Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bacci na sakad'ar ta, se dae har lokacin bata hak'ura ba ta sake juyawa ta kalli inda Bahijja ke zaune tun d'azun, ga mamakin ta a wannan karon ma seta sake ganin ta zaunen dae tana danna waya, bata san sanda wani tsaki ya su6uce mata ba, se kawae ta hak'ura ta lumshe idanun ta amma mamaki ya cika zuciyar ta na Bahijjan, babu 6ata lokaci kuwa wani daddad'an barci me cike mafarkan Rk ya kwashe ta, ba ita ta farka ba se asuba. Yau ma kamar kullum da wuri suka gama shiryawa kasancewar ranar Monday ce, Monday d'in data kasance daga ita seta exam d'in da zasu fara, haka kawae taji tana jin haushin Bahijja amma kuma data tuna za tayi tozali ne da Rk se wani murmushi ya su6uce mata, a wannan karon Jidda ce kawae ta lura da murmushin wanda tun jiya ta lura da sauyawar Ayrahn, ta kasa hak'uri seda ta kalle ta tace

"Ayrah wae meya faru naga daga jiya zuwa yau yanayin ki ya chanja?" d'an kallan ta tayi sanda take saka wani littafi cikin jaka sannan ta d'an ta6e baki kamar wadda ta gaji kana tace

"Ni fa ba komae nace"

"Haka kike ta fad'a tun jiya, Allah yasa haka ne" Jidda ta fad'a tana cigaba da nazarin ta, ba tace komae ba se d'an tura bakin ta da tayi tana k'arasa shirya kayan jakar ta, a ran ta se k'una k'uni take akan takura mata da suka yi tun jiyan.


.. Tunda suka zauna jin su kawae take suna hira amma bama ta jin abinda suke cewa ballantana ta fahimta, gaba d'aya hankalin ta ya karkata ne ga son ganin ya shigo cikin ajin, ba'a k'ara minti 1 ba kuwa se gashi ya shigo cikin ajin dae_dae lokacin da ilahirin ajin ya d'auki shiru, lumshe idanun ta tayi tana shak'ar k'amshin sassanyan turaren sa me dad'in gaske sannan ta bud'e tana maeda duban ta kan fuskar sa da taga ta k'ara kyau fiye da jiya, se kawae ta shagala da kallan sa, yau d'in duka ya juye mata ya sake komawa Doctor Rk d'in sa babu fara'a yana yin komae ne cikin tsare gida, yau karon farko taji yanayin da yake d'in ya burge ta, ta san da yana sakin fuska kuma matan da za suce suna son sa se sun fi na yanzu yawa, tana jin sa ya fara magana cikin nutsuwa k'warewa da kuma takatsantsan amma sam bata fahimtar abinda yake fad'a d'in, kawae dae ta san magana yake amma ita bin sa kawae take da kallo kamar wata doluwa tana jin kamar ta had'iye shi amma duk bata san dalili ba, wayar ta dake rik'e a hannun ta ce tayi vibrate daga hannun ta, ta d'an dakata tana jin kamar ta share wayar se kuma tayi k'asa da kan ta ta duba wayar, d'an k'aramin sak'o ya bayyana akan wayar, seta shiga da sauri ta shiga karantawa ganin daga number da yake

"Kallan fa?" shine abinda ke rubuce cikin message d'in daga number Rk, a'ah mamaki ne ya kamata har bata san sanda ta d'aga kae ta kalle shi ba, gashi dae anan lecturing d'in sa yake hankali kwance, toh kenan yaushe ya turo mata da message d'in? Toh yaushe ma ya gan ta tana kallan nasa, dan dae tunda ta zauna ba taga idanun sa akan kowa ba ballantana tace ya gan ta, a hankali ta sake maemaeta message d'in, se ta kae hannun ta ta rufe fuskar ta tana murmushi tuna duk kallan data masa ashe yana ganin ta? Lallae shi d'in na musamman ne

"Ke meye haka wae?" Bahijja da tun d'azu take lura da duk wani motsin Ayrahn ta fad'a k'asa k'asa, da sauri Ayrah ta kalle ta ba tare da tace komae ba ta d'auke kae

"Anya kuwa wannan yarinyar?" Bahijja ta fad'a a k'asan ran ta cike da mamaki, ita dae Ayrah bata sake bi ta kanta ba ta koma maeda hankali kan karatun da yake koya musu, amma duk iya k'ok'arin ta na ganin ta fahimta d'in ta kaasa, se kace wadda aka sanyawa hannu, a haka dae har ya gama lectures d'in baza tace ga abinda ta d'auka ba.



... Sanda suka koma Hostel bata lura da message d'in sa ba har seda ta zauna sannan taga message d'in nasa, da sauri ta shiga message d'in tana jin zuciyar ta na wani d'an bugawa a hankali kamar me jin tsoro

"Nan gaba da face mask zan dinga shiga class, idan ba haka ba wataran za'a neme ni a rasa kin cinyewa su Abbu ni" komawa tayi ta kwanta kan gadon ta tana sakin wata dariya gami da rufe fuskar ta, ashe dae duk yana sane da ita duk kallan da take bin sa da shi yana gani, ita kan ta ta rasa gane abinda ya shiga kan ta ta kasa d'auke idanun ta daga kan sa, tana ji kuma kamar idan ta dena kallan sa zata bud'e ido taga baya nan, mik'ewa tayi ta fita daga cikin d'akin dan lokacin duk su Jidda suna ciki, suka bita da kallo kowacce da abinda take sak'awa a ran ta, amma abinda yafi damun kowaccen su shine chanjawar ta ta cikin lokaci k'ank'ani.




.. Gyara zaman sa yayi kan kujerar da yake zaune kana a hankali ya furta

"Kin wuni lafiya?" seta lumshe idanun ta sannan tace

"Ehh.." murmushi yayi bayan ya d'an yi jimm kad'an yace

"Ina fatan bakya fita daga cikin makarantar nan?" seta d'an bud'e manyan idanun ta kamar tana gaban sa, sosae yadda ta bud'e idanun yayi mata kyau, sannan ta rufe bakin ta tace a hankali

"Ta66, ae na yiwa Yah Sadeeq alk'awarin bazan ta6a fita ba" ta fad'a a sakarce, yayi murmushi yana sake gyara zama muryar ta na masa wani irin dad'i yace

"Dats my Ayrah" itama murmushin tayi sannan ta dakata sanda yake furta

"Next week exam Uhmm?" kamar tana gaban sa ta jinjina kae kawae, shi kuma kamar yaga abinda tayi d'in yace

"Idan anyi hutu In Sha Allah zan zo, may be ma har da su Abbu" yayi maganar a nutse, hakan ba k'aramin dad'i ya mata ba tana murmushi tace

"Buhh baka bani labarin ba" ta fad'a tana tura bakin ta gaba, iska ya d'an fesar daga bakin sa sannan yace

"Ohh am sorry.." yayi maganar yana d'an dakatawa, yana tunanin tsayin maganar da zeyi, ya san tabbas ze dad'e yana yin ta abinda ya tsana kenan, dan haka ya janyo rubber water ya tsiyaya cikin tambulan ya sha, ya d'an sauke numfashi a nutse sannan ya d'ora da

"Tun bayan rabuwar mu, Allah ya bud'ewa Abbu sosae, harkokin da yake yi sosae suka samu kar6uwa a wajen mutane, ban san meyasa tun bayan rabuwar mu daga mu har ku babu wanda ya sake waewayar wani ba, bansani ba, abinda kawae na sani na sha tambayar su Abbu ku amma bana samun cikakkiyar amsa wadda zan kama daga wajen sa, tun ina tambayar sa har nazo na dena tambayar sa, se dae har lokacin kina nan manne a rae na, ina jin ki ne acan cikin zuciya ta wanda hakan ne yasa na kasa manta ki a duk tsayin shekarun nan, a cikin wannan lokacin ne na gama secondary school kullum arzik'in Abbu yana yin gaba, dan haka dana tashi yin University ba'a nan nayi ta ba, sena tafi can Cyprus na karanci Medicine, yanzu haka ni cikakken likita ne, muna zaune anan cikin garin Kano saboda harkokin Abbu da suka cigaba, yanzu haka ina da asibiti na kae na wanda shima Abbun ne ya bud'e min, abinda ya kawo ni garin nan kuwa, sanadin k'anin mahaefi na ne da nazo sanda ze bud'e wani Company, tunda nazo kuma Abbu yace kar na zauna haka nan shi ya nemar min wannan lecturing d'in cikin makarantar nan duk da ni ba za6i na bane, da son raena ne aekin da nake kawae ya ishe ni, toh dae dan farin cikin Abbun yasa na fara lecturing d'in, se dae yanzu maganar da nake miki tuni Daddy (k'anin Abbu) ya gama bud'e Companyn komae ya kammala, dan haka ina saka ran ni kam daga wannan semester na gama koyarwa a makarantar nan... And.. ina me tabbatar miki In Sha Allah duk sanda muka had'u zan baki labarin a nutse" ya k'arasa maganar yana sauke wani gauron numfashi lokaci guda kuma yana 6alle murfin gorar ruwan daya ajje ya shanye tass sannan ya ajje ta yana sauke numfashi, dariya ya bata daga inda take zaune jin yadda yake sauke numfashi kamar wanda yayi wani aekin wahala, se dae kuma a ran ta tana cigaba da mamakin rayuwar Rk d'in, lallae Allah abin godiya ne da kuma d'aukaka, dan kuwa shine me yin yadda yaso a kuma lokacin daya ga dama

"Uhmm, fad'a min kad'an daga naki kafin mu had'u" sauke numfashi Ayrah tayi sannan a hankali ta shiga sanar dashi makarantar da tayi da er gwagwarmayar da tasha har zuwa yanzun, duk da ba wasu shekaru ne da ita na azo a gani ba, ga kuma ga6un ta dake damun ta, amma duk yadda take ganin Raj d'in take kuma jin sa a jikin ta bata sanar dashi abubuwa da dama daga rayuwar su ba wanda take ganin kamar sirrin su ne wannan da ba kowa ya kamata ya sani ba, shiru Rk yayi yana nazarin maganganun Ayrah a ran sa yana sake tsarkake sunan Allah

"Ikon Allah" kuwa ya maemaeta yafi sau nawa

"Akwae wata magana dana ke so muyi, amma kafin nan ina so ki gama exam kafin ki koma gida.."

"Wace maganar toh?" ta fad'a kamar za tayi kuka, murmushi me sauti yayi sannan yace

"Ae nace se kin gama exam tukunnah" shiru tayi tana tuna yanayin Rk d'in a cikin aji da kuma yanzun kamar bashi bane, kamar mutum biyu ne masu kama d'aya wanda wancan da yake shigar musu aji daban shi kuma wannan da suke waya daban

"Promise?" ta fad'a tana d'aga yatsan hannun ta kamar yana gaban ta

"Yeah.."

"Ohk". Wayar sa da tayi k'ara bayan ajiye wayar Ayrah yabi da kallo, ji yayi kamar kar ya d'aga dan a yanzun yana so ne ya dinga samun lokacin daze zauna kawae ya dinga hasaso kyakykyawar fuskar ta, kallan wayar yayi dan ganin me kiran nasa, seya kae hannu ya d'auki wayar ganin Daddy ne ke kiran, ya kae kunnen sa da sallama d'auke a bakin sa

"Likita kana ina ne?"

"Ina d'aki" yayi maganar cikin girmamawa

"Ohk ka same ni a d'aki na idan babu abinda kake" babu musu ya amsa da "toh" sannan ya mik'e bayan ya jefa wayar a aljihun sa ya zura takalmi ya fito daga d'akin nasa cikin nutsuwa. Kae tsaye parlourn Daddyn ya wuce, a hankali ya zura kan sa ciki yanzun ma da sallama a bakin sa cikin nutsatsiyar muryar sa, amsawa Daddy yayi yana kallan sa lokacin da yake k'ok'arin zama a k'asa

"Tashi ka zauna akan kujera magana nake so muyi ae" seya d'an yi murmushin nan nasa me tsada wanda ke sake fito da aenahin tsagwaron kyawun sa ya zame akan kyakykyawan Carpet d'in dake shimfid'e a k'asan d'akin yace

"Daddy nan ma ya isa" murmushi Daddy yayi a ransa yana sake jaddadawa kan sa lallae abinda suka yanke ba suyi laefi ba

"Amm yaushe zaku yi hutu ne?" seda ya d'an yi shiru sannan yace

"Ina tunanin baza mu wuce 1 month ba"

"Toh Allah ya taemaka, me kake shirya mana zuwa lokacin?" yamutse fuska yayi dan shi sam bema fahimci maganar Daddyn ba dan haka ya furta abinda ke ran sa

"Daddy ina ganin zan ajiye lecturing d'in nan gaskiya am tired" ya fad'a dan da gasken ya gaji da lecturing d'in musamman daya kasance dama ba za6in sa bane, ga kuma muhimmiyar maganar da yake so daya koma yayi wa Abbun magana akae, wadda yake had'e da albishir d'in daze fad'a musu su duka cewar bayan tsawon shekarun nan ya had'u da Ayrah, wanda hakan na nufin Abbu ze had'u da Abba, may be ma abotar su ta da ta dawo sabuwa duk da be san abinda yasa kowa yayi watsi da d'an uwan sa ba

"Haba haba dae Raj ka gaji kuma?" jinjina kae yayi ba tare daya kalli Daddy ba

"Toh ya za kayi da Abbun ka kuma?" Daddy ya tambaya yana kallan sa

"Zan same shi da maganar In Sha Allah"

"Toh hakan ma yayi, seka maeda hankalin ka waje guda kenan, Allah ya taemaka.. Ameen" shiru ne ya biyo baya Daddy na tunanin ta inda ze farawa Rk maganar se can dae yayi k'arfin halin fad'in

"Kana jina koh?"

"Ehh.." Rk ya fad'a, kafin Daddy ya kae ga cewa komae wayar sa ta shiga ruri, seya janyo wayar yana kallan me kiran, da sauri ya kalli Rk yace

"Raj je ka, za muyi maganar In Sha Allah, zan yi waya ne yanzun" jinjina kae kawae yayi ba tare da yace komae ba ya mik'e ya fice daga d'akin.


... A d'aya 6angaren kuwa Umma ce ta fito daga d'akin ta, dae_dae lokacin da Yah Sadeeq ke tsaye bakin k'ofar d'akin sa hannun sa dafe da k'ofar d'akin yana sauke numfashi kamar wanda yayi tsere, da sauri Umma ta k'arasa tana kallan sa

"Sadeeq lafiya kuwa?" tayi maganar tana rik'o shi

"Haki kake?" ta fad'a sanda ta gama d'ago shi tana kallan fuskar sa, da sauri ya k'ak'alo murmushi ya wanzar a fuskar sa dan bega sanda ta fito ba se maganar ta kawae yaji, sannan yace bayan ya ida mik'ewa tsaye

"A'ah Umma me kika gani? Kawae gajiya ce" ya fad'a cikin k'arfin hali, seta saki ajiyar zuciya sannan tace

"Toh jeka kwanta ka huta haka nan Uhmm?" jinjina kae yayi kawae yana juyawa ya koma cikin d'akin a hankali, ya baje kan gado yana jin yadda k'irjin sa ke masa wani irin zafi kamar ze rabu da jikin sa. Komawa Umma tayi ta zauna tana d'ora hannun ta akan kuncin ta, lamarin duniyar nan sosae yake bata tsoro musamman a en kwanakin nan da abinda zasu ci yake gagarar su, dae_dae lokacin da Abba yayi sallama cikin gidan, Umma ta mik'e cikin son kawar da damuwar dake shimfid'e kan fuskar ta tace

"Sannu da zuwa"

"Yawwah sannu ka dae" ya fad'a yana son karantar yanayin ta, seta riga shi yin gaba dan bata so ya karanto raunin dake tattare da ita ballantana har shima yaji ya sake karaya

"Wallahi ban samu komae ba" Abba ya fad'a muryar sa a raunane gwanin ban tausayi bayan ya zauna, ajiyar zuciya Umma tayi sannan tace

"Babu komae, Allah ze kawo ko zuwa gobe ne In Sha Allah" seya jinjina kae kana yace

"Ina wannan yaron? Allah yasa yaci wani abun ko dan rashin lafiyar sa" kallan d'akin da Yah Sadeeq ke ciki Umma tayi sannan tace

"Ehh toh yaci zance, amma kasan halin sa ba son cin abincin nan yake ba, yanzu haka ma yayi bacci"

"Bacci kuma? Lafiya dae koh?" Abba yayi tambayar cike da fatan lafiyar ce, ba tare da tunanin komae ba Umma tace

"Ehh lafiya k'alau"

"Toh madallah, bari na kira mana Ayrah" Abba ya fad'a yana fiddo wayar sa daga aljihu, da sauri Umma ta kalle shi tace

"A'ah Abban su kada ka kira ta, bana so ta fahimci ko da akwae wata matsala daga nan wajen mu, kasan halin yarinyar nan" shiru Abba yayi cikin na'am da zancen nata kafin yace

"Toh shikenan.." daga haka yayi shiru yana cigaba da tunanin rayuwar su ta baya data yanzu, shida yake ajiye abincin wata a gidan sa tafi tafi ya koma siya kad'an kad'an, yanzu kuma da yanayin rayuwar ya sake juyawa se gashi wataran a cikin gidan sa an tashi babu ma abincin da za'a ci, ya riga yayi na'am da k'addara, ya yadda da ita kuma yasan Allah ne ya k'addaro masa ita amma ta sanadin Abbu, Abbu yayi musu wani gi6i a rayuwar su da baza su ta6a mantawa ba, ta dalilin sa abubuwa da dama sun faru kuma suna kan faruwa ma, baya tunanin ze iya yafewa Abbu abinda ya masa koda kuwa basu sake had'uwa a duniyar nan ba, yana jin koda yace zeyi hakan ma toh kuwa wani 6angaren nashi baze ta6a yafewa kan sa ba, abinda ma baya tunanin ze faru kenan, wanda shi a gare shi ma baya fatan sake had'uwa da koda me irin halin Abbu ne ballantana kuma shi kan sa Abbun......


Mhiz Innocent...... ✍️



https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd



*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*

*CHAPTER ONE*


✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨


Page 025_026



___Kae tsaye Hostel suka wuce su biyun har lokacin suna tattauna maganar da tak'i k'arewa, dukan su mamaki yak'i sakin su, a haka har suka k'arasa d'akin su Jidda, ko sallama babu wadda ta iya a cikin su saboda yadda suka k'agu su isar da labarin nan, Jidda dake facing k'ofar d'akin tace

"Kae jama'a lafiya kuwa?" bud'a hanci Abeeda ta shiga yi ita a dole ta kawo musu abu me muhimmaci

"Jarida na kawo muku me tsada!" tayi maganar sanda take neman waje ta zauna, sakkowa Ruks tayi daga kan gadon ta sannan ta k'araso tana kallan Abeeda tace

"Kinga kawae ki fad'a mana meya faru?"

"A'ah wallahi nawa zaku siya?" Abeeda ta fad'a tana sake gyara zaman ta, k'aramin tsaki Bahijja ta saki kafin tace

"Don girman Allah ki fad'a mana, haba mana" dariya Abeeda tayi kana ta sakko da jakar ta dake mak'ale a kafad'ar ta ta sanya hannu ta d'akko wayar ta tace lokaci guda kuma tana danna wayar

"Ke kam Bahijja Allah ya shirye ki da son gulma wallahi"

"Oho dae, mu dae fad'a mana kawae"

"A'ah an shiga 3" Abeeda ta fad'a tana d'an bud'e ido ganin da tayi wayar ta ta sam tak'i dannuwa, ga dae ta ta kawo amma kwata kwata tak'i dannuwa

"Kashhh! Shegiyar waya seda ta kwafsa min wallahi" ta fad'a tana dafe kan ta, Bahijja ce ta d'auki wayar itama ta ta6a, ganin da tayi babu abinda ke motsi a wayar ya sanya ta fad'in

"Kinga fad'a mana da baki kawae pls" Khadeejah da ta gama k'uluwa dan takaeci da haushi tace bayan ta ja k'aramin tsaki sannan ta maeda duban ta kan su Bahijja

"Doctor Rk" sunan sa suka ji ta ambata ne ya sanya dukan su kallan ta, Abeeda ta d'ago ba tare da ta kalli Khadeejah ba tace, dan gaba d'aya ita kan ta seda taji ta muzanta da abinda wayar ta mata bayan cika bakin da ta gama yi

"Ina Ayrah ta cikin d'akin kun nan? Toh soyayya suke da Doctor.." dukan su suka cigaba da kallan ta kowannen su na ganin kamar zarewa tayi yasa take wannan maganar, Jidda tayi k'arfin halin fad'in

"Wait mana hajiya! Wane Doctorn kike magana kuma wace Ayrahn kike magana akae?" tayi maganar cikin tsare ta da idanu, murmushi Abeeda ta saki sannan tace

"Dama nasan ba yadda za kuyi ba shiyasa na d'auko muku hoto, amma kada ku damu zan kae a duba min wayar, idan ta gyaru zan dawo na nuna muku hoton dana d'auka na shi shi da ita yau da suka fita.." daga haka ta mik'e ta fice Khadeejah tabi bayan ta, kusan a tare suka bita da kallo kamar wasu dolaye, ta bar su da tunani kala kala, sun kae wajen minti 1 a hakan sannan Bahijja tayi k'arfin halin fad'in bayan ta kalle su

"Kada fa ace da gaske Abeeda take" wani murmushi Ruks tayi sannan tace

"Haba Bahijja kada ki zama shashasha mana, Doctor Rk fa take magana wae yana soyayya da wannan yarinyar? Dududu ma nawa take?" shiru Bahijja tayi na d'an wani lokaci kafin can tace

"Ke wallahi ba tun yau nake zargin yarinyar nan ba, dama na dad'e ina tsoron kada kyawun ta ya rinjaye shi mu shiga 3" se a lokacin Jidda tace

"Hmmm, kuna tunanin kyawu ze rud'i kyakykyawa ne? Bana tunanin haka gaskiya" tayi maganar tana d'an k'ank'ance idanun ta kamar me tunani

"Toh koma dae menene akwae wata a k'asa" Bahijja ta fad'a, kafin wata a cikin su tace komae sallamar Ayrah ta ratso cikin d'akin, babu wanda ya iya amsa mata se bin ta da suka yi da kallo dukan su, kallo irin na tuhuma, ganin irin kallan da suke mata ne ya sanya ta sake had'e kyakykyawar fuskar ta ta k'araso cikin d'akin

"Daga ina kike?" Bahijja tayi k'arfin halin fad'in hakan, kallan ta Ayrah tayi da mamakin jin furucin ta, kafin Bahijja ta gama fahimtar irin kallan da Ayrahn ke mata ta jiyo k'aramar muryar ta tana fad'in

"Toh ina ruwan ki?" ta fad'a tana hararar gefe gami da murgud'a baki sannan tayi wucewar ta kan gadon ta, dukan su suka bita da kallo kafin Ruks ta jinjina kae tana ta6e baki cike da mamakin halin Ayrahn

"Cha66 d'i jam!" Jidda ta fad'a tana cigaba da kallan Ayrah. Ta 6angaren Ayrah kuwa ba ta bi ta kan kowa ba ta zura hijab ta shige toilet, kamar wasu sokaye suka sake bin ta da kallo, yarinyar ta chanja musu sosae, duk da dama tun can sun fahimci miskila ce ta k'in k'arawa, amma yanzu abin yayi gaba sosae, dole su jira Abeeda dan su tabbatar da abinda ta fad'a musu, duk da abin ne akwae wuyar yadda.



... Babu nisa su Ayrah suka yi last paper d'in su ya zamana se komawa gida kenan. A 6angaren Abba kuwa se Allah ya taemake shi lokacin da ze je d'auko Ayrahn ya kar6i albashin sa, dan haka ba k'aramin dad'i yaji ba. Ranar daze tafi ya gama shiryawa cikin manyan kaya na wani yadi, daga d'aki ya fito lokacin Umma na d'akin Yah Sadeeq ta kae masa abinci, ta kalle shi tana murmushi tace

"An fito kenan?" shima murmushin ya maeda mata sannan yace

"Wallahi kuwa zamu wuce" yayi maganar yana d'ora hular sa samfurin zanna bukar akan sa

"Toh Allah ya tsare.."

"Ameen Ameen.. amma kafin nan zan biya nayi wa Baban Zaenab ya me jiki, saboda jinjirar da aka haefa masa da aka sallamo su daga asibiti"

"Toh ayi mata sannu, gobe idan Allah ya kaemu se mu shiga mu duba ta"

"Toh madallah" Abba ya fad'a yana yin gaba, seda ya shiga d'akin Yah Sadeeq dake zaune akan gadon sa yana danna er k'aramar wayar sa, Abba yace

"Sadeeq!"

"Na'am Abba zaka wuce ne?"

"Ehh ba kaci abincin ba" d'an murmushi kad'an yayi sannan yace

"A'ah yanzun dae zan ci, Allah ya dawo daku lafiya Abba"

"Ameen_Ameen" Abban ya fad'a yana mik'ewa ya fice daga d'akin. Kae tsaye seda ya fara zuwa ya gaeda mara lafiyar sannan ya dawo ta hanyar gidan sa dan wucewa titi ya nemi abin hawa, a k'ofar gidan nasu yaga wata mota me kyau, tunda suka gan shi suka sauke glass d'in motar, wani malamin su Ayrah ya sauko ya k'arasa da murmushi kan fuskar sa yace

"Barka da wannan lokacin Alhaji" yayi maganar yana mik'awa Abba hannu, shima Abban mik'a masa hannu yayi suka gaesa yana amsawa da

"Barka dae, ashe kae ne?"

"Wallahi kuwa, ina zuwa haka ne?" Abba yace

"Zan je d'auko Ayrah ne kasan da yake sun gama exam" murmushi malamin nasu yayi sannan yace

"Ahh toh ae dama daga makarantar ne aka aeko mu muzo mu d'auke ka a motar nan mu wuce can makarantar"

"Toh Ikon Allah" Abba ya fad'a yana bin motar da kallo, dan sosae abin ya cigaba da bashi mamaki, tabbas makarantar tasu Ayrah mutane ne masu karamci da sanin ya kamata

"Allah ya saka da alkhaeri" Abba ya fad'a

"Ameen Ameen.. Muje koh?" ya fad'a yana yin gaba sannan Abba ya rufa masa baya zuwa wajen motar, shi malamin ya shiga gaba yayin da Abba ya shiga baya, a haka driver ya soma driving babu dad'ewa suka d'auki hanyar Zaria.



... Ayrah ta gama had'a komae nata ta kammale shi inda ya kamata, wani irin d'oki ne keta d'awaeniya da ita, ji take kamar tayi tsuntsuwa ta gan ta a Kano taga Abban ta, Umman ta da uwa uba kuma Yah Sadeeq d'in ta, gaba d'aya ta kasa sukuni tun d'azun wayar ta ke hannun ta tana jiran kiran Yah Sadeeq ko Abba, Jidda ce kawae a d'akin tun d'azu su Bahijja suka fita ko sallama ba suyi ba, bata k'ara minti 5 ba kuwa sega kiran Abba a wayar ta ta, zumbur ta mik'e dan dama k'iris take jira ta d'aga wayar tana karawa a kunnen ta

"Abba kunzo?" ta fad'a tun kafin Abban yace komae, murmushi Abba yayi kana yace

"Qwarae kuwa ke muke jira yanzu haka" jin da tayi yace suke ya

Please Login or Register in order to submit comment