Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan bayan tabbatar da ba zamu aura miki Raj ba, kiyi min afuwa Ayrah!" ta k'arasa fad'a tana sake jin wani irin takaeci, se da Ayrah ta sauke sheshshek'a sannan tace

"Umma ni ba abinda kuka min, wannan dalilin ne ma yasa nake ta sauri in dawo gida dan nasan za'a iya tunanin hakan, Umma ba kuyi laefi ba dan kun yi tunanin hakan musamman daya kasance a washe garin ranar da kuka hanani auren sa ne kuka neme ni kuka rasa.. Umma ni baku min komae ba, nice ma zan baku hak'uri.."

"Kuull..ki bar fad'in mu miki hak'uri Auta, babu abinda kika mana mu ma" Umma ta fad'a tana sakin Ayrahn, bata sake cewa komae ba se k'arasawa da tayi inda Abba ke zaune har lokacin, tsugunawa tayi tana kallan sa, dae_dae lokacin daya d'auke kae yana jin zuciyar sa na karyewa

"Abba..!" ta fad'a har lokacin tana kallan sa

"Ayrah je ki huta bazan iya cewa komae ba, kiyi hak'uri kawae.." Abban ya fad'a, wani irin sanyi taji yana ratsa kafatanin jikin ta, ko ba komae yau d'in gata ga iyayen ta kuma da alama sun yafe mata, gashi ma har neman yafiyar ta suke yi

"Abba ni zan nemi yafiyar ku don Allah.." Abba be iya cewa komae ba se girgiza kae kawae da yake yana ajje numfashi a hankali, Yah Sadeeq kuwa da yake gefe murmushi ne kawae ke fita daga kan fuskar sa, tana shirin mik'ewa dan komawa d'aki Abba ya juyo kamar wanda ya tuna wani abu

"Ayrah!" seta juyo a hankali tace

"Na'am Abba.."

"Kin san mutumin daya saka aka d'auke ki?" tsayawa tayi tayi shiru tana hasaso fuskar Alhaji Mato, kwata kwata ba zata iya cewa ga fuskar sa ba dan haka ta girgiza kae kamin tace

"A'ah Abba bansan shi ba.."

"Idan kika gan shi zaki gane shi?" shiru tayi tana nazari, ko da ta san shi ma bata tunanin zata iya gane shi ballantana bata san shi ba dan haka a nutse ta furta

"A'ah Abba.."

"Tashi kije Allah yayi miki albarka" lumshe idanu tayi kamin ta mik'e tare suka wuce cikin d'akin ta ita da Umma, shiru Abba yayi bayan barin su wajen yana nazari, ya zama dole ya gano mutumin daya d'auke masa yarinya ya kae ta wani waje dan a d'aura musu aure, idan kuma ya tuna da maganar auren Raj dake kan er tasa se ya sake jin jikin sa yayi sanyi, a yanzu be san wanene Raj d'in ba be san ko halin su d'aya da mahaefin sa ba, be san yadda za'ayi su kasance sirikae tsakanin sa da Kabeeru ba, abinda be ta6a tunanin ze kasance a rayuwar su ba, abinda ya guda tun farko, se dae gashi Allah yayi ikon sa akan su ta hanyar da basu ta6a zata ba, seya koma ya jingina bayan sa da jikin bango yana cigaba da sak'a da warwara.




... Da sallama ya shigo cikin d'akin hannun sa d'auke da envelope, Mummy dake zaune kan kujera ta mik'e tana fad'in

"Alhaji sannu da zuwa"

"Yawwah sannu kadae, ina Muneerahn? Na gan ki ke d'aya?" murmushi Umma tayi sannan tace

"Toh Alhaji ae dole ka ganni ni d'aya a kwanakin nan, kasan sha'anin amarya fa yanzu haka tana wajen gyaran jiki"

"Toh madallah, ga kati dae ya iso" ya fad'a yana mik'a mata envelope d'in hannun sa, da sauri ta sanya hannu ta kar6a da murmushi kan fuskar ta take fad'in

"Kae toh Masha Allah.." ta fad'a tana k'arasawa ta zauna kan kujera ta fara fito da katinan masu kyau da k'ayatarwa, girgiza kae Daddy yayi yana murmushi ganin yadda Mummyn ta shagala da kallan kati, ko bi ta kansa ba tayi ba hakan ne ya sanya shi jan k'afafun sa ya bar d'akin. Be dad'e da fita ba Muneerah ta shigo cikin d'akin cikin hijab har k'asa hannun ta d'auke da jaka da had'ad'd'iyar wayar ta, k'arasawa tayi da sauri kan kujerar tana kallan Mummy kamin ta saka hannu ta tu6e hijab d'in jikin ta, nan take shigar dake jikin ta ta bayyana, gajeran wando tiet ne a jikin ta da vest irin me bin jikin nan hakan ne ya bayyana yanda ta cika daga sama ba kamar da ba wanda ke nuni da siyo shi ba natural bane, haka zalika hips d'in ta ma sun k'aru ba kamar da ba dake kamar 1, kan ta babu d'an kwali se dae kamar ko yaushe a kitse yake da kitson attachment daya zuba a gadon bayan ta, ta k'ara wani irin mahaukacin fari bauu, fatar nan ta sake d'ashewa, da alama ba mae ta shafa ba se dae ko k'waya ko kuma allura

"Kin dawo?"

"Ehh Mummy, na gaji wallahi"

"Toh sannun ki, gashi nan kati ya iso" farr tayi da idanun ta kafin ta kalli katinan, seta saka hannu ta d'auki guda d'aya ta kalla ta shiga karantawa, sunan ta ne gashi nan ya fito 6aro 6aro dana Rk, wani murmushi ya k'wace mata tana jin ita kam burin ta ya gama cika daga lokacin data auri Rk d'in, ajiye katin tayi seta d'auki wayar data ajje a gefen ta kamar koda yaushe ta danno number sa, amsar d'aya ce dae kamar kullum baya kusa, bata gaji ba ta sake kira amma har ta katse be d'aga ba, a karo na 3 ta sake gwada kiran na sa cikin sa'a kuwa ya d'aga wayar se dae bece komae ba, daga inda take ta maraeraece fuska kamar za tayi kuka

"Haba Baby, ina ta kiran ka amma kak'i d'agawa, na maka magana ta whatsApp kak'i kula ni, ya kake so nayi? Auren mu saura kwanaki amma kak'i tsayawa muyi magana ko da akan shirye_shiryen bikin ne" tsaki ya saki akan la66an sa, ya kasa gane wannan dalilin na had'a auren sa da Muneerah, idan so suke zumuncin su ya d'ore ae ba dole seta hakan zasu biyo ba, shi abinda ma yake tsoro kada ace zumuncin su ya rabu saboda auren nan, dan a yadda yake ji har abada baze iya zama da wata a matsayin matar sa ba in dae ba Ayrah ba, toh ina ze kae ta?

"Yaya na!" ta katse masa tunani da fad'in hakan

"Wannan ne dama dalilin kiran?" ba tare data kawo komae ba tace tana murmushi

"Ehh shine kawae.."

"Ohk" ya fad'a yana katse wayar sannan ya jefar da ita gefe

"Hello" ta furta bayan jin kamar kiran ya katse, seta sauke wayar daga kunnen ta tana kalla cike da takaecin katse wayar ba tare da sun k'are maganar ba, seta cigaba da kallan wayar kamar me nazari ko kuma me kallan wani abun a cikin wayar

"Ke lafiya?" Mummy ta fad'a tana kallan ta

"Mummy, Yah Suraj ne mana, Mummy har yanzun fa baya d'aga waya na ya yake so zuciya ta tayi?" ta k'are maganar kamar zata fasa ihu, tsaki Mummy taja sannan tace

"Dallah rabu da shi, kwana nawa ya rage ya shigo hannun ki? Ke dae kawae ki maeda hankalin ki wajen gyaran jikin nan, dukkan magungunan nan ki tabbatar kina shan su kamar yadda suke a tsare, baki ga har kin fara chanjawa ba kina ta cika tako ina? ina me tabbatar miki a hannun ki zaki kama shi, dan kuwa da kan shi ze dinga bibiyar ki ba dae ke ki bi shi ba.."




_*Ina fatan yanzu kun fahimci abinda nake k'ok'arin nuna muku, kowanne abu idan kaga writer tayi akwae dalilin yin sa, akwae dalilin rubuta shi, babu yadda za'ayi kayi abu babu dalili, nayi hakan ne dan janyo hankalin wasu iyayen masu saurin yankewa 'ya'yan su hukunci ba tare da sun yi dogon bincike b duk kuwa sa irin yaddar da kayi musu, su kan su ae gashi nan yanzu sun yi nadamar hakan da suka yi, dama kuma shi novel ya gaji haka, na san dukan ku baku yi tsammanin Umma ko Abba wani a cikin su ze d'auka Ayrahn da kan ta guduwa tayi ba, dukan ku nasan kun ta'allaqa ne akan zasu zata sace ta akayi, wannan dalilin ne yasa na juya muku kwanya, babu yadda za'ayi abinda readers ke tunani kae kuma kayi shi a wani lokacin, dan kuwa littafin ze zama lami ne, ze zamana kowa da kowa yasan abinda ze faru a gaba kenan, wannan ba shine kyakykyawan novel ba wanda tun farkon fara karantawa kasan abinda ze faru a gaba. Ina fatan za'a dena tambaya ta dalilin da yasa nayi hakan.*_


Kuyi manage da wannan pls..



https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd



*CHAPTER TWO*


*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*



Page 037



___"Allah ko Mummy na?" Muneerah ta fad'a tana murmushi cike da jin dad'in zancen Mummy, murmushin itama Mummy ta maeda mata dashi kana tace

"Kada ki saka kokwanto a ran ki, kamar yadda na fad'a haka ne ze kasance" farr tayi da idanun ta dake d'auke da lashes na kanti, wanda da tasan yanda ya sake shigar da k'ananun idanun ta da bata saka ba, amma ita gani take haka zalika ji take baya ita, mik'ewa tayi tana kallan Mummy tace

"Yunwa nake ji Mummy kin gama abinci ne?" yamutsa fuska Mummy tayi sannan tace

"Se dae idan yunwar kike ji ki dafa ko indomie ce ki ci" bata sake cewa komae ba se hanyar kitchen data wuce kawae.



... Sanye yake cikin k'ananan kaya, fuskar sa ta sake yin wani shahararren kyau kamar wanda ake k'arawa kyau, haka zalika kwantacciyar sumar kan sa ta sake yin bak'i da sake kwanciya, jikin sa babu abinda ke tashi se k'amshin sassanyan turaren sa me dad'in shak'a, a nutse yake takawa zuwa part d'in Abbu cike da fata a cikin ran sa, cikin sa'a kuwa k'ofar parlourn nasa a kulle take, lumshe idanun sa yayi sannan ya bud'e ya d'an kalli gefe da gefe sannan ya sanya spare key d'in daya d'auko daga d'akin Ummee ya bud'e k'ofar, a hankali ya tura kan sa cikin d'akin, kamar wanda ya fara ganin d'akin yau haka ya soma wuwwulga idanun sa ko ina na cikin d'akin, cikin sauri ya shige bedroom d'in Abbun sannan babu 6ata lokaci ya soma bincika inda yasan Abbun na ajiye abubuwa masu amfani a cikin wajen, ya kae wajen minti 30 yana binciken be samu abinda yake nema ba, har cikin ran sa ya d'an ji sanyi kad'an akan zargin daya soma yiwa Abbun nasa, se kuma ya dakata abu na k'arshe dabe duba ba shine saman wardrobe, cikin sauri yanzun ma ya soma bincikawa har zuwa sanda ya d'akko wata leda, be bud'e ba seda ya sakko da ita k'asa, cikin k'ank'anin lokaci ya shiga fito da abinda ke cikin ta, bayan ledar akwae wata ledar a ciki sannan wata jaka, seya tsaya ya bud'e madaedaeciyar jakar dae_dae lokacin da wani envelope ya bayyana, haka nan kawae yaji jikin sa yayi wani mugun sanyi duk da har zuwa lokacin be san menene a ciki ba, a nutse ya shiga zaro takaddun dake ciki, be tsaya ba seda ya fiddo su duka kana ya saka hannu ya d'ago su cikin hannun sa ya shiga karantawa, a hankali yake karantawa kamar me tsoron karantawa ko kuma me koyon karatu, abinda dae yake guda d'in shine ya faru, wato sunan Abban su Ayrah daya fito 6alo_6alo a jikin takaddar, runtse idanun sa yayi na tsawon minti 1 yana jin 6acin rae, zafi gami da wani irin takaeci mara misaltuwa, meyasa Abbun sa yayi haka? Meyasa Abbun sa ya zamo cikin mutanen da za'a kiran su da butulu?

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" shine abinda ya shiga maemaetawa a cikin bakin sa har lokacin kuma bugun da zuciyar sa ke yi be saitu ba, ya kae wajen minti 2 a hakan sannan ya mik'e dan tuna a inda yake, beyi k'asa a gwuiwa ba wajen d'aukar ledar ya maeda ta saman wardrobe sannan ya d'auki envelope d'in ya fito dashi, karo suka kusa yi da Ummee dake shirin shigowa cikin d'akin, da mamaki take kallan sa

"A'ah Raj! dama kana nan? Abbun naku ya dawo ne?" seda ya d'aga idanun sa da suka yi d'an ja saboda 6acin rae sannan yace

"A'ah.." ya fad'a yana shirin wucewa

"Kae lafiyar ka kuwa a kwana biyun nan?" baya a mood d'in yin magana sosae, musamman kuma a yadda yake jin 6acin rae na taso masa haka nan ya sanya shi saurin girgiza kae sannan yace

"Lafiya ta k'alau.." daga nan yayi gaba yana cigaba da kare envelope d'in hannun sa

"A'ah wannan envelope d'in fa?" seya dakata da sauri kamar baze juyo ba se kuma ya d'an lumshe idanun sa sannan yace har lokacin be juya ba

"Takaddu ne akan asibiti, nazo d'auka ne saboda naga baya nan" jinjina kae Ummee tayi ba tare data kawo komae a ran ta ba kawae ta k'arasa cikin bedroom d'in yayin da shi kuma ya cigaba da tafiya, yana shirin fita daga d'akin Abbu ya shigo cikin d'akin sanye cikin farar dakakkiyar shadda, kallan sa yayi da mamaki yace

"A'ah Raj!.."

"Wajen Ummee nazo, tana bedroom.." shine abinda ya furta kawae ba tare daya kalli Abbun ba kuma be jira cewar sa ba ya fice daga d'akin, da kallo kawae Abbu yabi shi dashi sannan ya dawo da duban sa cikin d'akin yana girgiza kae. Kae tsaye d'akin sa ya wuce, babu 6ata lokaci ya jefar da envelope d'in hannun sa sannan ya nemi kan side drawer ya zauna, gaba d'aya kan sa ya matuk'ar kulle, ashe maganar Yah Sadeeq gaskiya ce? Ashe iyayen Ayrah basu yi laefi ba da suka hana shi auren ta? Tabbas Abbu ya shammace su ya yaudare su sannan ya saka k'afa yayi fatali da yaddar da Abba yayi masa bayan irin tarin hallacin da Abban yayi musu su duka, meyasa Abbun yayi haka? Abba mutum ne me kirki wanda ya d'akko su daga rana zuwa inuwa, amma Abbun daya tashi se ya d'auki Abban ya maeda shi cikin ranar shi kuma ya koma cikin inuwar

"Yah Allah! Why Abbu? Why?" ya fad'a a hankali yana cusa hannayen sa duka cikin sumar kan sa, gaba d'aya ji yake inama ace wannan abun ba gaskiya bane ba? Inama ace mafarki ne kawae yake yi, idan kuwa gaske ne ya zama dole ya nemowa kan sa da kuma shi kan sa Abbun mafita kamin lokaci ya k'ure musu, ranar gaba d'aya sukuku ya wuni, ko bacci be iya yi ba saboda wannan al'amari daya hargitsa masa kwanya.


.... A d'aya 6angaren kuwa kwanakin da suka biyo baya seya zamana wata kulawa ta musamman iyayen ke bawa Ayrah, kamar ma k'ara musu soyayyar ta akayi dan hatta kulawar data ke samu a yanzun tafi ta da, ita kam farin ciki take ji kamar tayi mene, tana kuma iya bakin k'ok'arin ta wajen ganin ta faranta musu ran su ba tare data 6ata musu ba.

.. Suna zaune su duka a tsakar gidan suna hira cikin farin ciki da k'aunar junan su, Ayrah na daga gefen Umman ta cikin doguwar rigar wani yadi me matsakaecin kyau fuskar ta yanzun babu laefi ta d'an samu albarkacin kwalli data saka, dan haka ya 6oye kaso da yawa daga yanda tayi zuru zuru, tayi kyau sosae duk da bayan kwallin babu wani abu data k'ara a fuskar ta, se kuma mayafi data yafa shi a kan ta ta zubo dashi kan kafad'ar ta, kallan Yah Sadeeq daya d'an rik'e k'afar sa tayi kana tace

"Yah Sadeeq k'afar ce?" murmushi yayi sannan ya girgiza kae kana yace

"A'ah Auta, ba k'afar bace ba.."

"Ayrah.. Je ki d'auko masa maganin nan ya shafa, kin san halin sa dae.." babu musu ta mik'e zuwa cikin d'akin dan d'akko masa maganin, dae_dae lokacin da wani yaro yayi sallama cikin gidan, dukan su suka amsa masa sallamar

"Wae a waje wani yace ayi masa iso.." Abba ya kalli yaron kana yace

"Waye?"

"Yace wae Raj sunan sa.." tana shirin fitowa taji sunan da aka ambata, seta dakata da sauri tana jin yanda bugun zuciyar ta ya k'aru, ko taku d'aya ta kasa k'arawa daga inda take kamar me tunani. Kallan Umma Abba yayi sannan ya maeda kan yaron yace

"Fad'a masa ya shigo" fita yaron yayi, ita kuma Umma ta koma d'akin ta ta d'auko babban mayafin ta ta yafa sannan ta fito ta nemi waje ta zauna, tunda taji Ayrahn shiru tak'i fitowa tasan taji wanda akace ze shigo, Ayrahn har mamaki take bata a kwanakin nan, duk irin yadda take k'aunar Raj d'in amma tun dawowar ta gida bata sake maganar sa ba, bata sake koda maganar abinda ya shafe shi ba, kuma duk Umman tasan hakan ya ta'allak'a ne da tun farko data fahimci basa k'aunar sa, toh amma yanzu kam yaya zasuyi tunda har igiyar aure ta ratsa tsakanin su?. Da sallama ya shigo cikin gidan sanye cikin bluen shadda jamfa da wando wad'anda suka matuk'ar yi masa kyau, se dae yanzu ma babu hula a kansa, kusan tare suka amsa masa sallamar sanda yake k'arasowa cikin gidan, a nutse ya tsuguna daga gefen tabarmar da Yah Sadeeq ke kae kan sa a k'asa ya furta

"Barkan ku da wannan lokaci.." cigaba da kallan sa Umma tayi, da alama har yanzu nutsuwar sa tun ta yarinta tana nan, haka zalika kamannin sa suna nan se dae kamar ma yanzun an k'ara masa kyau ne

"Barka dae.." Abba ya fad'a

"Ka zauna mana" Yah Sadeeq ya fad'a ganin har lokacin be zauna ba, shiru ya d'an yi yana jiran jin ta bakin wani daga cikin Abba ko Umma, kamar sun san me yake nufi kuwa se Umma tace

"Ka zauna mana" se a lokacin ya zame takalmin k'afar sa sannan ya zauna har kuma lokacin be kalle su ba, ya ajje envelope d'in dake hannun sa a gefen sa, seda ya d'an numfasa sannan ya fara magana a nutse

"Abba.. Zuwa nayi in rok'i alfarmar ka don Allah.. Sannan kuma in baka hak'uri akan abinda ya faru.. bazan 6oye maka ba Abba a lokacin da naga wani na na neman auren Ayrah hankali na ya matuk'ar tashi, nasan abinda ya kamata inyi shine in d'auko ta in dawo muku da ita, toh amma bani da tabbacin idan na dawo da ita zaku aura min ita, ko kuma ita ta amince da aure na saboda yadda ta nuna a lokacin kwata kwata itama ba zata ta6a aure na ba, kuma a lokacin bansan dalilin ta na hakan ba Abba yasa kawae na yanke shawarar neman auren ta acan d'in idan yaso idan muka dawo na shirya kar6ar koma wane irin hukunci ne, duk da banyi la'akari da ku yaya zaku d'auki al'amarin ba, amma don Allah kuyi hak'uri Abba, ku min afuwa don Allah.." ya k'are maganar yana sauke numfashi kamar baze d'ora ba se kuma ya janyo envelope d'in gefen sa ya cigaba da fad'in

"A yanzu na gano dalilin da yasa kuka hanani auren Ayrah Abba, ku dubi girman Allah ku yafe mana mu masu laefi ne, kuma yanzu haka gashi na dawo maka da takaddun ka badan mu biya ka abinda muka yi maka ba, a'ah inaso ne na fara warware wannan matsalar kamin inje gata gaba.." kallan envelope d'in Abba yayi sannan ya girgiza kae yana murmushi

"Shi Kabeerun ne ya aeko ka?" seda ya d'an yi shiru sannan ya girgiza kae cike da takaeci kana yace

"A'ah Abba.." sake girgiza kae Abba yayi dama yasan za'a rina

"Ka d'auki takaddun ka maeda su inda ka gan su, duk lokacin da Kabeeru ya gane yayi laefi kuma yana neman yafiya ta seya d'auko yazo ya bani, kada ka sake saka kan ka cikin wannan maganar.. Zancen aure kuma dani da mahaefiyar ta duk bamu so ba, ba kuma mu ta6a tunanin hakan ze kasance ba saboda abinda mahaefin ka yayi, se dae ya zamuyi? Allah ya riga ya rubuta ita matar ka ce, ko da ba ta hakan ba in dae Allah ya nufa se anyi auren nan se kaga dukan mu ma mun mutu kuma a d'aura muku auren, dan haka ni na yafe maka daga kae har Ayrahn in dae akan auren nan ne, na san iyayen ka ma basu sani ba saboda haka wannan ya rage naka kaje kayi musu bayani da kan ka, ku sasanta da kan ku.." a hankali ya lumshe idanun sa yana jin wani nauyi na raguwa daga cikin k'irjin sa, ko babu komae ya samu matsala d'aya ta kau, yanzu se yaji da d'ayar data rage masa

"Nagode sosae Abba.. Allah ya saka da alkhaeri.. Umma nagode" ya fad'a yana mik'ewa

"Allah ya tsare" Umma ta furta da murmushi kan fuskar ta dan seta ke ji kamar little Raj ne wanda ta sani tun shekarun baya, d'aukar envelope d'in yayi a ran sa yana sak'a lallae akwae aeki a gaban sa, Yah Sadeeq ne ya mik'e ya taka masa zuwa k'ofar gidan, be baro wajen ba seda Rk d'in ya hau motar sa sannan ya juya, ya kasa hak'urin rashin ganin ta tun shigowar sa dan haka ya furta

"Amm pls Yah Sadeeq bata nan ne?" juyowa Yah Sadeeq yayi kana ya d'an yi murmushi sannan yace

"A'ah tana d'aki, ko a kira maka ita ne?" da sauri ya girgiza kae yana d'an lumshe idanun sa, duk da yanda idanun sa ke k'ishirwar ganin ta amma gwara ya hak'ura dan haka ya furta

"A'ah barshi kawae nagode.." daga haka yaja motar sa ya bar layin yayin da shi kuma Yah Sadeeq ya koma cikin gida. Kallan Abba Umma tayi bayan fitar Rk d'in

"Abban su yaya wannan auren ze kasance kenan?" d'an shiru Abba yayi sannan yace

"Wannan ya rage nasa Ruk'ayya.."

"Ina ganin kafin ta koma ko kae zakawa Baban nasa bayanin yanda auren ya kasance?" da sauri Abba ya kalli Umma cike da mamakin jin kalaman ta

"Ruk'ayya kin san me kike cewa kuwa? Ashe har Kabeeru yayi arzik'in da zan je wajen sa yi masa bayanin wani abu? Bakya tunanin wani abu ze d'arsu a cikin ran sa?" ya k'are maganar yana girgiza kae sannan ya d'ora da

"Bana fatan wannan ranar tazo.." se kuma a lokacin itama Umman ta fahimci hakan dan haka ta furta

"Toh Allah ya kyauta, zamu iya bashi ita?"

"K'warae babu damuwa.." Abba ya fad'a. A hankali Umma ta yaye labulen d'akin ta shiga, tana kwance akan gadon ta kamar me bacci, k'arasawa Umma tayi kan gadon tana fad'in

"Ayrah wae bacci kike yi ne?" da zata iya shiru zata yi dan haka kawae take jin kunyar Umman tun zuwan Rk

"A'ah Umma" ta fad'a har lokacin tana kwance

"Toh tashi zamu yi magana.." Umma ta fad'a bayan ta nemi waje ta zauna, tashi zaune Ayrahn tayi tana had'e jikin ta kamar me jin sanyi

"Meyasa kika k'i fitowa ko gaesawa kuyi?" tura d'an k'aramin bakin ta tayi sannan tace

"Ummaaa.." taja k'arshen sunan, murmushi Umma tayi tana girgiza kae sannan tace

"Ki bar damun kan ki, In Sha Allah in dae mu ne mun amince da auren ku, dan haka ki bar damun kan ki haka nan, Allah ya tabbatar da alkhaerin sa" hannun ta ta d'auka ta rufe fuskar ta tana murmushi, duk da har lokacin akwae d'an haushin sa kad'an da take ji amma yanzu da Umman tayi magana taji matuk'ar dad'i, seta d'ora kan ta akan cinyar Umman kawae ba tare da tace komae ba

"Ayrah.." Umma ta fad'a tana murmushi..




... Kwanakin da suka biyo baya amarya Muneerah ta cigaba da shirye_shiryen aure, yayin da 6angaren ango Raj yama manta da maganar auren musamman ma daya kasance shi kan sa Abbun ya fita a harkar sa saboda yadda ya lura sam auren baya gaban sa, dan haka hatta lefe Ummee ce ta saka aka had'a aka kae, be tashi sanin suna nan kan bakar su ba duk da yanda aka bashi katin d'aurin aure wanda tunda ya ajje su be sake bi ta kan su ba ballantana ko gayyata ce yayi, se ana i gobe d'aurin aure ya sake tabbatarwa sanda yaga gidan nasu ya fara cika da jama'a, haka zalika har lokacin be huta da sak'onni da kuma kiran wayar Muneerah ba, wanda gaba d'aya baya kulawa ita kuma kamar tsohuwar mayya bata hak'ura duk da yadda Mummyn ta tace tayi watsi da shi ze neme ta da kan shi amma ita ta kasa hak'uri, shi gaba d'aya hankalin sa da tunanin sa ya ta'allak'a ne akan yanda ze sami Abbu suyi magana

Please Login or Register in order to submit comment