Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cike da tsoro, gyara mata kwanciyar daya dake yi shine ya tabbatar mata da ba yanzu ne yake kissing d'in nata ba, duk jikin ta a matuk'ar sanyaye ta hak'ura da k'ok'arin tashin ta koma kawae tayi shiru se dae har lokacin akwae ragowar k'walla manne cikin manyan idanun ta. A hankali kuma taji wani irin bacci na sakad'ar ta, so take ya cika ta ta mik'e amma yak'i sakin ta dan haka kawae ta hak'ura ta bada kae bori ya hau, babu dad'ewa bacci me dad'i ya d'auke ta, seta shiga sauke ajiyar zuciya a nutse, se a lokacin ya sauke ajiyar zuciya kamin a hankali ya furta

"Rigimammiyar mata ta.." k'arar da wayar sa tayi ne ya sanya shi kallan inda take, be san me kiran nasa ba, kamar ze share se kuma ya kalli Ayrahn dake baccin ta hankali kwance kamar bata da damuwa, ya lumshe idanun sa wata matsananciyar k'aunar ta na sake ratsa shi, cikin dabara yanda ba zata farka ba ya shiga zame ta daga jikin sa har zuwa sanda ya k'arasa zame ta gaba d'aya, ya kwantar da ita kan gadon sannan ya lullu6a mata blanket kana ya sake kallan ta, ji yake kamar ya sake kissing nata se dae baya so ya 6allowa kan sa ruwa dan haka kawae ya k'arasa inda wayar tasa take dae_dae lokacin da ta sake yin ringing

"Muneerah!" shine dae sunan daya sake bayyana akan screen d'in, tsaki yaja akan la66an sa dan har ga Allah ya manta da wata Muneerah musamman a yanzu da yake tare da Ayrah

"Itama matar ka ce, at least yaci ace ka san a wane hali take" shine abinda zuciyar sa ta raya masa, ya sake jan wani gajeran tsakin yana maeda duban sa kan er rigimar tasa, yanzu taya ze fita ya bar ta cikin d'akin nan ita kad'ae? Idan kuma ya fita kafin ta tashi in ta tashi taga baya nan fa meze faru?


Mhiz Innocent.....✍️



https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd


*CHAPTER TWO*

*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*



Page 039



___A hankali ya maeda duban sa kan gadon yana kallan ta duk da fuskar ta ce kad'ae ake iya gani gaba d'aya jikin ta na lullu6e ne da blanket, ajiye wayar yayi kan kujerar kafin ya k'arasa a nutse zuwa wajen gadon, hannu ya saka ya janyo side drawer dake gefe ya matso da ita dab da gadon sannan ya zauna akae, murmushi ne ya su6uce a kyakykyawar fuskar sa sanda yaga tayi juyi seya kasance ta koma kallan inda ya zauna d'in, a hankali ya d'an lumshe idanun sa sannan ya kafe kyakykyawar fuskar ta da kallo, sosae kyawun ta ya sake bayyana da tana baccin, dogayen lashes d'in ta sun kwanta luff luff akan idanun ta, ya shafe wajen minti 3 a haka yana kallan nata sannan ya sake lumshe idanun sa kana ya kwantar da kan sa a gefen gadon. A hankali ya k'arasa kan gadon sannan ya d'an rank'wafa kad'an kana ya shiga hura mata sassanyar iska daga cikin bakin sa akan fuskar ta, dan baya so yayi wani abun daze zama takura a gare ta, a nutse ta shiga bud'e manyan idanun ta sanda taji iskar akan fuskar ta, seda ta gama bud'e idanun nata dae_dae lokacin da ta sauke idanun na ta akan sa, da sauri ta tashi zaune ganin yadda fuskar sa take a dab da ta ta, seda ta tashin sannan ya matsa daga kan gadon, ita kuma taja bargon da take ciki ta sake rufe jikin ta gaba d'aya, murmushin gefen baki ya saki lokaci d'aya yana kae hannun sa kan kwantacciyar sumar kan sa ya shafa, ya lumshe idanun sa yana taune gefen lips d'in sa na k'asa

"La'asar tayi.." ya fad'a a hankali bayan ya maeda duban sa kan ta

"D'an mik'o min hijab d'ina" ta fad'a ba tare data kalle shi ba tana d'an tura baki, bin inda hijab d'in nata yake yayi da kallo, seya saka hannun sa a hankali ya d'auka sannan ya jefa shi kan kujerar daya ajje wayar sa, itama hijab d'in tabi da kallo kafin ta dawo da kallan ta kan sa idanun ta sunyi rau rau

"Don Allah ka bani" ta fad'a har lokacin bata sakko daga kan gadon ba kuma bata cika blanket d'in data rik'e ba, seda ya lumshe ido sannan ya sake zuba mata idanun sa kana yace

"Ko inzo in sauko dake ne?" yayi maganar calmly, harara ta jefa masa kamar idanun ta zasu fad'o har seda hakan ya sanya shi yin murmushi me k'ayatarwa, kamar zata yi kuka tace

"Ni dae Allah ka bani hijab d'ina sallah fa zan yi" seda ya soma takawa kamar ze hau kan gadon sannan yace

"Bari kiga abinda za'ayi.." ya fad'a kamar ze d'aga ta, babu shiri ta saki bargon da sauri ta dirga ta d'ayan 6angaren ta fad'a toilet bayan ta sake murgud'a baki, lumshe idanun sa yayi bayan ta shige band'akin, seya samu kan sa da tuna yadda yaga rigar jikin ta tabi jikin ta ta kwanta sosae ta matuk'ar yi mata kyau, bud'e idanun sa yayi kamin ya fesar da iska daga bakin sa kana ya fice daga d'akin. Be dad'e ba ya dawo dan yana idar da sallah ya taho, sanda ya dawo yayi dae_dae da lokacin da take k'ok'arin fitowa daga cikin toilet d'in, akan sa idanun ta ya fara sauka, da sauri tayi maza taja k'ofar ta koma ciki tana ji kamar ta fasa ihu, kallan inda hijab d'in ta ke ajiye yayi da alama bata d'auka ba, yayi wani murmushi kana ya d'auki hijab d'in ya k'arasa bakin toilet d'in, bece komae ba yayi shiru yana jiran jin ko za tace wani abu, kamar kuwa tasan jira yake se yaji tace cikin er k'aramar muryar ta

"D'an ban hijab d'in nan don girman Allah" ta fad'a a shagwa6e tana kwa6e fuska

"Gashi" ya fad'a bayan ya matsa jikin k'ofar sosae, seda ta d'an yi jimm kad'an kafin a hankali ta saka hannun ta kan hannun k'ofar ta d'an bud'e ta kad'an, shi kuma ya mik'a mata hijab d'in, seda ta sauke ajiyar zuciya sannan ta saka hannu ta kar6a, kafin ta gama kar6ar ya saka hannun sa d'aya ya tura k'ofar se ganin shi tayi cikin toilet d'in, k'ara ta saki lokaci d'aya tana wara manyan idanun ta, ganin sa da tayi cikin toilet d'in, cikin rashin sanin abin yi kawae ta rungume shi gudun kada ya ganta a yadda take d'aure da d'an k'aramin towel tana fashewa da kuka kawae, wata k'atuwar ajiyar zuciya ya sauke sanda ta fad'a jikin sa d'in, seda ya tafi hutun tak'aetaccen lokaci sannan ya fizgo numfashin sa kana ya sake lumshe idanun sa, a hankali ya fesar da iska daga bakin sa yana shak'ar daddadan k'amshin dake tashi daga jikin ta wanda ya had'u da k'amshin sabulu suka had'u suke bada wani sassanyan k'amshi me dad'in shak'a, hannun sa ya d'aga da nufin d'orawa akan farin gadon bayan ta dan bata damar sake kwanciya cikin jikin sa bayan uwar rungumar data masa, seya jiyo muryar ta cikin rauni tana furta

"Ka fita don Allah, ka fita don Allah.." abinda take fad'a kenan ilahirin jikin ta na rawa, bugun da zuciyar ta keyi yana iya jiyo shi saboda yadda jikin ta ke manne da na shi, ba k'aramin gudu yake yi ba, wanda ya had'u da nasa bugun zuciyar da ya chanja tun lokacin da ta rungume shi, sheshshek'ar data cigaba dayi har kuma lokacin tak'i sakin sa kamar ma sake shigewa cikin jikin nasa take yi duk dan kada ya gan ta shine ya sanya shi sakin ajiyar zuciya sannan yace cikin wata shak'ak'k'iyar murya kamar ba tasa ba

"Zan fita.." ya fad'a yana k'ok'arin kae hannun sa kan ta, se kuma ya dakata saboda yanda yaji jikin sa ya sake yin wani mugun sanyi, se kawae yace cikin d'an k'arfin hali

"Toh cika ni Madam" se a lokacin ta d'an rage kaefin rungumar data masa, amma duk da haka bata sake shi ba

"Is ohk, na kulle ido na, bazan kalle ki ba shikenan?"

"Tsakanin ka dawa?" ta fad'a cike da sakarci, duk da yanda rungumar data masa ta shige shi sosae har ta sanyaya duk wata ga6a ta jikin sa hakan be hana shi yin murmushi ba sannan ya furta

"Da Allah" ya fad'a yana kulle idanun nasa da gaske, se a lokacin ta sake shi a hankali sannan ta mik'e tana kallan fuskar sa, da gasken idanun sa a rufe yake hakan ne ya sanya ta saurin saka hijab d'in ta har lokacin jikin ta na wani irin rawa dae_dae lokacin da shi kuma ya fice daga band'akin, bin sa tayi da harara kamin tace kamar zata yi kuka

"Wannan ae iskanci ne" ta fad'a tana murgud'a baki gami da sake harara kamar yana gaban ta. Ajiyar zuciya ya sauke sanda ya fito daga toilet d'in ya nemi waje ya zauna idanun sa a kulle har lokacin jikin sa a sanyaye, yana nan zaune ta fito kamar wata munafuka se sussunne kae take, seda ta saci kallan sa sannan ta k'arasa wajen kayan ta ta fidda wata riga kana ta koma toilet d'in ta saka sannan ta fito, babu 6ata lokaci ta tayar da sallah, har lokacin data idar idanun sa na a rufe ne, seta sake kallan sa kafin ta d'auke kae kawae.


.. Wajen k'arfe 9pm ne, yana zaune kan kujerar d'akin yayin da take zaune akan gado tayi shiru kamar me tunanin wani abu, so yake ya kawar da wannan bak'untar data shiga tsakanin sa da Ayrahn amma kuma yanzu yana cikin wata matsalar ne yasan ba lallae ta saki jikin ta a yanzu ba kam, amma duk da haka ya gaji da ganin ta shiru haka nan, ba kuma yaso ya tuna mata da maganar da zata 6ata mata rae amma yanzu kuma ya zama dole ya mata d'in in dae yana son zaman lafiya, gwara ya fara gamawa da wannan matsalar kafin yazo yaji da waccan d'in. A hankali ya mik'e ya k'arasa kan gadon gefen ta, ya d'aga kae ya saci kallan ta yadda take zaune kan ta akan gwuiwar ta tayi shiru, hannu ya mik'a a nutse ya kamo tattausan hannun ta cikin nasa, janyewa ta soma yi, shi kuma ya sake rik'e hannun gam lokaci d'aya yana girgiza mata kae fuskar sa a narke, kallan sa tayi kafin ta d'auke kan ta tana jin kamar tayi kuka idan ta tuna wani abun

"Ayrah don Allah kiyi hak'uri kin ji? Ki dena fushi da ni haka nan, yana ta6a zuciya ta, kin san yadda nake k'aunar ki, bana son ganin ki cikin damuwa, bansan da wane baki zan yi amfani wajen baki hak'uri ba, amma ni dae don Allah ki yafe min ki dena fushi da ni, ina so ne ki koma asalin Ayrahn ki, me so na, me yawan fara'a a gare ni, wadda bata son gani na cikin damuwa.." ya k'arasa maganar yana lumshe idanu, d'aga narkakkun idanun ta tayi ta kalle shi k'irjin ta na d'an bugawa, se taji tausayin sa ya kamata, ita kan ta zata so ta koma waccan Ayrahn amma bata san yanda zata yi hakan ba

"Na dad'e banga murmushin ki ba, pls ki min ko da hakan ze faranta min.." yayi maganar har lokacin muryar sa a k'asa yana d'an murza hannun ta dake cikin nasa, bata san sanda tayi murmushin ba wanda ya taho da wani hawaye, seta saka hannu ta d'auke hawayen tana jan ajiyar zuciya, k'awataccen murmushi ne ya wanzu akan kyakykyawar fuskar sa kana yace

"Dats my beauty.." seda ya d'an yi shiru yana tunanin ta inda ze fara mata magana, baya so ya sake 6ata mata mood amma wannan lokacin ne ya dace yayi maganar dan haka yace

"Babe kina so ranar lahira na tashi da 6ari d'aya a shanye?" cikin rashin fahimta ta d'aga dara_daran idanun ta ta kalle shi, seda ya lumshe idanun sa saboda yanda yaji kallan nata har cikin jikin sa kana yace bayan ya jinjina kan sa

"Kiyi hak'uri inaso naje wajen Muneerah in duba halin da take ciki" ya fad'a yana kallan cikin idanun ta, duk da yanda idanun nasu ke cikin na juna hakan be sanya ta janye nata ba

"Muneerah!" ta maemaeta akan la66an ta cike da rashin fahimta

"Ya ilahee kasa kada ta d'auka da zafi" ya fad'a cikin zuciyar sa har lokacin yana kallan ta

"Matar da aka aura min yau nake nufi" cikin sauri ta fizge hannun ta daga cikin nasa wata k'walla na taruwa cikin manyan fararan idanun ta, ba ita taso kukan ya fito ba kawae seta fara kuka wani irin zafi cikin k'irjin ta, runtse idanun sa yayi yana jin babu dad'i har cikin ran sa, a hankali ya saka hannu ya jata cikin jikin sa, babu musu yanzu kam ta cigaba da rera kukan ta a hankali, seda tayi me isar ta sannan ta koma sauke ajiyar zuciya, se a lokacin ya cigaba da magana

"Kiyi hak'uri..." ya fad'a, shiru tayi tana sauraron bugun zuciyar su daya had'u waje d'aya, ita wani lokacin har mamaki yake bata musamman yadda kalmar hak'uri bata masa wahala a bakin sa kamar ba Rk ba, cikin raunanniyar murya tace

"Ka tafi toh" ta fad'a bayan ta tashi daga jikin nasa, shiru yayi yana bin ta da kallo cike da tausayawa

"Kin amince naje?" seta jinjina kae tana saka hannu ta d'auke hawayen da suka k'i tsaya mata

"I love u.." ya fad'a a nutse da tattausar muryar sa, bata iya cewa komae ba se bugun zuciyar ta daya k'aru, shikenan itama waccan d'in k'ila haka zeje ya fad'a mata yana son ta, wani kukan taji ya sake taho mata, se tayi saurin jan ajiyar zuciya dan bata so kukan ya fito, cigaba yayi da bin ta da kallo kamar me son gano wani abu, yana son watsa ruwa a jikin sa amma baya son ta zargi wani abun a ran ta dan haka kawae ya mik'e ya d'auki wayar sa ya fice daga cikin d'akin jikin sa a matuk'ar sanyaye lokaci d'aya kuma 6acin rae na taso masa daya tuna wannan k'ak'ababben aure da aka lak'aba masa. Bin sa tayi da kallo sanda ya fice daga d'akin zuciyar ta na sake karyewa, bata ta6a tunanin zata ta6a raba Raj ita da wata ba, se gashi k'addara tasa hakan ta faru, a hankali ta lumshe idanun ta tana bawa kukan daya taho mata damar fitowa ko zata samu sassaucin abinda take ji a cikin zuciyar ta.


... Kae tsaye gidan nasa ya wuce har lokacin fuskar sa a cunkushe, sosae yake jin takaecin zuwa gidan da zeyi wajen wata matar, amma haka dae ya cije kawae ya tafi gidan. Gida ne me girma wanda ke d'auke da part 2, nashi da kuma nata, gidan ya ginu ya had'u kuma iya had'uwa, yana parking motar ya sauka, baya son 6ata lokaci dan haka ya d'auki ledar daya shigo da ita kae tsaye ya wuce part d'in da yasan anan ze same ta. Bin parlourn yayi da kallo wanda shima an zuba kaya kamar babu gobe, be bi takan komae ba ya k'arasa bedroom, knocking ya fara yi bayan ya dakata, tana zaune kan gado sanye cikin lifaya, tun d'azu dama ta k'agu yazo hak'uri kawae take yi, dan haka tana da tabbacin shine

"A bud'e take" ta fad'a bayan ta bud'e fuskar ta dake rufe, wadda itace ta fara rufe ta se taga ba zata iya ba kawae ta bud'e ta, kallan sa tayi sanda ya shigo cikin d'akin tana jin wani irin farin ciki musamman idan ta tuna yau d'in ta mallake shi bayan duk wannan gwagwarmayar da ta sha. A nutse ya k'araso cikin d'akin har lokacin be kalli inda take ba, seda ya ajje ledar sannan ya nemi gefen k'aramar kujerar dake cikin d'akin, wajen minti 1 bece komae ba, ita kuma ji take kamar ta tashi ta rungume shi dan dae ta tuna fad'an da tasha a wajen Aunties d'in ta ne da babu abinda ze hanata aekata hakan, shiyasa yanzun ma kamar yadda suka umarce ta tayi shiru tana saurarar sa

"Kina lafiya?" ya fad'a bayan ya daddanne zuciyar sa, murmushi ta saki jin tambayar tasa me nuni da kulawa ga wanda ake tambaya, hakan ne ya sanya ta karyar da kae sannan tace

"Lafiya k'alau Baby, se dae gajiyar biki kuma!"

"Ga abinci nan idan kina buk'ata, akwae komae a kitchen shima in kina buk'ata, bayan nan akwae wani abun da kike buk'ata?" ba tare da tunanin komae ba tace

"A'ah Baby.."

"Ohk" ya fad'a yana mik'ewa a nutse ya fice daga d'akin. Bin sa tayi da kallo sannan ta kalli ledar daya shigo da ita, wani murmushi ya su6uce mata data tuna yau d'in ita da Rk zasu zama abu d'aya. Tana zaune kan gadon ta cigaba da jiran shigowar sa, har wajen minti 30, awa 1, bata sare ba har lokacin, se dae gajiyar zaman da tayi, da kuma wannan shegiyar lifayar dake jikin ta, dan haka kawae ta sauko daga kan gadon ta ware lifayar gaba d'aya ta jefa ta gefe sannan ta koma ta zauna tana cigaba da jiran sa, tun tana cigaba da saka ran shigowar sa har ta sare, a lokacin ne kuma ta fara tunanin ko dae ta bishi d'akin na sa? Maganar Aunties d'in nata suka sake dawo da ita hayyacin ta seta koma tayi zaman da6aro kan gadon tana jin kamar ta rusa ihu, ita kam da sun bar ta da yanzun bin sa d'akin nasa za tayi ita babu abinda ya dame ta, basu san halin Rk bane, ita data san shi ita ta san shi, tun tana kokawa da baccin da ke ta kawo mata hari har ta bada kae bori ya hau kawae ta shiga sharara baccin ta.

.. Shi kuwa 6angaren sa yana komawa d'aki wanka kawae yayi ya fito ya shirya cikin k'ananan kaya sannan yabi lafiyar gado, gaba d'aya tunanin sa da hankalin sa na kan Ayrah ne daya baro ita kad'ae cikin d'akin, dan ma dae daga waje ya kulle ta ne in case, saboda akwae komae na buk'ata a cikin d'akin, a hankali ya lumshe idanun sa zuciyar sa fall da tunanin Ayrahn barkatae. Muneerah kuwa ba ita ta farka ba se wajen k'arfe 8 na safe, da sauri ta mik'e mamaki ya sake kamata ganin har lokacin babu shi cikin d'akin, kae tsaye wanka ta fad'a tayi sannan ta fito tayi Sallahr asuba, dan dama tun a gida ta riga ta saba bata tashi Sallahr asuba se 8 wani lokacin ma har fin 8 d'in ma, duk da kasancewar safiya ce hakan be hana ta d'aukar nighties ta saka ba, wata shu'umar riga ce irin me net d'in nan kuma me bin jiki, gaba d'aya undies d'in ta ana ganin su saboda yanda rigar take me raga raga kamar gidan sauro kuma dududu da kad'an ta wuce gwuiwa, seda ta sake gyara fuskar ta sannan ta fito daga d'akin zuwa part d'in sa. Tura k'ofar tayi cikin sa'a ta jita a bud'e seta k'arasa fuskar ta d'auke da murmushi ta tura kan ta cikin d'akin, wani sassanyan k'amshi ne ya ziyarci hancin ta wanda ya tilasta mata lumshe k'ananun idanun ta kana ta cigaba da tafiya bayan ta chanja tafiya ta d'an soma jijjiga jikin ta da yanzun babu laefi akwae su saboda uban magungunan data dinga d'irkawa cikin ta. Fitowar sa kenan daga wanka d'aure da madaedaecin towel, hannun sa rik'e da comb yana taje sumar kan sa ta tura k'ofar d'akin, idanun ta suka sauka akan bayan sa da take iya hange, wata k'atuwar ajiyar zuciya ta sauke saboda yanda taji gaba d'aya jikin ta ya amsa da ganin sa da tayi a haka, dan kuwa tunda take bata ta6a ganin sa a haka ba, da sauri ya juyo dan be ta6a tunanin rashin kunyar ta ta zata bar ta ta shigo d'akin sa washe garin ranar da aka kawo ta ba, amma ga mamakin sa se yaga ita d'in ce, ajje comb d'in hannun sa yayi bayan ya d'auke idanun sa daga kan ta sanda ta sakar masa wani tattausan murmushi, sosae k'irar jikin sa ta tafi da imanin ta, a yau da take ganin faffad'an k'irjin sa a bud'e dake d'auke da wasu kwantattun bak'ak'en gashi masu kyawun gani, kawae seta k'arasa ba tayi wata wata ba ta rungume shi ta baya tana sakin ajiyar zuciya, tsaki ya saki cikin ran sa wani 6acin ran na taso masa, se yayi k'ok'arin danne shi kada 6acin rae yasa yayi abinda be kamata ba

"Baby meyasa jiya daga fitar ka baka dawo ba? Nayi kewar ka Baby sosae, na d'auka za muyi spending night d'in mu ne cikin farin ciki, at least dae ka taya ni farin cikin wannan ranar dana dad'e ina jira" iska ya fesar daga bakin sa kafin ya d'an kautar da kan sa ya shak'i iska dan abinda ke tashi daga jikin ta sam be masa ba, dan in dae ba hancin sa ke masa k'arya ba wani d'an k'arni k'arni yaji tana yi, abinda dae be sani ba shine itace keyi ko kuma turare ta saka me k'arni haka? Me tayar da zuciya!? hakan ba mamaki bane dan kuwa bleaching d'in da take yi shahararre ne, tayi d'au da ita, kae seka rantse dama can farar ce ba bak'a ba, hannu d'aya ya saka duk da yadda yaji tsigar jikin sa na wani irin tashi ya janye ta daga jikin sa kana ya matsa gefe ya d'auki wata tattausar brown d'in jallabiyya ya d'ora akan towel d'in sannan ya zame shi ta k'asa, seta kalle shi duk da yadda ta d'an ji babu dad'i amma hakan be hanata furta

"Haba Baby ka bari mana inji d'umin jikin ka don Allah" da sauri ya d'aga idanun sa ya kalle ta cike da mamakin kalaman bakin ta, se kuma ya d'auke yana neman kan gadon ya zauna ya d'an kishingid'a da pillown dake kan gadon sannan ya furta har lokacin idanun sa a lumshe

"Ina kwana?" bak'in bakin ta ta tura gaba sannan tace

"Kae Baby, toh lafiya k'alau.." ta fad'a tana k'arasawa kan gadon, a hankali ta haye kae ba tayi wata wata ba ta fad'a jikin sa tana rik'o shi sosae kamar zata koma cikin sa tana sake shigar da jikin ta cikin jikin sa, da wani irin sauri ya bud'e idanun sa sanda yaji ta kane_kane cikin jikin sa, hannun sa duka biyun ya saka ya janye ta daga jikin sa kafin ya mik'e yana kallan yanda take wani sake gaggantsarewa tana kuma narke fuska ita a lallae dole shagwa6a take yi, shi sam bema lura da abinda take yi ba, dan idanun sa na kan fuskar ta ne yace fuskar sa a tamke

"Ke wae er kunyar nan irin ta mata baki da ita ne?" ya fad'a ran sa a matuk'ar 6ace cike da haushin wannan banzan halin na ta....


Mhiz Innocent......✍️

https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd


*CHAPTER TWO*

*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*



Page 040


___Yanayin ta sam be nuna ta damu ko taji haushi ko zafin maganar daya fad'a mata ba, se dae ta kama kan ta bata sake gigin ta6a jikin sa ba, seda ta sauko daga kan gadon sannan ta sake basar da maganar daya fad'a mata kana tace

"Amma dae ko ba komae ka fad'a min dalilin daya hana ka dawowa a jiyan koh?" k'aramin tsaki yaja har lokacin be kalle ta ba, baya jin ze k'ara koda rabin awa ne a cikin gidan nan da wannan matar, dan tabbas idan ta cigaba da wad'annan halayen na ta zuciya na iya tunzura shi ya fad'a mata maganar da ba zata ta6a mantawa da ita ba har abada

"Zaki iya fita in shirya ko kuma na bar miki d'akin?" yayi maganar yana fiddo da wasu kayan daga cikin wardrobe, seda ta d'an sake gantsaro jikin ta kafin ta matso gaban sa tace

"Bari na fita Baby, amma don Allah ka dawo da wuri.." shiru yayi na en wasu sakanni kafin yace sanda ya juya ya ajje kayan hannun sa kan gado

"Sorry.. Ba'a nan zan kwana ba.." da mamaki take kallan kyakykyawar fuskar sa da kullum take gani take kamar ana k'ara masa kyau ne

"Ba'a nan zaka kwana ba kuma Baby?"

Please Login or Register in order to submit comment