Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

knowing where they were going sai da suka shigo carport drivern ya gyara parking ya fita ya bud'e masa yaji yana fad'a masa sun iso,,ya d'ago zai yi magana ya gansu a cikin mansion,a fusace bakinsa har wani kyarma yake ya taune lips yana matse forehead d'insa,yana d'agowa ya kwashe shi da wani irin gigitaccen mari,cikin hayaniya yace "Here i insisted u to brought me.!?"

Baturen yana dafe da cheeks d'insa ya furta "Sorry sir"

Cikin hayaniya Rafeek yace "Ka ci ubanka kai da sorry d'in"

Duka maidservant dake harabar mansion d'in suka fara sauke kawunansu k'asa bcos sun san masifar sa babu wanda ba zata shafa ba musamman idan yaga wani yana kallonsa,a zafafe ya koma mota cikin masifa yace "bring me back to where u take me.. Quickly.!"
Saurin fad'awa mota drivern yayi yaja a 360,guard d'insa suka dafo musu baya,da mugun gudu suka d'auki hanyar komawa 9 Albert street,a bakin Store na Ali Jerich suka yi parking,tun kafin motar ta gama tsayawa Rafeek ya fice yana dube²,guards d'insa suka dafo masa baya suma suna tayasa duk da basu san mene ne actual abunda ya kawo su ba,ya koma dai² inda ya tsaya d'azun yana dubawa,yaga babu alamun su,a hankali ya lumshe idanunsa yana juya kansa kad'an²,Clark ya matso kusa da shi yace "Sir.!"
Da sauri ya bud'e rinannun idanunsa ya watsa masa wani irin kallo,a masife yace "Who told u to came.!?"

Clark yana raba ido yace "Sorry sir"

A masife Rafeek yace "Sorry for ur self."

Ya juya ya ci gaba da dubawa,almost 2 hours suna wajen mall d'in yana duba ta inda zai ganta but shiru,tun daga kan motocin dake parke a gefe har wad'anda suke wucewa amma ko mai kama da ita bai gani ba,again Clark bai yarda ba ya matso kusa da shi da niyyar ya tambaye shi ko zai fad'a musu abunda yake so sai a duba musu record na CCTV cameran mall d'in,Rafeek ya juyo da sauri ya kalleshi,duka shi ba don Clark d'in yayi maganar ba ya manta ma da akwai wani CCTV a gurin,ya girgiza kansa da sauri ya wuce yayi gaba,Clark yace ko zai bari suje su control room,yace A'a basu san me yake nema ba,suka wuce yana gaba har cikin mall d'in,basu jima ba sosai bayan sun samu yin magana da Manager mall d'in aka kai su control room,gaba d'aya Operators d'in aka tara masa su,daga shi sai su a cikin room d'in sai Clark sauran duk ya kora su waje ya fad'a musu abunda ya kawo shi,vedio recording surveillance footage na last 2 hours and half aka fara search,babu jimawa aka masa playing,ya zuba idanunsa a saman screen yana watching,bayan wucewar wasu seconds cam1 ya nuna dai² zuwansu da shigarsu gurin,da aka ci gaba da tafiya cam2 ya sake nuna ainihin shigowarsu mall d'in,duk abunda suka yi da inda suka shiga a hankali cameras suka yi finding out,suna fita camera1 ya sake nuna inda suka tsayar da cab Nusrah na rik'e da ita,abunda ya basu wahala kad'ai shine number cab da suka shiga,duk iya k'ok'arin su na son su gano lamarin ya rikitar da su,hankalin Rafeek a tashe yasa suka fita daga mall d'in,a hakan bai hak'ura ba yasa suka bi hanyar da suka nufa,guards d'insa suka fara k'ok'arin binsa yace su koma gida,ba dan sun so ba haka suka tafi suka kyale su su 3,wasa² tun ana batun counting hour daga 1,abu ya fara tafiya up to 5 hours,sun zagaye duk inda suke tunanin cab d'in sun ta bi,but ko irin colour d'in cab da suka shiga bai gani ba,kan dole ya hak'ura yasa drivern ya juya suka nufi mansion,,suna tsayawa a harabar gidan security'nsa suka bud'e masa ya fice idanunsa sun sauya launi,veins d'in kansa sun fito rad'a² a waje kana kallonsu,bai kula kowa ba duk yadda suke welcoming nasa,ya wuce inda entrance yake,wani irin security door ne na dim glass na ciki zai iya ganin na waje,palm d'insa kad'ai yayi shone daga gefe,door d'in yayi welcoming nasa kafin ya bud'e ya wuce ciki Clark ya biyo shi rik'e da phone da suit d'insa,"Subhanallah..!" Shi ne kad'ai abunda na iya fad'a a lokacin da nayi arba da cikin mansion d'in,fan's duk yadda zan fad'a muku tsarin sa ba lallai ku fahimta ba,but ku hasko kawunanku a ciki,k'arshen had'uwa iya tsari da duk wasu alatun more rayuwa babu wanda idanunku ba zasu hasko muku ba,tun daga kan parlor gidan ya kasance wani irin aljannar duniya ne,chairs kad'ai da aka zuba aka yi decorating sun kai five set a first floor kad'ai,parlor guda d'aya ne amma yadda aka yi ginin da wasu irin pillars da fitilu ke zagaye da shi sai ku yi tunanin sun kai hud'u,ko wanne an masa decoration da different colours,wannan yana wane wannan saboda tsaruwarsa,na tsakiyar shi ne yake d'auke da two set kuma duk ciki ya fi girma,sauran dake zagaye da shi an baza musu wasu irin rantsatstsun royals,dai fitowar wata y'ar dattijuwa data had'e cikin wani rantsatstsen super jikinta sai haske yake gold ta ko ina ga sanyayyan k'amshi da take bazawa ta nufo inda yake k'ok'arin zama saman wasu lafiyayyun armchairs tana tafiya tana kallonsa har ta karaso inda yake "Rafeek.!" Tayi calling nasa out,bai iya d'agowa ba sai da ya kwanta yana sakin wasu irin ajiyar zuciya masu nauyi,ta zauna kusa da kansa tana lumshe ido da bud'ewa ta shafa kansa,saurin juyawa yayi ya rungume ta with his coloured eyes yake kallonta ya kasa magana,hankalinta a tashe tace "Rafeek.! Mene ne yake damunka haka.!? Ka kalli yanayin da kake ciki kuwa.!?"
Yaci gaba da sauke ajiyar zuciya da k'arfi,ta rik'o fuskarsa slowly ta zuba masa idanu,a tsorace ya d'ago idanunsa da suka fara tara hawaye yace "Hajiya.! I've seen it not for awhile" ta tsaya kallonsa kafin ta samu courage na tambayarsa "Wace ce ka gani Rafeek.!?"

Yace "Ita.!" Hajiya da bata fahimci inda zancen sa ya nufa ba tace "Lydia.!?"

Yayi saurin girgiza mata kai,tayi squeezing face tace "Wace ce ka gani d'in Rafeek.!?" Bud'e bakinsa yayi da kyar yace "Hauwa.!"
Wata irin mik'ewa tsaye Hajiyar tayi tana kallonsa da mamaki tace "Rafeek.! Anya kuwa ita ka gani.!?" Ya girgiza kai yana matse kansa da runtse idanunsa,Hajiya ta koma ta zauna tace "Me ya kawo su UK to idan su d'in ne.!?" Da kyar yace "Ban sani ba Hajiya,but am scared don't know ko ta yi aure yanzun.."

Ya k'arasa yana yana had'awa da dafe saitin zuciyarsa,Hajiya ta kalleshi da tausayawa tace "Zai iya kasancewa hakan ne,zai kuma iya kasancewa ba haka ba,amma ni dai abunda nake son fad'a maka kada kasa damuwa a ranka,ka san condition da kake ciki,idan kace za ka sawa ranka damuwa komai zai iya faruwa da kai,ka san kuma abunda bana so kenan,kayi addu'ah in sha Allah idan Hauwa'u rabonka ce zata dawo.." (Hhhh.! Lallai kun makaro)
Ya lumshe idanunsa hawaye suka sauko daga idanunsa,Hajiya tana kallonsa tace "Cry Son.! Cry as if it will make u feel better,cry alot until u feel like ur tears come to an end,ba zan hana ka kayi ba,na san rad'ad'in da kake ji a yanzun bai kai kwatankwacin irin wanda kasa taji a shekarun baya ba" a hankali Rafeek ya zame ya kwanta a jikin Hajiya yaci gaba da kuka sosai kamar k'aramin yaro,Hajiya tana hawaye take ci gaba da shafa kansa,sai da yayi mai isar sa sannan yayi shiru ya ci gaba da sauke ajiyar zuciya,Hajiya ta ci gaba da masa nasiha cikin sanyayyan kalamanta sai da ta tabbatar ya fara samun nutsuwa sannan ta barshi.

*A month leave...*
Al'amari ya tsananta a b'angaren Rafeek,tun daga ranar da yaga Lolly a Ali Jericho Store cikin ikon ubangiji sai bai sake ganin ko da shade d'inta ba bare itan kanta,even though ya saka masu kawo masa report ya baza su a duk inda yake tunanin zai ji wani abu apart of her life,and a kullum cikin jiran tsammanin jin labarin an ganta yake amma shiru duk tsayin lokacin nan.

Ya kammala shirinsa cikin wani suit mai 3in1,niyyar fita yake yi saboda yanzun ko yana k'asar jinsa yake bai da sukuni har sai ya fita sab'anin da,tun daga ranar da incidence d'in ya faru ya daina zama a gida,tare da Clark da driver'nsa Jack suka fito a mota suna gaba yana back seat sai tunani yake,direct Albert street suka nufa cikin rantsatstsiyar motarsa k'irar mercedes benz GLK 350,cikin wata guda daya gabata duk ya hana maidservant d'insa sukuni ya mayar da Ali Jericho gurin zuwansa duk da ba komai yake zuwa yi ba,but thinking he could see her one day shi yake d'awainiya da zuciyarsa har yanzun kuma ya k'i sallamawa,,suna k'arasowa bayan sunyi parking Clark ya fito ya bud'e masa k'ofa,ya fito a hankali cikin mutuwar jiki,ya fara tafiya but ba cikin store d'in ya nufa ba,ya d'auki hanya ya fara tafiya phone d'insa k'irar iPhone 11pro yayi mata irin rik'on nan da ko yaya aka tab'a ka zata iya fad'uwa kamar bai san ciwon kud'in daya siya ba,yayi nisa da inda suke yana tafiya a gefen street daf da juna sun zo wucewa a tare suka gogi kafad'a da matashin dake tafiya hankalinsa akan waya,kasancewar Rafeek ya fi buguwa ya tafi zai fad'i saboda hankalinsa sam baya tare da shi like the young man,da sauri matashin ya mik'a hannunsa ya rik'osa ganin har ya kusa kaiwa k'asa,d'agowa Rafeek yayi yana rik'e da matashin zai yi magana idanunsa suka sauka kan kyakykyawar fuskar matashin dake masa sannu cikin harshen nasara,gaba d'aya jikin Rafeek ya mutu ya kasa motsawa saboda tsoron abunda ya hango a fuskarsa. Ya tsaya dai² da kyar matashin ya kalleshi zai sake magana shima ya k'ame,suka fara kallon-kallo,their resemblance to one another greatly frightened them,kowa sai sake kallon d'an uwansa yake da wani irin yanayi,lumshe ido Nuraz yayi ya bud'e ya sake kallon mutumin dake tsaye in front of him,a hankali yaji maganar Annie ta fara dawo masa kamar yanzun take sanar da shi
_"The resemblance of Rafeek in ur face as if it were being torn apar ya sake jefa zuciyarta a damuwa..!"_
Ji yayi maganar tana masa wani irin amsa kuwwa a cikin kunnuwansa da sauri ya rufe idanunsa yana jin jikinsa na shivering,Rafeek daya samu abun yi ya ci gaba da kallon Nuraz without yana iya blinking idanunsa saboda tsananin mamakin kamar da suke yi da matashin,Nuraz yayi k'arfin hali ya bud'e idanunsa da suka rikid'e,fuska ta juye da wani irin bayyanannen b'acin rai,ko mintuna biyu bai sake yi ba ya juya ba tare da yayi magana ba ya bar wajen,Rafeek ya bisa da ido,ganin yana neman rasa nutsuwarsa like someone who has lost his mind ya juya to where he left his driver da Clark,cikin hayaniya yace Clark yayi masa following footstep na Nuraz,yana son sanin wane ne shi da duk abunda ya shafi rayuwarsa,Clark ya amsa da sauri yabi bayan Nuraz da ya fara yin nisa da inda suke.....



#Sorry for da late update...


#Share pls.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*


*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥



*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2

*May Almighty Allah bless u with his divine grace and grant u all that u ever longed for.. I wish u my dearest brother peace,love,happiness and success on ur birthday... Have a grand day.!*🎉🎊

*@ALIYU MUH'D USMAN*
*(Mazan fama).♥*


Pᴀɢᴇ 20.
#Sᴇʟғ-ᴅᴇᴄᴇᴘᴛɪᴏɴ

He didn't know he was being followed behind ya ci gaba da tafiya fuskarsa d'auke da wani irin damuwa har ya k'araso apartment d'insu ya danna doorbell,Bareerah ta zo ta bud'e masa tayi masa barka da zuwa,bai iya amsawa ba ya wuce ciki,,Clark ya samu apartment d'in kusa da su ya b'oye yana hangensa,yana kallon lokacin daya shiga apartment d'in ya sake hango Bareerah tana rufe door,ya tsaya yayi investigating arean sosai sannan ya juya da sauri ya koma inda ya bar motansu.

Nuraz yana shiga kai tsaye ya wuce bedroom bai bari kowa ya san halin da yake ciki ba,wani irin yanayi yake jin kansa a ciki,gani d'aya yayi ma mutumin but ya fara jin wani k'iyayyarsa yana taso masa from the root na zuciyarsa,though bai tabbatar da zargin da yake yi akansa ba,amma zuciyarsa ta gama finding nasa out hukuncin da zai masa,saman bed ya zauna yayi flexing legs,hannayensa dafe da chin d'insa ya fad'a duniyar tunanin wane irin wulak'anci zai yiwa mutumin daya furta baya sonsa.!? Ya kamata ya kyale shi.!? Zuciyarsa ta bashi amsan ya kamata dai kayi masa abunda har numfashinsa na k'arshe ba zai manta ba kamar yadda yayi destroying muku happiness,,ya kwashe tsayin lokaci yana tunani da neman shawarar zuciyarsa,a hankali ya saki ajiyar zuciya,yayin da wata zuciyar tace "When ever ka kyale shi baka hukun tasa ba,it's like u take a knife and pierce it with urself,,ya kamata ko dai ba zaka rama duka ba,kayi masa kwatankwacin abunda yayi maka,ya wulak'anta ka,ya tozarta ka tun kafin ka zo duniyar,ko har ka mantan irin halin da ya jefa mahaifiyarka da kai kanka.!? Shekaru ashirin da takwas².! Kun shafe su kuna rayuwa ku kad'ai cikin bak'in ciki da rashin tabbas,shin wannan mutumin ne ya cancanci yafiya.!?"
Shiru yayi yana tunani a fili da wani irin murya yace "I'll never forgive u Mr Rafeek.. U must reap what u sow with ur own hand.. Any one who does something wrong must accept his consequences.!"
Inwardly sai ya ci gaba da sak'a abunda yake ganin idan yayi musu zai samu sassaucin irin nauyin da yake ji a k'irjinsa.

In the morning ya fito cikin shiri kamar babu inda za shi,ya zauna parlor suka gaisa da Annie taga duk yayi wani iri,fuskarsa babu fara'a,za ta tambayeshi taga yayi shiru ya zubawa one side ido,silently ta kira sunansa "Habibiiy.!" Ya d'ago kad'an yana sauke ajiyar zuciya,Annie ta kalleshi da kyau tana yin ajiyar zuciya tace "what wrong.!?" Ya girgiza kai yace "nothing" tace "Sure.!?" Ya lumshe idanunsa yace "very much sure mah",tayi taking deep breathe tace "Allah ya sa" sunyi shiru yana tunani,ya tuna yana da appointment da gidan TV na BBC (British Broadcasting Corporation),ajiyar zuciya ya saki daya bayyana a hankali ya sake taking breathe kafin ya mik'e tsaye da sauri,Annie tana kallonsa tace "Ina kuma za kaje ka mike haka da sauri.!?" Yace "Annie akwai wani d'an aikin da zanje na yi yanzun" tace "Allah ya taimaka" ya amsa da sauri ya fita daga gidan ya d'auki hanyar *ASYLUM WELCOME.*

***
Yana zaune cikin katafaren parlor'nsa sanye da training suit,kasancewar safiya and fitowarsa kenan daga gym zai wuce bedroom d'insa ya fasa ya zauna kallon tattaunawar da za'ayi,da yake yana yawan kallon programme d'in,,Jennet Alex ta bayyana a saman screen na k'aton cinema dake parlor'n,headline d'in kad'ai yaji ya sake neman guri ya zauna hannunsa da cup na coffee yana sipping,shahararriyar baturiyar ta fara koro jawabi cikin harshenta cike da kwarewa
"Welcome back to our health programme of today,,my name is Jennet Alex,welcomes u again guys to be with us in our field of professionals,,today we jumped up to the world of professionalism,where we researched and tracked down a renowned psychiatrist,whom u call DR PSYCHO.. Firstly we will now go straight to Dr psycho to hear a brief history of him,before we go into the programme,Dr welcome to be in our health programme of today.."
Nuraz dake gefe zaune cikin shigarsa da babu chanji,red wine colour long sleeve,black colour trouser and waistcoat yayi murmushinsa mai kyau yace "Thank u Jennet"
Lokacin da aka hasko fuskarsa kad'an ya rage zuciyar Rafeek bata fito ba,ganin saurayin da suka had'u ko sati ba'a yi ba,ya sake nutsuwa jikinsa a mace,zuciyarsa sai fad'a masa take duk inda ya fito tabbas suna da generation,ya saka idanunsa akan screen na cinema d'in cike da fargabar abunda zai faru gaba.
Jennet ta mayar masa da murmushin sannan ta ci gaba da watso masa tambayoyi cikin harshenta "Dr da farko za mu so jin sunan ka da tak'aitaccen tahirin rayuwarka,irin gwagwarmaya da kayi kafin ka zo wannan matakin."
Ya sake yin murmushi a hankali ya furta "Asalin suna na shi ne *NURAZ BIN HAUWA.!"*
Baturiyar ta girgiza kai tace "Ko za mu iya sanin asalinka.!?"
Yayi nodding kad'an yace "Asalina Nigerian ne,haifaffen can ne a state d'in Kano,a wani local government da ake kira municipal,,na fara rayuwa a can har ma na fara schooling,though ban gama primary school ba muka koma Lego's state da zama saboda wani dalili,a can ne na samu dama na k'arasa primary school d'ina na tafi secondary,bayan na gama,muka sake komawa Kano State,bamu jima sosai ba kuma,cikin hukuncin ubangiji big mom d'ina ta nema min admission a jami'ar Oxford,inda a nan na kwashe shekaru 7 na farko ina matakin karatun doctorate degree,bayan na gama ba'ayi taking long ba na sake dawowa nayi wani course na neman zama licensed psychiatrist,,daga nan kuma bayan na samu abunda na zo nema lokacin na fara tunanin komawa k'asata nayi aiki Allah bai nufa ba,aka yi min tayin aiki a wani Psychiatric hospital mai suna ASYLUM WELCOME,wanda yake a Unit 7,newtec place magdalen road,Alhamdulillah.! Yanzun da fara aiki na a nan na samu shekara d'aya da wasu watanni kenan,wannan shi ne tak'aitaccen tahirin NURAZ BIN HAUWA.."

Jennet ta jinjina kai tace "Excellent Dr.. But mene ne ya ja ra'ayinka ya zama ka zab'i wannan field d'in.!?"

Ya lumshe idanunsa a hankali ya bud'e da wani irin yanayi kwance a idanunsa ya furta "Mahaifiyata itace silar da tasa ni zab'ar wannan b'angaren.."

Jennet ta jinjina zancen tace "Shin a iya lokacin nan wane irin taimako ne kake bawa al'ummah haka har ya janyo ka yi suna cikin tak'aitaccen lokaci.!?"

Yayi murmushi kad'an yace "Taimakon farko da nake bawa majinyanta na,a duk lokacin da aka cemin Nuraz kai zaka kula da wannan patient d'in na kan yi k'ok'arin jansu a jiki mu saba da su sosai,ta yadda idan na zo aiki ba zan sha wahala ba,saboda sometimes za ki ga wasu likitocin namu saboda rashin sabo tsakaninsu da patients kana k'ok'arin bawa mutum kulawa,wannan rashin samar da alak'ar sai yasa k'arshe a samu matsala ko su rufe mutum da duka,idan aka yi rashin sa'a masu duka ne ko su kwaci makami suji maka ciwo saboda su tunaninsu ya jirkita ya zama daban da namu,so dole dai kafin ka tunkare su kai tsaye akwai buk'atar shak'uwa a tsakanin kai da su,after then zaka bada lokacin ka,da duk wata kulawar da zata taimakawa majiyancin.."

"Good Dr,kenan dai kana son cewa kafin likitoci irin ka,su tunkari majinyaci musamman b'angaren ku yana da kyau su fara samar da alak'a mai k'arfi tsakaninsu da patients d'insu ta yadda ba zasu damu ba a lokacin da ake duba su.!?"

Yace "Haka ne.",Jennet tace "Da fatan likitoci a b'angaren halayyar d'an adam suna tare da mu,kuma sun ji abunda Dr Nuraz ya fad'a,,but Dr bari mu koma baya kad'an cikin tarihin ka,a baya munji ka ce big mom d'inka ta kaika makaranta,and ka ce saboda mahaifiyarka ka zab'i wannan b'angaren,shin mahaifanka suna nan a raye ne ko kuwa mutuwa suka yi a lokacin,sannan mene dalilin duk da ka ce mahaifiyarka ce.!?"
Sai da yayi taking deep breathe kafin ya d'ago idanunsa da suka fara sauyawa ya furta "Suna nan a raye" Jennet ta kalleshi tana murmushi tace "Masu sauraro da ni za mu so jin su wane ne mahaifan DR NURAZ,and yaya ne ka yi rayuwa da family'n ka a tak'aice."

Ya lumshe ido ya bud'e yayi ajiyar zuciya mai nauyi yace "Mahaifana ba wasu bane,sannan na kasance ni kad'ai ne a gurin mahaifana,na taso a rayuwata ba ni da elder brother ko wasu little siblings,na rayu a wajen Big mom d'ina,duk da a cikin gidan mu bamu kasance da wani relatives namu ba,mun rayu mu kad'ai big mom d'ina da maidservant,sai Mommy na though she was unconscious bayan ta haife ni,sai kuma ni kai na kenan,dalilin da yasa na zab'i zama psychiatrist kamar yadda na fad'a a bayan saboda Mommy na ne,,sanadinta na zab'i wannan field d'in.."
A hankali cikin sanyayyar muryarsa ya fara finding out irin rayuwar da suka yi tun kafin a haifeshi,irin wahalhalun da suka sha kafin ya zo wannan matakin har ya dire a k'arshen,but abu guda ne bai yarda ya fad'a ba,sunan mahaifinsa though Jennet ta so ya fad'a,ya tsaya a nan yace "Idan har lokacin sanin ko wane ne mahaifinsa yayi zai bayyanawa duniya,though ya san ba b'oyayye bane,sunan sa kad'ai idan ya fad'a gaba d'aya duniya zata girgiza,but shi har yanzun yana doubting ne akansa,anya ya cancanta ya zama uba.!? Mahaifiyarsa ita ce komai nasa a rayuwa,,dan haka yana so al'ummar duniya su shaida hakan,kamar yadda mutumin da yayi ik'irarin shi ba mahaifinsa bane,shima ba yau zai fad'awa duniya shi d'ansa bane,saboda haka zai ci gaba da amsa sunansa na *'DAN MACE..* Kamar yadda society da k'abilar malam bahaushe take kiransa da shi.."
Yadda tattaunawar ta kasance zuwa bayyanar tarihin sa yasa al'ummah da dama kuka,Rafeek na zaune ya k'afe screen na cinema da ido yana hawaye da wani irin nadamar abunda ya aikata a zuciyarsa,he feels that time where running back,surely da there is nothing will stop him from turning it first,a hankali yayi descending daga saman chair yayi collapsed on to the ground,bakinsa na wani irin karkarwa yake fad'in "Astagfirullah wa'atubu ilaik.. Allah na tuba,na san ni bawanka ne mai tsananin taurin kai,na wulak'anta kyautar da kayi min a lokacin da ya kamata ace na nuna godiya ta gare ka,na tozartar da su,ya Allah ka dubi halin da nake ciki ba don hali na ba ka dawo min da su cikin rayuwata.."
A cikin wannan mawuyacin halin da yake ciki Clark ya shigo masa da report d'in binciken daya sa shi yayi masa ya riskeshi hankalinsa a tashe,ganin uban gidansa na kuka babu ji ya kira Hajiya ya sanar da ita,ita kanta hankalinta a tashe ta zo apartment d'in ta tarar da shi durk'ushe a k'asa hawaye wasu suna bin wasu a fuskarsa,idanunta sun yi wani iri saboda tausayinsa ta rik'o shi tana tambayarsa "RAFEEK kanka d'aya ka ke neman mayarwa da kanka bara ta za dawo bana.!?"
Jin muryar mahaifiyarsa yasa ya d'ago jajayen idanunsa da sauri ya kalleta yana girgiza kai,muryarsa sai rawa take da kyar yace "Hajiya ina jin tsoron abunda zai faru da ni gaba,tun a baya kunyi k'ok'arin fahimtar da ni abunda zai iya faruwa amma a lokacin sai nak'i saurarenku,na watsa muku k'asa a ido,bayan na butulcewa mahalicci na ta hanyar nuna masa kyautar da ya bani ba komai bace face k'azantacciya,al'halin ni nayi silar samar da ita ta tsarkakakkiyar hanya,,Hajiya da wane idon

Please Login or Register in order to submit comment