyo ta suna waya da su Afaf tana cewa za su zo Nigeria,wani ihun da Afaf tayi tun a wayar yasa da sauri ta janye wayar a kunnenta,can bayan ta mayar da wayar taji Afaf tana cewa "but private jet d'inku za ku biyo ku zo ne ko kuwa? Na ji fa an saka dokar hana zirga² since the issue of this virus has arisen?" Nusrah tayi saurin katse Afaf da cewa "what? Wai da gaske ake maganar virus d'in dama?" Afaf tace "It's been almost 1 month fa and half yanzun da fara maganar ma,kawai dai bai yi k'arfi ba sai cikin week d'in nan" hurriedly Nusrah ta juya tana kallon inda yake,yadda ta barshi a haka yake yana zaune sai murmushi yake zubawa because shi ya san dama babu inda za suje cikin lokacin tunda aka fara rufe stations sai anga yadda hali yayi tukun.

A sad'ad'e tayi shiru bata ce komai ba har suka gama waya da Afaf ta kira su Kalthom suka sha hira,sai da ta bari ta gama komai,ta kalleshi ta b'alla masa harara because ta fahimci murmushin da yake yi mata then ta wuce bathroom,sarai ya ganta ya ga abunda tayi but sai bai yi mata magana ba ya ci gaba da murmusawa abunsa yana clicking computer,Nusrah kam tana shiga bathroom wurin first aid drawer d'insu ta wuce,dama ta bayar an siya mata abun gwajin ciki,tayi murmushi ta cire guda,ta fara yin fitsari bayan ta saka kan tsinken ta ajiye ta wuce ta cire kayanta,bayan ta gama wankan,she tied a towel and went to the place where she put the thing,idanunta suna sauka kai taga it marked two lines,ai bata san lokacin data fasa k'arar murna ta fara tsalle ba,Nuraz yana zaune yaji ihunta da sauri ya ajiye computer ya nufi hanyar bathroom yana kwala kiran "Roohii! What happened? Open the door please!" yadda ta jiyosa yana magana yasa ta d'an nutsu but continue to dance in the bathroom,yana tsaye bakin bathroom d'in rik'e da handle jin shiru bata zo ba yace "Open the door i said" murmushi ta saki tana yarfe hannu da d'an tsalle,then ta k'arasa jikin k'ofar ta bud'e,a rikice ya rik'ota yana lek'en cikin bathroom d'in yana fad'in "ihun na mene ne kike yi?" Murmushi tayi tana kallonsa sai ta sake fasa k'ara ta k'ank'amesa tana fad'in "I'm pregnant Hayat!" Wani irin zaro ido yayi na surprise sai kuma ya d'agata suka fara juyi a gurin in a state of ecstasy,sai da suka d'auki lokaci suna murna ya tuna ya sauketa yana kallon idanunta yace "ya akayi kika tabbatar?" Bakinta ya k'i rufuwa sam ta nuna masa stripes d'in tana cewa "I did the test" wani wawan runguma ya sake yi mata,a guje ya sureta yayi sama da ita,bai direta ko ina ba sai saman bed yana cewa "woah! Yarinya Allah ya kaman min ke,dama tunda kika yi musu yau zanyi shagali" wani zaro ido ta fara yi sai kuma ta had'e rai ta fara k'ok'arin sauka daga bed d'in tana cewa "Ni wallahi babu wani abun da zaka min" murmushi ya saki da sauri ya rik'o waist d'inta ya had'a jikinsu,yana kallon fuskarta da tayi kicin² yace "Didn't i tell u not to make a hasty decision?" Ta sake had'e rai tace "tou ni ina ruwana? Do i have anything to do with u?" Yace "ba ruwa ba har river nile ma kina da shi in dai da ni ne" ta hararesa ta murgud'a baki tace "Let me go na shirya,gurin Mom ma zanje naga baby na,tunda ita ta yi min yaji" yayi dariya yana d'ora hannunsa a wuyanta d'ayan kuma ya saka cikin towel d'inta yana feeling yace "O'ohhh! Kin sauke fushin da kike yi ne madam?" Ta tab'e baki tace "tou ni ya zanyi idan ban daina ba? Bayan a kanta ma sai da kasa naji duk na rasa k'warin jikina" yayi murmushi,bai ce komai ba yana kallonta ya d'aga ta,a hankali ta sauke hannayenta a wuyansa tana kallonsa yayi mata murmushi yana lumshe idanunsa yace "thank u" tayi dariya kafin tayi magana ya wuce da ita gaban mirror. Shi ya shirya ta tsaf in a royal blue na wani summer women wide leg rompers cotton linen backless jumpsuits ya kawo turban cap yasa mata,lips d'inta sun sha red chapstick,yadda tayi masifar kyau a cikin kayan shi kansa sai da ya sake yana kallonta,tayi juyi a gabansa tayi fari da idanu tana d'aga masa gira tace "ya ka gani?" Yayi ajiyar zuciya yana rungume ta tsam a jikinsa cikin kunnenta da wani munafukin voice yace "U're so beautiful,i love u" ta k'ifta idanunta tana sakin sirrintaccen murmushinta ta rik'o hannunsa da sauri tace "love u too,muje tou naga Babynah" yayi murmushi daga haka ya rik'ota zuwa gefen jikinsa suka fice daga apartment d'in.


Suna shigowa flat d'in suka tarar da Maysam sai cilli take da throw pillows tana ihu da dariya,Nusrah ta bud'a ido tana kallon y'arta da babu abunda yake damunta sai wasanni take abunta,Nuraz yayi murmushi yana sake mak'ale ta a jikinsa yace "kin gani ba,i told u dama bata tare da ko wane irin damuwa" tab'e baki tayi ta d'auke kai daga kallon Maysam tace "Mmm! Ai shi kenan tunda zan haifo wani baby'n soon,sai Mom su rik'e Maysam mu kuma mu d'auki new one" murmushi ya saki mai sauti yace "No! Ni bazan iya barinta ba,sai dai su karb'i sabon,kin san ko hausawa ma cewa suke da tsohuwar zuma ake magani" tace "if it's not available dole ayi da sabo ai" suka yi dariya a tare,Lolly ta taho hannunta rik'e da bowl tana fad'in "HABIBTIY! Where are u?" Da gudu Maysam ta sauka kan chair da take tsalle² ta b'oye bayan kujera tana lek'en hanyar da Lolly take tahowa,Lolly ta k'araso tana dubawa bata ganta ba,ta waiwaya a hankali suka had'a ido da Nusrah dake murmushi tana satan kallon inda Maysam ta b'uya,Lolly tayi dariya tace "yaushe kuka shigo min ku kuma?" Nuraz dake kallonta yace "Mom yanzun muka zo,where is my Dad?" Hannu ta watsa cike da zolaya alamun bata sani ba,za tayi magana da gudu Maysam ta fito tana ihun "Mami oyoyo!" Nusrah tayi dariya ta bud'ewa Maysam hannu ta shige jikinta tana dariya,Lolly ta bud'e ido tace "shi kenan na kamata" Maysam ta bata fuska while su duka suna yi mata dariya,cikin surutunta da zak'in murya tace "ni baci kama ni ba" suna yi mata dariyar yadda take rufe ido tana surutu Mr Rafeek ya fito daga bedroom,da suka zauna bayan sun gaisar da iyayen nan suka fara hira,yanayin yadda suke yi da irin shakuwar dake tsakaninsu idan ba wanda ya sani ba sai ya rantse Nusrah is not their daughter-in-law,they all set wani kunyar surukai aside,su a garesu kallon y'a suke mata,Mr Rafeek dake zaune yana kallon iyalinsa dake cikin farin ciki yayi wani lafiyayyen murmushi,Lolly dake zaune next to him tana kallonsa tace "lafiya dai Yallab'ai kake murmushi?" Ya sake yin murmushi yana kallon cikin idanunta cike da shauk'i yace "I just remember something about our past life" a 360 Lolly ta had'e rai tace "za ka fara kou?" Yace "Just as we can't change what has happened,i just can't stop talking about what i have done to u dear,ni kaina na san ban kyauta ba,and that's why har yanzun nake jin haushin kaina da fifita karatun boko akan addini na" ta tab'e baki ita dai bata ce komai ba,ya kalleta yayi murmushi yace "kin san wani abu kuma?" Tayi jim tana kallonsa tak'i cewa komai,ya sake yin murmushinsa mai kyau yace "kin tab'a tunanin wani abu game da abubuwan da suka faru da muka dawo UK? I mean before then and after? Shin kinyi tunanin abunda ya faru lokacin da kuke shirin tafiya ku barmu a airport?" Lolly dai ta zuba masa ido sai kallonsa take yi but ta kasa magana,yana yi mata wani irin murmushi yace "Everything that had happened long time ago,daga ranar da na fara ganin ku a bakin Ali Jericho store,har zuwa komai da ya faru tsakaninmu was all planned,except rashin lafiyan da nayi lokacin and Clark shi ne manager shi ya tsara komai" mamaki ne ya cika Lolly tana yi masa wani irin kallo tace "plan fa kace?" Ya gyad'a kai yana yi mata murmushi then ya fara bada labarin a nutse "Sure! Duk abunda ya faru was just a planned,taron y'an jaridun da suka zagaye mu and everything har zuwanmu gida tare all shirinsa ne" ba ita kad'ai ta ji mamakin maganarsa ba hatta su Nusrah duk sai suka mayar da hankalinsu kansa suna sauraren ya warware musu yadda al'amarin ya faru,here he began to explain "If u haven't forgotten,lokacin da muka fara had'uwa da ku was at Albert street kun fito daga store,sure a wannan lokacin da na ganki na shiga rud'ani da taraddadin anya kece da gaske ko kuma dai idanuna suke yaudarata? But before i can regain my composure har kun b'acewa ganina neman duniya babu ku a wajen,na shiga tashin hankali sosai da na duba ban ganki ba,because da jimawa na je Nigeria neman ku saboda na nemi afuwar laifin da nayi miki,sannan na tabbatar miki a shirye nake na karb'i yaro na sannan na dawo dake gare ni,but sai dai mun rasa inda kuke,we had a hard time in finding u,mun d'auki tsayin lokaci muna jiran samun labarin ko wanda ya tab'a ganin ku but we lost,daga nan bayan lokaci na dawo UK na bar komai a hannun Baba da Yaya Abdullahi,sai idan na samu aiki yayi min sauk'i nake zuwa na duba halin da ake ciki,a haka lokaci yayi ta wucewa babu wani feedback,cikin haka kwatsam Allah ya karb'i rayuwar Abbanah,bayan rasuwarsa still bamu hak'ura ba muna kan neman ku amma kullum shiru babu wani labari har d'auki tsayin shekaru.. Ranar da Allah yayi nufin za mu had'u na ganku a bakin Ali Jericho bayan na dawo cikin nutsuwata i just started to check where ur car had gone,but surprisingly ko k'urar inda motar yabi bamu gani ba,a nan na ji damuwata ya dawo sabo because i didn't even know zan sake ganin ki ko shi kenan kin sake b'acewa?" Yana kallon yaransa da ita kanta Lollyn da tayi shiru ta zuba masa idanunta yace "Do u know of any surprise? At this point da nake tunanin i just lost all the opportunities and hope,Clark was the first person to suggest mu duba CCTV footage na Ali Jericho,time d'in da sam tunanin yin hakan bai wani zo min a kai ba,but na amsa kawai saboda kada na bashi kunya,mun shiga cikin store yayi magana da manager,a nan shi da kansa ya shigar da mu control room and gathered all the operators suka fara bibiyar footage na hours back,tun daga farkon zuwan ku har k'arshe lokacin da kuka fita baby tana rik'e da ke duk mun gani,what we wanted to get a time d'in is ur cab number but unfortunately camera's basa d'aukan hoton wajen,jiki na ya sake yin sanyi na fara tunanin ina ne zan sake ganinki kuma? At the time because of the stress i was going through ciwo na ya dawo sabo,while a gefe d'aya kuma tun daga ranar kullum sai munje Albert street cike da saka rai akan za mu sake ganinku,it took us long har ya kasance ko ba na k'asar akwai security da suke zuwa su duba ko Allah zai sa a gano inda kuke,wata rana cikin irin lokacin da nake gari a lokacin mun fita bakin store na Ali Jericho haka kawai sai na tsinci kaina da son yin tafiyar k'afa,a hankali na bar securities d'ina a wajen because ba na son a dame ni,na fara tafiya zuciyana a raunane ina tunanin idan ban same ku ba mene ne zai faru? Ban san daga ina ko yaya aka yi ba sai naji na buge da wani abu,na tafi zan fad'i because i was not feeling strong naji an rik'e ni,ina d'agowa muka yi ido hud'u da Noor nan take gabana ya fad'i,at first glance da na yiwa fuskarsa nayi realizing lallai duk inda ya fito we had a strong connection,immediately kuma sai kalaman Hajiyata suka shiga dawo min,for 28 years i never thought about it but at the same time they came into my head as if she was saying it right away,abu na farko da ya dakatar da ni lokacin shi ne irin kallon da Noor yayi min,nan da nan naji wani irin abu yana shiga raina da jikina,i was very scared and afraid of how to explain wane ne ni da matsayina a gurinsa,haka ya wuce ya bar wajen but ban bari ya b'ace ba kamar yadda kika yi,nasa aka bi bayansa,tun daga ranar sai naji na fara samun sauk'in damuwata,while a gefe d'aya nasa ana bibiyarsa but babu wani gamsashen bayani,wata rana again time d'in ina zaune ina kallon program a BBC,all of a sudden sai ga Noor ya sake bayyana,so it was there na samu duk amsoshin da nake nema game da shi,but the fear of how to deal with the problem is what really stops me every time i intended to approach u,wannan tsoron da Clark ya fahimta a tare da ni da fahimtar gaskiyar al'amarin da yake tsakaninmu,ya same ni da batun and informs me he has a plan to make if na bashi dama,ni kuma lokacin da yake ba wani ganewa nake yi sosai ba kullum ina cikin damuwa da ciwo na amsa masa,tun daga ranar he continue to run his plan without my knowledge,batun Noor kuma tun ranar da ya gane suna binsa na dakatar da Clark from his follow-up,abubuwan da suka faru in the past na san kun sani,though zuwan mu Nigeria na san kun yi mamaki a lokacin da muka had'u,but shima dai ba wani abu ne na musamman ba,because tun a ranar da kuka bar k'asar da muka je gidan da kuke zama muka samu labarin babu jimawa jirginku ya bar k'asar,da muka samu labarin Nigeria za ku tafi here na yi deciding mu biku can d'in,daga nan muka koma gida muka yi sallama da Hajiyata tayi min addu'ah... Sai ga shi zuwan ya zama wani babban nasara a tare da ni,i didn't think of any problems zai faru tsakaninmu until we got back to UK,lokacin da kuke k'ok'arin barin airport hankalina ya tashi na kasa tunanin komai,here Clark said he knew what he was going to do,so a nan dai yayi magana da y'an jarida,ba'a d'auki lokaci ba saboda dama kullum cikin jiran kad'an suke sai ga su kamar kuraye sun zagaye mu suna neman labari.. I was very happy with the idea of Clark because i didn't think it would work,but damar da na bashi ya janyo min nasara,har abunda ya faru ya so zarta tunani na,wannan ya sake ba ni damar amincewa da Clark,a dalilinsa yau gashi ina rayuwa cikin farin ciki da nutsuwar da ciwon da nake tare da shi,ake tunanin nan da wani lokaci zan iya rasa rayuta yayi sauk'i sosai,even the doctors themselves wondered what was the cause of this healing process?" Ajiyar numfashi Lolly tayi tana tab'e baki tace "Mmm! You tried so hard" Nusrah ta fara dariya saboda yadda taga Lolly tana magana,cike da tsokana tana kallon Nuraz tace "but Daddy Hayat fa is more stubborn,babu ruwan Mom dama" Nuraz ya zaro ido yana had'e rai yace "Ke! Ki shiga hankalinki kafin na b'ata miki rai yanzun" ta hararesa ta murgud'a baki tace "ai gaskiya na fad'a" ya gyad'a kai yana harararta yace "za kiyi baya ni,ai zan kama ki" Mr Rafeek yayi dariya yana shafa kan Nuraz yace "No beta just be patient,ni na san babu ruwanka kai mai hak'uri ne" Nusrah ta bud'e baki da sauri tace "Laah! Daddy ba shi da wani hak'uri" yayi saurin kallonta yana had'e rai zai yi magana su duka suka fashe masa da dariya,Nusrah tayi masa gwalo tana dariya,ya kad'a kai bai sake cewa komai ba,mintuna kad'an Angelyn ta fito daga kitchen tana tura trolley za ta shigo wajen su aroma na grilled fish da yaji decoration yana turiri ya bugi hancin Nusrah,hurriedly ta mik'e tana rufe baki saboda wani irin tashin da zuciyarta ya fara,she made her way to their bedroom dake cikin apartment d'in a guje,Nuraz ya mik'e ya biyo bayanta da sauri yana tambayarta abunda yake faruwa,bata tsaya ba shi amsa ba ta wuce bathroom and started throwing up,ya tsaya a bayanta ya rik'eta yana shafa bayanta har ta gama,ya wanke mata baki yana kallonta yana jera mata sannu,ta lumshe ido a hankali tana jin jikinta yayi mata wani iri,ya kalli yadda tayi luf a jikinsa yace "ina yake miki ciwo?" Ta girgiza masa kai a hankali muryarta yayi sanyi tace "babu ko ina,sai rashin k'arfin da nake ji kad'ai" yace "sannu,let's just go and have some rest,ko da abunda kike buk'ata kuma?" D'an murmushi tayi masa tana lumshe idanu da bud'ewa tace "bacci kad'ai zanyi,shi nake ji,sai grape's da nake jin son sha" yayi murmushi yace "alright! Muje ki kwanta za'a kawo yanzun,u know i have party tonight" ya k'are maganar yana yi mata murmushin tsokana,saurin kallonsa tayi tace "wane shagali kuma? Ni fa ba ni ma da lafiya" yace "za kiji sauki ai,muje ki huta kafin dare za ki koma normal" kamar za tayi kuka ta bishi da kallo tana fad'in "I can't" yana jin ta ce haka ya fara murmushi yace "za ki iya baby,u're strong ai" bubbuga k'afa ta fara yi a k'asa tana cewa "Allah bazan iya ba" da sauri ya d'auke ta ya wuce yana cewa "I can see if u really can't" suna fitowa ya wuce hanyar bed,a 180 ta fara wuntsila k'afa tana cewa "dan Allah ka bari sai an jima,na yarda zan iya" yana jin ta fad'i haka bai san lokacin da yayi murmushi ba,a hankali ya nufo lips d'inta ya fara sucking,suka yi ajiyar zuciya tare,ya kalleta kad'an yana shagwab'ewa yace "baby nayi yanzun?" Wani irin zaro ido tayi tace "A'a kuma a nan za kayi?" Ya d'aga kai yace "da nan da gidan mu duk d'aya ne" tayi saurin girgiza kai tace "A'a ka bari idan mun koma,haka kawai kasa min ihu,kai da baka iya samun abu kayi shiru ba,salon ka kunyata ni irin na lokacin da na haifi Maysam" wani dariya yayi da bata tab'a ganin yayi irinsa ba yana kallonta da narkakkun idanunsa duk ya mak'aleta yace "sauk'in abun ma ba ni kad'ai nake yin haka ba,wata idan dad'in yayi mata yawa har cewa take,idan baka yi ba zan mu..t..uu..!" Ya k'arasa furucin a rabe,wani irin kallo tayi masa tana had'e rai tace "Allah ni babu abunda nake cewa,sharri kake yi min" murmushi yayi yana dungure mata kai yace "Yan! Yan!! Yan!!! Shut up my friend,who do u think will agree?" Ta hararesa tace "kai zan fad'awa ka yarda" ya zaro ido da sauri yana fad'in "Ehhh! Lallai yarinyar nan na kula tunda kika gama ganin girma na raini ya shiga tsakanin mu,but i have to get rid of this contempt today" yana fad'a bai jira ba ya fara aika mata some hot messages that would make her lose her composure,da sauri tana fizgar numfashinta da kyar ta rik'osa tace "please Hayat kar kayi min haka,ka bari mu tafi" shi kam ba wani ganewa yake yi sosai ba lokacin yana sakin wani moan na fita daga nutsuwa yace

Please Login or Register in order to submit comment