Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta jiyo muryar Muneerah na fad'in

"Kin ci sa'a yau an miki uzuri, saboda haka se ki kiyaye" ta fad'a ita a lallae dole se an gane wata ce ita a wajen Rk d'in, kallan ta kawae Ayrah tayi tana jin wani irin takaeci da haushi na musamman na zuwa suka tirnik'e ta, dan haka yanzu ma ba tace komae ba se sake d'auke kan ta da tayi, daga haka ta sanya k'afa ta fice daga Office d'in, galala Muneerah ta bita da kallo sanda ta gama ficewa daga Office d'in sannan ta dawo da duban ta kan Rk tace

"Baby wannan d'alibar ka ce?" kallan Muneerah yayi kallo irin na cikin ido wanda ya sanya ta kauda kan ta gefe se dae har lokacin bata ji yace komae ba dan haka ta sake furta

"Baka tunanin shirun da ka mata bayan abinda tamin kamar ze janyo min raeni ne"

"Meye had'in ki da ita?" yayi maganar cikin basarwa, se tayi shiru kawae tana mamakin wannan mutumin, yaja Papers d'in data kawo ya had'a su da ragowar sannan ya mik'e yana zura wayar sa cikin aljihu yace

"Zan fita"

"Da wuri haka Baby? Ina zaka je?" yamutsa fuska yayi ba tare da ya bawa tambayar ta ta muhimmaci ba yace

"Zaki tafi ne?" a shagwa6e ta furta

"Haba haba kae kuwa Yaya na, ni fa hira nazo na taya ka" kansa ya d'an dafe dan shi yana jin kamar ciwon kae take k'ok'arin saka masa, a yayin da ita a 6angaren ta tana yin komae ne dan saboda ta burge shi, jin da tayi bece komae bane ya sanya ta fad'in

"Ohk muje na raka ka" ta fad'a tana murmushi

"No babu buk'ata" ya fad'a yana d'aukar key d'in motar sa yayi gaba ita kuma ta rufa masa baya zuwa wajen, ya shiga motar sa yayin da ita kuma ta shiga ta ta kowanne ya tada tasa. A hankali take takawa fuskar nan ta ta kamar wadda aka yiwa duka, se cika take tana batsewa, wayar ta ce tayi k'ara ta zaro ta daga cikin hijab d'in jikin ta sannan ta d'aga tana karawa a kunnen ta, daga can 6angaren Yah Sadeeq yace

"Ayrah.."

"Na'am Yah Sadeeq" ta fad'a tana d'an tura bakin ta gaba kad'an, daga can 6angaren yayi murmushi kana yace

"Yau kuma waya ta6a min k'anwa ta? Ko dae wannan likitan ne?" daga inda take ta d'an yi murmushi jin yadda Yah Sadeeq d'in ya gano hakan da wuri, ko da yake hakan ba abin mamaki bane dan kusan koda yaushe k'orafin ta baya wuce akan Rk

"Shi ne" ta fad'a tana sake kwa6e fuska kamar tana gaban sa

"Wae ni kam meyasa doctorn nan ya takurawa k'anwa ta ne?"

"Oho masa" kafin Yah Sadeeq d'in yace komae ta sake fad'in

"Yah Sadeeq ina Umma?"

"Umma na gida, idan na koma zan kira ki In Allah ya yadda se ku gaesa" bata san sanda wani murmushi ya su6uce mata ba, haka suka cigaba da hira da yayan nata cike da k'aunar juna.


... Ita da Jidda ne cikin Cafe d'in, mutumin ya kalle su sanda Ayrah ke fad'in

"Pls kayi mana kaaji" seya jinjina kae sannan yace

"Ohk, amma zan je na samo mae idan zaku jira ni"

"Babu matsala.." Ayrah ta fad'a tana neman waje ta zauna, dae_dae lokacin da mutumin ke shirin fita daga wajen yayi dae_dae da lokacin daya shigo cikin madaedaecin Cafe d'in, yana sanye cikin wata kyakykyawar riga da bluen jeans wad'anda suka matuk'ar yi masa kyau, kamar koda yaushe yanzu ma kan sa babu komae se kwantacciyar sumar kan sa da koda yaushe kamar ana k'ara mata shek'i ne da kyau, dakatawa mutumin yayi da murmushi kan fuskar sa yana fad'in

"Doctor.. doctor barka da zuwa" yayi maganar yana mik'a masa hannu, Rk ya mik'a masa hannu suka gaesa shima da wani tsadadden murmushi akan fuskar sa, Jidda data ga shigowar sa sanda ta mik'e tace

"Barka da wannan lokaci Sir"

"Barka" yayi maganar har lokacin hannun su na cikin na juna shi da mutumin

"Bari naje pls Ayrah, me zan siyo miki?" murmushi tayi kana tace

"Mango" dariya Jidda tayi k'asa k'asa sannan tace

"Nima bansan meyasa na tambaya ba bayan na san ina tare da mayyar mangoro Ayrah!!" ba saurarar su yake ba kuma be damu da kallan wadda ta gaeshe shi ba amma tabbas wannan maganar ta sauka cikin kunnen sa har be san sanda yayi sauri ya d'aga kae ya kalli Jiddan ba, ita kuwa sosae hakan ya mata dad'i har da chanja tafiya ko da ta janyo hankalin sa, se dae abinda bata sani ba sam bema kalli fuskar ta ba balle akae ga kallan tafiyar ta, bega wadda take bayan ta ba saboda ita Jidda ta taso zata fita ne, kafin kuma ya maeda duban sa wajen seya jiyo mutumin nan na fad'in

"Raj pls bari na d'an je na samo mae zan yi wani aeki ne, idan babu damuwa a jira ni pls" yayi maganar yana murmushi, se kawae ya d'aga masa kae yana lumshe manyan idanun sa, shi kuma yace

"Toh nagode" yayi maganar yana bin bayan Jidda data fita, tunda taji sunan da mutumin nan ya ambata ta d'aga dara daran idanun ta ta kalli wanda aka kira da Raj d'in, bata san sanda ta mik'e ba har handout d'in dake kan cinyar ta ta zame, shima ita yake kalla yana so ya bar k'wak'walwar sa tayi aekin daya dace, cikin en sakannin da basu wuce 2 ba idanun su suka sark'e cikin na juna, a lokaci guda zuciyoyin su suka buga wanda har seda Rk ya d'an lumshe manyan kyawawan idanun sa, yanayi ne da be ta6a jin sa akan kowacce d'iya mace ba, wani sabon al'amari ne daya dad'e yana bashi mamaki, dukkan su se suka kaasa d'auke idanun su daga cikin na juna duk da yadda hakan ke azalzalar zuciyoyin kowannen su, sun kae tsawon minti 1 a haka kafin Ayrah tayi watsi da duk wani tsoro, wasu wasi tare da taraddadi ta watsa su gefe sannan ta tattaro jarumta kana ta d'aga yatsan ta dake rawa kamar me, ta nuna shi sannan ta bud'e bakin ta daya mata wani irin nauyi bayan ta lumshe idanun ta sanda wasu kyawawan hawaye suka zuba akan fuskar ta ta furta....


Mhiz Innocent.....✍️




https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd



*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*

*CHAPTER ONE*


✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨


Page 019_020



"Raj!?" ta k'arashe maganar da sigar tambaya, lumshe nasa idanun yayi daga cikin nata yana jin yadda zuciyar sa ke azalzalar sa na k'ara k'aemi, cigaba tayi da kallan sa har lokacin bugun zuciyar ta be koma dae_dae ba jira take kawae ta tabbatar, taji daga bakin sa cewar da gaske shine Raj, a hankali ya jinjina kan sa sannan da muryar sa wadda ta d'an shak'e shima saboda tsananin mamaki yace k'asa k'asa, wanda idan ba dan babu hayaniya a wajen ba da ko ita da take a cikin wajen ba zata ji ba

"Ayrah!!?" seta shiga jinjina kae da sauri wasu hawaye na cigaba da ambaliya akan kuncin ta sannan lokaci guda kuma ta saki wani murmushi duk da har lokacin bata dena kukan ba, ta kaasa daurewa, ta kaasa cijewa, har izuwa lokacin wani irin azalzala zuciyar ta ke yi tana wani irin zillo dan haka cikin k'ank'anin lokaci da kuma sauri ta k'arasa ta rungume shi lokaci guda tana runtse idanun ta ko zata ji sauk'i daga abinda take ji a cikin zuciyar ta, k'irjin ta ya cigaba da bugawa da sauri da sauri kamar wadda tayi gudu, kamar wani soko ya tsaya kawae bayan sauke wata doguwar ajiyar zuciya, yana jin yadda ta rik'e shi sosae da alama tsananin farin ciki ne ya sanya ta hakan, wani sassanyan murmurshi ne ya wanzu akan kyakykyawar fuskar sa sannan akan la66an sa ya furta

"Har yanzu dae bata chanja ba" hannun sa ya saka ya zame ta daga jikin sa sanda take kuka me d'an sauti, a hankali ya k'arasa ya zaunar da ita kan kujerar wajen sannan ya saki hannun ta a ransa yana furta

"Astagfirullah" a kunnen ta abinda ya fad'a d'in ya sauka duk kuma se taji wata matsananciyar kunya ta kama ta, ta kaasa controlling kan ta a lokacin, ta rasa abinda za tayi taji sauk'i, farin ciki da kuma mamaki gami da son tabbatar da abinda ta gani ne ya sanya ta rungume shi ba tare da wani tunani ba, yana tsugunne akan k'afafun sa daga k'asan inda take yana cigaba da kallan kyakykyawar fuskar ta, shi kan sa har ya zuwa lokacin ya kasa dena mamakin shin da gaske Ayrah ce? wannan d'in Ayrahn sa ce? Dae_dae lokacin ta d'ago jajayen idanun ta ta sauke su a kan sa farar fuskar nan tayi jawur haka zalika a d'an shagwa6e ta kalle shi, be san sanda wani murmushi ya su6uce masa ba, babu shakka ita d'in ce, kuma har yanzu halayen ta na nan

"Da gaske Raj d'ina ne kae?" ta sake tambaya dan har lokacin tana tantama ne, musamman yadda tasan Raj d'in ta basu da hali, amma wannan tana ganin sa ne mutum me kud'i, a yadda ma taji ana kiran sa kamar likita ne in dae ba tayi mistake ba, idanun sa ya kashe mata wanda hakan ya sanya ta saurin kauda nata idon tana jin wani irin bak'on al'amari da tunda take bata ta6a jin sa akan kowanne d'a namiji ba, yanayin da take ji a yanzun wanda ke tafiya da dukkan wani bugun numfashin ta

"Raj Kabeer" yayi maganar yana mik'ewa ya zauna gefen ta dan ya sake tabbatar mata da shi d'in ne ba wani ba, a hankali ta sake lumshe idanun ta tana jin wani irin dad'i na cigaba da ratsa ta, ita kam yau wace irin rana ce me muhimmaci a wajen ta? Wace irin ranar farin ciki ce a gare ta wadda a cikin ta taga Raj, yau gata ga Raj d'in ta bayan tsawon wasu shekaru?

"Meyasa baku sake zuwa gidan mu ba?" tayi maganar tana langa6ar da kae gami da kallan sa, se dae a wannan karon bata kalli k'wayar idanun sa ba, kafin ya kae ga cewa komae me Cafe d'in yayi sallama ya shigo wajen, da mamaki ya kalli Rk dake zaune kujera d'aya da wata 'ya mace, abin ya matuk'ar bashi mamaki har hakan seda ya bayyana akan fuskar sa amma ya maaze yace

"Doctor!!" dukan su suka kalle shi dan sam basu san da shigowar sa ba saboda yadda suka shagala da son jin abubuwa da dama daga kowannen su

"Pls jira ni a waje!!" Rk ya fad'a bayan ya d'an kalli Mutumin, cike da mamakin dae ya furta

"Ohk.." sannan yayi waje ya nemi waje ya zauna har lokacin yana cigaba da mamakin Rk d'in, kamar bashi ba..

"Bansani ba, nima bansan dalili ba" yayi maganar a ransa yana zurfafa tunani ko ze gano dalilin da yasa basu je gidan su Ayrahn ba amma ya kaasa, ita tunda ta gano shine Raj duk wannan tsoron nasa da take ji se taji kamar ya tafi, gaba d'aya ma ta manta shi a matsayin Rk kawae tana masa kallan Raj ne

"Kullum ina tunanin ka, amma baka ta6a zuwa waje na ba" tayi maganar kamar zata saka kuka, d'an shiru yayi yana cigaba da kallan ta sannan yace bayan ya lumshe idanun sa

"Ban san a ina zan same ki ba Ayrah, ki min uzuri pls.." yana gama maganar aka shiga kiran sallah a masallaci, dan haka dukan su suka yi shiru har zuwa sanda aka idar da kiran Sallahr sannan suka mik'e kusan a tare, Rk ya kalle ta sannan ya mik'a mata wayar sa daya fito da ita daga cikin aljihu yace

"Samun contact naki" babu musu ta kar6i tsaleliyar tsadaddiyar wayar tasa ta sanya number ta a ciki sannan ta mik'a masa a ranta tana jin farin ciki mara misaltuwa, daga yanayin yadda ta fahimta abubuwa da dama sun chanjawa Raj d'in nata, kamar bashi ne Raj d'in da ba, kamar an chanja shi ne da wani sabo, ko da yake ba abin mamaki bane komae ikon Allah ne, da farko sune a sama yanzu kuma Raj d'in se dae ma shi ya taemaki wasu ba dae a taemaka masa ba, babu abinda Allah baya iya yi, yadda tayi shiru kamar me tunani ya bashi damar cigaba da k'arewa kyakykyawar fuskar ta kallo yana cigaba da karanto abubuwa da dama

"Muje koh?" yayi maganar a hankali kamar me rad'a, seta d'aga kae ta kalle shi kana ta lumshe idanun ta a lokaci guda tana bud'e su, itace ta fara yin gaba sannan yabi bayan ta har suka fito, me Cafe d'in nan ya mik'e yana kallan sa yace

"Doctor zaka wuce ne?"

"Yeah" ya fad'a a gajarce

"Tohm shikenan, Allah ya tsare" ya fad'a yana d'an satar kallan Ayrah yana so yaga wace me sa'ar ce wannan da Doctor d'in da kan sa yake kula ta

"Ameen" ya fad'a yana wucewa zuwa wajen motar sa Ayrah na binsa har zuwa sanda ya bud'e murfin gaba sannan ya juyo ya kalle ta, se yaga a yanzu da suka fito haske sosae ma kamar tafi kyau, d'an guntun murmushi ya wanzu a gefen bakin sa sannan yace

"I will call u Uhmm?" ya k'arashe maganar yana rufe idanun sa kad'an sannan ya bud'e, jinjina kae tayi ba tare da tace komae ba, haka kawae take jin babu dad'i har cikin ran ta, ji take ina ma su kasance a haka har abada, gefe guda kuma tana ganin kamar idan ya tafi d'in za'a sake maemaeta wancan karon, wato baze sake dawowa ba se bayan wasu shekaru, ko kuma yana matsawa daga wajen zata farka ne daga bacci taga duk abinda ya faru d'in mafarki ne ba gaske ba, haka dae ta kawar da duk wad'annan kawae ta jinjina masa kae sanda yake shigewa cikin motar, ta cigaba da tsayuwa har zuwa sanda yaja motar ya bar wajen yana cigaba da kallan ta, itama shi d'in take kalla. A hankali ta sauke wata ajiyar zuciya sanda ya 6acewa ganin ta, seta shiga jan k'afar ta data mata wani nauyi ta shiga takawa tana cigaba da tunanin Raj d'in, tana tuna Raj d'in da daga farko take masa kallan mutum mara kirki, mugu kuma mara tausayi, mutumin da mazan ajin su kaff ba taga wanda baya tsoron sa ba ballantana kuma akae ga mata, matan dake rububin sa kamar me, se gashi a rana d'aya a kuma lokaci d'aya hakan ya juye zuwa wani sabon al'amari, daga yadda zuciyar ta ke cigaba da harbawa tana tunanin Rk d'in ta fahimci akwae wani gagarumin abu, se dae ta gaza gane menene shi?. Cikin farin cikin daya gaza 6oyuwa akan fuskar ta ta shiga d'akin nasu, dukkan su suka bita da kallo, sabon abu ne da ba kasafae suka saba ganin sa akan fuskar ta ba, abu ne ma da zasu iya cewa in dae ba da Yah Sadeeq, Umman ta ko Abban ta take waya ba basa ganin irin wannan annurin akan fuskar ta, se dae na yau ma ya shallake wad'ancan d'in, dan kuwa tana shigowa ta jefar da Handout d'in hannun ta sannan ta kwanta akan gado tana sakin wani k'awataccen murmushi gami da lumshe idanu, da mamaki Jidda da Ruks suka kalli junan su, se kuma cikin k'arfin hali Ruks ta furta

"Ayrah lafiya kuwa?" da sauri ta bud'e idanun ta dan gaba d'aya ma ta manta ba ita kad'ae ce cikin d'akin ba

"Eh. Ehh" ta fad'a tana mik'ewa zuwa toilet, suka sake bin ta da kallo sanda ta shige toilet d'in

"Ikon Allah" suka had'a baki wajen fad'ar hakan, babu dad'ewa ta fito, Jidda ta dube ta tace

"Ga mangoron ki nan cikin leda"

"Bash shi kawae, zuwa da safe zan sha" tayi maganar tana janyo hijab dan gabatar da Sallah

"Toh lallae akwae damuwa" Jidda ta fad'a tana bin ta da kallo sanda take k'ok'arin tada Sallahr.. Wajen k'arfe 9pm ne na daren ranar tana kwance kan gadon ta, tun d'azu take expecting kiran sa amma kuma tana fatan kafin ya kira ace su Jidda sunyi bacci, se dae ba taga alama ba dan kuwa hirar su suke kamar yadda suka saba kullum se sunyi ta kamar farilla, se juyi take kawae akan gadon tana tuna kyakykyawar fuskar sa, ada sanda yake a Doctor Rk bata ta6a tsayawa ta k'are masa kallo ba ballantana har ta gano wannan kyan na musamman da matan ajin nasu kan kod'a shi akan sa ba, se yau ta kalle shi ta tabbatar da hakan, ta kuma ga zalla kuma aenahin kyau daga Raj d'in.

.. Sanda ya koma gida kae tsaye d'akin sa ya wuce yau ko sashen Mummy be je ba, dan so yake kawae ya gama abinda yake ya kira ta yaji abubuwa da dama daga wajen ta, toilet ya fad'a ya watsa ruwa a jikin sa sannan ya fito ya shirya cikin wata brown d'in had'ad'd'iyar jallabiyya, ya zauna yayi karatun qur'an kamar yadda ya saba sannan yayi addu'o'i ya mik'e daga kan abin sallah, yana shirin ninkewa yaji ana knocking k'afar d'akin, d'an tsaki yaja sam be san wani ya kula da shigowar sa cikin gidan ba, kamar ba zeje ya bud'e ba se kuma ya ajje daddumar kan gado sannan ya fito parlourn ya k'arasa ya bud'e k'ofar, kawae seta sanya kae cikin d'akin ta shigo hannun ta d'auke da warmers d'in abinci guda 2 ta ajje a tsakiyar parlourn, sanye take cikin doguwar rigar shadda wadda tasha aeki ta fito tayi kyau da ita, fuskar nan kamar koda yaushe ta k'ara fari, tsaki ne ya su6uce masa akan bakin sa yana lumshe ido, ya akae tasan ya shigo gidan?

"Baby yau baka shigo kaci abinci ba, yasa nace bari na kawo maka d'aki, ina fatan ban yi laefi ba?" tayi maganar tana matsowa kusa dashi, bece komae ba ya k'arasa ya zauna kan kujera sannan yace har lokacin be kalle ta ba

"Sannun ki" seta saki murmushi tana dawowa itama ta zauna kan kujera tana shak'ar k'amshin turaren jikin sa daya cakud'e dana sassanyan k'amshin sabulun sa, ko second 5 ba tayi kan kujerar ba ta zame zuwa k'asa tana fad'in

"Bari nayi serving naka" shi bema jita ba dan gaba d'aya hankalin sa ya tafi kan Ayrah ne, tunda ya baro makarantar ya kasa dena tuno kyakykyawar fuskar ta, gaba d'aya ta chanja, duk da dama tun tana yarinya kyakykyawa ce amma yanzu ta k'ara wani shahararren kyau kamar ita tayi kan ta, se dae har yanzu halin ta na nan, ga6untar nan da shagwa6ar nan har yanzu babu abinda ya ragu, tilas abinda ya tuna d'in ya sanya shi sakin sassanyan murmushi yana gyara zaman sa kan kujerar da yake, Muneerah data d'aga kae ta kalle shi taga murmushin da yayi, abinda yake da tsada a wajen sa, se gashi yau kusan zata iya cewa babu dalili yayi shi, seta samu kan ta da gyara zaman ta tana murmushi dan ita ta d'auka da ita yake

"Yaya Daddy ya maka magana kuwa?" ta katse masa tunanin tana fatan Daddyn ya masa magana kuma ya kar6i zancen hannu bibbiyu, da mamaki ya d'an kalle ta sannan ya d'auke kae

"Magana? Anya kuwa!" ya fad'a cikin er basarwa, seta yamutsa fuska sannan tace

"Ohk toh ka sauko kaci abincin mana" ta fad'a tana cigaba da satar kallan sa ganin da tayi yanzu babu wannan murmushin akan fuskar ta sa, iska ya furzar daga bakin sa dan shi kam kwata kwata baya jin wata yunwa, toh wata ma yunwa zeji bayan gaba d'aya hankalin sa da tunanin sa na wajen Ayrah ne

"Ban jin yunwa fa" ya fad'a yana zuba mata idanun sa, cikin er rawar murya ta furta

"Haba mana Baby, pls kaci kada ka kwana da yunwa!" ta fad'a cike da kulawa kamar itace zata kwana da yunwar bashi ba, baya son dogon zance kuma ya k'agu ta fita dan yana jin idan har ta k'ara wasu mintuna bata fita ba toh ze tashi ne ya bar mata d'akin ita d'aya, dan haka ya furta

"Ohk.. zaki iya tafiya, se da safe.." kallan sa ta cigaba dayi dan ita kam sam bata gajiya da kallan sa, jin shiru ya sanya shi sake fad'in

"Ko na bar miki d'akin ne?" yayi maganar in a serious tune, da sauri ta mik'e sannan tace

"Ohk bye luv, kayi bacci lafiya.." ta fad'a tana cigaba da kallan sa, ba tare daya kalle ta ba ya furta

"Ohk" ya k'arasa maganar yana janyo wayar sa dake gefen sa, babu yadda ta iya haka ta fice daga d'akin zuciyar ta a cunkushe, ita ta k'agu kawae ayi auren nan kowa ma ya huta. Number ta ta ya lalubo ya danna kira, a 6angaren ta tana kwance kan gadon ta hannun ta rik'e da wayar ta ta tana jiran kiran sa tun d'azun, ganin kira da wata sabuwar number ya sanya ta tashi zaune da sauri tana kallan jerin gwanon numbobin dake shimfid'e reras akan wayar ta ta, kamar yadda yake special haka number sa ma take special, haka kawae taji a jikin ta shi d'in ne dan haka ta sake kallan gadon su Jidda taga duk bacci suke sannan ta d'aga tana karawa a kunnen ta, kafin yace komae tace bayan ta tura bakin ta daga inda take

"Se yanzu ma zaka kira?" murmushi yayi daga inda yake yana kishingid'a a inda yake kwance sannan yace

"Am sorry.."

"Naqi ni dae, Allah kuwa tun d'azu fa nake jira ka kira" wani murmushin ya sake yi mara sauti yana karanto zallahr k'uruciyar dake tattare cikin maganar ta, da alama ko soyayya za'ayi da ita ba zata zama cikin mak'aryata ba, cikin k'asa da murya ya furta

"Amin afuwa Uhmm? Raj ne fa" ya fad'a da er tsokana a maganar sa, se tayi murmushi kawae

"Ina Umma? ina Abba? Ina Yah Sadeeq?" yayi maganar kamar ba Rk ba, seta sake gyara zama sannan tace

"Alhamdulillah kowa lafiya k'alau, ina Abbun ku"

"Abbu yana lafiya.."

"Raj!" ta fad'a dan ta k'agu ta masa tambayar data tsaya mata arae sosae

"Na'am" ya fad'a a nutse

"Kae likita ne?" murmushi yayi daga inda yake sannan yace bayan ya d'an lumshe idanun sa kad'an

"Yeah! likita ne, ki gyara zama na baki labarin rayuwa ta tun bayan rabuwar mu" kamar tana kusa dashi ta shiga gyara zama, dae_dae lokacin da Bahijja ta farka daga bacci saboda wani fitsari daya matso ta, ta kalli Ayrah dake zaune kan gadon ta sannan ta furta

"Ayrah" cike da mamakin ganin ta, da sauri Ayrahn ta juyo tana kallan ta, se dae ba tace komae ba har Bahijjan ta shige toilet d'in, babu dad'ewa ta fito memakon ta nemi waje ta kwanta seta zauna tana cigaba da kallan Ayrah, haushi ya kama Ayrah ta had'e face d'in ta tsaff, sannan cikin had'e ran dae ta furta

"Gobe zamu yi wayar" bata jira yace komae ba ta katse wayar sannan ta juya ta kwanta tana jin kamar ta tashi ta rufe Bahijja ta duka, cigaba da zama Bahijjan tayi dan so take ta gane da wanda take waya saboda abu ne da basu ta6a gani ba a wajen Ayrahn tunda tazo ba, kamar wadda aka tsikara ta janyo wayar data wulla gefe ta lalubo number Yah Sadeeq ta danna kira, se dae har ta tsinke be d'aga ba, ta sake kira nan ma dae be d'aga ba, a ranta kawae ta bada cewar may be ko bacci yake shiyasa be d'aga ba, duk da dae ta saba kiran sa a irin wannan lokacin kuma ya d'aga amma jiki da jini, k'ilan yau yayi wani aekin ne me wuya yasa yayi bacci da wuri, haka ta koma ta shiga lalubo number Abba.. se wata zuciyar ta zuga ta akan labarin baze musu armashi ta waya ba, kawae seta ajiye wayar tana murmushi a ranta tana sak'a gwara ta bari idan ta koma gida gata gasu Abban ta fad'a musu wannan babban albishir na cewar taga Raj, tasan suma za suyi farin ciki matuk'a k'ilan ma su fita farin cikin ko dan sanin da tayi iyayen nata na son farin cikin ta fiye da nasu....


Mhiz Innocent......✍️




https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd



*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*

*CHAPTER ONE*


✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨


Page 021_022



___Bata dad'e da kwanciyar ba taji wani

Please Login or Register in order to submit comment