Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata san lokacin data rungume ta ba tana sakin ajiyar zuciya,Annie tayi murmushi ta shafa kanta,ya kalle su kad'an ya wuce ciki yana mamakin halayyarta,direct bedroom d'insa ya wuce ita kuma suka shigo tare da Annie,a parlor suka zauna tayi mata sannu da dawowa,Annie tace "Sannu daughter ya skul.!?" Tace "Alhamdulillah Annie na dad'e sosai da dawowa ban ganku ba" tayi murmushi tace "Mun je wani unguwa ne and bamu dawo da wuri ba,ina fatan babu matsala ko.!?" Tayi murmushi tace "Babu Annie" Annie ta girgiza kai tace "haka ake so.." Since ta dawo daga skul ta fahimci akwai abunda yake faruwa a gidan saboda yadda mutanen cikinsa suka koma wasu iri,da daren ma dai da yake sun saba had'uwa a parlor taga daga ita sai Annie da Bareerah,haka tayi ta kallon k'ofar d'akin Lolly da nasa but shiru sun k'i fitowa kuma duka ranar ma bata sa Lollyn a idanunta ba tun da suka gaisa da safe kafin ta fita,zuciyarta duk sai tayi mata wani iri ko cikakken awa d'aya Annie bata yi da dawowa ba tayi mata sallama ta koma bedroom, though ba bacci take ji ba amma zaman shirun da basu saba yi ba yau sai taji daban,data shiga bedroom gefen window ta tsaya tana duba balcony taga ko yana can tunda mafi yawan lokaci idan baya son hirar da suke a parlor can yake zuwa,da bata ga alamun sa ba nan d'inma ta koma saman bed ta kwanta ranar gaba d'aya haka gidan ya kasance kamar gidan makoki.

     In the morning bayan tashinta daga bacci before 8am ta gama shiryawa though she had no lectures sai tayi zamanta a bedroom,kamar wasa ta d'auki wayarta,network take k'ok'arin bud'ewa da niyyar shiga yanar gizo-gizo,alamar da ta gani yasa ta tuna jiya an turo mata message,kamar ba za ta duba ba ta bud'e a hankali idanunta suke bin content d'in bata k'arasa karantawa ba idanunta suka fara zubo da hawaye wayar ta sub'uce ta fad'i jikinta sai rawa yake,sai da ta gama kukan sannan ta mik'e a hankali ta d'auki wayar ta fita,direct tana fitowa ganin babu kowa a parlor bata jira ba tayi knocking door d'insa,shiru² tana jiran taji ya yi magana,ta gaji da tsaiwa ga maganar sai ci mata rai yake,tayi kamar za ta koma sai ta tuna abunda yake jikin text d'in ta fasa,daga k'arshe dai taji baza ta iya tsayawa ba ta bud'e ta shiga,since she had entered the room the fragrance of his scent's da turarukan d'aki da aka yi amfani da su suka kaiwa hancinta ziyara suka sa ta lumshe idanunta ta bud'e ta ci gaba da shiga,ta tsaya a tsakiyar d'akin kafin ta dakata ta ci gaba da bin ko ina da kallo,komai a tsaftace yake a zaune bisa muhallinsa,ganin baya nan yasa taji jikinta yayi sanyi,matsawa tayi jikin glass curtain wall ta janye labulayen gurin hasken rana daya fara d'agowa sosai ya sake haskaka d'akin taja numfashi data hango balcony babu alamu mutum,slowly her brain began to count the date's,harshenta ta d'an datse had'e da runtse idanunta tunawa da ba a weekend ake ba,tasa hannunta ta bugo k'eyarta tana fad'in "Shirme kawai,since today's u don't have lectures sai kika yi tunanin everyone is unemployed.!?" Bata jima sosai ba taje ta gyara labulayen data bud'e,ta juyo da niyyar fita idanunta suka hango mata wani had'ad'd'en diary,ta zuba idonta a gurin tana kallo ko babu komai ta ji ya burgeta kuma yayi matukar yi mata kyau,a hankali taje inda yake ta d'auka tana kallonsa da juya shi a hannunta har ta yi niyyar mayarwa ta ajiye taji ba za ta iya tafiya bata ga abunda yake rubuce a ciki ba,fasa ajiyewa tayi ta nemi guri ta zauna daga bakin bed d'insa,carefully ta warware threads d'in da aka d'aure sannan tayi unzipping diary d'in,blank ta tarar da first page ta tab'e baki a hankali sannan ta bud'e next,shi kansa second page d'in babu wani dogon rubutu wasu few words ne kad'ai a jiki,yadda aka yi rubutun da calligraphy ya so cakar da ita,bcos ba kowa yake iya yinsa ba yasa dole idan ba nutsuwa mutum yayi ba sai su bashi wahala,she kept her eyes wide open tayi gesturing face,she wanted to know what was written but she had suffered a lot before she could say the words clearly *"THE SECRET OF MY LIFE"* A beautiful smile released da ta gano abunda aka rubuta ta gyad'a kai tace "Ummhhum.! Lallai ma,dan kada a karanta shi ne aka rubuta da calligraphy.!? To sai na karanta..!" Next page ta sake bud'e and then she slowly re-spelled it out *"NURAAZ BIN HAUWA.!"* ajiyar zuciya tayi sannan taci gaba da bin content d'in dake k'asa tana sake bud'e shafukan gaba tana ci gaba da bi a hankali,duk wani labarin rayuwarsa shi ne a rubuce including the one he didn't tell her,wani abun idan ta gani sai taji ta kasa daurewa sai ta tsaya ta yi kuka idan ta dakata ta bud'e shafin data tsaya,next page bayan ya gama rubuta tarihin rayuwarsa abunda ya rubuta shi ne "Everyone can take risks but achieve goals it's just for a talented.." wani abun mamakin daya sake d'aure mata kai shi ne abunda ta gani rubuce data bud'e page d'in dake gaba "I found her.!" This is what has been written and there is no further information that allow anyone to understand what did that means.....
   

       #Hhh! Da alamun an zo gurin da asirin sa zai tonu 💃 let's go 🏃 to see the secret he always hidden.....
   

       
#Share pls.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*      

                   *'DAN MACE..*
              (Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥

  
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*    
https://my.w.tt/29u2S26SG2

 
Pᴀɢᴇ 28.
#Hɪꜱ ᴛʀᴜᴛʜ

    Tsayin lokaci ta d'auka shiru tana tunanin mene ne hakan yake nufi.? Ta tambayi kanta ya fi a k'irga amma ta kasa ganewa,da taga za ta b'atawa kanta lokaci wajen tunani da son bincikar abunda ba ganewa za tayi ba ta tab'e baki tace "ko me haka yake nufi oho.!" Next page ta bud'e taci gaba "Had'uwar mu ya kasance wani babban k'addara ne daga Allah.!" Nutsuwa ta sake yi sosai tana karantawa har ta kai k'arshen page,though bai fito ya bayyana ko da waye suka had'u ba zuciyarta ta gama finding mata mace ce yake magana akai,ta sake tab'e baki felt like she was keeping,but she found herself unable to keep up,ci gaba tayi da bibiyar rubutun yadda yake zayyana irin yadda yake ji game da ita a ransa ya sake tabbatar mata zarginta akan lallai mace ce and ba wai yana nufin mahaifiyarsa ba,wani page data bud'e taga hotuna sun zubo a hankali tabi su da kallo kafin ta fara bi tana tsintowa,kasancewar a kife suka zube sai bata samu damar gane ko waye a jiki ba,ta d'ago su tana fad'in "Ohh.! Allah ya kamaka" she turned the images confidently tana murmushi,her eyes wide open kamar za su fad'o k'asa with signs of fear,fuskarta tana sake bayyana tsananin mamaki a fili ta furta "Where did he get those pictures.!?" Tana rike da su sai juya su take tana k'are musu kallo da tunani,duk inda tunaninta da hangen nesanta suka kai sai data bincika but the situation was beyond her knowledge,she was quietly thinking lokaci guda her mind began to remember ranar da suka je gidansu tare bayan sun taho a hanya sun tsaya a wani photo studio har yace ayi mata passport,ta sake kallon pictures d'in a fili ta tambayi kanta "To ai passport aka yi min ranar,,where did he got these.!?" Zuciyarta tace "idan baki manta ba kayan da suke jikinki a lokacin sune wad'annan ai" tana jinjina lamarin har ranta tace "kenan a ranar aka d'auke ni ban sani ba ko yaushe ne hakan ya faru.!?" Murmushi tayi kad'an tace "Ikon Allah" a saman page d'in idanunta suka sauka inda ya rubuta "I had hidden my love for her ba tare da tunanin abunda zai faru da rayuwata ba,continuously hoping to have the power to express my love for the first time,ita ce kad'ai nake ji a cikin jini na,,but i don't know why all the time i tried to express my love i couldn't tell her that few words.! Abunda ban sani ba ashe abunda zai faru da rayuwata kenan,,,na b'ata tsayin lokaci ina ci gaba da kasancewa b'oyayyen masoyin da ba'a san da zamansa ba and mara amfani..!" Next page ta sake bud'ewa "The day i was about to express my love for her,i just came back ina zumud'i bcos my mind was telling me that i was going to be the lucky,but lokacin dana ganta tsaye da wani,naji zuciyata ta yi rauni.. I felt like my heart were explode,na bawa kaina laifi and na tuhumi kaina why i hadn't said it before,that *I love her.!?"* Ido Nusrah ta zaro tana fad'in "Then who is she.!?" Ta fad'a tana saurin bud'e d'ayan page d'in like ance mata idan ta duba gaba za tayi finding out amsarta.
     "Ke ce.!" Taji an fad'a as his voice crossed her ear's,murmushi tayi tace "Ni kuma.!? How did i become his love.!?" Sai da tayi maganar sannan kuma tayi saurin d'ago kanta because she made sure that the speaker was near her and hakan da yake fatuwa was not a dream or a thoughts,tana d'agowa karaf idanunta suka sauka a kansa,yana tsaye daga bakin k'ofa his hands were pouring into his trouser pocket,wani irin yawu ta had'iya cikin in'ina da kame-kame irin na mara gaskiya,ba tare data furta komai ba tayi saurin rufewa ta ajiye,ya lumshe idanunsa ya bud'e slowly ya fara takowa to where she was,a tsorace ta d'aga kai ta kalleshi yadda fuskarsa take babu wadataccen annuri yasa taji y'ay'an cikinta suna kad'awa,sai da yazo daf da inda take sannan ya zauna daga gefen bed d'in yana kallonta,as she silently bowed her head to the ground ya bashi dariya sai dai ya gimtse yak'i yi and instead of ya tambayeta daya zauna sai yayi mata shiru,a tsorace ta daga kai ta sake kallonsa,so take tayi magana amma ta kasa saboda yadda ya tsare ta da idanunsa,can dai da taga no way out ta daure tace "I'm sorry.!" Ya sake gimtse fuska yace "Me yasa kika tab'a min abu.!?" Kai tsaye tana runtse idanunta tace "I'm so sorry ba da gangan nayi ba" ya girgiza kai yace "how long have u been here.!?" Tace "D'azu ne babu jimawa" ya gyad'a kai yace "What did u come in for.? Ko dama kina zuwa ki yi min bincike idan bana gida.!?" Tayi saurin girgiza kai tace "A'a!" Yace "Uhhuumm! Tell me" tace "Ban tab'a shigowa ba sai yau" yace "Really.!?" Tayi saurin girgiza masa kai tana kallonsa,idanunsa ya lumshe yace "Uhmmm.! What did u see in it.!?" Tace "Nothing" yayi saurin bud'e idanunsa yace "Really.!?" As he spoke ita kanta bata san yaushe ta saki murmushi ba,he adjusted his position zuwa yanayin kwanciya yace "Since u don't see anything karanta min from the beginning!" Saurin zaro ido tayi tace "What.!?" One eye brow ya d'aga mata ba tare da yayi magana ba,pages d'in data wuce ta tafi haskowa ta juyo ta kalle shi tace "There are many fa.!" Yace "What.!?" Tace "Pages d'in" tsayawa kallonta yayi yace "Ohh! Ashe kin karanta kenan.?" ta gyad'a masa kai,yace "Well,,have u finished ur research Miss.Researcher.!?" Ta sunkuyar da kai saboda kunya ta kasa amsawa,yayi shiru yana kallonta da tunanin ya bari ta ga abunda yake ciki ko dai ya fad'a mata da kansa.!? Zuciyarsa tace "Kawai tunda ka samu dama ka fad'a da bakinka zai fi ma'ana,idan ta karanta babu tabbas ya burgeta" ajiyar zuciya yayi nan ya tsinci kansa da fad'in "U know what.!?" Tayi saurin kallonsa tana girgiza masa kai,sai yayi shiru ya kasa magana,yayin da wani sashi na zuciyarsa kuma yana fad'a masa ya kyaleta kawai tunda bata gani ba,jin yadda yayi shiru yasa ta d'ago kanta suna had'a ido tayi saurin d'auke nata ta mike tsaye zumbur as she continued playing with her middle finger tana kame²,ajiyar zuciya yayi yace "Where do u think to go.!?" Tana in'ina tace "Am! Dama ina son tafiya ne" ya gyad'a kai yace "Baki isa ba yarinya" ta marairaice fuska kamar za tayi kuka tace "Amma ai na baka hak'uri" yace "Ina ruwana da hakur'in da kika bayar.!?" Ta juya tana kallon k'ofa yace "Get seated,babu inda za kije sai kin karanta min abunda kika gani" tayi shiru ta sunkuyar da kai,ya kalleta ta gefen ido ya d'auko diary d'in yana juya shi a hannunsa yace  "Ko dai na ara miki ne.!?" Tayi shiru bata ce komai ba,ya tab'e baki yace "Shi kenan tunda ba kya so za ki iya tafiya" tayi saurin katse shi "Ina so mana" yace "Really!?" Ta gyad'a masa kai,yace "Ok let me think" tayi shiru kamar zatace "Wane irin tunani.!?" Sai kuma ta fasa jikinta babu wadataccen kuzari ta juya ta fara tafiya,har taje bakin k'ofa bai ce mata komai ba ita kuma tana jin jikinta yana bata kallonta yake yi,sai da yaga tana shirin fita ya dage ya furta *"I LOVE U.."* Kamar wacce aka dasa haka taji duk jijiyoyin jikinta sun tsaya she quickly turned to him,itan shima yake kallo a yadda ta ga irin kallom da yake mata babu tantama shi yayi maganar,continuously looking at him zuciyarta cike da tsoron abunda ta jiyo,yana kallonta babu shakka ko tunanin wani abu a ransa ya maimaita fad'ar *"I love u.!"*
   
    Wani mugun fad'uwa gabanta yayi cikin k'ank'anin lokaci jikinta ya shiga rawa,she could not believe kunnenta sun ji dai²,hannunsa ya mayar k'asan kansa ya tallafe yana lumshe idanunsa da bud'ewa ya sake sauke su akanta yace "I really *Love u"* saurin jingina tayi da k'ofar she felt her legs were too weak har tana jin kamar suna neman kayar da ita saboda tsabar shock da kalamansa suka sa ta shiga,kafin kace me yayi saurin tashi ya tarota ta k'arasa sauka a jikinsa,ta runtse idanunta tana jin yadda zuciyarta take beating,sassauta murya yayi dai² yadda za ta ji shi yace "I don't want to play with ur heart,wannan shi ne gaskiya ta" wani irin kuka ne ya kwace mata da k'arfi,quickly yayi saurin covering bakinta da hannunsa yana cewa "Shhhhh! Don't let Annie hear u tana parlor" ta d'ago idanunta tana kallonsa but ta kasa magana sai hawayen da suke sauka,ya mik'e tsaye yana rik'e da ita ya furta "Do u love me.!?" Tayi shiru saboda bata san amsar daya dace ta fad'a masa ba,ita dai ta san so but she doesn't make sure za tace tana sonsa ne ko A'a za tace,yaja wahalallen breathe yace "Don't bother ur self,if u don't like me kawai ki fad'a,bcos i know that as Allah (S.W.T) created us differently,haka ma zuciyoyinmu suke daban²,so ba zan takura sai kin so ni dole ba,amma ina son ki sani *INA SON KI.!"* Tayi saurin yin k'asa da kanta yayin da take tuhumar kanta da cewar "Why wasn't he became as my first choice.!?" Ta sake fashewa da kuka tana jin zuciyarta na mata wani irin k'aik'ayi,da sauri ta zame daga rik'on da yayi mata ta fice da sauri ya bita da kallo har ta fita,bayan tafiyarta yadda ta bar wajen tana kuka yasa ya ji kamar ta tafi masa da zuciyarsa,ya tsaya yana tunanin abun yi,ganin tsaiwar ma b'ata lokaci ne babu shiri ya d'auki diary d'in ya bita,Annie dake zaune a parlor taji an bud'e k'ofa for the first time tayi tunanin shi ne bcos tana son yi masa maganar zuwan su hospital,ta d'ago kanta taga Nusrah ta wuce da gudu,tayi shiru ta bita da kallo tana tunanin me ya kaita bedroom d'insa,bata gama tambayar kanta ba ta ganshi shima ya fito fuskarsa a had'e,kafin tayi magana taga ya bi bayanta,mamaki k'arara a fuskarta take tambayar kanta "Me ya had'a su.!?",yana shiga bedroom d'in ya tarar da ita zaune saman bed ta zazzage jakarta tana dubawa,ya tako a hankali har bakin bed d'in ya zauna yana kallon yadda take wargaje komai yace "What are u looking for.!?" A hankali bata yi tunanin zai ji ba tace "My remedies" yayi saurin kallonta yace "are u sick.!?" Ta gyad'a masa kai kawai,silently yana tunanin me yake damunta? K'asa² ya furta "can i ask u about..!" Bai k'arasa ba tace "No.! Don't ask." Yayi shiru yana nazari,can ya rasa me zai yi kawai sai ya shiga mik'a mata diary da yake rik'e a hannunsa,tayi saurin kallonsa tana k'ik'k'ifta idanunta tace "What shall i do with it.!?" Yayi jim kafin yace "I just brought u because.." Sai kuma ya kasa kaiwa k'arshe,girgiza masa kai tayi alamun ya barshi,yayi shiru yana kallonta yaga ba ta da niyyar karb'a,a hankali ya tashi zai fita,har ya kusa kaiwa k'ofa tace "Uhmm! Ka ba ni to.!" Ya juyo yaga shi take kallo tana mik'o masa hannu,yayi ajiyar zuciya a hankali ya ajiye mata,ya juya zai fita tace "Uhmm! Baka ji ba" ya tsaya kyam a inda ba tare da ya juyo ba yace "Fad'i ina jin ki" tace "u never told me when did i get it back to u" softly yayi murmushi yace "Duk lokacin da kika yi ra'ayi" yana fad'a ya fice,murmushi ta tsinci kanta da yi,quickly ta fara tattara everything she out back into the bag saboda zumud'in taga mene ne a cikin diary d'in har ta manta da abunda take nema,mik'ewa tayi tsam bayan ta gama ta nufi inda ya ajiye mata a saman study table d'inta,ta d'auka ta koma saman bed tayi flexing legs tana sakin ajiyar zuciya,da sauri tayi ta bud'e Page's d'in data wuce,har ta kawo wanda ta gama karantawa kafin ya shigo ta duba taga ta gama karantawa,da sauri ta sake bud'e page d'in gabansa.

     Yana fitowa Annie followed him with a look of suspicion,shi kansa sai a lokacin daya d'aga kansa ya ganta,duk da bai san tana gurin ba amma ya tabbatar ta ga wucewarsa,yayi saurin wucewa zai bar gurin ta kira sunansa,ya juya a hankali yana kallonta tace "Come" babu musu ya wuce duk da yadda zuciyarsa take tsinkewa ya zauna saman armchair without ya yarda sun had'a ido,she just stared at him and tana girgiza kai kafin tace "Ka je hospital d'in kuwa.!?" Ya girgiza kai yace "A'a yanzun dai zanyi shirin zuwa" tace "Ok.! Allah ya tsare hanya" yayi saurin kallonta saboda yadda tayi maganar ya ji kamar ba iya abunda za ta fad'a ba kenan,yace "Annie akwai wani abun ne kuma.!?" Ta kalleshi tace "Like what.!?" Yayi shiru bai ce komai ba,itama bata sake cewa komai ba,dan kansa ya tsargu yace "Annie babu abunda ya had'a mu" ta kalleshi tana gesturing fuskarta tace "Na tambaye ka wani abu ne.!?" Ya girgiza kai yace "fad'a miki kawai nayi.!" Tace "Na ji,tashi ka tafi" ya kasa tashi saboda yadda take harhad'e fuska yace "Wollahi Annie da gaske there was nothing,babu abunda nayi mata ki yarda da ni" ta sake zuba masa ido tace "Ka ji na ce ka yi mata wani abu.!?" Ya girgiza kai yace "A'a" tace "Toh tashi ka tafi" da kyar ya mik'e ya fara tafiya,Annie ta bi shi da kallo a hankali,can bayan ya bar wajen tace "Da ni kuke zancen duk zan yi maganin ku" tana fad'in haka ta tashi itama ta bar wajen,yana shiga bedroom d'insa kasa zama yayi,ya d'auki wayarsa ya kira line Nusrah,just in time ta bud'e page d'in data tsaya,idanunta suka sauka a kan wani had'ad'd'en Calligraphy da akayi shi cike da k'warewa,ta k'urawa rubutun ido tana son gane me aka rubuta wayarta tayi k'ara,tayi saurin janyo wayar tana ci gaba da kallon rubutun ta amsa kiran tana sa wayar a kunnenta,muryarsa ta jiyo yana fad'in "Na san Annie will ask u whenever she comes in,please.." Tayi saurin d'aga wayar ta kalli sunan da yake kai,bata ji me ya ce ba k'arshen ta maida wayar tace "Why would she ask.!?" Yace "Baki ganta ba da kika fita.!?" Tace "Ehh" yace "Ehh.! Kika ce.? Kina nufin dana fad'a miki tana parlor kin manta.!?" Ta sake cewa "Ehh!" Yayi ajiyar zuciya a hankali yace "Ok then" zai katse kiran tayi saurin cewa "Then tell me,me zata tambaya.!?" Yayi shiru yana tunani can yace "No,i don't know" tace "kuma kace za ta tambaye ni.!?" Yace "Ehh! She'll ask u" tayi ajiyar zuciya bata ce komai ba,yace "Za muyi magana!?" Tace "Umm!" Tana fad'a taji alamun bud'e k'ofa,ta d'aga kanta taga Annie ce take shigowa,da sauri tace "Latter" ta kashe wayar ta ajiye,kallon da taga Annie tana yi mata yasa ta sha jinin jikinta,Annie ta nemi guri a bakin gadon ta zauna tana k'are mata kallo kafin ta watso mata tambaya "Ke da waye kike waya baby.!?" Tayi tsuru² ta kasa magana,Annie tace "Dake nake magana" a hankali tace "Wani ne" Annie cikin mamaki tace "is Nuraz became someone else.!?" Ta sake sunkuyar da kai,Annie ta gyad'a kai tace "Me ya had'a ki da zuwa bedroom d'insa daughter.!?" Nan ma tayi shiru bata iya bata amsa ba,ta girgiza kai tace "Do u love him.!?" Ji tayi kamar za ta nutse k'asa dan kunyar data kamata,Annie tayi murmushi tace "Fad'a min daughter kina son shi.!?" Ai da sauri Nusrah ta sauka akan gadon tayi hanyar bathroom,Annie tayi dariya tana girgiza kai and then she walked out.

    Bedroom d'in Lolly ta nufa bcos akwai maganganun da take so suyi,tayi knocking door d'in taji shiru,ta sake knocking Lolly tana jin haka ta san ba Bareerah bace ta taso ta bud'e mata,bata iya kallonta ba har ta shigo,Annie ta kalle ta sosai tace "are u sick.!?" Ta girgiza kai tace "A'a" tace "What's wrong with u.!?" Quickly looking at her as she did,irin kallon da take yi mata yasa ta wuce a hankali tace "Nothing",Annie ta tsaya a inda take tace "Can we talk.!?" Ta juyo tana kallonta tace "Ehh!" Ta fara tafiya a hankali har ta isa inda take tace "Kin san me nake son fad'a miki.!?" Ta girgiza kai tace "I want u to take all ur stress out of ur life" ta had'iye saliva's da kyar tace "I can't adda" tace "Why not.!?" Lolly ta koma ta zauna tana jin zuciyarta tana yi mata wani iri tace "I just don't want our.." Annie sat down next to her tana dafa shoulder d'inta tace "kiyi k'ok'ari ki raba kanki da damuwa,kin fi kowa sanin babu abunda hakan zai k'ara miki face yasa ki sake shiga wani halin,and kin san tunda akwai yaro a tsakanin ku dole har yanzun kuna da alak'a" tayi shiru tace "But Adda shi yace nayi masa alk'awarin babu abunda zai sake had'a mu,and to stay away from his family,ba zan sake neman inda suke ba,kuma na yi masa alk'awarin,me yasa su zasu shigo rayuwar mu.!?" Annie tayi ajiyar zuciya tace "Manta da wannan zancen,abunda nake so dake kawai ki nuna musu basa gabanki,and ki yafe musu a wuce wannan matsayar" kai tsaye tace "I forgive them but Adda.." Annie tace "Tunda kin yafe musu kada ki sa damuwarsu a ranki,ki ci gaba da harkokin ki yadda kike yi,magana ne sai kin ga dama kiyi akan duk wani abu da za suyi,but kada ki kasance mai manta alkhairi ko yaya yake" ta girgiza kai tace "In sha Allah i'll never forget" Annie tace "Well,do u know what's going on.!?" Ta girgiza kai tana kallonta Annie tayi murmushi tace "Ur angel found u a new son in-law" murmushi tayi tace "Really.!?" Annie ta lumshe ido ta bud'e tana yin murmushi tace "Haka naga alama" Lolly tayi shiru tana tunani fuskarta ta canja zuwa yanayin damuwa tace "amma Adda bakya tunanin abunda ya faru.?" Annie tace "Mene ne ya faru.!?" Tace "u know what happened few days ago tsakaninta da wannan yaron.." Annie tayi murmushi tace "Baki tambayi waye saurayin ba kin fara maganar tsoro da abunda ya faru kwanaki" ta tsaya tana kallonta a hankali tace "To waye shi.!?" Annie tayi dariya tace "I won't talk about it right now,idan lokaci ya yi zaki sani" tana fad'ar haka ta mik'e ta fita

Please Login or Register in order to submit comment