Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta tambaya tana jin wani irin haushi ganin har lokacin yama k'i kallan koda shigar jikin ta ne ballantana hakan ya tabbatar mata da ze iya jan hankalin sa, jinjina kae kawae yayi

"Amma meyasa? Amarya ce ni fa.." tayi maganar tana ji kamar ta rusa ihu, shiru yayi na en wasu sakanni kafin yace a nutse lokacin daya zubawa fuskar ta kyawawan idanun sa

"Ohk in zauna kada in yi abinda ke gaba na koh?" ya tambaye ta cikin tsare gida, seda ta zame nata idanun da yanzun ma suke d'auke da lashes na kanti kafin tace

"A'ah.. Ba haka nake nufi ba fa.." ta fad'a da er rikicewa da kallan da yake bin ta dashi, gefe guda kuma tana jin dad'i dan tasan yanzu kam tabbas yaga shigar jikin ta, abu d'aya take jira shine yayi wani abun daze nuna shigar ta ta ta tafi dashi, jin da tayi shiru har na wajen minti 1 ya sanya ta gyara tsayuwar ta tana d'an sake kad'a jikin ta kana tace

"Bari na baka waje Baby, ina jiran ka da safe kenan? Amma ina fatan ya kasance daga yau kuma ba zaka sake fita ba se mun gama cin amarcin mu" ta fad'a tana jin kamar ta sake rungume shi dan dae kawae ta tuna maganar sa ne ta d'azu kamar be ji dad'i ba hakan ne ya sanya ta fasa yi d'in se kamo hannun sa da tayi cikin d'arr d'arr ta zuba masa wani kiss da har seda ya bada wani sauti

"Muaahh" wato tayi shi cike da salo na jan hankali, se dae abinda bata sani ba shi kam ko a jikin sa, ya k'yale ta ne ma yanzun kawae dan kada ya zama mara adalci, amma daga shigar ta ta har abubuwan da take yi babu abinda ya ji shi cikin jikin sa, kwata kwata banda ma takaeci dake mak'ale a cikin ran sa. Cikin wani irin salo take takawa sanda zata fice daga d'akin tana wani karaeraya kamar zata 6alle, shi kam gogan naku bema san tana yi ba dan gaba d'aya hankalin sa yayi gaba wajen Ayrah ne.



... A 6angaren ta kuwa tunda ya fita da daren nan bayan ta gama kukan ta ta godewa Allah seta koma ta zauna tayi shiru zuciyar ta fall cike da tunani, seda ta d'an jima cikin d'akin sannan kuma ta fara jin wani irin tsoro na ratsa ta, a hankali take duban k'ofar d'akin se taga kamar wata inuwa ta gifta, da sauri ta runtse idanun ta tana jin yadda ilahirin jikin ta ke rawa, tunda take zata iya cewa bata ta6a kwana a waje ita d'aya ba, ta saba da jin motsin mutane kafin tayi bacci, se dae yau kwata kwata bata jin motsin komae shiru ne kawae ya ratsa ko'ina, haka kawae tayi ta tsarguwa, da dae ta gaji gaba d'aya se kawae ta koma kan gadon ta shige cikin blanket gaba d'ayan ta, tayi lamo tana jin wata k'walla na sakko mata, har lokacin bugun zuciyar ta be koma normal ba haka zalika tsoron be ragu ba, dae_dae kuma lokacin da er k'aramar wayar ta tayi k'ara, k'arar data sake rikita ta, take jikin ta ya cigaba da rawa kamar mazari zuciyar ta na cigaba da harbawa, seda ta soma nutsuwa sannan ta fahimci ringing d'in wayar ta ne, ta d'an lumshe idanun ta a hankali kana ta mik'a hannun ta har lokacin tana cikin bargon ta d'auka, ba tare data duba me kiran ba kawae ta d'aga wayar ba tace komae ba se sauke numfashi da take akae_akae kamar wadda tayi tsere

"Auta!" ta jiyo muryar Yah Sadeeq, wata sassanyar ajiyar zuciya ta saki sannan ta kwa6e baki da murya tace

"Yah Sadeeq.." duk da yanda yaji muryar ta amma be kawo komae ba saboda ya riga ya san halin Ayrah ciki da bae

"Shine kika tafi babu ko sallama koh?"

"Kae Yah Sadeeq, Abba ne fa yace wae mu tafi.." murmushi yayi kana yace

"Toh shikenan Allah yayi miki albarka Auta, ya baku zaman lafiya, duk sanda na samu lokaci zan shigo mu gaesa dan har na fara missing naki" zuciyar ta ce ta sake karyewa amma dan gudun kada ta tayarwa da Yah Sadeeq d'in hankali ya sanya ta fad'in

"Nima haka fa.." tayi maganar a sanyaye, babu laefi sun d'an jima suna hira a wayar, wadda ta kwashe kaso da yawa cikin damuwa da kuma tsoron da take ji kafin daga bisani suka yi sallama, zuwa lokacin dama ta fara jin bacci, dan haka cikin sauri ta k'ank'ame idanun ta ta rufe su ruff tana jiran d'aukar baccin. Barcin daya d'auke ta dududu befi na awanni 2 ba, data fara baccin seta firgita ta tashi, dan haka tun kafin asuba ta mik'e zaune, zuwa lokacin tsoron nata ya d'an soma raguwa kawae seta fad'a toilet tayi wanka sannan ta fito ta tayar da sallah, bata tashi daga kan daddumar ba se wajen k'arfe 8 kana ta mik'e ta koma kan gadon zuciyar ta a matuk'ar karye, idanun ta sun cika taff da hawaye..

Wajen k'arfe 10 ya isa Hotel d'in yayi parking motar sa sannan ya sauka kae tsaye ya wuce d'akin, a nutse ya saka mukullin hannun sa ya bud'e sannan ya tura k'ofar d'akin kana ya tura jikin sa cikin d'akin, acan tsakiyar gadon ya hango ta ta lullu6e jikin ta da bargo kan ta akan gwuiwar ta tayi shiru idanun ta akan k'ofar, ganin sa da tayi ya sanya zuciyar ta saurin karyewa bata san sanda wasu hawaye masu d'umi suka fara sintiri akan kuncin ta ba lokaci d'aya kuma tana cusa kan ta cikin k'afafun ta, runtse idanun sa yayi yana jin wani irin tausayin ta na ratsa shi, cike da sassarfa ya k'arasa cikin d'akin, kae tsaye ya haye kan gadon beyi wata wata ba ya jata cikin jikin sa yayi mata wata kyakykyawar runguma, dae_dae lokacin data fashe da kuka kenan me cin rae tana sake jin wani irin rauni a tare da ita, sake rungume ta yayi yana jin yadda bugun zuciyar ta ke fita da sauri da sauri, a hankali ya d'ora kan sa akan ta dake kan k'irjin sa sannan ya shiga shafa bayan ta a hankali lokaci d'aya wani tausayin ta na sake lullu6e shi, sosae take yin kuka wanda ke fita tun daga k'asan zuciyar ta, shi kuma be hana ta ba se dae har lokacin be dena shafa bayan nata ba, a hankali cikin rarrashi ya furta sanda ya kae bakin sa cikin kunnen ta

"Kukan ya isa haka plsss.." ya k'arasa yana jan k'arshen maganar tare da hura mata iska a cikin kunnen na ta lokaci d'aya kuma yana sake shigar da ita cikin jikin sa, a hankali ta shiga rage sautin kukan na ta, har zuwa sanda ta koma sauke ajiyar zuciya, se a lokacin ya saki k'atuwar ajiyar zuciya sannan yace a hankali

"Am sorry, am deeply sorry pls.." ba tace komae ba har lokacin kuma be sake ta ba dan sosae yake jin nutsuwa da take cikin jikin na sa

"Plss Babe.." ya sake fad'a nan ma dae a hankali kamar me rad'a, kamar jira take suma kuma hawayen kamar jira suke se suka zubo kan fuskar ta sannan ta fara maganar cikin raunanniyar murya

"Don Allah kada ka sake tafiya ka bar ni anan kaaji?" tausayin ta ne ya sake kama shi, shi kan sa baya son barin ta amma babu yadda zeyi dole se dae ya raba kwanan ko da d'ad'd'aya ne, yau idan ya kwana anan gobe ya kwana acan

"Toh In Sha Allah" ya fad'a sannan ya d'ora da

"Nan d'in ne bakya so?"

"Tsoro nake ji ni dae, bana son nan gaba d'aya" tayi maganar tana k'ok'arin tashi daga jikin na sa, kamar kada ya sake ta amma seya sake ta d'in a hankali, se kuma a lokacin ya fahimci yanda ilahirin jikin sa yayi wani mugun sanyi, wata iriyar kasala ta gama rufe shi kamar kada ya motsa daga inda yake

"Shikenan.. Zan fita na samo gidan da zamu zauna kafin komae ya daedaeta.." da sauri ta d'aga narkakkun idanun ta ta kalle shi jin da tayi yayi zancen fita, ya fahimci abinda ya sanya ta kallan na sa ba tare da ta shirya ba dan haka ya d'an yi murmushi kana yace

"Kar ki damu da rana zan fita, dama Abbu na nema na, sena biya ta wajen su Abba ma mu gaesa"

"Don Allah zan bi ka.." ta fad'a da sauri bayan ta rik'o hannun sa, hannun nasu yabi da kallo saboda yanda ya sake jin tsigar jikin sa ta tashi, ganin inda yake kalla ya sanya itama ta kalla, da sauri ta saki hannun nasa tana tura k'aramin cute lips d'in ta, nan ma seya sake bin bakin nata da kallo lokaci d'aya yana lumshe lumsassun idanun sa, ya kae wajen second 30 a haka sannan ya bud'e yana kokawa da zuciyar sa yace

"Muje kici abinci"

"Na ci kafin ka shigo!" ta fad'a ba tare da ta kalle shi ba

"Kin ci?" ya fad'a yana kallan ta sosae, seta jinjina kae kawae tana sake kaucewa kallan daya ke bin ta da shi, jin bece komae ba ya sanya ta sake fad'in

"Allah kuwa kuma ka duba ka gani idan ban ci ba" ta fad'a tana nuna masa abincin da ke ajje, seda yabi wajen da kallo sannan ya dawo da duban sa kan ta yace

"Matso kiyi bacci kafin na dawo.." yayi maganar yana kishingid'a akan gadon lokaci d'aya yana mik'a mata hannun sa d'aya, tura bakin ta gaba tayi kafin tace

"A'ah.." ta fad'a tana d'ora kan ta akan kafad'ar ta, tilas abinda tayi d'in ya sanya shi lumshe idanun sa yana sakin murmushi, hannun sa ya kae kawae ya janyo ta se gata cikin jikin sa, ya gyara kwanciyar sa sannan itama ya gyara mata ta ta kwanciyar cikin jikin sa duk da yanda take ta neman k'wacewa daga jikin nasa, wanda hakan ya bawa ma6allan rigar jikin sa na sama damar 6allewa, hakan ne ya bawa kyakykyawar farar fatar sa me d'auke da bak'a sid'ik d'in gargasa bayyana, ba tare daya lura ba ya sake manna ta da k'irjin sa, hakan ne ya bawa kan ta damar kwanciya akan zallahr fatar sa dake ta tashin wani sassanyan k'amshi, k'atuwar ajiyar zuciya ya sauke sanda hakan ya faru, ya lumshe idanun sa bugun zuciyar sa na k'aruwa

"Kiyi bacci" yayi k'ok'arin lalubo kalmomin biyu ya had'a ya fad'e su, ita kan ta sosae zuciyar ta ke bugawa musamman ma jikin ta dake ta rawa kamar mazari, amma duk da haka be sake ta ba, ganin bashi da alamar sakin ta ne ya sanya ta hak'ura ta runtse idanun ta tana jiran zuwan bacci, cikin ikon Allah kuma babu dad'ewa baccin ya d'auke ta seta koma tana sauke numfashi akan k'irjin sa, wanda hakan ya sanya shi saurin lumshe idanu gami da janye ta daga jikin sa a hankali yana jin yanda bugun zuciyar sa ke cigaba da k'aruwa fiye da d'azun, ba zeso wani abun ya shiga tsakanin sa da Ayrahn a Hotel ba, ba dan haka ba yau yadda yake jin sa babu abinda ze hana shi bin abinda zuciyar sa ke raya masa duk da yadda ita kan ta Ayrahn har yanzu bata koma asalin Ayrahn ta ba. Seda ya shiga toilet ya watsa ruwa sannan ya fito har lokacin tana baccin ta a nutse babu hayaniya, da alama dama baccin jiyan be wani wadace ta ba, hakan ne ya sanya shi saurin shiryawa ya fice yana fatan har ya dawo bata farka daga baccin ba, kafin nan ya samo musu mafita.


... Sanda ya isa gidan kae tsaye parlourn Abbu ya wuce dan yana da tabbacin yana nan, da sallama ya shiga d'akin, Abbu dake zaune kan kujera hannun sa d'auke da laptop yana aeki ya amsa sallamar har lokacin be d'auke idanun sa daga kan laptop d'in ba, a nutse ya k'arasa cikin parlourn ya zauna a k'asan had'ad'd'en carpet d'in dake malale a tsakiyar d'akin

"Barka da safiya.." ya fad'a yana kallan Abbun, se a lokacin Abbu ya sauke ajiyar zuciya sannan ya rufe laptop d'in ya ajje ta gefe kana yace

"Barka dae doctor ya Muneerahn?"

"Alhamdulillah.." ya fad'a a nutse

"Ya kamata ka koma bakin aekin ka haka nan likita.. Kasan bana son zama haka nan, ko kuma dae kada wannan satin ya cinye baka koma ba.."

"In Sha Allah" Rk ya fad'a, a ran sa yana sak'a ta yadda ze fara yiwa Abbu zancen Abba, sam be san ta inda ze fara ba, ko ya sak'a ga ta inda ze fara d'in se yaga beyi ba seya bar shi, ya kuma tsarawa yaga beyi ba ya kuma barin sa. Wayar Abbu ce tayi k'ara, ya kalli me kiran nasa sannan yace sanda wayar ke hannun sa yana shirin amsawa

"Bari na amsa kira.." yayi maganar yana kara wayar a kunnen sa, be san me suke tattaunawa cikin wayar ba se dae kawae yana jin Abbun na magana da alama akan kud'i ne suke magana, magana ta k'arshe da Abbun yayi itace taja hankalin sa

"What? Me kake nufi? Wallahi baze ta6a yiwuwa ba, idan ma makirci kake k'ok'arin shiryawa ka fasa yi, dan kuwa ni ba shashasha bane, 50 millions wasa ne?" yayi maganar cikin d'aga murya kuma cikin 6acin rae, lokaci d'aya kuma yana jefar da wayar gefe sannan ya koma ya zauna kan kujerar da6ass zuciyar sa na bugawa

"Abbu lafiya kuwa?" shine abinda ya iya furtawa yana kallan Abbun da gumi ke tsatstsafowa akan fuskar sa duk da yadda sanyin A.C ke ratsa gaba d'aya parlourn, kamar jira yake yi ae kuwa ya soma fad'in

"Ni Mukhtar ze yiwa shashanci? Tunda nake ban ta6a yadda da kowa ba bayan kae da d'an uwa na, ta yaya ma zan yadda da wani inje yaci amana ta, ban san kuma wane tsautsayin ne ya sanya na bawa Mukhtar har 50 millions ba, se gashi mutumin banzan nan na fad'a min wae an masa kutse cikin Account d'in an kwashe duka kud'in, shin wannan maganar kamawa ce? Ni ze mayar mutumin banza? Toh wallahi seya fito dasu, k'arya yake yi so yake ya cuce ni Allah ya kama shi, nayi dana sanin shigar da bare cikin harkar kud'i na, toh wallahi se yayi kashin kud'in nan ko zeyi mene, millions 50 fa?" Abbu ya k'arashe maganar yana mik'ewa har lokacin yana jin zafi cikin k'irjin sa, sam ya kasa zama se safa da marwa yake cikin d'akin daga k'arshe ma seya haye sama kawae ya bar Rk da tunda ya fara magana bece masa uffan ba a zaune. Bin sa yayi da kallo sanda ya ida hayewa saman kana ya dawo da duban sa cikin parlourn, lumshe idanun sa yayi cike da takaecin halin mahaefin nasa, be so haka halin sa yake ba, amma duk da haka zeyi k'ok'arin chanja shi, se dae wannan kad'ae ya isa ya nuna maka Abbun na tsoron kada a aekata masa abinda yayi wa Abba shiyasa tun farko yak'i yadda ya shigar da bare cikin harkokin kud'in sa, se dae yau gashi ya shigar kuma an samu akasi, amma da yake shi ga abinda ya aekata sanda aka yadda dashi se yake ganin kowa ma haka ne, cutar sa akayi aka ci amanar sa ba tsautsayi bane. Sosae zuciyar Rk ke zafi, daze iya da yau d'in ze sanar da Abbu yasan komae game da zancen su shi da Abba, da irin abinda ya aekata masa, daze iya daya tsaya gaban Abbun ya fad'a masa abubuwan dake ta yawo a cikin kan sa, se dae baze iya ba, har lokacin Abbun na matsayin uban sa ne shiyasa yake neman hanya mafi sauk'i daze isar da sak'on sa wajen Abbun, koda hakan ze saka Abbun yayi nadama ya nemi yafiyar Abba akan abinda yayi masa shi da iyalin sa, ya tarwatsa musu farin ciki da rayuwar jin dad'i zuwa ta k'unci, baya so ya bar Abbun se ranar al_k'iyama sa had'e da Abba, sam baya fata hakan ya kasance. Mik'ewa yayi a hankali dae_dae lokacin da yake lumshe idanun sa lokaci d'aya ya fesar da huci daga bakin sa, be san me ze cewa Abbun ba koya shiga cikin d'akin, be san da wane baki ze yiwa Abbun magana ba, dan ze ga kamar idan yayi maganar zata zama kamar magana ce a fakaece yake fad'awa Abbun, hakan ne ya sanya shi jan k'afafun sa ya bar d'akin..

.... Da mamaki Abba ke kallan Alhaji Mato dake tsaye k'ofar gidan nasa jikin wata hamshak'iyar mota er uban su, lokaci d'aya annurin fuskar sa ya gushe, kamar ya juya ya koma se kuma ya kalle shi yace a nutse

"Me ya kawo ka k'ofar gida na?" wani murmushin gefen baki Alhaji Mato ya saki kana ya sanya hannu ya gyara zaman babbar rigar jikin sa, hannu ya mik'awa Abba bayan ya matsa kusa dashi sosae yace

"Ae ka bari mu gaesa koh?" ya fad'a da murmushin da Abba ya kasa gane manufar yin sa

"Kaaga zaka fad'i abinda ya kawo ka ko kuma nayi tafiya ta?"

"A'ah ae bata kae ga nan ba Alhaji Kabeeru.." ya k'are maganar yana sakin wata dariya kafin ya d'ora da

"Wannan zuwan ae ba nawa bane naka ne" ya k'arasa maganar yana nuna Abban, da mamaki Abba ya cigaba da kallan sa dan yau d'in gaba d'aya Alhaji Maton ya chanja kamar bashi ba yana wasu abubuwa a juye wad'anda ya kasa gane su, jin Abban bece komae ba ya sanya shi fad'in

"Zuwa nayi a bani kud'in da nayi asara akan d'iyar ka, dubban kud'ad'en dana kashe akan karatun ta, dubban kud'ad'en dana kashe dan naga ta zama wata amma saboda bak'in ciki irin naka wanda har d'iyar ka ma bakya k'yale ba ka saka k'afa kayi fatali dani d'in dae dazan rufa muku asiri.. Saboda haka yanzu base gobe ba ka shiga gida ka fito min da kud'i na gaba d'aya kada ko naira 5 tayi ciwo, dan kuwa babu inda zan je se kud'i na sun fito.." Alhaji Mato ya fad'a yana cigaba da kallan yanayin Abban daya chanja lokaci guda..


Mhiz Innocent....✍️




An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment