Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


     In the morning,ya fito cikin shirin tafiya hospital,itama ta fito da shirin fita skul suka had'u a dining,bai kalleta ba ya zauna ya fara break cikin sauri,ta waiwaya bata ga Annie ba ta ajiye handbag d'inta a parlor ta nufo hanyar kitchen,yi tayi kamar za ta wuce ta saci kallonsa tayi murmushi kad'an tace "Good morning" yana ci gaba da abunda yake yi ya amsa "morning how are u.!?" Tace "Alhamdulillah" bai sake cewa komai ba daga nan itama haka,ta lek'a kitchen taga Bareerah suka gaisa tace "Annie fa.!?" Tayi murmushi tace "Ina tunanin suna tare da Aunty" tayi murmushi tace "Ok" ta juya ta koma dining,tana zama ya tashi da sauri ya wuce,ta fara break taga ya wuce d'akin Lolly,har ta gama bai fito ba,ta tashi ta tattara kayan ta kai kitchen sannan ta yiwa Bareerah sallama,handbag d'inta ta d'auka ta wuce d'akin Lolly,tayi knocking ta shiga da sallama,Lolly tana kallonta tayi murmushi tace "Baby har kin shirya.!?" Tayi murmushi tana zama tace "Good morning Aunty" tace "Morning dear,how are u.!?" Tace "Alhamdulillah.!" Ta kalli Annie da yake ita sun gaisa tuni,Annie tayi mata murmushi tace "Saura tafiya skul ko daughter.!?" Ta gyad'a kai tace "In sha Allah" Annie da Lolly suka musu addu'ar fatan alkhairi sannan suka musu sallama suka fito,yana gaba tana binsa a baya,shi ya fara shiga mota ta bud'e side ta shiga ta d'aura seatbelt,a hankali ya fara drivern,sun yi nisa da apartment d'insu ta cikin mirror ya d'aga kansa kad'an ya kallo baya,yaga wani motan kamar tana following d'insu ya tab'e baki ya d'auke hanya,almost five minutes again ya sake ganin motar,duk inda yayi sai yaga tare suke tafiya,idan ya k'ara speed sai yaga motar itama ta k'ara,idan ya tafi slowly still yaga dai motar ta yi slow,ya rasa gane ma'anar hakan,tambayar kansa yayi "Why do they following me.!?" Rashin wanda zai bashi amsa yasa yaci gaba da drivern but inwardly ya damu sosai da rashin sanin dalilin,sun yi nisa sosai har sun kusa da skul d'in ya juya ya kalleta k'asa² ya furta "Do u talked to him.!?"
     Ta waiwayo a hankali tace "A'ah" yace "Me yasa.!?" Ta juya tana kallon side tace "he didn't ask ai." Ya juyo da sauri ya kalleta yace "Sai ya tambaya.!?" Ta gyad'a kai,ya girgiza kansa yace "Ki sanar masa" tace "Toh ai bai tambaya ba!" Yace "there's no need to ask" tayi shiru tana tunani,ta jiyo shi yana fad'in "Idan kika fad'a masa ba tare daya tambaya ba,zai fi d'aukan maganar serious" ta jirkita kai gefe,silently tace "Toh",suka yi shiru duka,har suka zo skul d'in babu wanda ya sake magana,ta sauka tayi masa godiya,sannan tayi masa sallama,tana kallo ya fara tafiya da reverse kafin ya juya kan motar ya d'auki hanyar fita daga skul d'in,sai da taga yayi nisa sosai sannan tayi ajiyar zuciya ta fara tafiya,tana daf da shiga class wayarta tayi vibration,ta ciro ta daga jaka ta tsaya answering,sunan Aatif yasa ta tsaya gefe ta zauna saman wasu kujeru,sai da suka fara gaisawa ya tambayi lafiyarta,sun tab'a hira kad'an yace zai shigo anjima kad'an idan ya fito daga office,tace Allah ya kawo shi lafiya,har zai katse kiran tayi saurin cewa "Idan ka zo i'll tell u the story ko.!?" Tayi furucin kamar tana tambaya,yayi murmushi yace "Duk yadda kika ce" tayi ajiyar zuciya kad'an tace "sai ka zo toh" suka yi sallama,kiran yana katsewa ta tsaya tunanin yadda zata fuskance shi ta fad'a masa,da kyar ta lalubo idea sannan ta tashi ta shige class ganin tahowar Mr.Thomas Martin.

    Bayan sun fito daga lectures suna tare da Veronica Jackson,Maria Robles sai Sarah Alee da yake ita y'ar 9ja ce karatu ya kaita suke gaisawa sosai har mutunci ya had'a su suke fita tare,a wajenta ta san su Maria da Veronica kasancewar apartment d'aya suke zaune,suna tafiya za su cafeteria kiran Aatif ya shigo wayarta,ta d'an tsaya kad'an ta fito da wayar tayi answering,sallama tayi masa ya amsa yana fad'in "Ina gimbiyata za taje ne take tafiyar k'afa.!?" Tayi murmushi tace "Ba dai ka ganmu ba.!?" Yayi murmushi yace "A'ah ban ganku ba amma dai na gano ki ke d'aya" tayi murmushi tace "Ba ni kad'ai bace ai" yayi murmushi cike da zolaya yace "Idanuna ni kuma ke kad'ai suka nuna min" tayi murmushi bata ce komai ba,yace "Ina za kuje ne.!?" Tayi ajiyar zuciya tace "cafeteria" yace "Okay.! Bari mu tafi tare" tayi saurin katse shi tace "A'a mu had'u a can" yayi shiru kamar bai son hakan sai kuma yace "Ok.!",basu jima sosai da shiga cafeteria ba suka sa akawo musu drink da snacks,tana zaune tayi facing inda duk mai shigowa za ta gansa,ta hango shi yana shigo wajen,sanye yake da white trouser da white shirt mai V-neck,idanunsa a cikin sunglasses mai duhu,tunda ya shigo ta kalle shi haka nan taji gabanta ya fad'i,ta lumshe ido a hankali ta bud'e taci gaba da kallonsa har ya zauna d'an nesa da su kad'an,k'arshen had'uwa,kyau da tsari Aatif yana da su kuma ya kai namijin da ko wace mace za tayi fatan samunsa,tsarin rayuwarsa da komai nasa cikin nutsuwa yake yinsa and dai² iyawarsa yana bawa duk wanda suke tare girma da muhimmanci,fari ne shi sosai dan ya fi Nuraz haske,kana kallonsa zaka gane yana tattare da duk wani nau'in hutu da jin dad'i,sai dai fa idan ana batun kyau dole ne a fara ambaton Nuraz kafin ace shi,asalin mahaifinsa D'an Nigeria ne daya fito daga jihar Gombe,k'aramar hukumar Akko,cikin garin *KUMO* haka ma Mamansa itama y'ar Gombe ce amma ita ainihinta a *JEKA DA FARI* ta taso,,kiranta yayi duk da ya ganta bata d'auka ba ta nemi excuse wajen su Sarah ta nufi inda yake,tun kafin ta k'araso ya zare glasses d'in idonsa yana sakar mata murmushi,ta sake yi masa sallama ya amsa,ta zauna tana gaishe shi,cikin sakin fuska ya amsa mata yana tambayarta lectures,shiru suka yi na wani lokaci kafin yasa a kawo musu drinks,ta kalleshi tace "Bana shan komai fa",ya kalleta zai yi magana tace "Ai mun sha tare da su Sarah" ya tab'e baki kad'an bai kulata ba yasa waiter ya kawo,ya tafi kawowa tayi shiru tana tunani,ya d'an buga table d'in kad'an,tayi saurin kallonsa yace "Yaya ne.!?" Ta girgiza masa kai tace "Nothing" yace "Allah ya sa" tayi saurin kallonsa saboda kalmar daya fad'a sai taji kamar Nuraz ne a gurin,tayi shiru ta sunkuyar da kai ya katse mata tunani "Ehmn.! Wane labari ne kike son fad'a min.!?" Ta d'ago da sauri tana had'iyan wasu irin terrified saliva's,a hankali tayi blinking idanunta tace "My story" ya gyara zama yana murmushi yace "Wawhh.!" Tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya yace "Kin yi shiru,and u know am eager naji" ta d'anyi calming kanta sannan a hankali ta fara fad'a masa,tunda ta fara yake kallonta da wani irin yanayin tausayinta a idanunsa har ta gama,fuskarta da hawaye sosai ta d'ago idanunta for da first time tunda ta fara magana ta kalleshi,yadda ya zuba mata idanunsa ko k'iftawa babu yasa taji duk guiwoyinta sunyi sanyi,a hankali cikin mutuwar jiki ya ciro handkey ya mik'a mata,ta karb'a a hankali ta goge fuskarta,ta mayar masa ya karb'a yasa a aljihu,kusan mintuna biyar taji bai ce komai ba,ta kalleshi yayi shiru da alamun tunani yake fuska da damuwa,kamar za tayi magana Sarah ta k'araso ta musu sallama,Nusrah ta kalleta tana k'irk'iro murmushi,suka gaisa da Aatif ta kalli Nusrah tace "Baby we will go home" Nusrah tace "Ku jira mu wuce tare sai ku sauke ni a hanya" Sarah za ta amsa Aatif yace su tafi zai kaita gida da kansa,tayi saurin kallonsa za tayi magana taga bai kalleta ba,suka yi sallama da Sarah,tana zaune su Maria suka zo wucewa,suka yi waving d'in juna tana kallo suka fita daga cafeteria,a hankali tayi ajiyar zuciya,bayan tafiyarsu babu jimawa Aatif ya mik'e yace "Muje na kaiki gida" ta tashi bata ce komai ba har suka fito inda yayi parking,ya bud'e mata front seat ta shiga,ya rufe ya koma side d'in driver ya shiga,sai daya fara sa seatbelt sannan ya tada motar suka fara tafiya a hankali har suka fita daga skul d'in,a bakin apartment d'insu ya tsaya,da wani irin murya ya rarrasheta,after ya nuna mata shi ita yake so ba komai ba,suka yi sallama yace idan ya isa gida za suyi waya,ta masa fatan komawa lafiya,a hankali ya d'age glasses yayi reverse tana d'aga masa hannu,har ya kusa fita daga arean sannan ta juya zata shiga gida,ta fara tafiya ta hango motar Nuraz tana shigowa line bata tsaya ba ta shige ciki.
   
      Tun da ta dawo ta shige d'aki tayi zamanta a can tana jiran kiransa,har after maghreb bata sake fitowa ba,sai da Lolly tayi kiranta jin shirun ya yi yawa,ta fito rik'e da wayarta ta zauna kusa da ita,Lolly ta kalleta tace "Ke kam baby kina jin dad'in zama kiyi shiru,shi kenan shi mutum sai yayi ta zama cikin d'aki shi kad'ai" tayi murmushi bata ce komai ba,wayarta ta duba taga ko Aatif ya kirata,taga babu alamun miss call akai,ta bud'e network ta fad'a duniyar gizo²,nan ma ta duba babu sak'onsa,tayi shiru tana tunani,har to 11 tana zaune shiru duk bayan mintuna ta sake dubawa ko ya kira sai taga bai kira ba,zuciyarta ta damu sosai,Nuraz ya saci kallonta ya ganta a damuwa,yayi shiru yana tunanin yadda zai tambayeta ko ta samu sun yi maganar da shi.!?,idea ya zo masa ya d'ago yana niyyar tambayarta ta mik'e tana k'irk'iro hamman k'arya tace "Aunty good night" ta kalleta tace "Toh.! Angel sai da safe" ta kalli Annie tace "Annie sai kin shigo." Ta gyad'a mata kai tana lumshe ido,ta yiwa Bareerah sallama ta wuce,har ta tafi idanunsa suna kanta,ya rasa me zaice da zaisa ya bar wajen ba tare da su Annie sun gano shi ba,zuwa wani lokaci ya mik'e shima yayi musu sallama,ya wuce bedroom d'insa.....
   
   
   
   
   
#Share pls.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*


*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥



*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2


Pᴀɢᴇ 22.
#Pʟᴀɴ ᴛᴏ ɢᴏᴛ sᴇᴄʀᴇᴛ ᴍᴀʀʀɪᴀɢᴇ

Da ya shiga kasa zama yayi yana ta tunanin yadda zai samu suyi magana da ita a daren kafin safiya amma ya rasa,ga shi ba number ta gare shi ba bare ya kira ta,ya zauna shiru a gefen bed yana tunanin idan basu yi magana yanzun ba sai dai da safe kenan,wata dabaran ya zo masa ya bud'e network d'in wayansa da tunanin yayi search a IG,Twitter zuwa sauran chart ko zai ganta sai ya tambayeta yaji idan ya yi sa'a tana online,yayi saurin d'aukan wayar ya fara dubawa,duk sunan da yake tunani idan yayi search zai samu sai da yayi amma ya rasa ta har Angel da Lolly ke kiranta ya sa bai ganta ba,ya hak'ura cike da damuwa ya ajiye wayar,wata zuciyar tace "To ka fita ta balcony mana idan ba ka so kowa ya sani" yayi shiru yana tunani,can da yaga hakan kamar shi ne mafita ya tashi da sauri,yaje jikin bright glass curtain wall d'in ya bud'e k'ofar da take sada shi da balcony ya fita,dai² window bedroom d'in ya tsaya yana tunanin yayi magana ko a'a.? Ya jima yana tunani ya rasa yadda zaiyi ya koma bakin pool ya zauna saman d'aya a cikin kujerun wajen,shiru yayi ya d'ora chin d'insa a saman hannunsa daya had'e guri d'aya yana tunani,ya juya kad'an ya kallo center window d'in sun,wayansa daya fito da shi ya duba yaga lokaci ya tafi sosai 12 saura mintuna,duka arean ya yi wani irin shiru baka jin hayaniyar komai,ya d'aga kai looking to the sky kamar yana counting Star's,da yaga yana b'ata lokaci ya mik'e a hankali ya koma bedroom ya rufe k'ofan,daren ranar da kyar ya samu yayi bacci.
Da safe ya tashi a d'an makare,ya fito da niyyar dubata,ya tarar tuni har ta tafi skul,ya koma ya gama shirin fita yayi sallama da su Annie,bayan ya baro gida yana tafiya still yau d'inma ya ga motan jiya tana following d'insa,ta mirror ya ci gaba da kallon motar yana tunanin mene ne had'insu da shi da suke bibiyar sa.!? Yayi deciding ya tsaya,gefen street d'in yayi parking yana kallon motar ya ga ta tsaya a d'an nesa da inda yake ya bud'e mota ya fita,inda motar take ya nufa ya tsaya dai² side d'in driver yayi knocking,a hankali aka sauke glasses d'in,Clark dake ciki ya kalleshi bai yi magana ba yana jiran yaji me Nuraz d'in zai fad'a,cikin matuk'ar had'e rai yana kallon baturen da fuskar tuhuma yace "why are u following me.!? Do i have any relations with u.!?" Clark ya tab'e baki kad'an cikin harshensa yace "why should i go after u.!?" Nuraz ya d'age shoulders yace "I don't know,but this is what i want to know.. Do we have any relationship that u always followed for.!?" Clark yayi ajiyar zuciya ya fara d'age glasses d'in saboda bai san me zai ce ba,da sauri Nuraz yasa hannu ya rik'e yana kallonsa angrily "Since u can't say anything,stop following me,if u were sent ne kaje ka fad'awa wanda ya aiko ka na fi k'arfinsa,nafi k'arfin yayi min wani abu,,idan baka ji ba ka sake bina kuma..!" Soundly yayi making snap,without ya sake cewa komai ya girgiza kai ya wuce,as he walked across the place a d'an fusace k'asar wajen tana motsi ya bawa Clark tsoro,quickly yayi swallowing some of the terrified saliva's da suka mak'ale a bakinsa,waya ya fara k'ok'arin yiwa uban gidansan,from the other side Rafeek ya d'auka,Clark yace "Sir. The boy realized we were following him" Rafeek ya lumshe ido ya bud'e yana sakin numfashi da kyar yace "Just come back home",daga haka bai sake cewa komai ba ya ajiye wayar yana sakin ajiyar zuciya while a fili yana maimaita fad'in "Astagfirullah wa'atubu ilaiik"

***
Da safen bayan tashin Nusrah daga bacci kafin ta sauka daga saman bed she began to check her phone to see whether Aatif had called tana bacci,ta cire lock taga babu miss call bare text,ta ajiye jikinta a sanyaye ta wuce bathroom tayi wanka,duka jikinta a sanyaye tayi shirin tafiya skul,ko breakfast bata jira ta yi ba tayi sallama da su Lolly ta tafi,she said she had morning lecture and the teacher was so hot that she didn't want to miss out,da Annie tace ta kira Yayantan ya kaita,she smiled softly tace ta san bacci yake yanzun,ba sai ta tashe shi ba,za taje ta hau cab kawai,suka mata fatan alkhairi ta fita,since her heart was broken ta fito ta tsaya bakin street ta nemi cab suka wuce,da ta shiga skul ma a time d'in bata da wani lecture kasancewar ranar sai 12 noon za ta shiga class,cafeteria ta wuce ta samu guri ta zauna tayi shiru tana tunani,bayan wani lokaci tayi deciding kiran wayar Aatif,miss call biyar tayi masa amma bai d'auki ko d'aya ba,ta tura masa text message,she was telling him if he saw the call he had to called her back,har to 11 tana zaune cikin cafeteria bai kira ba,ita kuma bata gaji ta tafi ba,still at that time there was nothing da ta ciwa cikinta,she was sitting all the time,,bayan lokaci tana ta zaune she looks out her phone to see whether he calls her ko ita ce bata ji ba,still ta ga wayam,ta gaji da zaman ta mik'e ta fara tafiya a wahalce,yinin ranar babu abunda ta tsinta a skul,lectures d'inma ba sosai ta gane abunda aka yi ba,4 dot suka fito ta kamo hanya tana tafiya ita d'aya cos tana jin ba zata iya tsayawa jiran su Veronica ba kasancewar za suje library,tayi musu sallama ta wuce.

Yadda ya bar wajen a fusace haka ya shige motarsa had'e da banging door d'in da d'an k'arfi,duk dama ba dad'in zuciyarsa yake ji ba cikin week d'in haka ya fizgi motar ya bar arean,sai daya fara zuwa hospital ya kammala aikin da yake yi after then he plans to go to Oxford University to pick her up,4:00pm sharp ya tsaya inda ya saba ajiyeta yana tunani da addu'ar Allah yasa bata koma gida ba,yana zaune cikin motar yana kalle² da tunanin inda zai ganta,can daga d'an nesa da inda yayi parking kad'an ya hangota zaune ta buga tagumi,yayi still yana kallonta na wani lokaci kafin ya cire seatbelt ya bud'e motar ya fita cikin mutuwar jiki,har ya tsaya kusa da ita bata sani ba,ya saki siririn ajiyar zuciya ya zauna kad'an bai yi magana ba,kusan mintuna goma ya d'auka da zaunawa a gurin yaga alamun tayi nisa sosai a hankali ya d'aga idanunsa ya kalleta,gabansa yayi mugun fad'uwa daya kalleta a nutse,yadda tayi zuru² cikin yini guda idanunsa suka hango masa wani irin tashin hankalin da take ciki,a hankali ya kira sunanta cikin muryar tsoro,ya maimaita kiranta ya fi a lissafa bata ji ba,sai da yayi tapping a dai² fuskarta sannan taja dogon ajiyar zuciya a hankali ta kalleshi,suna hada ido tayi saurin lumshe nata idanun,hawayen dake mak'ale trying not to cry tun safen began to pour out,cikin kid'ima yana kallonta da tashin hankali ya kasa magana sai wasu irin saliva's da constantly yake swallowing,yaga ba ta da niyyar dainawa gashi sai kallonsu ake yi,babu shiri ya mik'e ya kama hannunta,jakar da komai nata ya d'auka muryarsa a shak'e da tsoro yace "let us leave the place" ta d'ago kanta tana girgizawa alamun bazata tashi ba,idanunsa ya lumshe ya bud'e yana kallon mutanen dake wucewa suna kallonsu wasu har gulma suke ya sake cewa "get up,kina kallon yadda ake kallonmu fa,kada kisa ayi tunanin na yi miki wani abu" tana kuka tace "Ka yi tafiyarka kawai,ni babu inda zanje" ya kalleta da wani irin fuska yace "Za ki tashi ko sai na b'ata miki rai.?" Ta sake Kecewa da kuka muryarta tana wani irin kyarma tace "Ni ka rabu da ni,idan na tashi ina zanje ne.!? I have no other advantage,what good is my life.? The father who gave birth to me said that he didn't want me,he doesn't need me,amfanin me zan yiwa duniyar da mutanen cikinta.!?" Wani irin tausayinta yaji ya sake kamashi a hankali ya furta "Na ji tashi mu tafi" ta sake girgiza masa kai za tayi magana ya fizgota and talking in agony "What kind of person are u? Ayi ta binki ana maimaita magana d'aya baza ki saurara ba,if u have the right kill urself,akanki aka fara da za'a gama a kanki.!? Su mutanen da kike damuwa da su an fad'a miki dan kin shiga wani halin za su damu ne.!? I don't want a stubborn person,if u can get up idan ba zaki iya ba kuma zan wuce na barki" ta sauke kanta k'asa tana ci gaba da kuka,yana kallonta yace "will u get up.??" A hankali ta mik'e tana had'a hanya yayi saurin rik'e ta yana mata wani irin kallo,suka k'arasa inda ya ajiye mota ya bud'e ya taimaka mata ta shiga sannan ya bud'e back seat ya sa jakarta ya koma d'aya side d'in ya shiga ya tada motar,sai da suka fita daga skul d'in har sunyi nisa yayi parking,bai kalleta ba yace "what happened yesterday.!? Did u talk to him.!?" Ta kad'a masa kai tana goge hawayenta,yace "Ehmn!" Ta d'ago ta kalleshi taga ya zuba idanunsa akan hanya duk da a tsaye suke guri d'aya,ta sake goge hawayen da suka sake tahowa ta fad'a masa yadda suka yi da shi,yayi shiru yana tunani a hankali yace "why don't u call him.!?" Tayi shiru bata amsa ba,ya cire belt d'in ya juya backseat ya d'auko jakarta,tana kallo ya bud'e ya ciro wayarta ya kalla yaga akwai lock ya mik'a mata yace "bud'e",babu musu ta cire yace "call him",ta tsaya kallonsa ya juyo ya kalleta yace "call him" babu musu ta fara kiran line sa,har wayar ta katse ba'a d'auka ba,yace ta kuma kira,ta daure ta sake kiransa still ba'a d'auka,ta sake maimaitawa daf da kira na uku zai katse aka d'auka,tayi ajiyar zuciya a gajiye ta amsa sallamar da yayi,ta daure ta gaishe shi,ya amsa a sanyaye cikin daurewa tace "Why don't u call.!?" Da farko yayi shiru can kuma yace "Am sorry baby,uzuri ne ya rik'e ni that's why i didn't call,but when i got out of the office i would call in sha Allah" tayi ajiyar zuciya tace "Ok.!" Bai jira ta sake magana ba ya katse,Nuraz ya kalleta yace "what did he say.!?" Tace "He said he'll call me when he comes out of the office" ya gyad'a kai yana tab'e baki,a hankali yace "Ok duk lokacin da ya kira ki sanar da ni" har ta amsa kuma tace "Well. I don't know how to tell u" bai kalleta ba yace "za muyi waya.!?" He spoke as if he were asking her permission,ta gyad'a masa kai tace "toh" yace "To ajiye number,duk yadda kuka yi sai ki sanar da ni" ta sake gyad'a kai,ya fad'a mata digit d'in tayi saving,har ya tayar da motar ya juya yana kallonta na wasu seconds bai yi magana ba ya fara driven ya mayar da hankali kan tuk'in suka bar arean,a wani had'ad'd'en eatry ya parker ya fita ya barta a motan,yaje yayi mata lafiyayyen take away ya dawo,tana zaune shiru ya bud'e back seat ya tattara jakarta da komai yasa su gefe ya ajiye mata take away d'in sannan ya koma front seat bai kalleta ba still yace "Koma can ki ci abinci" ta d'ago kanta da sauri ta kalleshi tace "I'm not hungry" ya d'ago idonsa ya kalleta yace "really.!?" Ta kad'a masa kai,ya tab'e baki yace "je ki ci tukuna,the words come later" ta bud'e baki zata sake magana ya kafeta da ido,babu shiri ta had'iye nata maganar ta fita a sanyaye ta koma baya,ta d'auka leather da ta gani ta fara bud'ewa,package ne madaidaici sai bottle water ta fito da shi ta bud'e chicken noodles ne sai tiriri yake,da grille fish da yaji spices a saman,aroma d'in yana bugar hancinta taji yawunta ya tsinke,y'ay'an cikinta suka fara kukan yunwa,a hankali ta d'auki fork d'in data gani tayi bismillah ta fara ci,sam bata yi tunanin haka yake da taste ba abincin yana kallonta ta mirror ta fara cin abincin a hankali,bata wani ci sosai ba ta tattara komai za ta mayar taji maganarsa "what have u done.!?" Ta d'ago a hankali tace "I'm satisfied" ya tab'e baki yace "Kada ki mayar maza ki cinye su,idan kin bari waye zai ci.!?" Tace "Allah na k'oshi" ya girgiza kai "D'an abun da kika cin nawa ne,ko jaririn dake koyon cin abinci aka bawa wannan dai ba isarsa zai yi ba" ta marairaice za tayi masa musu yayi saurin juyowa yana kallonta "Ki cinye nace,nifa na tsani muyi ta jayayya,ke cikin naki ma sai kin masa mugunta.!? Dubi fuskarki da kanki,i think all the day this is what u started eating.. Azumi kike yi ne.!?" Ta girgiza masa kai a hankali,ya had'e rai yace "Maza ki cinye mu tafi" ta lumshe ido a hankali ta bud'e taci gaba da ci,tana jin ta kai linter har kamar za ta yi amai ta d'ago tace "Na k'oshi" ya janye idanunsa akan tablet d'in da yake pressing ya kallota ta mirror,yadda abincin yake kamar yaro ne yaci yasa ya tab'e baki yace "Sai ki fita dashi kisa a trash",ta kalleshi tace "babu kyaufa",ya juyo kad'an yana kallonta yace "If u don't want to pull out,how do u want to deal with it.!? Su nan babu ruwansu da almajirai bare kice a bayar" tayi shiru tana tunani ta d'an kad'a kai a hankali she feels nervous ta bud'e motar,har ta sa k'afarta a waje yaga yanayin dake fuskarta a hankali yace "ba ni nan" ta juyo a hankali tana kallonsa kafin ta mik'a masa ya karb'a,tana kallonsa taga ya bud'e,a hankali yake ci shima d'in kamar baya so,ta jingina da seat

Please Login or Register in order to submit comment