Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mik'a masa a nutse tace

"Gashi" babu musu Abban ya kar6a kofin ya sha ruwan sosae sannan ya ajiye shi yana sauke ajiyar zuciya

"Don Allah ka dena d'aga hankalin ka haka nan, in dae akan wannan maganar ne nayi mata bayanin dalilin ka na hana ta auren sa" girgiza kae Abba yayi sannan yace bayan yayi murmushi me ciwo

"Ba wannan kad'ae ba, yanzu fitar da nayi wae neman auren Ayrah akazo yi"

"Ikon Allah.. Amma shine ka shiga damuwa haka?" Umma ta fad'a tana sake kallan Abban

"Kin san wanene yazo neman auren nata?" Abba ya fad'a yana sake tuna fuskar Alhaji Maton, girgiza kae kawae Umma tayi sannan Abba yace

"Alhaji Mato!" da mamaki Umma ta cigaba da kallan Abba har wajen second 30 ba tace komae ba se kuma can tace

"Alhaji Mato kuma? D'an sa ko kuma shi kan sa?"

"Shi dae kae.." Inji Abba

"Wae Alhaji Maton dana sani Abban su?"

"Ko shakka babu" Abba ya fad'a a gajarce, jinjina kae Umma ta shiga yi tana sake tuna waye Alhaji Mato, neman auren Ayrah yazo yi? Toh a'ina ma ya san ta?

"Lallae mutanen duniya babu kunya"

"Wallahi kuwa, ya d'auka wani banzan kud'in sa ze rud'e ni ne, in manta wane ne shi, Mutumin da be san k'addara ba, toh na d'auki 'yata kuma na bashi duk abinda ya same shi ae cewa zeyi itace" Abba ya fad'a yana sake jin takaecin Alhaji Maton

"Allah ma ya kyauta Abban su" Umma ta fad'a tana sake jinjina wannan al'amari

"Kamar fa har yanzu bata daena kuka ba, kije ki rarrashe ta mana" Abba ya fad'a bayan ya sake jiyo sheshshek'ar Ayrah daga cikin d'akin ta, Umma ta girgiza kae kana tace

"Bar ta Abban su, bar ta tayi kukan, dole ne dama tayi, babu amfanin rarrashin yanzu dan koma nayi ba denawa za tayi ba, tun d'azun ta kasa furta komae tun bayan dana gama fad'a mata abinda Baban Raj ya aekata mana"

"Allah ya kyauta" shine kawae abinda Abba ya fad'a kawae.




... A 6angaren Rk kuwa koda ya mik'e kae tsaye d'akin Abbu ya wuce yana jin yadda kan sa ya masa wani irin nauyi, haka zalika manyan k'wayar idanun nan nasa ta d'an lumshe kamar me jin bacci, ko sallama be iya yi ba ya fad'a cikin d'akin, dukan su suka kalle shi se dae babu wanda ya tanka masa har ya k'araso ya nemi waje ya zauna yana kallan su su duka, ganin basu da niyyar cewa komae ne ya sanya shi d'aga idanun sa da suka d'an lumshe yace

"Abbu ko zan iya sanin dalilin ku na cewa bazan auri Ayrah ba?" yayi maganar yana jin zafin ta har cikin ran sa, dan ko maganar ma baya son furta ta dan kawae ya zama dole ne yayi ta dan sanin aenahin abinda ke faruwa, Abbu be kalle shi ba dan haka kawae yake jin kamar idan ya bari suka had'a idanu da Rk d'in nan take ze fahimto rashin gaskiyar dake tattare cikin idanun sa, Ummee tace cikin zafi

"Ka tashi ka bamu waje Malam, idan kuma kana so a fad'a maka abinda ya faru ne mutuncin Baban Ayrahn ya zube a wajen ka toh se kayi magana" ta k'arashe maganar tana d'auke kan ta daga kallan sa, da sauri Abbu ya d'aga ido ya kalle ta cikin mamakin jin furucin ta, ita kam tak'i yadda ta kalli kowa dan bata so k'warin gwuiwar data tattaro su tashi a banza, da mamakin dae ya maeda idanun sa kan Ummee sannan murya a cunkushe yace

"Mutunci kuma Ummee?"

"Ehh mana, toh kasan abinda ya aekatawa mahaefin ka kuwa? Ina tunanin ae baka manta sanda mahaefin ka ke k'ark'ashin mahaefin Ayrah ba koh?" ta fad'a tana tsare shi da idanun ta, be iya cewa komae ba kawae ya cigaba da kallan Ummeen da lumsassun idanun sa, Ummee ta gyara zama tace

"Toh duk uban aekin da mahaefin ka keyi masa cewa yake yi ze biya shi k'arshen shekara, amma da yake Abbun ka me hak'uri ne be ta6a nuna gajiyar sa ba koda kuwa a fuska ne, haka mahaefin ka ya duk'ufa yana masa aeki tuk'uru har zuwa sanda k'arshen shekarar tayi, amma kasan me mahaefin nata ya masa daga k'arshe? Guduwa yayi ba tare daya sallami Abbun kud'in aekin wahalar daya dinga masa kwana da kwanaki wata da watanni ba, ina ganin ko dan wannan abun ae yaci ace ka k'auracewa er mutumin daya yaudare ku koh?" Abba ya d'aga kae da sauri ya kalli Ummee da wani irin kallo irin kallan nan na "Meyasa zaki aekata haka?" se ita kuma ta d'auke kae bayan ta jinjina kae har lokacin fuskar ta a had'e, cigaba da kallan ta Rk yayi yana rarrabe maganar data fad'a d'in, shi sam yama kasa gane alk'iblar wannan magana

"Amma kaga da yake Allah ba azzalimin bawan sa bane ae gashi nan yanzu mahaefin ka yayi arzik'in da ba'a so yayi" Ummee ta sake fad'a tana kallan Rk, lumshe idanun sa yayi yana cigaba da sauraron bugun zuciyar sa da yanayin fitar sa ya sauya cikin k'ank'anin lokaci, se a lokacin Abbu ya iya bud'e baki dan yin magana, dan shima ya tabbatar idan ba hakan suka yiwa d'an nasu ba baze ta6a hak'ura ya bar zancen ba, kuma yana ganin lokaci yayi da zasu sake yiwa tufkar hanci dan haka yace

"Saboda haka ka bud'e kunnen ka da kyau kaji, ni na riga na yafewa Abban Sadeeq amma fa bazan iya had'a alak'a dashi ba.." Abbu ya fad'a yana jin maganar tasa wani banbarakwae da ita, ganin har I zuwa lokacin Rk be bud'e idanun sa ba ya sanya shi fad'in

"Dan haka ina me farin cikin sanar da kae na nema maka auren er uwar ka Muneerah.. kuma an baka, yanzu abinda ya rage kawae shine tsaeda lokacin d'aurin aure!" idanun sa ya bud'e da wani irin sauri, wanda saboda jimawar da suka yi a rufe ya sanya suka sake lumshewa suka kuma chanja colour daga aenahin colour d'in su zuwa ja, wani irin kallo yake bin Abbun dashi ido cikin ido wanda shi kan sa Abbun ze iya cewa tunda yake be ta6a ganin Rk d'in ya masa irin wannan kallon ba, saboda ya sani Rk d'in yaro ne me tarbiyya da sanin ya kamata amma yau shine ke kallan sa ido cikin ido duk kuma da Abbun ma shima kallan sa yake amma hakan be sanya shi ya janye k'wayar idanun sa ba, cikin murya me kauri kuma a d'an fusace ya furta bayan ya sake k'ank'ance idanun sa

"Muneerah!!?"



Hhh jama'a ina tunanin kamar yanzu wasan ze soma fa, nasan kan ku ya kulle sosae 🤧🥱 toh babu damuwa ku dae kawae ku cigaba da kasancewa da alk'alami na zaku ji yanda komae ze tafi..🌚😌

Mhiz Innocent.....✍️










https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd



*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*

*CHAPTER ONE*


✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨


Page 029_030



___Kallan sa Abbu har ma da Ummeen suka yi jin yadda yayi maganar kamar ba shi ba haka zalika idanun sa sunyi jawur fuskar sa babu annuri ko kad'an

"Raj!" Abbu ya kira sunan sa ganin har lokacin idanun sa na kan su ne, se a lokacin ya lumshe idanun sa zuciyar sa na wani irin tafasa, haka jijiyoyin kan sa sun firfito saboda tsananin 6acin rae, a hankali ya bud'e idanun nasa da suka sake lumshewa sannan cikin k'arfin hali ya furta

"Abbu Muneerah fa kace"

"Ehh ko nayi sa6o ne bansani ba?" Abbu ya fad'a yana kafe shi da idanun sa, be sake bi takan kowa ba dan a yadda yake jin ran sa na suya komae ze iya faruwa ya mik'e duk da yadda yake jin d'an jiri jiri na d'ibar sa amma haka ya fice daga d'akin, bin sa da kallo dukan su suka yi har ya fice d'in sannan Ummee ta maeda duban ta kan Abbu tace

"Kaga kuwa yanayin yaron nan?" ajiyar zuciya Abbu ya sauke sannan yace

"Nagani mana, 6acin ran sa ko wani abun ba shi ne ze sa mu fasa abinda muka yi niyya ba, ina ganin gwara ma ya kwantar da hankalin sa ya kar6e ta hannu biyu a matsayin mata, dan kuwa babu abinda ze hana mu d'aura musu aure idan ranar da zamu tsayar tazo" jinjina kae Ummee ta shiga yi cike da na'am da zancen Abbun sannan tace

"K'warae kuwa, kuma ina ganin wannan ce kad'ae hanyar da zamu bi dan ya manta da batun waccan yarinyar"

"Ni abinda ke bani mamaki ashe har yanzu Abban Sadeeq na cikin Kano amma bamu ta6a had'uwa ba?" Abbu ya fad'a cike da mamaki, murmushi Ummee tayi kana tace

"Allah yana son ka ae shiyasa hakan bata ta6a kasancewa ba"



.. Kae tsaye d'akin sa ya koma har lokacin zuciyar sa na masa wani irin zafi, ya kwanta kan gadon sa ringingine yana sauke wani zazzafan numfashi daga bakin sa, hannun sa ya d'ora a kan sa tunani barkatae sunk'i barin k'wak'walwar sa, abubuwa na neman cakud'e masa, ya Abbu yake so yayi da rayuwar sa? Tun farkon rayuwar sa be san wani abu wae shi bijirewa umarnin iyaye ba, se dae gashi yau sun zo masa da wani abu da yake ganin ze iya bijire musu a kan sa, Muneerahn da idanun ta ke a bud'e, wayayyiya wadda wayewar ta tayi yawa, gefe guda kuma ga Ayrah, Ayrahn da yake mutuwar so, son da be san iya adadin sa ba, se dae ga wata k'addara na neman giftawa cikin alak'ar su, meyasa Abban ta zece baze aure ta bayan shine yayiwa mahaefin sa laefi? Meyasa ze yanke wannan d'anyen hukuncin? Duk inda d'iyar sa take yasan tana can zuciyar ta a cunkushe da hukuncin da mahaefin ta ya yankewa rayuwar su, seya mik'e zaune yana mantawa da rayuwar wata Muneerah dan kuwa yasan abu ne me matuk'ar wuya auren su ya yiwu dan baya tunanin ko da bashi da wadda yake so ze iya auran Muneerah duk da kasancewar ta er uwar sa ballantana kuma yana da ita. Wayar sa ya d'auka ya sake kiran number Ayrah se dae kamar d'azun yanzun ma abinda take fad'a masa shine wayar a kashe take, jefar da wayar yayi yana runtse idanun sa lokaci guda kuma yana sanya hannayen sa duka biyu ya cusa su cikin sumar kan sa, meya kamata ya aekata yanzun? Tabbas ba dan dare yayi sosae ba babu abinda ze hana shi tashi ya tafi gidan su Ayrahn dan yasan tabbas Abban ta ne ya k'wace mata wayar dan kada tayi magana dashi, gaba d'aya zuciyar sa ta kasa sukuni ta kasa hutawa ko dae_dae da second d'aya ne a cikin daren nan, bacci kuwa beyi ko da gangancin d'aukar sa ba balle kuma ya d'auke san.





... Tun d'azu yake sintiri cikin d'akin ya kasa zama, ran sa a matuk'ar 6ace yake so yake kawae ya tuna mafita akan wannan al'amari, be ta6a tunanin yarinyar nan da yake so er gidan Ibraheem bace, Muttala dake gefen sa shi kan sa ya kasa cewa komae, kawae yayi shiru ne yana kallan Alhaji Mato, ya kae wajen minti 5 a haka sannan ya d'aga kae yana kallan Muttala fuskar sa d'auke da wani shu'umin murmushi yace

"Muttala!"

"Na'am yalla6ae" Muttala ya fad'a yana d'aga kae ya kalle shi, Alhaji Mato ya nemi waje ya zauna kan kujera sannan ya fara magana

"Ayi yadda za'ayi a d'akko min yarinyar nan daga daren yau zuwa safiyar gobe bana son 6ata lokaci.." kallan sa Muttala yayi sannan yace

"Ranka ya dad'e satowa kuma?" shima kallan sa Alhaji Maton yayi kana yace

"K'warae kuwa, zan tafi da ita wani k'auye dana ta6a zuwa aeki, acan zan samu wanda ze d'aura mana aure" jinjina kae Muttala yayi kana yace

"An gama ranka ya dad'e, In Sha Allah zaka ji ni daga yau d'in zuwa gobe" jinjina kae Alhaji Mato yayi yana murmushi a ran sa yana ayyana yadda Ayrahn zata zama mallakin sa.



... Washe gari da safe wajen k'arfe 7 yana sanye cikin k'ananan kaya da suka matuk'ar amshe shi, se dae fuskar sa a cunkushe take kamar wanda akama mutuwa, haka zalika idan ka lura ma da kyau zaka ga har wani 6urmawa idanun sa suka yi, se dae da yake shi d'in na musamman ne hakan ma k'ara masa kyau yayi, wayar sa ya sake d'auka ya sake danna kiran ta a karo na barkatae, daga wannan kiran baya tunanin ze sake kira se dae kawae a tsince shi a k'ofar gidan nasu, cikin sa'a se yaji wayar na ringing, babu shiri ya mik'e tsaye zuciyar sa na cigaba da bugawa tare da sautin yadda ringing d'in ke fita. A 6angaren ta kuwa ita kan ta bata samu ta rintsa ba tun jiyan, data gama kukan ta kawae seta kwanta tayi shiru abin ta tana tunanin halin d'an adam, koda Asuba ma kafin kowa ya fito ita ta riga kowa fitowa tayi alwala tayi Sallah ta koma ta kwanta har lokacin idanun ta suna nan a yadda suke sun yi jawur haka zalika sun kumbura. Tana nan zaunen ta janyo wayar ta ta kunna ta sannan ta shiga contact a hankali ta lalubo number sa zuciyar ta na cigaba da harbawa da k'arfin gaske, tana so tayi fatali da duk wani abu daya ke so ya kawo mata cikas dan haka ta d'an runtse idanun ta sannan ta bud'e ta sake d'ora idanun ta kan jerarriyar special number sa, tana shirin yin blocking number tasa sega kiran sa ya shigo, seta tsaya tana sake k'arewa number kallo kamar me son karanto wani abun, tabbas ya kamata ta isar da abinda ke ran ta, ta fad'a masa babu ita babu shi koda hakan zesa ya rabu da ita kada ya sake gigin koda kiran ta ne, dab da zata tsinke ta d'aga wayar, daga 6angaren sa ya sauke wata 6oyayyiyar ajiyar zuciya sannan yace a hankali kuma a tausashe yana son kawar da duk wani 6acin ran dake d'awaeniya dashi

"Ayrah!" da sauri ta runtse idanun ta tana jin yadda zuciyar ta ke bugawa ta kae wajen second 30 a haka sannan ta bud'e, dan shi har ya fara tunanin ko Abban ne ya d'aga da kan sa seya ji ta tana fad'in

"Kada ka sake kira na, ka manta ka ta6a sanin wata me suna na ko me kama ta ballantana ni, kayi k'ok'ari ka goge duk wani lokaci da muka ta6a kasancewa tare, ka manta da babin rayuwa ta, kada ka sake kira na a waya dan kuwa har abada bazan ta6a auran mutum irin ka ba" daga haka ta katse wayar bata jira yace komae ba ta jefar da wayar a gefen ta tana fashewa da kuka lokaci guda kuma tana tuna yadda ta kawowa Abba Rk a farko amma daga k'arshe su suka koma cikin arzik'in yayin da suka tura su su kuma suka koma cikin k'uncin rayuwa. Tsayawa yayi kamar wani sak'ago, ya sauke wayar daga kunnen sa yana sake k'arewa wayar kallo, anya kuwa ita d'in ce? Anya kuwa Ayrahn sa ce? Menene haka ya faru wanda ya chanja mata ra'ayi haka daga daren jiya zuwa yau d'in? Me akace mata yayi da zata jefe shi da wad'annan kalmomin? Tabbas da tasan yadda kalmomin nata suka jefa shi cikin wani irin yanayi da bata fad'a masa ba, meya same ta haka? Shin ba shine ya kamata ya fad'i hakan ba tunda iyayen tane suka yiwa nasa iyayen laefi ba? Amma beyi hakan ba se ita? Kodae dama bata son sa ne tuntuni? Ko kuwa dae akwae wani 6oyayyen al'amari wanda dukan su basu sani ba? Lallae ya zama dole yasan gaskiyar al'amarin nan, yasan dalilin Ayrahn na jifan sa da wad'annan muggan kalaman, zuciyar sa dake masa wani irin zafi tana kuma harbawa da k'arfi ya danne da hannayen sa yana runtse idanun sa, ya kae wajen minti d'aya a hakan sannan ya bud'e idanun sa yana fesar da iska me zafi daga cikin bakin sa sannan kae tsaye ya fice daga d'akin bayan ya d'auki mukullin motar sa. Da sassarfa ya k'arasa inda motar tasa take ya shiga ya tashe ta da sauri duk da shi d'in ba ma'abocin gudu bane, Abbu da fitowar sa kenan daga parlourn sa yaga tashin motar Rk d'in, mamaki ne ya kama shi sosae dan shi kam yayi tunanin tun yau Rk d'in ze koma asibiti bakin aeki, dan shi indae ta 6angaren sa ne babu lokacin 6atawa, kowanne lokaci baya barin sa ya tafi a banza seya nemo abinda zeyi a cikin lokacin wanda ze saka ya samu kud'i, shiyasa ko lokacin da Rk d'in yaje Zaria yaga baze iya barin sa haka nan babu wani abun daze samu kud'i ba, dan haka shi in dae ta shine tunda jiya ya dawo toh yau ma ya d'ora kan aekin babu wani 6ata lokaci

"Toh ina ze je haka?" Abbu ya tambayi kan sa, ganin dae babu wanda ze amsa masa tambayar ne ya sanya shi cigaba da tafiya a ran sa yana cigaba da tunanin inda Rk d'in zeje.


... Driving yake yi amma har lokacin tunani yak'i barin ruhi da k'wak'walwar sa, shi likita ne yasan illar da tunani kan iya haefarwa dan ya kan sha bawa mutane shawara akan hakan, amma a wannan karon shi kan sa ya kasa hana kan sa, se yanzu ya fahimci ashe idan k'wak'walwa na son yin tunani ba mutum ke tsarawa kan sa yin tunanin ba ita da kan ta take yin tunanin kuma babu yadda ka isa kayi da ita. A haka dae har ya k'arasa unguwar ta su yana tuna kwatancen data masa, a d'an nesa kad'an ya tsaya da gidan yana kallan cikin layin da babu kowa kasancewar safiya ce dan kuwa har lokacin ko 8 ba tayi ba, seya d'aga lumsassun idanun sa dake d'auke da bacci ya dubi gidan a ran sa yana sak'a tabbas nan d'in ne in dae yabi kwatancen data masa dae_dae, wayar sa ya janyo da take ajje kan kujerar kusa dashi ya danno number ta cike da fatan ta d'aga wayar, se dae addu'ar sa bata kar6u ba dan kuwa har ta gama ringing d'in bata d'auka ba tana kuma jin wayar na ringing ta san me kiran shiyasa tak'i kula wayar, wani kiran ne ya sake shigowa seta mik'e daga kwanciyar da take tana ganin blocking d'in da tayi niyyar yi tun d'azun shine kawae mafitar da tasan idan tayi ze dena kiran ta, kafin takae ga aekata abinda tayi niyya Umma ta d'aga labulen d'akin ta lek'o

"Ayrah ki fito ki samu wani abun ki ci" se ta d'aga kae da sauri sannan ta furta

"Toh.." kawae, itama Umman bata takura ba dan tana so ne ta bari ta gama kukan ta sannan ta rarrashe ta, idan ba haka ba tasan yanzu tunzura ta kawae zata yi, Umman na fita Ayrah ta maeda kallan ta kan wayar dae_dae lokacin da wani sak'o ya shigo cikin wayar, seta dakata ta shiga cikin sak'on, gajeren sak'o ne daga number Rk a hankali ta shiga karantawa

"Don Allah ki fito ina k'ofar gidan ku, inaso naji tabbacin maganar dake fitowa daga cikin bakin ki, ina so na tabbatar da abinda kunnuwa na suke ji" fuskar ta a matuk'ar tamke haka zalika ran ta ya sake 6aci, tana ga lokaci yayi da zata kira shi da sunan dake ta yawo a cikin k'wak'walwar ta koda hakan zesa ya fahimci ta gane wanene shi da mahaefin sa, ko kuwa ya d'auka saboda son da take masa zata iya fatali da umarnin iyayen ta? Ko kuwa me yake nufi da ita?

"Butulu" shine sunan dake ta yawo a k'wak'walwar ta, wayar ta ta ta d'auka ta danna number sa a blocking sannan ta jefar da ita gefe ta mik'e tana sanye cikin doguwar rigar atamfa ta zari hijab ta saka sannan ta lek'o tsakar gidan tana hange, babu kowa a tsakar gidan taji dad'in hakan dan bata so ta sake 6atawa Abba ko Umma rae daga dawowar ta jiya bayan 6acin ran data saka musu a jiyan, a hankali ta shiga takawa cikin tsakar gidan har zuwa sanda ta fice daga cikin gidan...


... Wanda ke driving d'in ya kalli Muttala yace

"Nifa na gaji wallahi, tun jiya muke a wajen nan amma har yanzu banga alamar zata fito ba" tsaki Muttala yaja kana yace

"Gaggawar ta menene? Wallahi idan ta nine bank'i mu sake kwana cikin motar nan ba tunda dae babu wanda ya ganmu har yanzun" Muttala ya fad'a har lokacin idanun sa na kan k'ofar gidan su Ayrah.. A dae_dae lokacin ne Ayrah ta fito daga cikin gidan, a hankali ta shiga bud'e manyan idanun ta dan hango inda motar sa take. A lokacin ne shi kuma kiran Abbu ya shigo wayar sa, seya d'auki wayar yana karawa a kunnen sa idanun sa a lumshe dan yanzu kuma be san da wanne Abbun yazo ba gashi kuma rok'on da yayi wa Ayrah baya tunanin taji ta kar6a zata fito, se abin ya sake masa yawa, daga can 6angaren Abbu yace

"Ka shiga asibitin ne?" shiru yayi na d'an wani lokaci kafin a hankali ya bud'e bakin sa bayan ya kae hannu ya shafa kwantaccen sajen dake kwance luff luff akan fuskar sa

"Abbu ban shiga ba tukunna" shiru Abbu yayi yana sake karanto yanayin Rk d'in daga cikin muryar sa, yace a hankali

"Ko dae akan maganar dana maka jiya ce?" shiru yayi dan ko ya bud'e bakin sama be san abinda zece ba, Abbu yace

"Toh ka bud'e kunnen ka da kyau kaji, in dae akan maganar nan ce ka kwantar da hankalin ka kamar an riga an d'aura muku aure ne da Muneerah, dan haka ina ganin ka ajje komae a gefe ka koma bakin aekin ka" kafin yace komae Abbun ya katse wayar, seya jefar da wayar yana sake jin yadda yanayin nasa yake sake ta'azzara, abubuwa na neman yiwa zuciya da k'wak'walwar sa yawa. A hankali ta cigaba da takawa har lokacin fuskar ta babu walwala manyan fararen idanun nan nata sun yi zuru zuru kamar mara lafiya, da sauri wanda ke driving cikin motar ya bud'e k'ofa ya fita yayin da Muttala ya koma mazaunin driver, seda ya kalli cikin layin ya tabbatar babu kowa sannan ya k'arasa inda Ayrah take, ita sam hankalin ta be kae kan sa ba yana kan motar Rk da take kalla dan tabbatar da tasan ce, beyi wata wata ba ya matsa bayan ta ya shak'a mata wani abu dake jikin handkerchief d'in hannun sa, lumshe idanun ta tayi tana jin wani irin yanayi cikin kan ta kafin a hankali ta kae hannun ta tana shirin dafe kan ta, take wani jiri ya d'ebe ta cikin sakannin da basu wuce 10 ba ta fice a hayyacin ta se kawae tayi baya zata fad'i mutumin ya saka hannun sa ya tare ta ya jata zuwa cikin motar har lokacin yana d'an juyawa bayan sa dan tabbatar da babu wanda ya gan shi, dae_dae lokacin da yake k'ok'arin k'arasa shigewa da ita cikin motar Rk ya bud'e idanun sa daga lumshe sun da yayi tun d'azun, kamar ance ya kalli wajen se kawae ya hange ta jikin wani mutum yana cusa ta cikin mota, seya sake rufe idon ya bud'e dan tabbatar da abinda ya gani d'in gaskiya ne ko kuwa idanun sa ke masa gizo, cikin wani irin zafin nama ya tura k'ofar side d'in da yake yana shirin fita zuciyar sa na wani irin zafi tana cigaba da harbawa kamar zata faso k'irjin sa, Muttala yaja motar da k'arfin gaske tun kafin ma mutumin ya gama saka Ayrahn cikin motar, seya koma da sauri zuciyar sa na bugawa yama kasa tunanin komae kawae ya figi motar da wani irin gudun da tunda yake ze iya cewa be ta6a yin irin sa ba, sosae su Muttala suke gudu kamar zasu tashi sama yayin da shima ya cigaba da bin su, kawae burin sa ya san inda zasu je, ina zasu kae ta? Me zasu mata? Meyasa suka d'auke ta? Kwata kwata tunanin sa be kae ya kira police ya sanar dasu ba kawae shi dae burin sa ya cim masu. Sosae suka cigaba da tafiya kuma inda Allah ya taemake su

Please Login or Register in order to submit comment