Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fad'awa yazo ya sanarmin halin da take ciki,,bayan kwana biyu da faruwar al'amarin Hajiyar su Maimunatu ta kula da rashin zuwanta tasa Maimunatun ta shiga ta duba ko lafiya bata ganinta cikin kwanakin.? Bayan zuwan tan suka d'an keb'e a d'aki duk dama an samu su ido,a hakan tayi iya kar k'ok'arinta cikin bada sallahun azo a fad'a min halin da take ciki ko Allah zaisa na rok'i Baba ya kyaleta taci gaba da zuwa makarantar,ta kwashe duk abunda yake damunta ta zayyanawa Maimunatu,tana kuka Maimunatun na taya ta har ta gama bata labarin abunda ya faru,Maimunatu tayi mata alk'awarin in sha Allah zata yi duk k'ok'arin da zata iya ta zo ta sanar min,Hauwa tayi mata godiya suka fito tare,da ta rakota bakin k'ofa suka sake tsayawa a nan suna ci gaba da y'an maganganunsu,kafin suyi sallama aka samu wani cikin y'an gidanmu ya kaiwa baba gulmar ga Hauwa can ta fita,babu b'ata lokaci Baba ya zo ya iske su zaure suna magana,nan d'in ma bai tsaya bin ba'asi ba ya korata gida bayan ya sauke mata kyawawan rankwashi masu shiga jiki,Maimunatu na kallon yadda take kuka,ta fice tayi gidansu da yanayin damuwa,,bayan komawarta gida bata iya fad'awa kowa ba har Hajiya data aikata,kuma ko da ta dawo ta tambayeta ce mata tayi tana lafiya daga haka bata sake cewa komai ba,,yanayin rayuwar gidansu Maimunatu rayuwa ce da suke yinta a sauk'ak'e,yanayin mu'amalar su da zaman takewarsu sun kasance suna gudanar da rayuwar su tamkar abokai tsakanin iyayen da y'ay'an,idan suna tattare da damuwa iyayen suna jansu a jiki su ji damuwarsu,itama Hajiya mahaifiyar sun a lokacin data kula da yanayin da Maimunatun ta shiga cikin kwanakin,haka ta sata gaba da tambayar lafiya take ganinta cikin damuwa.? Tana ta tambayarta da damuwa a fuskarta,tana lallab'ata saboda tana so ta sake sosai sannan taji mene ne ya kawo sauyin da aka samu,zuwa lokacin kasancewar damuwa tayi mata yawa sai bata sake b'oyewa mahaifiyartan ba ta zayyana mata komai da yake faruwa da Hauwa,,Hajiya ta shiga damuwa ta rarrashi Maimunatu sai da ta kwantar mata da hankali,and ta bata albishir idan Alhaji ya dawo zata san yadda tayi aka nemawa Hauwa'r sassauci,cos tana ganin lallai rayuwarta a cikin gidan akwai hatsari,sannan su da suka sani baya daga cikin hak'k'in mak'otaka kana ganin b'arna tana faruwa ka rufe baki ka zuba ido,dole tana bukatar inda zata zauna ba tare da tsangwama ko takurawa ba,ya dace ace itama ta zauna ne kamar ko wane d'a da yake k'ark'ashin iyayensa cikin y'anci,,sun gama maganar a ranan bayan Abba'nsu ya dawo tayi masa bayanin abunda ta ji daga bakin Maimunatun,shi kansa yayi mamaki sosai ace irin haka tana faruwa,abunda ya sanarwa Hajiya shi ne bai san yaya zai yi ya iya taimakawa ba,Hajiya ta kawo shawaran ya nemi mahaifin Hauwa suyi magana,idan ya fahimce shi,shi kenan ta san zai sassautawa yarinyar kuma rayuwarta zata samu salama,kwanaki biyu tsakani Alhaji zakar ya samu Babanmu a k'ofar gida,bayan sun gaisa cikin mutunci kamar yadda aka saba Abba'nsu Maimunatu yana kallon Baba yace
"Malam Baba! Gurinka na zo,wata y'ar magana nake so muyi da kai,yau kwana biyu kenan ina sa rai da ganinka Allah bai nufa zamu had'u ba sai yanzun,ina fatan ba zaka damu da abunda zaka ji daga gare ni ba.."
Baba yana kallonsa da mamaki,murmushi kwance saman fuskarsa yace
"Toh! Alhaji Allah yasa muji alkhairi"
Alhaji zakar ya kalleshi da murmushi shima a fuskar sa yace
"In sha Allah ma alkhairi ce."
Gyara zama Baba yayi yace "Toh Alhaji ina saurarenka,wace irin magana ce wannan d'in.?"
Sai da Alhaji zakar yayi ajiyar zuciya ya san tabbas maganar da zai yiwa Baba,idan har bai masa kyakykyawar fahimta ba zasu iya samun sab'ani,haka kuma idan yayi shiru yaci gaba da zuba ido yasan lallai rayuwar marainiyar zata sake shiga wani halin,to amma da yake yayi nufin aikin alkhairi ne har zuciyarsa shi yasa sai ya daure yace
"Dama Malam baba magana ce nazo da ita nake son mu tattauna,Allah yasa zaka fahimce ni,dan ba akan komai nazo muyi magana da kai ba sai akan gidanka."

Baba yana kallonsa yace "Akan gida na..?"

Alhaji yace "K'warai kuwa,akan gidanka."
Baba yana binsa da wani irin kallon mamaki da rashin yarda ya sake daurewa yace
"Toh ina jinka.."
Alhaji zakar yana kallon Baba ya fara zayyana masa duk abubuwan dake faruwa a gidansa,da mugun mamakin yadda akayi ya sani Baba yake ta kallonsa,har ya gama magana Baba bai ce masa komai ba,Alhaji zakar yayi shiru yana ta kallon baba yaji ko zai yi magana amma yaji shiru,dole tasa shi tambayar baba
"Malam Baba baka ce komai ba..?"

Baba dai yana kallonsa har lokacin da kyar ya bud'e baki cikin kaushin kalami yace "toh Alhaji me zance.?? Tunda Allah yasa munafukai sun fara sawa gidana ido,har sun fara yawo suna yamad'id'i da ni a gari,da tona asirin gidana.. Zance ya lalace tunda har al'amarin gida na ya shiga gari.."

"A'a Malam Baba kada kace haka,wannan magana sam baka fahimci yadda take ba,,ni dai ka sanni kuma kasan ba mai shiga harkokin da ba'a sani bane,amma tunda kaga na tsayar da kai nayi maka magana kasan ba zai wuce na hango maka damuwa bane a cikin gidanka na sanar da kai. Toh amma tunda har Allah yasa magana ta batai maka ba,Allah ya huci zuciyarka kuma ya baka hak'uri idan har na b'ata maka rai.."
Ajiyar zuciya Baba yayi yace "ai Alhaji wannan batun tunda kazo da shi na san bazai wuce tsaigumi aka kai maka ba,kuma kaima ga shi ka tabbatar min,amma tunda haka abun yake,kafin a fara zagina akan maganar yarinyar nan,dole ne tunda yake nine mahaifinta na zartar da hukuncina akanta ta yadda babu wanda zai sake zuwa min da magana makamanciyar wannan,,zan aurar da ita kowa sai ya huta,da ta d'auko min maganar da zata fi k'arfi na gara na zartar da hukuncin da zan kashe bakin mutane.."

Alhaji yana kallon Baba da mamaki yace "Malam Baba aure kace.?" Baba yace "Haka nace",cikin muryar rarrashi Alhaji zakar yace "kada kayi haka malam Baba,yarinyar nan duka nawa take da zaka ce zaka aurar da ita.? Ko a k'auye yanzun tuni an waye an daina irin wannan auren,bare mu da muke cikin birni,,ya kamata kayi tunani dai kafin ka zartar da hukuncin da zai iya kaika ga yin dana sani a gaba."

"Alhaji ina ganin wannan hukuncin shi ne dai²,tunda har Allah yasa ka fad'i sak'on da ya kawo ka,kana iya tafiya na gode.."
Alhaji yaci gaba da kallon Baba da mamaki "Amma malam Baba ban tab'a tsammanin haka daga gareka ba,wannan al'amari idan har ka tsaya ka nazarce shi da kyau,na tabbata zaka gane gaskiyar da nake son ka fahimta."

"Alhaji maganar fahimta ya k'are,tunda har ka fad'i sak'on daya kawo ka,yanzun naka ido ne,,abunda nake fad'a maka a yanzun shi ne batun auren Hauwa na gama yanke hukunci,in sha Allah cikin satin nan zan d'aura mata aure,da ma hak'k'i na ne na aurar da ita ga wanda yayi min,yadda nayi niyya haka zanyi aure babu fashi.."
Cikin takaici Alhaji zakar yaci gaba da kallon Baba but bai sake ce masa komai ba ya mik'e da niyyar barin gurin tunda al'amarin yafi k'arfinsa,ya yiwa Baba sallama yana niyyar shiga gida,Baba dake zaune har lokacin yana kallonsa cikin d'aga murya kamar wanda aka bawa umarnin yin magana yace
"Yawwa Alhaji ina da wata y'ar maganar nima."
Waiwayowa Alhaji zakar yayi yana kallon Baba duk da yaji haushinsa amma haka nan daga inda yake tsaye yace "fad'i maganarka ina sauraronka."
Shima Baba daga nan inda yake yace "Yawwa! Dama ina so ne na baka cigiya tunda har Allah yasa nace zan aurar da ita,ba tare da samun tsayyaye ba shi ne nake son shaida maka,ko da Allah zai sa ka samu wani mai rangwamen gata kamar ta da yake buk'atar auren,dan Allah ina rok'on alfarma ka sanar masa yazo gida na ina da matar da zan bashi sadaka.."
Cike da takaici Alhaji zakar ya bi Baba da kallon sakarci ba tare da ya ce komai ba ya juya zai shiga gida,baba yaga yayi masa magana bai tanka ba hakan tasa shi sake cewa
"Yawwa Alhaji,,nace tunda yake Allah yasa har kana ganin tayi k'arama da aure yanzun,kuma kai d'in kana da ma'aikata a gidanka,shin mai zai hana ko su ne ka nemawa d'aya daga cikinsu aurenta tunda kana tausayinta tayi k'arama da aure.. Ka ga dama jihadi kake son yi.. Shi ne sai naga zaifi kyau na sanar da kai,sadaki ma kad'ai idan ka biya ya wadatar a d'aura musu aure,daga nan sai ka ajiyeta a gidanka,kaci gaba da kulawa da ita ko itama ka bata aiki a gidan naka,tunda yake ni mahaifinta na yi ba dai² ba.."
Maganar ta yiwa Alhaji zakar zafi,still bai tanka ba ya wuce gida ransa a b'ace har yaji nadamar samun Baba da maganar,shigarsa gida a cikin wannan yanayin suka yi maganar da Hajiya,yadda suka yi duka da baba ya sanar da ita tunda ita ta sashi shiga maganar tun farko,,Hajiya ta lallab'a ta kwantar masa hankali,followed by maganar ta akan me zai hana tunda har Allah yasa al'amarin ya zo da haka kuma Baba da kansa ya bashi damar neman auren yarinyar ga hadiman gidansa,su nunawa masa cewa maganar da yayi cikin izgili a shirye suke su tabbatar da cikarta..??,Alhaji ya zuba mata ido yana kallo cikin rashin fahimta but yayi k'ok'arin yin magana
"Hajiya me kike son cewa..?"

Tace "so nake ka amince da batun neman auren yarinyar."

Yace "Hajiya wane irin batu kike yi haka.? Ni zan nemi auren k'aramar yarinya kamar wannan,sa'ar y'ata fa.?? Ita kike cewa na nemi aurenta..?? Yarinya y'ar shekara sha hud'u.? "

Tace "Alhaji nifa ba kai nake nufi ba."

Yace "to waye zan nemawa aurenta.? Kin san dai bani da ikon zartar da ko wane irin hukunci akan ma'aikatan gidan nan cos bani ke da su ba,mu kuma ba wani babban d'a namiji gare mu ba bayan Rafeek,idan munce shi,duka shekarunsa nawa suke.? Besides yanzun yake shekara ta biyu a jami'a."
Hajiya tace "ni dai alhaji kawai kayi hak'uri da batun shekarunsa,wannan al'amari ne da ya kamata ace munyi iya kar k'ok'arin mu wajen ganin mun taimakawa marainiyar nan,ina tausayin rayuwar yarinyar nan har zuciya ta,kallonta nake kamar Maimunatu na,idan a yanzun da muke da dama bamu taimaka mata ba,mu yaya zamu yi a gaba..?? Kada fa ka manta taimakon maraya abune mai kyau,kamar yadda annabi (S.A.W) yace a hadisi:"Ni da mai taimakon maraya,zamu kasance kamar haka ✌🏻a gidan aljannah,sai ya raba tsakaninsu da wani abu,maleek (R.A) yayi nuni da yatsunsa biyu manuni da na tsakiya,,idan ka duba duka nima bawai ina dagewa bane akan lallai sai munyi hakan zai nuna kulawarmu gare ta ba,sai dan ina ganin yin hakan shi ne zaifi bamu damar taimaka mata ba tare da anyi zarginmu ba,ni ina yi mana kwad'ayin matsayin ne kawai,wannan ne yasa nake sake tunatar da kai,,shin a lokacin da wani namu yake neman taimako mu baza mu nemi taimakon wasu bane..? Ya kamata ka duba maganata da kyau,tamkar jihadi ne zamu yi idan har munyi nasara..!"
Alhaji zakar yayi shiru bai ce komai ba tsayin lokaci yana nazarin maganarta,Hajiya ta sake yin amfani da wannan damar ta dunga kawo masa hujjoji da dalilan da take ganin idan har sun taimaki Hauwa zasu samu lada har gurin Allah,,hankalin hajiya bai kwanta ba,sai data tabbatar Alhaji ya amince zai nemawa Rafeek auren Hauwa.. Wannan shi ne mafarin lamari,ina nufin mafarin matsalolin rayuwar Hauwa da mu kanmu.....




#Share.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*      

                   *'DAN MACE..*
              (Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥

  
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*    
https://my.w.tt/29u2S26SG2

     *The gift u gave me was more than perfect in each and every way..Thank u so much for it Cweet Mammah (Manab). I will always preserve and keep it with me forever.*

Pᴀɢᴇ 5.
#Tᴜʀᴍᴏɪʟ

    Bayan Alhaji zakar ya gama yanke hukunci,shawaran samun Baba yayi a washe garin ranar da nufin ya sanar da shi ya amince da maganar,but da nufin nemawa Rafeek auren Hauwa zai je kamar yadda Babanmu ya buk'ata,kamar wancan lokacin suka had'u a k'ofar gida,Alhaji zakar ya rattabawa Baba buk'atarsa,a nan Baba ya fututtuke fuska gani yake kamar cin fuska ya kawo Alhaji zakar,bud'ar bakin Baba a take yace
   "Haba Alhaji,,kada ka mai dani wani shawaragi mana,banda kai ko k'aramin yaro na koma ai kasan babu yadda za'ayi na yarda da cewa kamar kai zaka amince ka nemawa dank'a auren y'ar wajena.. Sai dai kuma ban sani ba ko ka zo ne ka zolaye ni kaji an samu wanda ya taya,amma ba kai da kanka kace ka zo nemawa dank'a aurenta ba,,ina laifinma kace mai gadin ka ko y'an aiken gidanka..? Wannan kam ina iya yarda kuma na amincewa da kai."
   Alhaji zakar yayi dariya da yake ya san iya gaskiyarsa ya fad'a yace "ko kad'an malam Baba ban zo da nufin na zolaye ka ba,,alal hak'ik'a kamar yadda ka ji na fad'a maka babu batun wasa a magana ta,wannan itace gaskiyar zuciyata kuma ita na fad'a maka,ko ka yarda ko kada ka yarda ni na san ban zo da nufin na yaudare ka ko na cutar da kai ba,kada ka manta tun farko kai ka bani dama kuma naga na yaba da tarbiyyar yarinyar ka,ina da buk'atar amfani da wannan damar daka bani,shi yasa na zo gare ka da batun,idan ka amince kamar yadda ka fad'a ranar jumu'ah idan Allah ya kaimu sai a d'aura auren,dama kace a cikin satin nan ka shirya aurar da ita ko ba haka ba.??"
   Baba yace "haka nace,,amma batun kana neman aurenta wa dank'a na fasa,ni da kaina zan nemo wanda ya dace da ita na aura masa."
   Alhaji ya sake yin dariya yana kallon Baba daya fututtuke fuska yace "amma malam Baba kasan ba haka muka yi da kai ba tun farko ko.?"
    Baba yace "to yaya muka yi..?? Ina ce nina baka dama tun farkon.. Yanzun kuma naga hakan bai minba na canja.!?"

      Alhaji yace "haka ne kai ka bada dama,nima da naga ina buk'ata nazo da k'ok'on barata,kayi hak'uri ka yarda,kaga zumuncinmu ya sake k'arfi ko ba haka ba.?"
   Baba dai yaga kamar Alhaji zakar na neman maida lamarin wasa duk da shi har zuciyarsa yake maganar,tsam ya tashi ya bar masa gurin ba tare da ya samu damar ce masa komai ba,Alhaji har lokacin yana dariya saboda yadda Baba yayi fushi akan y'ar maganar shima ya tashi ya bar wajen,sai dai wannan karon ko daya tashi maimakon ya shiga gida,kai tsaye ya nufi gidan mai unguwa dan yafi son ace manyan unguwa su shiga cikin lamarin yarinyar ko da Baba ba zai bawa Rafeek aurenta kamar yadda ya fad'a ba,yana so aja hankalinsa ya fasa aurar da ita a wannan lokacin,,anyi sa'a Alhaji ya samu mai unguwa a gida,suka yi magana ta fahimta,ba'a d'auki lokaci mai tsayi ba mai unguwa ya aika d'an sak'o ya kira masa Baba,yaje aka sake maimaita zancen kamar yadda tun farko suka yi tsakaninsu shi da Alhaji zakar a gaban mai unguwa da y'an majalisar mai unguwa,jama'a suka shaida yadda akayi,mai unguwa ya bawa Baba hak'uri akan ya janye batun aurar da Hauwa a matsayinta na karamar yarinya saboda matsalolin da ake fuskanta game da aurar da k'ananun yara,sai dai fa Baba ya kafe yace shi bai ga dalilin da zai sa ya canja ra'ayi ba,duk yadda za'ayi anyi akan ya sakko amma ya kafe kamar lalataccen k'arfe,bisa dole mai unguwa da sauran yan majalisarsa suka hak'ura suka kyale shi bcos y'arsa ce kuma shi yake da iko da abarsa,yana da damar yayi duk abunda yaga yayi masa dai²,a nan ko da suka ga an ciza an busa bai amince ba Alhaji zakar ya sake gabato da buk'atarsa ta son amincewar Baba da batun nemawa Rafeek auren Hauwa'r idan ya amince,Baba yaga da gaske Alhaji zakar yake babu batun wasa,nan take ya amince,mai unguwa suka shiga cikin maganar aka tsaida ranar jumu'ah ta zama ranar d'aurin auren Hauwa da Rafeek.
     Anyi addu'o'i na neman sanyawar albarka kafin daga nan taron ya tashi,magulmata kuma suka samu na yi,aka tafi aka fara yad'a cewar Baba ya ga kud'i shi yasa ya amince ya bada y'arsa ga d'an Alhaji zakar ba tare da tunanin abunda zai faru gaba ba,,cikin k'ank'anin lokaci gari ya d'auka,duk inda ka zaga maganar auren ake,lungu da sak'o duk inda mutum baya tunani taje har ta wuce,,ranar jumu'ah bayan an sakko daga masallaci aka d'aura auren *Rafeek Zakar Labbo* da amaryarsa *Hauwa Baba Muhammad*,abisa mafi ingancin sadaki,d'aurin auren daya samu halartar manyan mutane daga b'angaren Alhaji zakar da Baba cikin har da manyan y'an siyasa na k'asa daya shiga ya fita ya gayyato duk da yake bai jima da fad'awa harkar bin y'an siyasar ba (kuji fa baba da k'arfin hali,mutumin da bai da wadataccen matsuguni shi ne ya fad'a siyasa).
   A dai² lokacin da ake ta hidimar d'aurin aure,a b'angaren ango babu wanda ya sanar da shi badak'alar da ake a gidansu,bcos baya garin yana Zaria da yake a can yake karatu (A.B.U),kuma lokacin bai jima da komawa ba,wannan dalilin yasa Alhaji yace kada a sanar masa shi da kansa zai masa bayanin komai idan an gama hidimar,da yake ma duka ba a lokacin zasu tare ba,yafi so sai Hauwa sun kammala secondary zuwa lokacin ta k'ara girma sai ayi biki,shima Rafeek zuwa lokacin ya kammala degree d'insa na farko,akan haka Alhaji zakar ya bar batun but yace duk lokacin da Rafeek yazo hutu zai had'a su duka ya sanar da su matsayinsu ga juna,,bayan an yi d'aurin aure a ranar at that night Alhaji yasa aka d'auko Hauwa da y'an kayanta daga gidanmu aka mayar da ita gidansa,a cewarsa wannan lokacin it was his greatest right to take care of her and all her other needs kasancewarta matar d'ansa,daga ita har d'an nasa kuma duka k'ark'ashinsa zasu ci gaba da zama zuwa sanda za su kammala karatunsu,matan daya aiko d'aukan amarya suka isar da sak'o,da aka sanar da Baba buk'atar Alhaji zakar yace a basu ita su tafi,bcos shima yana ganin tunda har Allah yasa ya aurar da ita all her right to nourish,watered,dress and lodge fall off his neck a yanzun komai nata ya koma wuyan mijinta,shi yasa ana fad'a masa sak'on Alhaji zakar babu musu ya sallamawa matan ita,at that day she cries as if her life depends on it saboda rashin mahaifiya ko wani da zaiyi d'awainiya da kai a irin wannan lokacin abune da yake tab'a zuciya,,duk wani nau'in gata da y'a take samu a yayin barinta gida babu abunda aka mata,daga gurin mahaifi har y'an uwa babu wanda yayi tunanin siya mata wani abun arziki da idan taje gidan aurenta zai amfane ta,a haka matan da suka zo tafiya da ita suka tattarata suka nufi gidan alhaji zakar.

   Zuwanta cikin gidan Alhaji zakar becomes such as the opening of a new page of life filled with light and peaceful,yadda Hajiya take kaffa² da kulawa da ita ta mayar da ita tsakaninta da Maimunatu babu bambanci,haka kowa na gidan ya d'auke ta,ma'aikatan gidan suna girmamata kamar yadda suke yiwa asalin masu gidan,Alhaji ya d'auketa tamkar y'ar cikinsa abunda zai yiwa Maimunatu haka yake yi mata,nutsuwa da kwanciyar hankali suka sake bak'untar ta,cikin lokaci kad'an tayi wani sauyawa na ban mamaki,kyaunta da nutsuwarta da suke b'oye suka sake bayyana.

    Rafeek ya dawo hutu Alhaji ya had'a su yayi musu nasiha sannan ya gabatar da Hauwa a matsayin matar daya zab'a masa,cike da nuna biyayya Rafeek ya nuna amincewarsa da zab'in da suka yi masa,cos dama shi bai cika shiga harkar mata ba,yayi godiya ga zab'in mahaifinsa tare da alk'awarin zai rik'e amanarsu kamar yadda suka shaida masa amanace gare shi,,tun daga lokacin da Rafeek ya san matsayin Hauwa a gurinsa bisa ga umarnin mahaifiyarsa ya kasance yana kyautata mata da janta a jiki sama da yadda suke wasa da dariya da Maimunatu kanwarsa,duk da a bayan kafin zuwan wannan lokacin idan ta ganshi tana gaisheshi da bashi girma a matsayin yayan k'awarta,daya bayyanar mata a matsayin mijin aurenta hakan bai sa ta canja daga yadda take ba,sai k'arawa ma da tayi,cikin hukuncin ubangiji a hankali tun bata sake da shi ba,yanayin mu'amalarsa da barkwancinsa yasa ta fara sakewa da shi,kafin a d'auki lokaci shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakaninsu,har ya kasance idan yana gari,ya zo hutu duk inda zata je shi yake mata rakiya,ya zame mata kamar wani bodyguard,mutanen unguwa kuma duk lokacin da suka gansu tare nan zaka ji yan gulamammaki suna ci gaba da yad'uwa,but da yake Rafeek ba mutum ne shi mai yawan magana akan abunda babu ruwansa baya tab'a kulawa.

     Alhaji ya maida Hauwa makaranta mai kyau tare da Maimunatu,aka ajiye su class d'aya,gurin zaman su da komai tare suke yinsa a gida ko a makaranta,their closeness to each other continued to grow as they were blood relatives before.

   Laying and rising is kinda loss of living,haka nan a wajen ubangiji shekara is like a day,su Hauwa sun gama secondary school bayan wucewar shekaru uku masu kyau,yayin da Rafeek ya kammala degree d'insa har ya nemi wucewa masters but ba'a Nigeria ya nema ba,ya nema ne a k'asar Ghana,though har zuwa lokacin basu tura masa sun bashi admission ba,Alhaji zakar yayi deciding tunda Allah yasa duk suna zaune a gida,mai zai hana ayi bikinsu,zuwa lokacin da can k'asar za su kirashi sai ya d'auki matarsa ko ya barta a nan gurinsu,da ace suna ta zaune basu san matsayin auren nasu ba,da ya sanar musu hukuncin daya zartar sun yi farin ciki sosai,bayan y'an kwanaki aka tashi hidima,Alhaji zakar ya yiwa Hauwa akwatunan lefe guda bakwai kowanne cike taf da kaya na gani a yaba,aka tsaida ranar biki sati guda,,anyi hidima sosai a bikin auren su,yadda ya kashe dukiya babu wanda ba zai yi tunanin y'ar cikinsa yake aurar wa ba,tsayin kwanaki uku akayi biki bisa al'ada da tsari aka gama,aka kai amarya gidanta dake nan a cikin unguwar K'ofar Na'isan itama,tsakanin mu duka babu nisa sosai,tun da muka rakata muka dawo ake ta labarin gidanta,yadda aka kashe mata dukiya a d'akunanta,ko wata y'ar gatan ba zata nuna mata komai ba,a haka dai aka baro amarya a gidanta cikin rufin asirin Allah,,,a kowane dare kamar yadda ko wane ango da amarya suke kasancewa bayan sun kad'aita,a tarihin aure da ma'aurata suma gare su haka ce ta faru tsakanin su,lokacin da komai ya lafa sun samu nutsuwa cike da k'aunar juna da nuna kulawarsu ga juna Rafeek ya lallab'ata tayi bacci,but a gurinsa shi kuma baccin ya k'i zuwa masa,saboda tsananin farin cikin daya tsinci kansa a ciki,a haka ya ga wayewar gari lafiya wacce ta kasance musu mafari.

    Kamar yadda na sanar da kai Rafeek ya nemi admission amma basu kirashi ba har time d'in,cikin hukuncin ubangiji duk kwanakin da aka d'iba a baya basu neme shi ba,sai ga shi kwatsam rana a sama,kimanin kwanaki uku da tarewarsu sun aiko masa sak'on sun bashi gurbin karatu,duk lokacin daya shirya daga nan zuwa sati guda yana iya tuntub'ar su,,a lokacin da Rafeek ya samu sak'on sai da yaji kamar yace ya fasa tafiyar dan yana ganin kamar zai cutu

Please Login or Register in order to submit comment